Farisat tace hawaye na bi yo kuncinta....
"Murmushi Jabir ya saki tare da faɗin "kar ku damu, Allah ya fargar damu da wuri, zan iya cewarashin nauyin bakin Insu ne ya ba mu daman bincike, in sha Allah ze yi free" jinjina mai kai sukayi
cike da tsan-tsan farin ciki, "ku muje mu kwanta" Yasmin tace tare da miƙewa ta farasharehawayenta, "Uncle mun gode" tace tare da sallaman su ta wuce jiki a mugun sanyaye danzuciyarta ya karye ga fitowan shi, bin ta da ido suka yi har ta ɓacewa ganin shi, sauke numfashi
me ɗumi Farisat tayi tare da kallon SSB cike da ƙarfafa kai tace "Uncle mun gode, Allahyabi yaka da mafificin sakamako, Allah ya tsare maka zuri'a ya kare maka su, yanda ka faranta manaAllah ya faranta maka, Yaya Samir mutum ne me matuƙar mutumci da daraja a gare mu" tanakai
nan ta miƙe a natse ta sallamesu ta ma su Rahma maganan suka dafa wa Yasmin baya..
Sauke numfashi yayi cike da jin daɗi addu'o'in na ta tare da kallon Insu da ta lumshe ido, kamohannunta yayi ya matse cike da ba ra ƙarfin gwiwa, ɗago na ta hannun tayi ta ɗaura a samannashi tare da jingina da kafaɗan shi, bin ta yayi da ido fuska cike da murmushi, "waye shi!" Alhaji
Munnir yace da mamaki, gyara zama Jabir yayi ya koro musu bayani, "Allahu Akbar lallai wannanyaro ya ga jarabawa" Hajiya tace cike da tausayawa, "gaskiya ne" suka ce jikkuna a mace....
Tunda ya fita daga side ɗin masjid ya wuce kai tsaye be fito ba se da ya gabatar da isha'i cikinjam'i, fitowa yayi a natse shi da Sa'eed da ya iske shi a can, gida suka wuto kai tsaye, side ɗinIƙilima suka wuce a natse, da sallama suka shiga parlorn dake ta tashin ƙamshi amarya, wucewaɗakin shi Sa'eed yayi kai tsaye ya rufo ƙofa, da ido ya bi shi, sauke numfashi yayi a hankali yataka a natse ya nufi bedroom ɗinta, yana shiga ya tadda ta zaune saman sallaya tana tasbihi, wuce wa gefen da sofa yake yayi ya zauna a natse, tana idar da tasbihin ta juyo a natse kai aƙasatare da faɗin "barka da shigowa yallaɓai" tayi maganan cike da natsuwa da girmamawa mehaɗeda ladabi da biyayya, jinjina mata kai yayi idon shi ƙyam akanta tare da faɗin "yawwa zaunadakyau, ina da magana me matuƙar mahimmaci da ke, gyara zama tayi kai a ƙasa ba tare dataɗago ba, gyara zama shima yayi tare da fuskantar ta....
"Ba se na zauna ina miki dalla-dalla ba, zan miki su a dunƙule ina fata ki fahimceni da kyau, "akwai amanan da na roƙa aka ba ni, dalilin da yasa na nemi wacce zata tayani riƙe amanankenan, an sanar da ni ilimi da tarbiyyanki da tausayi da sanin yakamatan ki, wannan su sukasani
jin zaki iya har na nemi da a nema min aurenki" yana kai nan ya tsahirta tare da bin ta da ido, jinjina kai tayi jin ya tsaya cike da fahimta, yaron ƴar uwata Insiyyat ce ba zaki rasa sanintaba, duk da ba da sunan wata ƙila ki ka santa ba, sunan shi Sa'eed amma Abba nake son a dingakiranshi" zare ido tayi tare da tuna kalaman su Insu ɗazu, "Alhamdulillah!" Tace a ƙasan zuciya cikedafarin cikin jin ɗaya daga cikin ƴaƴan Anty zata riƙe a hannunta, ta jima tana addu'an Allahyakawo wani dama da za ta sakawa Anty da iyalanta, duk da ta san duk abinda za ta musubazekai
kwatan wanda suka musu ba....
"Kin yi shiru" yace a natse, gyara zama tayi a natse tare da faɗin "in sha Allah, Allah ya ba muhaƙurin zama da juna" tayi maganan a natse cikin sanyin muryanta "amin" yace cike da jindaɗi, shiru suka yi ba wanda ya kuma cewa komai, katse shirun na su yayi da faɗin "sunana Jamil kefa?" Zare ido tayi cike da mamakin ko sunanta ma be sani ba kenan, "Iƙilima" tace a hankali, "toIƙilima in ba damuwa zamu iya samun dinner?" Yayi maganan cike da roƙo, murmushi ta saki
tare da faɗin "to" ta miƙe ta fice a natse, bin ta yayi da ido cike da jin gamsuwan zama da ita....
Haɗiye wasu kauraran yawun tsoro suka yi tare da bin su da ido, kallon sakannin Sarari yamusuya wuce ya zauna a saman kujera one seater tare da faɗin "waya aka wannan can?" "I! I! Itane" ɗaya daga cikin guard ɗin yace jiki na ɓari, kallon inda take zaune rungume da ƙafan Abdull yayi
tare da fadin "kar mu ɓata lokaci zamu je farauta" ya na rufe baki suka rufumma guard ɗinhakasuka jikkata su a ƴan mintoci, "sannun ku da aiki" Kainuwa yace tare da dukan ƙafaɗun su, kallonmatasa ukun dake gefe yayi fuska yalwace da murmushi yace "Fela, Ɗan amana, Zaiba kar takasance cikin hankalinta" wani ihu suka saki suka yi kan Sa'adatu dake zaune ko gezau, daalamun natsuwanta ba ya tare da ita, janyeta daga kusan da Abdull Fela yayi, tureshi tayi taredararrafawa zata koma kusa da shi, janta Zaiba yayi da ƙarfi be yi wata-wata ba ya shaƙa matahodan ibilis, tun tana bubbuge-bubbugen neman kamo ƙafan Abdull har ta lula duniyar samajannati, ɗago kai yayi ya kalli Kainuwa tare da faɗin "a mana afwa, me gida ya ɗan ja daganan"
"ku yi aikin ku" Kainuwa yace a dake tare da watsa mai jajayen idanun shi, "an gama" yacetaredazaro wata falleliyar adda, lumshe ido Sarari yayi tare da sadda kan shi ƙasa, be yi wata-watayadatsawa ƙaurinta, wani gigitaccen ihu ta saki wanda ya amsa wajen, rumtse ido Sarari yayi cikeda mazantaka, haka suka dinga saran ƙafafun kaman sun samu itace, se da suka tabbatar sunraba su da gan-gan jikinta sannan suka ɗago, juyowa Kainuwa da ya juya tun fara sarandasukayi yayi tare da faɗin "ku shiga ciki ku wanke jikin ku" yana kai nan ya tsallaka malelen jinindakeneman hanya ya isa gare ta ya riko hannunta.... Miƙewa Sarari yayi idan shi akan shi, ɗagowa yayi tare da faɗin, "tana nan" zaro wayan shi yayi yalalibi number ya danna kira, ringing ɗaya aka daga tare da faɗin "Sarari ka ke, mutuminkwanabiyu baka kawo mana ziyara ba" murmushi ya saki tare da faɗin "wataran zan zo dan miƙogaisuwa, yanzu da dalilin kiran" "ina jinka" "mun je ƙaddamar da aiki ne muka tadda aiki acan, sedai waƴanda suka aikata suna wajen" "wannan me sauƙi ne yaran waye?" kallon sakanninyamusu tare da faɗin "ba na jin haihuwar Bertuwa ne, daga ina ku ke?" Yayi maganan tare dajefamusu tambaya, "Yarban" ɗaya daga ciki yace baki na ɓari, "ƴan garin da babu maza ne" yacecikinmaganan shi na marasa ji, "bari in turo yara, amma yakamata ku bar wajen yanzu" "yanzukuwa" yace tare da sauke wayan, "Ɗan kuka a ɗauki ƙafafun nan a birne, Fela cicciɓota muje" yanakai
nan ya fice saurin dafa mai baya suka yi zukata ƙal, suna tababtar da fitansu suka mimmiƙeahanzarce suka dafa musu baya dan ba ƙaramin razana suka yi ba....
Fitan su babu jimawa, motan Shila da muƙarrabanta ya faka, sakkowa tayi bayan ɗaya dagaciki
ya buɗe mata ƙofa tare da bin anguwan da ido, murmushin zaki fahimta ne ta saki tare dawucewa gate ɗin a ishe, saurin turawa gate ɗin wanda ya shige gaban ta yayi ta shige a gadarance, juyowa tayi ta kallesu tare da faɗin "duk wanda muka tadda ya wuce inda ba'a dawowa, itamatana ba mu abinda ya kawo mu ku aikata" jinjina mata kai suka cike da girmamawa, murmushi tasaki tare da faɗin "ka zo hannu Alhaji Namadi" tayi maganan fuska cike da murmushi idantanabin gidan da kallo ...
Tura mata ƙofan parlorn ɗaya a cikin su yayi ta shiga a gadarance, da jini ta fara cin karo, batagama tunanin jinin menene ba ta hangi Abdull kwance cikin jini, da sauri ta ƙarisa inda yaketareda zare ido waje cike da ɗin bin mamaki tace "Sa'adatu ba dai ke ki ka kashe shi ba!" Ta jefatambayan tare da duƙawa akan shi tana kallon ikon Allah me cike da firgici, banko ƙofanpolicesuka yi tare da saurin zagaye su....
Zare ido Shila tayi tare da miƙewa zumbur ta nufi ɗaya daga cikinsu tare da son yin mai bayani
wani gigitaccen mari ya sakin mata, kallon police ɗin dake tsatstsaye dan jiran umurni yayi tareda faɗin "kubtattarasu ku kai su mota" fashewa da kuka Shila tayi tare da ɗaura hannu a samamkai cike da nadaman ƙwaɗayin da ya ingizota ta zo gidan a wannan lokacin, tattarasu sukayi
suka saka a mota suka nufi station dasu.... Tsaye yake a parking space ɗin side ɗin idan shi akan motocin dake doso wajen, suna ƙarisowaaka bubbuɗe musu mota suka sakko fuskoki ɗauke da murmushi, bin su kawai yake da idocikeda mamaki manyan ƙasan ne masu mutumci da kima a idanun jama'an ƙasa, ganin idanunsuakan shi ya sa shi saurin basarwa tare da nufarsu cike da girmamawa ya miƙa musu hannusukayi musabaha, iso ya musu har cikin parlorn hutawan mr president, suna zama ya ɗauki telephoneya kira sashin ma'aikata ya ba da umurnin suka kawo abubuwan taɓawa, gyara zama vicepresident yayi tare da faɗin "ina ga a sanar da Mr president isowan su ko?" Murmushi Jabir yasaki tare da faɗin "yana zuwa yanzu in sha Allah" yana kai nan ya nemi waje ya zauna taredazarowayan shi ya turawa SSB saƙo....
"Please Nafsii!" Insu dake zaune saman cinyoyinshi ɗare-ɗare tace kaman zata fasa ihu, jankunninta yayi da ɗan ƙarfi tare da faɗin "meyasa wannna kunnin baya jin magana ɗaya ne?" Shagwaɓe fuska tayi tare da sa hannunta biyu ta riƙo hannun shi dake kan fatan kunnintatareda faɗin "zafi" "auh shi zafi ki na iya jin shi sau ɗaya kenan?" Yace tare da lakace mata ido, "toNafsii gobe" tace cike da taɓara, "ba zaki kwana dasu ba Gorgeous, Mairah na tare da su, tawakilce ki" yayi maganan tare da kallon wayan shi dake kan table ɗin gabansu da yayi haske, "sun iso" tace tare da kallon shi, jinjina mata kai yayi tare da kallon ta, murmushi ta sakinmai
cike da ƙarfafa mai gwiwa tare da sauka a jikin shi ta ja hannun shi alamun ya miƙe.... Miƙewa yayi idon shi akan ta, ka nazarci kalaman su, ka fahimci manufarsu, ka karanci
buƙatunsu" murmushi ya sakin mata tare da jawota a natse ya sumbaci saman goshinta yarumgumeta tsam, tsayin sakanni suka ɗauka a haka kafin ya zarota ya sumbaci laɓɓanga, murmushi ta sakin mai idanta a cikin na shi, hitting kumatun ta yayi a hankali tare da faɗin"bazan daɗe ba kar ki yi barci" jinjina mai kai tayi tare da bin shi da ido, murmushi ya sakin matatareda juyawa a natse ya fice, murmushi ta saki tare da nufar sofa ta kwanta....
Yana sauka parlorn ƙasa SSG dake zaman jiran sakkowan shi ya miƙe da sauri ya miƙa mai fileɗin dake hannun shi a girmame tare da faɗin "su 15 ne kaman yanda binciken ya nuna babuɗaya" jinjina mai kai yayi tare da amsa ya nufi parlorn a natse dafa mai baya yayi cike da
takatsantsan, tura ƙofan SSG yayi suka shiga a natse, murmushi ya sakin musu tare da nufar
kujera ya zauna a natse, kallon yanda fuskokin su ke fidda murmurshi yayi tare da sakinmusumurmushi cike da girmamawa gare su ya fara marabtan su dan duk sun girme mai nesa bakusaba, daga iyaye se manyan Yayyi....
"Barka da fitowa ranka shi daɗe" vice president yace cike da girmamawa idan shi akan SSB, murmushi ya sakin mai tare da faɗin "yawwa ranka ya daɗe, "ina ganin su za su iya ba muwajesaboda tattaunawan be shafesu ba uban gayya yace idon shi akan SSB, murmushi ya saki taredakallon SSG da Jabir tare da faɗin "ku ba mu waje" ba musu suka fice, gyara zama yayi idanshi
akan su.... Kallon former president yayi tare da faɗin "taɓo mana yallaɓai ko" ba musu ya ɗau systemɗindake gaban shi ya danna kira ya juya da fuskan system ɗin ya fuskanci SSB, murmushi ya saki
idan shi akan screen ɗin system ɗin dan ya ƙosa ya ga fuskan wanda ze bayyana, ana ɗagawafuskan Alhaji Namadi ya bayyana ras, wani nagartaccen murmushi ya saki tare da bin fuskanshi
dake sakin murmushi da ido.... Gyara zama uban gayya yayi tare da faɗin "tun da Allah ya sa ka shigo gidan muke ta waƙanzuwa taya ka murna Allah be amince mana ba se yau, duk da Alhaji Suraj (vice president) yacemana yana ta neman dama ba'a ba shi ba, ina ganin a cikin mu Alhaji Nura (former president) nekawai ya samu daman isowa gare ka bayan shigowanka gidan" tsahirtawa yayi tare da kallonsystem inda Alhaji Namadi ke bin su da ido, "yallaɓai bismillah" yace a girmame, murmushi yasaki tare da faɗin "ai zaka iya wakilta na Alhaji Aminu (Alhaji Aminu Chanba me kuɗin anguwarsuLailah) amma tunda ka bani dama bari in amfani da shi wajen taya me girma shugaban mugabaɗaya murnan samun hawa wannan kujera, ina maka fatan ka zarce ka kuma zarcewa saubaadadi" murmushi SSB ya saki tare da faɗin "nagode ranka ya daɗe" cike da girmamawa....
"Sahabee mun zo gaisuwa da neman iri ne" Alhaji Aminu Chanba yace tare da gyara zama, jinjinamai kai yayi alamun yana sauranshi, "duba da abubuwa marasa daɗi sun faru tsakanin ka daAlhaji Nura zamu iya ce maka ba mu bashi goyon baya ba ko kaɗan, mun tsawatar mai matsayinmu na manya gaba da shi" "ba komai ina ga wannan issue ɗin ya wuce ai" SSB da ya fara ƙosawada zantukan su yace murmushi be bar saman fuskan shi ba....
"To ma sha Allah, mun ji daɗin fahimtar da ka nuna a kan abun, Allah ya ƙara haɗa kawunanmu, ina ganin shikenan abinda ya kawo mu ko?" Ya idda maganan tare da kallon su, jinjina kai sukayi
fuskokin su cike da murmushi, "ma sha Allah ina matuƙar godiya da wannan karamci da kukanuna mun" SSB yace fuska cike da murmushi, murmushi Alhaji Namadi ya saki tare da faɗin"babu komai Sahabee yiwa kai ne, muna goyan bayanka a duk wani abu da zaka yi, se dai zanbaka shawara akan kafin ka zartar da hukunci ka dinga shawartan waƴanda suka tsaya makaharAllah ya kai ka ga hawa wannan kujera, ba ina ƙalubalantar ƙwarewanka ga abinda ka keyi bane, a'a amma idan ka tuntuɓesu suka ba da na su shawarwarin kaman abin ze fi dacewa dubadasunfika sanin abun sun kuma fika shekaru" jinjina kai yayi cike da fahimta tare da faɗin "hakaneranka ya daɗe in sha Allah hakan ba ze gagara ba" "to ma sha Allah, Allah ya ta ya ka riƙo" "amin"yace a girmame, "na so zuwa a yi zaman tare dani wasu izurori ne suka ta so mun, amma inkomai
ya dai-daita zan shigo dan mu tattauna akan wani batu" "to ranka ya daɗe Allah ya amince" murmushi ya saki cike da nasarorin da suka yi hasashe tare da katse kiran, murmushi suformerpresident suka saki cike da manufofinsu tare da sallamanshi suka mimmiƙe, miƙewa yayi yaanatse ya musu rakiya har parking space, suna ficewa daga wajen ya saki wani nagartaccenmurmushi tare da juyawa, sauke ido yayi akan Jabir da SSG dake tsaye suna sakin mai
murmushi.... Murmushi ya saki tare da shigewa gaban su ya nufi ciki dafa mai baya suka yi zukata ƙal, zamaasaman two seater's yayi tare da faɗin "hasashen ka ya tabbata Jabir, Alhaji Namadi shineshugaban tawagan" murmushi ya saki tare da jinjina kai, "matemakin shi kenan anan?" SSGyacetare da sakin murmushi, murmushi ya saki tare da faɗin "Alhaji Aminu Chanba ba, saurandukmember's ne" "amma sun yi asara, anyi girman banza" Jabir yace cike da takaicin su, murmushi
SSB ya saki tare da faɗin "kar ka saka damuwan su a zuciyarka ka damu kan ka, wannankaɗannedaga cikin halayen masu san zuciya" yana kai nan ya miƙe, "yakamata ku ƙarisa gida meetingɗinya isa haka" yana kai nan ya nufi barin wajen, bin shi da ido suka yi har ya ɓacewa ganinsu, numfashi suka saki me ɗan sauti tare da kallon juna.... Yana kife system ɗin gaban shi babban yaron shi ya iso da sauri riƙe da waya a hannu, kallonshi
yayi cike da nazari tare da faɗin "zauna" zama yayi tare da faɗin "an kama Shila a gidan
Sa'adatu!" "Meya kaita?" Yace a natse idon shi akan shi, "ba na ce ga dalilin ba, se dai policesun
je gidan saboda masaniya da suka samu na kisan kai da aka yi, a nan suka kamata ita da yarantahannu dumu-dumu" "wa aka kashe?" Yace tare da gyara zama, "yaron nan ne" yace a natse, "itaSa'adatun fa?" "Ba labarin ta na gidan" jinjina kai yayi tare da faɗin "abincika idan ta samuwani
abu a amsa, in ba ta kai ga samu ba a tabbatar da gobe ba ta wayi gari a wajen nan ba, a aikatainda ta aikashi, dan in ta kai gobe za ta iya buɗe baki" ya idda maganan a natse babu wani
alamun tashin hankali tare dashi ta ɗau wayan shi ya danna kira ya miƙe a natse ya bar wajen, jinjina kai yayi cike da bin umurni ya fice daga wajen a hanzarce....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
Created and written
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fifty seven
A ƙofar wata ƙaramar private hospital suka faka mashinan da suka hayo da napep, suna sakkowasuka yi ciki a ɗan hanzarce, da razani waƴanda ke zaune a reception suka tare su tare da
tambayansu lafiya? Dan yanayin su be yi kama da waƴan da suke cikin hankalin su ba....
"Mara lafiya muka kawo ina likitan?" Kainuwa yace tare da baza ido, "ina take!" Ɗaya dagacikinnurse's ɗin dake wajen tace tare da nufo wajen ta fara neman mara lafiyan, "Fela kawo ta" Ɗankuka yace tare da ja gefe Fela ya bayyana, zare ido suka yi a razane tare da rumtse idanu, "subhanallahi waya mata haka! Kun faɗawa police kuwa!" Doctorn da ta iso wajen a lokacintacecike da ruɗu...
"Ba ruwan mu da wani police, ku amsheta ku mata abinda yakamata kuna ɓata mana lokaci" Zaiba yace tare da watsa musu jajayen idanunshi, girgiza kai tayi tare da faɗin "ba zamuiyaamsanta ba se police sun shigo cikin, ku je ku taho da ƴan sanda tukun" tayi magana taredayunƙurin barin wajen, "ke likita! zo ki amsheta ku je da ita ciki, baki ga halin da take ciki bane?Ta zubda jini da yawa" Ɗan kuka yace zuciya na habƙoro, "dokan kenan" tace a dake tare dajuyawa, "kin ci uban Babanki da dokan! mu zaki faɗawa doka! Ke da dokan na haɗa na ciremukuduk wata albarka, ƴar iska mara hankali, muna faɗamiki ta zubar da jini da yawa ki na wani kawomana doka, to na soke dokan daga yau, wallahi ki ka bari ta mutu a wannan yanayin se kinbi taatake ba tare da kin ƙara sakan guda ba" ɗan amanan Sarari yace murya a kausashe cike da
ɗaukan alwashi tare da zabura da nufin isa gareta...
Tunda ya fara banbamin jikinta ya fara kyarma, ba ta samu lafawan shi ba se da ya dasa aya, komawa gefe tayi ta raɓe cike da tsoro, sauran nurse's da ma'aikata kuwa ba wanda cikinshi beburge ba, isowa wani matashi wanda ba ze gaza 33 year's ba yayi jiki na ɗan ɓari a hanzarcetareda faɗin "Kainuwa ka ke na Sarari bawan Allah, sun buga daku sun barku, wallahi ƙaryanɗanhalas bare kuma shege, dashen Allah ka ke ba na mutum ba" guntun murmurshi ya saki taredafaɗin "ka iya ka huta likita boka turai" murmurshi ya saki cike da razanin da be gama sakinshi bayace "Allah yasa dai lafiya, banga rauni a jikin ɗayanku ba"....
"Fela matso kusa" Kainuwa yace muryan shi na canzawa, zare ido yayi tare da haɗiye wani
kakkauran yawu, saboda faɗawa da idanshi yayi kan Sa'adatu dake a sume kamar gawa, "ƙanwarmu ce, a mata duk wani abun da ya kamata" yace tare da kallon shi, zaro hanky yayi ya gogezufatare da faɗin "ba damuwa, se dai ba ma da kayan aikin da zamu iya riƙeta a wajen mu, wannanissuen general hospital ne, su ke da kayan aiki wadatattu" ya idda maganan idon shi na yawoakan su, "se yaya kenan!" Sarari yace a dake, fiddo ido ya kuma cikin shi na murɗawa cikedatsoro yace "in ba damuwa zamu iya bata temakon gaggawa kafin ku kai ta can" yayi magananahankali, shirun daƙiku suka yi kafin Kainuwa ya kalli Sarari ganin irin kallon da ya mai ya sashi
faɗin "to ku je ku yi duk abinda ya dace" ya idda maganan tare da jan kujera ya zauna kusadaSarari, da sauri ya ba nurse's umurnin fiddo da gado ya wuce da hanzari dan shiryawa... Zaro waya Sarari yayi ya danna number Kabir, ringing biyu ya ɗaga gyara zama yayi tare dafaɗin"tun ɗazu nake kiran ka ba ka gani ba ne?" "Ban gani ba" yace hankali kwance, "kana ina ne?" Yajefa mai tanbayan cike da kulawa, "asibiti" yace tare da miƙewa tsaye, "lafiya dai ko!" Yacecikeda kulawa me haɗe da tsoro, "da sauƙi, kiran me ka ke mun ɗazu?" "Dama su Goggo ne sukenemanka" "har sun dawo kenan?" "Eh tun ɗazu, me ku ke a hospital?" "Sa'adatu muka kai" yaceadake...
Miƙewa tsaye Kabir yayi zumbur ƙirjin shi na bugu da ƙarfi tare da faɗin "ta mutu ne!" "Dasauranta, se dai ta rasa ƙafafu duka biyu" zare ido yayi tare da damƙe bakin shi da hannu, "yanzuzamuga da wani ƙafan za ta dinga takun isa da gadara, zamu ga inda zata samu bakin cigaba wamutane rashin kunya" jinjina kai yayi tare da faɗin "wani hospital ne!" "Ka zama namiji, kadainakyarman murya kamar mace, zamu wuce da ita general yanzu" yana kai nan ya katse kiran....
Fashewa da wani raunataccen kuka Kabir yayi cike da ruɗu me haɗe da rikicewa, miƙewa yayi
zumbur ya fara zagaye ɗakin yana kuka me cike da rauni tare da tuno shuɗaɗɗun abubuwa, tsayawa cak yayi kaman wanda aka tsaida, tsayin sakanni ya ɗauka kafin ya juya ya nufi ƙofakamar wanda aka ja ya fice a guje, kai tsaye gidan su Harari ya nufa.... Be samu zarafin ɗaga musu sallama ba ya faɗa ciki, "subhanallahi" Baba dake kishingiɗe yanasauraran labari a Radio yace tare da miƙewa zaune da sauri, "Kabir lafiya kuwa!" Mama dakezaune bakin murhu tace cike da zallan mamaki idanta akan shi, girgiza kai yayi tare da faɗin"suSalisu ne suka bi Sa'adatu!" "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" Baba yace murya na rawa taredamiƙewa tsaye da sauri, "to fa!" Mama tace ko a jikita dan ta so hakan, "ba abinda suka matako!" Baba yace a rikice....
"Sun cire mata ƙafafu!" Yace a raunane idan shi na zubda ruwan hawaye, "ƙalu inna lillahi wainna ilaihirraji'un" Baba yace tare da tafe hannu, "ƙafafu kuma! Allah me iko" Mama tace adake, "ba mu ga ta zama ba Kabir kai ni gidan kar su ce za su kasheta su ɗaurawa kan su wani
damuwan" Baba yace a rikice tare da yin ƙofa....
"Ba ka ɗauki makullin machine ɗin ba" Mama tace da ƙarfi, "amso min Aminullah" yace taredaficewa, juyawa Kabir yayi da niyyan ficewa tambayan Mama ya dakatar da shi, "baka yi farinciki
da hakan ba ko?" Lumshe ido yayi tare da faɗin "ba zan iyawa kaina a dalci ba bare in ma wani
akan ƴan uwana Mama, duk abinda ta shuka me cike da takaici da baƙin ciki hakan be sa nakasajin zafin abinda suka aikata mata yau ba" yayi maganan cike da rauni, murmurshi ta sakinmai
tare da jinjina mai kai, juyawa yayi ya fice jiki a sanyaye.... Kai tsaye general suka yi ko da suka isa ba su rigada sun ƙariso ba, tsayuwan jiran isowansusukayi cike sa ƙosawa aiko ba su yi cikakkkun mintina 20 ba suka ƙariso, da sauri suka yi inda suke, "ina take!" Kabir yace a kiɗime, kallon sakannin Sarari ya mai tare da juyawa ya nuna mai
Kainuwa da ya fito daga napep saɓe da ita, zare ido suka yi shi da Baba zukata na bugu daƙarfi
saboda ganin yanda aka naɗe gundilmin gwuwoyinta da bandeji.... Ganin yanda suke kallonta a razane yasa Sarari faɗin "ku wuce da ita, ku tabbatar sun yi abindayakamata" jinjina kai suka yi tare da wuce wa, da sauri Kabir ya dafa musu baya idan shi nazubdazafafan ruwan hawaye... Matsowa kusa da shi Baba yayi a sanyaye murya na rawa yace "Salisu a she ban isa da kai badama! Salisu a she ba zanci albarkacin mariganyi ba! Shin in kun kasheta me ze amfane kune?" Ya idda maganan zuciya a raunane, ɗago kai yayi ya kalleshi cike da tabbaci yace
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 92 Chapter of 109