da lokacin shi yayi ba, damuwata sauran guminmu, yasake yayi wasa da shi se na yi wasa da zaman lafiyarshi, sannan kowa ya kama gabanshi, kunsanabinda ake kira da nafsi-nafsi?" Dariya Walki ya saki tare da faɗin "haba Na Shehu duk jahilcinmu kuma se mu kasa sanin wannan ai se a ƙiyama za tayi aiki" "to a duniyar ma aiki zata yi, kowayayi ta kan shi, dan wallahi ku ka sake ku ka faɗa hannun Sarari bana da bakin belin ku" yanakai
nan ya miƙe ya bar wajen cikin tafiyar shi na ƴan Allah ya shirya, miƙewa suka yi kowa yayi nashi
waje....
"Sun ce sun ganta" "to shikenan ya zo da sauƙi, bari na san abinda zanyi" yace cike da samunsassauci, "to yallaɓai dan Allah a ƙoƙarta a turo sauran kuɗin aikin nan na su, dan ba mutumci neda su ba" "kar ka damu Haƙilu, zan turo maka yanzu har da wanda zaka taso" "to yallaɓai nagodeAllah ya ƙara girma" yace cike da ɗin bin farin ciki, murmushi ya saki tare da katse kiran, miƙewayayi zumbur ya nufi haɗa kayan da ze buƙata....
"Yaron nan na ga kanshi na rawa a ƴan kwanakin nan" Kainuwa dake tsaye kusa da Sarari yacetare da kallon shi, girgiza kai yayi tare da faɗin "ku ƙyalesu, kar wanda ya ɗau matakin komai
akan su, dama da buƙatan ta amshi hukuncin akan abinda ta aikata" Sarari yace cike da rashindamuwa, "amma Sarari ze iya shafan masu jinyarta, dan ba din na isa wajen akan lokaci badatuni sun cutar da su, dama ba damuwar mu ita ba" Ɗan Kuka yace cike da rashin jin daɗinabindaSararin yace, kallon sakanni ya mai, tare da jinjina kai alamun ƙorafin shi ya karɓu....
"Ku gargaɗesu, su tsaya iya kanta ita da ta jajibosu, banda taɓan jikin juna" yayi maganancikedagargaɗi, jinjina kai yayi tare da juyawa ya wuce da sauri fuska cike da jin daɗin daman da akabashi.... Kallon shi Kainuwa yayi tare da faɗin "baka ganin ta can-canci yafiya?" "Har abada" yace taredajuyawa ya shige gida, bin shi da ido yayi cike da jinjina lefin da tayi wanda ba barsu sun sani basedakon abun yake shi ɗaya, ya dai san in wanda suka sani ne abu me sauƙi ne ya yafe danbecikaruƙo ba, "ya!" Kabir da ya iso wajen yace tare da bin shi da ido, murmushi ya saki tare da faɗin"beshirya ba har yanzu, mu ƙara mai lokaci" jinjina mai kai yayi tare da sauke numfashi me ƙaraminsauti, "kar ka damu babban Yaya, in muna da rai ze manta komai nan kusa" "Allah ya sa" yacejiki
a mace ya wuce....
"Yawwa Yaya Samir tashi an kammala gyara ɗakin an haɗa ruwan, ka watsa jikin ka ya saki dakyau mu ji daɗin baka labarai, kasan yau labarai har seka ture, dan na yaushe gamone" Farisat data fito daga ɗakin Anty tace tare da kallon shi, bin ƙofar ɗakin yayi da ido zuciyan shi na rauni, "dan Allah Yaya Samir!" Tace cike da magiya....
"Ba yanzu ba Anty Farisat" yace murya a sanyaye, "abinci ka ce ba yanzu ba, wankan ma bayanzuba!" Tace cike da mamaki, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "har yanzu takuran nannaki nanan ko Anty Farisat?" Murmushi ta saki tare da faɗin "to ai kaine Yaya Samir" "to tunda yacebayanzu ba malama ƴar jarida ki bar shi mana se lokacin da yayi ra'ayi" Insu da ta fito daga sideɗinYaya tace tare da kama haɓa....
"Yawwa baby Insu faɗa mata dai" yace cikin farin cikin ya samu me belin shi a daga tuhumanFarisat, "ai shine nake faɗa mata Yaya Samir, tace zata takura maka zamu samu saɓani daitayanzu kuwa" murmushi ya saki tare da faɗin "zo zauna kusa da ni" murmushi ta saki tare daƙarisawa ta zauna ba tare da murmushin saman fuskanta ya ɓace ba, "ina kallon Antyna afuskanki, kar ki dinga nisa" murmushi ta saki tare da faɗin "wai kai ma! Haka fa Yaya yake cewa, yanzuda na shiga ma na tadda suna maganan da uncle Kamil" tayi maganan cike da jin daɗi....
"Tana fa sane" Yasmin tace tare da banka mata harara, farr tayi da ido tare da faɗin "bansanjanzance baby, zo ki wuce inda ki ka fi wayau" "kar ma ki fara wannan sumbatu dan ba me yiwuwaba ne" dariya ta saki tare da faɗin "bari in haɗa bom, Hajiya Nafisatu" ta kira sunan Babiyadaƙarfi tare da ɗaga kai" danne mata baki Yasmin tayi tare da hayewa kanta suka yi ƙasa, "aiki yasame ku" Farisat tace tare da kauda kai, murmushi Samir da idanshi ke kansu ya saki cikedaɗinbin farin cikin ganin ba abinda ya taɓi shaƙuwa da ƙaunar da suke wa junansu tare da mai daduban shi ga Salman da ke faɗin "wallahi video zan muku in ɗaura a tiktok"....
"Malamin ina iyalin? Ban ganta cikin ƴan tarba ba" yace idan shi akan Salman, murmushi yasaki
tare da kauda fuska, fiɗɗo ido yayi tare da faɗin "ya ne! Kar ka ce mun har yanzu kai ɗaya kake?""Tambayi ƙanwarka" yace tare da sakin murmushi, "wani irin ya tambayeni, wai my Jannahmeyasa ka ke mun haka ne?" Farisat tace cike da takaici, dariya ya saki tare da faɗin "me kumanayi? Cewa fa kawai nayi ya tambayi ƙanwarshi ban kama suna ba, kuma ƙannin shi a wajennanda yawa" "ba wani nan wallahi dani ka ke" tace kamar zata saki kuka, dariya Insu da Yasminsukasaki tare da bin ta da ido, "to I'm sorry, Samir tambayi Yasmin ƙanwar ka, shikanen" yace taredaɗaga hannu sama, "wait!" Yace cike da mamaki idanshi na yawo akan su, kallon shi suka yi
fuskoki cike da murmushi....
"Salman kunyi aure ne!" Yace cike da zumuɗin jin amsa hannunshi akan Farisat, jinjina mai kai
yayi tare da faɗin "eh" "Anty ta ga auren!" Yace cike da fata, girgiza mai kai tayi tare da faɗin"two year's da wasu watanni kenan" "na san zata so ta gani, amma Anty ni ma bangani ba, kar ki
fushi" yace cike da gaskiyanshi, murmushi suka saki tare da bin yanda idan shi ya cika da hawayeda ido, rumgumo Salman yayi tare da faɗin "I'm so happy, nayi matuƙar farin ciki da jin kasamumuradin ranka, Anty Farisat kina farin ciki da tarayyan ko?" Ya idda maganan idan shi akanta, "sosai, yana kula dani kamar yanda Anty ta hasaso, yana matuƙar ƙaunata" tayi magananidantadake cike da hawaye akan Salman dake bin ta da ido, "wow!" Yace tare da sakin shi fuska cikedamurmushi, jawota Salman yayi tare da faɗin "zamu ɓata Kushi ban da kuka" murmushi ta saki
tare da dukan ƙirjin shi, "auch" yace tare da ranƙwashin kanta a hankali....
"Kana dai gani Yaya Samir a gabanka suke harkokinsu babu ko jin nauyinka" Insu tace taredakallon shi, murmushi ya saki tare da faɗin "baby Insu zan so ganin hakan ai" "se a bi wani sarkin" Salman yace tare da banka mata harara, "ke har kina da bakin magana! Yasmin ji yau wai Insukemaganan ana abu ba'a jin kunyan mutane, Yaya Samir bari in faɗa maka babynka da baby Insuduk aure ne da su" Farisat tace cike da takaici insu, "what!" Yace da matsanancin mamaki taredabaza musu ido....
Zare ido suka yi lokaci guda tare da kallon shi, dariya su Gude dake gefe suna jiyo komai sukasaki, isowa wajen Sadam yayi ya zauna kusa sa shi tare da faɗin "ai duk an ɗauresu an miƙasugidan bayin Allah, fatan mu dai su riƙe su da amana su kula da cikin su".... Dariya Salman ya saki tare ra kai mai bugu a kafaɗa, shafa kafaɗan yayi tare da faɗin "toai
gaskiya ne ko" "ƙwarai kuwa Sadam, Insu har da ɗiya" Babiya dake ta can kusa da su Gudetaceda ƙarfi, "me! Daughter! Kuna nufin baby Insu ta haihu! Ta haifa wa Anty jika!" Yace a rikice, "sosai kuwa, ita ma Farisat ba din Allah ya amsa ba da da nata zaka taddata" tace cike da tabbaci, "wow! Dama duk kun girma wai!" Yace cike da farin ciki me haɗe da mamaki....
"Ai duk sun riƙa" Sadam yace tare da sakin dariya, harara Farisat ta banka mai tare da kaudakai, "to nayi shiru" yace cike da danne dariyar dake taso mai, bin su kawai yake da ido me cikedamamaki, sadda kai Insu tayi tare da faɗin "dan Allah ka daina min irin wannan kallon YayaSamir, sani jin kunya ka ke" tayi maganan tare dw rufe fuska da tafukan hannu, dariya suka saki cikedamamakin wai ita ke jin kunya yau....
"Sannu da aiki Insu!" Farisat tace tare da sakin dariya, "Malama ƴar jarida kar fa in matsomiki
number" tace tare da banka mata harara, murmushi Samir ya saki me cike da farin ciki taredafaɗin "nayi matuƙar farin ciki sosai wallahi, naji daɗi matukar, Allah ya wanzar da farin ciki arayuwarku, ya gafartawa Anty yasa tana kyakykyawan makoma, na tabbatar yanda ta rayucikininganta rayuwar ƴaƴan mutane Allah ba ze wofintar da nata ba, Allah ze cigaba da kula damu" ya idda maganan tare da zaran tissue ya goge hawayen da suka gangaro mai, "sosai kuwa" Salman yace tare da ɗaga kai sama yana me maida na shi hawayen, "ai ta samu sheda a bakunanjama'an anguwa, banga wanda ya buɗe baki ya aibatata ba, sun yi kuka iya kuka, kowa ya buɗebaki abu ɗaya yake faɗi, "baya goya marayu da masu uba" Gude tace cike da jin takaicinkantada
ta kasa gano gaskiya har Anty ta bar duniya.... Murmushi ya saki tare da fadin "where is my daughter!" Ya jefa tambayan idan shi akanInsudake bin Gude dake yaban Anty da ido, murmushi ta saki tare da dawo da dubanta gare shi cikedayanayinta tace "tana gidan su Yaya Samir" "ai wannan ba abin arziƙi ake da ita ba, wai fa kunyannan da mutanne 1000 take, na faɗa mata ta ajiye a 2000 ta zo amma taƙi Yaya Samir, wallahi
kuma in ka bibiya tana kuka ta barota" Farisat tace cike da takaici, "ni baki ga ko tambayaninatake banyi ba" Yasmin tace tare da nuna nata takaicin....
"Kar mu yi haka dake baby Insu" yace cikin komawa serious, jinjina kai tayi tare da faɗin"toYayaSamir" "wataƙila tunda kai ka yi magana taji" Salman yace tare da sakin dariya, "oh kar kucinyemin ɗiya ɗanya" Mami da ta riski batun tace tare da doko sallama ita da zugan yaranta, murmushi Samir ya saki tare da miƙewa da sauri ya nufeta yana isa ya rumgumeta tare dafaɗin"Mami!" Fashewa da kuka tayi cike da rauni, tun ɗazu take san zuwa amma ta kasa, ba ta santazo ta tadda rauni a saman fuskokin su, se da su Rahma suka iso sannan ta samu ƙarfin gwiwanzuwa....
"Se haƙuri Mami" Habiba tace tare da kallon ta, "oh ashe mu zamu gane ma Amina dawowanshi"tace cikin muryan kuka" janye jiki yayi a natse ya goge hawaye, "sannu da haƙuri Samir sannu, adaure, da ciwo kam, amma ba abinda yafi ƙarfin haƙuri" tayi maganan cike da kulawa, jinjinamata kai yayi tare da bin su Rahma da ido, nuna Safinat yayi tare da faɗin "Rahma!" Dariyasukasaki tare da girgiza mai kai, "oh to ina take?" Yace fuska ɗauke da murmushi....
"Gani nan Yaya Samir" tace cike da jin daɗi, murmushi ya saki tare da faɗin "to ke kuma wacece?"Safinat" tace murya cike da murmushi, zare ido yayi cike da mamaki, "ga abun mamaki nanHasinat auta" Sadam yace tare da nuna mai ita, "kaii wannan autan Mami ce ta girma haka!" Yacetare da kama haɓa "Aiko ita ce" Mami tace fuska faɗaɗe da murmushi, "ai duk ta fi su jikingirma, ya a kayi ku ka yarda ta ƙwace muku girman?" Yace idan shi akan su, dariya suka saki ba taredasunce komai ba, murmushi ya saki tare da faɗin "ku ƙariso ciki" yayi maganan tare da riƙohannun Mami suka yo ciki....
Zaunar da ita yayi a saman kujera tare da kallon Sahabee cike da ƙauna yace "Uncle kawowaMami ruwa" murmushi ta saki me faɗi tare da tuno shuɗaɗdun shekaru, haka yake duk sandabaƙo ya zo gidan yana nan haka ze hutar da Anty ya kula da su yanda yakamata....
"Yawwa wani magana ma muke yi?" Yace idan shi akan Yasmin, "akan barin Mairah da Insutayi" tace tare da gyara zama, "no baby ai mun gama wannan, na kuma san ba zata kuma ba, kobabyInsu?" Ya idda maganan cike da salon tambaya tare da kallon ta, murmushi ta saki tare dajinjinamai kai, "tab ba dai Insu ba" Rahma tace da tabbaci" "falyaƙul hairan dai" tace cike da takaici, "sorry beb haka gaskiya ta gada" tace tare da sakin murmushi....
"Ya sunan daughtern nawa?" Yace tare da gyara zama, "Farisatul Mairah" Yasmin tace taredasakin murmushi, faffaɗan murmurshi ya saki tare da jinjina kai cike da ƙaunan me sunan, "bani
wayanki inda network in kira Anty Salwa" Farisat tace tare da miƙa ma Rahma hannu, "naki fa!" Tace cike da mamaki, "ba service" tace idanta akan ta, "ke dai faɗi gaskiya Malama, kawai ki ceba kati" tace tare da sakin ƙaramar dariya ta miƙa mata....
"Wannan batu ne kawai, amma ai ke kin san ba'a rasa nono a riga" Farisat tace tare da bankamata harara ta kai hannu ta amshi wayan, "na nawa kuma! Ai kamawa take a ɗaure me ɗaurewaHajiya, dan haka yi abinda ke gabanki, "matar Doctor Salman guda ki ke faɗawa haka!" Safinat
tace tare da kama haɓa cike da danne dariyar dake taso mata....
"Barta Safinat saboda zan amfana da ƴan matsabban da ke ciki shine take ƙare min tanadi" tacetare da fara neman number, "aiko se kin amfana, dan na ga alamun ba so take ba, shiyasatakesan hasalaki ki bata" "aiko se na yi" tace tare da danna number ta saka a speaker, kallonUmar
dake bakin ƙofar ɗakinsu yana leƙo su Insu tayi tare da faɗin "zo auta" murmushi ya saki taredanufota.... Yana isowa ta kamoshi tare da faɗin "Yaya Samir baka ga autan Anty da Yaya ba ne?" Da mamaki
ya bi ta da ido, jinjina mai kai tayi tare da faɗin "shine auta, na ga baka kula dashi ba, sannanshima se tsoron zama kusa da kai yake, tun ɗazu ya shige ɗakin su se leƙen ka yake" ta iddamaganan murmushi ɗauke a saman fuskan ta, miƙa mai hannu yayi cike da mamaki, kamawayayi a hankali ba musu, zaunar dashi a gabanshi yayi tare da faɗin "na ganshi a airport na kumaganshi anan gida, se dai ban ɗauka ɗan Anty na ba ne, duk ɗaukana yaron Munari ne" "tobaɗanmarainiya wayon naka ba ne, kana cewa kowa Anty se ni da ka gama rainawa" Munari ta cafkemaganan cike da takaici, "ai be ganin kowa se su, mu da muka kwaso jiki da namu yaranmabekokallo inda muke ba bare su" Shamsiyya tace tare da miƙewa cike da takaici ta fara harhaɗakayanta.... Sakin ido da baki yayi yana binta da kallo me cike da mamaki, "Shamsiyya meye hakan?" Habibatace rai ɓace, "a'a fa Inna Habiba gaskiya na faɗa, bakya ganin be kallon ko inda muke ne, duktsiya dai ba ze iya sauya mu matsayin jinin shi ba, ƴan uwanshi halak malak cikin uwa da uba, sukuma ba za su tashi daga matsayin ƴaƴan kawun shi ba" "dan Allah kar wanda ya ƙara
tambayanta ku barta ta tafi" Nafi tace rai ɓace, juyowa tayi a fusace tare da faɗin "zanci ubanki
Nafi, dake nayi!" "A'a fa Anty Shamsiyya meye haka dan Allah!" Halima tace rai ɓace, "kunamason jan zancen ne, ta tafi mana ga hanya, duk wanda ze bi ta ƙofa abuɗe take" Suwaiba tacekoajikin ta, "hmm Inna Suwaiba kenan" tace tare da tasa yaranta ta fice, bin ta da ido suka yi zukatacike da mamakin hali irin na ta....
"Yawwa ta ɗaga" Farisat tace tare da gyara zama, "Anty Salwa!" Tace a zumuɗe, "na'amƴanmatan Salman" dariya ta saki tare da faɗin "yana jinki dai, ki na ina ne haka?" "To tsoronyaji nakeko shakka! Ina kitchen" murmushi ta saki tare da faɗin "ja kujera tukun" "lafiya! Ban fa sanrashinarziƙin ki" tace tare da ɗaure fuska ksman tana ganinta, dariya ta saki tare da miƙa ma Samir
wayan...
"Ke bunburu me cikin zani" yace murya cike da murmushi, "Samir!" Tace da ƙarfi murya narawa, "kee easy mana, kar ki tarawa kan ki maƙofta" yace tare da zare ido kaman yana gabanta, "wayyoAllah! Wayyo ƙirjina! Samir kai ne! Kai ne ka dawo! Samir!" Ta jera tambayoyin cike da rikicewa, murmushi kawai yake saki ƙwaƙwalwa na tuna irin zamantakewan da suka yi cike da shaƙuwadaƙaunan juna....
"Ni ne Salwa, ni ne cikashin SSS ɗin Anty, gani a gida ido na muradin ganinta ba ta" fashewadakuka tayi tare da faɗin "Samir, Salman, Salwa" murmushi suka saki cike da tausayinsu, "zanzo, ina nan zuwa" tace tare da kashe kiran ƙitt, "to Allah yasa ba kaya ta tafi haɗawa ba" Sadamyacetare da sakin dariya, "ai wannan jazaman" Yasmin tace tare da sakin nata dariyan, "sabodakai
Anty ta saka sunan shi" Insu tace tare da nuna mai Umar, "Umar!" Yace cike da mamaki, jinjinamai kai tayi tare da faɗin "tun ranar da ta haifeshi aka bata shi ta ɗaga shi tace Samir ɗinayadawo" rungume Umar yayi idan shi ƙyam akan Insu, "ƙwarai kuwa ta faɗa mana ba dan Malamtasaka sunan ba, dan Samir ɗinta ne" Sadam yace fuska cike da murmushi....
"Allah sarki Anty na" yace cike da kewa, "Insu fa Uncle Sahabee ta aura" Salman yace taredakallon shi, zabura yayi tare da saurin riƙo Umar da ya yi ƙasa ze faɗi, "me!" Yace tare da kallonsu,
"kai ne nace ka watsa ruwa dan kaji daɗin jin labaran ka ce ba yanzu ba" Farisat tace tare dakallon shi, "ku ban labari" yace cike da zaƙuwa, gyara zama Farisat tayi ta fara rattafo mai, baabinda fa ɓoye, "Allah me iko! Yanzu Mairah ɗiyar Uncle Sahabee ne!" "Eh" suka ce bakunaahaɗe, "Allah me iko!" Ya kuma cewa cike da mamaki, "ita kuma wanna matar Mejor Shureim" Farisat ta kuma cewa tare da dafa Yasmin, murmushi ya saki tare da faɗin "na so ganin shi" "zezogaidaka Yaya Samir" tace cike da tabbaci, "oh su baby ba ko kunya" Safinat tace tare da sakindariya....
"Ku tsaya ina my wife! Banji kun ce komai akanta ba, kar dai ita ma kun mata aure!" Ya iddamaganan idan shi a warwaje, "wace!" Farisat tace da mamaki a muryanta, hararan wasa yazabgamata tare da faɗin "takwarar Hajiya" dariya suka saki tare da kallonshi, "ma sha Allah tananan" Jummai tace cike da farin ciki, "to yanzu na ji magana, ai da na tadda kun ba wa wani ne, dasekun amso min abata" yace cike da gaskiyanshi, dariya Salman ya saki tare da faɗin "wai damakana riƙe da wannan maganan!" Kallon shi yayi da mamaki tare da faɗin "kyautar Anty nafa! Koka manta ne, tun ranar da ta haifeta tace Samir na maka mata, Nafisat da Umar za su ƙararayuwa ƙarƙashin inuwar aure guda, taya zan manta, ai kyautar Anty me daraja ne" "wowasheita Nafisat ma an daɗe da badata" Sadam yace tare da sakin dariya... Dariya Salman ya saki tare da faɗin "se ka yi hoɓɓasa, kar ka zama Baba na soro" "ai hanyandatsayi, su yi ta yi muna bayan su" "auh" yace murya cike da murmushi, "yawwa tunda ga kusemutattara mu je duba Sa'adatu ko?" Farisat tace tare da kallon su Rahma, "a dawo lafiya Safinat
tace tare da kauda kai, "a'a kar ki ce haka dan Allah, ai ba dan halinta zaki ba" Yasmin tacedakulawa, "wannan in dan halinta ne me za'a mata na arziƙi" tace cike da takaicinta, "to kingani
dan Allah zaki, Anty Iƙilima ma ta zo tana can" Insu tace tare da kallon ta, "to se mu yi hoɓɓasadan zamu koma gidajen mu, amma Yasmin ke ma yau zaki koma ko?" Tayi maganan tare dakallon Yasmin, harara ta banka mata ta kauda kai...
"Yau ne mana, ya dawo anga dawowan shi lafiya sun zanta me yayi saura kuma" Babiya tacetare
da kallon su, "dan Allah Hajiya daina batun nan" Yasmin tace fuska a ɗaure, murmushi Farisat tasaki tare da faɗin "ai Hajiya ki yi haƙuri kawai ki kauda ido na kwanaki akan mu" "a'a Farisat banda ke wallahi, ga baki ga hanci ma se kin kwana" Suwaiba tace tare da kallon ta, "ku mujebayinAllah, muna cigaba da zama za'a samu matsala" tace tare da yunƙurawa, murmushi Salmanyasaki tare da bin ta da ido....
"Ina Sa'eed ɗin? Shi banganshi ba" Samir yace tare da kallon su, murmushi Insu da ta miƙetasaki
tare da faɗin "yana Ɓadamayya shi da Nafisat, a can suke karatu, bari mu dawo Yaya Samir akwai
labarai" jinjina mata kai yayi fuska faɗaɗe da murmushi, "autan Mami muje ki ji wani batu, anaikoni" ta idda maganan tare da jawota suka nufi barin parlorn, "to kwa gaidata da jiki" "Babiyatace da ƙarfi, "to Hajiya za ta ji" Insu tace da ɗan ƙarfi tare da ficewa janye da hannun Hasinat....
"Me!" Hasinat tace da ƙarfi cike da mamaki, wanda ya sa Farisat taka burki da sauri, "menene!" Tace tare da juyowa ta kallesu, ganin yanda su Yasmin dake kusa da ita suka baza mata idocikeda mamaki ya sa Rahma dake gaba ɓangaren me zaman banza faɗin "menene wai!" "Ƙarinbayani
muke jira daga gare ta, wai uncle Kamil ne ke san Hasinat" Yasmin tace cike da mamaki, "wanne!" Rahma tace cike da nata mamakin, "guda ɗaya dai da ki ka sani" tace tare da maidadubanta ga Insu dake faɗin "menene abin mamakin to, ta burgeshi, ya ji kuma ze rayu da ita"
"kayya Insu, anya ba haɗe-haɗen ki ba ne!" Farisat tace cike da tantama....
"Oh wai me ku ka maidani ne!" Tace tare da kama haɓa, "in ma haɗe-haɗen naki ne kin yi, ai
alheri ki ke haɗawa Insu, rabu da su" Rahma tace cike da farin ciki, "bare ma ba haɗe-haɗennawa ba ne Anty Rahma, shi da kan shi ya same ni da maganar ranar da ku ka tafi" "yace miki
me!" Farisat tace cike da mamaki cikin katsan mata hanzari, "kwatantamin ita yayi mana" tacecike da ƙosawa "ke kuma se ki ka gano ita ce" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "eh mana, kun san ma da ya yakwatanta ta?" Tace fuska na faɗaɗuwa da murmushi, "a'a suka ce cikedasan
ji, "wai wannan me ajin" tace tare da sakin dariya, "auh" suka ce cike da dariya, "wallahi ai yagaclass fa, na ce mai uncle Kamil ai duk ɗan Bertuwa akwai class, yace "ita wannan na ta na dabanne" dariya suka kwashe da shi cike da nishaɗi....
"Jamu muje baiwar Allah yamma ta kawo jiki" Safinat tace tare da kallon Farisat, ba musutamamotan key suka cigaba da tafiya, "Allah ya sa su zama alheri ga junansu" Yasmin tace cikedajindaɗi, "amin, dama manyan mu sunce "mahaƙurcu mawadaci" kinga da kin kafe se wannanwawan da yanzu kina can kin fara haɗiyar baƙin ciki" Rahma tace cike da gaskiyanta, "wallahi fa, wai ya aiko an ɗaukan mai kayan shi ma kuwa!" Farisat tace tare da kallon ta, "da gudu ma, ai
wannan shine yanke talaucin shi, ba ze taɓa bari ba" dariya suka saki cike da shaƙiyanci, "wallahi
fa" tace tare da gyara zama, "auf kun tunamin" Insu tace tare da zaro waya ta nemi number tadanna kira....
"Ana ɗagawa tace "uncle Kamil" baza mata ido gaba ɗaya suka yi, "na manta fa zaka gaidaƙanwar Anty Iƙilima, gashi har mun ɗan yi nisa, bari in kira Yaya Sadam ya kawo ka can" shirundaƙiku tayi kafin tace "to shikenan" tana kai nan ta zare wayan ta danna number Sadam, ringingbiyu ya ɗaga tare da ɗaga mata sallama, "wa'alaikumussalam Yaya Sadamdan Allah ka ɗakkouncle Kamil yanzu ka kawo shi general, ze duba Sa'adatu da jiki ne" "okay" yace tare da zarewayan ya katse kiran, murmushi ta saki tare da zare nata, "aiko dan kin ce uncle Kamil ne, ammaya rantse ba dalilin da ze sa ya je dubata" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "to ya ze yi, wallahi shaf na manta da ze je ya dubata da jikin" tace tare da kallon Hasinat....
"Haba Anty Hasi menene kuma?" Tace tare da sakin dariya, "yarinya ta kamu ne ita ma" Safinat
tace tare da tintsirewa da dariya, harara ta banka musu tare da kauda kai, "abun fa ba sauki
wallahi" Yasmin dake na ta dariya tace tare da kallon Hasinat, "ni ku sauke ni in koma gida" tacetare da kallon su cike da gaskiyanta, "meyasa!" Suka ce da mamaki, "shima fa can ze je" tacecikeda shagwaɓa, "ji ƴar ƙauye dan Allah, to shine me?" Safinat tace cike da takaici, "a'a da
gaskiyanta fa, amma Anty Hasi ba wani abu, ba'a gaban mu ze tattauna dake ba, se munkoma
gida ze zo har gidan Mami ya gaidasu ku samu zama,
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 99 Chapter of 109