suka tattara suka koma cikin parlor aka buɗe babin hiran yaushegamo, kallon tafkeken agogon dake manne a bangon parlorn tayi tare da kallon Nafisat cikedabada umurni tace "raka Sa'eed ya kwanta dare yayi tsayi" jinjina kai tayi tare da faɗin "to" kokafin ta kai ga miƙewa Sa'eed dake kusa da Ibrahim ya miƙe a natse, miƙewa tayi ta ajiye Mairahdake jikinta suka wuce ɗakin da aka ware mishi, saurin tashi daga inda take Fadila tayi ta isawajen da Mairah take tare da duƙawa kusa da ita, ɓata fuska tayi tare da kallon ta, "oh sorrybaɗaukan ki zanyi ba Angel zuwa nayi mu san juna, sunana Fadila sistern ki, ke ya sunanki?" Taiddamaganan tare da miƙa mata hannu fuska yalwace da murmushi, "lallai kin fi kowa wawta Fadila, ai ba tayi wayon gane me ki ke faɗi ba" Kausar tace tare da sakin dariya, "oh Allah" tace taredakwaɓe fuska, murmurshi suka sakin mata ido akanta, juyawa ga Insu tayi tare da faɗin "yasunanta?" ko kallon inda take ba tayi ba bare ta sa ran samun amsa, "sunan su ɗaya da Hajiya" A'isha tace cike da farin cikin jin sunan Mairahn, "wow! Hajiya ashe takwararki ne, dama nagani
a diaryn Uncle yarinyar shi ta farko sunanki ne, na biyu sunan Mommyna, na uku Insiyyat nahuɗu Aminat, ma za kuma na ga Sadam Sa'eed da Abdussamad" ta idda maganan hankali
kwance, da mamaki Insu ta kalleta, ganin da gaskiyanta tayi maganan ya sata kauda kai taredasauke sassanyan ajiyan zuciya....
Miƙewa Alhaji Jamil yayi tare da faɗin "ina ga yakamata mu zo mu wuce yanzu" ya idda maganantare da kallon su Jabir, ba musu suka mimmiƙe, Fadila ce ma Lawiza ta fito" Ibrahimyacetaredakallon ta, da sauri ta miƙe ta nufi side ɗin su, ƙarisawa kusa da Mairah Jabir yayi bisa mamakinsuda ya miƙa hannu ta cafke, ɗaukanta yayi shima cike da ɗin bin mamaki, "Angel kin gane uncleko?" Yace cike da farin ciki, "shiii, shiiii" tace tare da yamutsa fuska, murmushi ya saki taredafaɗin "jini ba ƙarya ba" ɗago kai Insu tayi tare da faɗin "fitsari za tayi ka sauketa kar ta ɓatamakajiki" "oh shiii ɗin wai fitsari kenan!" Abubakar yace tare da sakin murmushi, murmushi ta saki
tare da kauda kai, "lallai uwa ta daban ce, yanzu har kin gane me take son yi?" Kamil yacemurmushi faɗaɗe a fuskan shi "Nabila ta shi ki kaita tayi" Lubabatu tace idonta akan Mairahn, miƙewa tayi zumbur ta nufeta tana miƙa hannu ta ƙanƙame Jabir tare da fashewa da kuka, "ohba ta so" Jabir yace tare da jijjigata, "ke wuce ta kai ki ki yi wallahi in ki ka yi a jiki se jikinki yafaɗa miki" Insu tace cikin ɗaure fuska, miƙa mata hannu Nabila tayi bi sa mamaki suka gatabatana ta, suna wuce wa, Jabir yace "yaushe ki ka koma haka Insu?" Murmushi ta saki tare da faɗin"inba haka aka mata ba ba zata yarda ba, kuma fitsarin ya matseta tun da ka ga tayi shii sobiyu"
jinjina kai yayi cike da gamsuwa tare da kallon Nafisat da ta shigo....
"Ya yi barcin?" Tace tare da kallon ta, jinjina kai tayi tare da faɗin "eh" "lallai yayi gado, hakamesunan shi ke da saurin barcin nan" Hajiya tace tare da sakin murmushi, "ai su biyu suka yi gadon, ita ma wannan haka take, tana kwanciya se barci" Insu tace tare da nuna Nafisat dake sakinmurmushi, "ina Mairah?" Tace tare da baza ido, "wow! Sunan da ku ke kiranta da shi kenan!" Asma tace tare da kallon Nafisat, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "eh" "gaskiya ya mundaɗi" tace cike da gaskiyanta, "a haɗa mata abinci ne?" Nafisat tace tare da kallon Insu, "kinga abincinne?" Tace tare da kallon ta, "ɗazu uncle ya si yo, tare da kayan sawa, ga wani ma a jikin mu" tacetare da sakin murmushi, kallon kayan jikinta tayi da kyau, tun fitowanta ta lura da kayanajikinsu, se dai tayi nauyin bakin tambayan a inda suka samo...
"Ki haɗa ki ajiye se anjima se ta ci" tace a natse, ba musu ta miƙe ta nufi ɗakinta fitowa tayi dababban basket ɗin dake cike da siyayan Mairah da babban leda, tsayawa tayi kusa da Insutaredafaɗin "ɗaki na nawa?" "Na biyu ɓangaren hagu" tace a sukunance, wuce wa sama tayi da ɗan
hanzari, tsayawa tayi cak saboda arba da hoton Insu da Anty da tayi, bin hoton tayi da idokamara lokacin ta san shi, "wow!" Tace tare da nufar shi a natse, shafa fuskokin su tayi cike da ƙaunaido na tara ruwan hawaye, se da ta gamsu dan kanta ta goge hawayen da suka ɓata mata fuskata wuce ɗakin, duk da tsarin ɗakin ya ɗau hankalinta amma bata ɓata lokaci wajen ƙare mai kalloba ta ajiye baske ɗin a inda ya dace ta juya ta fice....
Tana sakkowa ta tadda su Jabir sun fice, A'isha da Kausar da Lubabatu tsaye suna sallamanHajiya, takawa gaban Nabila dake saɓe da Mairah tayi ta amsheta a natse ta koma sama, "segobe Hajiya" Lubabatu tace tare da sakin hamma, "dan Allah gobe ku huta" Hajiya tace cikedagajiya da zirga-zirgan da suke a kwanakin, "ai haƙuri zaki yi Hajiya har a fice bikin nan" Kausar
tace tare da sakin murmushi, "to kuje dai" tace tare da nuna musu hanya, ba musu suka rankayasuka fice, miƙewa Yasmin tayi tare da faɗin "bari in watsa ruwa in zo ayi gashin ƙafan nan" taidda maganan tare da shigewa lungun da ze sada ta da bedroom's ɗin cikin parlorn... Mimmiƙewa su Nabila suka yi ko wacce tayi na ta ɗakin, kallon Hajiya Insu tayi tare da faɗin"Anty Yasmin ke tare da ke?" Murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "shekara ɗaya kenandadawowanta nan" "meyasa! Lafiya dai ko!" Tace cike da mamaki, "Allah yayi wa mijinta rasuwa" zare ido tayi da tsan-tsan mamaki tare da faɗin "Daddyn Fadila ya rasu!" Jinjina mata kai tayi
cike da tuna yanayin da suka shiga bayan mutuwan shi, "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahya gafarta mai, ina sauran yaran?" "Dangin babansu sun kwashe su, ita ma Fadila dan tunyanaraye ya ba ni ita ba dadin haka ba ba za su barta ba" "ba su kyauta ba, meyasa za su kwashematayar" "da ma da zuciya ɗaya suka kwashe su da ba abinda za mu ce Insu, amma ba tsakani daAllahba ne, duk dan ƙwaɗayin hawa kan abinda ya bari ne ya sa su aikata hakan, shiyasa da nagaabinze kai ga cin zarafi da mutuncinta na ce ta haƙura ta bar musu komai ta dawo gida, yara kuwainrayayyu ne duk wahalan da za su gana musu za su rayu" sauke wani ƙaƙƙarfan numfashi Insutayi
cike da zallan mamakin labarin...
"Ammi na haɗa yana can, zan kwanta" Nafisat da ta sakko tace idonta akan Insu, jinjina matakai
tayi tare faɗin "kar ki manta da alwala da azkhar, ki tabbata kafin ki kwnata kin yi sallahko
raka'a biyu ne" jinjina mata kai tayi tare da ma Hajiya se da safe ta wuce na ta ɗakin, miƙewaInsutayi a natse ta nufi Hajiya a natse ta kamata ta temaka mata ta miƙe suka nufi na ta bedroomɗin, tana zaunar da ita tace "ina kayan gashin?" "A'a barshi jeki ga yarinyar nan kar ta tsorata itaɗayaa ɗaki" tayi maganan cike da kulawa, murmushi ta sakin mata tare da miƙewa a natse ta
sallameta ta fice, da ido ta bi ta cike da so da ƙauna....
Tura ƙofan ɗakin Nafisat tayi a natse, ganinta zaune akan praymat da alamun idar da sallantakenan ya sata takawa ta shige ciki, miƙewa tayi ta naɗe darduman ta ajiye a ma'ajiyarshi tanufi
gado, tana hawa ta sakin mata murmushi tare da faɗin "se da safe Ammi" jinjina mata kai tayi
tare da bin ta da ido, tana tsaye a kanta har ta jiyo sauyin saukan numfashinta, kashe haskenɗakin tayi ta fice tare da kullo mata ƙofan, kai tsaye ta nufi na Sa'eed, ganin yanda yake barcincike da kwanciyar hankali ya sata rufowa ta nufi up stairs a natse.... Da sallama ta shiga ɗakin, da Mairah dake zaune dafi'an a saman gado tayi arba, murmushi tasakin mata me faɗi tare da rufe ƙofan baki ɗauke da addu'a ta nufeta, da sauri ita ma ta yunƙuradan nufarta, tana zuwa ta ɗauketa ta cillata sama tare da juyi da ita, banda ɓaɓɓakan dariyabaabinda take, se da ta ji jiri na niyyan kwasan su yasa ta tsahirtawa tare da haɗa fuskokinsuwajeguda, "wanann Mairahn waye?" Tace tare da girgiza kansu dake manne waje guda, "mailanmammy ne" tace tare da sakin murmushi, murmushi ta sakin mata cike da tausayinsu ita daFarisat da ta san tana cikin wani hali, "kina kewan Mommy ko?" Tace tare da kallon ta, "a jemammy" tace tare da kwaɓe fuska.... Ajiyeta tayi tare da faɗin "zaki je amma se kin fara cin abinci" tana kai nan ta jawo bowl ɗindaNafisat ta ajiye a bedside drower ta buɗe, jin da ɗumi ya sata faɗin "zo ki ci abinci" tayi maganantare da ɗagata ta zaunar da ita a jikinta, haka tayi ta feeding ɗinta cike da tsan-tsan sondatakedannewa dan nuna kara ga ƴan uwa da iyaye, tana ƙoshi ta maida shi ta ajiye ta goge matabaki
da tissuen data zaro ta kwantar da ita, jawo ledan da ke ɗauke da shopping ɗin da Jabir yamatatayi ta ciro kayan barci riga da wando masu taushi da laushi ta saka mata, maida ta tayi ta
kwantar ta miƙe ta shige toilet.... Ba ta jima ba ta fito da alamun alwala ta yo, murmurshi ta sakin ma Mairah dake ta lumsheidoalamun barci yana gab da kawo mata ziyara, wuce wa dressing room tayi ba ta jima ba ta fitosanye da dogon hijab, hayewa praymat tayi ta kabbarta sallah, tana idarwa ta zame hijabin, kayan barcin da ta sako ya nayyana, hayewa gadon tayi a natse ta jawota kusa da ita sosai tafarakaranto addu'a barci, tana gamawa ta tofesu ta ja blanket ta rage hasken ɗakin zuwa dumlight, "good night" tace a hankali hannunta na shafa kanta....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fourty six
"Bangane ba doctor!" Gude dake zaune a office ɗin doctor tace tare da zabura ta miƙe tsayearazane ta baza ma doctor dake zaune a gabanta ido, "please zauna ba wani abun firgici bane" yace a natse cikin son kwantar mata da hankali, girgiza kai tayi tare da faɗin "taya zan zaunadoctor! Magana fa ka ke na cire ma ɗana ƙafa!, Gurgu fa ka ke nufin ce mun ze zama"...
Ta idda maganan a firgice, girgiza kai yayi tare da faɗin "a'a Hajiya ba gurgu ze zama ba, pleasezauna in buɗe miki bayanin yanda zaki fahimta" yayi maganan tare da nuna mata kujerandatatashi a kai, zama tayi daɓas tare da sakin ƙaƙƙarfan numfashi me huci, tura mata bottle ɗinruwan dake gaban shi yayi tare da faɗin "please sha" ba musu ta ɓalle murfin ta kai baki dantanamatuƙar buƙatan shi....
Se da ya tabbatar ta ɗan samu natsuwa sannan ya gyara zama tare da faɗin "ba tun yanzubanafaɗa muku matuƙar ya cigaba da ma kan shi allura ze iya rasa wani gaɓa na jikin shi" "hakanedoctor se dai tun lokacin ya daina" tace murya na rawa cikin taren numfashin shi, jinjina matakai
yayi tare da faɗin "abun ya riga da ya shige shi, ya mai illan da mu kan mu ba mu hankaltadashi
ba se yanzu, matuƙar muka ce zamu cigaba da ba shi magani abun ze lafa ne kawai ammabazebar shi ba, sannan ze iya harba ɗayan ƙafan kinga ze yi asaran su gaba ɗaya kenan, ammainakacire wannan ɗayan da ta kamu za'a ɗaura shi akan magani yanda ɗayan ze kasance cikinaminci, sannan za'a saka mai ƙafan ƙarfe ze cigaba da hidiman shi ba tare da ya samu ko wacce matsalaba" ya idda maganan cikin son fahimtar da ita, bin shi kawai take da idon dake shatata da ruwanhawayen tausayi ɗanta.... Miƙewa tayi a sanyaye tare da faɗin "bari in yi magana da Babanshi tukun" tana idda maganantajuya ta fice zuciyanta na tsintsinkewa dan ta sadaƙar na Sudais ya zo ƙarshe, dan a yanda takawo shi ta san ya gama... Kai tsaye ɗakin da aka wuce da Sudais bayan gwaje-gwajen da aka yi mai da suka zo tayi tsayawatayi a bakin ƙofan ta zuba mai ido, banda asa-asan neman sassauci ba abinda yake ya jiƙesharkaf da zufa, tun daren jiya yake a haka, be rintsa dai-dai da na second guda ba, zama badaɗi
kwanciya ba ze yuwu ba, se dai yayi goho ya tirke ƙafan, goge hawaye tayi ta juya da sauri, "Mommy me suka ce!" Halima da idonta yayi jazur tace tare da kallon Gude da ke a rikice, girgizamata kai tayi tare da faɗin "ina waya na?" "Gashi" Nafi tace tare da miƙa mata, "kira Daddynku" tace tare da sakin hawaye ta jingina da bangon ɗakin.... Ba musu ta danna number shi ta kara a kunni, yana ɗagawa ta miƙa mata da sauri tare dafaɗin"gashi ya ɗaga" amsa tayi da sauri ta kara a kunni tare da fashewa da ƙaƙƙarfan kuka,
"subhanallahi lafiya kuwa Gude!" Yace a tsorace, "shikenan rayuwar ɗana ya ruguje, kumakai nesanadi, ka kashe mun ɗa da ranshi" tayi maganan cikin rishin kuka, "me ki ke faɗa ne haka! Meyasame shi! Kunga doctorn ne!" Ya idda magana a rikice, "ka zo ka ji abinda suke cewa akanshi, Sudais ze zama gurgu" ta idda maganan tare da zare wayan ta katse kiran cike da ɗin bintakaicinshi....
Zare ido Nafi da Halima suka yi a tsorace, se dai ba su samu zarafin furta tambayoyin dakemusukai komo a zuciyoyinsu ba, danna number Babiya tayi ta kara a kunni ƙirjinta na bugu da ƙarfi....
"Oh Allah waye kuma ke kwaɗamun kira da wannan safiya haka!" Babiya tace tare da ɗaukanwayanta dake kusa da ita ta bi number da ido, murmushi Baba Mari ta saki tare da faɗin"anyadasauran idon nan kuwa Hajiya?" "Ai ido kuma ya tafi Mari" tace tare da ɗagawa ta kara a kunni.... Kuka Gude ta saki me fidda sautin na shiga ukuna, "subhanallahi waye haka ke shirin tsaidamunda bugun zuciya!" Babiya tace a rikice, kuka Gude ta kuma saki tare da faɗin "Babiya!" "Nashigangaɗu Gude waya mutu!" Babiya tace a rikice, zuba mata ido Baba Mari tayi a tsorace....
"Babiya Sudais za'a cirewa ƙafa" tace cikin rishin kuka, "subhanallahi cire ƙafa kuma to akanme!
Meya sami ƙafan?" Ta jera mata tambayoyin a ruɗe, jan hanci tayi tare da faɗin "wai ƙafantaruɓe, tun shekaran jiya rabon shi da ingantaccen barci, na jiya yafi matsanta mai be yi barci bakwata-kwata se mabuga yake a parlor yana kukan ƙafa, shine yau da safe na kawo shi asibiti
suna gama gwaje-gwaje suka tabbatar da se an cire ƙafan dan ta gama ruɓewa" tana kai nantafashe da kuka, "ƙalu inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, wannan yaro ya ga jarabawa, a she ƙafar
nan ruɓewa take shiyasa yake ta rama da baƙi ba wanda ya hankalta, yi shiru bari in kira
Abdussamad gamu nan, asibitin da aka kwantar da shi kwanaki ne ko?" "Eh nan ne" tace muryaadisashe, "to gamu nan daina kuka yi ta mai addu'a, addu'anki tafiyayye ne" ta idda maganantareda sauke wayan da sauri....
"Kinga Mari kin fini sanin kan waya dubo mun number Abdussamad ya zo mu tafi" tace a rikicetare da miƙa mata wayan, ɗaga hannu da niyyan amsa tayi jiki a sanyaye Farisat ta kwaɗosallama, "shikenan gama Farisat nan zo ki kira mun number Babanku, dama flashing zanmai, dan bani da kuɗi a wayan" Babiya tace tare da kallon ta, "meya faru!" Tace cike da tsoro, "Sudaisaka kai asibiti za'a cirewa ƙafa" tace a rikice.... Me! Cirewa kuma!" Tace da mamaki, "wallahi yanzu uwan ta kira ni tana kuka gunun bantausayi, kira mun Abdussamad da Ali, yakamata mu je wajen nan" tace tare da miƙa mata hannu, taɓebaki tayi ta ɗago wayanta dake riƙe a hannunta ta lalubo number Yaya ta danna kira ta miƙamata.... Yana ɗagawa tace "Abdussamad kana jina?" Ko maida hankali ga amsa sallamanshi da yaɗayamata ba tayi ba, "eh ina ji Hajiya" yace cike da ladabi tare da sakin murmushi, "kana jina ko?" Takuma cewa a rikice, "eh Hajiya lafiya kuwa?" Yace cike da ɗan damuwa a muryan shi, "to
shikenan kana ji na ko Abdussamad?" "Eh" ya kuma cewa a natse, "yanzu Gude Yayarka takirani
tana kuka, wallahi in na ce maka ba ta tsinkar mun da zuciya ba na yi ƙarya Abdussamad"...
"Tana kuka me taɓa zuciya akan ɗan wajenta Sudais yana can yashe a asibiti wai za'a ciremai
ƙafa, shikenan ka ga ya cuci kan shi ya cuci uwarshi da ta damu da shi, uban dama ba abindayadame shi tunda har da shi a bada gudummawar sabauta rayuwar ɗan" ta idda maganancikedadamuwa, "subhanallahi yaushe matsalan ya faru?" Yace da damuwa, "kayya Abdussamadinafaɗa maka yanzu-yanzu ta danno mun kira kuma kana tambayar yaushe abun ya faru, toyanzu
haka suna can a asibiti ba a riga an shigar da shi injin da ze datse ƙafar ba" ta idda magananaƙufule, "Yaa subhanallah, Allah ya ba shi lafiya me inganci, bari zan tafi asibitin yanzu, kukumaHabibu ya kai ku tunda yana gidan" "to abinda yakamata kenan, dama ina jiran jin me zakacene, wannan dai asibitin da suke ta zirya da shi ne tun fara samun matsalan, bari in sa Farisat takiramun Ali shima in karanta mai abinda ya same mu da wannan safiya, amma wallahi Sudais yacuci
kan shi ya cuce mu, ko wannan tsinkewan zuciya da na yi ai an cutar da ni" ta idda maganantareda sauke wayan ta miƙa ma Farisat dake zaune idonta akanta, "kira mun Ali yaji halin da akeciki"tace tare da gyara zama.... Miƙa mata wayan tayi bayan ta danna mai kira tare da miƙe ƙafa kaɗan, amsa tayi da sauri takara a kunni yana ɗagawa tace "to duk inda ka ke Ali ka hanzarta zuwa asibiti, ɗan ƴar uwankagayi can za'a sare mai ƙafa, sun ce ba ze ƙara amfani ba ya ruɓe" tana kai nan ta zare wayantamiƙa ma Farisat dan ta san ya buɗe baki ba shirun kusa ba, murmushi Farisat ta saki dantasanme hakan ke nufi, katse kiran tayi ta ajiye wayan, "yana ɓude baki se Allah ni ba Gude ba yasauke takaicin a kaina, tashi mu tafi Babanku yace muje Habibu ya kai mu" ta idda maganantareda kallon Farisat.... Da mamaki ta ɗago kai tare da faɗin "ina!" "Ban san rashin arziƙi Farisat, asibitin mana" tacenata idon akanta, "ai ku je kawai" tace tare da sakin hamma, "yanzu ke saboda rashin tausayi yarona can cikin halin ha uwali ki ke gaba da shi!" Tace da ɗin bin mamaki, "gaba kuma! Akanme! Bazan iya zuwa ba ne, kin san doctor ta hanani motsi me ƙarfi" ta idda maganan tare da kishingiɗa, "ƙarshen motsi me ƙarfi jirgi ki ka hau ki ka je Ɓadamayya, se duba ɗan uwanki dake nan-nankusa da gida ki ke maganan an hanaki motsi" hamma ta saki tare da faɗin "Hajiya Nafisat ki
hanzarta kar ki ƙure lokaci har a shige da shi ba ki samu daman ganin shi ba, kambaki sanyandanayi jinya kwana biyun nan bayan dawowan mu ba, ni kaɗai na san halin da nake ciki, Allahyabashi lafiya me inganci ina gida ma zan iya mai fatan alheri ya kai mai har inda yake" ta iddamaganan hankali kwance....
"Ke dai da riƙo ki ke, daɗina da Insu kenan ba ta sakawa kanta wannan damuwoyin, Mari shiryomuje tunda tana gidan, ki kira sauran iyayen na ku ki sanar musu da halin da ake ciki" jinjinamata kai tayi tare da sakin hamma, wucewa ɗakinta tayi ta dau hijab ta fito a tsorace ta fice, dafamata baya Baba Mari da ta sako na ta hijabin tayi a hanzarce, sakin hamma Farisat da ta bi sudaido tayi tare da ɗaukan wayanta da ta ajiye kusa da ita ta danna number Insu ta gyara kwanciya....
"Wow!" Insu da ke zaune a two seater's Fadila zaune kusa da ita tace idonta akan iPad ɗindakeriƙe a hannunta, zura hannu kan screen ɗin Fadila tayi ta ja hoton da take kallo yayi samawani
ya bayyana a cikin idanun su, "dubi wannan Insu be burgeki ba dan Allah?" Ta idda maganantareda kallonta, "ba ƙarya kam, yayi kyau sosai" tace fuska faɗaɗe da murmushi, miƙa ma FadilaiPadɗin tayi tare da faɗin "gaskiya hotunan duk sun yi kyau" "mun gode" Asma tace tare da sakinmurmushi....
"Oh su Asma ba ko kunya, pre-wedding pictures ne fa" Nabila tace tare da kama haɓa, hararatadalla mata tare da faɗin "ko na Engagement ne Ina ruwanki!" Tace tare da kauda kai, "maidawuƙan amarsu" tace tare da sakin dariya saboda ta san ta gama kunnata....
"Insu kalli wannan ze yi kyau a calender's da bags na gift's ko?" Fadila tace tare da nuna matahoton Asma da mijin da zata aura wanda suka yi matuƙar kyau, jinjina mata kai tayi tare dafaɗin"sosai kuwa ze ƙayata su sosai" "Asma ki tura wannan ne a saka, in ya so wanda muka fiddadaseki ce a maida shi a wanda za'a ƙawata event's centern da shi ranar dinner" jinjina mata kai tayi
cike da gamsuwa, "Nafisat zaki gani ne?" Tace tare da miƙewa ta koma side ɗin saitin kujerundaNafisat ke zaune da Mairah a jiki ita da su Lubabatu dake ta tsara yanda hidiman gobe na
mother's day ze kasance....
"Ka wota anty Lawiza" Insu tace tare da miƙa ma Lawiza da ta zo wuce wa goye da yarinyartahannu saboda ayyukan da take, murmushi ta sakin mata ba musu ta juyo ta kwanto ta ta miƙamata, tana amsan yarinyar Mairah dake jikin Nafisat ta zame a natse ta tako cikin tafiyantanayara ta ƙariso wajen, ba wanda ya lura da zuwanta se kukan Insiyyah ƙarama da aka ji, da
mamaki suka kalleta, Mairah ne tsaye se tureta take fuska a yamutse, da mamaki Insu ta bi tadaido, saura kuwa dariya suka saki cike da mamaki, murmushi Lawiza ta saki tare da faɗin"dagaskiyanki Mairah ke baki lale abinki ba wata ta zo tana lale miki" ta idda maganan murmushi
faɗaɗe a saman fuskanta....
Ɗaure fuska Insu tayi tare da faɗin "wuce wajen Mami" kwaɓe fuska tayi tare da taɓewa alamuntana gab da sakin kuka, "zo ki hau abinki rabu da ita" Lawiza tace tare da cicciɓanta ta ɗauraasaman cinyan Insu, tana zama ta fara ture Insiyyah ƙarama buge hannunta Insu tayi tare dafaɗin"zaki sauka yanzu" fashewa da kuka tayi hannunta a kan Insiyyah ƙarama alamun ba ta dai
haƙura ba, ɗauketa Lawiza tayi tare da faɗin "rabu da ita" Lawiza tace tare da maidata a bayatagice fuska faɗaɗe da murmushi.... Kallon Mairah da ta wani lafe a jikinta tayi da mamaki dan ta san na ta mata hakan tare daƙoƙarin sauketa a jikinta, "Insu meyasa ki ke da saurin hannu ne wai!" Yasmin tace cike darashinjin daɗin sukan Mairahn da tayi, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "Anty Yasmin danfabaMommynta ne take wannan ɗafen, wallahi in ta na nan kallo ban isheta ba" ta idda maganantareda ɗaukan wayanta ta da ya ɗau kuwwa, "ƴar halak" tace tare da ɗagawa ta baza ma screenɗinido saboda video ne....
"Ina Mairah?" Tace tare da miƙewa ta can ta zauna, karama Mairah wayan tayi, tana ganinmemagana tayi saurin kai hannu biyu ta riƙe wayan kaƙam tare da faɗin "mammy" cike da yarinta, da mamaki suka kalli Insu, "dama tana magana!" Kausar tace cike da mamaki, murmushi Nafisatta saki tare da faɗin "tana kiran sunaye dai" "tana kuma gane mutane?" Lubabatu tace taredakallon Nafisat jinjina mata kai tayi tare da faɗin "eh" ita ko Mairah da ta haɗa ido da Mommynta
smile yaƙi ɗaukewa a saman fuskanta, se bin Farisat dake share hawaye take da ido cike dakewanta da tayi, "Mairahn Mommy ya na ga kin rame kin yi baƙi ne" tace cike da rauni, "eh" tacefuska yalwace da murmushi, "to dama na san za'a zo nan" Insu tace tare da kara kanta, "bamamata wanka ba kuma mu bata abinci ne" tace tare da sakin ƙaramar dariya....
"Duk abinda ku ke Allah dai na ganinku wallahi, yanzu Mami har dake ake zalintarta ko? Bantunanaki da hakan ba" tayi maganan da ƙarfi yanda Nafisat za taji, murmushi Nafisat ta saki batare da tace komai ba, "Mairah ba sa baki abinci ko?" Tace idonta akan ta, jinjina kai tayi taredafaɗin "eh" cike da yarintar ta, "Allah sarki Allah ya saka miki, Mami ba ta miki wanka ko?" Takuma jefa mata tambayan cike da gaskiyanta, nan ma da eh
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 69 Chapter of 109