baɗini, Allah ya hanashi gamoda duk wani sharrukan dake cikin mulki, Allah ya sada shi da alherukan dake cikinta" ya iddakaranto addu'an a natse murmushi faɗaɗe a saman fuskan shi, "wow wacece haka!" Dattijuwantace tare da kafeshi da ido, murmushi dattijon ya saki tare da faɗin "amen wacece!" Murmushi yasaki tare da faɗin "your daughter in-law" murmushi ne ta kuɓuce musu tare da bin shi da ido, "ohkuna sa ni jin kunya" yace tare da kare fuskan shi da hannu, dariya suka saki cike da so daƙaunanda suke mai... Zare ido ƴan mata biyun dake zaune wanda su kayi bala'in kama da matasan samarin dakezazaune suka yi tare da faɗin "brother dama kana da girlfriend!" Harara ya watsa musu taredakauda kai, "wallahi banyi tsammani ba" ɗaya a cikin ƴan matan tace tare da tashi tayi indayake, "brother let me see her" ɗayan da ta ta so tace tare da zama kusa da shi, kauda kai yayi batareda yayi ko wani yunƙuri ba...
"Mu ma muna son ganinta" dattijon yace cike da kamala, "please brother kaji su Daddy manasonganinta" tace a marairaice, guntun murmushi ya saki tare da ɗago waya a natse ya wuce indayaadana hotunanta ya miƙa musu, zare ido wacce ta matsa akan ya ba su tayi tare da faɗin"wonderful she is beautiful" ta idda maganan idonta ƙyam akan hoton Yasmin da ba ta sandawanzuwan shi ba ma, ranar waliman bikin Annur ya mata sanye take da hijab maroon colour harƙasa, tana tsaye da alamun wani take jira, tasowa sauran suka yi suka rufu akan wayan, nankowa ya fara furta albarkacin bakin shi, "to ku ba mu" dattijuwan tace tare da miƙa hannu, "oneminute Mommy" matashiyar tace idonta akan hotunan da suka fara ja suna gani...
"Minha!" Mommy tace da ɗan sauti, "sorry Mommy" tace cike da fata, "tashi ki kai musu" Shureimyace tare da kallon ta, miƙewa da sauri tayi ta nufe su, "brother ta na da kyau sosai" ɗayanbudurwan tace idonta akanshi, murmurshi ya saki tare da dafa kanta cike da wani yanayi yace"i
known and mentally fit" murmushi ta saki tare da faɗin "kana sonta kuma sosai?" Guntunmurmushi ya saki tare da jinjina mata kai, "brother" tace cike da son je fa mai wani tambayan, "shii Mihna" yace tare da saka hannun shi a saman laɓbanshi, murmushi ta saki tare da binshi daido, abu ne da ya kasance sabo a gare su, tun da suke ba su taɓa jin yayi magana akan watamaceba da sunan yana so se yau... Murmushi Daddy ya saki tare da ɗago kai ya zube mai ido, kauda kai yayi ba tare da yace komai, "ka na sonta?" Yace cike da kamalan shi, zuba mai ido suka yi gaba ɗayansu dan san jin amsandaze ba da, "yes i really love her" yace tare da baza musu na shi idon, murmushi suka saki cikedafarin ciki yayinda matasan suka miƙe suka fara taka rawan farin ciki....
"Se dai ita ba ta sona" yace a hankali, tsayawa cak suka yi tare da zuba mai ido, miƙewa yayi yakoma kusa da Daddy ya zauna a ƙasa kusa da ƙafafun shi tare da riƙo hannun na dama a hankali
tare da faɗin "ban san me na mata ba ba ta so na, shekara biyu da watanni kenan ina miƙamataƙoƙon bara tana dawo mun da shi babu ɗigon ko ƙwayan hatsi, tana da natsuwa, hankali, girmama na gaba, sanin yakamata, biyayya ladabi, ba abinda ba ta haɗa ba, su suka munjagorawajen isa gareta se dai ta kasa ɗaga kai ko sau ɗaya ta kalleni bare ta fahimci inda na dosa,
addu'a kullum nake Allah ya rage mun abinda nake ji a zuciyata game da ita, se dai wa kullumƙara jinta nake a cikin zuciyata, ba ta ga maciji ga duk wanda ze mata magana na, tana matuƙargirmama Annur amma saboda magana da yake yawan yi mata a kaina ta fara ja baya da shi, narasa ya zanyi, Daddy ko ba na da nagartan da za ta iya maido mun da so ne?" Ya idda magananaraunane murya na rawa hawaye na gangara....
Sakewa jikkunan su gaba ɗaya yayi, banda bin shi da kallon tausayi ba abinda suke, sharehawaye Mommy tayi tare da girgiza kai cike da tabbaci tace "daina faɗin haka Shureimkai kedanagartan da za'a so ka kuwa, ita ma ba ta fahimce ka ba ne, na san duk ranar da ta fahimcekazata maido maka da so, har da tukuicin ƙauna" ta idda maganan cikin muryan rarrashi, girgizakai
yayi ba tare da ya ɗago ba tare da faɗin "yaushe Mommy! Ba wannan ranar, bana jin wannanranar na tafe nan kusa, Yasmin ba zata taɓa sona ba, tace babu gurbin soyayya a zuciyanta" yaidda maganan raunin shi na bayyanuwa, murmushi Daddy ya saki tare da girgiza ma Mommydake yunƙurin magana kai, shiru tayi tare da bin shi da ido, ko ba'a ce musu ɗansu kuka yakebasun fahimci hakan, lallai son da yake ma yarinyar ba ƙaramin so ba ne tunda har ya ke zubdahawaye haka akanta, ba ƙanƙanin abu ke sa shi kuka ba tun da ya taso har girman yayi, sedai yaugashi yana kuka rurus akan so, lallai ya kamu da matsanancin so wanda be san madafa ba, sedasuka tabbatar ya samu natsuwa da gamsuwa dan kan shi sannan Daddy ya ɗagoshi ya zaunar akusa da shi... Murmushi ya sakin mai tare da faɗin "ka zama namiji mana Babana, maza ba sa sarewa, tsayawasuke a filin daga har se sunga karshen yaƙi, ka tabbata kana sonta?" Jinjina kai yayi tare dafaɗin"matuƙar so" "to ka ƙara dage damtse, ka jajirce, ka gayyato dakiya da haƙuri ka ƙulla amintadasu, zaka yi nasara" ya idda maganan cike da ƙarfafashi, jinjina kai yayi a natse yana me jinzeƙarajira ko nan da shekaru hamsin ne masu zuwa, murmushi Mommy ta saki tare da faɗin, "zatafahimceka Son, zata so ka, ka ƙara haƙuri, komai ze zama labari" jinjina mata kai yayi idonshi
akan ta, "ka kuma cigaba da faɗawa gagara misali, mu ma zamu taya ka, na san ze dube mu" "insha Allah" matasan suka ce jikkuna a sanyaye, "ku zo nan" yace musu tare da kallon su, dagudusuka yo kan shi kowa na faɗa mai kalamai masu sanyi...
"A ina take?" Daddy yace a natse, "a nan Bertuwa ne, Balaji 2, kama san iyayenta, ƴar latebarrister Amina Sa'eed Bertuwa ce" yace a natse, "wow! Kana nufin yarinyar barrister ce!" Mommy tace cike da jin daɗi, "ita ce" yace a natse, "in sha Allah matarka ce" tace a zumuɗe, murmushi Daddy ya saki tare da faɗin "a she ƴar gida ce, ko jiya muna tare da mahaifinta
barrister Abdussamad Umar Bertuwa, lallai in ka auri ɗiyarsu zanyi matuƙar farin ciki, danwaƴan nan mutanen ba na banza ba ne" "in sha Allah ze sameta Honey Allah dai ya juyo dahankalinta gare shi" Mommy tace a zumuɗe, "amen" suka ce cike da fata, ɗaukan wayanshi dakeneman agaji yayi ya miƙe tare da faɗin "akwai admin meeting ɗin da zamu yi yau na mantadalokaci sam, se na dawo" yace tare da ficewa, da murmushi me ɗauke da tsan-tsan ƙauna sukabi
shi....
"Lallai labarin nan yayi matuƙar faranta mun" Daddy yace tare da kallon Mommy, "dole" tacecike da murmushi, ɗiyar barrister Amina Sa'eed a gidana, zan yi farin ciki da hakan" ya kumacewa fuska faɗaɗe da murmurshi, murmushi Mommy ta saki tare da faɗin "a she ba a banzaɗanake santa ba" dariya Daddy ya saki tare da bin ta da ido.... Da sallama ciki-ciki ya shiga parlorn, amsawa kanninshi suka yi hankulansu akan zabgangabansu, "ina Mommy?" Yace fuska a muttuke, "tana ciki" Nafi tace tare da kauda kai, wucewabedroom ɗin ta yayi kai tsaye ba tare da neman izini ba, tura ƙofan yayi ya faɗa tare da ɗagasallama, "wa'alaikumussalam wai ni Sudais ba na ce maka ka daina faɗomin daki haka babusallama ba ne?" Gude tace cike da ɓacin rai tare da kallon shi, "na fa yi" yace tare da nemanwajeya zauna, "ka yi a ina? Dama se an shigo ake sallama ne?" "Ni duk ba wannan ba, ki na da labarinauren Farisat kuwa?" Yace idon shi akan ta, "Farisat!" Tace da mamaki, "eh Farisat ɗin uncleAbdussamad" "to a kaina take da zan nemi sani?" Tace tare da kauda kai, "ke fa matsalarki kenan, kwata-kwata ba kya tsayawa ayi abin arziƙi dake" yace cike da rashin jin daɗi...
"Da ubanka ne ba'a abun arziƙi ba dani ba, tashi ka fice mun anan kar in saɓa maka, da ruwanadaaurenta ne? In ta ga dama 5a mutu babu auren ba ni da damuwa da hakan" "kai kai Mommygaskiya ki na da matsala, yarinyar ɗan uwanki ne fa, ki daina magana irin haka babu kyauko
kaɗan, shiyasa ga shinan Allah ya bar miki na ki a gida suna shirin zama guzumaye" ya iddamaganan tare da miƙewa, tashi tayi da sauri ta yi kan shi tare da faɗin "ni ka ke faɗawa maganahaka?" Kafin ta ƙariso ya fice da sauri "da ka tsaya in same ka a wajen da ka sha mamaki, datayi
aure da kar tayi duk matsalar su ce ba nawa ba, kuma wallahi ka shirya na ka auren nanbadaɗewa ba, shi ma me goya maka bayan a wannan karon ba sauraranshi zanyi ba" ta idda
maganan zuciya a matuƙar ɓace.... Zaune suke a ƙasa grass carpet ɗin dake malale da sculpture garden, kallon Insu Nachmatayi
tare da faɗin "wallahi tunda da aka kafe jadawalin exams natsuwa na ya gudu" dariya Insutasaki
tare da faɗin "to meyasa?" "Ba zaki gane ba ne Insu" tace cike da damuwa, "meyasa ba zanganeba?" "Saboda ke gifted ce ko in ce ma talented ce ke, ki na da baiwarki tattare da ke irinwaƴannan abubuwan sam ba ganewa za ki yi ba" "to tunda haka ki ka ce na ja bakina na tsuke" tacetareda sakin murmushi me faɗi, "harara ta maka mata tare da fadin "yafi miki" "hi girls" Khalimdayaƙariso wajen yace tare da bin su da ido... Murmushi suka saki a tare idonsu akan shi, "what!" Yace ido waje, dariya suka saki tare dakaudakai, "no" yace tare da zama kusa da Insu, "ya yau ɗin?" Yace da kulawa, "Alhamdulillah" taceanatse, "an kafe muku jadawalin exams kuwa?" Yace da kulawa, "wallahi sun kafe" Nachmatacecike da damuwa, "kar ki damu, in sha Allah zaki haye, ke dama ba na da haufi akan ki" ya iddamaganan tare da kallon Insu, "ku na da matsala" tace tare da kauda kai "no gaskiya ne" yacetareda sakin murmushi, "barta kaji yaushe zan zo lesson?" Tace a natse, "ai se dai mu haɗu a Librarykin san dokan hana shiga hostel in dai ba na jinsinka ba ne ya fara aiki, jiya kusan karya Ahmadsecurity's suka yi da ƙyar ya sha" "kai amma sun burgeni, Allah ya sa su cigaba da hakan" Nachma tace cike da farin ciki ...
"Meyasa!" Yace da mamaki "haba suna shirin maida mana da hostel gidajen iyayen su, kowani
mara tunanin se ka ga ya shawo wanka wai ya zo taɗi" ta idda maganan cike da rashin jindaɗi, dariya Insu ta saki tare da faɗin "gaskiya sun samu sake" "matan ne suka ba su fuska, ammayanzu wane su" ...
Tace tare da amsa sallaman Labib da Hisham, "daga ina haka!" Insu tace tare da kallon su, "class"Hisham yace cike da gajiya tare da zama gefenta, "yakamata ku je ku fara cin abinci tukun, 3fayanzu" "no bar batun abincin nan gajiya ne kawai da fargaba, an kafe mana jadawali yau" Hishamyace tare da ɗaukan orange juice ɗin gabanta ya kafa kai, "wai kuma!" Nachma tace tare dakallon Labib, "wallahi duk mun tsure" yace tare da sakin dariya, "ai mu ma duk hakan take" tacetare da taya shi dariya, "ina ga ba'a mannawa ƴan Shari'a Law ba dan na ga da karsashinsu" Hisham yace tare da ajiye bottle ɗin juice ɗin hannun shi....
"Ance muku su ku ne kuma?" Insu tace tare da bin su da ido, miƙewa Khalimyayi tare da faɗin"akwai training dai, kar ku makara" "in sha Allah muna bayanka" Labib yace da kulawa, "alright
Insu gobe ne rantsarwa ko?" "Eh in sha Allah" tace tare da ɗago kai ta kalleshi, "Allah ya bashi
ikon amsan komai da nasara" "amen nagode" tace cike da jin daɗi.... Murmushi ta saki ya wuce ba tare da ya kuma cewa komai ba, "yawwa please turamun hotunannan" Hisham yace tare da miƙa mata wayan shi, jawo wayanta tayi ta cire password ta shigawhattapp kai tsaye ta miƙa mai tare da faɗin "send with yourself" "oh Allah" yace tare da amsa, "bari in tura ta xender" yace tare da yunƙurin fita, "banyi saving ɗin shi akan waya ba" tacehankalinta akan maganan da Labib yake da Nachma "kinji tsiyan na ki ko?" Yace tare da faralaliban sunan shi, karo ya ci da group ɗin Aminan juna, cike da mamaki ya ɗago kai tare dafaɗin"dama ki na cikin Aminan juna!" "Eh" tace idonta akan shi, ganin irin kallon da yake mata yasatafaɗin "Yasmin ce duk ta sa aka saka mu, ni wallahi ban san halin da suke ciki ba ma, na yi muteɗin su da daɗewa" jinjina kai yayi tare da faɗin "kin kyauta" "ba dai kaima kana ciki ba!" Tacedamamaki, "no bana ciki" yace a natse ya cigaba da neman sunan shi, "ya aka yi kasan groupɗin?" Tace idonta kafe akan shi, "yanzu labarin wannan group ɗin ɓoyayye ne?, Ina ne be zaga ba?Kota ina maganan shi ake" "oh" tace tare da basar da zancen....
Yana gama turawa ya miƙa mata tare da faɗin "zamu tafi training" "ni ma daga nan gida nayi" tace tare da yunƙurin miƙewa, "please kar ki manta da mana video's da photo's" yace cikedamagiya, "ko banyi ba zaku tadda a media" tace tare da sakin murmushi, "no na ki muke somudai"yace cike da roƙo, "shikenan, kun samu kun gama" tace tare da kallon Nachma dake cewa"kokefa, har kin fi jiya kyau" dariya ta saki tare da faɗin "dan ban sha fa mai ba ne" dariya duksukasaki tare da bin ta da ido, "oya mu tafi" tace tare da jan hannun Nachma, suna juyawa sukahangoJabiida da wasu ƴan mata suna tunkaro su, dariya Nachma ta saki tare da faɗin "ga mutuniyar ki
nan yau harda gayya" "na ganta share" tace tare da kame fuska, dan a kwanakin nan Jabiidatasako ta gaba....
"Yanzu shikenan Yaya ba zamu je rantsarwan ba!" Yasmin tace kaman za ta saki kuka, murmushi
Yaya ya saki tare da faɗin "in sha Allah bayan rantsarwan za muje mu taya shi murna" kwaɓa- kwaɓa tayi da fuska tare da faɗin "Insu ta saka rai ba zata ji daɗi ba idan ba mu je ba" "to jirgi maba ze tashi yau ba, sannan tun jiya aka saka dokan daina shige da fice a garin" Balarabe yacetareda hurga mata harara, shikenan ya zamu yi, Allah yasa hakan shine mafi alheri" tace cikedasanyi, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "in sha Allah daga baya zamu" "Allah ya yarda" tacetare da miƙewa, "ina Farisat?" "Tana garden" tace tare da juyowa ta kalleshi, "okay Sa'adatufa?"
"Tana shirin hadda" jinjina mata kai yayi cike da gamsuwa... Da sallama ya shiga gidan tare da ja ya tsaya saboda ganin ɗakin Sa'adatu a rufe, "ina taje?" Yacetare da kallon Shila dake zaune dirshan cikin ado kamar ko yaushe ƴan matan ta dake nemamata kuɗi zagaye da ita, "ta fice sabgan gabanta" tace tare da juya kai, da mamaki ya kalletakafin yace wani abu Ziza ta fito cikin wasu matsiyatan kaya masu jan hankali, murmushi tasakinmai tare da faɗin "ta fita tun ɗazu, idan wani abu ka ke buƙata ni ina nan" ta idda maganancikeda salon ɗaukan hankali tare da juya jiki, murmushi ya saki tare da kai hannu da zummanriƙota, "kull kar ka fara" Sa'adatu da ta shigo tace a zafafe, da sauri ya janye hannu tare da juyawaabirkice, wani banzan kallo ta jefa mai tare da faɗin "da me kake shirin yi?" Ta jefa mai tambayantare da takowa ciki, "da shine kuskuren da zaka aikata wanda ba zan taɓa yafe maka ba, banahaɗa hanya da shashashu wanda ko wani doki ke hawansu ye sukuwa, wuce muje" ta iddamaganan a zafafe cikin ba shi umurni, wuce wa sim-sim yayi kaman funafukin da aka kama...
Yana shigewa ta juyo tare da nuna Ziza cikin matuƙar ɓacin rai tace "ina hankalce da duk wani
takun ki, ki bi a hankali, ba ko wani banzan iri ke shukuwa a gonata ba se irin da na zaɓa nadarje, kar ki bari in waiwayo kan ki dan ba ɗan iskan da nake ɗagawa ƙafa akan shi" tana kai nantashige ta bar su sake da baki, juyawa ga Shila tayi jiki a mace, maka mata harara tayi tare dafaɗin"a barikin ki ka tsaya wata ke miki iyaka da wanda ta sanadiyyan shi ki ka shigota, to cigabadatsayuwa watarana tsayuwan ma gagagranki ze yi" ba abinda tace se wuce wa ɗakinta da tayi jiki
a mugun sanyaye....
"Sa'adatu menene haka?" Ya tari numfashinta daga shigowanta, ɗaga mai hannu tayi a zafafetare da faɗin "na kashe maganan ka barta ta mutu murus, kar ka ce zaka tadota dan na rantsedaAllah ba zaka ji da daɗi ba" tayi maganan cikin juya ido da karkaɗa kai da ƙafa, shiru yayi batareda yace komai ba, dan ya fahimci a sama take, "daga ina ki ke?" Yace cike da kulawa, zareveil
tayi ta rataya a inda take ratayewa da jaka tare da faɗin "ƙasan layi na je" "lafiya ko?" Yaceanatse, "waya na je amsa, wani banzan da wahala ta haifa ne ya na ce mun a kwanakin nanwallahi" tayi magana cike da takaicin shi, "oh a gaskiya ki ƙoƙarta ku rabu dan bana sonwataalaƙa ta ƙullu a tsakanin ku ko ta gaisuwa ce" murmushi ta saki tare da faɗin "zan kaɗashi
kwanan nan bari in gama wanke gara" ta idda maganan tare da sakin murmushi, "to ki yi ahankali kar gara ya wanke ki" shima yace tare da ɗaura murmushin dole a saman fuska, "waneshi dan wacce ta haife shi, ai na fi ƙarfin wanda ya bada gudummuwa dan samuwar shi barekuma shi" jinjina kai yayi tare da nufar gado a natse...
"Ka zo mun da wannan alluran kuwa?" Tace tare da bin bayan shi, "wallahi na sha'afa, kodayakeban je chemist ɗin ba ma sam, amma zan ƙoƙarta ko zuwa gobe in kawo miki" "dan Allahkaƙoƙarta, kwayoyin nan ba abinda suke iya mun yanzu, se na samu na ɗan soka nake jin dai-dai, sukuma ƴan iskan masu chemist ɗin nan ba mutumci ne da su ba, kana fara musu bayani sesuceba sa da shi" ta idda maganan cike da damuwa, bin ta yayi da ido tare da nazarin zantukanta, nanda nan wani idea ya faɗo mai a zuci, murmushi ya saki tare da faɗin "ai ba za su siyar miki ba, gwamnati ta hana siyarwa, ana kama shi da lefin soke lasisin shi za'ayi, mu ma a waje na
musamman muke samu" "to ka sanar min, dan bana son jiranka lokacin da nake buƙata,
murmushi ya saki tare da faɗin "zan kai ki har can" murmushi ta saki tare da faɗawa jikinshi....
"Ash" yace tare da yunƙurin ɗagota, matse shi tayi tare da faɗin "barni a ƙirjinka" murmurshi yasaki tare da gyara mata kwanciya tare da faɗin "a she Farisat za tayi aure?" Ɗago kai tayi damamaki ta kalle shi, "ina nufin ki na da labarin bikin?" Yace na shi idon akanta, tabe baki tayi
tare da faɗin "ba na da haɗi da shi bare in nemi jin labari ko da yake wannan mara aikinyintaturomin event's card ɗin" "wa ce?" Yace tare da sunkuyawa ya kalleta, "wannan me shirinshigaramin mana" ta kuma cewa hankali kwance, "ban gane ta fa" yace da ƙosawa, "menene
damuwarka akan sanin ma wacece!" Tace tare da miƙewa daga jikin shi, taɓe baki yayi taredafaɗin "ba komai" "Insu" tace tare da dira daga gadon, "Insu! Dama kina da numberta!" Yacedamugun mamaki, juyowa tayi ta watsa mai ido, kallo me cike da ka kama kan ka ta mai kafintajuya tare da faɗin "ba na da shi ita take da nawa" tana kai nan ta shige toilet... Murmushi ya saki tare da dira ya nufi inda ta ajiye jakan da ta shigo da shi, zagewa yayi dasauri
ya fiddo sabon wayan da aka ba ta a kwalin shi, ajiyewa yayi ya maida hannu a hanzarce cirowanda take amfani da shi yayi ya juya da sauri ya ɗakko wayanshi ganin ba ko wani passwordawayan ya sa shi tafiya whattapp kai tsaye, nan yayi ta bincikan account's yana shiga na Insuyakunna wayan shi ya kwafe lambar, yana shirin juyawa dan maida mata a inda ya ɗakko muryantaya sauka a kunnuwanshi, "in ka ce in baka ma zan baka menene na birkita mun kaya haka?" Dasauri ya juya tare da baza mata ido, maida kayayyakinta tayi ta tako a natse ta miƙa mai hannu, "bani tunda ka gama ɗauka" miƙa mata yayi a natse taɓe baki tayi tare da faɗin "kaje ka watsaruwa na rage maka" tayi magana tare da yaye towel ɗin dake ɗaure a jikinta ta jefar ta ɗauki rigawanda marabanshi da babu ba tazara ta zura, wucewa yayi jiki a sanyaye ba tare da ya bar wayanshi ba.... Murmushi ta ƙirƙiro ta ɗaura a saman fuskanta ganin sun kusa ƙarisawa inda su Jabiida sukajasuka tsaya dan jiran ƙarisowan su tare da baza musu ido, murmushi Jabiida ta saki tare dafaɗin"ba dai class zaku koma ba!" "No gida zan tafi" tace murmushin da ta dolanta ma kanta bebar
saman fuskanta ba, "wow se mu tafi tare dama wani barth day muka je na ce ma friend's ɗinamubiyo ku gaisa" tayi maganan cikin tsan-tsan fi'ili tare da nuna mata su, kallon su tayi fuskannanna yanda yake tare da faɗin "sannun ku dai" "yawwa" suka ce idon su akan ta, "muje ko Nachma,
sauri nake bye" tace tare da ɗaga musu hannu ta raɓe su ta wuce janye da hannun Nachma, danne baki Nachma tayi cikin danne dariya tace "kin fa guma" ɗalla ƙyalesu surutu za ta yi tazubawa wanda ba komai a ciki banda fariya" "ni wallahi dariya take mugun ban" tace taredasakin dariya me sauti.... Bin su kawai Jabiida tayi da ido cike da takaici dan ita fa ba dadin Mommy tace ta dinga
shishshige mata ba da ba ta yanda za'ayi ta zo tana ɓata lokacinta akan wannan yarinyar datakeda ji da kai, in tana fariya ita ɗiyar president ne kafin Babanta ya ci na ta Baban ne ya ci, itahar
yanzu ma uban ta be hau karagan mulkin ba tukun, ita ko na ta na kai daramdam... A natse ta shiga parlorn baki ɗauke da sallama, bin parlorn tayi da ido cike da mamaki, jama'anecike maƙil kaman za su fasa parlorn, murmushi Hajiya da ta hangota ta saki tare da tashi tayoinda take, murmushi ta saki ganin Hajiya na tunkarota tare da ƙarisawa da sauri tare da faɗin" Hajiya yau baƙi ne damu?" "To ga sunan dai duk ƴan taya murna ne suka iso" dariya ta saki tareda faɗin "gida yayi albarka ma sha Allah" murmushi ta saki tare da fadin "jeki kimtsa ki sakkoamiki lalli da kitso gasu can ana ta zana musu" tayi maganan cike da kulawa, murmushi ta saki
cike da yabawa da karamcinta tare da faɗin "zanyi na bikin Anty Farisat ne" "au haka ne fa, kinfini gaskiya biki na ƙaratowa, to bari kar ki yi yanzu se zaki tafi se a kirata ta zo ta miki" "nagodesosai Hajiya" tace tare da wucewa wajen hoton su da ake shirin cirewa da sauri...
"Ya da haka bayin Allah? Duk da ma ba kusan waye shi ba" tace tare da bin su da ido, "megidaneyace a cire za'a kai can white house ne" ɗaya a ciki yace tare da kallon ta, "oh to ku bi a hankali" tace tare da sakin murmushi ta juya da nufin wuce wa sama, "Insu" Abubakar yace tare dayafutowa, da sauri ta wuce inda yake tare da faɗin "dama kuna ciki ake fa hayaniya haka?" Tayi
maganan tare da ƙarisawa kusa da shi, murmushi ya saki tare da faɗin "to ya zamu yi? Dalili tasaka hakan, ga Antyn ki" ya idda maganan tare da nuna mata matan dake zaune kusa da shi, murmushi ta saki cike da girmamawa tare da faɗin "barka da zuwa Anty" murmushi ta saki tareda faɗin "wannan ita ce Insun?" "Ita ce gata nan ƴar firit rashin jinta kuma ƙato" yace taredakallon Insu, dariya ta saki me faɗi tare da faɗin "wato zuwa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 109