Share this page
wanda ya can-canci wannan aikin a cikingidannan se ita, maganan canzata ma be taso ba" yayi maganan tare da kallon ta, "okay se a fahimtarda ita me take yi, kar ta dinga sakaci, me kuma tace yau?" Ta idda magana tare da kallonshi, "wai an kai wa SSB mata yau" "what!" Matashiyar budurwa ƴar kimanin shekaru 28 da ta fito dagawani madai-daicin lungu tace tare da kallonsu, "no Dear kar ki damu zo abin ki" yace taredamiƙa mata hannu, "Dad ka fa ji abinda ka ce, sannan kace kar in damu" tace kaman za ta saki kuka, "no no, kar ki yi kuka yanda sauran suka tafi ita ma haka zata tafi" tura baki tayi taredashagwaɓe fuska, murmurshi ya saki tare da faɗin "alƙawari na ne wannan" jinjina kai tayi taredasakin mai sumba a kumatu ta miƙe, tana gab da ficewa daga wajen dattijuwan tace "Jabiida" "yesMom" tace tare da juyowa, "ina zaki?" Tura baki gaba tayi tare da faɗin "ina dawo zan faɗamiki, sauri nake" tana kai nan ta fice, bin ta tayi da kallon mamaki, murmushi Dad ya saki tare dafaɗin"ki jira in ta dawo ra faɗamiki mana" "no Honey yarinyar nan ta fara yawace-yawace maradalili yanzu, sannan kasan me ne ne a gaban mu, be kamata ana barinta fita mara dalili ba" ta iddamagana tare da baza mai ido, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "da gaskiyan ki, zan yi maganadaita" "okay, yakamata kafin a fidda zan can tsaidashi a takara yarinyar da aka kai ta kama gabanta" Mom ta kuma tacewa idonta akan shi, jinjina kai yayi tare da kai kofin tea baki.... Tana fitowa ta tadda an shigo mata da kaya, murmushi ta saki tare da faɗin "ka ga masuyi danAllah" tana kai nan ta nufi stool ta ja ta zauna, haka tayi ta dube-dube, kafin ta fara shafa mai, kowa yasan ba ta da tsatsibe-tsatsibe wajen shiryawa, tana kamawa ta miƙe ta zage jakantataciri riga da wando ma su sauƙin nauyi ta saka, tattausan hula ta saka a ka ta warwari tissuetagoge fuska, tsayawa tayi a gaban mirror tana ƙarewa kanta kallo, ban da murmushi ba abinda take saki, jin ƙarar da wayanta ya ɗauka ya sata nufar inda ta ajiye da sauri..... Ganin Yaya ke kira ya sata ɗagawa a zumuɗe ta kara a kunni, "oh Allah Yaya wannan mutuminyayi kewan Anty kuwa? Ka ga inda yake rayuwa kuwa! Wow aljannar duniya guda Yaya" tacetareda gyara zaman hulan kanta, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "ki huta tukun zamu yi maganain kin tashi" "I'm sorry Yaya" tace a hankali, "nothing my baby ki kwanta kinji?" Yace da kukawa, jinjina kai tayi tare da faɗin "bye" "bye sweaty" yace tare da sauke wayan, sauke wa tayi tanajinkaman ba ta kyauta ba da tayi mai maganan, ajiye wayan tayi tare da miƙewa, rurin da wayandake gaban gado zaune cikin amintaccen kujera ya ɗauka ne yaja hankalinta, ƙarisawa tayi dasauri tare da ɗaga wa ta kara a kunni, "ranki shi daɗe an kammala shirya abincin" ta ji saukanmuryanMaude a kunninta ras, da mamaki ta zare wayan daga kunnin tare da faɗin "wayyo rayuwa" tanakai nan ta ajiye ta fice a natse, tunda Maude ta jiyo ƙaran takunta ta zubawa hanya ido, tanabayyana ta zare ido tare da faɗin "wannan ƴar amaryance ko amaryance!" A ƙasan zuciya, murmushi Insu ta sakin mata tare da faɗin "sannu da aiki Baba" murmurshin dole ta saki taredafaɗin "a'a ranki shi daɗe ai aikin mu ne" tayi maganan tare da nuna mata hanyan dainingɗinbamusu ta bi ta, jan mata kujera tayi ta zauna tare da faɗin "bismillah Baba zauna mana" tayi maganan tare da kallon ta fuska yalwace da murmushi, girgiza kai tayi tare da faɗin "a'a ranki shi daɗe" ta idda naganan tare da zaran plate da spoon ta fara zuba mata rayayyan indomie dayaji hanta zaƙo-zaƙo, yanda ƙamshin ya doki hancinta ya sata lumshe ido tare da faɗin "wow" tanagama zuba mata ta tsiyaya mata juice ta ja gefe ta tsaya, jan plate ɗin tayi gabanta sosai tafaracin abincin a natse, banda santi a ƙasan zuci ba abinda take, dan da gaske abincin ya tafi daita..... "Ranki shidaɗe gashi yau yallaɓai ya yi tafi" Maude dake hankalce da yanda take cin abincintacetare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da faɗin "ba damuwa Baba ai ina nan zamuhaɗuin ya dawo" ta idda magana a natse, jinjina kai tayi tare da faɗin "gaskiya ne ranki shidaɗe, Allahya dawo mana da shi lafiya, in ya tafin ne ba dawowan wuri ba, se yafi shekara uku huɗu" damamaki Insu ta ɗago ta kalleta tare da faɗin "be zo gida ba!" Ganin kalamanta sun samushigayasata gyara tsayuwa tare da faɗin "wallahi fin haka ma ranki shidaɗe, shiyasa da yawan matar daake kawowa ba za iya jurewa, suna ganin ya tafi se su nemi saki" guntun murmurshi Insutasaki tare da faɗin "aiko da gaskiyan su, ba za ta zama su ɗaya ba kaman mayu" "wallahi fa ranki shidaɗe amma ke ba'a nan ki ke ba ko?" Murmushi ta saki tare da faɗin "a Bertuwa nake" "shiyasa, a she tsallake gari a kayi, ai a nan iyaye sun daina ba shi auren ƴaƴansu, kema nasaniyayenki ba su san waye shi ba" tace a hankali, bin ta da ido Insu tayi tare da girgiza kai, murmushin samun nasara ta saki tare da ƙarisawa kusa da ita ta kai baki kusa da kunnintatareda faɗin "zargi ake fa mata maza ne, dan ba abinda yake iya taɓukawa a gado, yanda aka kawomatan haka suke tafiya se dai su gaji su kai court a raba auren" ta idda maganan cike da tabbaci...... Zare ido Insu tayi tare da faɗin "mata maza!" "Eh mata maza, amma fa kar ki ce ni na faɗamiki, aure kusan goma aka mai amma shiru ba bayani" danne dariyar da ya kusan kuɓuce mataInsutayi tare da faɗin "amma wannan matar kalanta kalan munafukan farkon ƙarni ne, Anty tacebiyu ita tace goma" tayi maganan a hankali, "me ki ka ce?" Maude tace tare da kallon ta, "nomamaki kawai nake, to ba'a neman mai magani ne?" Tace tare da kama haɓa, "ba ze sha ba, kewannan fa murɗaɗɗene da ki ka gani, Allah sarki gaki ƙarama dake, za'a sabauta miki rayuwa" kauda kai Insu tayi da sauri ta murmusa kafin ta juyo tare da faɗin "ni kuma! To me ya sakoni amaganan?" "Haba ƴan nan, ko in ce ma jikalle auren me shekaru haka ga ƙarama kamanki ai sabauta rayuwarki ne, abun takaicin ma shine ba ze iya taɓuka wani abu ba, dama ze iya nesemuce da sauƙi" "a'a matayen dai za'a tausayawa Baba, ni ai ba matar shi ba ce" tayi maganantareda kafe Maude da ta zare ido da ido, "ki na nufin ba aura miki shi a kayi ba!" Tace a razane, murmushi Insu da ta gama karantar ta ta saki tare da girgiza kai, "to wacece ke! Ke ya sa Hajiyata kawo ki!" Tace a tsorace, "yarinyar ƴar uwarshi mana" tace a sukance, "na kwafsa" Maudetacetare da sakin murmushin yaƙe, murmurshi Insu ta sakin mata tare da jan kujeran baya kaɗantamiƙe, cike da yanayinta ta ƙarisa kusa da Maude sosai ta kai bakinta saitin kunninta tare dafaɗin"ba zan faɗawa kowa kin ce mun Uncle mata maza ba ne" tana kai nan ta sadda kai ta saki dariyata haye sama, haɗiye yawun razani Maude tayi tare da jinjina kai, tana ɓacewa ganinta ta saki numfashi me ƙarfi tare da faɗin "Maude watarana se kin ɗau wuƙa kin daɓawa kan ki indai bazaki dinga tsananta bincike kafin ki yanke hukunci ba" tana idda faɗi ta juya ta fice..... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Thirteen Da sallama a baki suka shiga parlourn da gudu Sa'eed da Umar suka yi kan su tare da musuoyoyo, murmushi suka saki tare da rungumesu, "har kun dawo?" Babiya dake zaune fuskayalwace da murmushi tana bin su da ido tace cike da kulawa, murmushi suka saki tare da iddasashigowa cike da farin cikin ganinta Farisat tace "eh Hajiya" "ma sha Allah, ya Annur ɗin?" "Yanaagaida ki" Yasmin tace tare da zama.... "Ina amsawa" tace tare da amsan cake ɗin da Umar ya fiddo a ledan gifs ɗin ya miƙa mata" "toharda tsaraba ne?" Tace tare da gutsiran kaɗan ta miƙa mai sauran, "ina Sahabee?" Nafisat tacetaee da kallon Sa'eed, "yana side ɗin Yaya" yace a girmame, "okay" tace tare da miƙewa riƙedasauran ledan gifs ɗaya da yayi saura ta nufi can.... "Shagali yayi shagali Hajiya se kinga yanda abun ya bada kala" Farisat tace tare da gyara zama, murmushi ta saki tare da faɗin "na ga alama ai, ina su Salmanun? Banji ko ƙaran buɗe gateba" "awaje ya tsaya muka sauka suka shige gidan Ammi" Yasmin tace tare da sauke veil ɗin dakesaman kanta, "ko da naji, in ce banji diran mota ba, bayanku kuwa Maman shi ta zo ita da ƙanwarnan tashi me rawan kan tsiya muka sha fira, ba su jima da tafiya ba" dariya suka saki taredakallon ta, "ai wannna yarinya Allah ya mata rawan kai, yanda ki ka san ɗakin su ɗaya da Insiyyata" murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "Allah sarki Mami ba ta same mu ba" "aikotanashigowa ku ta tambaya" Murmushi Farisat ta saki tare da faɗin "Hajiya Hasena kuma ba ta da rawan kai" "a'a a'a aikotana da shi" Babiya tace tare da kallon ta, miƙewa Yasmin tayi tare da faɗin "gashi Baba Tinenetaceakawo miki" ta idda maganan tare da ajiye mata ledan da ke hannunta, "ma sha Allah a shetanatune, har can ku ka je?" "Eh mun biya mun gaida Yaya Ali" tace cike da gajiyan dake taso mata.... "Lallai kun kyauta, ya ku ka gan shi?" Tace da kulawa, "albishirin ki" Farisat tace a zumuɗe, "gorofari ƙyal kaman haƙwaranki" Babiya tace fuska yalwace da murmushi, "yau Yaya Ali ya samujam'in sallah duka" tace a zumuɗe, "ma sha Allah, Allah ya ƙaro sauƙi" "amen ya Allah ai baƙaramin farin ciki na yi ba da ya faɗa mana" Farisat tace cike da zallan farin ciki, "ai da daɗi" Babiya tace ita ma nata fuskan faɗaɗe da farin ciki, "bari in zo in faɗa ma Insu na san ba ƙaraminfarin ciki za tayi ba" Yasmin tace tare da ɗaukan jakanta ta saɓa.... "Ah-ah kar ku kirata yanzu, Babanku yace a barta ta huta tukun" "sunyi magana da Yaya ne!" Tace cike da farin ciki, "sunyi ɗazu ba jimawa, se zuzuta gidan da ta sauka take, da alamudai yamata kyau" dariya suka saki cike da farin ciki tare da faɗin "ai tunda tana can zamu gani ne" "ai Insiyyah ba zata bar zuzuta lamari ba" Babiya tace tare da sakin murmushi, "to Hajiya bari inzoinnuna miki hotuna da video's ki ga amarya da ango yanda suka fito da fitan su" "to ku fara shirinsallah tukun gab ake da kira, in zaki wuce ki tashi Sa'adatu" tace da ƙarfi dan nisa da Yasmintafara, juyowa tayi da mamaki tare da faɗin "ba ta tashi ba har yanzu!" "Wallahi ba ta tashi ba, Farisat ɗau maganin nan ki kai ma Mari ta dafa mata ma" saurin ƙarisowa cikin parlournBabaMari tayi tare da faɗin "gani da kaina Hajiya" ta idda maganan tare da ɗaukan ledan, "HajiyaYasmin jeki shirya bari in tasheta" tace tare da nufar inda ɗakin yake, jinjina mata kai tayi cikedamamaki ta bi ta da ido har ta gittata, dan ta san ba ta cika tsulla kanta a abinda ba'a sakataba.... Ƙwanƙwasa ƙofar tayi a hankali tare da kiran sunanta, juyawa inda Yasmin ke tahowa tayi tareda sakin mata murmushi, "ba ta buɗe ba ne Baba Mari?" Tace da kulawa, "ina ga ta shiga toilet ne" tace cike da murmushi, "ze iya yuwuwa, ki je kawai Baba Mari tunda ta tashi za ta fito" jinjinamata kai tayi ta wuce, wucewa ita ma tayi ba tare da ta kawo komai ba... Dawowa Baba Mari tayi hannu riƙe da makulli, sakawa tayi tana murɗawa ya buɗu, sabodacirekey ɗin da tayi bayan ta kulle ƙofan, tana shiga ta taddata kwance tana ta sharar barci kamanmatata, ga roban maganin da ta sha yashe a ƙasa, saurin rufe ƙofan tayi tare da wucewa toilet dasauri ta ɗibo ruwa ta watsa mata tare da bin ta da kallon ƙyama, a firgice ta ɗago kai taredaɓatafuska.... "Kin bar wannan barcin asaran ko za ki cigaba da yi ne?" Tace murya a kausashe, miƙewa tayi tazauna tare da jingina da gaban gadon, hamma ta saki tare da lumshe ido, "ƙwayan ki ka ƙarashayau ma ko Sa'adatu? Yanzu ba zaki wa kan ki karatun ta natsu ba ko? Dube ki, dubi yanda ki keƙarewa a tsaye ki ke lalacewa, saboda ɗaurawa kanki masifa da bala'i da ki ka yi, wallahi ki yi wakan ki karatun tanatsu tun kafin duniya ta miki" ta idda maganan cike da takaici.... "Baba Mari ya ki ke mun magana haka kaman baki san me ke faruwa ba?" Tace cikin muryanbugaggu, "ba abinda na sani, wannan wawancin ki ke kira da hujja? Ba kyada hujjar nunawa" "shikenan dama ba lallai ki gane ba, dan ba ke abun ke naƙasawa ba, kalli nan" tayi maganatareda nuna saitin ƙirjinta, "ciwo take mun, ji nake kaman in fincikota in jefar, azalzalata take, tahanani na samu sukuni ko na sakan guda, ba na iya barci, ba na iya tunani me kyau, se na shasannan nake samun sassauci, shima sassaucin ba zan same shi a salama ba? Kin ta kura munBaba Mari, ki barni na rayu yanda nake so" ta idda maganan tare da ƙoƙarin yunƙurawa.... "Tirr dake Sa'adatu, tirr da butulu kamar ki, lallai kin zama tsintacciyar mage da ba ta mage, kin cika asalin butulu me manta alheri, kin zama ɓakar ashana me ƙona gari, kin zama ɓakar kunamawacce ba ta banbance na gida da na waje in zate harbi, yanzu duk faɗi tashin da Hajiya tayi akaninganta rayuwarki da wannan sakayyan za ki saka mata? Wallahi kin matuƙar ba ni kunya, dawanda ya mutu na dawowa da Hajiya se tayi Allah wadai da sanin ki da tayi" tace zuciya namugun tafarfasa, "tayi Mari tayi" tace da ƙarfi tare da tafiya luuu, saurin riƙe bango tayi taredafadin "se me ɗan tayi, kafin tayi uwar da tayi silan zuwana duniya ta rigata, kinga in ita tayi basabon abu ba ne" ta idda maganan tare da kama ƙofan toilet.... Cike da zallan mamaki Baba Mari ta bi ta da ido, "me ke faruwa Baba Mari?" Yasmin d ata zowuce wa ta jiyo kaman hayaniya ta shigo tace idonta na yawo akan su, saurin sai-saita yanayintaBaba Mari tayi tare da faɗin "kinga faɗa nake mata akan barcin lalalcin nan shine take ƙoƙarinkare kanta" ta idda maganan tare da sakin murmushi, "oh Baba Mari za ta daina a hankali, Hajiyatace shawara ne, jeki dafa mata maganin in mun kammala dinner ta sha" "to Hajiya Yasmin" tacetare da ficewa ... Murmushi ta sakin mata tare da faɗin "Yaya Annur yace a ce miki kin kyauta da baki zo ba" murmushi ta saki tare da juya ido saboda juyawan da kanta yake, dan maganin be gama aiki yanda take so ba, "ya kan? Kin sha maganin kuwa?" Tace da kulawa, jinjina mata kai tayi batareda tace komai ba, dan ta san tana buɗe baki zata fallasa kanta, "okay jeki yo alwala, in kinfitoseki ga hotuna" jinjina mata kai tayi ta shige dafe da bango.... "Yaya Sadam na saka ruwan" Hasena tace tare da zama kusa da shi, jinjina mata kai yayi yaajiyewayan dake hannun shi ya tashi ya wuce bedroom ɗin Salman, murmurshi Mami ta saki taredafaɗin "gida tun yau yayi fayau" murmushi Salman ya saki tare da faɗin "ba Insu ko?" "Ehduksenaji gidan ba daɗi" tace cikin nuna yanda taji ba daɗi, murmushi ya saki tare da faɗin "kunnuwanmuza su huta da surutunta, kullum cakwai-cakwai kamar Aku, ba ta gajiya da surutu sam" dariya Rahma ta saki tare da faɗin "ƴan can dai sun gamu da aiki, Yaya Salman meyasa Sa'adatubataattending ɗin class ne?" Da mamaki ya kalleta tare da faɗin "bangane ba!" "kusan 2to3 weekskenan ba na ganinta a school, so na ɗauka ko ba ta da lafiya ne ma" cike da mamaki ya bi tadaido, "any problem!" Mami tace tare da kallon shi, "no" yace tare da sakin fuska a zahiri, a baɗini kuma se mai-maita kalman 2to3 weeks yake.... Ba ta samu daman barci ba, ko da ta koma zama tayi ta cigaba da kwasan dariyar yanda fuskanMaude yayi lokacin da ta ce ita ba matar shi ba ne, se da ta gama darawa ta jawo wayantatadanna number Ali ta saka a speaker ta ajiye a kusa da ita, yana ɗagawa yace "Insiyyah" "ohAllahYaya Ali a miss you over" tace cike da zaƙuwa, sautin murmurshin shi ne ya sata sakin murmushi tare da faɗin "ina Baba Tinene na, da Sani Dear?" "Ga su nan muna zaune" yace cike da jindaɗi, "Baba Tinene I love you, I miss you" tace murya cike da dariya, dariya Baba Tinene ta saki taredafaɗin "i love you too Insiyyah, kin sauka lafiya?" "Alhamdulillah Baba Tinene zan so ki ga aduniyar da sarauniya Insu ke mulki, gaba ɗaya masarautan a ƙarƙashina take" ta idda maganancike da zaƙuwa, dariya Baba Tinene ta saki tare da faɗin "ma sha Allah, wani abu ma se nazowannan masarauta" dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "zaki zo Baba Tinene one day oneday dai".... "To Insiyyah Allah ya amince, ga Sani" tace tare da bawa sani wayan, "Dear Insu" yace taredasakin murmushi, "Dear Sani anya kuwa kayi missing ɗina?" Tace tare da kama haɓa, "sosai ma, har kuka fa se da nayi" yace murya na rawa, "oh Dear banda kuka, in ka yi se nayi, kai kanadamasu rarrashi ni kuma ba na da" ta idda naganan cike da yanayinta, dariya ya saki tare dafaɗin"to kar ki yi" "yawwa ka gaidamun da sauran ƴan uwana, ina Yaya Alin?" "Za suji, ga shi nan" yacetare da miƙa mai.... "Yaya Ali ya ƙafan?" Tace a natse, "Alhamdulillah ƴar albaraka ƙafa da sauƙi, ɗazu su Farisat sukabar nan" "ma sha Allah sun zo ne?" "Eh sun biyo daga friends day ɗin bikin Annur" "oh Allahnamanta, dama yau ne?" "Tabbas yau ne, dan sun biyo ta nan mun gaisa" "to Allah ya saka musuda alheri, magungunan ba su kusa ƙarewa ba ko?" "A'a da saura" yace zuciya cike da farin ciki, "toAllah ya ƙara maka lafiya, bari in barka haka nan an fara kiraye-kirayen sallah" "mu ma nanɗinhaka yake, ƙafa na takuwa Insiyyah, yau da ƙafafuna na je masallaci" yace cike da farin ciki, ihuta saki cike da jindaɗi tare da faɗin "Allah mun gode maka, Allah abun godiya, Allah ya ƙaramaka lafiya" "amen-amen" yace tare da katse kiran, dariya Baba Tinene ta saki tare da faɗin"yaujama'an gidan nan sun ga ta kansu da ife-ife... Ajiye wayan tayi ta miƙe da sauri ta fara taka rawa tana juyi ita ɗaya tana dariya me tafe dahawaye, se da ta tabbatar ta gaji dan kanta ta zauna tare da warwaran tissue ta goge hawayenda suka ɓata mata fuska, ɗaga kai tayi tare da faɗin "Anty Yaya Ali ya fara samun sauƙi" tanakai nan ta miƙe ta koma kusa da wayan ta ɗauka ta danna number Lailah ta kara a kunni.... Tana ɗagawa tace "albishirin ki Anty Laila?" "Goro fari ƙal-ƙal, wani abun alherin ne ya samemu?" Tace murya na bayyana daɗin kiran na ta da taji, "na shigo Ɓadamayya yau" tace da ƙarfi, "what! Wai da gaske ki ke!" Tace cike da mamaki, "wallah gani ma zaune daramdam" "wowYayabe faɗamin ba, ko da yake na ga missed call ɗin shi jiya, wata ƙila maganan ze mun" tace cikedafarin ciki, "to ina ganin, ki turo mun address ɗin ku, in na samu natsuwa zan zo" "to shikenanzanturo miki, a gidan Momy ki ka sauka?" "No ba'a nan ba ne, yaranta sun ce ba ni da masauki anan, shine ta kawo ni inda nake da" "okay bar zancen se mun haɗu, bari in turo miki" "to" tace taredakatse wayan ta ajiye tayi bathroom.... Fitowa tayi ruwa na ɗiga a fuskanta ta ɗau hijab ta saka ta hau kan praymat ta kabbarta sallah, tana idar da azkhar ta miƙe ta koma saman gado ta jawo waya ta dannawa Salwa kira, tanaɗagawa ta tari yunƙurinta da "gani a Ɓadamayya" "da gaske!" Tace a kiɗime, "wallahi" tacetareda sakin murmushi, "ke a week ɗin nan zan shigo" tace cike da farin ciki, "serious!" Tace taredagyara zaman waƴan, "wallahi, za mu zo duba uncle ɗin Abban su" "Allah ya kai mu, in kinshigoki faɗa min" "haba ai dole baby, "kin sami Yaya Sahabee a ƙasan kuwa?" Buɗe ido tayi dantunawada abinda Maude ta faɗa mata tare da faɗin "a'a yayi tafiya yau" "yasan yau zaki zo kuma?" Tacea hankali, "ban sani ba fa" tace cike da son basar da zancen, fahimtar hakan yasa Salwa sakinzancen ta jawo wani, sosai suka sha fira har se da aka tsaida sallah a masallacin gidan sannantasallameta ta ajiye wayan ta kuskuro baki ta tada sallah .... Tana idarwa ta koma kan gado ta danna lambar Lurwanu, suna cikin magana telephone ɗingidaya ɗau ruri, sallaman shi tayi ta sauka ta ɗaga, "Ma dinner is ready" muryan wata matashiyar mace ya doki kunnuwanta "I'm okay" tace tare da ajiyewa ta koma kan gado, number Yayatadanna ta gyara zama.... Murmushi Yaya dake zaune a one sitter na general parlour ya saki tare da kallon su Farisat dakekallon shi, "ita ce!" Yasmin tace tare da kafe shi da ido, jinjina mata kai yayi tare da sakinmurmushi ya ɗaga ya kara a kunni, yana ƙoƙarin sallama tace "my Dear Yaya" murmushi yasaki tare da faɗin "zumuɗin ne ya hanaki sallama?" "I'm very sorry Yaya Assalamu alaikum" tacecikeda zaƙuwa, murmushi ya saki tare da faɗin "wa'alaikumussalam" "Yayana ka wuni lafiya?" "Alhamdulillah Insu baby ya Hajiya?" "Tana lafiya" tace a hankali, "me ke faruwa?" Yace a natse, "ba ma tare gida ɗaya" tace a hankali, murmushi ya saki tare da faɗin "kar wannna ya dameki, kema ba zaman gidan za ki yi ba, zuwa jibi za ki je school ki yi registration, sati me zuwa kumazaki fara ɗaukan lectures" yace a natse, "da gaske Yaya!" Tace kaman zata fasa wayan, "in sha Allah" yace fuska na ƙawatuwa da murmushi, "Allah ya kai mu Yaya, ya saka maka da alheri" "amen" yace tare da miƙawa Babiya dake ta sakin murmushi.. "Insiyyah" tace a raunane, "oh sarauniya Nafisat baki yi barci ba?" Tace cike da danne abindaketaso mata, "taya zanyi barci ban ji yanda ki ka sauka daga bakin ki ba" dariya ta saki tare dafaɗin"na sauka lafiya sarauniya Nafisat gani nan cikin aminci" "ma sha Allah haka Allah yaso zaki nesada mu, ba dadin ƙaddara na aure da ya jefaki ta can ba, ai da ba zamu rabu ba" tace muryanarawa, "sarauniya Nafisat ki ƙarfafa kan ki, ki daina bayyana damuwa" tace tare da goge hawaye, murmushi Babiya ta saki tare da miƙa wa Farisat wayan ... "Oh baby" tace da ƙarfi, "oh Mrs Salman Bukar" tace tare da sakin dariya, "ni ce nan faɗa daƙarfi, zan baki Ɓadamayya da kewaye" tayi maganan tare da sakin dariya, goge hawayen da ya zubomata tayi tare da faɗin "sun tarbeki da mutuntawa ko?" Share na ta hawayen tayi tare da faɗin"sosai, banyi zato ko tsammani ba, Anty Luba Anty Yasmin Anty Kausar Anty A'isha kowa yazotarbana, Uncle Jamil da Kamil gaba ɗaya kaman za su cinye ni dan farin cikin gani na" ta iddamaganan cike da tabbaci.... "Wow Insu nayi farin ciki, Uncle fa?" Tace a hankali, "baya nan, yayi tafiya, amma sun ce yakusadawowa" murmushi ta saki tare da faɗin "Allah ya dawo dashi lafiya, za muyi magana anjima" "to" tace tare da goge hawaye.... "Masoyiya!" Yasmin da ta amshi wayan tace murya na rawa, "sorry masoyiya kar ki yi kuka" tacea hankali cikin danne na ta kukan, miƙawa Nafisat wayan tayi da sauri tare da faɗawa jikinYaya, murmushi ya saki tare da fara hitting bayanta a hankali.... "Antyn Insu" tace a sanyaye, "na'am sarauniyan gidan Anty" tace a hankali tare da ɗaga wayankaɗan daga kunninta ta saki kuka mara sauti, jin Nafisat na faɗin "hello ki na jina?" yasatamaidawa tare da faɗin "ya school?" "Anty Insu yau fa ki ka tafi" tace a shagwaɓe, "to in yaunefa?Kar ki dai yi wasa da school" tace da kulawa, "in sha

Chapter 17 of 109