ƙaddarori, kana ɗayadaga cikin ƙaddarorin" Insiyyah tace a natse idonta a rufe, jinjina kai Yaya yayi tare da faɗin"tamutu tana jin akwai wani gurbi da bata ma adalci ba, ta tafi da fatan son nemawa wannangurbinadalci, duk da ya haramta mata neman shi amma ba ta fasa ba, a ko wani yanayi da hali datakeciki yana nan daram a zuciyata, se bayan sanin labarin da nayi na fahimci gaskiyan Momy datacemata "bata san wanda take so da wanda take ƙi ba" fahimtar zuciyar matarka na ga waninkababu sauƙi, dan ba kowa ze iya fahimtar hakan ba, se dai na jure a tsayin rayuwar da mukayi namata adalci dan duk da fahimtar da tayi ba sona take ba, ba ta gaza mun adalci ba, shiyasani mana kwatanta mata adalci ko zata samu natsuwa" ya idda maganan a hankali, "sune suka zota'aziyya ɗazu!" Sadam yace tare da goge hawaye, jinjina kai Yaya yayi tare da kallon shi, "yanacikin wanda suka zo?" Nafisat tace a sanyaye, nan ma jinjina musu kai yayi, "Sahabee SadamƁadamayya, SSB?" Insiyyah tace tare da kafe shi da ido, murmushi ya saki tare da faɗin"eh" zareido Farisat tayi tare da faɗin "dama shine ya zo!" "Ji dan Allah" Sadam yace tare da ɗaure fuska, "wallahi ban kalleshi da kyau ba ne" tace a natse, "shi ne ya haramta mata neman shi ammabeharamtawa kan shi nema da jin lafiyarta ba" Insu tace tare da gyara zama, da mamaki Yayayakalleta tare da faɗin "a ina ki ka ji wannan!" "Ibrahim shine kunnuwan shi a gidan nan" taceadake, "Ibrahim!" Su Farisat suka ce a razane, murmurshi Yaya ya saki tare da faɗin "shine" "habano wonder shiyasa sam be kama da driver ba" Sadam yace tare da kallon Yaya, "Ibrahimyashigocikin mu ne matsayin driver da Alhaji Sunusi ya ba ta kyauta, se dai kasantuwar mu na lauyoyi
waƴanda ba sa abu kai tsaye se da zuzzurfan tunani yasa na fara karantar shi a natse sabodaabubuwa da yake yi kamar mara gaskiya, ni na fara gano waye shi na sameta na faɗa mata, nanta tashi hankalinta akan a sallame shi, duk da na san sanin waye shi ba ƙaramin farin ciki yahaddasa mata ba, amma saboda kar ta shiga haƙƙina ta zaɓi a sallame shi, ni na nuna matabaza
mu sallame shi ba ze cigaba da zama damu, saboda na san ko yaya ne zata samu kwanciyar
hankali idan wanda yasan shi yake magana da shi kullum ya kasance a kusa da ita, a wannanlokacin muka fahimci waya ba ta kyautan gida, a she Sahabee ne ya bata Alhaji Sunusi miƙamata kawai yayi"....
"Lallai zuciyan Momy me kyau ne duk da abin nan da ya faru amma ta zo mana ta'aziyya" Yasmintace jiki a sanyaye "meyasa ka zaɓi wannan lokacin dan ba mu wannan labarin?" Insu taceidontaƙyam ana Yaya, ganin yanda duk suka zuba mai ido ya sashi matse hannun Insu dake cikinnashi
tare da faɗin "dan in bayyana muku wani abu da ba ku san da shi ba" gyara zama suka yi taredazube mai ido.....
"A dalcin da take son ma wannan gurbin da ta tafi da burin son yi mai adalci ku take so kuyi mai, so take ɗaya daga cikin ku taja ragamar yi mai" yayi maganan idon shi na yawo a samanfuskokinsu, "ba mu gane ba Yaya" Sadam yace idon shi akan shi, "yau na ɗaurawa ɗaya daga cikinkuauresaboda cika wasiyyan da Antyn ku ta bani" yace cike da dakiya "aureee!" Farisat tace a rikice, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "eh aure, mahaifiyarku ce ta nemi wannan alfarman" jinjinamishi kai suka yi cike da gamsuwa, "wacce aka ɗaurawa auren!" Farisat tace cike da fargaba, "Insiyyah" yace tare da kallon ta, lumshe ido tayi hawayen da suka cika idanunta suka gangaro, matse hannun yayi a natse, girgiza kai Farisat tayi tare da faɗin "da shi Yaya! Insu ba ta dajarumtar zuciyan fuskantar lamari me nauyi haka, kar ka manta ba lafiyar zuciyar ke garetaba" murmushi ya saki tare sa faɗin "tafi kowa sanin wacece ita amma ta yarda ta ba da wasiyyaakanita za'a ba shi, tayi tunani akan ki se taga a lokacin kin maida duk wani natsuwanki ga Sudais, tahaƙura dan bata so labari ya mai-maita kan shi, ta koma kan Yasmin se dai rashin yawanhayaniyanta yasa ta fahimtar ba zata iya ba, ta sauke idonta akan Insu saboda fahimtar datayi
zata iya" jinjina mai kai suka yi cike da gamsuwa, "shikenan yanzu Yaya raba mu da Anty Insuzaka yi" Nafisat tace cike da damuwa, girgiza mata kai yayi tare da faɗin "kuna tare ba inda za'akaita yanzu, se ta gama makaranta" murmushi ta saki tare da share hawaye....
"Zaki iya Insu!" Sadam yace tare da duƙawa a gabanta, jin ba ta ce komai ba ya sa Farisat faɗin"inba zaki iya ba se dayarmu ta maye gurbin ki" motsa baki tayi a hankali tare da faɗin "zanyi danAnty, zan sa shi fahimtar Anty ba me san kanta ba ne, da kan shi ze buɗe baki ya faɗi adalcinAnty da ƙarfi, duk duniya se sun ji sun sheda" ta idda maganan da ƙarfi, jinjina mata kai sukayi
cike da gamsuwa da zata iyan, "Allah sarki Anty a she shiyasa take ta nunashsheni ja bayadaYaya Sudais amma na kasa ganewa" Farisat tace tare da goge hawaye, "tana gudun ki faɗadanashina kaman yanda tayi ta faman dako har ta koma ga ubangijinta, tana yawan ce mun, yaranta ba za su auri waƴanda suke so ba se waƴanda ke san su saboda tasan watarana zasusosu" murmushi suka saki tare da kallon yanda yake maganan cike da kewa, zaro waya Farisat tayi
da sauri ta danna number ta kara a kunni.....
Tura ƙofar main parlorn gidan yayi ya shiga sallama a ciki-ciki, zuba mishi ido matashiyar
dattijuwan dake zaune saman one sitter dake parlorn tayi cike da tausayawa, zama yayi aƙasakusa da ƙafafunta tare da kwantar da kan shi a gwiwoyin ƙafafunta, shafa kan shi tayi cikedakulawa tare da faɗin "haƙuri shi zaku yi Salman, kuka da damuwa ba ze amfane ku da komai ba, ku dai cigaba da mata addu'a" sakin hawayen da suka cika mai ido yayi tare da ɗago kai a hankali
ya fara sharewa" "Mami ina tausayin yaran nan, da ita kaɗai suka saba, ita ce ƙawa ita ce
aminiyarsu, ita ce koman su, ba wata me shaƙiƙiyar ƙawa a waje, yau ba ta ba za su ƙara ganintaba, taya za su iya jurewa, haka na fito na barsu suna kuka, ba wacce take iya saka komai acikinta, duk sun firgice sun ɗimauce" ya idda maganan murya na rawa hawaye na zubowa, goge natahawayen Mami tayi tare da faɗin "suna da Allah kuma suna da mu, zamu yi iya bakin ƙoƙarinmudan ɗebe musu kewa, mahaifiyarsu ba ta yada na mu ba duk da muna raye, taya zamu yadanatabayan ba ta" jinjina kai yayi tare da kallon Mami, fara share mai hawaye tayi tare da faɗin"tashi
ka zubo abinci ka ci, ka sakawa ranka dangana, Allah ya gafarta mata ya bamu juriyan rashinta"
"amen" ƴan matan dake tsaye a gefe suka ce tare da share na su hawayen, "Rahma je ki zubomai
abincin" Mamu tace tare da kallon wacce ta kira da sunan, juyawa wacce aka kira Rahma tayi dasauri ta nufi dining area, miƙawa ɗaya daga cikin biyun da suka ƙariso cikin parlor wayanshi yayi
tare da faɗin "sa mun a caji" ba musu ta amsa ta wuce da sauri, kallon shi wacce ta rage tayi tareda faɗin "brother Insu tayi magana kuwa!" Jinjina mata kai yayi ba tare da yace komai ba....
"Allah sarki Insu" tace cike da tausayawa, sallama wani farin dattijo yayi ya shigo cike da kamala, zama yayi saman two sitter tare da faɗin "yaushe ka shigo?" "Yanzu" yace a hankali, "bangankaamasjid ba da la'asar ban ganka da magrib ba" "eh ba ma anguwan ne, naje siyowa Insu maganinda Dr ya turo a siya mata ne" jinjina kai yayi tare da faɗin "ya jikin na ta?" "Alhamdulillahdasauƙi" "Allah ya ƙara mata lafiya, ka dinga ba su baki duk da abu ne mawuyaci su iya jurewaayanzu amma za su fahimta a hankali" jinjina mai kai yayi cike da gamsuwa, ajiye plate ɗindataciko da abinci Rahma tayi tare da faɗin "ka cinye duka brother" tayi maganan fuska yalwacedamurmushi, hararanta yayi tare da faɗin "ga jaki ko, ku zo mu ci" da sauri sauran suka ta sosukazazzauna suka fara cin abincin a natse, bin su da ido Mami da Abba suka yi cike da farin ciki....
Tun daga airport suka rarrabu, Alhaji Jamilu yayi gidan shi, Alhaji kamil ma yayi gidan shi gogama yayi na shi gidan shi da Alhaji Munnir, matan kuma suka wuce gidan Hajiya, kallon shi Alhaji
Munnir yayi jiki a mace tare da faɗin "abinda ya faru a wajen nan" ɗaga mai hannu yayi taredafaɗin "yakamata ka je gida dare yayi" murmushi ya saki ganin alaman baya buƙatan ayi maganan, miƙewa yayi ya nufi wani ƙofa dake parlorn, turawa yayi ya shige a natse, wani ƙawataccenpharmacy ne me matuƙar burgewa, ɗaukan mai maganin da yake amfani da shi yayi ya fito, fridge ya nufa ya ɗakko ruwa mara sanyi ya nufe shi kai tsaye, ɓallamai maganin yayi ya miƙamai ba musu ya amsa, tsiyaya mai ruwan yayi ya tura mai gaban shi, ɗauka yayi a natse yashamaganin, miƙewa Alhaji Munnir yayi tare da faɗin "Jabir da Abubukar gobe in Allah ya kai muzasu sakko" jinjina mai kai yayi ba tare da yace komai ba, har ya kai ƙofa ya jiyo kamilalliyar muryanshi na faɗin "ka kira Ibrahim kace mai ya taso ranar da ya ga ya dace" jinjina kai yayi ya fice, yanatabbatar da fitan shi ya ɗago kai ya bazawa ƙofan jajayen idanun shi....
Be yarda ba a lokacin da Ibrahim ya sanar dashi ta mutum, se da ya je ya tabbatarwa kanshi,
shikenan Insiyyar shi ta tafi inda su Daddy suka tafi, yanda be ƙara ganin su ba tun lokacindaakasanar mai da mutuwar su haka ita ma ba ze ƙara ji da ganinta ba, shi yakamata a ce ya tafi baitaba, meyasa mutuwa ta kasa kawo mai ziyara ne? Meyasa take ta ɗaukan masu lafiya takebarinshi shida ba abinda yayi mishi saura, lumshe ido yayi tare da sakin hawayen da ya kasa dannewa, wasu shuɗaɗɗun batutuwa ne ke mai yawo a ƙwaƙwalwa, buɗe ido yayi da sauri tare da zubesuakan dattijuwar matar dake duƙe a gaban shi tana mai barka da dawowa, jinjina mata kai yayi
tare da danne haƙwaran saman bakin shi a leɓen shi na ƙasa, "an gama shirya daining" tacealadabce, miƙewa yayi a natse tare da faɗin "ku kwashe yau ba zanyi dinner ba" yana kai nanyanufi bedroom ɗin shi ya shige, sauke numfashi tayi da ƙarfi tare da faɗin "ko me yasa shi kukakuma! Allah masani" tana kai nan ta miƙe ta fice daga side ɗin, kai tsaye side ɗinsu na masuaiki
ta nufa, gaida me wanke-wanke da ke kame kan ƙaramar yarinyar ta tayi tare da shigewaɗakinta, wayanta dake caji ta ɗauka ta danna kira ta zauna tare da jiran wanda take kira yaɗaga.....
Kallon Hajiya dake zaune jiki a sanyaye A'isha tayi tare da faɗin "lallai yau na ƙara tabbatar daduniya ba'a bakin komai take ba, Insiyya ta rasu shikenan" murmushi Hajiya ta saki tare dafaɗin"rayuwar kenan, in lokaci ya zo ka shirya baka shirya ba se ka tafi, shiyasa nake ta mai-maitamuku kalaman ku yi biyayya ga mazajenku ku zauna da maƙofta lafiya, maƙofta sune mutanenfarko dw za su fara ba da shedan waye ku, kuma Manzon tsira yace "wajabat" miji kuwa yardanshi da amincewan shi shine tsanin da za ku shiga aljanna, yau kunji da kunnuwan ku yandamaƙofta ke zancen kirki da mutumcinta, kunji yanda mijinta ke yabon halayenta" Hajiya tacecikeda alhinin da ya kasa barinta, "Allah yasa mu dace" Yasmin tace a sanyaye, "wa ze ce Insiyyazatariga SSB rasuwa" Kausar tace tare da kallon Lubabatu, "ai komai na Allah ne, me lafiya ya mutuya bar majinyaci" Lubabatu tace cike da rashin ɗaukan batun da mahimmaci, "gashi kuwamungani" Kausar tace tare da sauke numfashi da ƙarfi....
"Hajiya wai me mijin nata da ya buƙaci ganun ku yace?" A'isha tace tare da kallon Hajiya, "menene matsalanki da son jin abinda muka tattauna?" Hajiya tace tare da kafeta da ido, "a'abakomai" tace tare da sakin murmushi, "ke ma dai Anty A'isha da neman zance ki ke, me kozece
banda ya nema wa matarshi yafiya" Lubabatu tace tare da kauda kai, "wallahi ba ya da kunyakuwa in dai haka ne" Yasmin tace rai ɓace, "ke me kunyar kenan, shiyasa zaki gane haka, shi daba shine da shi ba ai ba ze fahimci abun kunya ya aikata ba" Lubabatu tace cike da takaicinYaya, "kunga yanda ya dinga yi kuwa? Kunya duk ya dabaibaye shi, ba ku ga yanda ya kasa sakewaba, ko kallon inda SSB da Yaya Munnir ke zaune ba ya iya wa" Kausar tace tare da kallon su, "yanama da sa'a tunda ya samu ganin shi, na farko na ƙarshe ne ai" A'isha tace tare da kallonHajiyadake cewa "ku tashi ku koma gidajen ku" tana kai nan ta miƙe, "Hajiya ana kiran wayanki" yarinyar Kausar dake tare da ita tace tare da miƙa mata wayan, ganin me kira yasata shigewabedroom ɗinta da sauri.....
"Ni banga wannan ɗan shaye-shayen da Farisat ke so ya zo musu gaisuwa ba" Rahma tacetareda kallon na kusa da ita, "be zo ba kam" budurwar tace tare da kauda kai, "me ruwanku dazuwanshi? Kar kuma in ƙarajin kin faɗi wannan kalman Rahma" Mami tace rai ɓace, "Mami wallahi
Farisat ba ta san ma wanda ya dace da ita ba, yaron nan da gaske yana shaye-shaye, danranar damuka je gaida Momyn Hajar mun ganshi a anguwan shi da gugun ƴan shaye-shayen" ta kusadaSalman tace tare da kallon Mami, "Allah ya shirya" Abba dake bin su da ido yace cike da rashinjindaɗi, "ni banga abinda ma ta gani a tare da shi ba ta na ce akan son shi" murmushi Salmanyasaki
tare da faɗin "kyau mana" "wallahi ka fishi kyau brother, ina ma ze haɗa kan shi da kai" waccebata ce komai ba tace cike da takaici, yanda ta yi maganan cike da takaici ya sa shi sakinmurmushi, gyara zama Abba yayi tare da faɗin "ke ki ka ga haka auta, ita da ke so ai ba zatagani
ba, yafi mata duk mazajen duniya kyawu a idanunta" "tab Abba wannan ɗin!" Tace da mamaki, "eh mana" Salman yace cike da danne damuwa, "Safinat tashi ki ɗakko mun wayana" yacetareda gyara zama, tashi tayi da sauri saboda jin ringin ɗin ya kusa katsewa, "tsaya kar ki cirowayene?" Yace da ɗan ƙarfi, "my Kushi"(farin ciki na) dace da ƙarfi, da mamaki ya mata alamuntakawo, tana miƙa mai kiran na katsewa, bin wayan yayi da ido mamaki na bayyana kanshi asamanfuskan shi, duk tsayin lokacin da ya ɗauka yana dakon sonta ko sau ɗaya bata taɓa mistakeɗinkiran shi ba, se dai ma shi ya kira ta ƙi ɗagawa, "waye!" Mami da ta lura da yanayin da ya faɗalokaci guda tace tare da kallon shi, yana niyyan bata amsa wani kiran ya shigo, ganin ita neyasashi ɗagawa ya kara a kunni zuciya na tsintsinkewa....
Sauke ajiyan zuciya Farisat tayi tare da goge hawaye da ya zubo mata, "Yaya Salman" tacea
hankali, "na'am Farisat lafiya kuwa!" Yace a ɗarare, zuba mai ido su Mami suka yi saboda sunanda ya kira, ta ɓangaren Farisat kuwa tunda ta danna kira ta kara a kunni su Sadamsuka zubamata ido, "lafiya, da gaske ne kana sona?" Tace murya na rawa, jinjina kai yayi tare da faɗin"ehda gaske ne" goge hawayen da ya zubo mata tayi tare da faɗin "to ka turo iyayenka su tambayanmaka aurena" "um!" Yace a razane tare da fidda idanu gaba ɗaya waje, sauke wayan tayi takatsekiran tare da fashewa da kuka, jin ta katse kiran yasa shi kallon Mami, ganin irin kallon datakebin shi da shi ya sa shi miƙewa ya faɗa jikinta ya saki kuka me ƙarfi, a ruɗe ta ɗagoshi taredatambayan shi abinda ya faru, Abba ma a rikice ya yo inda yake dan jin abinda ya faru, suRahmakuwa gaba ɗaya sun tsorata banda mai-maita salati ba abinda suke, duk a zaton su Insucetamutu, "ka faɗa mana meke faruwa Salman kar ka kashe mu da sauran kwanan mu" Abba yacearikice, "Farisat" yace tare da ɗago kai, "meyafaru da ita!" Mami tace a razane, "zata aure ni" yacetare da sakin hawaye, zare ido gaba ɗayan su suka yi tare da baza mai su, "da gaske!" Safinat tacetare da riƙo hannun shi, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "haka ta faɗa min yanzu, tace inturasuAbba su tambayan mun aurenta, zata aure ni" ya idda maganan tare da share hawaye, murmushi
Abba ya saki tare da faɗin "shine ka ke kuka kamar ƙaramin yaro? Godewa mahaliccin ka zakayi
ai" "Alhamdulillah" yace tare da share hawaye, murmushi Mami ta saki tare da faɗin "to ɗagani, wani gabjeje da kai ka danne tsohuwa" dariya su Rahma suka kwashe da shi, "Hasina amshi
wannan gobe da sassafe ki wa yara sadaka" yace tare da zura hannu a aljihu, kuɗin ciki gabaɗayaya fiddo ya miƙa mata, tashi yayi idon shi akan waya ya nufi bedroom ɗin shi, yana tura ƙofanyakara waya a kunni..... Murmushi Mami ta saki zuciya ƙal ta kalli Abba tare da faɗin "Allah ya tabbatar da wannanal'amari, na san Salman ze zame mata mijin marainiya" jinjina kai Abba yayi tare da faɗin"inshaAllah zan tuntuɓi Alhaji Abdussamad bayan sadakan bakwai, yanzu be kamata na mai magananba" haka ne" Mami tace cike da farin ciki, su Rahma kuwa bakuna sun kasa rufuwa,,,, ta cikinɗaki
kuwa Salman yana shiga ya faɗa a saman gadon shi dake lailaye tare da faɗin "Faruk my Kushi taamince da ni" ya idda maganan murya na rawa.... Murmushi Yaya ya saki tare da miƙa wa Insu maganin da ya ɓallo mata, amsa tayi a natse, ruwa
Nafisat tayi saurin bata, tana sha ya amshi kofin ya ajiye tare da faɗin "anan zamu kwana?" Jinjina mai kai Sadam yayi tare da kallon shi, miƙewa yayi a natse ya isa kusa da Farisat kamotayayi cike da kulawa tare da faɗin "wannan ba hukuncin da yakamata ki yanke da gaggawabane, kina buƙatan lokacin nazari kafin ki yanke hukunci" girgiza kai tayi tare da faɗin "Yaya shi neburin Anty, a ko wani lokaci tana ƙwaɗaitamin shi a matsayin miji na gari, duk da bata fitokai
tsaye tace in so shi ba, na haƙura da duk wani ƙauna da nake ma Yaya Sudais dan banga amfaninshi ba, duk mutumin da ya kasa zuwa maka ta'aziyya akan rashin mahaifiyarka da ka yi becan- canci ya cigaba da rayuwa a tunaninka ba bare a zuciya" jinjina mata kai Yaya yayi tare dafaɗin"Allah yasa ya zame miki yanda ta hasaso miki" yana kai nan ya umurci da su tashi su je sukwanta a ciki.....
"Anty Lailah ba na jin wannan auren ze haifar da ɗa me ido, kinga su Kausar ba sa ƙaunar koganin mu, bare su mana magana, kusan shekara biyar kenan da na haɗu da Yasmin a facebookbamaganar da ban mata ba amma ko sannu ta kasa ce mun, ya ki ke ganin ɗiyar Anty zata shigaahalin nan su amsheta da mutumci" Khadijatu tace cike da fargaba, "ni ma nayi wannantunaninse dai ƙaddara ta rigayi fata mu bi abin da addu'a" Lailah tace cike da damuwa, "dama Farisat koYasmin ne, Insu ba ta da ƙoshin lafiyar fuskantar babban lamari haka" Salwa tace cike da
damuwa, "muyi ta addu'a, in alheri ne Allah ya tabbatar in ba alheri Allah ya watsa lamarintunkafin tafiya yayi nisa" Lailah tace tare da kallon su" "amen" suka ce a sanyaye.....
"Ina jinki Maude" Hajiya tace tare da zama a saman sofa, shirun mintina tayi ta gama saurarantakafin tace "okay na fahimta" tana kai nan ta sauke wayan, numfashi me ɗumi ta fesar taredatuna kalaman Yaya, "Insiyya me lefi ce a gare ku, ta aikata muku lefin da har ta koma ga
mahaliccinta ba ta daina nadama da roƙan yafiyar ku ba duk da baku san tana yi ba" "munyafemata har abada, ba mu riƙe ta ba" Hajiya tace tare da goge hawaye, jinjina kai Yaya yayi taredafaɗin "akwai wani saƙo da ta ba da na baki" yace tare da miƙewa ya shige bedroombe jimabayafito hannu riƙe da madai-daicin takarda, miƙawa Alhaji Jamilu dake ta bin shi da ido yayi taredafaɗin "dan Allah ku ma saƙonta adalci duk da ba ta kasance adala a gare ku ba" ba wanda yacemishi komai a cikin su, se gyara zama da Alhaji Jamilu yayi ya buɗe takardan, "Assalamualaikum
zuwa gare ki Momy, Insiyya ce ɗiyarki, wataƙila saƙona ya riske ki ko ki riske shi, ban sanwandaze faru ba a ciki, na yi nadaman duk abinda nayi, ina neman yafiyan ku gaba ɗaya, tabbas bankyauta ba na kasance butulu me san kanta da yawa, na haddasa muku ɓacin rai da baƙinciki
wanda yayi sanadiyyan su Daddy, da wannan raɗaɗi nake rayuwa kullum na san kuma da shi zanmutu, na yanke hukuncin rubuta miki wannan saƙon ne bayan na fahimci gaskiyan da na rufeidolokacin da ku ke faɗa min, adalcin da na kasa ma Yaya Sahabee nake son yi mai, se dai lokaci yaƙure min, likita ya sanar mun da cutar kansan jini da nake ɗauke da shi, a yanda nake jina nasangab nake da ajalina, dan Allah ki temaka mun ɗaya daga cikin jinina ta auri Yaya Sahabeebadinhalina ba, ba din lefuka na ba, ina rubuta miki saƙon nan ne zuciya cike da rauni, daga ɗiyarki
Insiyya" sauke takardan Alhaji Jamilu yayi tare da sauke ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya, "wannanshinedalilin da yasa na nemi magana da ku" Yaya yace tare da goge hawayen da suka jiƙa mai fuskasharkaf, sauke numfashi Hajiya tayi tare da miƙewa ta nufi wedrobe hijab ta zaro ta zura, isaindatake ajiye abubuwa masu mahimmanci tayi ta zaro wani farin takarda ta saka a ɗaya dagacikinjakunkunan dake jere ta fice daga bedroom ɗin da sauri.....
Comment fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Six
Kwance suke ko waccen su tayi nisa wajen tunani, ringing ɗin da wayan Yasmin ta ɗauka yasasudawowa daga hayyacin su, ɗago wayan tayi a natse ganin me kira ya sata ɗagawa ta saka ahandsfree ta kara a kunni, "ƙanwata" muryan Annur ya bayyana ras, "na'am" tace cikin sanyindaya zame musu jiki, "ba dai na tashe ki a barci ba!" Yace muryan shi na nuna alamun kamanyarazana, girgiza kai tayi tare da faɗin "no ban fara ba tukun" "to yanzu na samu sasauci, ya sister'sda brothers?" "Suna lafiya" tace a hankali, "to ma sha Allah ina gaishesu ɗaya bayan ɗaya, sannan please ku cire damuwa, an san abun damuwa ya same ku amma damuwar kan haifar dawata damuwar ne, dan Allah ku cigaba da mata addu'a kunji" jinjina kai tayi tare da faɗin"nagode" "no babu godiya a tsakanin mu, ni fa Yayanki ne, kome na miki kaina na ma wa" murmushi ta saki me ƙaramin sauti tare da faɗin "haka ne" "yawwa to a je a kwanta, se dasafe"
jinjina kai tayi tare da faɗin "se da safe" tana idda faɗi ta zaro wayan tare da ajiyewa a gefenta....
Kallonta Farisat tayi tare da faɗin "yana da mutumci ko?" Jinjina kai tayi tare da faɗin "sosai" "aina ku ka haɗu?" "Wani group ne BC (Bertuwa Celebrities) daga nan ne ya nemi iznina ya sakani
a Aminan juna" jinjina mata kai tayi tare da faɗin "yayi kyau" jawo wayan tayi ta buɗe datanansaƙonnin suka fara shigowa, duddubawa ta fara a natse, ganin saƙonnin group ɗin Aminanjunayayi yawa ya sata shiga ta fara bibiya a natse, sanarwa taga p,r,o sunyi na rasuwan Anty har dahoton ta da yayi ta yawo a media lokacin da ta ci nasara a shari'ar murɗiyan da wa su Kawunnanmarayu suka so yin musu da gadon su, sanarwa suka yi me jan hankali tare da umurtandukwani
member da ya kira ta ya mata ta'aziyya, sannan ranar addu'an bakwai za su zo yin mata ta'aziyyahar gida, share hawaye tayi tare da miƙa ma Farisat wayan, amsa tayi ta karanta saƙon datagani, nan ta fara bibiyan sauran charting ɗin, ganin yanda suke ta addu'a ya sata faɗin "a sakani aciki"jinjina mata kai tayi tare da juyawa ga Insu dake kwance lumshe da ido kamar me barci, "Nafisatkin yi barci ne?" Tace
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 109