Share this page
ta tashi a wajen ba se da ta gabatar da isha'i tana miƙewa ta haye gado ta kashewutanɗakin ta ja blanket, koda Farisat ta zo kiranta cin abinci ba ta samu zarafin amsawa ba danbarci ya daɗe da awan gaba da ita.... Fuska a ɗaure ya shiga parlorn, ja yayi ya tsaya tare da kallon Gude dake zaune a kujera oneseater, banda cika da tumbatsa ba abinda take, ganin bata ko kalli inda yake ba ya sa shi ƙarisawa ciki tare da neman waje ya zauna a one seatern dake gefen wanda take kai, "dagainaka ke?" Ta jefa mai tambayan a dake, da mamaki ya ɗago kai ya kalleta tare da faɗin "na faɗamiki bana son tambaya irin wannan, daga ina nake? Ina na je? Me nake yi? Ina zani? Duk banabuƙata, ni ba yaro ba ne Momy ina da hankali na san abinda nake yi, yaranki mata yakamataki dinga wa wannan tambayoyin ba ni ba" ya idda maganan a harzuƙe... "Kana da hankali ko? Tabbas ga hankali nan tunda har zaka iya danne ɗiyar mutane ba taredakunya ko tsoron mahaliccinka ba, tabbas na ga hankali" tayi maganan a fusace tare da miƙewaazabure, "wai me ke faruwa?" Yace tare da bin ta da ido, "ubanka ne yake faruwa Sudais, kaji naceubanka ne, yanzu irin wannan tarbiyyan muka baka? Ka rasa abinda zaka yi se bin matanbanza, inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, wato ba a shaye-shayen kaɗai ka tsaya ba ma har da binmata, lefi mafi muni cikin lefukan da mahalicci ya hana bayin shi aikatawa, wallahi kayi asara" kallomecike da zallan mamaki ya bita dashi tare da faɗin "wai akan me ki ke magana ne? Ya za'ayi ki kirani ki yi ta mun magana haka?" Ɗauke shi da wani rikitaccen mari tayi zuciya a matuƙar ɓace, nuna shi da yatsa tayi tare da faɗin "na faɗa maka dake ni kaman yanda na dake ka Sudais seintabbatar da ka isa ka riƙa ka kawo ƙarfi".... "Wallahi se na ci mutuncinka na walaƙantaka kafin ka walaƙantani a idan duniya, ai bansanaureka ke so ba se yanzu, tunda ka aiko mun da ɗan aike zan tabbatar na maka abinda ka ke so" "bangane aure ba, ni na ce miki aure nake so?" Yace tare da sakin hannun da ta riƙe kumatu dashi cike da mamaki, "ai ba se ka ce ba, tunda har tsaurin idonka yasa ka iya saɓule wando a gabanwacce ba maharramanka ba ka isa ne" tace tare da ƙoƙarin barin wajen, "ni dai na faɗa miki bawanda nake so se Insu ita kaɗai zan iya aura, sannan maganan wani saɓule wando da ki kebansan da zaman shi ba" "se ka je ka aureta ai da ubanka, ubanta shike ɗauke da shedan danneƴarmutane da ka yi, kasan kuwa ko mutuwa za ka yi ba ze taɓa yarda ya ba ka ƴar shi ba" a firgiceyaɗago kai tare da faɗin "a ina ya samu?" "A gidan ubanka ya samu" tace a harzuƙe tare da yokanshi gadan-gadan, riƙota Daddy da ya shigo yayi tare da faɗin "ba na ce kar ki tada magananba?"... "Ba zan iya shiru ba Daddyn su, wallahi se na ci mutumcin Sudais, ban san me yake so da ni ba, Sudais son ka she ni kawai yake, ka kasheni ka huta, da ganin irin wannan ranar gunda ganinranar mutuwata, ɗana ke raba mutuncin shi ga ƙadangarun bariki, ɗan da na haifa" ta iddamaganan cikin rishin kuka, "ya isa haka" Daddy yace tare da buga bayanta a hankali, sharehawaye tayi tare da faɗin "haba Daddyn su, wani so da ƙauna ne wanda iyaye ke nuna ma ɗansuda ba mu nuna mai ba?, Mun so shi fiye da sauran ƴan uwanshi, mun nuna mai gata fiye dasu, komai na shi ya ban-banta da na su, duk dan ya zama nagari, dubi irin sakayyan da yake mana, yaƙi makaranta, yaƙi sana'a, ya rungumi shaye-shaye da bin abokanan banza, duk wani aboki naarziƙi ba ya zama inuwa ɗaya da shi, yaƙi zama na garin da muke hangomai, a she duk nafilamuka sani ga farillan yau ya riske mu, zina, zina yake yi hankali kwance ba bu ko jin kunyar mahaliccin shi, ya buɗewa maƙiya ƙofa sun samu daman yi mun dariya san ransu" ta idda maganan cikin matsanancin ɓacin rai.... "Ki na ta wani jam'i ina bin ƙadangarun bariki, banda ita ɗin dawa kuma aka ce miki an ganni?Itama kawo kanta tayi, kuma wallahi ba wacce zan aura in dai ba Insu ba na faɗa miki" ya iddamaganan cike da ɓacin rai, jawo iron dake gefe tayi ta hurga mai a harzuƙe, saurin ja gefeyayi cike da mamaki, dan be yi zato ba, rikota Daddy yayi tare da faɗin "haba Gude dawo cikinhayyacin ki mana, bi komai a hankali" "gyaleni in naƙasa wawa inyi jinyarshi, barni in karyashi inganshi a zaune ze fi min alheri da ganin shi da nake tsaye a gabana yana faɗa min san ranshi, wato dan baka da sauran kunya a idanu har kana da bakin buɗewa a gabana kayi magana irinwannan, wallahi se dai ka mutu in dai ita ce kake so dan ba wanda ze neman maka aurenta, bari ma kaji da igiyoyin wani akanta tuntuni, kuma ka shiryawa auren Sauden Jummai nan ba dadaɗewa ba" tana kai nan ta fizge jikinta ta wuce bedroom ɗin ta zuciya na matsanancin ƙuna.... "Wallahi ba zan aureta ba, wannan yarinyar da ɗaiɗaikune a anguwarsu ba su gama saninwaceceita ba zaki ce zan aura?" "Kai ma ai ɗaiɗaikune ba su gama saninka ba" tace da ƙarfi daga ciki, "kafaɗa mata wallahi ba zan auri yarinyar nan ba, mace ɗaya nake so kuma se na mallaketa komeza'ayi" yayi maganan tare da juyawa ya fice a fusace, sauke numfashi Daddy yayi tare da binshi da ido.... A guje ta sakko kare da waya a kunni, buɗe ido tayi tare da bin su da shi a natse, ganin yandasuka zuba mata ido yasata sakin murmurshi tare da faɗin "nayi sallah" murmushi Alhaji Munnir ya saki tare da faɗin "kin kyauta" "bari zan kira ka zuwa anjima" tace tare da sauke wayantaƙarisa kusa da Alhaji Munnir ta zauna tare da faɗin "uncle Munnir I'm very sorry da abindayafaru ɗazu, ban so cewa komai dangane da hakan ba, ganin tana son maƙalawa Anty lefindabanata ba shiyasa na yi maganan" tayi maganan a marairaice cike da neman afwa, murmushi yasaki tare da jinjina mata kai tare da faɗin "a ina ki ka ji wannan maganan?" Sadda kai tayi taredafaɗin "Anty Laila ce ta faɗamin" girgiza mata kai yayi na tare da yace komai ba, "ba kayi fushi bako?" Tace a hankali, girgiza mata kai ya kuma tare da sakin murmushi, murmushi ta saki taredafaɗin "oh uncle Munnir kana da kirki" murmushi ya saki tare da faɗin "kin fini ai" dariya tasaki me ƙaramin sauti tare kallon shi, juya duban shi ga SSB dake magana da Jabir yayi a natse... A natse yake maganan ba garaje ba ƙosawa, "ka shigar da wannan ɗin a cikin waƴan can" jinjinakai Jabir yayi tare da ja baya kaɗan, "Ibrahim ya wan can aikin da ka ke aiki a kai?" Jabir yacetareda kallon Ibrahim, "na kammala na kai bayanan office ɗin assistant ceo" jinjina mai kai yayi tareda kallon Alhaji Munnir dake cewa "an zaɓi (IS company) a wannan haɗakan da Afghanistandatashiga" "wow yaushe aka sanar!" Kamil yace tare da gyara zama, ɗazu da safe na samu kiran" "albishir me daɗi na ta ya ku murna, haɗaka ce me matuƙar mahimmanci" jinjina kai yayi batareda yace komai ba, kallon Insu Ibrahim yayi tare da faɗin "jeki kwanta" yayi maganan fuskaaɗaure dan yasan za ta iya kawo wasu zantukan, kwaɓe fuska tayi tare da miƙewa a natse... Murmushi Abubakar ya saki tare da faɗin "good night" "night uncle Abubakar ka gaida minIkram" "za ta ji" yace tare da danne dariyar shi, "bye uncle's tace tare da ɗaga musu hannu, "bye"suka ce da kulawa, har ta kai ƙafa kan stairs ta juyo da sauri ta nufeshi kai tsaye babu tsorokoshakku ta shige jikin shi ta ƙanƙameshi, zare ido suka yi gaba ɗayan su tare da bin ta da ido, ɗagowa tayi a hankali ta manna bakinta a saman goshin shi ta sakin mai wani masifaffensumbame sakar da jiki, janye bakinta tayi a natse fuska faɗaɗe da murmushi tace "good night Uncle, Allah yasa kayi barci me masifar daɗi" tana idda faɗi ta janye jikinta ta nufi up stairs a guje.... Tunda Ibrahim yayi magana yake bin ta da kallon ƙasan ido, duk abinda take yana hankalcedaita, ganin ta juyo ta nufoshi gadan-gadan ya sa shi haɗiye wani kakkauran yawun tsoro danyahangi abinda take shirin yi daga ƙwayan idanuwanta, be ankara ba ya jita a jikin shi, tsayawa caknumfashin shi yayi ba tare da ya ankara ba, be samu sauke numfashi ba se da ta zare jikintaanashi, sauke ɓoyayyen numfashi yayi tare da ƙoƙarin sai-saita kan shi, tana kai bakinta samangoshin shi ya gama sarewa da lamarinta, bin ta yayi da ido har ta ɓacewa ganin shi, gyaranmurya Jabir da ya hankalta da yanayin da ya shiga yayi tare da faɗin "ina ga zamu zo muwuceyanzu, ka samu ka kwanta ka huta" jinjina mai kai yayi ba tare da yace komai ba, sallamanshi suka yi suka fice a natse.... Sauke ƙaƙƙarfan ajiyar zuciya yayi tare da jingina jikin shi a jikin kujeran da yake kai, lumsheidoyayi na tsayin mintocin da be san ko nawa ba, so yake ya fahimci wani abu wanda shi kanshi besan ko menene ba, se da ya gaji dan kanshi ya miƙe a hankali, faɗawa idon shi yayi akanwayantadake yashe a saman kujera, sa hannu yayi ya ɗauka a natse tare da bin wayan da ido, yanakunnawa hoton ta da na Anty ya bayyana, lumshe ido yayi tare da kafe wayan da ido, be samukaudawa ba har se da hasken ya ɗauke, takawa yayi a hankali ya isa gaban fafaɗeɗen hotondaya fara marabtanshi, kafeshi da ido yayi kaman me neman wani abu, wasu shuɗaɗɗun abubuwane ke zuwa mai suna wuce, wani guntun murmushi ya saki tare da kai hannu a hankali ya shafofuskanta, "meyasa?" Yace a ƙasan maƙoshi tare da haɗiyan zuciya, juyawa yayi da nufinbarinwajen idon shi ya faɗa kan Insu dake tsaye rungume da hannu fuskanta faɗaɗe da murmushi.... Kauda fuskan shi yayi da sauri dan ba abinda yake hangowa tattare da ita se Insiyyat ɗinshi, murmushi ta saki tare da faɗin "Uncle mun yi kyau ko?" Be ce komai ba se raɓeta da yayi dazumman wuce wa, "my phone Uncle" tace tare da miƙa mai hannu murya a shagwaɓe, miƙamatayayi a natse ya bar wajen, murmushi ta saki tare da bin shi da ido har ya haye sama, juyawadadubanta kan hoton tayi tare da sakin murmushi, "yana kewan ki sosai Anty" tace tare da sumbatan goshin Anty cike da so da ƙauna, ɗaga wayanta tayi tare ew faɗin "na mantashi nedanna sha'afa da ce miki good night, good night Anty" ta idda maganan tare da sakin murmushi, kara kunninta tayi tare da faɗin "me ki ka ce? Banji ba ɗan mai-maita" shirun daƙiƙu tayi taredafaɗin "ki ka ce night baby? Oh night Insu? Oh yanzu nagane night baby Insu" ta idda maganatareda sakin murmushi ta wuce sama da sauri.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Twenty five Murmushi ta sakin ma Lawiza dake zaune saman kujera idonta akan hanyar da ta biyo, murmurshi ta sakin mata tare da miƙewa cike da yaba kyawun da tayi, sanye take da doguwar riga da wando da baby hijab gaba ɗaya brown colour, asalin pencil sun fidda kyakykyawansuranta ba lefi, "kinyi matuƙa kyau" Lawiza tace murmushin saman fuskanta na ƙayatuwadandagaske tayi masifar burgeta, murmushi ta saki tare da ƙarisawa kusa da ita a hanzarce, ƙasadamurya tayi sosai tare da faɗin "Uncle ya fita ne?" Murmurshi ta sakin mata me faɗi tare dagirgizakai, "good" tace tare da juyawa da sauri tayi sama, "yana office" tace a natse.... Juyowa tayi kaman za ta saki ihu tare da faɗin "Anty Lawiza!" ƙaramar dariya ta saki taredafaɗin "na cikin gida" fiddo ido tayi tare da faɗin "yana da office har a gida!" "Eh" tace tare dakafeta da ido, "a ina yake!" Siririn hanyar dake gefen bene ta nuna mata tare da faɗin "kai tsayeze sadaki da ƙofan office ɗin" "wow" tace tare da juyowa dan nufar can "yana tare da baƙi" taceanatse tare da sakin murmushi, "oh Allah Anty Lawiza" tace tare da tura baki gaba, "da gaske" tace tare da komawa ta zauna, dan ta san bata da lecture se 4.... "Su oga Jabir na tare da shi" "oh wannan ai ƴan gida ne, an kai musu wani abu ne?" Girgizamatakai tayi tare da faɗin "an shirya musu breakfast in sun gama abinda suke za su fito su ci" "nagodeFeita" tace tare da ficewa da sauri ta yi kitchen, tana shiga ta tadda ma'aikatan na ta aikintsaftacewa, kai tsaye gas ta nufa ta kunna ta ɗau tukunya ta ɗauraye ta ɗaura, nufar inda kayanhaɗin tea suke tayi da sauri, zaɓan wanda za ta iya amfani da su tayi ta koma gaban tukunyan, cikin mintinan da ba su wuce 40 ba ta haɗa amintaccen tea me fidda ni'imtaccen ƙamshi, gabaɗaya ƙamshin ya baɗaɗe kitchen gaba ɗaya, dakko madaidaiciya flaks tayi ta juye, goge gefendaya ɓaci wajen juyewa tayi ta ɗakko madai-daicin tray ta ɗaura a kai, tea cup's shida ta ɗaukatajera ta ɗau madaidaici bowl ta zuba sikari dai-dai ko da za'a samu me son ƙarawa... Ɗauka tayi ta fice a natse, banda bin ta da ido ba abinda ma'aikatan ke yi, kai tsaye parlorntakoma, murmushi ta sakin ma Lawiza da ta kafeta da ido, ƙarisawa kusa da ita tayi ta ajiye, zarantissue tayi saman center table ta ɗago da cup ɗaya ta tsiyaya tean ta miƙa mata, "sha ki ji komai yayi dai-dai?" Tace tare da sakin mata murmushi, murmushi ta saki tare da amsa ta kai baki, tanakurɓa ta lumshe ido tare da amsan ɗanɗanon da ya garwaye bakinta, buɗe ido tayi akantasaboda kafeta da nata da tayi, murmushi ta saki tare da faɗin "komai yayi" murmushi ta saki tasunfuta tayi inda ta nuna mata.... Knocking ƙofar tayi tare da turawa a natse ta shiga, da mamaki suka ɗago kai gaba ɗayansusukazuba mata ido banda SSB da yayi saurin janye na shi, su huɗu ne, shi Jabir Alhaji Munnir Abubakar, murmurshi ta sakin musu babu wani fargaba ta wuce gaban table ɗin dake gabanshi ta ajiye tare da faɗin "good morning uncle's" ta idda gaisuwan tare da sakin faffaɗan murmurshi idonta na yawo a saman fuskokin su, "morning Insu har kin tashi?" Alhaji Munnir yace da kulawa, "eh na tashi tun ɗazu" tace tare da sakin murmushi, kallon Abubakar dake kallonta tayi taredafaɗin "se 4 zan shiga" jinjina mata kai yayi ba tare da yace komai ba, kauda kai Jabir yayi cikedadanne dariya dan ya fahimci dalilin da yasa SSB ya ɗaure fuska.... Wuce wa gefen shi tayi kai tsaye tare da faɗin "Uncle ka tashi lafiya?" Ta idda gaisuwantaredatsayawa kusa da shi, se da ta kusan cire rai da samun amsa sannan ta jiyo saukan muryanshi adaƙile "lafiya" murmushi ta saki tare da faɗin "ma sha Allah ya gajiyan jiya?" Ɓata fuska yayi tareda kallon Abubakar, murmushi ya saki tare da faɗin "Insu muna tattaunawa akan wani batumemahimmaci ne inba damuwa koma saman sofa ki jira mu kammala" shagwaɓe fuska tayi cikedayanayin jin ba daɗi tare da faɗin "to uncle Abubakar amma bari in zuba muku tea kusha zakuji karsashin tattaunawan" tayi maganan tare da zaran tissue, ɗaɗɗagp cup's ɗin tayi ta zubamusu, ba wanda ƙamshin be dakanwa hanci ba, banda haɗiye yawu ba abinda suke, har da oga kwata-kwata shugaban ƴan dakiya, tana gama zubawa ta ajiye ma Alhaji Munnir dake kusa da itatareda faɗin "uncle Munnir kar ka bari a baka labari" murmushi ya sakin mata tare da bin ta daido, ajiyewa Abubukar da Jabir tayi ta ɗau na shi ta ajiye mai a kusa dashi, cike da yanayinta tace"danAllah ku sha, sannan ku ba ni mark" tayi maganan tare da nufar sofa ta zauna, zaro wayantatayi ta haye whattapp ta fara charting.... "Sauke ajiyan zuciya yayi a hankali tare da ɗaukan file's ɗin gaban shi ya ajiye a gaban Alhaji Munnir, ɗago kai yayi ya kalleshi tare da faɗin "na menene?" "Kai za ka jagoranci aikin" yacetareda kwantar da jikin shi a kujeran da yake kai, "ni kuma!" Yace da zallan mamaki, ba abindayacemai se lumshe ido da yayi ya buɗe a kyestawan sakan guda, murmushi Jabir da Abubukar sukasaki cike da farin ciki tare da ba shi hannu, "na taya ka matuƙar farin ciki" Abubakar yace fuskacike da farin ciki, "nagode, nagode sosai" yace cikin zallan mamakin da ya kasa barin shi.... "Bismillah" Abubakar yace tare da ɗaukan cup tean da ta ajiye mai ya kai baki, ɗaukan na susukayi cikin matsanancin farin ciki suka kai baki, "wow" Abubukar yace tare da zare bakin shi, "pleaseka sha zaka ji daɗin shi" yace tare da kallon SSB da ko motsi be kuma ba tunda ya jingina dagujera, ɗago jiki yayi a natse ya ɗau kofin ya kai baki, ruwan tean na taɓan harshenshi ya lumsheido tare da ja a hankali, yana haɗiye wanda ya ja ya cire kofin ya watsa mata idanun shi dakeɗauke da abubuwa mabanbanta.... Baiwar Allah Insu ba ma tasan suna yi ba tayi nisa da charting da Salman dake sanar da itagwajin da za su a yau, kallonta yake kai tsaye ba tare da wani hijabi ba, irin wannan teanshinewanda Insiyyat ɗin shi ke mugun so, ba ze iya mantawa da kalan ɗanɗanon shi ba, duk da yakwashi tsayin lokaci raban da ya sha, ita ta saba mai da shi, tun baya maida hankali a kai har yafara, lumshe ido yayi tare da ƙara kai kofin baki, ba wanda ya ƙara cewa komai, duk sunnatsusuna shan tea, a jiye kofin yayi a natse ba tare da ya ce komai ba, murmurshi Jabir ya saki taredafaɗin "a ƙara ne?" Lumshe ido yayi tare da maida jikin shi ga kujeran, "Insu" Alhaji Munnir yaceanatse, "na'am" tace a hanzarce tare da ajiye wayan ta taso tayo inda suke, "kun gama meetingɗin?" Tace fuska washe da murmushi... "Uncle na buƙatan ƙari" yayi maganan tare da nuna mata cup ɗin da ya ajiye, da sauri ta ɗauflaksɗin ta tsiyaya mai wani, ta ajiye mai a gabanshi, murmurshi Abubakar ya saki tare da faɗin"yayi daɗi sosai, Allah ya ma hnnun da ya haɗa albarka" "amen ya ma wacce ta koya albarka" tacetareda sakin murmushi, "amen" yace tare da sakin murmushi, "kai dai da wannan daughterntakaseAllah" Jabir yace tare da ɗaukan wayan SSB dake gefe saboda ƙaran shigowan saƙo da yaji, dubawa yayi a natse ya maida ya ajiye, kallon shi suka yi cike da son ƙarin bayani, "saƙonhalartan taron bayyana shi matsayin ɗaya daga cikin ƴan takaran President na jam'iyya meci ayanzu suka turo" Jabir yace tare da kauda kai..... "Subhanallah kasan na manta da wannan batun, har tenuren ya ƙare?" "Eh ai mun shiga ƙarshenshekaran nan da wasu watanni masu zuwa za'a buga gan-gan zaɓe" "lallai abun ba wuya" Abubukar yace tare da kallon Insu dake bin su da ido, "wallahi har yanzu ban gama gamsuwadamutanen nan ba subda wani manufa akan miƙa ƙoƙon bararsu gareka ba" Alhaji Munnir yacetare da kafe shi da ido, ɗago jiki yayi ya ɗau tean da ta ƙara mai ya kai baki yana zare baki yace"in suna da wani manufa na daban ma za su sha mamaki ne" jinjina mai kai yayi cike da gamsuwa, duk zancen da suke tana fahimtar inda suka nufa se dai yunƙurin to fa nata ba tayi ba dantasanwannan maganan ba na ta ba ne, jan wayan Jabir yayi ya tura taƙaitaccen saƙo, yana ajiyewayakalli Alhaji Munnir tare da faɗin "ka sanarwa Hajiya yakamata a je wajen da ita" jinjina kai yayi batare da yace komai ba... Ajiye cup ɗin yayi a natse ya zari tissue ya goge baki ya ja kujeran baya kaɗan ya miƙe, saurinmatsawa kusa da shi tayi kaman me san cewa wani abu, tsayawa cak yayi dan san jin abindazatace, jin ba ta ce komai ba, shi kuma be motsa ba yasa Abubukar dake danne dariya faɗin "InsuUncle na sauraranki" fidda ido tayi tare da juyawa ta kalleshi, wai dama tsayuwan jiran jinmezata ce yake? Ganin yanda duk suke ƙumshe dariya ya sa ta sakin murmushi tare da ƙara matsawa kusa da shi murya ƙasa-ƙasa tace "Uncle kayi kyau sosai" juyowa gefen da take yayi fuska cike da mamaki tare da baza mata ido, jinjina kai tayi tare da juyawa ga Abubakar cikedayanayinta tace "uncle Abubakar one picture please" tayi maganan a marairaice, jinjina kai yayi dan yasan ba ze iya magana ba, yana zaro waya ta riƙo hannunshi a natse tare da sakin murmushi ta kalli camera, yana ɗauka ta saki hannun tayi inda yake a guje, "mu gani uncleAbubakar" tace tare da amsan wayan, fuska cike da murmushi take bin hoton da ido, "kanadanumber na?" Tace tare da kallon shi, jinjina mata kai yayi cike da kulawa, "please uncle Abubakarka tura mun ta whattapp" "shiga ki tura" yace tare da ajiye cup ɗin hannun shi yayi inda SSByayi mutuwan tsaye, riƙe hannun shi yayi a natse tare da faɗin "muje" ba musu ya bi shi kamanwani mara lakka.... Tana turawa ta kwashe treyn da kayan kai ta ɗau wayanta ta fice, da sauri Lawiza ta amshi treyntare da faɗin "da baki ba wa kan ki wahala ba, za'a kwashe muje ki yi breakfast" "Uncle yanaina?"Tace idonta akan ta, "dining room" tace a natse murmurshi ta saki tare da faɗin "Anty LawizaAllah ya hana Abban Iman yi miki kishiya ina zuwa" tayi maganan tare da shigewa diningroomahanzarce.... Jan kujerar kusa da shi tayi ta zauna saboda tadda Feita da tayi ya saka mai abinci har ya faraci, soyayyan bread ta saka ma kanta ta tsiyaya juice ɗinta da kullum se an haɗa an ajiye matatafara ci a natse, gaba ɗayansu mai da hankali suka yi a abinda ke gaban su, ba wanda bakinshi yasaɓa da ɗan uwan shi, tun da ya ajiye spoon ta tsahirta ita ma, miƙewa yayi a natse, jan kujeratayi ta miƙe tare da ajiye ma Abubakar wayan shi, yana nufar ƙofa ta bi shi da sauri, dariyasukasaki cike da abubuwan da suke hanga, kaɗa kai Jabir yayi tare da faɗin "like mother like daughter" murmushi Alhaji Munnir ya saki tare da faɗin "sun ɗan ban-banta, Insiyyat ba tadasaurin sauka in tayi fushi, ita kuma tana da saurin sauka" dariya Abubakar ya saki tare da faɗin"ba abinda ya ban-banta ta da mahaifiyarta se yarintar da ke ɗawainiya da ita, amma ita matanada zuciya da saurin fusata, ba ta da wuyan haw sannan ba ta jimawa take sauka, ban faɗa makayanda muka yi da ita ranar registration ba ne?" Jinjina mai kai yayi tare da faɗin "duk banki ba, ita ba ta da riƙo kana ganin jiya sakanni kaɗan ta sauka kamar ba ta samu saɓani da Luba ba" "shine muka ce maka ita ma Insiyyat ba ta da riƙo, kafiya ne da ita, ko kamanta sulhun da kakemusu tsakaninta da SSB?" Jabir yace cike da tuna wasu shuɗaɗɗun lokuta, dariya Alhaji Munnirya saki tare da faɗin "ba zan iya manta wannan ba, musamman ma last sulhu da na musukafinyatafi UK" dariya suka kwashe da shi cike da tuna baya.... "Na maganann takardan da ya hurgawa Naja'atu take ko Murjanatu?" Abubakar yace taredakallon shi, "Nuratu" yace tare da sakin murmushi, dariya Jabir ya saki tare da faɗin "kai ranar nanan tada hankalin maza, ka ga yanda SSB ya rikice kuwa? Ita kuma Insiyyat se kuka take kamar wacce ta rasa iyaye" yayi maganan tare da kwashewa da dariya, "wai tsaya kasan har yaubansanme ya haɗa rikicin nan ba" Abubakar yace tare da kallon su, dariya Jabir ya saki tare da faɗin"kishi ne kawai na mata ya motsa, kasan Naja'atu" "ba fa Naja'atu ba Nuratun?" Alhaji Munnir yace fuska yalwace da murmushi, "to Nuratu ai duk ɗaya sunayen haɗe mun suke, ka ganetako?" Yace idon shi ana Abubakar, "na so dai gane ta" yace tare da gyara zama, "wata me ɗan murjewa nan fara me idanu" "oh naganeta, ko ba gajeran nan dake kusa da chair's din suAbdullahi Gambo ba?" "Ita, ka ganeta kuwa, to akanta rikicin

Chapter 33 of 109