Share this page
Allah kar ku manta mun da file ɗin nan" "oh Allah ba dadin kinyi magana ba ma da wallahi mun manta" tace tare da sakin murmushi, "ai na sani, wannankaɗanne daga halin ki" tace tare da katse kiran, saka wayan a jaka tayi fuska ɗauke da murmushi tashige ɗakin Babiya hannunta akan veil ɗin dake saman kanta tana gyara zaman shi.... "Hajiyan Allah mun fito" tace cike da kulawa, "tun yanzu zaku tafi?" Tace da mamaki tare damiƙewa zaune daga kishingiɗar da tayi, murmushi ta saki tare da faɗin "ta can suna ganinmunmakara ke kuma kina ganin mun yi wuri, se yaya kenan?" Ta idda maganan tare da kama haɓa, "wannan ai shashasha ce, ba ta ƙi ku sallaci assalatu a can ba, kar ku biye mata" Babiya tacetareda sakin murmushi, "ai rana ya ɗaga Hajiya, kuma dole ta ƙosa, tun da aka kaita fa ba wandayajea cikin su banda Farisat ita ma ba ta koma ba tun ranar da suka je ita da su Lailah" Habibadakeshirin komawa Dimau anjima tace tare da sakin murmushi, "to se kun dawo, ku gaishe sudakyau" Babiya tace da kulawa, "za su ji" tace tare da ƙarisawa kusa da Habiba.... Zama a kusa da ita tayi tare da faɗin "dan Allah Anty Habiba ki cewa Sha'awanatu ta yi munbitimis ɗin nan a turo mun, wallahi ina masifar san sha" ta idda maganan fuska a marairaice, kallonta Habiba tayi fuska yalwace da murmushi tare da faɗin "zan faɗa mata".... "Ke ma dai Habiba akwai ɗaurewa ƙarya ƙugun zama, yanzu in tayi ma wa ze kawo mata nanɗin?" Babiya tace tare da kallon Habiba, murmurshi ta saki tare da faɗin "zan dawo ganindoctora watan gobe kin manta ne?" "Anyi haka" tace cikin tunawa, "to ai shikenan, se ki taho matadashi, ita ka dake ta saka lallaci ta kasa iyawa har yau, inda ta maida hankali ta koya da yanzubatahucewa kanta takaici ba" Babiya tace tare da miƙewa ta fice, da murmushi Habiba ta bi ta, Insukuwa kwaɓe fuska tayi ta zuba ma Habiba ido, "yi haƙuri" tace cike da kulawa.... "Ammi mun gama shiryawa" Sahabee yace tare da kallon Insu, miƙewa tayi ta bi su da dubamecike da burgewa, dan ba ƙaramin kyau suka mata ba, "ku yi gaba ina fitowa" tace tare da juyadubanta ga Habiba, "Anty Habiba ina miki fatan sauka lafiya, zamu yi waya in kin isa" tacedakulawa tare da rungumarta, jinjina mata kai tayi ba yan ta zame jikinta a nata cike da ƙauna, "agaidamun uncle Hamidu da kyau" tace tare da juyawa ta fice da sauri, da murmushi me cikesatarin ƙauna ta bi ta.... "Baba Mari se mun dawo" tace da ƙarfi, "to a gaidata" Baba Mari dake kitchen tace da ƙarfi, "insha Allah" tace tare da ficewa da sauri, tana fita farfajiyan gidan ta taddasu tsai-tsaye a kusadamota da alamun fitowanta suke jira, murmushi ta saki tare da faɗin "ku shishshiga mana, Habibumu haɗe a ƙofar gidan Yaya Salman" jinina mata kai yayi da kulawa, ficewa tayi da sauri danamso ma Yasmin file ɗin da take ta magana a wajen Farisat.... "Dan Allah hanzarta" Salman yaca tare da saka ma Mairah takalmin da Farisat ta ajiye mai, "dukwannan saurin da nake my Jannah ba ka gani ba!" Tace kaman zata saki kuka, "na gani ƙarahimma" yace da kulawa, "me yace maka wai?" Tace tare da kallon shi, "be ɗauka yau mumazamu je ba, shine yace a temaka a ba wa su Nafisat Mairah su je da ita yayi kewanta" yacetaredaɗaga Mairah ya saɓa a kafaɗa, murmushi ta saki cike da jin daɗi tare da faɗin "ai can zamuwuni" "na faɗa mai" yace a natse... Tura ƙofan parlorn Insu tayi baki ɗauke da sallama, amsawa suka yi tare da bin ta da ido, "lafiyakuwa!" Tace tare da zube musu ido, "wannan kuma aike za'a tambaya" Farisat tace tare dasaɓajaka, "ki ce ina da sa'a file ɗin da ku ka yi magana da Yasmin na zo amsa" tace tare da zamaatwoseater's, zage jakan dake kafaɗanta tayi ta ciro ta miƙa mata tare da faɗin "kun fito ne?" "Eh" "yanzu mu kayi waya da Sadam yace muje ze biyo mu" jinjina mata kai tayi tare da faɗin"okaytamiƙe ta nufi ƙofa, tana fitowa ta tadda Habibu tsaye a bakin driving side murmushi ta sakinmai tare da faɗin "ban jima ba ko?" Murmushi ya saki tare da buɗe ƙofan ya shige a natse, ɓangarenme zaman banza ta buɗe ta shige, tana daidaita zama Nafisat ta jefo mata tambaya.... "Ba ta bada Mairahn ba?" Tace a natse, "zata ita ma" tace a natse tare da zaro wayanta dakeringing, "oh Allah Yasmin kar ki sheƙeni da kira mana" tace kaman zata saki kuka tare da ɗagakiran ta kara a kunni, "Yaya Salman yace yau suma za su zo, kin san anjima member's ɗinAminanjuna za su zo suma" "au yau ne zuwan na su!" Tace da mamaki, "eh baki ga sanarwan da YayaSagir yayi ba ne jiya a group?" "Ban shiga gidan ba ma kwata-kwata ina ga tun posting ɗinhotunan dinner da nayi" tace a natse, "aiko anjima da la'asar suka ce, kun taso ne?" "A'a sela'asarɗin mu ma" tace tare da sakin ƙaramar dariya ta katse kiran, "na san ta fara kuka yanzu haka" Nafisat tace tare da danne dariyarta.... A kusan tare suka isa gidan, tunda gateman ya taɓi ƙofan Yasmin da Shureimsuka fito a zumuɗe, sojojin dake ba je a gidan kuma suka zuba ido, ganin motan Hisham ne ya shigo ya sa jikinYasminsanyi, se dai fuskanta be ƙi bayyana farin cikin ganin shi da tayi ba, ko gama dai-daita parkingbe yi ba motan su Insu ya danno kai a natse, a guje tayi parking lot ɗin cikin ɗin bin zumuɗi, binbayanta Shureim yayi saboda hango motan Salman da ya shigo.... Yana ƙoƙarin riƙota Nafisat ta ɓalle murfin ɓangarenta ta fito, ihu suka saki a tare suka rungumejuna ƙaƙam, sakkowa su Sahabee suka yi a natse fuskoki cike da farin cikin ganinta.... "Zare belt ɗin jikinta tayi ta fito a natse, "wayyo Allah na baby Insu!" Tace tare da sakin Umar dasauri tayi inda Insu ke tsaye tana sakin mata murmushi, rumgumeta tayi ƙaƙamtare da sakinhawaye, "wayyo ƙirjina" Insu tace da ɗan ƙarfi, saurin sakinta tayi tare da fiddo ido waje.... Murmushi ta sakin mata tare da taɓan ƙirjin, "sorry!" Tace tare da goge hawaye, "Mommy!" Tacea zumuɗe ta yi inda Farisat ke tsaye tana sakin murmushi ta rumgumeta so tight tare da faɗin"zaku kashe ni da farin ciki yau" ƙaramar dariya Farisat ta saki tare da faɗin "a'a kar ki mutudanAllah" dariya ta saki me yalwa tare da janye jikinta ta nufi Salman, murmushi ya sakin matatareda faɗin "Amarya ƴar shagali" "ƴar biyan buƙata ƴar bidiri, kana ganin yanda uncle Shureimyafara ajiye tunbi saboda tsaban kula da ya samu" Insu tace tare da sakin ƙaramar dariya, murmushi suka saki tare da kallon Shureim da ke ta sakin murmushi, ba ƙarya kamya murje.... Miƙama Mairah hannu tayi da kulawa, da mamakin su ta miƙa mata nata, tana ɗaukanta talafeaƙirjinta, "lallai amarya ki ke kuwa abar san ganin kowa" Insu tace tare da amsan wayan daHisham ya miƙa mata, "lallai kin taki sa'a" Salman yace tare da sakin murmushi, "Ummantanefa, tayi kewanta ne" Farisat tace fuska yalwace da murmushi, "wannan kuma daga ina!" Insutacecike da mamaki tare da ɗago ido daga screen ɗin wayan ta sauke a fuskan Hisham, "yaunaga anyi posting ɗin" yace na shi idon a saman fuskanta, jinjina kai tayi ta miƙa mai wayan taredafaɗin "kar ka damu mutane ne baka da gadon su suna da na ka saboda tsaban rashin nayi" tayi maganan hankali kwance... Menene!" Farisat tace da kulawa, "hoton da muka yi ranar sister's and brother's day aka maidanama, se posting suke kowa kuma da abinda ze rubuta" Hisham yace cike da damuwa, "autoƙarya suka yi? In zaku ma fito ku faɗawa junanku gaskiya ku fito ku daina wani ƙunbiya-ƙunbiya"Farisat tace tare da banka mai harara... "Wai dan Allah meyasa mutane ku ke haka ne! Shikenan babu wani alaƙa ta shaƙuwa tsakaninmace da namiji se ta soyayya! Wallahi ba wannan ne a zukatan mu ba, mu ƴan uwa ne waƴandasuka shaƙu da juna" ya idda maganan tare da kafe Farisat dake banka mai harara da ido cikedagaskiyanshi, tsaki taja tare da faɗin "zaku yi bayani da turanci ne ma, in mafaɗin magana wawane majiyin shi ai da hankalin shi, wa zaku ma alaye? Inba son juna ku ke ba me ne ne na kiranjunan ku da sunan da ku ke yi?" Kama haɓa yayi tare da faɗin "ikon Allah menene a cikinsunan?Boyfriend da girlfriend ne ba wani abu ba, yanzu budurwata se in kirata da wannan sunan?Habama ai wallahi ba yanda ma za'ayi hakan ya faru, a yanda fassaran sunan ta zo a haka mukaɗauketa, boyfriend nufi boy yaro friend aboki, yaro aboki, ita kuma in ce mata yarinya ƙawa, shikenan fa Mommy dan Allah ku dinga fahimta.... Ya idda maganan tare da sakin murmushi idon shi akan ta, "se ka yi, zaku yi bayani ne, zangatainda budurwa ko saurayi ze amince da wannan shashancin na ku" tace cike da takaici "danAllahdaina son fahimtar da ita, ba fahimta za tayi ba, bayin Allah akwai masauki a ciki ko mu tattaramu koma inda muka fito?" Insu tace tare da kallon Yasmin da Shureim da ke bin su da murmushi, "muje ciki" Yasmin tace da sauri tare da nuna mata hanya, ba musu ta shige riƙe da hannunUmarda Sa'eed, dafa mata baya Nafisat da Sahabee da Hisham suka yi zukata ƙal, "muje Mommy" Yasmin tace tare da kallon Farisat dake magana da Salman, ba musu suka shige suka dafamusubaya.... Suna zama Yasmin ta miƙa ma Nafisat Mairah ta wuce kitchen, dafa mata baya Shureimyayi dasauri, shigan su Babu daɗewa suka fito hannaye riƙe da treyn da suka ciki da snacks da lemudaruwa, suna ajiyewa Insu ta saka hannu ta ɗau milk donuts ta kai baki tare da faɗin "wallahi shiyasa nake sha'awan zuwa gidan amare saboda irin waƴan nan abubuwan" murmushi Shureimya saki tare da zama kusa da Salman, "seki ƙoƙarta ke ma ki zama amarya kinga se ki yi tadannahankalin ki kwance" Farisat tace tare da kallon ta, ko kallon inda take ba tayi ba bare tayi tunanin samun amsa.... "Ina brother Sadam?" Shureim yace cike da kulawa, "yana tafe akwai wani shari'a da yakenazarta ne amma ba ze jima ba ze iso" Salman yace cike da kulawa, "to Allah ya temaka yabashi sa'a" yace da kulawa, "amen" yace cike da farin cikin addu'an.... "Mommy ki ci mana" Hisham yace tare da kallon Farisat, kama haɓa tayi tare da faɗin "ohni Farisat wai Hisham kana da matsala da ni ne?" "A'a" yace tare da danne dariyar shi, "ya yi makakyau, ka sanni farin sani ba baƙi ba, kuma kasan abinda zan iya aikata maka" "wallahi na sani, yaushe ki ke gida, zan kawo miki ƙanwar ki ta gaidaki" "wacce!" Tace tare da banka mai harara, "future wifey na mana" yace tare da kama haɓa, "wai ku da gaske ku ke!" Tace cike da mamaki, "wallahi da ƴar caras ɗina a gefe" yace tare da sakin dariya.... "Amma yaran nan kun ma kan ku" tace cike da takaici, dariya gaba ɗayansu suka saki bandaInsuda ta saki murmushi, "wallahi duk ɗaukana sun gyarota, ashe ni suka maida wata bi can" tacemurya ba daɗi, miƙewa Insu tayi ta tsiyaya ruwa a madai-daicin kofin dake gabanta ta miƙamatatare da zama kusa da ita, "sha ki sanyaya zuciya" tace tare da sakin mata murmushi, kaiwabaki tayi ta shanye duka ta ajiye cup ɗin, "ki daina yanke hukunci da abinda zuciya ta rayo miki Mommy ba ko wanne ke zama gaskiya ba" ta yi mata maganan cike da kulawa, murmushi Shureim ya saki tare da miƙewa cike da kula yace ma Salman da Hisham su tashi su nufi part ɗinshi, ba musu suka miƙe, miƙa ma Salman hannu Mairah tayi tare da shagwaɓe fuska.. "Ɗaukanta yayi ya wuce saɓe da ita a kafaɗa, suna ɓacewa ganin su Insu ta kalli Yasmintaredafaɗin "ɗau wannan treyn da ba mu taɓa ba ki bi su da shi" "a'a bari in zuba musu wani" tacetareda wuce wa kitchen, miƙewa Nafisat tayi da sauri ta tafi taya ta, murmushi Farisat ta saki taredafaɗin "Alhamdulillah, Yasmin ta samu natsuwa" murmushi Insu ta saki tare da jingina da jikinkujeran da take kai, ba su jima da zuwa ba Sadam ya iso, haka suka wuni cikin nishaɗi, bandakwasan shafta babu abinda suke, ko da rana tayi gaba ɗayan su suka shiga kitchen suka haɗalunch, haka suka zauna suka ci a tare zukata cike da farin ciki, suna sallahn la'asar Insu tafarashirya su Umar dan tafiya islamiyya.... "Baby Insu da kin bar su gobe sa je" Yasmin tace fuska a marairaice, girgiza mata kai tayi taredafaɗin "sun yi fashin hadda ba za su yi na islamiyya ba kar su yi biyu babu, gashi gab suke dafaraexams" tace da kulawa tare da taya Umar saka safa, "ko me zaki yi ba zata barsu ba, gundaki barta kawai" Farisat tace tare da kallon Yasmin, "to menene amfanin fashin? Tun ɗazu takeganinsu, sannan in sun zaunan me za su mata? Duk wani abinda ba su yi shi tun zuwan subayanzu ba yin shi zasu yi ba" tace a natse tare da miƙa ma Nafisat niƙab ɗinta, amsa tayi ta ɗauraanatse, ɗaga waya tayi ta danna number ta kara a kunni... Ana ɗagawa tace "ka kusa isowa Habibu?" Shirun daƙiƙu tayi tare da faɗin "to sannu" tayi maganan tare da sauke wayan, kallon su tayi tare da faɗin "kowa ya ɗau jakan shi yana bakingate" jinjina kai suka yi suka mimmiƙe, sallamansu suka yi cike da natsuwa suka fice a natse, "kara manta da addu'an hawa abin hawa da na fita gida" tace da ƙarfi, jinjina kai suka yi suka fice, "shikenan Nafisat Ɓadamayya zata koma yanzu!" Yasmin tace jiki a sanyaye... Murmushi Insu ta saki tare da faɗin "eh in sha Allah" "wayyo Allah wallahi ban so" tace kaman zata saki kuka, "to waya ce miki jiran jin ra'ayinki ake!" Farisat tace tare da kama haɓa, dariyaInsu ta saki tare da faɗin "ita da kanta ta zaɓi can, ko da yake makarantar ne tana da kyau, anakwasan tsagwaran ilimi, kinga wa ze hanata" tayi maganan a natse, "gidan Anty Lailah konaAnty Khadijatu zata zauna?" Tace a sanyaye, "ga babba me ze kaita gidan ƙarama" Farisat tacedakulawa.... "To Allah yasa hakan ya zame mata alheri damu da su baki ɗaya" tace a sanyaye, "amen, AntySalwa ma wai a bata Sa'eed ya shiga secondary a Kautal" Farisat tace cike da damuwa... Da mamaki suka bita da ido, cike da ɗin bin mamaki Insu tace "da yaushe aka yi hakan!" "Ranar da za ta tafi mana ta sa mijinta ya roƙi Yaya" tace cike da takaici, "se yace me!" Yasmin tacecikeda mamaki, "be dai nuna musu ze ba da ba be kuma nuna ba ze bada ba" tace tare da kallonsu, "hmm" Yasmin tace kaman zata saki kuka, "ba inda ze je" Insu tace tare da kauda kai, "Allahyasaamma ita ma banda neman magana ai ba rasa yara tayi ba, yara huɗu reras a gabanta tacewani a bata Sa'eed, ga uwar mijin nan nata me shegen sa ido, yanda ba ta son wani ya raɓi gidannanta ya Sa'eed ze sake yayi rayuwa a cikin gidan cikin aminci" Yasmin tace cike da damuwa.... "Ɗan ƴar uwarta mana, dalilin da yasa za ta so ɗaukan shi kenan, niyyarta me kyau ne, sedai bainda ze je, Anty ba ta taɓa ra'ayin raba ƴaƴanta ba, dan haka a haɗe za su cigaba da zama" Insutace tare da baza musu ido, "dan Allah ku bar ma wannan maganan, ba ta yanda ze bar Bertuwaya koma Kautal, ita ma ba dadin aure ba ya za'ayi ta koma can da rayuwa" Farisat tace taredalumshe ido.... "Allah yasa" Yasmin tace tare da miƙewa ta nufi ƙofan da aka danna ƙararrawan sanar da zuwanwani, tana buɗewa ta tadda ɗaya daga cikin sojojin dake gidan tsaye, kallon shi tayi da mamaki dan ba sa zuwa se da dalili, gaidata yayi a girmame tare da sanar mata da baƙin da suka iso, murmushi ta saki me faɗi tare da jinjina mai kai cike da farin ciki ta ba shi umurni su shigo, tanakai nan ta juya tare da sanar musu da isowan su Annur, mimmiƙewa suka yi cike da farinciki, kokafin su ƙarisa ƙofan matan sun fara shigowa, nan waje ya ɗau harama, "ina me house ɗin?" Zubair yace tare da kallon Yasmin fuska faɗaɗe da murmushi, "yana part ɗin shi tace taredawuce wa da sauri tayi part ɗin.... "Yaya Balarabe bismillah, dan ni kai kaɗai na gani" Insu tace tare da ƙarisawa kusa da shi tariƙohannun shi, "mu da baki gani ba ma baƙin zaman zamu yi ba" Rukayyah tace tare da bankamataharara, "oh zafi ki ka ji?" Insu tace tare da kallonta ta sakin murmushi, "me ze kai ni jin zafi abinda ba wuta ki ka faɗan mun ba" tace tare da kauda kai bayan ta banka mata harara.... "Daughter" Momcy tace tare da sakin ma Farisat murmurshi, "Momcy barkan ku da zuwa, ai dukna ruɗu ne" Farisat tace tare da sakin mata murmushi, "ai dama haka ki ke kamar tsohuwa" Laɗifa tace tare da sakin murmushi, "wallahi da shekarun Laɗifa, ai ba ta yau ba ce ni" tacetareda sakin murmushi, sallama Yasmin tayi su Shureim dafe a bayanta, nan aka buɗe babinhira, "Insu tashi ki kawo musu abin taɓawa" Farisat tace tare da kallon ta.... Kama haɓa Insu tayi tare da faɗin "tsakani da Allah duk wajen nan Insu kawai ki ka gani Mommy!" Dariya suka saki tare da kallon ta, "to ai duk ciki ke ce ƙarama" Zubair yace taredasakin murmushi"a'a brother wallahi da shekaruna, wani irin ƙarama kuma" tace da mamaki, "ehmana tunda tana da 22 ai ta girma" Farisat tace tare da banka mata harara, "22! Wa ɗinwai! Insun!" Khalid yace cike da mamaki, murmushi Farisat ta saki tare da faɗin "wallahi shekaruntakenan, ka ga manyance kamar ƴar 30 ko?" Tace fuska cike da murmushi, "wallahi sister, duk ɗaukana ta kai haka" yace cike da mamaki... "Kai ma dai Khalid wani irin 30" Momcy tace tare da kallon shi, wallahi sister Amina" yacedatsan-tsan gaskiyan shi, "ai kowa ya kalli Insu yasan yarinya ce, se dai banyi zaton 22 ba" Sagir yacetare da sakin dariya, "ta faɗa muku san ranta ne kawai" Insu tace tare da miƙewa tayi kitchen.... "Wallahi haka ke gare ki, Yaya Balarabe dan Allah shekarun Insu nawa ne?" Tace tare da kallonBalarabe, murmushi ya saki tare da faɗin "na manta" murmushi Yasmin ta saki tare da kaudakai, "to sister Yasmin fa!" Laɗifa tace tare da sakin dariyan zaro idon waje Yasmin tayi tare da narkema Shureim ido, murmushi ya saki tare da kauda fuska, "23 da wasu watanni, dan ba ta cika24ba, ta zaranta da Insu wata 20, lokacin da Anty ta rasu kuma Insu na da 16 Yasmin na da 18batagama cikawa ba ma, Sadam na da 20 ni ina da 22 yanzu da rasuwan Anty shekara Shida, kuƙirgamun" tace tare da gyara zama, "Allah ya gafarta mata, 22 kenan" Annur yace a natse, "lallai Insuashe ƙanwar ƙanwar mu ce, ta ɗau girman dole ta ɗaurawa kanta" Hafsat tace da mamaki.... "Au har yanzu naman nawa ku ke ci! To ku ɗau toothpick ku yi sakuce" tana kai nan ta ajiyemusuruwa da lemu da ta jero a trey ta koma ciki ta ɗakko snacks ta jera musu ta koma ciki a natse... Nan suka baje ciki tare da kwasan hira, cike da shaƙuwa, 6 na bugawa ta fito daga kitchenhannuriƙe da ƙaton trey ta nufi dining area, tashi Hisham yayi da sauri ya nufeta tare da fara temakamata.... Komawa ciki tayi ta kwaso sauran suka shirya dining ɗin tsaf, ɗaga kai tayi ta kalli inda suketareda faɗin "dinner ya kammala" da mamaki suka kalleta, ɗaga kafaɗa tayi tare da jan kujeratazauna a natse tare da zaran plate ta fara serving ɗin kanta, jan kujeran kusa da shi Hishamyayi ya zauna tare da faɗin "Meenat fa ta fiki shekaru" ɗago kai tayi ta banka mai harara, murmushi ya saki tare da mata alamun zuge baki da hannun shi, ƙwafa ta saki tare da maida kanta gaabincin da ta zuba, tasowa suka yi suka yo wajen a nannatse suka ja kujera suka zazzauna, janmaShureim kujera Yasmin tayi a natse murmushi ya sakin mata tare da zama ya ja mata na kusadashi zama tayi a natse ta zari plate ta fara zuba mai.... Tana gama zuba mai ta ajiye a gabanshi tare da mai alamun ya ci, jinjina kai yayi idon shi akanta, "dan Allah mun kusa tattarawa chairman a mana haƙurin mintoci" doctor Muwaddah tacetareda sakin dariya, maida duban shi gareta yayi tare da sakin murmushi, Yasmin kuwa saddakai tayi cike da nauyi, "ina ce ba ku gani ba" Farisat tace tare da kallon doctor Muwaddah, "haba Farisat mu kuma na yau ne?" Tace tare da sakin murmushi, kama haɓa Insu tayi tare da ɗago kai damamaki tace "to shine me? Ku ɗin baƙinsu ne? Yau na ga ikon Allah dan Allah uncle Shureimkalli matarka mallakin ka ne ba wanda ya isa taka maka burki, mutane se saka idon fitina kuwayasan abinda ku ke aikatawa, ku kalli juna ku ci da juna ku kula da juna, burgemu zakuyi, dama kun zo gidan amare me ku ke tsammanin gani, ai na su da sauƙi ke me magana ya kukeyi a gaban jama'a?" ta idda maganan tare da kallon Farisat... "Ina ce a gaban mu ku ke har kokin ku, wa ya taɓa ce muku kunyi abinda be dace ba" ta iddamaganan cike da takaici, "wai ai Mommy gama hawa ne, yanzu ne ma naga tayi sauƙi" Hishamyace tare da sakin dariya, "yanzu ɗin ma dan Allah ya haɗata da me taka burki ne, ka jira tahaihuka ga zabari, wallahi in kun san ido ma zaku zo ku saka mun kar ku zo gidana se na cika shekara, wataƙila a lokacin na ɗan ɗaga muku ƙafa, amma sati da biki ai idona ma ba gani zaku yi ba" Insutace cike da gaskiyanta.... "To dama daughter waya isa zuwa gidanki da wuri ki goge mai haddan dake kan shi ya samuyahaddace da ƙyar, ai ko za'a se an dawo" Momcy tace tare da sakin dariya, "wallahi Momcy kushazamanku nagode zamu yi ta gaisawa ta waya, in na ɗan kwana biyu kwazo" tace cike da gaskiyanta, "ni ma dai na kin zanyi, a gaskiya a jira a kwana biyu" Hisham yace tare da sakinmurmushi, "au kai ma haka ka ke Hisham?" Mardiyya tace tare da sakin murmushi, "ai yafi haka, waƴan nan da ki ka gani bakin su ɗaya" Farisat tace cike da takaici, dariya suka saki tare dakallon fuskanta.... "Insu Allah ya baki soja, dan ya mana maganin wannan bakin na ki da komai aka faɗa yanadaamsan bayarwa" Farida tace tare da sakin murmushi, "wallahi ba amen ba, ai auren soja ƙaddarace babba" tace tare da sakin murmushi, "ƙaddara!" Su Laɗifa suka ce da mamaki taredazube mata ido, zare ido tayi tare da baza musu na ta idon, tuno katoɓaran da tayi yasata sakinmurmushi tare da faɗin "oh Allah na tabo matan sojoji ba mazajen nake nufi ba, waƴan nansaƙagon da ake ajiyewa gida nake nufi, tsakani da Allah duk inda ka wulƙa ƙato tsaye da makami yana bin ka da ido" tace cike da gaskiyanta.... "To ai dan lafiyanki da na mijin ki aka ajiye su" matan Khalid tace tare da sakin murmushi, "wallah ban so, Allah ya hanani soja" tace da iya gaskiyanta, "to Allah ya baki likita shine mesanyi wataƙila ya jure halin ki" Hafsat tace idonta akan abincin da ke gabanta, "ai wannanɗansanda ne dai-dai da ita, kin san dama lawyer se police abokan juna ne" Sadamyace tare dasakinmurmushi, "haka zamu yi da kai Yaya Sadam! Na san inda zan ajiyeka" tace tare da kauda kai, murmushi Salman ya saki tare da faɗin "ku daina ma ƴar uwata jajibe-jajibe, in sha Allahjaruminjarumai zata aura wanda ze kula mun da ita da dukkanin ƙarfin shi" wani nagartaccen murmushi ta saki tare da faɗin "shiyasa nake masifar sanka, Allah ya baka ƙarfin gwiwan ƙara gida" tayi maganan tare da danne dariyan dake san kuɓuce mata.... "Akan ki" Farisat tace a harzuƙe, dariya ta saki me yalwa tare da kaucewa da sauri sabodabugunda ta kawo mata, saurin riƙo hannunta Salman yayi tare da faɗin "easy mana Kushi, ai gidanJannah da sunanki kaɗai a ka gina"

Chapter 64 of 109