Share this page
jawota ya birkitata tayi ƙasa, miƙa hannu yayi a hankali yakashe wutan ɗakin.... Murmushi ya saki tare da ajiye wayan cike da yaba karamcin su yace "ita ma kukan take ammatana cewa wasu kar su yi" goge hawaye Gude tayi tare da faɗin "na jita" tare da sakin murmushi me haɗe da tahowan hawaye, murmurshi ya saki tare da jinjina kai, "ina ga a sanarwa ƴanuwadaabokan arzuƙa su taya mu d addu'an" Gude tace a sanyaye, murmurshi ya saki tare da faɗin"yanzu kuma?" Harara ta dalla mai tare da faɗin "ina ce yanzu a gabanka Insu ta tabbatar mundain sha Allah ze dawo, sannan mu mai addu'a" "yi haƙuri, yanzu wa za ki sanarwa?" "Bari inkiraHajiya" "kina ganin yaran nan ba su faɗa ba?" "Bana jin, se dai ko in sun yi shiru dan jiraninfaɗamusu da kaina, amma na kwaɓesu" ta idda maganan a sanyaye, "ai ko kowa ya kwaɓu bandaHalima dan ba zata iya shiru ba" yayi maganan cike da takaici halin Haliman, murmushi tasaki tare da faɗin "bari in kira Abdussamad tukun, kai kuma ka kira ƴan uwanka, tana kai nantadanna number Yaya ta kara a kunni.... "What!" Yasmin dake kare da waya a kunni tace tare da tashi zumbur a mugun firgice, "heycalmdown" Sudais yace murya cike da murmushi, "kana ina ne?" Tace a rikice, "hospital" yace anatse, "gani nan zuwa" tace a hanzarce, "no kar ki zo, be riga da ya zo ba fa se nan da two weeks" yacetare da sakin dariya, sauke numfashi me ƙarfi tayi ta zauna daɓas tare da faɗin "dan Allahdagaske!" Ta jefa mai tanbayan hawaye na wanke fuskanta, "wallahi haka dai yace" "Allahyayarda, Allah ya amince, Allah ya so hakan, Allah ya nuna mana ranar" ta idda jero addu'o'in tare dasakin ƙayataccen murmushi me haɗe da zuwan hawaye, "Amin, ki natsu please" yace cikedakulawa, "wallahi ba zan iya ba, ji nake kaman yau ranar ta zo in ga Yaya Samir, Yaya Samir ɗinmu, me baby da baby Insu" ta idda maganan tare da sakin nagartaccen dariya cike da tuna shuɗaɗɗun shekaru, murmushi Sudais ya saki tare da faɗin "auh, baki manta ba kenan?"... "Ya za'ayi in manta, shi fa ya saka mana sunayen ko ka manta ne? Ni ce matarshi ta farkoInsutabiyu" dariya ya saki me sauti tare da faɗin "dake a garin gaba-gaba muke ba" dariyan da takeyi ne ya faɗaɗa tare da faɗin "Yaya Samir sarkin dariya, in maka na Hajiya tace "me kyautandariya""oh mu ba ma dariyar ko!" Yace tare da kama haɓa, murmushi ya saki tare da faɗin "kuna yi, amma Yaya Samir kankat ne, ni ban taɓa ganin fusatanshi ba, in fa muka yi lefi ya zo Anty taceyahukunta mu se ya tasa mu yayi ta murmushi" murmushi Sudais ya saki yana me tuna halayyanɗan uwan na shi, "wallahi be fushi, mutumin kirki na gari Allah ya dawo mana da shi cikinaminci, bari in sanarwa Farisat"... "Na kira ta tana amsa waya, tunda zaki kira kin hutashsheni" murmushi ta saki tare da faɗin"tona fasa gaskiya ka kira ta da kan ka" "haba baby" yace a marairaice, ƙitt ta katse kiran, murmushi ya saki tare da zaro wayan, yana shirin danna number Farisat aka fara ƙwaƙwasa ƙofan, zarewayan dake saman kunninta Gude dake magana da Suwaiba tayi tare da faɗin "bismillahkushigo" ba musu aka turo ƙofan, sallama ɗauke a saman laɓɓa Abdallah da Nafi'u suka shigo.... "Maraban ku, Abdallah ku ne da ƙwanƙwasa ƙofa kaman baƙi?" Gude tace tare da maida wayantaa kunni, murmurshi suka saki cike da kunya suka ƙarisa kusa da Sudais dake ta sakin murmushi suka zauna, "ka tahomun da saƙon nan?" Sudais yace tare da ba ma Nafi'u hannu, saka hannuaaljihu Abdallah yayi ta zaro bluetooth ya miƙa mai tare da faɗin "har mun kusa isowa na tunabanɗakko ba muka koma" "ka samawa kan ka kwanciyar hankali" Sudais yace tare da amsa fuskacike da murmushi, "yau ina masu jinyan?" Nafi'u yace da kulawa, "ba su daɗe da tafiya gidaba, Mommy tace su koma su yi dinner" "hakan da kyau, yanzu da zamu shigo muka haɗu da Doctor Hafiz, na ce mai ya riƙe mana kai ya samu zarya a saman titi" murmurshi Sudais ya saki idonshi akan shi, "se ya saki murmushi kasan ba ya gajiya da murmushi, wai in sha Allah a week ɗinnanza su sallameka" "Allah ya amince wallahi na gaji da zama waje gudan nan" yace cike da fata, dariya suka saki tare da gyara zama .... Amsan towel ɗin da take tsane gashinta yayi tare da cigaba da tsane mata, "meyasa ba zaki busar ba? Kaman ze fi" yace cike da kulawa tare da leƙa fuskanta, girgiza kai tayi tare da faɗin"ban cika soba, ko wanke kai nayi na fi son ya bushe da kan shi" "zaki iya mura fa" "se inshamagani" tace tare da sakin murmushi, murmushi ya saki tare da cigaba da tsane mata gashin, ban da sakin mai murmushi ba abinda take, yana gamawa ya ajiye tawel ɗin a gefe ya miƙar daita a hankali, bin ta da ido yayi cike da so da ƙauna, "oh Nafsii kaya" tace tare da marairaicefuska, murmurshi ya saki tare da jan hannunta a natse suka yi dressing room, ba su jima ba sukafitosanye take da wata haɗaɗɗiyar abaya wacce ta gaji da tsone, banda walwali da ɗaukan idobaabinda abayan ke yi, "nayi mamaki, yaushe aka kawo kayannan nan?" Tayi tambayan taredakallon shi "yau bayan fitan mu" yace tare da ɗago hannunta dake cikin na shi ya sumbata, "bari inɗakko wayana" tace idonta akan shi, jinjina mata kai yayi ta zare hannunta ta fice a natse, saukenumfashi a hankali yayi tare da lumshe ido, ana ganin tafiyanta za'a gane ba dai-dai yakeba.... Ba ta jima ba ta dawo hannuta riƙe da wayanta, ajiye turaren da yake fesawa yayi ya takoanatseya kama hannunta suka fice a natse, ɗago wayanta tayi ta danna number Farisat, ringingbiyutaɗaga, "Malama ƴar jarida ya ki ka wuni?" Tace cike da zakwaɗi, murmushi SSB ya saki taredakallon ta, "lafiya lau Insu baby ya gidan? Ya su Hajiya? Ina my Mairah da Umminta?" OhYaaRahim wannan tambayoyin duk ni zan amsa su ne?" Tace tare da sauke ƙafanta a cikin parlorn.... "Wallahi a gajiye nake ne shiyasa na haɗe miki su gu guda" tace tare da sakin hamma, "kinshigaoffice yau ne?" "A'a" tace tare da kare wani hamman, "ikon Allah bari in barki ki yi barci ki tashi tukun" tace tare da zama kusa da Fadila, "a'a yi magananki kai tsaye ina sauraranki, Dimaumukaje yau shiyasa gajiyan yayi yawa" "Dimau kuma! Yin me!" Tace cike da mamaki me haɗe datsoro, "Anty Gude ne" "kar ki ce mun cikin ya zube!" Tace cikin katsan hanzarinta, "to ya za'ayi?" Tacecike da jimantawa, "wallahi na so ta haifi cikin, ban ji daɗin ɓarin ba, Allah ya ba ta lafiya mealbarka, ya ba ta wani me albarka, ya sa zubewan cikin ya zame musu alheri ita da uncle Hamidu""amin ya Allah, ai ba wanda hakan ya wa daɗi" tace cike da jimantawa, "se Hajiyar Allah" Sadamyace da ƙarfi, zare ido Babiya tayi tare da riƙe baki, dariya suka saki gaba ɗayansu.... "Tsakani da Allah Sadam ba ka kyauta mun ba, ni na bata cikin da zaka ce ina mata baƙinciki, yanzu se ka saka Insu ta fara jeromun zance dan kasan ta sa rai, ni dai na ce be kamata tayi ciki awannan shekaru na ta ba, ban ƙara da komai ba, ban kuma rage ko A ba" murmushi Insudakejiyota ta saki tare da faɗin "to Allah dai ya ba ta lafiya" "amin, ga Kantun Ghana da Bitimis ɗindaki ka ce Shafa'atu ta miki nan mun taho da shi" "har ta yi!" Tace cike da mamaki, "wallahi tayi kuma ba kaɗan ba da ɗan yawan shi, nacesu bani tunda zamu kai amar-amar Hasinat se in kai miki, "bikin ya taso ne?" "Eh nan da twoweeks dai suka ce" tace tare da gyara zama, "ma sha Allah, Allah yasa a ƙulla alheri, Anty Hasinatza'a zama manya" ta idda maganan tare da sakin dariya.... "Sannu to, wato ke kowa ma baki bari ba ko" "wallahi na so ganin fuskanta ranar tahowa ingayanda ze koma" "ai zamu ganin miki, kuma ze zo ya taddaki" "zan kira su in taya murna" "hakanya kamata" tace tare da kare hamma, "oh kin ga da ki ka yi maganan two weeks, se na tunadalilin kiran da na miki, da gaske ne Yaya Samir ze dawo!".... "Wallahi yanda ki ja ji mu mu haka muka ji, ni Halima ma ta fara tseguntamun, kin san taredaitada Anty Gude muka je can, "Allah ya yarda ya kuɓuto da shi cikin aminci" "Amin ya AllahyaUncle!" "Yana lafiya akwai maganan da nake so mu yi in ki na cikin natsuwa" "to in keɓene?" Tacetare da yunƙurin miƙewa, saurin dakatar da ita tayi da faɗin "a'a ba damuwa ki yi zamanki, natsuwanki kawai nake buƙata... Komawa tayi ta zauna tare da faɗin "to ina tare dake" "yawwa akan maganar iƙilima ne AntynSa'adatu" "eh ina jinki, amma dan Allah daina dangantata da wannan walaƙantacciyar" tayi maganan cike da takaicin sauraran sunan da tayi, murmushi ta saki tare da faɗin "to Anty Farisat" "meya faru?" Tace cike da ƙaguwa, gyara zama tayi tare da rattafo mata komai, "tsayawai ki na nufin uncle Jamil na Ɓadamayya dai ɗan uwan Uncle!" Tayi maganan murya na rawacike da son tabbatar da abinda ta ji, jinjina kai Insu dake sakin murmushi tayi idonta akanMairahdake ta wasa da sajen SSB dake magana da Yasmin a natse... "Kin yi shiru!" Tace cike da ƙaguwa, "shi ki samu ko gobe ne ki je ki yi maganan da ita, intaamince se su Yaya su je wajen iyayensu su tambayi auren kawai ba abinda za'a ɓata lokaci bane""wani gobe yanzu zani, wanna batun ba na tsayawa jira ba ne" tace tare da miƙewa zumbur tafara laliban inda ta ajiye hijab da car key, dariya Insu ta saki tare da faɗin "bakya bari se gobeba?" "A bari ya huce shi kan kawo raban wani, daina zancen a jira Insu" ta idda maganantaredazare wayan ta katse kiran ta ajiye ta cigaba da neman abinda take nema.... Dariya Insu ta saki tare da zaro wayan ta ajiye a gefenta, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin"wato kin biyewa Jamilu ko?" Murmushi ta saki tare da faɗin "dama na daɗe da lura gidanshi nabuƙatanka gyara, tunda ya lura da kan shi yanzu har ya nemi temako zamu tsaya kai da fataharse gidan ya gyattu" dariya Lubabatu ta saki tare da faɗin "to a maida hankali wajen samokayangyara dan kar a koma gidan jiya" "ina da tabbaci akan se ya ji daɗin yanda gidan shi ze koma, godiya da fatan alheri ba ze daina mun ba har nan da shekaru goma ma su zuwa" dariya Kamil yasaki tare da faɗin "wannan haka ne" murmushi ta saki tare da faɗin "yaushe ka shigo uncleKamil!" "Kina amsa waya" yace fuska cike da murmushi, "to ku mu yi hoɓɓasa an fara kiran sallah" Hajiya tace tare da miƙewa.... Miƙewa tayi a natse tare da faɗin "Mahmah zamu yi magana bari in gabatar da farali" murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "ki haɗa da nafila" murmushi ta saki tare da takawa inda SSBketsaye rungume da Mairah, "amsheta" yace a hankali, miƙa hannu tayi a natse idonta akanMairah, maƙalƙale shi tayi tare da ɓoye fuskanta a kafaɗan shi, murmushi ya saki idon shi akan Insudatafiddo ido ta saki baki cike da mamaki, ɗago kanta yayi tare da faɗin "jeki wajen Ammi" kwaɓefuska tayi cike da taɓara, "ke zonan!" Insu tace fuska a ɗaure, narai-narai tayi da fuska taredakallon SSB dake sakin murmushi, shafa kanta yayi tare da faɗin "jeki" ba musu ta kama hannunInsu kaman zata tsala ihu, wuce wa tayi tare da faɗin "zaki gane ne da neman zance da ki keyi" murmushi ya saki tare da girgiza kai ya juya ya fice shi da Kamil dake ta sakin murmushi.... Da sauri ta wuce ɗakinta na gidan tuna a can ta ajiye hijabin a saman gado lokacin da ta jefitsari, ɗauka tayi a hanzarce ta zura ta fito, "ina Sadam!" Tace a rikice idonta akan Babiya dake bintadaido, "wai lafiyanki kuwa Farisat! Meya faru ne!" Jummai tace cike da mamaki, "lafiya lauwallahi se alheri, key ɗin motanshi ze ban inje in dawo banga nawa ba" "yana nan a kujeran da ki kazauna, duba gefen kujeran dan na ganshi a hannun ki ɗazu" Suwaiba tace idonta akanta, babumusu ta zura hannu, akan shi ta sauke, nagartaccen murmushi ta saki tare da faɗin "na ganshi Hajiya bari inje in dawo ba zan daɗe ba" tayi maganan tare da nufar ƙofa.... "A'a kar mu yi haka dake Farisat, zo faɗa min inda ki ka nufa" Babiya tace tare da yafuto ta, murmushi ta saki me faɗi tare da faɗin "abin alheri ne ke shirin faruwa Hajiya, da Insu na yi wayayanzu" "eh" Babiya tace tare da tatttaro natsuwarta, "ina uncle Jamil Yayan Uncle?" "Na ganeshi" tace a ƙage, "shine yace a tambayo mishi amincewan iƙilima inta amince se su Yaya sutambayo ayi auren a kaita can" ta idda maganan cike da farin ciki, sakin baki Babiya tayi hannuriƙe da haɓa, "ma sha Allah kai wannan labari shi ake badawa, amma na ji ma wannan yarinyadaɗi, Allah yasa ta amince" Jummai tace cike da jin daɗi.... "Ai dole Jummai tun yaushe ake jiran zuwan mijin be zo ba, amma dama ya santa ne?" Suwaibatace idonta akan Farisat da ta ƙosa ta tafi, "a'a Insu ne ta haɗa abun" ta idda maganan taredajuyawa, "ke jirani ƴan nan muje tare dan ta fi ɗaukan maganan da mahimmanci, ko ya santakokarya santa in Allah yace matar shi ce se anyi, Allah dai ya ma wannan ƴa albarka da ta haɗawannan abu, da yaran nan nake kwana da su nake tashi, duk da ance ita ƙaramar ta samumiji amma wallahi suna raina" ta idda maganan tare da zura hijabinta dake kusa da ita ta fice, binsuda ido kawai suka yi cike da farin cikin labarin da Farisat ta ba su.... A ƙofar gidan Farisat dake jin tamkar ta zama tsuntsuwa dan ƙosawa ta taka burki, sakkowasukayi a natse kaman babu wani abu dake azalzalan zuciyansu, kai tsaye gidan suka dumfara, dasallama ɗauke a baki suka shiga, amsawa Sadiya dake tuƙa tuwo tayi cike da tsan-tsan farinciki tare da faɗin "Anty Iƙilima" da ƙarfi, da sauri Iƙilima da shiganta ɗakin kenan bayan ɗauraalwalada tayi ta fito, ganin Farisat da Babiya ya sa fuskanta washe da farin ciki, da sauri tayi indasukecike da ladabi ta ma Babiya sannu da zuwa ta riƙo hannun Farisat, "ku mu shiga ciki" tacecikedajin daɗin ganinsu, "a'a ba mu buta mu ɗaura alwala tukun tunda an fara kiraye-kirayen sallahn" Babiya tace fuska cike da murmushi.... Ba musu ta wuce inda butocin gidan suke ta ɗakko biyu ta wuce ɗaki flaks ɗinsu da suke zubaruwan zafi ta ɗakko ta tsiyaya musu ruwan ta sirka ta ajiye musu, "Hajiya ga fitilla ko zaki kamaruwa" Sadiya tace cike da girmamawa tare da miƙa ma Babiya touch light, murmushi ta saki cikeda yaba ladabi da karamcinsu ta amsa ta wuce bayin, kallon Farisat Iƙilima tayi tare da faɗin"Akwai bayi a ɗakin Baba muje in buɗe miki ki shiga" "a'a ba zan kama ruwa ba" tace tare daduƙawa ta fara alwala.... Suna idarwa Sadiya ta kawo musu tuwon da tayi saurin kwashewa, "a'a Sadiya ba'a dafa damuba taya za'a ci damu?" Babiya tace cike da dattako, murmushi Iƙilima ta saki tare da faɗin "darabonku ne Hajiya shiyasa Allah ya turo mana ku" murmushi ta saki tare da faɗin "to saka kaɗan" bamusu ta jawo plate ta buɗe miya, "wow gatsika ne!" Farisat tace tare da kallon ta, murmushi tasaki tare da faɗin "ke ma kina son shi kenan?" "Sosai kuwa, ai ni da gatsika akwai amana" tacetare da gyara zama, murmushi suka saki tare da bin su da ido, "to ku saka hannu mu ci taremusamu lada da albarkan juna" Babiya tace tare da gyara zama, nan suka wanke hannu sukafaraci a natse.... "Iƙilima zo zauna akwai abinda ke tafe damu" Babiya tace ganin Iƙilima na shirin ficewa dagaɗakin, dawowa tayi ta zauna a natse ƙirjinta na bugu da ƙarfi dan tunda ta gansu take dannefargaban dalilin da ya kawo su a lokacin, murmushi Farisat da ta lura da canjin yanayin tasaki tare da faɗin "kwantar da hankalin ki" murmushi ta saki tare da jinjina kai, sallama Sadiyadatafita da kwanonin da suka yi amfani da shi tayi ta zauna kusa da Iƙilima cike da mamakinabindaya sanyayata haka, "to Farisat yi musu bayani" Babiya tace tare da kallon Farisat, murmushi tasaki tare da faɗin "Hajiya ai wuƙa da nama na hannunki" murmushi ta saki tare da gyara zamatafara rattafo bayanai.... Tunda ta fiddo dalilin zuwan Iƙilima da Sadiya suka yi suman zaune tare da bin ta da idondakeshatata da ruwan hawaye, ba su daina kallonta ba se da ta dasa aya, sauke wani naunayanajiyanzuciya suka yi tare da kallon juna suka fashe da kuka a tare, "ah ah haba mana abin farinciki neai, ba na kuka ba" Babiya tace cike da tausayin su, "wani farin cikin be gamsarwa se an zubdahawaye Hajiya" Sadiya tace cikin rishin kuka, jinjina kai Farisat dake sharan hawaye tayi cikedagazgata ta.... Ba wanda ya kuma ƙoƙarin hanasu barin su suka yi suka sha suka ƙoshi kafin Babiya tace"Iƙilimame ki ka ce game da batun?" Yaro dai yana da mata ɗaya da yara uku ko Farisat?" "Biyu ne Hajiya" Farisat tace a natse, goge hawaye Iƙilima tayi cikin dishashshiyar murya tace "dukabindaki ka ce Hajiya" "a'a Iƙilima, wannan ana son jin ra'ayinki me, zama ne na har abada, mutuwamuke fata ya raba, ba ni ko Farisat ko Insu za mu zauna miki dashi ba" jinjina kai tayi tare dafaɗin "Hajiya ki na da daman yanke ko wani irin hukunci a rayuwata, wallahi na amince dukabinda ki ka yanke zan bi, uwa ki ke a gareni, sannan iyaye suke da haƙƙin nema ma ɗiyoyinsumazajen farko" wani nagartaccen murmushi Hajiya ta saki cike da jin daɗin kalaman Iƙilimantare da faɗin "to na zaɓan miki shi Iƙilima na tabbatar da ze riƙe ki amana ya riƙe maraicinki" hawayen dake zubo mata ta goge tare da faɗin "nagode Hajiya, Allah ya saka da alheri ya ƙarawazuri'a albarka, kutsowanku rayuwarmu kun haifar mana da abubuwan farin ciki marasa adadi, wanda baki ba ze iya furta yawan su ba, ƙwaƙwalwa ba zata iya ƙiyasta wa ba, muna fatanalheri a gare ku ko da yaushe dan ba mu da abin saka mu ku yanzu da nan gaba" murmushi sukasaki idon su dake tsiyayan hawaye akanta.... Gyara murya Farisat tayi tare da faɗin "a yanda Insu tace abin ba ze ɗauki lokaci ba, ba musankokin shiryawa hakan ba?" "Ta shirya" Sadiya tace a zumuɗe, kallonta Iƙilima tayi da mamaki, "daina kallona haka, ta shirya Farisat, ko yau ne, akwai ƙannin Baba da zan baku number suyanzu duk wanda aka samu kira a ciki yayi, se a tura su yi magana da su" "hakan yayi sosai damayanzu nake maganan ko za'a kira mana Kabiru" "be garin ya tafi Yarban ɗazu, Yaya Salisunekenan" "to shikekan in sha Allah su Abdussamad za su je dan zantawa da su" "Allah ya yardaHajiya" tace cike da farin ciki.... "Ina ganin ko za'a yi maganan bikin a jira ayi na Sadiya tukun kaman ze fi" Iƙilima tace a natse, "eh to kina da gaskiya a nan" Babiya tace cike da yaba sanin yakamatan ta da ƙaunarta gaƴar uwanta, "akan me! Kin san tun yaushe nake addu'an ganin wannan lokacin kuwa! Ke ma kinsansaboda me yasa na ƙi bayyanawa duniya Abdullmalik duk da irin ɗin bin ƙaunar da yake nunamun, dan jiran wannan lokacin ne, sannan ya zo ki ce wani a dakata, ba za'a dakata ba, zankai ki ɗakin mijinki da hannuna zan bawa mijinki amanar ki" ta idda maganan cike da damuwa, murmushi Babiya ta saki tare da faɗin "Sadiya ai ba wani abu ba ne, tunda akwai maneminaƙasa" "a'a Hajiya dan Allah kar ku biye mata, dan Allah aje a nemi auren, Abdullmalik gini yakekuma iyayenshi sun ce se ya kammala ze yi aure" "auh to ai shikenan ke Iƙilima ki yi haƙuri, inAllah ya kai mu lokacin da ya kammala shiryawa se ki zo bikin cikin mutumcin ki" "Hajiya bazaniya samun natsuwa ba matuƙar na barta a gidan nan ita kaɗai" tayi maganan cike da gaskiyanta, "ba ni kaɗai ba ne da su Yaya Salisu" Sadiya tace cikin taren numfashinta, girgiza kai Iƙilimatayi tare da kallon Farisat, murmushi ta saki tare da buɗe baki da niyyan magana, muryan Hariradaya riga yi na ta ya taka mata burki "muna maraba da ita a gidan mu" kallon bakin ƙofar sukayi dasauri cike da mamaki, murmushi ta saki tare da takowa ta shigo, zama tayi kusa da Sadiyataajiye kwanonin hannunta tare da faɗin "Anty Iƙilima in dai wannan ne matsalarki ba ki damatsala, muna maraba da Sadiya a gidan mu, har ranar da Allah ze kawo ranar na ta, HajiyaAllahya saka muku da alheri, tun ɗazu na shigo jin maganan da ku ke yi ne ya ja hankalina banƙarisociki ba" murmushi Babiya ta saki tare da faɗin "ina ganin komai ya ƙare yanzu kam, Farisat yunƙura mu wuce, in sha Allah zan zo mu zanta da iyayenki akan batun" jinjina kai Harira tayi cike da jin daɗi, miƙewa Farisat tayi fuska cike da murmushi, "am Farisat dan Allah kira manaInsu mu yi mata godiya" Sadiya tace cike da farin ciki, murmushi ta saki ta ɗago wayanta dakeriƙe a hannunta ta lalibi number Insu ta danna kira ta saka a speaker.. Ringing biyu Insu da ta fito daga ɗakinta saɓe da Mairah da ta shiryata cikin doguwar rigamekyawun gani ta ɗaga tare da faɗin "Malama ƴar jarida ba har kin je ba?" Murmushi Sadiyadataamshi wayan ta saki tare da faɗin "aiko ta zo ta isar mana da saƙo me ɗin bin daɗi" murmushi Insu ta saki tare da fara taka stairs, cike da yanayinta tace "Saady baby irin wannan zumuɗi hakakamar ance yau ne abun?" "Ai shima ze zon kamar yau ɗin Insu in sha Allah, Allah ya sakamiki daalheri, ya baki miji na gari, ya albarkaci zuri'arki, ya jiƙan Anty yasa tana kyakykyawan makoma" murmushi ta saki cike da jin daɗi tare da faɗin "amin Sadiya ai yiwa kaine" "haka ne Insumunagodiya, Allah ya duba gabanki da bayanki" "amin Saady ina amarya me jiran gadon?" "Gata" tacetare da miƙa ma Iƙilima, amsa tayi a natse tana buɗe baki kuka ya ƙwace mata, "oh Allahkukakuma Anty amarya!" Tace tare da saka ƙafarta a cikin parlor inda su Alhaji Jamil ke cike fal.... Riƙo hannunta Farisat tayi suka nufi ƙofa, dafamata baya suka yi a natse cike da farin ciki, "please daina mana kar ki sani ni ma inyi, ga Mairah nan ma ta fara narke fuska" ta idda maganancike da yanayinta, share hawaye tayi tare da faɗin "kuna tare ne?" "Eh" tace a natse tare daƙoƙarin zama, "ke dama muke jira mu wuce can" Yasmin tace tare da riƙe hannunta suka nufi dining area fuska cike da murmushi, "Insu ba na da bakin gode miki, se dai zan cigaba da addu'anAllah ya dawwamar da farin ciki a rayuwarki har abada" murmushi ta saki tare da jan ma SSBdaya iso wajen kujera, zama yayi idon shi akan ta tare da jan mata na kusa da shi ta zauna a natse, amsan Mairah yayi a natse ta kare wayan da kunninta ta zari plate dan zuba mishi abinci, "nagode Anty amarya in sha Allah duk yanda ake ciki zamu yi waya" "to" tace tare da miƙamaFarisat da ke ƙoƙarin rufe murfin ƙofan da ta buɗe ma Babiya ta shiga, amsa tayi ta zagayo ɓangaren driving ta shige tare da kallon su cike da kula tace "zan shigo gobe, in ban samudamaba kuma jibi, Sadiya ki turo mun da number's ɗin nan kar ki manta" jinjina kai suka yi taredaƙaramusu godiya suka sallame su suka ɗau hanya.... Ɗaukan wayan dake jikin Farisat Babiya tayi dan jin kaya-kayan da Insun ke yi tare da faɗin"ki najina Insu?" "Eh" tace a dai-dai lokacin da ta ajiye ma SSB abinci a gaban shi, "a gaskiya yarannansun yi farin ciki, sun ji daɗi, Allah shi kaɗai yasan ladan da ze baki akan wannan jahadi da ki kayi"murmushi ta saki tare da faɗin "ai har da ku a jahadin Hajiya, Allah ya

Chapter 85 of 109