natse ya sakko cike da kamalan shi, saura ma duk sakkowasuka yi, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "Ibrahim har ka rigamu zuwa kenan?" Murmushi yasaki tare da gaidata a girmame, "ga me gidan na ta nan" Ibrahim yace tare da nuna musuYayadake dumfaro wajen, ɗago kai yayi ya mishi kallon sakanni ya maida kai ƙasa, "Allahu akbar" Hajiya tace cike da tausayawa, yana ƙarisowa ya marabce su fuska faɗaɗe da murmurshi, miƙamusu hannu yayi suka yi musabaha da mazan, "bismillahn ku mu ƙarisa ciki" yace tare da nunamusu hanyar da ze sada su da side ɗin shi ta waje, ba musu duk suka ɗau hanya....
Suna isowa suka faka motoci a waje, sakkowa suka yi suka dafa mata baya, kai tsaye sideɗinbaƙi
ta kai su, tana tabbatar da zaman su ta fito a natse, kallon Shureim Annur yayi tare da faɗin"motocin SSB gidan nan suka zo" "na gani" yace tare da gyara zama, "kirata mana" Zubair yacetare da kallon shi, "oh wutan ciki gamu nan dai mun iso, komai ma ze faru a hankali....
Tana shiga parlor ta miƙa mata wayan tare da faɗin "suna side ɗin baƙi" "su waye?" Lailahtaceda kulawa, "baƙi ne suka zo mana gaisuwa" tace a hankali, "to ku tashi kuje mana" ƙanwar Lailahtace tare da kallon su, "Sadam kuje ka musu jagora, Farisat riƙe su kuje" tace da kulawa, "kumayakamata ku zo" Yasmin tace tare da miƙewa, "to ku je dai gamu nan" tace tare da bin sudaido, jinjina mata kai suka yi duk suka mimmiƙe, kama hannun Insu Sadam yayi suka fice a natse, dasallama suka shiga parlorn, gan8a ɗayan su suka zuba musu ido, ƙarisawa gefe suka yi sukazauna a natse, zaunar da Insu Sadam yayi ya ƙarisa kusa da su ya miƙa musu hannu a girmame, musabaha suka yi da shi gaba ɗayansu, "ina kanwartawa a nan?" Annur yace tare da bazaidotsakanin Farisat da Yasmin, ganin ba wanda yace komai ba kuma me yunƙurin cewa wani abuyasa shi zaro waya ya dannawa numberta kira, ɗago kai tayi a natse ta kalleshi tare da kashekiranta maida kanta ƙasa, gyara zama yayi tare da faɗin "Allah ya baku haƙuri da juriyar rashinta, agaskiya anyi rashi" "amen" suka ce baku na a haɗe, "ita ki ke bi?" Yace a natse, "wa ne?" Tacekai
a ƙasa, "ba kince Antynku ba ce ta rasu?" Yace idon shi akanta, jinjina kai tayi ba tare da tacekomai ba, "mahaifiyarsu ce, haka suke kiranta" Lailah da suka shigo tace tare da nemanwajetazauna, nan duk jikin su yayi sanyi, duk a zaton su Antynta ne saboda cewa Anty da tayi, kasacewa komai suka yi se bin su da kallo me cike da tausayawa da suka yi, "Allah ya baku juriyadahaƙuri" Shuriem yace jiki a mace, "amen" suka ce tare da goge hawaye, miƙewa Lailah tayi bayansun mata mata ta'aziyya ta fice, ba ta daɗe ba ta dawo ita da yaran dake gidan suka ajiye musuruwa da lemu, zaro waya Sadam yayi daga aljihu tare da ɗaga kiran da ya shigo ya kara a kunni....
"Muna side ɗin baƙi" yace a natse, "okay gamu nan" yace tare da zare wayan, "ku ɗan manaafwaana neman mu a cikin gida" jinjina mai kai suka yi cike da gamsuwa, miƙewa yayi ya riƙo hannunInsu tare da faɗin "muje Yaya na neman mu" mimmiƙewa suka yi tare da musu godiya sukafice, sauke numfashi Zubair yayi tare da faɗin "dole ta kasa zuwa wajen taron nan" "daina batuntaro
yaran nan sun firgita da wannan rashin, ka ga yanda duk suka zama kuwa? Duk da ba mutaɓaganin su a halin farin ciki ba, amma mutuwan daga gani ya girgiza su" pro1 yace tare da jinjinashaƙuwar da ke tsakanin su, "Allah ya yafe mata" Annur yace jiki a sanyaye, "lallai sun yi babbanrashi, dama Hajiya Amina mahaifiyar su ce?" Humen leader tace cike da mamaki, "kin santane?" Khalid yace da mamaki, "kai ma ka santa Hajiya Amina Abdussamad wacce ta tsaya tsayindakawajen neman wa yarinyar nan da mahaifinta ya mata fyaɗe adalci a kotu" tace cike da jimantalamarin, "Barr Amina Abdussamad!" Suka ce baki a haɗe, "ita" tace tare da kallon su....
Tunda suka zazzauna Yaya ya kira Baba Mari da Sa'adatu suka kai musu ruwa da lemu, zamayayi
suka ƙara gaisawa a natse tare da mai ta'aziyya, amsawa yayi a dake, "ciwo tayi ne?" Hajiyatacetare da kallon shi, "a'a haihuwa ta zo yi" yace a hankali, "Allahu akbar ka ce mun shahidiyace" Hajiya tace cike da jimami, "dama har yanzu tana haihuwa" ɗaya daga cikin matar da aka zodasutace da mamaki, kallon da Alhaji Munnir yayi mata tare da kauda kai ne yasa ta ɓame baki, "inayaran na ta, mahaifiyarta ta zo ne?" Hajiya tace cike da jimami, "bari in kira su, Allah ya wamahaifiyarta rasuwa shekara biyar kenan, se dai ƙanninta da suka zo" yace tare da zaro waya, zare ido suka yi da mamaki tare da kallon juna, sauke wayan da ya kammala kira da shi yayi tareda faɗin "ta rasu" "Allahu Akbar" Hajiya tace tare da goge hawaye, "wallahi ba mu da labari, inaYayanta Hassan?" Alhaji Jamilu wanda shine Babba a ƴaƴan Hajiya yace tare da kallon Yaya, "jiyaya koma an neme shi a wajen aiki" Yaya yace tare da gyara zama, sallama Lailah ita da sauranƴan uwanta suka yi, ganin waƴanda ke zaune ya sa su sakin ido da baki tare da bin su da ido, kuka Hajiya ta saki tare da rufe fuska da hijabin jikinta, kuka suka saki tare da duƙewa a wajen, haka suka yi ta kuka ba wanda ya iya cewa komai, "Hajiya ya isa haka, kema ba isashshenlafiyane da ke ba" Alhaji Jamilu yace tare da kallon ta, "kayya Jamilu bar ni inyi, Hajiya Yasmintarasuba na da labari, ga shi yau ita ma wannan ba ta" "se haƙuri suka ce jikkuna a mace, sallamaFarisat dake gaba riƙe da hannun yara biyu tayi ta shigo ta zauna nesa da su, shigowa suYasminsuka yi kawuna a ƙasa suka zazzauna, ɗago kai yayi ya zube musu ido, kana ganin su ba seanfaɗa maka ba, kasan jinin waye su....
"Waƴan nan duka ƴaƴanta ne?" Hajiya tace idanunta akan su, jinjina kai Yaya yayi a natse, "ma
sha Allah, Allah ya muku albarka, Allah ya raya ku ya jiɓanci lamurran ku, ya gafartawa
mahaifiyar ku" "amen" suka ce kawuna a ƙasa, "ya sunayen su?" tace tare da kallon Yaya, "gababan nan sunanta Farisat" gaba ɗayansu suka ɗago kai tare da kallon Farisat, fashewa dakukaHajiya tayi tare da faɗin "a she da gaske take da tace zata mun takwara, matso kusa takwaratamatso kusa" tayi maganan tare da miƙa mata hannu, ba musu ta miƙe a natse tayi kusa daita, tana zama ta fashe da kuka,....
"Wannan shine me bi mata Sadam" "Sadam!" Alhaji Jamilu yace da mamaki, jinjina kai Lailahtayi
tare da faɗin "eh takwaran Daddy" girgiza kai yayi tare da faɗin "ba mu taɓa sanin ta sakasunayen su ba" kauda kai tayi ba tare da tace komai ba, "ga ta ukun Yasmin" yace tare da nunata, "Allah sarki ku matso kusa da ni ƴan albarka" Hajiya tace a raunane, matsawa suka yi jiki asanyaye, "ga na huɗun Insiyyah" ɗago dara-daran idanun shi yayi ya sauke a saman fuskanInsiyyah da ko gezau ba tayi ba, bare ta nuna ta fahimci abinda suke a wajen, bin ta kawai sukayi
da ido cike da mamakin sunan da aka kirata da shi, "ga na biyar Nafisat, ga na shida Sahabee" mutuwar zaune suka yi cike da mamaki, "zo nan" Alhaji Munnir yace tare da yafuto Sahabee, bamusu ya tashi ya isa gare shi, zaunar da shi yayi a tsakiyan su tare da shafa kan shi, "ga nabakwai
Sa'eed, Umar shine na takwas ɗin" ya idda bayanin a sanyaye....
"Allah ya albarkace ku" Hajiya da ta kasa cewa komai tace tare da ƙara tsarkake buwayanmahaliccinta, duk waƴan nan yaran mutun ɗaya ne, wa ya isa ja da buwayan gagara misali, "Khadijatu a ina ku ke da zama?" Hajiya tace tare da kallon wanda ta kira da sunan, "Ɓadamayya"tace a hankali, cike da mamaki suka kalleta, "dama kuna can!" Alhaji Jamilu yace tare da kamahaɓa, "eh" Lailah tace a natse, "a can Hajiya Yasmin ta rasu?" Hajiya tace tare da kallon su, girgiza kai wacce da alama magana ne dameta ba tayi tare da fafin "anan Bertuwa ne, a wajenAnty ta rasu" "se haƙuri Salwa Allah ya gafarta mata" Hajiya tace tare da kallon wanda ta bataamsan, "haba Lailah amma a ce ku kasa sanar mana? Ba ku kyauta ba" Alhaji Jamilu yacecikedarashin jin daɗi, ba wanda tace komai a cikin su, kallon su Sadam Lailah tayi tare da faɗin"kutashi
kuje ku kammala da baƙin" ba musu suka miƙe a natse suka fice....
"Allah sarki rayuwa" Hajiya da ta bi su da ido tace cike da tausayawa, gyara zama Yaya yayi tareda faɗin "Hajiya idan ba damuwa ina son magana dake da shi" ya idda maganan tare da nunaAlhaji Jamilu, "to ba damuwa" Hajiya tace tare da miƙewa, tashi Alhaji Jamilu yayi a natsetaredariƙo hannun Hajiya suka dafawa Yaya baya, suna ɓacewa ganin su, wacce ta ƙi cewa komai tunshigowan su ta sauke ajiyan zuciya tare da faɗin "ƙarshen rayuwar kenan, ka shuka na gari kajeka girba, ka shuka na tsiya ma kaje ka girba, Allah ka ba mu iko da daman aikata dai-dai, kar mutafi da nauyin kowa akan mu" ba wanda yace komai a cikin su Lailah, se matashin kusa daitawanda da alamun mutuwan ya duke shi yace "kar ki ƙara cewa komai Lubabatu....
Suna shiga Annur ya gyara zama tare da faɗin "zamu zo mu tafi ne yanzu in sha Allah" "dakutsaya Yaya ya fito yana tare da baƙi ne, se ku mai ta'aziyya" "to bari mu jira shi" yace tare dakallon Sadam da yayi maganan, "a she Barr Amina mahaifiyar ku ce?" Yace cike da alhini, murmushi ya saki tare da faɗin "eh" "lallai jama'an gari ma sun yi babban rashi, Barr Aminaadalace me nemawa kowa adalci" Zubair yace murya cike da alhini, "adalcin Anty ya isa koina"
Insu tace cike da tabbaci, kallonta suka yi cike da farin cikin maganar da tayi da sauri sukarumgumeta tare da sakin kuka, haƙuri su ka dinga ba su na su hankulan a ta she....
"Wannan shine dalilin da yasa na nemi magana da ku" Yaya yace tare da goge hawayendasukajiƙa mai fuska sharkaf, "kana ganin babu wani matsala?" Hajiya tace tare da kallon shi, girgizakai
yayi tare da faɗin "babu in sha Allah" "shikenan Allah ya sa komai ya zo ƙarshe kenan" Hajiyatace murya a sanyaye, gyara murya Alhaji Jamilu yayi tare da faɗin "me da me ake buƙata?" "ba'abuƙatan komai" yace tare da zaro wayan shi dake neman a gaji, ɗagawa yayi ya fice a natse, kallon Hajiya Alhaji Jamilu yayi tare da buɗe baki ze yi magana, ɗaga mai hannu tayi taredafaɗin "ba yanzu ba" jinjina mata kai yayi ya koma jikin kujeran da yake kai ya tsuke baki....
Da sallama ya shiga parlorn, buɗe idanu suka yi waje tare da kallon shi, murmushi ya sakinmusutare da basu hannu su kai musabaha, gaishe shi suka yi a girmame tare da mai ta'aziyya, "amen-amen Allah ya amsa" yace tare da kallon Sadam dake cewa "sune jama'an Aminan juna" jinjinakai yayi tare da faɗin "ma sha Allah, Allah ya saka da alheri" yana kai nan ya shafa kan Insuyajuya, "Yaya Anty Insu tayi magana yanzu" Nafisat tace cike da farin ciki, juyowa yayi fuskafaɗaɗeda farin ciki tare da faɗin "da gaske Nafisat!" "Eh Yaya" tace tare da kallon shi na ta fuskanɗaukeda farin ciki, "zo muje" yace tare da riƙo hannunta miƙewa tayi a natse suka fice tare, "Alhaji
Abdussamad shine mahaifin ku!" Humen leader tace tare da kallon su, jinjina kai Sadamyayi tareda faɗin "shine" ba wanda ya kuma cewa komai a cikin su se mimmiƙewa da suka yi dantafiya, har bakin gate suka musu rakiya tare da musu godiya, suna ficewa suka juyo suka koma ciki....
Fitowa mazan suka yi dan halartan sallahn la'asar da aka kira, ana idar da sallah liman ya
dakatar da jama'an dake yunƙurin tashi, nasiha yayi na tsayin mintina biyar kafin ya juya gaYayadake zaune jiki a mace ya buƙaci walliyai su matso, matsawa yayi Alhaji Jamilu ya matsa anatse, cike da mamaki Alhaji Munnir da su Ibrahim suka bi Alhaji Jamilu da ido, shi ko gogan dakezaunekusa da Alhaji Munnir ko motsawa be yi ba bare ya nuna ya fahimci abinda suke yi a wajen, bayangabatar da duk sharuɗɗoɗin da addini da ƙa'idojin da al'ada suka tanadar liman ya gyara zamatare da faɗin "ma sha Allah aure ya ɗauru Allah ya zaunar da su lafiya, ya ba su haƙuri da juriyarzama da juna, "amen" jama'an dake cike da mamaki suka ce tare da kallon sunan wanda akakira, se a lokacin suka hankalta da wasu fuskokin...
Suna fitowa kai tsaye ya dumfari motar shi, da sauri Ibrahim ya buɗe mai ya shige, kallonshi yaɗago kai yayi a natse tare da faɗin "za mu yi magana" jiniina mai kai yayi tare da ba wa Alhaji
Munnir hanya ya shige, da sauri driver ya ja suka bar wajen, fitowa su Hajiya suka yi a natsesukashishshige mota, suka ƙara sallaman su a natse suka bi bayan motan shi, komawa ciki suLailahda su Farisat sukayi, bin su da ido Yaya yayi tare da sauke numfashi me sauti ya lumshe ido, wasu
shuɗaɗɗun batutuwa na mai kai komo a ƙwaƙwalwa....
Comment fans🥰🙏
🫀MUGUN TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
Created and written
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Four
"Ɗauki ku ci mana Farisat" Lailah tace tare da kallon Farisat da ta ƙure abincin da Sa'adatutaajiye a gaban su ta ja gefe da ido, girgiza kai tayi tare da faɗin "ba zamu ci ba" tayi maganantareda fashewa da kuka, "haba Farisat ke da zaki dinga tausan ƙannin ki ke kuma ke ƙara musudamuwa, yanzu me ne ne amfanin hakan? So ku ke wani cutan ya shige ku? Tun da muka zobawacce ta zauna taci abincin kirki a cikin ku" Khadijatu tace tare da share hawaye, fashewadakuka Yasmin tayi tare da faɗin "Anty Khadijatu taya zamu iya cin abinci bayan me lallaɓamudararrashin mu muci ba ta nan, bayan wacce take gayyato mu mu ci tare da ita tayi nisa damu, meyayi mana saura mu kuma, shikenan ai komai ya zo ƙarshe, Anty ta tafi da dukkanin walwalanmu, ba mu da sauran wani farin ciki".... Kuka gaba ɗaya suke yi cike da rauni, share hawaye Lailah tayi tare da faɗin "Allah yana sanedamu Yasmin, Anty Amina ba matsayin Anty kaɗai take gare mu ba, uwace, kuma uba ce, itaceta maye mana gurbin iyayen mu da ba su, yau gashi ita ma ta tafi inda suka je, mu ma abindakuke jin nan shi muke ji, se dai mun fawwalama Ubangiji komai mun rungumi jarabawar mu" turoƙofan general parlorn Yaya yayi ya shigo baki ɗauke da sallama, shigowa Salman da Sadamdakeriƙe da baƙin leda suka yi a natse, neman waje yayi ya zauna a natse tare da kallon su, "meyafaru?" Yace muryan nan a shaƙe...
"Ba mu san ya zamu musu ba Yaya, ba wacce ta saka komai a cikinta yau, tun jiya da HajiyaSuraiyya ta matsa musu suka sha tea har yanzu ba su ƙara cin komai ba, mun ce su ci suncesunƙoshi, ya zamu yi Yaya? Rashin nan gaba ɗayan mu aka mana, ba ma da kowa mu ma se ita, gashi
ta tafi, Yaya Hassan be ma san a inda muke rayuwa ba bare watarana musa ran ze zo dubamu, ita ɗin ce uwa ita ɗin ce uba, ita ce me tuntuɓan halin da muke ciki, yau gashi ba ta" Salwatacetare da fashewa da kuka me rauni tana tuna wacece Antyn ta su....
Gaba ɗaya jikin su ne ya mace, "ta mana komai, ta tsaya mana, ta kawar da damuwoyin mu, yauwa muke dashi da ze taya mu kuka ya taya mu dariya" Khadijatu tace tare da fashewa da kuka, kuka suke me taɓa zuciya, kana ji kasan daga ƙasan zuciyoyin su yake fitowa, goge hawayeSa'adatu dake sharɓan na ta kukan a gefe tayi tare da faɗin "ba wanda be san me ya farudarayuwata a cikin ku ba, uban da ya haifeni shi ya hakkemun, mahaifiyar da ta haifeni ta ji ciwonda raɗaɗin naƙuda ta danne komai ta hana ni ko wani yunƙuri na neman ma kaina adalci, ƴanuwa na da sauran iyaye kowa ya sani amma yayi shiru, ita ta ɗaga murya dan nema munadalci, ba ta samu sukuni da hutu ba se da ta tabbatar na samu adalci, ba ta sanni ba, n8a ta sandanginaba, labarina kawai taji daga wata makofciyar mu abokiyar aikinta, na fuskanci tsana hantarakyara daga wajen mahaifiyata da ƴan uwana saboda na buɗe baki a court na faɗi gaskiya, inacutuwa da zaman da nake da su, haka ta ƙara dawowa a karo na biyu dan nema min adalci, dagaƙarshe ɗakko ni tayi ta dawo da ni cikin iyalanta, ta bani makwanci me kyau, ta bani abinci metsafta, ta kula da lafiyata da ilimina, ta tsaya mun ga dukkanin wani damuwoyina, ba ta taɓaban-banta ni da ƴaƴanta ba, hatta da makarantar da suke zuwa nan nake zuwa, shin ku aka warashi
ko ni da bana da sauran wani gata a duniya? shin kuka zan ta yi ko kuma addu'a zan ta mata?Ji
nake da ni na tafi ita ta cigaba da rayuwa, dan rayuwarta na da matuƙar mahimmanci ga ireirena waƴanda irin ƙaddarata ya faɗa musu, me ya mun saura ni kuma, ta fi ƙarfin in kiratadagarkuwa, ta wuce wannan in na kirata da haka na rage mata matsayin da take da shi a wajena" taidda maganan cikin rishin kuka....
Girgiza kai Farisat tayi ta rungumota ta cigaba da rera kuka, gyara zama Yaya da yayi ƙoƙarindanne damuwar shi yayi tare da faɗin "shin ni ba kwamin kallon ɗaya daga cikin ku ne Lailah?Koban can-canci zama ɗan uwanku ba ne?" Girgiza kai Salwa tayi da sauri tare da faɗin "Yayakawuce Yaya a wajen mu kai ubane" murmushi ya saki tare da goge hawayen da ya gangaromai
tare da faɗin "ku saka hakan a zuciyan ku, zan tsaya a dukkani damuwoyin ku da ƙarfina daaljihuna, zan zame muku uban da ku ke kukan rashi, zan zame muku uwar da ku ke kewanrashi, zan zame muku Antyn da ku ke kururuwar rashi a yau" jinjina kai suka yi tare da goge hawayenda yake zubo musu, kallon Sa'adatu yayi tare da faɗin "har yanzu ki na da gata Sa'adatu tundakina da mu, zamu maye miki gurbin Antyn ki mu da sauran ƴan uwanki, kar ki taɓa jin ke baɗayadaga cikin mu ba ne, Antyn ki bata tafi ba se da tabar miki bangwayen jingina, muna fatanAllahya fiddo miki da miji na gari ki tafi gidan ki kema" jinjina kai suka yi cike da gamsuwa, kallonSalman da ke sharan hawaye Yaya yayi tare da faɗin "ka zama namiji mana Salman" kuka yafashe da shi tare da faɗin "Yaya ka gafarce ni, ko ranar da Anty zata rasu mun haɗu, munyi
magana da ita sosai, har na ce zan rakata hospital tace in bar shi ba za su jima ba, a she tafiyankenan ba zamu ƙara haɗuwa ba, da nasan in ta tafi ba zata dawo ba da ban barta ta tafi ba" yanakai nan ya duƙe yana kuka me taɓa zuciya.... Bin shi da ido Farisat kawai tayi cike da mamakin irin kukan da yake, murmushi Yaya ya saki tareda share hawaye, "ina Baba Mari?" Yace tare da kallon su Lailah, "gani Alhaji" Baba Mari daketsaye saman koridon dake tsakanin kitchen da general parlorn tana nata kukan tace taredagoge hawaye, "a zubo musu wani abincin wannan yayi sanyi" jinjina kai tayi tare da juyawatanufi
kitchen da sauri, "Sa'adatu ɗau wannan ki kai kitchen" yace tare da kallon Sa'adatu, da sauri taɗauka ta nufi kitchen, "Salman taya Sadam tattara su suje side ɗina" yace tare da kallonSalmanda fuskan nan yayi jazur, jinjina kai yayi tare da miƙewa a natse ya ɗau Umar ya riƙo hannunSa'eed" miƙewa Farisat da Yasmin suka yi a hankali suka dafa mai baya, kamo hannun InsuSadam yayi tare da riƙo Sahabee, tashi Nafisat tayi suka shige, gyara zama Yaya yayi taredafuskantar su Lailah da suka dawo da fuskokin da suka bi su da shi.....
Suna shiga suka nemi waje suka zazzauna, matsawa gefen Farisat Salman yayi tare da faɗin"danAllah kukan nan ya isa haka, addu'a zaku dinga mata za ta fi maraba da shi, kukan nan ba komai
yake ƙarawa mamaci ba, addu'an yafi" ya idda maganan a sanyaye, jinjina mai kai tayi ba tareda
tace komai ba, "Yasmin ku daina dan Allah" yace tare da kallon Yasmin, jinjina mai kai tayi itamabata ce komai ba, "ku dubi yaran nan, ƙwarin gwiwan ku suke buƙata, se dai ku kan ku ba kuƙarfafa kan ku ba bare ku ƙarfafa su, kukan nan ze iya cutar da lafiyar ku, dan Allah ku yi haƙuri, ku maye ma ƙannin ku gurbin Anty, Farisat ke ce wacce zata yi hakan, gashi kema kin kasaƙarfafa kan ki, Yasmin ko kun manta da Allah yana tare da masu haƙuri ne? Dole in muntunarayuwar da muka yi da ita mu koka, amma ba irin kukan nan da ku ke ba, na tabbata da yauAntyna raye se ranta ya ɓaci da kukan da ku ke" ya idda maganan tare da amsa sallaman Sa'adatudaBaba Mari da suka shigo hannuwa riƙe da treyn da suka haɗo musu abinci a kai, ajiye wa sukayi
suka fice....
Cire plates da spoons ɗin dake kan treyn yayi ya ajiye a gefe, jawo kulan dake gefe yayi yabuɗejuye rabin farar shinkafan ciki yayi ya maida sauran ya ajiye, jawo na miyan yayi a natse, zubamusu a kai yayi ya jera cokulan a gefen treyn, kallon su yayi ido cike da magiya, matsawa Farisattayi a natse ta ɗau cokali ta saka a ciki, ɗauka Yasmin tayi ta saka, gaba ɗayan su suka ɗaucokulan suka saka, kallon Sadam Salman yayi tare da mai alama da ido, jinjina kai yayi taredaɗauka a natse ya saka ya ɗibo ya kai bakin Insu dake zaune ba um ba um-um, buɗewa tayi anatse ta amsa, sauke ajiyan zuciya Salman yayi tare da duƙar da kai a dabarance ya goge hawaye, be haɗa komai da su ba bayan makoftaka, se Farisat da yake dakon so, amma ba abinda Antybata mai ba a rayuwa, dalilin kyakykyawan zuciyanta yasa shi ƙaunar jininta, "ka ci" Farisat taceahankali kai a ƙasa, girgiza kai yayi tare da faɗin "zan koma gida yanzu" yana kai nan ya miƙeyafice da sauri....
Sauke ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya Lailah tayi tare da faɗin "kuma sun amince!" "Eh" Yaya yaceahankali, "hmm Allah yasa kar labari ya mai-maita kan shi" Khadijatu tace cike da damuwa, "insha Allah alheri ne" Yaya yace tare da miƙewa idon shi akan Salwa tare da faɗin "mijinki yakirani ɗazu, yana san ki koma" narai-narai tayi da ido cike da damuwa, murmushi ya saki cikedaƙarfin hali tare da faɗin "na nemi alfarman ya barki ayi bakwai tukun" jinjina mai kai tayi cikedasamu sassauci, "se ki shirya ze zo ana gobe, in an yi addu'a zaku tafi" jinjina kai tayi jiki a sanyaye, "kuma ku shirya ranar zaku koma ɗakunan ku" yana kai nan ya wuce, ba wacce jikinta be yi sanyi
ba a cikin su, se dai ya za suji, kai tsaye side ɗin shi ya shiga, tadda su suna cin abinci ba ƙaraminfarin ciki ya sa mishi ba, da sauri ya ƙarisa ya zauna ya ɗau cokali ya saka, yana ɗibowa zekai baki
ya tsaya cak, zuba mai ido kawai suka yi suna tuna shuɗaɗɗun abubuwa, ganin sun sadda kai yasa shi ajiye cokalin a natse, ɗauka Insu tayi ta ɗibo ta kai mai baki, buɗewa yayi a hankali tazubamai, fashewa da kuka yayi tare da rumgumeta, zame jikinta tayi a hankali tare da fara sharemai
hawayen, haka suka cigaba da cin abincin ba din yana musu daɗi ba se dan kar su butulcewarahmar Ubangijin su....
Shinfiɗe Sahabee da ya ɗakko a ƙarshe a kusa da su Sa'eed yayi tare da jan musu blanket, addu'aya tofesu da shi ya miƙe a natse ya isa durowan wedrobe, duƙawa yayi a natse ya buɗe, ɗakkowani madai-daicin littafi yayi tare da maida murfin durowan ya rufe, miƙewa yayi a natseyaragemusu hasken ɗakin ya fice tare da rufo musu ƙofan, yana fitowa idon
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 109