office ɗin deputy chancellor admin, kallonta Nachma tayi tare dafaɗin"kina ganin hakan babu matsala kuwa?" Tace cike da ɗan shakku, kauda ido daga kanta tayi batare da tace komai ba, "Nachma ni ina ganin nan ɗin shi yafi dacewa, tunda daga inda yakamatamuje saƙon ya fito" Labib yace cike da son fahimtar da ita, jinjina kai kawai tayi jiki a mace, saukenumfashi Hisham yayi idon shi akan Insu da kaman ba ta san da wanzuwan su a wajen ba.... Umurnin da aka ba su na shiga na'ura ta sanar musu, ba wani ɓata lokacin ta murɗa handletashige suka dafa mata baya bakuna ɗauke da sallama, bin su da ido yayi cike da mamaki, "goodafternoon sir" Insu tace idonta akan shi, "afternoon how are you?" Yace tare da kauda kai, "I'mfine" tace a natse, gaishe shi suka yi kowa yaja baki yayi shiru ..
"Um'hum me ke tafe da ku?" Yace tare da ɗago kai ya kallesu, gyara tsayuwa tayi tare da faɗin"sir wani complain ne damu" "okay ba nan yakamata ku kawo ba, student's affair zaku, sukeda
alhakin kawo koken ku nan" yace idon shi na yawo a saman fuskokin su....
"Kaji ko" Nachma tace a hankali tare da kallon Labib, "sir kana nufin ba ma da daman zuwagareka matuƙar adalcin da can suka mana be gamshe mu ba?" Insu tace tare da kafe shi daido, ganin abubuwan da suke ƙumshe a idanunta ya sa shi faɗin "bismillah ku zauna" ba musutajakujera ta zauna tare da juyawa ta kalli Hisham da ya kasa zama, saurin jan kujeran yayi yazauna, su Nachma saka ja gefe suka tsaya, "ina jin ku" yace fuska a kame...
"Sir wannan ne me ƙorafin, sunan shi Hisham.." ta tsahirta tare da kallon Hisham, "Sharifudden" yace a hankali, "um'hum" yace a natse, kafin hutun ƙarshen shekaran nan an kafe sakamakoyafita da 3.49, second class lower, ƴar uwan karatun shi Sunaina Ahmad Yarban ta fita da 1.47passdegree, bayan dawowa hutu se ya samu kira saga students affair suka sanar mai da wancansakamakon da aka sanar mistake aka yi akan na shi, shi ke da 1.47 Sunaina na da 3.49, har sunyanke hukuncin akan ya koma 100level ya fara ɗaukan darasi daga farko, shine ba mu gamsubamuka zo jin ya aka yi mistake ɗin ta faɗa kan shi" ta idda maganan hankali kwance.... Bin ta da ido yayi cike da ɗin bin mamakin yanda ta zayyana komai ba tare da tsoro ko shakkuba, jawo waya yayi ya kira office ɗin students affair, ba tare da yace musu komai ba, ko mintinagoma ba'a ɗauka ba se ga shi ya shigo, miƙewa tayi da girmamawa ta ba shi kujeran da takekai, murmushi ya saki tare da zama idon shi akan deputy chancellor admin.... Nuna mishi su yayi tare da faɗin "sun kawo ƙorafi ne akan wani abu da ya faru" yayi magananidon shi ƙyam akan shi, "na'am inaji" yace a girmame, "akan wani mistake na maki ne ina ganin"
"oh tabbas daga can office ɗin tsara exams da fidda sakamako muka samu rahoton mu ma, munkira yaron mun sanar da shi abinda ya faru" yace a dake, "okay" yace tare da ɗaga waya yakiraoffice ɗin tsara jarabawa da fidda sakamako... Babu jimawa ya shigo a natse, miƙewa Hisham yayi tare da komawa gefen Insu, bayani yamai anatse, murmushi ya saki tare da faɗin "yallaɓai ai komai a bayyane yake, sannan haramunnebawa wani ƙoƙarin wani, wannan ne dalilin da yasa muka yi hanzari sanarwa dan kar mistakeɗinmu ya cutar da ɗaya daga cikin su, ina ga bayan wannan ba wani abu" ya idda maganan a
girmame, kallon Insu deputy chancellor admin yayi tare da faɗin "to kun ji, kuje ya dage dakaratu da maida hankali in sha Allah a gaba ze tsallake wannan matakin"...
"Sir kaman baka gane ƙorafin da muka kawo ba" Insu tace idonta ƙyam akan shi, ganin yakafetada ido ya sa ta fadin "gamsu akan mistake aka samu ne ba muyi ba, dalilin da ya kawo munankenan" tace a dake, "yanzu me ku ke so?" Yace fuska a ɗaure, "adalcin muke so, in ana somugamsu da abinda suka faɗa mana to a kira Sunaina Ahmad Yarban, ga HishamSharifuddentareda mu a basu questions ɗin ko wanne ya bada amsa, in Hisham ya faɗi zamu bar magananhar
abada ba zamu ƙara ta da ta ba" tayi maganan idonta ƙyam a kansu, "shut up my friend" mewakiltan students affair yace a tsawace, ko gezau ba ta yi ba bare a kai da firgita, "wacece ke da zaki tsaya kina tsara mana abinda zamu yi? Aikin ku kawo ƙorafi mara makamamu ɗauka ya kawo mu school ɗin? Ku wuce ku ɓacewa ganin mu, sannan daga yau kar muƙarajinmagana me kama da wannan a bakunan ku" yace a tsawace tare da nuna musu ƙofa da yatsanshi... Ko gezau Insu ba tayi ba dan ko sanin yana yi ba ta nuna tayi ba, se da ya gama banbaminshi tsafta kalli su Labib tare da faɗin "ku muje, in hagu ta ƙi se mu koma wa dama, rantsuwan da mukayi
akan tsayawa tsayin daka akan karatun mu, wannan rantsuwan ya shafi in aka tauye manahaƙƙinmu akan abinda ya shafi karatu mu ne mi adalci mu tabbatar da shi, mun san hanyar office
ɗin vice chancellor, sannan mun san chancellor gaba ɗaya, Alhaji Jamil Sadamko, sannanmemakarantar gaba ɗaya ma mun san shi, doctor Sahabee Sadam Ɓadamayya ba, ku muje zamunemi adalci a inda yakamata, dama mun zo ne dan sauke nauyi, tunda ba su shirya ba se muƙarisa wajen waƴanda ke shirye" tana idda maganan ta kama handle....
Tunda ta anbato sunan Alhaji Jamil suka tsure tana kiran me kankat duk suka baza mata ido, "kuzo, ku zo" me kula da abinda ya shafi jarabawa da sakamako yace ido waje, juyowa suka yi gabaɗayansu fuska a ɗaure kaman waƴanda suka haɗa baki, "wacece ke?" Deputy chancellor admin, yace a ɗan razane, "Insiyyah ƴar me sunan makarantar barrister Insiyyat Sa'eed Umar
Ɓadamayya" tayi maganan zuciya ɓace, haɗiye kakkauran yamu deputy chancellor adminyayi
tare da faɗin "yanzu me ku ke so?" "ba abinda muke so, zamu je inda yakamata" tace a dake, "kusaurara, ku fahimce mu ba muna nufin tauyewa ko wanne ku haƙƙi ba ne, amma ne ku a garemu, dan haka in ku ka fahimtar da mu a matse mu ma zamu nemo muku haƙƙin ku ba tare da wani
yaji ko ya gani ba" vice chancellor admin yace cikin murya rarrrashi.. Wani munafukin murmushi ta saki tare da faɗin "okay ai mun faɗa maka ƙorafin mu, a ba shi
haƙƙin shi se a zauna lafiya, in ya so ku ba wacce ku ke so first class in dai ba na mu ba ne" taceidonta na yawo akan su....
"Okay za'a gyara muku in sha Allah" yace tare da kallon ta, "maganan 100level da aka ce yakomakuma?" Tace tare da kafe shi da ido, "no ya cigaba da zuwa 200level din shi ba damuwa" baabinda tace se juyawa da tayi ta musu alaman su fita da ido, suna idda ficewa deputy chancelloradmin ya sauke numfashi me sauti tare da faɗin "kai ya muka yi da kai? ba na ce kar ka kuskuraka taɓa mishi marking shi ba?" Yayi maganan tare da kallon me kula da jarabawa da sakamako, "wallahi ban so taɓa ba, Minakshi ce ta matsa ta takura akan kar a barshi ya wuce, na yi taƙoƙarin fahimtar da ita amma ina taƙi fahimta" ya idda maganan kaman ze saki kuka, tsaki yajatare da faɗin "saboda ka zama shashasha se ta saka ka yin abinda ze tarwatsa rayuwarka, kacigaba da wannan gan-ganci tun da suka fara zuwa nan kai tsaye gaba office ɗin vice chancellorza su kai tsaye"....
Yayi maganan cike da ɗin bin takaici, "in sha Allah hakan ba ze sake faruwa ba" yace cike dafargaba, "daga ina yarinyar nan ta ke?" Vice chancellor admi yace tare da kallonsu, "Bertuwatafito amma kaman ta na da relation da vice chancellor" jinjina kai yayi tare da sauke numfashi "kusa ido akanta sosai, da alama tasan wani abu da ba kowa ya sani ba, sannan ku yi taka tsantsan da duk wani abu da ze haɗa rashin fahimta tsakanin ku" jinjina mai kai suka yi cike dafahimta, sallamansu yayi suka tashi suka fice....
"Wayyo Allah na, baby ina sanki kin ba su zufa da yawa" Nachma tace tare da sakin dariyataƙanƙameta, "kinga yanda vice chancellor admin ke sharan zufa kuwa?" Labib yace tare dasakindariya, sakin Insu tayi tare da faɗin "na shi ka gani, ba ka ga na barr Uzairu ba ne, ya kasa shaƙannumfashi me kyau" tace tare da ƙara fashewa da dariya, murmushi Insu ta saki tare da faɗin"Allah ya shiryi mara gaskiya" "amen, ai dama manyan mu na yawan cewa mara gaskiya bayadanatsuwa a ko ina yake, ji dai yanda ac ke ratsa office ɗin amma be hana shi haɗa zufa ba" Nachma tace cike da farin ciki, "wallahi haka ne, ba wanda ke da natsuwa a cikin su tundaInsutafara magana" Labib yace tare da kallon ta, "wai Insu a ina ki ka san me makarantan nanne?" Nachma tace cike da mamaki, "burga ne kawai" tace tare da sakin murmushi... Dariya suka saki gaba ɗayansu tare da kallonta, "Uncle ɗina ne" tace tare da bin su da ido, "serious!" Tace cike da mamaki, "yeah" tace tare da kauda kai, "no wonder" tace tare da sakinmurmushi, zare ido Insu tayi tare da faɗin "ƙarfe nawa?" Kafin Hisham da ya kalli tsintsiyanhannun shi ya ba ta amsa Nachma tace "barrister Tiyo!" "3: 47" yace a natse, jan hannunInsuNachma tayi da sauri suka yi department ɗin su...
Knocking suka yi tare da tura ƙofan a natse suka shiga, jawo Insu dake niyyan wuce wa wajenzamanta Nachma tayi da sauri tare da nuna mata barrister Tiyo dake musu kallon daga inakuke?Ƙumshe dariya yawancin ƴan class ɗin suka yi tare da zuba musu ido, dan sun san karonsudaBarr Tiyo...
"Daga ina?" Yace idon shi akan su, "sir daga office ɗin deputy chancellor admin" Insu taceanatsetare da kallon shi, da mamaki ya kallesu tare da faɗin "kun manta kuna da lecture ne?" "Nosir" Nachma tace tare da duƙar da kai, "Insu" yace da ɗan ƙarfi, "sorry sir" tace tare da baza mai ido, "ku wuce, kar ku kuma bari in rigaku shigowa class" jinjina kai suka yi tare da wuce wa da sauri.... Ba su sami fita daga class ba se da 5 ta buga, yana fita suka fara tattara komatsan su, masjidsuka wuce kai tsaye, sallahn la'asar suka gabatar suna fitowa suka tadda Khalimtsaye yanajiransu, harara ta banka mai tare da kauda kai, murmushi ya saki tare da kama kunnuwan shi cikedamagiya yace "sorry" dariya Nachma ta saki tare da faɗin "training ɗin har awa nawa ne?" Tajefamai tambayan suna ƙarisawa inda yake tsaye....
"Wallahi wani issue ne ya ta so mun nayi ƙoƙarin kiranku kuma ba wacce tayi picking phoneɗinta" "oh naji vibrating ɗin phone ɗina time ɗin muna office ɗin deputy chancellor admin" Nachmatace tare da gyara tsayuwa, "me ku ka je yi a can!" yace da mamaki tare da zare jakan dakebayanInsu, "wani issue ne amma komai ya wuce, ya training ɗin?" Tace da kulawa, "ba daɗi" yacetareda saɓa jakan....
"Yawwa Nachma ya maganan mu ne? Za mu samu fita a weekend ɗin kuwa?" Yace tare dakallonta, "da ƙyar gaskiya, Abba yace ze zo ban san ya zamu yi ba" tace tare da kallon su Labibdaketsaye can gefen parking space, kallon Insu da ba ta ce komai ba tun ɗazu tayi tare da faɗin"gafa
brothern ki can ya dawo bakin aiki" murmushi ta saki tare da kallon inda suke, "oh ance yafitadapass degree ko?" Khalim yace tare da kallon Insu, ɗaure fuska tayi tare da faɗin inji wa?....
"Ah maida wuƙan, kaman Minakshi na ji tana maganan" kauda kai tayi tare da faɗin "ka jawabudurwanka kunni, ta cire ido akan shi, wallahi tace za ta saka idonta akanshi se na ba ta
mamaki, shirmenta ya tsaya akan waƴanda suka ba ta fuska" ta idda maganan cike da takaici, "toa maida wuƙan ba ta nan" yace tare da sakin murmushi, "ai ban zarota ba tukun" tace taredasakin murmushi....
"Murmushi Hisham ya sakin musu tare da ba Khalim hannu, ba shi na shi yayi tare da faɗin"banganka wajen training ba yau?" Murmushi ya saki tare da janye hannun shi cike da murmushi yacegobe in sha Allah zan je" "Allah ya kai mu, Labib gobe ne wasan ku ko?" Ya mai maganantaredaba shi hannu, miƙa mai na shi yayi tare da faɗin "eh" "ku ƙoƙarta green club mayu ne" ƙaramadariya ya saki tare da faɗin "in sha Allah mu ma mayun ne" murmushi ta sakin ma Hishamdaketa sakin mata murmushi tare da faɗin "brother" "sister" yace cike da farin ciki, dariya NachmadaLabib suka saki tare da kallon su, "what guys!" Khalim yace tare da bin su da ido, tsagaita dariyanNachma tayi tare da faɗin "ba komai wani abu ne kawai ya ba mu dariya, ga Yaya Ibrahimnanyashigo" ta idda maganan tare da nuna motan dake nufo su, ɓata fuska Insu tayi tare da kaudakai, miƙa mata jakanta Khalim yayi tare da faɗin "se four za ki shigo gobe ko?" Jinjina mai kai tayi taamsa ta zage ta ciro atm ɗin shi ta ba shi, "amsa yayi tare da faɗin "banji alert ba" "na mantapin"tayi maganan tare da sallaman su Hisham ta wuce inda Ibrahim ya faka mota a natse, bintaNachma tayi tare da faɗin "please gobe karki manta mun da littafin nan" jinjina mata kai tayi
tare da buɗe motan ta shige, gaida Ibrahim tayi da mutumtawa, amsawa yayi da kulawa, bashi
hannu su Hisham da suka ƙariso suka yi cike da girmamawa, ba su na shi yayi da ɗin binkulawa, "sir" Khalim yace tare da salut ɗin shi, murmushi ya saki tare da ba shi hannu, gaisawa sukayi
cike da sabon da suka yi kafin ya ma motan key su nufi barin makarantar....
"Dan Allah ki daina mun tsawa haka, komai ya ƙare ba gani na zo ba" Sudais yace a tsawacetareda neman waje ya zauna, sakin baki Gude tayi tare da faɗin "in dai na maka tsawa kai kumaka
mun, sannu isashshe, wallahi baka isa ba Sudais, ina dai-dai da duk wani rashin mutumci dakake ji da shi, kai ba siɗiɗi ba kai ba siɗaɗa ba, in kira ka in nemi arziƙi akan ka zo ka kai ni wajeseka barni zaune ina jiranka kamar mara aikin yi, yau ko yaran maƙofta na nemi arziƙin suinadatabbacin a guje za su zo su kai ni, se kai nawa wanda nake da iko a kai" ta idda magananzuciyaamatuƙar ɓace, "da kin nemi arziƙin na su mana, hana ki nayi, dan Allah in zaki ki tashi na ajiyeki
akwai abinda nake son yi, in ba zaki ba in yi tafiya na, ke kenan kullum cikin gori da kunfar baki
da ƙorafi, wallahi za ki kashe kan ki da wuri in dai ba zaki dinga ɗaukan komai da sauƙi ba" yaidda maganan zuciya ɓace tare da miƙewa tsaye .. Sakin baki gaba ɗayan su suka yi tare da baza mai ido, "in ban kashe kaina ba ai kai zaka kasheni
Sudais, da ka ke wannan cika da batsewan da duka na kayi se in tabbatar da ka isa ka kawoƙarfi
Sudais, faɗa da tsawa ba ze gamsar da ni ba" tayi maganan tare da nufarshi, tsaki ya saki taredafaɗin "ke fa matsalanki kenan, wuce muje" ya idda maganan tare da juyawa ya fice daga parlourn, dafa mai baya tayi tare da gyara zaman mayafin jikinta.... Bata samu gamsuwar da take buƙata ba se da biyar na yamma ta buga, ɗaukan kayanta tayi tamaida a hanzarce ta nufi barin ɗakin, "ba dai tafiya za ki yi ba tun yanzu" wanda ke shinfiɗesaman gado yace tare da kallon ta, komai bata samu daman ce mai ba ta fice a hanzarce, tundata shiga reception me tarban baƙi ke bin ta da ido cike da mamaki, tana ficewa ya danna numberSalman da ya ba shi dan in ta fito ya sanar mai....
"Okay nagode" Salaman yace tare da sauke wayan ya kalli Yaya dake zaune a kujeran baya, kokafin yace wani abu Usman yace gata nan ta fito" yayi maganan tare da saita cameran wayanshi
ya ɗauketa hoto, "muje gida" Yaya yace ba tare da ya kallesu ba, "mu jira ta samu abin hawa" Usman yace tare da kallon Salman, "yakamata mu rigata isa gida" Salman yace tare da mamotakey ya fice da sauri....
Tsaida napep tayi ta shige tare da faɗa mai inda za ta, zaro wayanta dake neman agaji tayi anatse, ganin sunan Harira yasa ta ɗagawa tare da faɗin "kin tuna da ni yau kenan?" sautinmurmurshin ta ne ya bayyana rangaɗaɗau tare da faɗin "ina tune dake, yakike? In ba'a nemeki
ba bakya neman mutane" murmushi Sa'adatu ta saki tare da faɗin "kema ba neman mutaneki keba se ki na son sanar da wanj abu, yau kuma me ya faru da ki ka kirani?" Murmushi ta kumasaki
tare da faɗin "au sharrin da zaki min kenan?" "Ai haka ne" tace tare da sakin guntun murmushi, "to shikenan, dama kiran ki nayi in sanar miki an sako Baba yau, yanzu muka dawo daga gaisheshi" tayi maganan cike da farin ciki, shirun daƙiƙu tayi zuciyanta na bugu da ƙarfi, har ga Allahtama manta da lamarin shi sam, "hello ki na ji?" Tace da ɗan ƙarfi, "eh na ji, yana lafiya dai ko?" "Ehwallahi lafiyanshi ƙalau, mu da muke zaton ze rame se gashi da ƙibanshi, yaushe zaki zo?" "Zanzo, muna jarabawa ne in muka gama zan leƙo in ganshi" "shikenan Allah ya yardan miki" taiddamaganan tare da katse kiran, tsaki Sa'adatu ta ja tare da sauke wayan cike da takaici...
"Wato ka shirya ma wasan kenan? Karka damu na tanaji fili me yalwa da kyawu, zamu bugahankali kwance, se mu fidda gwani" tayi maganan zuciyanta na tafarfasa, "lafiya kuwa Hajiya?" Me napep yace da kulawa, "yi hidiman gabanka nawa nake yi" tace a harzuƙe, "Allah ya baki
haƙuri Hajiya" yace tare da maida hankalin shi ga tuƙi.....
"Wallahi na fara gajiya Abban Iman, na ce maka na iya ka ba ni key in dinga jan kaina ka ƙi, gashi
ai ka fara shanyani" Insu tace cike da taɓara, kallonta yayi tare da sakin murmushi, ɓata fuskatayi tare da kauda kai, "Allah ya huci zuciyar gimbiyan SSB, na isa in shanyaki, uzuri ne ya tasomun bakatatan" "uzuri!" Tace da mamaki, "eh wallahi" yace tare da danna horn, ana buɗemusugate ɗin farko ta bi wajen da ido cike da mamaki, kallon Ibrahim da ya amshi pass ɗin shi tayi
tare da faɗin "Abban Iman ya na ga gidan ya canza mun ne?" Murmushi ya saki tare da faɗin"dasaura ma se kin shiga ciki" "wow, meke faruwa?" "Ban sani ba, ni ma haka na taddashi" murmushi
ta saki cike da yaba kyawun da gidan ya mata ...
Yana taka burki ta buɗe ɓangarenta ta diro tare da faɗin "wow, kai wannan abun akwai laujecikin naɗi" tayi maganan tare da wuce wa ciki kai tsaye da sauri, sakin baki tayi tare da bin
parlourn da ido, ba abinda ba'a canza ba, murmushi Lawiza ta saki tare da faɗin rufe bakin" "AntyLawiza duka wannan bayan tafiyana makaranta ku ka yi!" Tace da mamaki, girgiza mata kai tayi
tare da faɗin "masu yi dai a ka kira, je ki shirya ki sakko ki ci abinci" jinjina mata kai tayi taredayin up stairs a guje, dariya Lawiza ta saki tare da nufar dining room....
Zaro waya Maude tayi ta danna number ta kara a kunni, "ina masu kula da tsaftan wajennan?Suzo su saka turare" tace tare da amsa sallaman da aka ɗaga mata a girmame, "ina jinki Maude" muryan Hajiya ya bayyana rangaɗaɗau, murmushi ta saki tare da faɗin "dama na ce hajiyakoza'asakko da Insu ƙasa ne?" Tayi maganan a ladabce, saurin tsayawa Lawiza da ke shirin gittawajentayi cike da mamaki, "meyasa!" Hajiya tace da mamaki a muryanta, "Alhaji Munnir ya kira yaceasama yallaɓai ze sauka, shiyasa na ce bari in tambaye ki ko ita za ta sakko ƙasa ne?" "A'a bartaainda take" tace a daƙile, "to shikenan Hajiya" tace a natse ba din ta so hakan ba, "ya shirye- shiryen?" Tace a natse, "Alhamdulillah Hajiya an kammala komai se abinda ba'a rasa ba" "tomasha Allah mu ma gamunan tafe, su Jamil sun je tarboshi jirginsu ya sauka" jinjina kai tayi cikedazumuɗi tare da faɗin "Allah ya iso da su lafiya" "amen" tace tare da sauke wayan...
"Oh Allah, ai se ta zaunan, in dai yallaɓai ne da kan shi ze fatattako ta ƙasan, shi da ko tv bayasoya cika ƙara da yawa bare wannan da ba ta zauna waje guda ba, rawan kanta yafi ta ƙarfi cakwai-cakwai baki baya hutawa" ta na idda maganan ta wuce ta nufi kitchen ganin ko sun kammalaabubuwan da ta sa su, girgiza kai Lawiza tayi ta fice daga parlorn..... A hanzarce ta watsa ruwa ta fito, shirya wa tayi cikin wando pencil brown colour da milk ɗinrigathree quarter, tattare gashinta tayi a tsakiyan ka ta saka mai ribom, baby hijab brown ta sakatare ta fesa perfume, da sauri ta juya dan ficewa, zare ido tayi tare da juyowa ta ɗau nostril
brown me adon butter fly ta maƙala ta fice a guje, tana sauka Lawiza na shigowa, "wowAntyLawiza kun gama burge parlorn up stairs da yawa, me ke faruwa ne?" Murmushi ta sakinmatatare da faɗin "muje ki ci abinci, kinyi matuƙar kyau" murmushi ta saki tare da rumgumetakaɗancike da farin ciki zare jikinta tayi tare da faɗin "ba na jim yunwa sosai yau, me ake shirinyi a
gidan haka?" "Me gidan ne ze yi aure" Maude tace tare da kafeta da ido, sakin baki tayi cikedamamaki...
Tun a hanya suka sauke Usman, suna shiga gida suka tadda su gaba ɗaya a general parlor sunata kwasan shafta, "yawwa ga Yayan nan ya dawo" Sadam yace tare da sakin murmushi, "Abdussamad lafiya kuwa?" Babiya tace idonta akan shi, maida duban su gare shi suka yi gabaɗayan su, ganin yanda suke bin shi da kallon zargi ya sa shi sakin guntun murmurshi taredafaɗin "lafiya lau" ɓata fuska Yasmin tayi ta miƙe ta nufe shi tare da taɓan goshin shi da wuyanshi, jin jikin shi ba zafi ya sata faɗin "gajiya ne ko Yaya?" Tayi mai tambayan da kulawa, shafa samanfuskanta yayi tare da jinjina mata kai, "muje in haɗa maka ruwa ka watsa ze ragu" tace taredariƙe hannun shi, miƙewa Nafisat tayi zunbur tare da faɗin "yau ni ce da wannan ladan" dariyasuSuwaiba suka saki tare da bin su da ido...
"Lafiya bro?" Sadam yace idon shi akan Salman, sauke numfashi me sauti yayi tare da faɗin"lafiya, ya school ɗin?" "Fine, tace wai ba kuje gwajin ba?" Yayi maganan tare da nuna Farisat, jinjina mai kai yayi tare da kallon ta, "ku yi haƙuri kawai da wannan gwajin tunda yaƙi yiwuwa" yace cike da rashin ba ma abinda ya faɗa mahimmanci, "a'a aiko za su yi, uzuri ne ya hana hakanfaruwa" Habiba tace tare da banka mai harara, murmurshi ya saki tare da kauda kai, "mudanamu ma da saura, har munyi mun wuce wajen" Balarabe yace tare da kallon Salman, "mujeYaya" Yasmin tace tare da kallon shi, "Anty Sa'adatu oyoyo" Umar yace tare da tashi yayi indatake tsaye a guje, juyawa Yaya da Salman suka yi tare da zuba mata ido ... Murmushi ta saki tare da faɗin "oyoyo Auta" ta idda maganan tare da ɗaga shi sama, saukeshi
tayi tare da sakin mai murmushi, "ina tsaraban da ki ka ce zaki kawo mun?" Yace tare da kallonta, murmushi ta saki tare da zare ido cike da ɗan tsoro-tsoro tace "na manta" tayi maganantareda shagwaɓe fuska, ɗaure fuska yayi tare da faɗin "ba ruwana dake" ya juya fuska, murmurshi tasaki tare da takawa ta shige gaban shi, zaro chocolate tayi a aljihun jakanta tare da faɗin"konabaka wannan?" tayi maganan tare da nuna mai, ɗago kai yayi fuska faɗaɗe da murmushi taredakai hannu ze amsa, saurin kaudawa tayi tare da faɗin "na fasa baka tunda mun ɓata" girgizakai
yayi tare da faɗin "ina yi dake" dariya ta saki tare da ba shi, amsa yayi ya wuce da sauri, dariyasuka saki tare da bin shi da ido, "ɗan nema, wato kana yi da ita tunda ka ga cakuleti" Babiyatacetare da kallon shi ...
Zare takalmi tayi fuska faɗaɗe da murmushi ta wuce ta shiga ciki, "Anty Suwaiba sannudazuwa"tace tare da shirin wuce wa bedroom ɗin ta, "daga ina kike?"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 29 Chapter of 109