Share this page
samu ɗayan su, gaba ɗaya zaka gansu a wajen, amma in wani abu na siyasa ne suna gefe suna sokawa juna muggan kalamai, to duk be kai zuci ba, dakansu suke tsara zantukan da za su jefi juna, wasan da ake son bugawa da Uncle kenan, yana ɗaukan ɓangaren nan a matsayin ƴan adawa, ya rufta, kafin ya gane me ma yake ciki seyaɗau shekaru, kafin lokacin da ze gano talakawa sun jigata sun cire tsammani, shikenan faantashi wasan ba shi, ya sauka ana Allah ya yi wadai da mulkin shi, ka ga mu kuma mun gamashigatasku, mabiyana da nake fariyada su a media duk za su guje ni, nawa ƴan adawan za su mundariya ta ƙare miki baby Insu, bye se na dawo, Abban Iman please ka fito da wuri" ta idda maganan tare da miƙewa ta isa gefen hoton su ta sumbaci kumatun Anty ta fice da sauri.... Ba wanda ya iya kauda ido daga kanta har ta fice, "a ina take samun irin waƴan nan maganganun?Ya aka yi kaifin tunaninta yake son shallake namu? Wake saka mata batutuwa haka a baki?Alhaji Munnir yace cike da zallan mamaki, "ɗalibar shari'a ce fa, tana da kaifin ƙwaƙwalwawandaya zarce na waƴanda suka kammala Isoul" Abubakar yace cike da zallan mamaki, "na nunamukuirin jawo hankalin da take a media kuwa? Ranar da na fara saurara na jima ina mamakinwai ita ɗin ce kuwa?" Jabir yace tare da kallon su... "Wallahi ban san tana yi ba, da wani suna take amfani?" Alhaji Munnir yace da zallan mamaki "Insu" yace a natse tare da kallon SSB da gaba ɗaya jikin shi yayi sanyi, "poster's sun zagayeƁadamayo gaba ɗaya, ba inda ba aka kai ba, abun farin cikin shine jama'a sun amsa da hannubiyu wasun su da kan su suke cire kuɗi su yi su raba" jinjina mai kai yayi tare da lumshe ido, "inaganin yakamata muyi rabo, dan ƙara jan ra'ayin mutane" yace a natse idon shi akan SSB... "A'a uncle Jabir, kar ma ka ja ra'ayin mutane da wani abu bare nan gaba suyi tunanin yaudaransua kayi da abun duniya, bana jin wani abun duniya na iya siyan soyayya, se dai in ta kasancebadanAllah ake yinta ba, ku ƙyale su da ƙaunar da suke mai, ku bar ƙauna ta nuna kanta da kanta, danAllah Abban Iman muje" ta idda maganan kaman za ta tsaga ihu, dan ta gaji da jira ne ta dawodan tasa shi, miƙewa yayi a natse tare da sallaman su ya fice, "uncle's ku duba maganata please, sannan maganan voters card ɗina kar a manta, dan ba na zanyi zaɓe" ta idda maganan taredabin fuskokin su da ido, murmushi Abubakar ya saki tare da faɗin "ba ma son rigima shekarunki basu kai ba" fiddo ido waje tayi tare da faɗin "uncle Abubakar ka ci tuwo a kaina da yawa, wallahnaisa 18 da wasu watanni ne da ni, ka ga na isa yin zaɓe, Uncle please ka ce su mun" ta idda maganan tare da kafe shi da ido, "jeki Ibrahim na jiran ki" Jabir yace tare da sakin murmushi.... "To Uncle ka ji?" Ta yi maganan a shagwaɓe murya a narke, jinjina mata kai yayi ba tare dayacekomai ba, "wow wannan shine Uncle ɗina, best Uncle in the world" tace tare da dafa ma Ibrahimbaya a guje..... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Thirty Tun daga wannan rana suka maida hankula gaba ɗaya ga zaɓen da ke hararosu, AlhamdulillahSSB ya samu karɓuwa ga jamma'an ƙasa, duk inda yaje dan campaign se ya tadda sun rigadasunwuce wannan wajen, abin har tsoro ya ke ba shi dan yanda suka ɗau dukkanin yardansusukamiƙa mai, be taɓa ɗaukan abinda wani mahimmaci ba amma ganin yanda mutane ke zaburadabuɗe murya akan goya mishi baya ya sa shi maida hankalin shi ga abun ka in da na in.... Sakkowa daga mota tayi tare da kallon Ibrahim dake ƙoƙarin sakkowa tare da faɗin "AbbaImandan Allah na shirya anjima muje?" Tayi maganan amarairaice tare da shagwaɓe fuska, "nafaɗamiki ba fita se bayan zaɓe SSB ne yace dan haka ki natsu" Ibrahim yace hankalin shi akanrufeƙofar mota, tura baki tayi ta nufa hanyar da ze sadata da ciki da sauri, zare ido tayi tare dakallonHajiya dake zaune saman two seater's, da tsan-tsan farin ciki ta ƙarisa gareta tare da rungumeta, "i really miss you" tace tare da ƙanƙameta, murmushi ta saki tare da hitting bayanta a hanakali, janye jikinta tayi tare da faɗin "har ina neman wajen zuwa ana mun yanga a she ma zanshigoinganki" ta idda magana tare da rumgumeta ta kwantar da kanta a saman kafaɗanta na dama.... Gyaran murya Alhaji Jamil yayi tare da faɗin "in fa hankalinta ya kaɗa wani wajen ba kuladamutanen da ke zaune a waje take ba" dariya Kamil ya saki tare da faɗin "ga tabbaci nankuwa" "au kai baka taɓa lura da hakan ba?" Yace tare da kallon shi, tura baki gaba tayi tare da zarejikinta ta miƙe a natse tare da faɗin "uncle's and Auntie's sannun ku da zuwa" tana kai nantahaye up stairs da sauri tare da faɗin "Hajiya bari in kimtsa" "to" Hajiya tace fuska faɗaɗe damurmushi... "Dame zaki yi zaɓen?" Salman dake zaune saman ɗaya daga cikin chair's ɗin dake jere a garden ɗin gidan Yaya yace tare da kallon Yasmin, kallo me cike da tsoro da rashin madafa ta mai tareda faɗin "wallahi na manta da zan buƙaci voters card sam, in haka ne ai ko Anty Farisat bazatayi ba dan ba ta da shi" "ke wallahi na so yi mantawa nayi sam, gashi jiya Insu ta ce an kawo matanata" "wannan ai ba ta ɗaukan komai da wasa" Salman yace tare da kallon su... Riƙe wannan" Yasmin tace tare da miƙa mai takardan hannunta, amsa yayi a natse ya zubeidanunshi a kai, kallon sakanni yayi ya kauda fuska tare da faɗin "Yasmin ki na son sheƙe ni neko?" Dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "wai dan ma kai ne" "a'a banga wanna ba" yacetareda banka mata harara "wallahi an rage abubuwa da yawa, Aminan juna za su ɗauka" tacecikedatabbaci, ɗaukan wayan shi dake gefe yayi ya danna number ya kara a kunni, ana ɗayawa yace"duk inda ka ke ka hanzarta zuwa ka kawo mun a gaji, da alama Yasmin ta daina ji da ni" dariyatasaki tare da faɗin "sha zamanka Yaya Sadam barni da shi" katse kiran yayi ya sauke wayantareda faɗin "a wani account za a saka matsabban?" "Ka saka a account ɗin Anty kawai" tace taredajuyawa ga Farisat dake faɗin... "Baki tambaye shi wanne ze sami daman zuwa a ciki ba?" "Ai ko wanne ku ka ce in halartainshaAllah zan ƙoƙarta in hakarta" "wow shiyasa nake jinka a rai Yaya Salman" Yasmin tace taredasakin dariya ta miƙe, "har mun gama kenan?" Yace tare da kallonta, "eh in akwai wani abuninnatuna zan sanar maka" tace tare da barin wajen, murmushi ya saki tare da maida duban shi gaFarisat dake bin shi da ido, ɗaga mata kira yayi tare da mata alamun menene? Girgiza kai tayi tare da sakin murmushi ta kauda fuska.... Fitowa Ziza tayi a hanzarce cike da tsoro ta ƙarisa inda Sudais ke tsayuwan jiran fitowanta, idonshi ƙyam akan ƙofar gidan, "menene? Meyasa ka ce in fito? Me kuma ka ke so yanzu kuma?" Tajera mai tambayan a ɗan tsorace tare da kallon bakin ƙofa, "zan zo anjima mu fita" yace taredariƙo hannunta, girgiza kai tayi ta zame hannunta a hankali, "meyasa?" Yace cike da mamaki idonshi akan ta, "ba zanje ko ina ba, a nan muka haɗu, sannan duk wata alaƙa anan muka ƙullata, anan mutumci na yake, ba zan bar nan zuwa ko ina dan kasantuwa da kai ba, in kana sonkasantuwa da ni to ka yaye duk wata fargaba ka zo gare ni, ni kuma na yi maka alƙawarinfarantamaka fiye da yanda ka ke hasashe" ta idda maganan tare da ba za mai ido.... "Ziza Sa'adatu mahaukaciya ce, ba ta da isasshen hankali" yace cike da damuwa, "kasanhakankuma ka ke mu'amala da ita? Kasan ba ta da hankali ka ɗakkota ka kawo ta tsakiyan mu? Sudaisna rasa gane inda ka nufa, kai ka mun alƙawarin zama da ni bakin rai bakin fama matuƙar nahaifi ɗan cikina na miƙa gidan marayu, se da na aikata komai na sadaukar da ɗan da na haifagajama'an da ban san su ba sannan ka juya mun baya, a gaskiya na yi matukar wawta da na yardada ƙarairayin ka, na manta waye namiji, na mance sharrin ku da sharrin zukatan ku" ta iddamaganan tare da goge hawayen da ya zubo mata, "no Sa'adatu kar ki ce haka mana" yacetaredarungumota, fashewa da kuka tayi tare da faɗin "me ka ke son inyi Sudais? Kana mun hakannedan ka fahimci na kamu da mugun sonka ko? Kana mun hakan ne dan ka fahimci ba zaniyanisantan ka ba ko?" Tayi maganan murya na rawa idanu na zubda ruwan hawaye.... "Duk ba yanda ki ke zato ba ne Ziza" yace tare da ɗagota ya fara share mata hawaye, "to menene?" Tace tare da jan hanci, "na san Sa'adatu tun kafin in sanki, sannan duk wannan abubuwanda ki ka ga tana yi danni take yi, ba na da haufi akan son da take mun, so nake na lallaɓataahankali mu rabu lafiya, ba na son ta fahimci ina da alaƙa dake na nesa bare na kusa, dannasantasosai za ta iya aikata miki wani mugun abun, zata cutar dake ni kuma ba zan so hakan ya farudake ta dalilina ba, bana maraba da duk abinda ze cutar dake, ki ƙara bani lokaci, wallahi nayi matuƙar kewan ki, ke ma kin sani amma zan mana wani ƙoƙari dan mu kasance da juna, zanshirya mana wani plan nan kusa karki damu" ya idda maganan cikin murya rarrashi tare dajawota ya ƙanƙame.... Jinjina kai tayi cike da gamsuwa, ta saka nata hannayen ta ƙanƙame shi, murmushi ya saki tareda faɗin "i know kar ki damu yanda ki ke ji haka ni ma nake ji" "nafika" tace tare da zare jikintatahaɗe bakin su, sosai suka bawa bakunan su kula cike da kewan juna, da ƙyar Sudais dake gudunkar tsautsayi ya sa Sa'adatu fitowa ta tadda su ya ƙwace bakin shi tare da sakin mata murmushi, "koma ciki kar daɗewan ki yaja hankali" jinjina mai kai tayi jiki a mace ta miƙe ta shige, nannauyan ajiyan zuciya ya sauke tare da rumtse ido ... Yana tabbatar da shiganta ya juya ya buɗe mota ya ɗakko takeaway ɗin da ya ma Sa'adatuyashige a natse, taɓe baki Shila dake zaune a kujera ƴar tsuguno a tsakar gidan maƙarrabantazazzaune kusa da ita tayi tare da banka mai harara, murmushi ya saki tare da shigewa ɗakin, "wahalalle" tace tare da juya dubanta ga Ziza dake tsaye a bakin labulen ɗakinta tana leƙenshi, "wahalalliya" ta kuma cewa tare da jan tsaki ta juya hankalinta ga lissafin da suke... "Insu!" Hajiya dake tsaye a bakin stairs tace da ƙarfi tare da kafe hanyan da ido, "na'am!" Insutace da ƙarfi sautin takunta na karaɗe kunnuwan Hajiya, murmushi ta saki saboda hangotadatayi cikin wani aminataccen shadda army colour da yaji stone work, murmushi itama ta saki tareda marairaice fuska, "sorry Hajiya na ɓata muku lokaci" tace fuska a marairaice, riƙo hannuntatayi tare da faɗin "muje kin yi kyau" murmushi ta saki tare da faɗin "bari in sallami Anty" tanakai nan ta zare hannunta ta wuce inda hoton su yake da sauri... "Anty yau ranar zaɓe, kina sane ko?" Tace tare da sakin murmushi, "okay okay, zamu je mudannakuri'un mu ga wanda ki ka fi kowa so a duniya, har da ni fa, ina da tabbacin kin fini san shi, ki tsaya ki ga yanda masoyan shi za su fito ƙwansu da ƙwarƙwata dan su kaɗamai yaƙininsudadukkanin zuciyoyin su, zan kaɗa nawa kuri'ar wake ce, ki ji hakan a zuciyanki, se mun dawo" taidda maganan tare da wuce wa inda Hajiya ke tsaye tana bin ta a ido cike da zallan mamaki, "muje" tace tare da riƙo hannunta suka fice.... Suna fita suka tadda motoci barbaje kowa yana ƙoƙarin shiga dan neman mazauni, da sauri wani security ya matso ya buɗe musu ƙofa, murmushi ta saki tare da gyara zaman jakan bayantatashige, dafa mata baya Hajiya tayi cike da kulawa, nan suka rankaya su da ƴan rakiya da security's wanda su kaɗai ma gayyane, kai tsaye airport suka nufa, suna isa suka shige airplaneɗin shi me ɗauke da sunan shi wato SSB Airplane, ganin yanda yaran su Lubabatu ke bintadakallon raini ya sata nafar VIP inda su SSB suke.... "Na san za'ayi hakan" Abubakar yace tare da sakin murmushi ya miƙe daga gefen SSBya koma gefen Alhaji Jamil dake magana da Jabir, zama tayi da sauri tare da faɗin "Uncle ka ɗakkovoter'scard ɗin ka?" Da mamaki ya ɗago kai ya kalleta, shagwaɓe fuska tayi tare da faɗin "tunatar dakai fa kawai nake son yi" jinjina mata kai yayi tare da lumshe idanu ya ɗaga kai sama, jin ba taƙaracewa komai ba ya sa shi sakko da kai ya buɗe ido a natse ya sauke mata, murmushi ya saki ganinyanda ta ɗaure fuska alamun ba ta ji daɗi ba, "kin ɗakko na ki?" Yace a hankali, ƙaramar dariyatasaki tare da faɗin "eh Uncle ai ba zan manta da shi ba, kuri'ata kan iya canza komai" murmushi yasaki tare da kauda kai a natse, "kin kyauta" yace a hankali tare maida idon shi ya lumshe.... A airport ɗin birnin Kautal dake arewacin ƙasar Ɓadamayo jirginsu ya dira, suna sakkowa sukatadda motoci tsatstsaye suna jiran isowan su, ba wani ɓata lokaci kowa ya shige suka ɗauhanya, kai tsaye gidanshi dake garin suka wuce, hutun awa ɗaya da rabi suka yi suka fito dan zuwakadakuri'a, shine farko, tun da ya isa wajen jama'a da suka je dan kaɗa kuri'a ke farin cikin ganinshi, yana kadawa yaja gefe, Insu ce ta dafa mai baya bisa jagorancin Hajiya wanda ta ɗankwalanatabayan Insu ta dangwala, suna gama dangwala na su suka tattara suka koma gida.... "A ƙara?" Lubabatu tace tare da kallon SSB da jikin shi yayi mugun sanyi saboda yanda jama'anKautal suka nuna mai ƙauna da yanda suka dinga mai fatan alheri tare da fatan in sha Allahseyahau kan kujeran mulkin Ɓadamayo ya mulke su, irin kalaman nan mugun tsorata shi suke, danyana gudun ya kasa musu adalcin da suke zato da fata, girgiza mata kai yayi tare da saukenumfashi me ƙarfi wanda ya ja hankulan su gaba ɗaya.... Murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "ci abinci, Allah ya na tare da kai" jinjina kai yayi ya ɗaucokali ya gutsiri lailayayyan tuwon garin da aka mulla musu ya kai baki, lumshe ido yayi cikedayabawa ga wacce ta girka tare da amsan yanayin da ɗanɗanon abincin ya zo mai da shi.... Gutsiran tuwon Insu tayi a natse ta dangwala miyan dake ta tashin ƙamshi ta kai baki, lumsheido tayi tare da faɗin "wow subhanallah abinci me daɗi ma duniya ce, Allah ka daɗawa hannundaya juya masara zuwa tuwo albarka" tayi maganan cike da santi, harara yawancin su suka bankamata, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "ci tukun se ki santin daga baya" "ai da kin bartatayi Hajiya banjin ta taɓa gamo da me zubin irin shi a gida" Lubabatu tace tare da sakin murmushi, dariya yawancin yaran suka saki tare da bin Insu da ta buɗe ido ta zuba ma Lubabatu da idocikeda shaƙiyanci.... Harara Alhaji Jamil ya banka musu tare da kauda kai, saurin ɓame baki suka yi tare da maidahankulan su ga abincin gabansu, murmushi Insu ta saki tare da faɗin "wallahi kaman kinsani Anty Luba, ban taɓa cin irin shi ba, se dai kema fa da alamun hakan ne, tunda ga uncle Munnir nan ya zage yana ta kwasan girki" ta idda maganan tare da sadda kai cike da danne dariyar yanda fuskan Lubabatu ya koma, matse dariya su Maude dake tsaitsaye a gefe suka yi sabodayanda fuskan Lubabatu ya canza lokaci guda, murmushi Alhaji Munnir ya saki tare da faɗin"dagaskiyan ki Insu, ina ga wannan ne karon farko" "wow uncle Munnir mu yi santi kaji kar muwani matse, kasan abinci matuƙar yayi daɗi ji za kayi kaman ba a duniya ka ke ba, kaman ka mutuneka yi dace da aljannar mahalicci" ta idda maganan cike da yanayinta, murmushi Alhaji Jamil yasaki tare da kauda kai, buɗe baki tayi da zumman magana SSB ya taka mata burki da faɗin"shiii eat"... Haka suka zauna a gidan har la'asar, suna idar da sallah suka tarkato suka fito, nan suka taddajama'a kaman za su fasa anguwar saboda tsananin yawan da suka yi, da ƙyar suka samuhanyarficewa, nan ma ba su haƙura ba wasun su sun hau abin hawa sun musu rakiya har airport, sedajirginsu ya tashi sannan suka samu sukuni... A magun gajiye suka isa gida, a parlor yawancinsu suka yada zango, hayewa sama Insu tayi kai tsaye dan rage kayan jikin ta, ba ta jima ba ta sakko ta wuce kusa da Hajiya ta zauna, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "da kin kwanta kin huta" miƙewa zumbur tayi tare da faɗin "Hajiyaai ko da daddare ba zan iya barci ba saboda farin ciki" ta idda maganan tare da nufar flat screentvn dake mamaye da bangon parlorn ta kunna, wucewa up stairs tayi a guje ba ta jima ba ta fitosanye da dogon wando tight pencil da karamar t-shirt da ya zauna mata ɗamau, ƙarisawagabantvn tayi ta soka USB n dake hannunta, ɗaukan remote tayi taja baya tare da lalubo waƙa, yanafara tashi ta ajiye romate ɗin ta fara juyi da taka rawa... Cike da tsan-tsan mamaki suke bin yanda take juyi kamar mara ƙashi da ido, nan yaran sukafaraɗaukanta video manya kuma na tafi da sakin murmushi, dan ba kaɗan ba ta burgesu, dukwani abu da take yana kallanta ta ƙasan ido be tsinke da lamarinta ba se da ta fara taka rawa, girgizakai kawai su Alhaji Jamil suke dan sun fahimci da gaske take, tana kai karshe ta duƙe taredasakin numfarfashi me haɗe da haki, ganin yanda take sakin hakin ya sa shi kafeta da ido cikedamamaki, saurin ƙarisawa inda take Maude tayi ta dagota tare da faɗin "sannu daina tsalletsallen tunda bakya da ƙoshin lafiyan yi" ta idda maganan tare da ajiye ta kusa da Hajiya datagaalamun damuwa ya bayyana a saman idanunta fiye da sauran... Kwantawa tayi tare da nannaɗe jiki waje guda ta cigaba da sakin hakin, ita da kanta ta tsorataawannan karon be taɓa mata haka ba, ko da za ta yi hakin be tsayi haka, amma yau gashi har datsinkewan zuciya yake haɗa mata, "sannu" Hajiya tace da kulawa, "to ai kunga yanzu se tanatsu, yarinya sam ba ta da natsuwa tayi ta wani abu shaka-shaka kamar goyon kaka, kowa na zauneshiru se ita uwar kazagi, kunga gobe se ta natsu" Lubabatu tace zuciya a matuƙar ɓace, "danAllah Luba bar wannan zancen mana" A'isha tace tare da kauda kai.... "Maude kamata ki kaita ciki ta kwanta" Alhaji Munnir yace da kulawa, amsawa da "to" tayi tanufeta tana kai hannu ta jiyo saukan numfashinta a hankali alamun tayi barci, "ai tayi barci ma" tace tare da ja baya a natse, gyara mata kwanciya Hajiya tayi da kulawa ta miƙe a natse tasallami SSB da su Jabir ta nufi ƙofar fita, da sauri su Lubabatu suka dafa mata baya.... Da sallama Salman ya shigo parlorn fuska faɗaɗe da murmurshi, amsawa suka yi idanuwansuakan shi, saboda yanda bakin shi ya kasa rufuwa, "albishirin ku" yace tare da zama kusa daLurwanu "goro fari ƙal-ƙal kamar zuciyanka" Yasmin tace tare da sakin dariya, dariya ya saki tareda faɗin "masu hasashen yawan ƙuri'u sun bayyana kuri'un wanda ya fi amma dai se munjiramunji tabbacin daga bakin INEC Chairman" "dan Allah!" Sadam yace tare da miƙewa zumbur yakoma kusa da shi, "wallahi" yace cike da farin ciki "faɗa mana na waye yafi yawa?" Farisat tacecike da ƙosawa... "Senator Garba Zakari, Senator Bashir Ridwan, Senator Mikeal Ugwuchukwu" ya idda faɗi cikedafarin ciki, "wow" tace tare da kallon shi "president fa!" Yasmin tace zuciyanta na tsinkewa, "SSBmana, ai kema kin san ai shi ze ci" yace tare da banka mata harara, ihu suka saki tare da mikewaa tare suka fara taka rawar farin ciki, dariya Hajiya ta saki tare da faɗin "ma sha Allah, Allahmaji roƙon bayinshi, wannan sallahn daren da ku ka sha na lafiya ne" "ai wallahi su kan su ba zasuyi gan-ganci hana shi ba Hajiya, mutumin nan fa ƙwarone na gasken gaske, suka hana shi maajikinsu za su ji, ke kin ga jama'a ranar kada ƙuri'a kuwa? Wanda be taɓa zaɓe ba ma bana yayi kuma shi ya danna mawa" Lurwanu yace cike da farin ciki... "Allah dai ya ba shi ikon cika alƙawuran da ya ɗauka" Habiba tace cike da farin ciki, "wayacemiki ya ɗau alƙawura? Wallahi ba abinda ya ɗauka, ya dai ce ya fito dan al'umma ƙasa ne, kumabazema kowa alƙawari ba, amma yana da ƙudirori da yake fatan cikawa idan jama'an ƙasa sunbashi goyon baya" Balarabe yace tare da kallon ta, "ya huta wallahi, ka ga ba me tuhumar shi akanbecika alƙawuran da ya ɗauka ba" Hajiya tace tare da kallon Yaya da ya shigo, da gudu Sahabeeyanufeshi ya rungume shi tare da faɗin "Yaya kuri'an Uncle ya fi na duk ƴan takaran president yawa a garin nan" murmushi ya saki tare da rungume shi cike da farin ciki tare da faɗin "ai banankawai ba Kautal Dimau,Yarban duk ana hasashen ya ƙere tsara" "hooo" Farisat tace cike dafarinciki, "sauran garuruwan ma ai ko yafi ko suyi kunnin doki dan ba wanda ze fishi" Balarabeyacetare da kallon su, "yaushe za'a sanar da na gaskiyan?" Yasmin tace tare da neman wayanta.... "Yau ne mana, ai dole su faɗa mana, Allah na tuba ma kowa ma yasan wa ya ci, dan dai sesunfaɗa ne kawai, amma ai mun isa alƙalanci da kan mu" Lurwanu yace tare da kallon Yasmindaketa kiran Insu, "oh ba ta ɗauka ba, ƙarfe nawa za su faɗa?" Tace cike da damuwa, "ke dai sakatashan news ki ba za ido ko yaushe ne ma za su faɗa" Balarabe yace tare da miƙewa ya nufi ɗakinshi, da gudu Farisat tayi kan Habiba tare da faɗin "Anty Habiba Allah yasa Uncle shine ze ci" "insha Allah shine, ku je ku yo alwala ku ƙara kaiwa Ubangijin mu kukan ku, mu jira tsammani" "to" suka ce tare da nufar bedroom's ɗin su da sauri, da murmushi suka bi su.... Zaune take a gaban tv idonta ƙyam akan INEC Chairman dake bayanin yawan ƙuri'un jam'iyyoyi ko kifta ido ba tayi, paper da pen a gabanta da alamun rubuta yawan kuri'un da ake faɗa take, murmushi SSB ya saki tare da kauda kai, shi kan shi dannewa kawai yake dan banda bugubaabinda zuciyanshi ke yi, duk buɗe bakin da INEC Chairman yake da bugun zuciyan shi furucinshi ke fita, "Insu ta so daga gaban tvn nan haka" Jabir yace a sanyaye cike da kulawa, dan sukansudakewa kawai suke amma sun tabbata da za'a tsaga jikin su ba za'a tadda ɗigon jini ba, girgizakai tayi natsuwanta gaba ɗaya akan tvn tare da faɗin "uncle Jabir please minti ɗaya, "rabudaitaJabir ba zata fahimci komai ba a wannan yanayin se ta ji abinda take son ji" Hajiya da ke zauneriƙe da casbaha a hannu tace cike da dakiya.... Ta ɓangaren su Farisat ma sun ɗau lamurransu gaba ɗaya sun fawwala ga mahalicci, sannansunɗaura idanuwansu ga tv sun saka fatansu ga abinda INEC Chairman ze faɗa sannan sunɗaurayardansu ga Uncle ɗin su ne ze ci, sauran ƴan ƙasa ma kowa fatan shi guda ne, SSB ya kasanceyaci, masu tv suna gaban shi masu radio na manne da shi, ta ɓangare su Mr president kuwa hankalunsu a kwance babu wani alamun tashin hankali tattare da su... Ganin INEC Chairman ya gyara murya ya sa hankulansu gaba ɗaya tashi, rumtse ido Insutayi ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri, ta wani ɓangaren ta na son jin me ze faɗa, ta wani ɓangarenbaga so, buɗe murya yayi da ɗan sauti saboda yanda ƴan jaridu suka zuba mai ido, tare da faɗin"the candidate of PSF Sahabee Sadam Ɓadamayya, won the highest vote" zare ido suka yi gabaɗayansu tare da zuba mai ido ƙiraza na bugawa da sauri da sauri, shi ko da be san halin dasuke ciki ba cigaba da maganan shi yayi, "and Sahabee Sadam Ɓadamayya of SPF declared as awinnerof president election

Chapter 41 of 109