sauke ajiyan zuciya tayi tare da sakin mai murmushi ta
bankawa Insu harara, dariya suka saki gaba ɗayansu cike da nishaɗi..... Haka suka kamma cin abincin cike da nishaɗi suna taɓa hira cike da shaƙuwa, suna kammalawaInsu ta tattara plate's da food flaks ɗin da suka yi amfani da shi ta wanke tas ta maida indataɗakko, fitowa tayi cike da natsuwanta ta nufi bedroom ɗin Yasmin ta ɗakko veil ɗinta da jakatafito a natse.... Da mamaki Yasmin tace "ina zaki!" "Gidan mu mana" tace tare da fara naɗa veil ɗin, "ina ceseanjima za ki tafi!" Tace cike da magiya, girgiza kai tayi tare da faɗin "marayun Allah na cannajirana, na gama abinda ya kawo ni ba zan miƙe ƙafa a gidan siriki nayi ta zama haka ba" taiddamaganan cike da yanayinta tare da zama ta fara saka takalmi, dariya yawancin su suka saki cikeda mamakinta....
"Wato gidan siriki!" Zubair yace tare da kama haɓa murmushi yalwace a saman fuskan shi, "ehmana, gidan siriki" tace tare da miƙewa ta saɓa jakanta, "da wa zamu wuce?" Tace tare dakallonSalman da Sadam da Balarabe, miƙewa Sadam yayi tare da fadin "muje" ba musu ta juya gaYasmin tare da faɗin "baby zamu yi magana in na koma, a dai cigaba da riƙe aure da hannubiyu, yi na yi bari na bari shine auren" tana kai nan ta fice da sauri saboda ficewan da Sadamyayi, dariya suka saki tare da bin ta da ido, da sauri Yasmin ta dafa mata baya, kallon Farisat Salmanyayi tare da faɗin "tashi muje" ba musu ta miƙe ta saɓa jaka, "dakko Mairah" yace tare da gyaratsayuwa, wuce wa ɗaya daga cikin bedroom's ɗin dake side ɗin tayi ba ta jima ba ta fito saɓedaita, amsanta yayi ya saɓa a kafaɗa suka sallami Shureim da ke ta bin su da ido, miƙewa Balarabeyayi tare da faɗin "anguwan nan na ku zanje, muje ku goyani ku goya abar hawa na" dariyaSalman ya saki tare da ficewa, dafa musu baya Shureim yayi a natse, mu ma ku mu yi hoɓɓasa" Annur yace tare da miƙewa....
"Baby Insu yanzu da gaske tafiya zaki yi!" Yasmin Tace kamar zata saki kuka, "wai zamanmezatayi ne!" Hisham da ya biyo bayan su tun fitan su yace tare da kallon ta, ƙwal-ƙwal tayi daidotare da faɗin "anjima se mu maidaki ko Hisham ya maidaki" girgiza kai tayi tare da faɗin"bakowa a gidan, Anty Habiba mun baro zata koma tun ɗazu, daga Hajiya se Baba Mari, ga suNafisatzasu koma ba za su ji daɗi ba in ba su tadda ɗaya daga cikin mu ba" ta idda maganan cike dagaskiyan ta, sauke numfashi a hankali tayi tare da faɗin "shikenan tunda Mommy na nan" "wataMommyn! Wallah gida zan tafi" "haba Mommy!" Tace idonta na tara ruwan hawaye....
"Ai maidasu da wuri ma, dan tafiya ba fashi, ina da magana da Yaya in na bari se anjima basamundama zanyi ba" tace tare da sakin murmushi ta wuce Salman ya dafa mata baya, "Yaya Salman!" Tace kaman zata saki kuka, "sorry" yace fuska yalwace da murmushi ya shige mota, "ai shikenan"tace tare da kauda kai...
"Me ke faruwa anan?" Annur yace tare da bin su da ido, "wai kuma!" Tace tare da sakin hawaye, dariya suka saki tare da bin ta da ido, "daughter Yasmin ya da kuka kuma?" Momcy tace fuskayalwace da murmushi, "shikenan duk tafiya za ku yi yanzu" tace murya na rawa, "to bari muzauna" Laɗifa tace tare da sakin dariya, rufe murfin ƙofar ɓangaren da Insu ke ciki Hishamyayi
tare da faɗin "kin gaida Labib ɗin ko?" "Eh munyi magana jiya yace jikin da sauƙi sosai" "ehhakayace mun" yace da kulawa, "okay zamu yi magana anjima" tace tare da sakin mai murmushi
murmushi ya sakin mata ya ja baya kaɗan kunna motan Sadam ya yi yaja a natse ya doshi ƙofa, haka suka shishshige kowa ya ɗau hanya, kuka Yasmin ta saki cike da rauni lokacin da sukaiddaficewa, dariya Hisham ya saki tare da juyawa yayi inda motan shi yake....
Rungumota Shureim yayi ya nufi ciki da ita, zaunar da ita yayi ya duƙa kusa da da ita tare dafarashare mata hawayen dake tsere a saman fuskanta, "ba su kyauta ba, amma na san uzurinsume
ƙarfi ne, ki daina kukan" yace da kulawa, jinjina kai tayi tare da kallon shi, "ƙyalesu mu mazamutafi wajen su Mommy anjima kaɗan musha nono" yace tare da sakin mata murmushi, nagartaccen murmushi ta saki tare da kallon shi cike da son tabbaci, jinjina mata kai yayi taredarungume kanta ya saka a faffaɗan ƙirjin shi cike da so da ƙauna....
Zaune suke a general parlorn gaba ɗayansu kowa da abinda yake hankali kwance, kama haɓaBabiya tayi tare da faɗin "yanzu Insu dama kin adana wannan danbun naman!" Tayi maganancike da mamaki, murmushi ta saki ba tare da tace komai ba, "ke ma kin san wannan a zauneyakeHajiya, ai na san kowa se ya cinye na shi nata na nan, Insu kuma da tsumulmula" Farisat tacetareda kallon Babiya, "adana dai" Sadam yace tare da tashi ya koma inda take ya ɗibi danbunkaɗanya kai bakin shi, "Sahabee ɗakko mun orange juice a fridge, wannan da abu me sanyi ze fi tafiya" yace tare da gyara zama.... Tashi yayi da sauri ya wuce dan cika umurni, sallama Ziyada tayi tare da shigowa a natse sabodahango Yaya da tayi zaune yana bin yaran shi da ido yana sakin murmushi, amsawa suka yi dakulawa, wuce wa gefen Babiya tayi ta gaidata a ladabce, amsawa tayi cike da jin daɗi, gaidaYayatayi a girmame amsawa yayi da kulawa tare da tambayanta iyayenta, amsawa tayi da sunalafiyata juya ga Farisat, harara ta banka mata tare da faɗin "ke yarinyar nan ba fa mutumci ne yaisheki
ba" ƙaramar dariya ta saki tare da fadin "afwan Mommy wallahi exams ne ya saka nayi busysosai" "kin kyauta" tace tare da kauda kai, "nagode Mommy ya Mairah?" "tana lafiya" tacematacike da kulawa.... Ƙarisawa kusa da Insu tayi ta duƙa tare da faɗin "teacher fa ya kuma taso ni" tayi maganantareda sakin murmushi, "na san za'ayi haka tunda na zo na tadda missed call ɗin shi uku, me yace?"
"Magana akan gasar nan ne dai" tace tare da sakin murmushi, "oh Allah ban san da wani yareyake son in fahimtar da shi ba" tace tare da buɗe bottle ɗin ruwa ta kai baki, "kai wannanteacherakwai natacce, ba ya haƙura haka ba tunda yayi-yayi tace ba zata koma ba" Babiya tace cikedatakaici, "a huce Hajjaju makkatun" Sadam yace tare da sakin dariya...
"Wallahi Sadam abin da takaici yayi-yayi tace a'a to ya haƙura mana" "mafitan shi yake dubawa" yace tare da amsan lemun da Sahabee ya miƙa mai, "thank you Uncle mie" yace tare da sakinmai
murmushi, murmushi ya sakin mai cike da jin daɗi ya koma inda ya tashi ya zauna, "bismillahdambu" Insu tace tare da miƙa mata roban dake gaban su, girgiza kai tayi tare da faɗin "kinmanta bana cin jan nama ne?" "Oh haka ne fa, baby Ziyada kin bar daɗi" tace tare da sakinmurmushi...
"Ki ce mai nace Allah ya nuna mana" tace a natse, murmushi ta saki tare da faɗin "ko kefa, har
kin fi jiya da shekaran jiya kyau" tana kai nan ta miƙe ta sallame su ta fice, "ita ma natacciyannekaman shi" Babiya tace cike da takaici, murmushi suka saki ba tare da wani yayi yunƙurintayataba, shigowa Nafisat tayi rungume da Mairah ta miƙa ma Farisat ita tare da faɗin "ta tashi yanzu"
"akwai sauro a ɗakin na ki ne?" Tace tare da amsanta, "ban dai jiba" tace tare da zama kusadaYaya, "yakamata ki tashi ma ki koma gidanki haka" Babiya tace mata da kulawa, "Nafisat cirominwaya na a caji in kira shi, in yagama uzurin shi mu tafi" "to" tace tare da nufar inda wayanyake....
"Assalamu alaikum warahmatullahi wa barakatuhu, ga kanun labaran mu na yau Asabar 25gawatan 9 me karantawa Karimatu Lawal Yahya, a yau ne zamu ji sabon titin da gwamnatinjahar
Kautal ta ƙaddamar da buɗewa, sannan zamu ji nauyin karatun jami'an da me girma shugabanƙasa ya ɗaukewa iya ɗalibai ɗari uku, sannan za muji harin da aka kaiwa mota me girma
shugaban ƙasa a kan hanyarshi ta zuba bikin ɗiyar ƴar uwarshi a garin Bertuwa" wani ras
zukatansu gaba ɗaya ya buga a lokaci guda, saurin jawo tv control Sadam yayi ya ƙara volumeadai-dai lokacin Salman ya doko sallama ya shigo....
Zuba ma tv ido suka yi cike da ƙosawa, saboda tafiya hutun sakanni da suka yi, "barkan mudadawowa, a yau Asabar 25 ga wannan watan gwamnatin jahar Kautal ta ƙaddamar da buɗesabontitin da ta shinfiɗa a jahar, babban titi ne wanda maƙiyasta suka bayyanar da tsayin kilomitadari
biyu da 60, wanda babban hanyace ta tashi daga cikin gari zuwa local government har huɗu, sannan a yau ne aka fidda bayanin ɗaukan nauyin karatun yara ɗari uku masu tafiya gabadasakandire da gwamnatin me girma shugaban ƙasa me ci a yanzu doctor Sahabee SadamƁadamayya tayi, sannan a daren jiya juma'a 24 ga wannan wata ne aka fidda bayani akanharinda aka kai wa motan me girma shugaban ƙasa akan hanyarshi ta zuwa ɗaurin auren ɗiyar ƴar
uwan shi, bayanin dai ya tabbatar mana da harin da aka kai ya cutar da mahaifiya ga me girmashugaban ƙasan, tana gida tana amsa jinya na musamman, se dai har yanzu babu wani masaniyaakan me girma shugaban ƙasa, muna musu fatan samun sauƙi da gaggawa" miƙewa Insutayi
zumbur tare da faɗin "Yaya Hajiya!" Ta idda maganan tare da duƙewa ta fashe da raunataccenkuka, da sauri Sadam ya riƙota na shi ƙirjin na tsananta bugu....
"Dama na sani ko kowa yaƙi zuwa bikin Yasmin Hajiya ba za ta ƙi zuwa ba, takwarar aminiyartada take matuƙar sone fa, inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, meyasa ba su nuna fuskanta ba, meyasa ba su nuna mana halin da take ciki ba, wataƙila sun kasheta ma" ta idda maganan cikinrishin kuka tare da zubewa a jikin Sadam, "shii ya isa haka, in sha Allah ba abinda ya samesu" Sadam yace a rikice, ɗaukan wayan shi dake gefe Yaya yayi ya danna number Lailah.... Kamo Farisat dake kuka da gunji Salman yayi tare da faɗin "dan Allah ku yi shiru, kukankuƙarata'azzara na su Sahabee ze yi bakwa ganin yanda suke kukan ne?" Ya idda maganan cike dadamuwa, girgiza kai tayi tare da faɗin "my Jannah Hajiya fa aka cutar wayasani ko har da Uncleɗin ma ɓoyewa aka yi, ita kenan mana Kaka ta nunawa a dangin Anty in mun rasata wa mukeda!" ta idda maganan a raunane, jinjija kai yayi tare da faɗin "in sha Allah ba abinda ya sameta, Nafisat ku daina kukan haka, jinjina kai Nafisat tayi tare da kamo Sa'eed da Umar ta zaunar, kamo Sahabee Farisat tayi jiki na ƙyarma, "kai wannan mugun ji Allah ka shiga tsakaninmudashi" Babiya tace cike da alhini, a dai-dai nan Lailah da ɗaga kiran Yaya da ya kuma mata sabodawan can ya katse bata ɗaga ba....
Sallama ta ɗaga mai a girmame, amsawa yayi cike da kamewa tare da tambayanta gida dalafiyan yara, "Alhamdulillah Yaya ya kuma ku ke?" "Alhamdulillah meke faruwa ne? Mungalabarai yanzu akan harin da aka kai wa su Hajiya" yace murya a kame, shiru tayi cike da faɗuwargaba dan ba ta so su ji ba, "ki na jina Lailah?" Yace a dake, "eh Yaya, wallahi mu ma jiya mukaji
labarin, amma se dai sun ce ba ta cikin ko wani haɗari" tace cike da damuwa, "shi Yayannakufa?" Ya jefa mata tambayan cike da son sanin abinda ya same shi, "gaskiya ba su faɗi halindayake ciki ba, kasan duk tsayin shekarun nan dama se dai aiki da yake zarowa amma wani labari
akan shi ba'a faɗe" tace cike da damuwa....
"Kun je ne?" Yace a dake, "a'a Yaya amma in sha Allahu zamu je, garin ne ya rikice tun darenjiyamatasa ke zanga-zanga, sun ƙone gidan former president ƙurmus, wallahi jami'an tsaro netakota ina, shiyasa ba mu samu zuwa ba, amma in sha Allah ko zuwa gobe in komai ya lafa zamujemu duba su" "ku jira mu goben zamu shigo Mu duba su" yace cike da dattakon shi, "to YayaAllahya kai mu" tace cike da jin daɗin, dan dama san zuwa su kaɗai ne ba sa yi....
Yana sauke wayan ya maida akalan kiran ga number Hassan yana ɗagawa suka gaisa ya jefamai
tambaya akan ko ya san abinda ke faruwa, "tabbas na sani jiya na gani a labaran karfe 11:00pm" yace a natse, "zaka samu shigowa goben ne?" Ya jefa mai tambayan a natse, "da wuya, ammainsha Allah weekend me zuwa zan ƙoƙarta in je can in duba su" jinjina kai yayi kaman yana ganinshi tare da faɗin "Allah ya amince, in sha Allah gobe zamu shiga" "Allah ya yarda in kunisakataɓo ni nayi magana da su" "to in sha Allah" yace tare da sauke wayan.... Ajiye wayan yayi a gefen shi tare da bin su da ido, ganin yanda duk fuskokin su ya canza yasashi
sakin guntun murmurshi tare da faɗin "ku shirya gobe zamu mu dubo su" jinjina kai Farisat tayi
da sauri tare da faɗin "har da su Sa'eed?" Jinjija kai yayi tare da faɗin "eh ba zama zamu yi bamuna duba yanayin jikin na su zamu dawo, jibi suna da makaranta ku kuma kuna da aiki" jinjinakai tayi cike da gamsuwa, miƙewa yayi ya wuce side ɗin shi, "to aike Farisat be kamata maajedake ba" Babiya tace tare da kallon Farisat, girgiza kai tayi tare da faɗin "kar ki kawo wannan
maganan Hajiya, in sha Allah ba abinda ze faru lafiya zamu mu dawo lafiya, Uncle da Hajiyafaaka cutar" ta idda maganan a raunane, kamo hannunta Salman yayi tare da faɗin "ya isa inshaAllah tare zamu" jinjina mai kai tayi cike da samun sassauci...
"To ai se a sanar da Mari gobe ta huta kar ta zo" Babiya tace tare da miƙewa a natse tayi ɗakinta, "tattarasu ku je ku kwanta" Insu tace tare da kallon Nafisat, jinjina mata kai tayi ta miƙe anatseta tattara su Sahabee suka wuce ɗakunansu, "please Insu kukan nan ya isa haka" Salmanyacecike da kulawa, jinjina mai kai tayi hawaye na tsirara a kuncinta, ba abinda take tunawa serayuwar da tayi da Hajiya me cike da kula da tausayawa, ɗaukan wayanta dake neman agaji
Farisat tayi ta kara a kunni da sauri tare da faɗin "Anty Salwa.... Ɗaukan wayanta dake ringing Sadam yayi ya miƙa mata tare da faɗin "Hisham, ɗagawa tayi takara a kunni tare da goge hawaye, "girlfriend wai da gaske ne abinda muka gani!" Hishamdaketsaye a gefen parlor idon shi akan Yasmin dake ta risƙan kuka Shureim da su Mommy na rarrashi
yace cike da ruɗu, jinjina kai tayi tare da faɗin "eh" "subhanallahi yanzu muka gani a labarai
wallahi" jan hanci tayi tare da faɗin "in Allah ya kai mu gobe zamu tafi mu ga yanayin jikinnasu, please kar ka sanar da Yasmin, dan na san zata tashi hankalinta" kallon Yasmin dake jiyokomai
yayi tare da faɗin "in sha Allah, in babu damuwa bari in duba ticket mu tafi tare" jinjina kai tayi
tare da faɗin "okay ka gaida su Mommy" "za suji" yace tare da sauke wayan, fashewa da kukaYasmin tayi cike da rauni, juyawa Hisham yayi ya nufi barin parlorn, "ka siya ticket ɗin damu" Shureim yace tare da kallon shi, jinjina kai yayi ya wuce bedroom ɗin shi....
"Ya isa haka" yace mata cikin muryan rarrashi, jinjina mai kai tayi cike da samun sasauci taredafaɗin "nagode" murmushi ya sakin mata idon shi akanta tare da faɗin "nagode" murmushi tasaki
tare da sadda kai ƙasa...
Zare wayan kusan a tare suka yi suka ajiye, "Anty Salwa zata tashi 10 na daren yau zata saukaaƁadamayya" tace tare da kallon su, "ta ji kenan?" Salman yace idon shi akan ta, "tace tunjiyataji""ina ta bar yaran?" Insu tace tare da kallon ta, "suna wajen kakarsu mana" tace tare ɗaukanruwatasha, sauke bottle ɗin tayi ta ajiye tare da faɗin "gobe ita ma zata juya" "Allah ya kai mu" Salman yace da kulawa, miƙewa Insu tayi tare da faɗin "yakamata kuma ku hoɓɓasa" tanakai
nan ta wuce bedroom ɗin ta....
Ta ɓangaren garin Ɓadamayya kuwa rikicewa iya rikicewa garin tayi, matasa sun harzuƙosunnuna ma shugabannin ƙasa da masu faɗa aji za su iya komai akan shugabansu, sun shirya fitonafito ga duk wanda ke da niyyar cutar da shi, sun tura saƙo iya sako wanda ze isa kunnuwanmasushirin aikata wani abu, daƙyar aka samu suka ɗan lafa shima dan me magana da yawunshuganƙasa ya sanar musu da bayani daga bakin shugaban ƙasar, "kai jama'a, komai na gan da bayyana"Alhaji Jamil yace cike da alhini, "wai ma ya aka yi journalist's suka samu bayanin nan ne!" Jabir
yace cike da ta'ajibi....
"Waze fidda kuwa banda ɗaya daga cikin mu, mu muka sani kuma muka binne a tsakaninmu, indai magana ya fita daga cikin mu ne, ɗaya a cikin mu ne talallaɓa ta tono, gashi abinda mukegudun bayyanuwan shi na gab da bayyana, kuma shikenan komai ya zo ƙarshe" Hajiya tacerai
ɓace, da mamaki Alhaji Munnir ya kalli Lubabatu dan ita zuciyar shi ta ɗarsawa, kauda kai tayi batare da tace komai ba, "Luba ke ce ko!" Alhaji Jamil yace murya a kausashe, "ni ce" A'isha daLubabatu suka ce bakuna a haɗe, da mamaki suka kalli juna kafin su maida dubansu ga suHajiyadake ma A'isha kallo me cike da mamaki....
"Ki yi haƙuri Hajiya, ba zan iya cigaba da jurewa ba ne" A'isha tace murya a sanyaye, "habaAntyA'isha ya zaki yi haka!" Abubakar yace murya ba daɗi, "Abubakar abun ba ya da sauƙi kamar
yanda ku ke tunani, ku maza ne gwanayen dakiya mu kuwa matane gwanayen rauni, abindaza
ku iya jurewa ba lallai mu iya ba" ta idda maganan a raunane, jinjina mata kai suka yi cikedafahimta, "shikenan yanzu idan manema labarai da masu hakkin kare lafiyanshi sun zo nemansani game da batun se ki musu bayani, ku ke nan ku yi ta aikata abinda zuciya ta raya mukubakwa zama da ƙwaƙwalenku ku yi tunani akan abinda ka je ka komo in kun buɗe baki, Allahyakyauta" Hajiya tace cike da takaici....
"Ayi haƙurin Hajiya wannan ya faru mu nemi hanyar gyara" Jabir yace a sanyaye, "gyarammeJabir! Ai komai ya lalace" Hajiya tace murya na rawa, "Allah ya baki haƙuri Hajiya, ba muyi hakandan ɓata miki ba, munyi hakan ne dan samama ɗan uwan mu mafita, a tunaninmu kenan, bamada wani hanya se wannan" Lubabatu tace murya na rawa ido na tara ruwan hawaye, "ya isahaka"Alhaji Jamil yace cike da fahimtansu, jinjina mai kai suka yi cike da samun sassauci, "Allahnasane da komai" ya kuma cewa a raunane....
Zaune suke cikin wani tanƙasheshen parlor da ya gama haɗuwa, ƙananun kofunan shayi agabanko wannen su, kallon vice président former president yayi tare da faɗin "dama na san bayacikinmotan nan, ya tabbata mutanen nan akwai abinda suke ɓoye mana" "tabbas akwai, yarannannafaɗa muku akwai abinda suke nufi damu, ku kalli wannan" yace tare da ajiye takardan dakeriƙeahannun shi, "tsayin shekaru biyu kenan ƙafarshi be taka office ɗin shi ba" yace cike da takaici, damamaki tsohon dake zaune yana bin su da ido ya kalle shi tare da faɗin "be zuwa office kenan?To me yake!" "Wannan amsan na garesu" yace tare da ɗaukan takardan, juya duban shi gaformerpresident yayi tare da faɗin "ban san so nawa za'a hanaka abu ka aikata ba, ba dadin Allahyasada kwananka a gaba ba da yanzu ba zancen nan muke yi ba, yakamata ka dinga abu da lissafi, yaron nan ba fin ƙarfin mu yayi ba, muna bin komai a natse ne dan in mun tashi cafkan shi mucafke shi a maƙoshi yanda ba ze iya kuɓuce mana ba, irin su se an koma kaman su ake iya samungalaba akan su, a gaba in ka ƙara wannan kuskuren, zamu barka da wawtanka, dan ba zamuyarda ka shafa mana kashin awaki ba, yana kai nan ya juya ga vice president....
"Ina son ka shigar da takardan neman zama da shi, anan zamu fahimci gaskiyan da suke ɓoye
mana, in ya so in zaman ya yiwu se ka nema mana zama da shi dan mu kai mai ziyara na farko, bamusan bayan wannan nawa ne ze bi yo baya ba" yana kai nan ya miƙe a natse tare da faɗin"zakuiya tafiya" yana kai nan ya ɗau sandarshi ya fara dogarawa a natse ya nufi ciki, sauke numfashi
suka yi gaba ɗayan su tare da miƙewa suka fice kowa da abinda yake saƙawa a zuci.....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
Created and written
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fourty four
A natse suka fito filin farfajiyan tashi da saukan jirgin saman gari, a jere suke kaman waƴandaaka jera, wannan na ɗaga ƙafa wannan ze ajiye, shiga me ɗaukan hankali suka yi cike da
mutumta kai, Salam dake riƙe da hannun Farisat da ta haɗe cikin wata ni'imantacciyar laceashan white colour ta yafa babban veil wanda ya saukan mata har baya ne a gaba...
Ta gefen su ta baya Yasmin da Shureim ne cikin shiga iri ɗaya niimataccen shadda goldengreen, an zuba musu ɗinki na ji da gani, suma riƙe da hannun juna ƙam-ƙam kamar wani yace zeƙwaceɗayansu....
Ta gefen su Insu ne cikin wata Abaya hex colour wanda yayi mugun amsanta, baby hijabmilksanye a jikinta wanda shima ya fidda mata wani ɓoyayyan kyawun da ba kowa ya santa dashi
ba,....
Jakanta goye a baya kamar ko yaushe, takalmin half cover me sauƙin tudu milk colour sanyeakafanta, saman fuskan nan ta ƙawatashi da fashion eye glass, hannaye ƙawace da agogodaawarwaro, yatsu sunji zabba ƙananu masu kyawun gani, se zuba sihirtaccen ƙamshi take, agefenta Hisham ne tafe cikin shadda fari ƙal da baƙin hula dake ta zuba shainin, ya ƙawataadonshi da duk abinda ya dace se ɗaukan ido yake suna tafe suna taba hira cike da shaƙuwa....
Ta bayansu Nafisat ce da su Sahabee cikin shiga na ɗaukan hankali, ta bayansu Yaya ne daSadam dake saɓe da Mairah a kafaɗa da Babiya, ba wanda be kashe kala ba, "ga su can" Farisat
tace tare da nuna Lailah da Khadijatu da Salwa da suka nufo su cike da farin cikin ganinsufuskanta washe da murmushi.... Murmushi Yaya ya sakin ma mazajen su dake biye a bayan su tare da tsayawa dan ba sudamanƙarisowa, suna isowa suka ba shi hannu cike da girmamawa, suka fara gaisawa, rungumeInsuSalwa tayi tare da faɗin "baby Insu wannan kwalliyar duk na duba Hajiyan ne?" Murmushi tasaki
tare da zame jikinta a natse cike da basar da maganan, rungumar Farisat Khadijatu tayi yayindaLailah ta rungume Yasmin, nan suka shiga ya hanya cike da kulawa, "ai Salwa ke ma kamatayayi
a miki ya hanyar tunda ke ma zuwa ki ka yi" Babiya tace mata tare da sakin murmushi, "wallahi faHajiya Babiya, gashi ba za'a huce gajiyan ba za'a ƙara ɗaukan hanya" tace tare da sakin
murmushi....
"To ai dubiyan mara lafiya ki ka zo, lada ne daga zuwa har komawa, taka dausayine fa dagacikindausayoyin gidan aljanna, kin ga ai ba asara" "wannan haka yake Hajiya Babiya" tace taredasakin murmushi, "ni fa ga wanda nake mamakin gani nan Yaya" Lailah tace tare da kallonYayahannunta akan Yasmin, "yanda ki ka ganta haka shima ya ganta, ba wanda yasan da tafiyar natase da muka haɗu a airport" Farisat tace tare da kallon ta, "sannu Shureim ba komai fa akebiyewamace ba" Lailah tace cike da dattako, murmushi ya saki ba tare da yace mata komai ba, ɓata
fuska Yasmin tayi tare da sadda kai, matse hannunta dake cikin na shi yayi a hankali cikedararrashi, ɗago kai tayi ta kalle shi tare da sakin mai murmushi, murmushi ya sakin mata cikedakulawa...
"Anty Lailah danbu na dai na kammale ko? Dan dashi zan ɗaga" Insu tace tare da kallonta, juyowa inda take tayi da kulawa tare da faɗin "inba yanzu da ki ka yi magana ba ma na manta" damamaki ta kalleta tare da faɗin "Anty Lailah!" Dariya ta saki tare da faɗin "na'am" "kiji indadaɗi
abinda ki ke ma mutane ne aka miki" Farisat tace tare da balla mata harara, "to ke Insu yanzuduk danbun da ki ke ajiye da shi be ishe ki ba se kin ƙara neman wani kin ƙara!" Babiya tacedamamaki, "wanda ya rage ba yawa Hajiya, kuma jiya Yaya Sadam be bar roban da na fiddobasedaaka kakkɓe roban da shi" tace tare da kallon Sadam, "kiji tsoron Allah baby Insu!" Yace taredakallonta kame da haɓa, dariya suka saki cike da farin cikin ganin juna...
"To abar batun, yana nan na adana miki, ina ganin saƙon ki jiya na nema
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 65 Chapter of 109