Share this page
kwana?" Ta jefa mata tambayanfuskayalwace da murmurshi, "ai nan nake kwana se bayan biki tukun" Baba Mari tace da kulawa, "ehkin yi dabara, to ki je ki huta bari in haɗawa Yaya tea in na gama zan rufe miki office ɗinhar ɗaki zan kawo miki keyn" ta idda maganan cike da yanayinta, "da ko kin kyauta" tace tare da shafakanta ta fice.... Ɗakko tukunya tayi ta ɗauraye ta ɗaura a saman gas, zuba ruwa kaɗan tayi ta wuce gefendakayan tea suke, tana gama haɗawa ta juye a butan shayi ta dau cup's biyu ta jera a samanmadai-daicin trey ta fice a natse, tana shiga parlor Yasmin dake zaune kusa da Suwaiba tace "zanzosha" "se kin zo" tace tare da sakin murmushi ta shige ƙofan da ze sadata da side ɗin Yaya.... Zabura Hajiya dake zaune saman dining chair kare da waya kunni tayi tare da faɗin "tanainayanzu?" "Tana can tana amsan hukunci, se dai Insu ma tace a ƙyaleta ta yafe" muryan Fadilayafito tangararan, "hakan yayi, kar a barta tasha a banza, Allah ya kai mu gobe zan jaddada musu" tace cike da takaicin labarin da Fadilan ta gama ba ta, zare wayan tayi tare da ajiyewa a kusadaita, ɗago kai tayi ta kalli SSB tare da faɗin "maganinta wata yarinyar gidan ta canza" da mamaki ya ɗago kai ya zube mata ido, jinjina kai tayi tare da faɗin "yanzu Fadila ke sanar mun, se dai tanacan hannun jami'an tsaro" lumshe ido yayi ba tare da da yace komai ba, "ya akayi aka gane?" Jabir yace cike da kulawa, "da kanta ta bayyana, ita ta tonawa kanta asiri" tace cike da takaici, "matsar Allah ne Hajiya" Abubakar yace cike da damuwa, "in haka ne Insu ba ta da tsaro acan, dan tunda ta iya aikata mata haka, za ta iya aikata komai dan ganin ta cutar da ita" Alhaji Munniryace cike da damuwa, "gaskiya ne, amma tana hannun hukuma" A'isha tace cike da al'ajabi, janye kujeran da yake kai baya yayi tare da miƙewa a natse, "me ka ci kenan?" Hajiya tacedamamaki, "na ƙoshi" yace tare da wuce wa parlor a natse... Da sallama ɗauke a baki ta tura ƙofan ta shiga, amsawa Yaya yayi tare da juyowa ya watsamataido a natse, murmushi ta saki tare da jan center table ta ajiye treyn ta ɗaga kofi ta tsiyayaruwantean ta miƙa mai a natse, murmurshi ya sakin mata tare da kai hannu ya amsa a natse bakinshi na furta "thank you" murmushi ta saki ta koma kusa da shi ta zauna tare da faɗin "news kakekallo?" "Eh ganin yanda Uncle ɗin ku ke ma maza bulala nake yi" yayi maganan tare da sakinmurmushi, dariya ta saki tare da faɗin "Uncle ya ba su mamaki, ya zame musu ciwon ido, yahanasu barci sam, se tangaɗi da layi suke kamar waƴanda suka ɗaga kwalba" ta idda maganantaredafaɗaɗa dariya a saman fuskanta, murmushi ya saki tare da faɗin "ɓatacce ɓatacce ne ko wani irinkira za a mishi ba ze taɓa ji ba, dan kunnuwan shi sun riga da sun doɗe" jinjina kai tayi taredasakin murmushi idonta akan tvn da ake nuna irin ayyukan da SSB ya shinfiɗa a watanni biyudahawan shi kujeran mulki.... Kurɓan tean yayi tare da juyowa ya kalleta da kulawa tare da faɗin "ya zamantakewan ki acankuwa? Komai yana tafiya yanda ya kamata?" Ya idda tambayan tare da baza mata ido, shirindaƙiƙu tayi tare da ɗago kai tana me maida hawayen da suka cika mata ido ta saki murmushi metarin ma'anoni tare da faɗin "Alhamdulillah everything is fine" ta sadda kai ƙasa, ajiye cupɗinyayi a natse tare da kai hannu ya kamo hannayenta cike da kula me haɗe da tarin so da ƙaunayace "me ke faruwa!" Ya jefa mata tambayan muryan shi na bayyana raunin da zuciyan shi yayi, jin ba ta ce komai ba ya sa shi faɗin "Insiyyah" ɗago kai tayi hawayen da ta kasa riƙewa sukabiyokuncinta, cikin murya me nuni da zallan fargaban da take ciki tace "na kasa, na gaza Yaya, meyasa da Anty zata yi wakilci baka ba ta shawaran saka me cikakkiyar lafiya ba? Ba zaniyaba, ban can-canci wannan aikin ba, ba na da ƙarfin zuciyan yi, ni ba kamar kowa ba ce Yaya, merauni ce ne, zuciyata a na ƙashe take, ba ta da lafiyan fuskantar wannan matsalar" ta idda maganantare da fashewa da matsanancin kuka ta faɗa jikin shi.... Lumshe ido yayi yana mai sauraran yanda take rera kukan, sautin shi ja ɗai ya isa sanarwamesaurare daga asalin ƙasan zuciyanta yake fitowa, tsayin lokaci suka ɗauka a haka kafin yaɗagotacike da ƙarfafa kai yace "waya ce miki bakya da wannan ƙarfin zuciyan? Kin fi masu lafiyanƙarfinzuciyan fuskantar ƙaddarorin da rayuwa ta tana da Insu, sanin zaki iya ya sa ta zaɓe ki, sarewabana ki ba ne Insu, me gajar haƙuri be taɓa samun cikar burinshi" ya idda maganan tare da sharemata hawaye, girgiza kai tayi tare da ɗago ido ta zube mai cike da raunin murya tace "ba zefahimta ba Yaya, baya fahimtar yare na, yaren mutum ɗaya yake iya ji kayi haƙuri wataƙilaabinda zance ya zafafeka amma gaskiyan kenan, kuma kai ka koya mun furtata ko me furtawanze janyo mun, yaren matarka yake iya ji ba ya jin na ɗiyarka, meyasa Anty ta tafi tabar Unclelokacin da yake matuƙar buƙatar ta? Meyasa wannan ranar da riske ni Anty ba ta kusa? NasoAnty na raye, da na ɗurƙusa na haɗa hannayena biyu na roƙe ka ka bar mai ita dan ita ce cikonrayuwar shi, ba dan nafi son shi akan ka ba, se dan ina matuƙar san farin ciki shi Yaya, wani raɗaɗi nake ji yana ta so mun daga ƙarƙashin ƙasar zuciyata, me ne ne hakan Yaya! Shinsoyayyane ko kuma shaƙuwa ne kamar yanda Anty tace! Shin yanda nake ji haka Anty da Uncle sukaji tsayin wannan lokutan, ind ai haka ne, sun cancanci a kira su da jarumai, sun cancanci a rubutasunayensu a kundin soyayyar duniya, ya zanyi Yaya, Uncle be min wani kallo na daban bandakasantuwata ta ɗiyar Insiyyat, ni kuma haka ƙaddara ta yi nayi Yaya" ta jero zantukan cikinmatsanancin kuka tana dasa aya ta saka hannu ta fara sharewa tare da jan hanci.... Ban da bin ta da ido ba abinda Yaya yake cike da matsanancin tsoro, "komai ze wuce Yayakomai ze wuce, ze zama labari kamar yanda labarin Insiyyat da Sahabee ya zaka labari, wannanzezamaYaya" ta yi magana hannunta na share hawayen da suja kasa tsayawa, riƙo hannunta yayi taredafaɗin "ki na san shi ne!" Rumtse ido tayi da ƙarfi tare da fashewa da kukan da ba ta san konamene ne ba tare da faɗin "ba so ba ne, shaƙuwa ne" "no Insu so ne, so me matuƙar haɗari" "Yayakayarda dani?" Tace idonta a saman fuskanshi, "i trust to you" jinjina kai tayi tare da faɗin"zanbinne shi ko da zamo dalili na binne nawa rayuwar, bayan komai ya faru na buɗe ido shi nanagani zaune kusa da shi idon shi biyu ya kasa rumtsawa, na ɗauka zanji tsanarshi fiye da komai aduniya, se na ji ko haushin shi ba ja ji, se na ji buƙata nake yace "ya ki ke ji Insiyyah" da ya furtakuma se na kasa amsawa Yaya, zan daure zan yi ƙoƙarin sunana ya shiga jerin waƴanda sukasadaukar saboda wanzuwan farin cikin abinda suke so" ta idda magana tare da sakin murmushi tare da goge hawaye, damƙe hannuta yayi da kyau tare da faɗin "zan kasance a gefenki taredagoyon bayan duk wani hukunci da ki ka yankewa kan ki, dan na san ba zaki yi dan cutar dakowaba" ya idda maganan tare da goge hawaye, guntun murmushi ta saki tare da jinjina kai ymtarungumeta ƙam-ƙam, tana sakin hawayen da suka cika idanunta... "Komai ze zama labari, karki damu" yace a hankali zuciyar shi na bugu, share hawaye Yasmindata zo shigowa ta tsinkayi maganan tayi tare da juyawa ta goma cikin parlor jiki a mugunsanyaye, kallonta Farisat tayi tare da mata alamun lafiya da ido, murmushi ta sakin mata tare da jinjinamata kai.... "Wai ina Farisat ɗin ne? Ta gama shirin ko se sun dawo daga ɗaurin auren anyi ta famanjiranfitowanta" Lailah dake tsaye cikin wani amintaccen shiga tace tare da kallon Habiba da itamatakashe nata kalan, "ta kammala yanzu za su fito" Salwa da ta zo gittasu tace tare da wuce wakitchen da sauri, "to shikenan Khadijatu da Munari da Jummai su shirya su" ƙarar da wayantayaɗauka ya sara dakawa daga abinda tayi niyyan faɗa ta ɗaga ta kara a kunni saboda ganinYayake kiran, shirun daƙiku tayi kafin tace "to Yaya" tana kai nan ta sauke wayan tare da faɗin"Anty Habiba muje matan governor da yaran shi suna waje" ta idda maganan tare da ficewa da sauri Habiba ta dafa mata baya.... Juyowa tayi ta buɗe hannu tare da ɗaga ido sama ta juya ta sakko da shi tare da faɗin "ya kukaganni baby's?" "Wow baby Insu irin wannan kashe kala da ki ka yi na lafiya ne, wannan aikoamaryan ma se ta ja gefe ta baki waje" Yasmin da ke cikin kaya irin na ta sak tace tare da sakinmurmushi, "gaskiya kayan sun amsheki, kwalliyan kuma ya ɗau ki" Asma tace tare da sakinmurmushi, farr ta kuma da ido tare da faɗin "da gaske ku ke ko zolayata ku ke?" Dariya sukakwashe da shi tare da bin ta da ido, "wallahi kin gama kashe mu, dama haka ki ka iya tsarakwalliya amma bakya yi Ɓadamayya daga mai se lips gloss" Fadila tace cike da mamaki, "wallahi ban taɓa ganin kwalliya a saman fuskani ba se yau" Nabila tace tare da kallon ta, "wallahi taiya, kuma yana mata kyau, matuƙar zata tsarashi se ta burge kowa, amma ba ta son yi" Yasmintacecike da takaici, ƙaramar dariya ta saki tare da faɗin "da ina yi kullum da yau ban burgekubababy's" ta idda maganan tare da duƙawa ta fara saka takalmi.... "Malamai ku fito" Farisat da ta turo ƙofan bedroom ɗin tace cikin shigarta me matuƙar ɗaukanhankali, "wow jiramu mu ɗau na tarihi, shikenan daga yau an cireki daga sahun ƴan gidannan" Yasmin tace cike da shaƙiyanci tare da jan hannun Insu suka nufeta, "wallahi zan ɓata miki rai Yasmin" tace a matuƙar hasale, "oh sorry daga faɗin gaskiya" tace tare da danne dariyarta, tsaki taja tare da faɗin "abinda yafi gaskiya ne, tana kai nan taja hannun Nafisat da ta iso wajenyanzuta wuce a zuciye, dariya Insu da Yasmin da suka kalli juna suka saki tare da bin bayansu.... "Barkan ku da zuwa, marabanku, sannun ku da zuwa, ma sha Allah" Babiya tace baki washedamurmushi tare da kallon su Mommy dake zaune na su fuskokin washe da murmushi, "ina wuninku" Hisham da ke zaune kusa da Mommy yace tare da kallonsu Babiya, "ma sha Allah lafiyalaukaifa" "Alhamdulillah" yace a natse, nan su Mihna suka fara kwasan gaisuwa, ajiye musuruwadalemu Salwa tayi tare da faɗin "waƴan nan ta ya zamu ba su?" Ta idda maganan tare da kallonescort's matan dake tsatstsaye a bayan su, "Kamila ku samu waje ku zauna ko" Mommy tacecikeda kamalanta, "to Ma" tace a natse tare da ma sauran magana suka zazzauna.... Shigowa cikin parlorn Farisat dake riƙe da hannun Nafisat tayi baki a zumɓure tare da kallonLailah da ta ɗago kai ta kalleta, "Anty Lailah wallahi ki shiga tsakani na da yaran can" tacekamarza ta saki kuka, "rabu da su, na yau ne kawai, gobe uwar haka mararin ganin ki za su yi, kinacangidanki kin bar musu na su gidan" tayi maganan cike da muryan rarrashi, kwaɓe fuska tayi tareda faɗin "ni ba inda zani, ina nan a gidan nan, ba wani gidan da zani" ta idda maganan taredafashewa da kuka.... Dariya su Habiba suka saki su Mihna na taya su yayinda Mommy ta saki faffaɗan murmushi, "kardai ki ce mun kin fasa auren!" Lailah tace tare da kama haɓa, girgiza kai tayi tare da gogehawayecike da rashin madafa tace "anan kawai zamu zauna" "aiko ba ze yuwu ba, wallahi tattaraki zamuyi mu miƙa ki gidan mijinki" Khadijatu tace tare da sakin dariya, kuka ta kuma fashewa dashi tare da faɗin "to na fasa auren" "a yaushe kenan, bayan an ɗaura" Balarabe da ya shigo riƙedahannu wani matashin yaro yace tare da juyawa ga matan dake bayanshi saɓe da baby girl akafaɗa riƙe da hannun yarinyar ƴar kimanin shekaru biyar, "bismillah shigo" yace cike da girmamawa shigowa tayi fuska yalwace da murmushi, da mamaki Khadijatu tace "Anty Sarah!" Murmushi ta saki tare da faɗin "sister Khadijatu ko?" Jinjina mata kai tayi tare da faɗin "ni ce" juyawa ga Lailah da ba ta gane ko wacece na tayi tare da faɗin "matan Yaya Hassan" "what!" Insuda Yasmin da Farisat da Lailah da Salwa da Nafisat suka ce cike da mamaki, ido waje, "wallahi itace, ai ba zan mata fuskanta ba duk da shekarun da yawa" tace fuska yalwace da murmushi tareda ƙarisawa ta riƙo yaron dake ta baza ido, bin ta da ido kawai suka yi da ɗin bin mamaki, "ƙarisoki zauna" Habiba tace cike da kulawa, ba musu ta ƙarisa kusa da Hamid ta zauna.... "Insu!" Hisham da ya ɗago kai da zumman excuse ɗin kan shi saboda ganin yanda mata kecikaaparlorn yace tare da miƙewa zumbur, jiyowa ta inda sautin ya fito tayi cike da mamaki taredafaɗin "Hisham!" Bin ta kawai yayi da kallo me cike da mamaki, murmushi ta saki tana me dannemamakinta, "daughter Insu ce!" Mommy tace da mamaki tare da kallon shi, jinjina kai yayi tareda faɗin "ita ce" murmushi Insu ta saki tare da tsallakowa ta zauna kusa da Minha dake tabintada ido tare da gaida Mommy, amsawa tayi cike da sakewa, "ke ɗiyar barristern Amina ne! Yaceaɗan rikice, jinjina mai kai tayi cike da tabbaci, "barrister Insiyyat fa!" Yace a ruɗe, "duk mutumɗaya ne" tace tare da sakin murmushi ta riƙo hannun Minha tare da faɗin "sister Minha nekoMihna?" Murmushi ta saki tare da faɗin "Minha" sakin hannunta tayi ta miƙe tare da faɗin"nayi fushi tunda kun ƙi kulani" ta idda maganan cike da yanayinta, murmushi suka saki tare dabintada ido, "ai ƙauyawane" Amen yace tare da sakin dariya, "na ɓata da kai" tace tare da kaudakai, zare ido yayi tare da sakin murmushi.... "Tare da uncle Hassan ku ka zo!" Farisat tace idonta akan Sarah dake ta sakin murmushi, jininamata kai tayi tare da faɗin "eh yana tare da tawagan mr president" zare ido Insu tayi ƙirjintanabugawa tare da faɗin "Hajiya ta zo!" "Eh yanzu za su shigo, tare da su muke" ta idda maganantare da kallon ta... "Wow!" Hisham yace a ƙasan zuciya cike da farin cikin jin Insu ƴar abar da yake matuƙar ƙaunacea duniyarshi, "ke ce aka canzawa magani!" Yace tare da fiddo da ido waje, "oh Allah yau nagaterere, Mommy dan Allah Hisham amma shine auta ko?" Insu tace tare da kallon Mommy, murmushi ta saki tare da faɗin "na uku ne" "shine yake abu kaman auta ko na fari" ta yi maganantare da sakin murmushi, "ungo naki nan Insu" Babiya tace tare da banka mata harara, dariyasukasaki tare da kallon ta, juyawa gare shi tayi tare da faɗin "ka ganni ba abinda ya same ni har nafi da lafiya, kwantar da hankalin ka ɗan uwa rabin jiki" girgiza kai yayi tare da faɗin "amma kinrame" "na kuma ƙara kyau ba" tace tare da sakin dariya, murmushi ya saki tare da girgiza kai, sallama A'isha dake gaba tayi cike da natsuwa su Lubabatu biye a bayanta, amsawa suka yi tareda zuba musu ido cike da farin cikin ganinsu, a guje su Asma suka yi inda suke.... "Oh ku ba kusan kun girma ba ne?" Insu tace tare da ƙarisawa ta shige jikin Hajiya, "ke kumameki ka yi kenan?" Salwa tace tare da marabtansu cike da fara'a, murmushi ta saki me faɗi tashafasaman kanta tare da faɗin "ya jikin?" Da sauƙi" tace tare da zare jikinta ta rungume Lawizadaketa sakin mata, "Salwa ban san sa ido, rabu mu da ɗiya" Hajiya tace cike da murmushi, "ohHajiyakaɗan muka miki har ki ka koma kale?" Lailah tace cike da murmushi tare da yo inda suke, "a'aai ni ƴa nake da ita ba jika ba" Hajiya tace tare da sakin murmushi, "bismillah ku ma isa can" Lailahtace cike da girmamawa,.... "Sannu da zuwa Bertuwa Anty Lawiza, yau kin shigo garin aminci da kwanciyar hankali, garinadalin salihin gwamna Sharifudden Muhammad" ta idda kiran sunan tare da tsayawa caktazareido, rumtse ido tayi ta juya da sauri ta baza ma Hisham dake bin ta da ido yana sakin murmushi ido, kauda kai yayi murmushi be bar saman fuskanta shi ba, "wallahi baka isa ba" tace taredayoinda yake, dariya ya saki tare da ɗaga hannu sama, "Mommy Daddy shine!" "Gwamna" Mommytace cike da murmushi, "kai amma Hisham ka gama dani, be fa taɓa faɗamin ba Mommy seyanzuda na gano da kaina" ta idda maganan tare da miƙewa ta isa inda aka ma su Hajiya ma sauki tareda faɗin "Yasmin! Zo ki ga Anty Lawiza da takwaran Anty" tayi magana da ɗan sauti sabodatazaran dake tsakanin su.... Ba za ido su Mommy suka yi dan ganin Yasmin dan tunda ta shigo ba ta fuskance su ba, sannansu ma ba su maida hankali akanta ba, miƙewa Yasmin dake zaune kusa da Munari tayi ta nufesua natse, "wow! Tafi haɗuwa a zahiri" Mihna tsce cike da fata, nan gaishe-gaishe ya tashi, shigowaBaba Tinene tayi da sauri tare da faɗin "Habiba Yaya Abdussamad yace a shiryawa baƙi abinci yanzu a kai side ɗin shi, yana tare da me girma governor da shugaban ƙasa" ta idda maganantare da shigewa ciki da sauri, miƙewa tayi da sauri ta ja Jummai da Suwaiba suka nufi kitchen.... "Meye?" Salwa tace tare da bankawa Farisat dake ta narke ido harara, tura baki tayi tare daɗagawayanta da kira ya shigo ta kara a kunni, "ina ji" tace kamar za ta saki kuka, "su shigo" tacetareda zare wayan, "su waye!" Salwa tace tare da kallon ta, su Yaya Annur ne suka dawo dagaɗaurinaure, "oh ai ba baƙi ba ne su shigo mana, banga ma matan ba yau" "se anjima dinner za suzo" "okay" tace tare da miƙewa, tana wuce wa suka yo sallama suka shigo, su kusan Talatin, zareidoFarisat tayi tare da faɗin "kumu gangara side ɗin baƙi" "ba ko ki isa ba, babu baƙo anan" Zubair yace tare da banka mata harara ya zauna a kusa da ita.... Wucewa gefen da Mommy take Shureim da Annur suka yi suka tashi Hamid da Mihna dakezaune kusa da ita suka zauna, da mamaki Farisat ta kallesu cike da ɗan shakku ta kalli Zubair taredafaɗin Mommyn shi ce!" Jinjina mata kai yayi tare da faɗin, "waƴan nan duk ƙanninshi ne, Daddynshi na tare da Yaya da mr president" ya idda maganan cikin sam fahimtar da ita, "wallahi wawiyace ni, ɗazu fa naji Insu na maganan wan can ɗan gwamna ne, amma ban kawo MommynYaya Shureim ba ne, oh Allah" tace tare da miƙewa ta nufeta, cike da girmamawa ta gaidata, "auba ku gaisa ba ne se yanzu!" Annur yace tare da kama haɓa, "wallahi ba mu gaisa ba, Yasminzoki gaisa da Mommyn Yaya Shureim" tace da ƙarfi.... Tasowa suka yi tare da Insu cike da yanayinta tace "au ni ba za'a ce in zo mu gaisa ba?" Ta iddamaganan tare da tsayawa turus ganin Mommyn Hisham ne zaune a inda take tana sakinmusumurmushi, "ku tsaya wai uncle Shureim dama Hisham ƙanninka ne!" Tace tare da takawa tayi inda yake, murmushi ya saki tare da faɗin "oh school ɗin ku ɗaya ko?" "Ɗan uwana ne fa nagani yankani" tace tare da sakin dariya, "Allah ya shiryeki, wato na gani yankani" Annur yace taredakallon ta, "ina wuni" Yasmin tace a natse cike da ɗan kame fuska, "lafiya lau daughter ya hidimanbikin?" Mommy tace cike da kulawa, "Alhamdulillah" tace tare da jan bakinta ta ɓame, "sister inlaw ina wuni" Hisham yace a natse tare da kallon ta, zare ido su Mihna da suka san kwananzancesuka yi tare da baza mata su, "kana lafiya?" tace a natse, "wait guys ban gane sister in-lawba! Kana nufin Yasmin da uncle Shureim wai" miƙewa Yasmin tayi fuska a kame ta nufi barinwajen, "wow ma sha Allah, gaskiya abun ya bada kala" Insu ta kuma cewa cike da yanayinta, "InsuYasmin Farisat ku kira Nafisat ku zo Yaya na san ganin mu" Salwa tace tare da juyawa dansanarwa su Khadijatu.... "Uncle Shureim ya baka sanar da ni an shirya juna ba?" Insu tace tare da kallon shi fuska cikedamurmushi, "ba a shirya komai ba fa" Annur yace tare da kallon ta, "ya haka kuma? Kar kusafarinciki na komawa ciki mana" tace tare da ɓata fuska, "to kin fi kowa saninta ai" Farisat tace taredamiƙewa, "ka bar mun komai zan gyara maka harka, bari mu amsa kiran Yaya zamu zanta akanbatun" tace tare da wuce wa da sauri, murmushi Mommy ta saki tare da faɗin "ba ta da matsalankomai" "ko tana da shi ba ta bayyanawa adana shi take a zuciya ta bayyana akasin shi a zahiri" Hisham yace tare da sakin murmushi idon akanta.... Da sallama ɗauke a baki suka shiga parlorn Yaya dake cike da su Alhaji Munnir, amsawa sukayi anatse tare da zube musu ido, a hankali Lailah dake gaba ta zauna kusa da Hassan da ya zubemusu ido cike da tausayawa, tana zama Khadijatu ta zauna kusa da ita Salwa ta biye mata, Sadam ya bi ta, haka suka yi ta zama, lumshe ido SSB yayi ganin be ga abinda idanun shi kemararin ganin ba, "ina su Insu?" Yaya yace tare da kallon Nafisat, "ga su nan" tace a natse, sallama Yasmin tayi riƙe da hannunta suka shiga, zama tayi kusa da Yaya tare da sadda kai ƙasa, murmushi Yaya ya saki idanshi akan fuskan Daddy tare da faɗin "ga iyalan na ta nan" "mashaAllah, lallai Allah ya albarkaci zuri'a, Allah ya gafarta mata, ku kuma ya shiryaku" "amen" sukacea natse, buɗe baki Alhaji Jamil yayi a natse tare da faɗin "Lailah kin gane wanda ke kusa dakekuwa?" Share hawaye tayi tare da fadin "Yaya Jamil na isa in kasa gane shi, ai jini ba wasaba" taidda maganan tare da fashewa da kuka, nan su Khadijatu suka fara taya ta.... "Kuyi haƙuri ku yafe mun, kuskure na aikata shi wanda kunyar fuskantar ku ya sani komawagefeina hangenku daga nesa" Hassan dake zubda na shi hawayen yace tare da bin su da ido, jinjinakai kawai suke cike da jin daɗin ganin shi tare da bin shi da ido, Farisat matso gaba" Yaya yaceanatse, miƙewa tayi a sanyaye ta ƙarisa gaban su ta zauna tare da sadda ido ƙasa, "ga ɗiyar takanita ce ka ɗaurawa aure yau" Yaya yace a natse tare da kallon SSB da ke bin Insu da kallonƙasanido, murmushi ya saki me faɗi tare da faɗin "Allah ya ba da zaman lafiya" "amen" suka ce cikedajin daɗi juya dubanshi ga Jabir yayi ya mai maganan sakanni, kallon Yaya yayi tare da faɗin"amina ganin mu ma amarya addu'an fatan zaman lafiya zamu wuce ba jimawa mr president nadazama na musamman" jinjina kai Yaya yayi cike da fahimta suka gyara zama suka fara karɓanaddu'an da Abubakar ke ratatowa.... Suna shafawa suka mimmiƙe a natse saurin ƙarisawa kusa da Ibrahim dake niyya ficewa Insutayi tare da faɗin "Abban Iman amma muna tare da Anty Lawiza ko?" Girgiza mata kai yayi taredafaɗin "da ita zamu koma" "kai Abban Iman" tace kaman zata saki kuka, "se wani zuwan" yacetareda sakin murmushi, "wani zuwa kuma?" Tace cike da takaici, leƙowa Jabir yayi ya yafutota, dasauri ta nufeshi tare da faɗin "gaskiya Anty Lawiza zata kwana" murmushi kawai ya sakinmataba tare da yace komai ba, "gani" tace fuska yalwace da murmushi tare da kallon shi, "ke akejiraza'a muku hoton tarihi" "oh" tace tare da sakin murmushi, "muje" yace tare da nuna mata hanya, ba musu ta saka kai a natse, tun daga nesa ya hangota, tana isa ta wuce gefen Hajiya tareda faɗin "amma Hajiya ba da ku za'a tafi ba!" Tayi maganan kaman zata saki kuka, murmushi tasakin mata tare da faɗin "ai yanzu an daina zuwa waje a kwana Insiyyah" tana niyyan maganaAbubakar yace "koma kusa da Uncle mana" ba musu ta tsallaka kusa dashi a natse tare dabadagab a tsakaninsu, haɗe gab ɗin yayi a natse tare da faɗin "are you happy?" Ya je fa mata tambayacikin muryan da ita kaɗai zata iya ji, ɗago kai tayi ta kalleshi da ɗin bin mamaki tare da faɗin"uncle Hassan!" Murmurshi ya saki tare da

Chapter 51 of 109