samu dawowa ba, ya ajiye kuɗi a saman gadon shi ki kawarmai" "okay to, su Yaya Ali fa?" "Ban sani ba ko za su dawo ta nan, amma Baban su Sudais yawucegida shi da Sudais da abokan shin nan" "okay shikenan" tace tare da zare wayan ta katse kiran, "har sun tashi" tace tare da kallon su, "ma sha Allah, Allah ya kai shi lafiya, ai lokacin da akacejirgin ze tashi ya yi" Habiba tace tare da kallon Farisat, "yanzu wai can American ze wuce kai
tsaye?" Suwaiba tace tare da kallon Farisat.... Murmushi ta saki tare da faɗin a Ɓadamayya ze sauka akwai wanda ze ɗauka a can sannansuwuce" tayi maganan tare da miƙewa tayi ɗakin Sadam, miƙewa Yasmin tayi tare da faɗin"zanwuce Hajiya se mun yi waya" "oh aiki zaki je ko?" Suwaiba tace tare da kallon ta, "eh" tacetaredagyara zaman hijabin jikinta, "hanzarta Allah ya ba da sa'a" Babiya tace cike da kulawa....
"Temaka ki cinye wannan ƙawar kirki" Harira tace tare da kai ma Sa'adatu shinkafa da miyandata ciko a cokali, yamutsa fuska tayi tare da faɗin, "kayya ƙawa na ƙoshi wallahi" "yi haƙuri ki ci, daga wannan ba zan ƙara ba" "ahaf se ka ce ban sanki ba ƙawa" tace tare da taɓe baki ta amsa, shigowa Sadiya tayi riƙe da waya a hannunta, murmushi ta saki tare da faɗin "kinga mutuniyar
ko" tayi maganan tare da saita cameran wayan a gefen Sa'adatu, "meye haka ƙawa! Ba fa ki dakirki" tace tare da sakin dariya me sauti, murmushi ta saki tare da faɗin "Anty na ce ke sanganinki" "auh to, wai yaushe Abdull yace miki ze dawo ne?" Ta idda maganan tare da kafetadaido....
"Saura sati biyu ba na faɗamiki ba ranar?" "haka fa! Wallahi na sha'afa ne kar ki ga lefina ƙawanaƙosa ya dawo inga yanda ya koma ne" murmushi ta saki tare da faɗin "na sani ƙawa, ai kinyi maƙoƙari ni ban iyawa" tace tare da juyawa ta fice.... Murmushi Iƙilima ta saki tare da faɗin "da alama ƙawarki ta yi lafiya sosai, kinji murya cakwai" dariya ta saki tare da faɗin "ba lefi kam, amma idan abun ya motsa tayi ta bige-bige kenantanakiran sunan Abdull mijinta Angonta" "wai shi Abdull ɗin har yau ba'a same shi ba ne?" "Towayasan shi ma!" Tace cike da takaici, "kai jama'a, yanzu me doctorn tace akan wan can matsalar?"
"Abinda ki ka saba ji mana, in sha Allah a hankali zata dawo dai-dai" "to Allah ya tabbatar" "amin, ina Abba?" "Ga shi yanzu shigowan shi daga school ya cire uniform ya fito" tace tare da kallonSa'eed dake sakin murmushi, "ki ce maza sun shawo yunwa?" Tace tare da sakin murmushi, "aikuwa dai se kin ga yanda idon ya fiffito" murmushi ta saki tare da faɗin "to a ji da shi seanjimain na kira" "okay ki gaida Mama dan Allah" "za ta ji in sha Allah" tace tare da ciro wayantakatsekiran ta juya dan komawa ciki....
"Anty Sadiya na gaisheka" tace tare da kallon Sa'eed dake zaune saman kujera one seater, murmushi ya saki tare da faɗin "ina amsawa ya jikin Anty Sa'adatun?" "Da sauƙi baka ji ta ba
ma?" Murmushi ya saki tare da faɗin "na ji" "to taso ka ci abinci kar su yi ta jiranka, lokacinislamiyya ya kusa" ba musu ya miƙe ya nufeta kasantuwar tana gefen dining table, jan mai kujeratayi ya zauna fuska yalwace da murmushi, cike da kulawa ta fara zuba mai.... Yana cikin ci Intisar da Hafiza suka shigo cikin shirin tafiya islamiyya, da mamaki ta kallesutareda faɗin "duk saurin nan da nayi!" Murmushi suka sakin mata tare da iddasa shiga, "har kunyi
lunch!" Tace cike da mamaki, jinjina mata kai suka yi fuskoki yalwace da murmushi, kallomecikeda tuhuma ta musu tare da faɗin "anya Anty Hafiza?" Murmushi ta saki tare da sadda kai, "kuwuto nan" tace cike da sanin yakamata, ba musu suka miƙe suka nufi dining area, suna zamatazuba musu abinci cike da kulawa ta fara jan su da hira, haka suka ci suka yi ƙat sannan sukatattara suka tafi islamiyya.... A zafafe yake tafe kamar wanda ke gudun jirgi ya tashi ya bar shi, banda murmushi SSGdaIbrahim dake dafe dashi a baya ba abinda suke saki, da sallama a baki ya afka parlorn, amsawaA'isha da Kausar da ba su daɗe da zuwa ba suka yi tare da bin shi da ido cike da mamaki, waige-waige ya fara cike da ɗoki, murmushi Yasmin da ta fito daga ɓangaren kitchen ta saki taredabinshi da ido, "ina take!" Yace cike da zumuɗi tare da nufarta, "gani!" Insu da ta fito daga kitchenriƙe da plate ɗin dake ɗauke da gasashshen nama tace tare da nufo shi gadan-gadan, nufartayayi shima a hanzarce fuska cike da murmushi suna haɗuwa ya ɗauketa yayi sama da ita yafarajuyi da ita, saurin ƙarisawa inda suke Yasmin tayi ta amshi plate ɗin fuska cike da murmushi tajagefe, sauketa yayi tare da saka hannun shi biyu ya kamo fuskanta, ganin yanda yake binfuskantada ido ya sa ta mai alamun menene!, Nagartaccen murmushi ya saki tare da faɗin "ɗan uwanki
yayi free!" Fiddo ido waje tayi ta kafe shi da su cike da shock, jinjina mata kai yayi fuska cikedamurmushi, wani ihun farin ciki ta saki tare da ɗane shi a zumuɗe ta ƙanƙame shi tare da sakinƙaƙƙarfan kuka, murmushi ya saki tare da saka hannun shi gaba ɗaya ya rungumota....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Sixty
Murmushi ta saki idanta akan Hajiya dake tsaye gefenta, murmushi ta sakin mata tare da faɗin"to Allah ya tsare hanya ya kai ku lafiya ya dawo daku lafiya, ki gaida mana da shi da kyau" "aminHajiya, in sha Allah ze ji" tace tare da kai jiki a natse ta rumgumeta, shafa bayanta tayi cikedasoda ƙauna kafin ta saketa, "to hanzarta" Kamil da ya iso wajen saɓe da Mairah a kafaɗa yacetareda sakin murmushi.... Zare jiki daga jikin Hajiya tayi ta rungume Yasmin, "Mahmah har na fara kewa" murmushi tasaki
tare da faɗin "ko za'a fasa tafiyan ne?" Fiddo ido waje tayi tare da zare jikinta da sauri, dariyatasaki tare da faɗin "kewa fa ki ka fara" "eh amma Mahmah ba maganan fasa tafiya" tace taredarungumo Fadila da Nabila, murmushi suka saki tare da rungumeta, sakin su tayi ta rungumeAnisa da idanta yayi ƙwal-ƙwal, "Aniy baby banda kuka, Anty Nafisat ɗinki na nan anjima kaɗanzata dawo" tayi maganan tare da shafa kanta, jinjina kai tayi tare da sakin hawayen da ya cikamata ido, "muje" Kamil yace tare da kallon agogo, jinjina kai tayi ta ƙara sallaman su ta nufeshi....
"Ga shi" Lawiza da ta iso wajen a guje tace tare da miƙa mata ledan dake ta zuba ƙamshi, tsayawa tayi fuska cike da murmushi har ta iso, miƙa mata tayi cike da kulawa tare da faɗin"Allah ya tsare hanya" "amin Anty Lawiza a kulamin da takwara" murmushi ta sakin mata taredajinjina mata kai, juyawa tayi ta wuce da sauri, tana isa bakin ƙofan motan security ya buɗemata, shiga tayi a natse fuska cike da murmushi, murmushi SSB dake zaune ya saki idan shi akantatare da riƙo hannunta, rufe motan yayi da sauri yayi motan su, shiga gaba mazaunin me zamanbanza Kamil yayi, a natse drivern ya ja suka bar wajen, fuskoki cike da murmushi su Hajiyasukabisu har suka ɓacewa ganin su suna masu musu fatan sauka lafiya.... Kai tsaye airport suka nufa, suna isa security's da guard's suka fiffito suka tsare duk inda
yakamata, sauka driver da Kamil suka yi dan ba su waje, kallon shi tayi tare da zuba mai ido,
murmushi ya saki tare da jawota a natse ta faɗa ƙirjin shi, ƙoƙarin ɗagowa tayi yayi saurinmaidata tare da faɗin "um-um, saurari kalamanta tukun" murmushi ta saki tare da kai kunnintasaitin zuciyar shi tayi shiru kaman me sauraran wani abu, se da ta kusan five minute's a hakasannan ta ɗago a hankali ta zuba mai ido... Ganin yanda yake bin ta da ido shima ya sa ta kai laɓɓanta saman na shi ta sakin mai sumbameɗauke da rikitattun bayanai, ɗagowa tayi tare da kai hannunta gefen kumatun shi na damacikeda yanayi na jan hankali tace "nan kusa, Gorgeous ba zata iya nisa da Nafsii ba" murmushi yasaki
tare da kai na shi laɓɓanta kan nata a natse ya, ɗagowa yayi ya sumbaci goshinta cike da kewa, "ina jira" yace a hankali, murmushi ta saki tare da kai kanta saman kafaɗanshi, murmushi yasaki
tare da faɗin "ke suke jira" ɗago kai tayi ta kalli farfajiyan wajen, hango Alhaji Jamil da Kamil daIƙilima tayi tsaye Kamil na ta kallon agogon dake ɗaure a hannunshi, cike da mamaki ta maidoda dubanta gare shi tare da faɗin "Anty Iƙilima!" Murmushi ya saki tare da shafa kumatuntatareda faɗin "zata duba jikin ƴar uwanta"....
Faffaɗan murmurshi ta saki cike da farin ciki tare da faɗin "uncle Jamil ya kyauta" jinjina matakai yayi idon shi akan ta, kashe mai ido ɗaya tayi fuska ɗauke da murmushi tare da buɗe jakatazaro baƙin glass ta saka, gyara zaman baby hijab ɗin jikinta tayi ta goya jakanta ta sumbaci
kumatun shi, ƙwanƙwasa glass ɗin tayi alamun su buɗe mata, ana buɗewa ta kaima saitinzuciyarshi bugu a hankali ta juya da sauri da nufin sauka, kai hannu yayi da zumman kamotatazille ta dira, sauka yayi a natse cike da kamalan shi ya riƙo hannunta suka nufe su....
Suna ƙarisawa inda suke suka rungumi juna ita da Iƙilima cike da farin cikin ganin juna, "yaisahaka" Kamil yace tare da kallon Insu, zare jiki suka yi a natse fuskoki cike da murmushi, kallonAlhaji Jamil dake ta sakin murmushi ta yi tare da ɗaga mai gaisuwa, amsawa yayi cike da jindaɗi, gaida SSB Iƙilima tayi da kulawa, amsawa yayi cike da kamalan shi, "ku muje mu kawai akejira" Kamil yace a ƙage, juyawa Insu tayi ta shige jikin SSB a hankali murmushi ya saki tare da hittingbayanta a natse, tana zare jiki ta miƙa ma Kamil hannu, miƙa mata Mairah yayi tare da maIƙilima
alamun ta wuce su je, sallaman Alhaji Jamil dake ta sakin mata murmushi tayi ta wuce.... Sumbatan kumatunta ta tayi a hankali ta shafa kanta, juyawa ga SSB tayi ta miƙa mai ita, amsanta yayi ya saɓa a kafaɗa, "yi wa Ammi bye-bye" yace tare da ɗago kanta, "Ami bye" taceahankali muryanta na rawa alamun gab take da sakin kuka, "bye" tace tare da juyawa ta bi bayansu Kamil a natse, suna tsaye a wajen har suka shige ciki kafin su juya zukata cike da kewanmatayensu suka nufi mota....
Sallama Gude da zugan yaranta da ƴan uwan Babansu Sudais tayi murya na bayyana farincikinda take ciki, shirye suke tsaf cikin shiga me matuƙar burgewa, wuce wa gefen Yasmin Sahabeeda ya shigo da su yayi tare da zaunawa saman kujera, da mamaki Farisat tace "Anty Gudeyanzufa muke jiran Habibu ya dawo ɗakko Umar a school ya kai abubuwan da aka haɗa can!" murmushi ta saki tare da faɗin "ai gashi mun rigaku kawo wa, Halima ku shige da shi sununamuku inda zaku ajiye" tayi maganan tare da kallon Halima da Nafi da wanda Nafi ke bi mesunaMaryam dake riƙe da kaya ruƙum-ruƙum, murmushi suka saki tare da wuce wa gefen dining....
"Anty Gude ai can ze sauka fa, zaman nan da ki ka ga munayi Habibu muke jira!" Farisat takumacewa fuska da murya ɗauke da mamaki, murmushi ta saki tare da faɗin "ba inda yafi can-cantaSamir ya sauka se gidan Amina, kuma na san shima hakan ze fi so" murmushi Babiya ta saki tareda faɗin "tabbas wannan haka yake" jinjina kai suka yi zukata cike da yaba sanin yakamatandatayi, "jama'a ku mu miƙe lokaci ya ƙarato" Habiba tace tare da ƙoƙarin miƙewa...
"Ya ƙarato kuwa, Daddyn su ma sauke mu suka yi a bakin gate suka wuce, yace ba ze iya
shiriritan mu na mata ba" murmushi Suwaiba ta saki tare da faɗin "yayi na su Yaya Ali kenan, ai
suna shigowa suka taddamu muna ta aiki suka juya suka fice" murmushi ta saki tare da wucewakusa da Babiya, "ina masu zuwa su yunƙuro" Babbar ɗiyar Gude me suna Shamsiyya tace taredakallonsu, "ai dukan mu ne fa ina ga" Farisat tace tare da miƙewa, "a'a mu dai a barmu a gidani da
Mari" Babiya tace tare da kallon su, "dama Hajiya Nafisatu ai ba zuwa zaki yi ba" Sadamdayafitodaga ɗakin shi yace fuska yalwace da murmushi, "dama ban ƙwallafa rai ba, bare inji haushi" tacetare da banka mai harara.... Murmushi ya saki tare da kallon Sahabee, "muje malamin" yace tare da gaida Gude ya fice, dasauri ya tashi ya dafa mai baya, kallon Yasmin Farisat tayi tare da faɗin "muje" a sanyaye, "kujezan jira Umar tukun" tace a hankali, jinjina mata kai tayi tare da kallon Shafa'atu ɗiyar Habibatace "muje Shafa" murmushi ta saki tare da miƙewa, tasowa ƙananun yaran Jummai da Suwaibasuka yi dan bin su, "ƙananun yaran nan su zauna da Hajiya ba gidan biki zamu ba, ze iso har indaku ke ku ganshi" ɗiyar Gude wacce ke bi wa Samir me suna Samira tace tare da bin bayansuFarisat, "Sadam fa can ya nufa, wasu su bi shi a rage yawa" Habiba tace tare da kallon su, "ai bawasu ba Anty Habiba muje" Suwaiba tace tare jan hannunta suka fice da sauri...
"Da sauran time kafin su sauka, wan can motocin su inso ne?" Insu tace tare da gyara tsayuwaidanta akan fuskan Kamil, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "tun ɗazu" juyawa ga Iƙilima tayi
tare da faɗin "Anty Iƙilima Yakamata ki je su sauke ki a hospital ko?" Girgiza kai tayi fuskaɗaukeda murmushi tare da faɗin "a'a bari muga isowan su tukun" "a'a Anty Iƙilima, kalli time ɗindamuka iso, yakamata ki je ku ga juna ku tattauna akan abubuwan da suka kamata, kin sangobezamu juya, in sha Allah zuwa yamma zamu zo can muga yanayin jikin na ta" ta idda maganancikeda fatan ta fahimceta, jinjina kai tayi cike da gamsuwa, "yawwa uncle Kamil rakata, "okay kematare zamu tafi, ma jira su a mota" jinjina kai tayi cike da gamsuwa ta bi bayansu....
Suna zaune a cikin mota motocin su yayi ta fakawa, se da ta tabbatar da sun gama fitowa sannanta kalli Kamil tare da mai alamun su je, ba musu ya ma drivern dake tsaye gefen motanmagana, nan ya ma security's magana kafin wuce wan mintina sun mammatso kusa, buɗe musu motasuka yi suka fito, kai tsaye suka nufi inda su Farisat ke tsayuwan jiran fitowansu Yaya, rungumeSadam tayi cike da zaƙuwa tare da faɗin "ɗan saurayi!" Da ɗokacin mamaki ya juya tare dajanyota ya rumgumeta cike da farin cikin ganinta, da zallan mamaki su Farisat da muryantayadaki kunnuwansu suke bin ta da ido, zarota yayi tare da faɗin "dama zaki zo!" "Yaya Samir faYaya
Sadam, aiko kwance nake ranga-ranga a ɗaga a tayar zan nemi alfarman su kawo ni in tarbeshi
bare ina garau" tayi maganan cike da gaskiyanta tare da rungume Nafi da ta kai mata jiki....
"Lallai kin shammace mu, ba wanda ya san za ki zo" Suwaiba tace cike da zallan mamaki, "ai banfaɗawa kowa ba Anty Suwaiba saboda ina son baku mamaki, ina Yaya Sudais?" Tayi maganantare da fara dube-dube, "gayi can zaune kan keke" Halima tace cike da farin cikin ganinta, "kekekuma! Ina kafar da za su saka mai?" "Tukunna ai Insu, da sauran lokaci" Jummai tace da kulawa, "okay haka ne kam, bari in gaida su Yaya Ali" tace tare da wuce wa inda suke.... Ƙarisawa inda Kamil ke tsaye Yasmin tayi fuska cike da murmushi tare da faɗin "uncle Kamil
gaka a garin bayin Allah" murmushi ya saki tare da faɗin "sauran garuruwan ma na bayinAllahne Mommyna" murmushi ta saki tare da faɗin "Bertuwa ta musammance, barka da zuwa uncle"
"yawwa ya ku ke?" Yace fuska cike da murmushi, "Alhamdulillah" tace nata muryan cike damurmushi, "uncle Kamil barka da zuwa" Farisat tace tare da ƙarisowa wajen, "barka dai Hajiyata"nan Sadam da su Sahabi da Salman da ya iso wajen dan gaisawa da shi saboda faɗamai isowanshi da Insu tayi suka gaisheshi a girmame, suna rufe baki su Suwaiba suka fara na su, hakayayi taamsawa fuska cike da murmushin jin daɗi, "muje uncle ka gaisa da su Yaya Ali" Yasmin tacetareda wuce wa gaba ba musu ya dafa mata baya.... Dawowa Insu tayi riƙe da hannun Lurwanu fuska cike da murmushi, "Anty Habiba kina kokallonYaya Lurwanu!" Tace cike da yanayinta, murmushi ta saki tare da faɗin "ina kallon shi Insu" "kinaganin irin wannan tumbin da ya ajiye ko ni ɗaya na gani?" "Ai har mu mun gani" Sadamyacetareda dafa kafaɗunta, "Alhamdulillah Anty Saratu ta iya kiwo" Farisat tace tare da banka musuharara, dariya suka saki tare da kamo wani batun, haka suka cigaba da tsayiwan jiran isowansu, hira kuwa shafuka-shafuka haka suka cigaba da buɗewa cikin jin daɗin ganin juna, fara fitowanda fasinja suka yi ne ya ja hankalin su suka zubda komai suka maida hankula ga wajen, "Yaya!" Umar yace da ƙarfi tare da ɗaga yatsanshi manuniya ya nuna shi da shi, kai ido gaba ɗayansuinda ya nuna suka yi cike da ɗoki me haɗe da zaƙuwa....
Murmushi Yaya ya sakin musu tare da nufo inda suke, kallon wajen kawai suke dan sanganinmuradin idaniyarsu da zukatansu, buɗe baki Farisat tayi da zumman magana fitowan wani
kyakykyawan matashin saurayi dake sanye cikin ƙananun kaya waƴanda duba guda zaka musukasan sun ci kuɗi sunyi nak, kayan kuma yayi mugun amsanshi ya yi mugun taka mata burki, rumtse ido yawancin su suka yi da ƙarfi saboda gudun faɗawa hasashe zukatansu na bugunluguden da be taɓa yi ba, lumshe ido Yasmin da Farisat da Sadam da Salman suka yi lokaci gudazukatansu na tsitstsinkewa tare da buɗewa a gaggauce suka zube akan saurayin dake tsayecakyana bin su da ido cike da wani yanayi da shi ya san na menene....
Lumshe ido Yasmin tayi hawayen da suka cika idanunta suka gangaro, duk tsayin shekarundazata ɗauka ba ta saka shi a ido ba, ba zata ƙi gane shi ba in ya bayyana a idanunta, fara takawatayi a natse ta nufi inda yake tsaye, fara takowa yayi shima a natse idanunshi akan ta, sunaisakusa da juna ya saki hawayen da suka cika na shi idanun ya buɗe mata hannun tare da motsabaki a hankali cikin zazzaƙan muryan shi yace "come" da sauri ta faɗa jikin shi tare da fasakukame rauni.... Rumtse ido yayi jikin shi na kyarma tare da faɗin "shiiii Baby!" Saurin ɗagowa tayi tare da kallonshi cike da mamaki, "ka gane ni Yaya Samir! Dama ka gane ni!" Tace a ruɗe, balla mata hararayayi me haɗe da murmushin da ya ƙawata fuskan shi dake ƙawace da sajen da yayi mugunamsan fuskan tare da dungure kanta a hankali, juyawa ta inda suke tayi da sauri tare da faɗin"yagane ni! Yaya Samir ɗin mu ya dawo da gaske!" ta idda maganan tare da duƙewa a wajentafasheda kuka me cike da farin ciki....
Nufo wajen Farisat da Insu da Sadam da su Sahabee suka yi da sauri jikkunan su na ɓari, sunaisasuka faɗa jikinshi tare da sakin kuka, rumtse ido yayi tare da ɗaga kai sama hawaye na biyogefen kunnin shi suna ɗiga a saman ƙafaɗun coffee t-shirt ɗin dake jikin shi, "Yaya Samir!" Sukace murya na rawa, girgiza kai yayi da sauri tare da sakko kai ya fara bubbuga bayansu a hankali....
Tsayin mintina suka ɗauka a haka kafin su janye jikinsu tare da bin shi da ido, "Baby Insu!" Yaceidan shi akan Insu fuska cike da murmushi, jinjina kai tayi tare da goge hawaye, "Anty Farisat!" yace tare da sakin ƙaramar dariya ya na bin ta da ido cike da kewa, "Yaya Samir!" Tace muryanarawa, "Sadam" yace idanshi akan shi, faɗawa ƙirjin shi yayi tare da sakin kuka cike da rashinmadafa, bubuga bayan shi yayi a hankali tare da miƙa ma Sahabee hannu, "Uncle?" yace cikedason tabbatarwa idan shi akansu, jinjina mai kai suka yi cike da tabbatarwa, murmushi ya saki tareda faɗin "Uncle ne ya girma haka! Lallai girman ɗan mutum ba wuya" ya idda maganan taredajanyo shi ya haɗashi da Sadam ya rungume su, murmushi kawai suke saki idanunsu na tsiraradaruwan hawaye.... Murmushi Yaya ya saki tare da takawa a natse ya isa wajen, saurin isa inda yake Insu tayi taredafaɗin "Yaya ba mafarki muke ba ko!" Ta jefa mai tambayan idanta dake zubda ruwan hawayetsaye a nashi, jinjina mata kai yayi fuska cike da tausayinsu zuciya na bayyana rauninshi, ƙwaƙwalwa na tuna shuɗaɗɗun abubuwa, jawota yayi kusa da shi tare da faɗin "Sadamkubashi
waje ya isa gare su" jinjina kai suka yi tare da zare jiki suka ja gefe, bin su da idon dake ɗaukedatsan-tsan ƙaunarsu yayi tare da faɗin "where is my Auntie's!" Ya jefa musu tambayan idanshi nayawo a saman fuskokin su, ba su Insu da suka kafeshi da ido ba, hatta su Gude dake gefe sunabinsu da ido se da ƙirazansu suka yi mugun bugawa, haɗiye kakkauran yawu suka yi tare da sakinmai murmushin yaƙe, ba za musu ido ya kuma cike da tuhuma, ganin yanda suke ta saddakai yasa shi ɗago kai ya kalli Yaya tare da faɗin "Yaya nauyin cikin ya hanata zuwa tarbana ne!" Yajefamai tambayan raunin shi na bayyana.... Murmushi Yaya ya saki tare da jinjina mai kai, "oh Allah zan hukunta babyn nan duk ranar dayazo duniya, tunda ya hana uwa ta zo tarban ɗanta" yayi maganan cike da yanayin shi fuska ƙawace
da murmushi, murmushi suka saki wanda iya kan shi saman baki, "isa gare su" Yaya yace jiki asanyaye, tare da nuna mai su Gude, jinjina kai yayi tare da takawa a natse ya isa inda suketsayeidansu akan shi suna zubda ruwan hawaye me cike da farin cikin ganin shi.... Yana isa ya faɗa jikin Gude da ta buɗe mai hannu jiki na kyarma tare da faɗin "Mommy!" Fashewada kuka suka yi a tare cike da rashin madafa, banda shafa bayan shi ba abinda gude da ta kasamagana ke yi, ganin yanda suka kasa sakin juna ya sa Daddyn su takowa a natse ya ɗagoshi, ɗago kai yayi ta kalleshi ganin shine ya sa shi faɗawa a ƙirjin shi tare da faɗin "Daddy!" Murmushi
ya saki tare da shafa kanshi na shi hawayen na biyo kumatunshi, "ga su nan duk dan kai sukazo" yace tare da ɗago shi ya nuna mai su Suwaiba, murmushi ya saki tare da faɗin "Anty Suwaiba, Anty Jummai, Anty Habiba, Yaya Ali, Yaya Lurwanu, Yaya Balarabe, Munari, Maryam, Samira, Shamsiyya, Nafi, Halima, Baba Abubakar, Baba Sagiru, Goggo Salame, Goggo Indo, goggoSakina, Shafa'atu" duk wanda ya kira se ya saki murmushi tare da goge hawaye.... Maida duban shi ga Salman yayi cike da farin ciki ya nufe shi ya rungume shi ƙaƙamtare dafaɗin"my friend Salman" ƙanƙame shi Salman yayi tare da jinjina kai sautin murmushin shi na
bayyana, "i really missed you" yace tare da dukan bayan shi, "I know" yace tare da kai mai dukaabaya, dariya suka saki tare da sakin juna, fuska cike da murmushi ya kalli Sudais, duƙawa yayi yarungume shi ƙam-ƙam duk da mamakin ganin shi zaune saman kujera da yayi "babban mutum" yace murya cike da shauƙi, "malamin" Sudais yace murya cike da dariya, sakin shi yayi ya ɗagotare da bin shi da ido, ganin irin kallon tuhuma da yake mai ya sa shi faɗin "ga AbdallahdaNafi'uka gane su" kallon inda ya nuna mai yayi cike da mamaki tare da faɗin "sosai kuwa, AbdallahNafi'u!" Yace tare da miƙa musu hannu ba musu suka amsa suka riƙe ƙaƙamcike da kewa, juyowa ta inda Salman yake yayi tare da faɗin "banga Saminu da Salwa ba" murmushi ya saki
tare da nuna mai inda Saminu ke tsaye idanu na shatatan hawaye, zare ido yayi da sauri yanufi
inda yake ya rungume shi ƙaƙam, fashewa da kuka yayi tare a faɗin "ka yafeni Samir, ni najakomai, ni na ja maka komai" murmushi ya saki tare da janye jikin shi tare da faɗin "nagodeSaminu, godiya zan maka, kai ne tsanin da ya kaini ga nasarar rayuwata" yana kai nan ya kamohannun shi ya cafke da ƙarfi, "ina Salwa?" Murmushi Farisat da suka ƙariso wajen ta saki taredafaɗin "ba ta san da dawowanka ba"....
"Ai da ta sani da ba za'ayi ba ta ba" Sadam yace tare da sakin murmushi, "ga uncle Kamil, shinewakilin da mr president ya turo dan tarbanka" Insu tace
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 97 Chapter of 109