lokaci a haka yasa Jabir matsowa tare da faɗin "ranka yadaɗe lokaci ba ya jira" ɗago kai yayi ya dalla mai harara tare da zareta a natse, riƙo hannuntayayi
ya ɗago ya sumbata, murmushi ta saki tare da bin fuskan shi da ido, "ke ce fatana da na
al'umman dake ƙarƙashina, dukkan farin cikin mu mun damƙa shi a hannunki, ki kula dashi
kamar yanda zaki kula da Nafsiinki" jinjina kai tayi cike da fahimta, murmurshi ya kuma sakinmata tare da sakin hannunta a natse, "muje please" Jabir yace tare da nuna mata hanya, bamusu ta shige gaba, da sauri security's suka wuce dan buɗe mata kofa....
Tana shiga ta sauke glass ɗin ƙofan gefen da ta zauna tare da ɗaga murya da ƙarfi cike datsantsan gaskiyanta tace "nayi maka alƙawarin sake nuna maka fuskata bayan nasaran da nakefata"murmushi ya sakin mata tare da jinjina mata kai, murmushi ta saki ta juyar da kai a natse, daazama driver ya ja bayan shigan da Jabir da security's suka yi suka ɗau hanya tare da rakiyan
jami'an tsaro....
Suna shiga farfajiyan court ɗin ido ya dawo kan jerin gwanon motocin da suka shigo wajen, dahanzari security's suka diddiro suka buɗe mata ƙofa a girmame, a natse ta fito hankalintaakanmaganan da Jabir ke mata, da sauri Habib ya ƙariso hannu riƙe da cikakken kayan aiki, warwarewa yayi ya kara mata ta baya, miƙa ma Jabir system da wayan dake hannunta tayi ta sakahannaye, tana gama sakawa ta gyara zaman shi a jikinta ta amshi hulan da yake riƙe dashi tasaka, murmushi ta sakin mai tare da faɗin "kar ka ce ni ce makararra?" Murmushi ya saki taredafaɗin "to da alama, tunda Nachma ma dai ta rigaki" "anya ba'a Ɓadamayya ta kwana ba!" Tacetare da kama haɓa...
"To ko dai a ina ta kwana ga ta dai a court yau" yace tare da sakin murmurshi, murmurshi tasaki
tare da faɗin "ina barrister Hisham?" "Gani kusa ranki shi daɗe" yace tare da bayyana kanshi
fuska cike da murmushi, harara ta dalla mai tare da faɗin "amshi wannan yakamata ku dubakafin mu kai ga shiga shari'an" ta idda maganan tare da amsan system ɗin hannun Jabir tamiƙamusu.... Tana gab da shigewa inda aka tanada mata kafin fara sauraran shari'an ta jiyo saukan muryanFarisat cike da alfahari, "barrister Insiyah Abdussamad Umar Ɓadamayya barka da safiya"
juyowa tayi fuska ɗauke da matsanancin murmushi tare da faɗin "Malama ƴar jarida in banganki
a wajen nan ba ai se na yi mamaki" murmushi ta saki tare da ɗaga hannu cike da san wankekai
tace "karkashin campany na zo, ba gaban kai na nayi ba" murmurshi ta saki tare da faɗin"inatakwara!" "Tana wajen abokan aiki, hango zuwanku nayi na ta so" "to bismillah my shiga ciki" tace tare da miƙa mata hannu, ba musu ta kama suka shige a natse.... Mimmiƙewa suka yi a tare idan su akan babban Alƙalin da ya shigo, ba su zauna ba se da yazauna a saman kujeran aikin shi, miƙewa maga takarda yayi ya koro bayanin ƙaran da waƴandaake ƙaran da abinda ƙaran ya ƙumsa sannan ya wuce ya ajiyewa Alƙali takardan, jawowa gaban
shi yayi ya duba sama-sama kafin ya ɗago ya buƙaci ganin lawyern me kare waƴanda akeƙara, miƙewa yayi ya gabatar da kanshi cike da sanin makaman aiki....
Jinjina kai yayi alamun gamsuwa tare da tambayan lawyern gwamnati waƴanda za su tsayawamasu ƙara, miƙewa Insu dake nazartan takardan dake gabanta tayi tare da faɗin "sunana
barrister Insiyyah Abdussamad Umar Ɓadamayya lawyern gwamnati, a tare dani akwai" taiddamaganan tare da nuna jerin su Hisham, miƙewa Hisham yayi tare da faɗin "barrister HishamSharifudde Bertuwa lawyern gwamnati" "barrister Habib Muhammad Ɓadamayya lawyerngwamnati" "barrister Nachma Kabir Yarban lawyern gwamnati" suna kai nan suka zaune tareanatse....
"Bismillah" Alkali yace idan shi akan shi, miƙewa lawyern su Alhaji Namadi yayi tare da faɗin"yame girma me shari'a, kafin in ce wani abu ina so court tayi duba na tsanani akan wannanƙara, bakomai ba ne illa yarfe da san ɓata suna na bayin Allahn nan, kowa yasan su waye su, jajirtattunmutane ne masu yaƙi akan farin cikin mu da kwanciyar hankulan mu, duk tatsuniyar gizodaƙoƙi
suka karanto, babu wani ingantaccen sheda ko hujjan da ke tabbatar da waƴanda ake ƙarasunaikata abinda ake tuhumar su a kai, kar mu ɓatawa court lokaci akan labaran ƙanzon kurege, iname kira a court da ta zubda wannan ƙara dan baya da wani ma'ana bare fa'ida" ya idda
maganganun cike da rainin da ya ma su Insu...
"Matsayinka na wa!" Nachma tace a dake tare da zuba mai ido, "matsayina na wanda ya gajiyayaga yau a cikin aikin" yace a zafafe tare da banka mata harara, guntun murmurshi ta saki taredakauda kai, "a court ku ke ba a filin faɗi ra'ayinka ba" alƙali yace tare da musu kallon gargaɗi, haƙurin suka ba da cike da girmamawa, "shin lawyer's ɗin gwamnati suna da abin faɗi?" Alƙali yace a natse...
"Eh ya me girma me shari'a" Hisham yace tare da miƙewa, fitowa filin wajen yayi tare da faɗin"ina ga lawyern da ke kare waƴanda ake ƙara ya manta da aikin shi, mutanen da ake ƙara basuwahalar da shari'a ba, sun amsa lefukansu hankali kwance ba tare da tursasawa ba, sannanumurni da yake akan yanke hukunci kai tsaye ina ga ya sha'afa akan lawyer ne shi ba alƙali ba" murmushi ya wancin jama'a dake cike a ciki suka saki tare da zuba mai ido, murmushi ya saki
tare da komawa ya ɗakko system ɗin gabanshi ya haɗa da babban allon tvn dake wajen, kai
tsaye fuskokin su ba Alhaji Namadi ya bayyana a white house lokacin da suka kai ma SSBziyara....
Sakin baki da ido gaba ɗaya jama'an dake cike a wajen suka yi cike da razani kalaman sunaƙarahaddassa musu tsana da ƙyamansu, cike da mamaki Jabir ke kallon Insu dan ba su san ta naɗi
tattaunawan ba, jinjina kai Alƙali yake cike da ta'ajibi, baza ido lawyern su yayi hankali a muguntashe dan duka ɗaya suka mai wanda ya ɗauke duk wani kalaman bakin shi... Dakatar da videon yayi tare da faɗin "ya me girma me shari'a, su suka kai kan su, sannansukafaɗi lefukan su da bakunan su ba wanda ya tilasta musu ko tirsasa su saɓanin soki burutsundalawyern me kare waƴanda ake ƙara ya tashi yana yi" yana kai nan ya koma mazaunin shi yazauna, miƙewa Insu tayi a natse tare da fiya tsakiyan wajen cike da zaƙwaƙwuranci tace "yamegirma me shari'a, abubuwa da dama sun faru a shekarun baya lokacin da mutanen nan kemulkan mu".... Mu talakawa ƙasa mun wahaltu da abubuwa da dama, "yunwa! Ƙishi! Cutuka! Fargaba! Zillimi!
Gaba ɗaya waƴan nan abubuwan ba wanda be kasance abokin ƙut da ƙut a gare mu ba, abinci
yayi tsada, talaka be samu dama siya, wasu gidajen sau ɗaya suke ji a rana, shima daƙyar akesamu a saka ba'a maganan ƙoshi ko daɗi a ci dai gudun kar a mutu, wasu na jigata wasunamutuwa, wasu na mawuyacin hali cikin fargaban rayuwa ko mutuwa, duk yunwa ya haddasahakan me shari'a, abinci yayi tsada, ruwa yayi ƙaranci, duk ta dalilin su, suna sane da duk abindake faruwa a ƙasar kuma suna da maganin da su ze kawo ƙarshen komai amma sun ƙi ba dawasuna kwance a gida su da iyalansu cikin AC suna hangen yanda muke mutuwa a labarai"...
"Ilimi yayi ƙaranci, sun kwashe duk dukiyan mu wanda za'a gina mu sun gina makarantunpriavetsun zuba nagartattun malamai suna gina su su da iyalansu ba tare da shan wahala ba sunagidakuɗaɗenmu na tseren shiga account's ɗinsu da suka buɗe a ƙasashen ƙetare, ilimi ya zamanamasu dashi se ɗan wane da wane, ya me girma me shari'a haƙƙin mu suka tauye suka ginakansuda ƴaƴansu, ko wannen su ya tara kuɗin da ba jikan jikanshi ba tattaɓa kunnin jikan shi mabashi
ba talauci kuma duk haƙƙin mu ne" ta tsahirta maganan tare da baza kuɗaɗen dake cikinaccount's ɗin su a majigin da ta kunna ko wanne account da hoton mamallakin shi a ciki, juyawaga alƙali tayi tare da faɗin "ya me shari'a ta'addanci, fasa ƙwari, tada zaune tsaye, duk sunesilarfaruwan su a ƙasar nan, sun hana mu abinci sun hanamu ilimin da zamu dogara da kai, sannankwanciyar hankalin da suka hangemu da shi shima sun ɗaura ɗammaran kwaceta daga garemu"....
Tsaro yayi ƙaranci, takala be isa fita neman halalin shi ba yana gudun ya fita a kama shi, koatashi bom, tsoron shi ba na mutuwa ba ne dan ya daɗe a mace, tsoron shi shan wahala nemeshari'a, mu fita makaranta aka ma mu, mata a keta wa wasun mu haddi, a maida wasunmukaruwai, wasun mu a saka musu cutan da har su koma ga mahaliccin su suna shan wahaladashi, iyayenmu su fita nema a farmake su, a wajen sana'an su a farmake su, su dawo gida a farmakesua cikin gidajen su, su fita masallaci a tashe su da bom, shin ina ake san talaka ya sa kan shi" tatsahirta tare da bin fuskokin su dake ɗauke da damuwoyi da ido....
"Kayan maye su ne, suke shigo mana da dukkan wasu mugayen makamai da ƙwayoyin maye, sungurɓata mana ƴaƴa, ƙanni, yayyi, iyaye, duk saboda wani manufa na su ta daban, sun juyamanaƙwaƙwalwa yaran mu, sun birkita musu natsuwan su, sun cutar da lafiyarsu, su dai waƴannanɗin dake gabanka ya me shari'ar, su ba su ƙwaya su sha su miƙa musu makamai su fito tsakiyangari suna kashe ƴan uwan su da ba su ji ba ba su gani na, alƙawari suka yi akan kare manalafiyarmu, ilmantar damu, kare hakkin ko wannen mu kafin mu kai ga dangwala musu ƙuri'ummu, sedai babu ɗaya da suka sauke, sun ci amanan mu, sun karya mana ƙashin bayan mu, sun cutar dalafiyan mu, sun kwace mana goben mu, duk hakan be musu ba sun sa muna kashe junanmu, sunkoma gefe suna bin mu da ido suna dariya" tana kai nan ta saki ƙananun videon su inda sukeba
ma matasa maka mai da inda suke ba su ƙwayoyi, da inda suke tattauna hare-haren da zasukai.... Gaba ɗaya jikkuna ya ɗau ɓari cike da mamaki, ashe su ba ma su fahimci illan da mutanensukamusu ba, a duhu kawai suke, juyawa tayi ga Alƙali tare da faɗin "shari'an mu abuɗe take kamar
yanda barrister Hisham Sharifudde Bertuwa ya faɗa tun farko, waƴanda ake tuhuma ba suwahalar da kowa wajen amsa lefukan su ba, sannan mun gabatar da hujjojin gani da ido, wandake bayyana su, babu ƙage a ciki ko wani abu me nuni da haɗawa aka yi dan musu yarfe, inaroƙonwannan kotu me daraja da gaskiya da ta duba zantukana da hujjojina ta mana adalci dagaabindaazzaluman mutanen nan suka mana" tana kai nan ta koma mazaunin ta ta zauna....
Shiru kotun ta ɗauka, baka jin komai se jaye-jayen numfashi da saukewa, sauke ajiyan zuciyamesauti alƙali yayi idan shi akan su Alhaji Namadi dake ta zare idanu suna goge zufan dake karyomusu, "shin lawyern waƴanda ake ƙara yana da ja dangane da hujjoji da bayanan da lawyer'sɗingwamnati suka gabatar?" Alƙali yace idan shi akan lawyern su, girgiza kai yayi tare da gogezufan goshin shi tare da miƙewa yace "babu" gyara zama alƙali yayi tare da faɗin "ga hukuncincourt bisa kundin tsarin dokoki na ƙasa"....
"Kotu!" Suka ce gaba ɗayansu tare da mimmiƙewa, rungume Insu Nachma tayi cike da farinciki
tare da faɗin "congrat friend!" Murnmushi ta saki tare da dukan bayanta cike da farin ciki tace"congrat friend" zame jikinta tayi tare da faɗin "sheɗanu a tafi inda aka tura dubban nanal'umma, hukuncin duniya kenan saura na lahira ɗiyoyin asara" dariya Habib ya saki tare dafaɗin"ba zaki musu video ba za'a tafi da su" ya idda maganan tare da nuna mata su, kai dubansugaresu suka yi zukata fes, tasa su jami'an tsaro suka yi dan ficewa da su daga wajen, "a sauka lafiya" Nachma tace cike da takaici ...
"Anya Nachma in aka baki hukuncin ba da hannunki zaki yi ba" Hisham yace tare da kamahaɓa, "ni fa ba zan jira satin da aka ce ba wallahi a yau za su tafi" dariya ya saki tare da faɗin "toai satinda aka bada dan su maidawa ƙasa abubuwan da suka sata ne, ana kawo wa court za ta tattarakomai ta miƙawa gwamnati dan cigaba da gyara ƙasa" "auh da sauƙi" tace tare da sauke ajiyar
zuciya....
"Taɓ ashe kema wuta ne!" Habib yace tare da kama haɓa, "da me ka ke zato!" Tace tare dabankamai harara, "a huce haka" yace tare da sakin dariya, juyawa Insu da fuskanta ke yalwace damurmushi tayi dan ɗakko karikitan ta, a hanzarce Jabir ya iso wajen tare da faɗin "ku tsahirtatukun a wuce da mutanen nan, wajen babu lafiya, al'umma na ta kiciniyar ƙwatan masulefindaga hannun jami'an tsoro!"....
"Subhanallah!" Insu data ɗago tace cike da damuwa, "no babu wani matsala yanzu za suwucedasu se ku fita, "yakamata a ƙara jami'ai" tace tare da kallon shi, "abinda ake ƙoƙarin yi kenan" yacecike da tabbaci, "okay ina Farisat!" Tace tare da baje mai ido, "gani me zaki mun?" Farisat dataisowajen rungume da little Insu tace tare da baje mata ido, "na san karanbanin ku na ƴan jaridane, yanzu se ki ce zaki ɗaukan rahoto" tace tare da sakin murmushi, "wane ni! Ai ban shirya samyJannah kuka ba" tace tare da sakin murmushi, "ah to in ma kin shirya ai ba wani abu haƙuri zamuba shi bayan addu'an uku mu ne mo mai wata ƴar safai-safai mu miƙa mai shikenan" Insutacetare da danne dariyarta, harara ta banka mata tare da faɗin "baki da kirki fa!" "A'a ba dai kunesarakan karanbani ba" tace tare da bin ta da ido, "kuma dai brother Allah ya yi mai farinjini, acikin masu zuwa gaisuwa ma za'a dace" Hisham yace tare da tintsirewa da dariya, banka mai
harara tayi ba tare da tace komai ba, "ah gaskiya ne fa, in ba'a so a rage karan bani kawai" "anyaHisham!" Habib yace tare da kama haɓa, "ƙyalesu kin ji sister ke da shi mutu ka raba in shaAllahse kun tsufa tare" Nachma tace tare da kallonta fuska cike da murmushin ƙauna, "a'a fa" Insutace tare da kallon ta, "barsu su mata alƙawarin kizo, wallahi kar su lasa miki zuma a baki ki ji
zaƙi ki ga kaman ba za su zare ba, babu ruwan mu" Hisham yace tare da sakin dariya, "ohbayinAllah!" Nachma tace tare da kama haɓa, "rabu da su sister" Farisat tace fuska yalwace da
murmurshi, "to in ba mu faɗa mata gaskiya ba wa take da shi da ze faɗa mata" Insu tace taredamiƙa mata hannu, saka mata little Insu tayi tare da faɗin "ku fara faɗawa kan ku tukun" dariyasuka saki tare da bin ta da ido....
Comments fans 🙏🥰
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Sixty Nine
Last page🤗... Ta waje kuwa ba ƙaramin gumurzu aka sha tsakanin al'umman ƙasa da jami'an tsoro akankaresu Alhaji Namadi ba, daƙyar suka shigar dasu cikin mota bayan jina-jina da suka musu, bandajannumfarfashi daƙyar ba abinda suke dan da gaske jama'an suke na abarsu su kashe su da
hannayensu, ko za su samu sassauci daga baƙin cikin da suka dasa musu..... Daƙyar suka ja motoci a guje suka bar wajen dan yanda suke harzuƙowa suna jifan gilasanmotocin da duwatsu suna fashewa, su kansu jami'an tsaron sun tsorata dan a yanda sukezasuiya haɗawa da su ma ba su sani ba... Kai tsaye prison aka wuce da su, inda za su yi zama sati guda kafin kotu ta haɗa duk wani dukiyarda sukayi rubda ciki akai ta damƙawa gwamnati dan cigaba da ma ƴan ƙasa aiki sannana
ƙaddamar musu da hukuncin kotu na kisa ta hanyar rataya,....
"Ku taso muje" Jabir da ya dawo da jami'an tsoro da security's yace tare da kallonsu cike daalfahari, ba musu suka rankaya cikin zoben da jami'ai suka musu suka fice, suna fita ruwancamera's ya fara haska fuskokin su, nan journalist's suka yunƙuro dan tattaunawa da su, sedai
jami'an tsaro sun hanasu ƙarisowa gare su, har mota suka raka Insu, tana daidaita zama Farisat
ta amshi little Insu suka yi sallama ta wuce wajen abokan aikinta tare da rakiyan Jami'ai, sallamada su Hisham tayi suka wuce motocin su tare da rakiyan jami'ai, "muje" Jabir da ya shiga kusadaInsu yace tare da kallon driver dake jiran umurni, jan motan yayi a natse ya ɗauki hanya sauranmotocin dake cike da jami'ai da security's suka dafa musu baya....
Tana kai jiki a general parlorn taji an suntumeta an ɗagata sama an fara juyi da ita, saninwandaze iya aikata hakan ya sata ƙanƙameshi tare da ɓaɓɓakan dariya, se da ya gaji dan kan shi yasauketa ya jawota jikin shi sosai saboda sanin jiri ze iya kamata, "Congratulations!" Jama'adakecike da parlorn suka ce muryoyin cike da farin ciki, ɗago kai a natse tayi ta zube musu idanundake cike da hawaye, kallon fuskokin su dake cike da murmushi me ɗauke da tsan-tsanƙaunadaalfahari take a karye, sakin hawayen da suka cika mata ido tayi tare da matse jikinta a nashi, sumfutan ta yayi ya manna ta da kirjinshi ya wuce sama a gurguje, da idon dake cike da ƙaunasuka bi su fuskoki na yalwatuwa da murmurshi.... Be direta a ko ina ba se a saman sofan dake bedroom ɗin shi, yana ajiyeta ta saka hannayentatasaƙalo wuyan shi ta haɗa goshin su ta saka idanta a cikin na shi cike da maganaɗisun sonshi
dake fizganta tace "na soka kafin in ganka, na soka bayan na ganka, ina sonka!" Ta idda maganantare da fashewa da kuka, murmushi ya saki me tarin ma'anoni kafin ya ɗauketa kacokanyazauna ya zaunar da ita a jikin shi, ɗago haɓarta yayi ya ƙure fuskanta da ido saboda ƙin ɗagoidoda tayi, murmushi ya kuma saki tare da faɗin ....
"Furta kalman ina sonki yayi matuƙar ƙankanta ga son da nake miki Insiyyah, zan rage masanwani quality ne wanda ba zan so hakan ba, girman ƙaunarki a zuciyanta ido ba ze iya gani basaboda girmanshi, tunani ba ze iya hasasoshi ba dan ya wuce duk wani tunanin me tunani, ba
zance da sanki na ta so ba se dai sanki shine ƙarfin gwiwan cigaba da walwalan rayuwata, kecehasken da ta haskaka rayuwata, ke ce farin ciki da ta yalwata rayuwata, ke ce ƙarfin gwiwandake ƙarfafa ni, ke ce gaskiyan da na daɗe ina jira, kin bani abubuwa masu matuƙar mahimmanci, kin mallakamun abubuwan da ko da yaushe na ɗaga ido na kalla ko na tuna a take farinciki kecika zuciyata, ba zan iya lissafa karamcinki a gare ni ba, Insiyyah ke ce sirrina, matata, rayuwata, ke ce zahiriyyan Sahabee, ba zan taɓa faɗuwa ba matuƙar babu sunanki a jikin nawa, ke cesanadiyyan ɗaukakata, a taƙaice ke ce Sahabee" ɗago ido tayi ta zuba a cikin nashi dake kannata, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "kalman ba za ta isar mun da saƙon da zuciyata ke dakoba, tayi
ƙanƙanta" haɗe bakin su tayi waje guda jikinta na kyarma, cafke laɓɓanta yayi na shi jikinnaɓari, se da suka tabbatar da sun isar da saƙunan dake azalzalan zukatansu kafin su janye ga juna, rungumeshi tayi ƙam-ƙam tare da faɗin "i hate you!" Tare da fashewa da kuka, "hate youtoo!" Yace tare da ɗaga kai sama hawayen da suka cika idanshi suka biyo gefen kuncin shi.... After 8 year's
A wannan shekarun da suka shuɗe abubuwa da dama sun faru, na daɗi da rashin shi, na rashinshi rasuwar Hajiya Farisat Ɓadamayya da na Hajiya Nafisat, Babiya Bertuwa se na MaudedaLamunde, asalin jijjiga wannan ahali biyu sun jijjiga da waƴan nan rashi da ya kasance saƙonjuna, sun koka, sun tsawaita alhini daga baya sun dangana sun bisu da addu'a dan sun fahimci shi
kaɗai ne ƙauna.... Abubuwan farin ciki kuwa ba za su ƙirgu ba, a ciki akwai auren Nafisat da Samir, akwai naHisham da Hamid da Sudais wanda ya auri autan Anty Jummai, amaren da aka sha shagali duksun haihu sun ƙara, Farisat ta ƙara biyu bayan little Insu, takwaran Mami da takwaran Yaya, Yasmin na da uku, takwaran Abba takwaran Yaya se Insiyyat, Nafisat na da biyu Amina daFatimaGude, se me gayya me aiki me girma first lady, uwar gida kuma Amaryan mr president Hajiyabarrister Insiyyah Abdussamad Umar Ɓadamayya ta ƙara huɗu twins waƴanda suka ci sunanSa'eed da Sadam, se Yasmin se Insiyyat wacce ake kira da Nur, rayuwa waƴan nan ahali sukeyi
me cike da aminci, ƙaunar juna, tausayin juna, tare da yarda da juna...
Sunan Insu ya ɗaukaka ya shahara a duniyar shari'a da wajenta, ta gudanar da ayyuka manya- manya mabanbanta wanda ya ɗaga sunanta ta sanu ita da abokan aikinta HishamNachmadaHabib waƴan da suka kasance mata da miji, sun buɗe ƙungiya me taken "lauyoyi ba sa taɓaƙarya" wannan ƙungiyar ya ƙara ɗaukaka su, ako wani lokaci maimaita kalaman hamdala gamaƙaginsu suke dan ya yi musu komai...
Ta ɓangaren rayuwarta da goganta kuwa kullum ƙaunarsu ga juna ƙara gana yake, ba ga haɗakomai da hidimanshi, lokacin shi ba ta yarda wani abu dangane da aiki ya ratsa a ko da yausheaka tambayeta waye ƙarfin gwiwanki takan ce maza biyu ne mahaifina da mijina, wannankalman na matuƙar yin ma SSB daɗi fiye da tunani....
Ta ɓangaren mulkin me girma shugaban ƙasa kuwa se san barka ƴan kasa na ta faɗin "kwalliyata biya kuɗin sabulu" kamar yanda ya alkawarta musu ya cika alƙawuranshi, ya tsaftace musuƙasa daga dattin da gurɓatattun shugabanni suka zuba a ciki, ya wanke musu zukata dagatabonda suka dasa musu, ya shimfiɗa aiki a birane da ƙauyuku, ya yalwata asibitoci da makarantudama'aikata da kayan aiki, kayan masarufi sunyi ƙasa, matasa sun samu aikin yi, tsaro ya yawaitaaƙasa, ɗan ƙasa na iya fita yayi tafiya tsayin dare ba tare da fargaban komai ba, ƴan ƙasa sunzama ƴan gata, ko ina ka gita ba zancen da suke a zahiri da baɗini se na ɗan amanar Ɓadamayo, ya gama tenuwarshi lafiya, jama'an ƙasa sun ƙara miƙa ƙoƙon bararsu na ya ƙara tsayawatakara, be watsa musu ƙara a ido ba ya amsa ya fito aka ƙara buga gan-gan zaɓe ya lashe da ƙuri'umafi
yawa, nan ya ƙara ɗaura ɗammaran yin aiki da gaskiya da amana, SSB ya tashi daga SSBabakunan su ya koma ɗan amanar Ɓadamayo, duk wanda ya tashi furta wani kalma akanshi sedai
kaji yana mishi fatan gamawa da duniya lafiya....
Ta ɓangaren rayuwarshi kuwa, kasuwancin shi ya ƙara habbaƙa, ya ƙara wadata ƙasanshi daabubuwan buƙata cikin rahusa me sauƙi, duniyar iyalan shi, shaƙuwanshi da su har mamaki yake
ba masu kallo, baya haɗa lokutansu da komai, ya dasa ma yaran ƙaunarshi me tsanani a
zukatansu.... Kukan yarinya ƴar kimanin shekara guda da rabi ke tashi a general parlon gidan Yaya, kukatakeme tuƙuƙi wanda ke nuna buƙatan agajin gaggawa da take nema, rungume da ita yarinyaƴar
kimanin shekaru 8 take tare da jijjigata, "oh Yaa Allah! Me kuma aka mata?" Gude da ta shigoparlor tace tare da kai hannu ta amsheta, "babu komai Hajiya kuka kawai take" yarinyar tacekamar zata saki kuka....
"Ina Ammin taku?" Tace tare da saɓa ta, "tana side ɗin Yaya" tace tare da bin fuskan yarinyar
dake sassauke ajiyan zuciya da ido, ba musu ta wuce gaba yarinyar ta dafa mata baya, sallamaɗauke a baki ta shiga parlor dake side ɗin Yayan, ganinsu barbaje suna ta kwasan hira ya satafaɗin "yayi miki kyau Insu! Kin kyauta, yanzu yarinya na sharɓan kuka haka ke har kin samudaman zama kina maida yanda aka yi wato!" Kwaɓe fuska tayi tare da faɗin "dan Allah ya akesoin yi ne wai, shikenan kar in huta dan na haifeta! Wannan ɗafen ni ban saba da shi ba, bansaninda ta kwaso shi ba!" Ta idda maganan cike da takaici.... Murmurshi Yaya dake zaune tsakiyan su ya saki tare da faɗin "amsheta ta daina kukan" bamusuta miƙa hannu, saka mata ita tayi tare da faɗin "tana sane fa Abdussamad yarinyar nan batasonyara suna ɗaukanta, zuwa nayi na taddata a hannun little tana jijjigata se kuka take, ita a ruɗeitakuma ta birkice" "little!" Insu tace cike da mamaki "ita fa gata" tace tare da nuna little Insudaketsaye fuska cike da damuwa, murmushi Yasmin ta saki tare da miƙa mata hannu ta kama, "inaAntyn ku?" Insu tace tare da zube mata ido, "tana ɗakin uncle Sahabee" "kun ji ko na faɗa mukuMairah ba ta son moruwa kuna maida abun wasa, ita fa na ba yarinyar nan da zamu tafi dubojikin Baba Mari shine ta ƙaƙabawa little ta tafi hidimanta!" Ta idda maganan cike da ɓacinrai, dariya su Farisat suka kwashe da shi tare da kallonta....
"Wallahi ku daina dariya, idan akwai abinda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 108 Chapter of 109