musu baya shi dasuZubair, har bakin mota suka raka su, miƙa ma Nafisat dake ta bakin ƙofa gifts ɗin Shureimyayi
tare da miƙawa Salman da Sadam hannu suka yi musabaha, "mun gode sosai, Allah ya maidakugida lafiya" "amen-amen" Salman da Sadam suka ce cike da yabawa da sanin yakamatansu, "toMomyna se mun ganku jibin, kar ki yarda ba'a zo dake ba" Shureim yace tare da sakin ma Nafisatmurmurshi, jinjina kai tayi cike da kunya, jan motan Salman dake sakin murmushi yayi sukawuce....
Sauke numfashi Shureim yayi tare da faɗin "ku mu je ko" jinjina mai kai suka yi suka komaciki,,,, kallon Yasmin da ke magana da Sadam Farisat tayi tare da faɗin "meyasa ki ke haka ne Yasmin?
Me wannan mutumin ya miki haka?" "Wane!" Tace tare da kallonta cike da mamaki, "Chiaman" tace tare da kafeta da ido, "oh Allah Anty Farisat ni wallahi ina barin inda yake nake mantawadaAllah ya halicce shi ma, jinin mu ne kawai me haɗu ba, kin san bana san mutun me girmankai, wannan ko ba girman kai kawai ke ɗawainiya da shi ba, ji yake kaman yafi kowa" "to me ruwanki
da wannan?, gaisuwa wannan ki kasa ɗagawa mutumi, ki daina wannan ɗabi'an, ba na nunawaba ne, yanda muke mutumta kowa da girmamawa shima haka zaki mutunta shi ki girmamashi, ba sa'anki ba ne a shekaru, ba sa'anki ba ne a ilimi da sanin rayuwa, ta komai ya kyere miki banason wannan wawtan" ta idda maganan tare da baza mata ido, jinjina mata kai Yasmin tayi cikedagirmamawa tace "in sha Allah" "yawwa Yaya Salman ina za kayi damu kuma?" tace idontaakanhanya, "siyar da ku zamu yi mu ci tsire da kuɗin" Sadam yace tare da sakin murmushi, "inaaayaro, ai munfi ƙarfin haka, se dai ku se jirage da gidaje" Farisat tace tare da sakin murmurshi, dariyasuka saki tare da kallonta ta mirror, "masoyiya Insu ta kira kuwa?" Yasmin tace tare da kallonsu, "a'a ina ga ba ta sauka ba tukun, tana sauka na san zata kira ta sanar" Salman yace hankalinshi
akan hanya, "gidan Yaya Ali zamu mu ƙara duba shi da jiki" Sadam yace tare da kallon Farisat, jinjina kai tayi tare da faɗin "kun kyauta" tana kai nan ta maida akalan hiranta ga su Yasmin....
Suna shiga anguwan wani ni'imtaccen iska ya doki fuskanta, murmushi ta saki tare da ƙaraƙasada glass ɗin gefenta, ta leƙa kai tare da lumshe ido, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin"wajenyayi miki kyau ko?" Dawo da kanta cikin motan tayi tare da sakin murmushi cike da yanayintatace "yayi kyau sosai, fulawoyi sun ƙawata anguwan, gashi shiru-shiru babu hayaniya, anguwannan yayi kama da wani yanki a Suwuizalan" ta idda maganan murya cike da nuna karsashi amaganan, murmurshi Hajiya ta saki tare da bin ta da ido, murmushi Alhaji Munnir dake gabayasaki tare da girgiza kai, yanayinta ɗaya da Insiyyan farko, yanayin maganan su, kamanninsu, rashin ɗaukan abubuwa a saka a zuciya, sak ita babu wani ban-banci, tsayawa driver yayi atafkeken gate ɗin da ya gaji da haɗuwa tare da danna horn, zubawa gate ɗin ido kawai tayi tanakallon ikon Allah, security's ne majiya ƙarfi huɗu suka wangale gate ɗin, jan motan driver yayi anatse tare da ƙarisawa inda suke, ƙarisowa biyu daga ciki suka yi tare da tambayan shi abindayakawo shi, bayani ya musu tare da nuna Alhaji Munnir, "sir" suka ce tare da ƙamewa, murmushi yasaki tare da faɗin "barkan ku da aiki" "yawwa sir" ɗaya yace tare da sakin mai murmushi, Insukuwa baza ido kawai tayi tana kallon wajen, ba abinda yakamata a sa a wajen wanda ba'a saba, matsowa wanda da alamu ya nuna babban su ne yayi suka gaisa da Alhaji Munnir, ɗagowayayi
ya ba su umurnin su saki hanya, da sauri suka danna wani abu dake gefe, ƙasa ƙarafa masukaurin dage tsakiyan hanya suka yi, da sauri driver yaja suka nufi gate na biyu, yana dannahornsuka wangale gate ɗin, babu wani bincike suka ɗaga musu hannu suka wuce, haka suka yi tawuce gates, se da suka wuce biyar sannan suka faɗa danƙareren katafaren filin gidan,
"subhanallah" Insu tace a ƙasan zuciya tare da buɗe ido, da gaske ta tsorata, kai tsaye parkingspace ɗin dake ɗanƙare da motoci suka yi, sakkowa suka yi a natse, bin wajen tayi da ido, danwajen ya gama razanata ba shi da maraba da wajen se da motoci, "muje" Hajiya tace tare dariƙohannunta, bin ta tayi kamar wata wawiya, murmushi Alhaji Munnir ya saki tare da zaro wayayadanna number ya kara a kunni, a na ɗagawa yace "a sanar da Maude akwai baƙi a side ɗinmegida" yana kai nan ya sauke wayan ya koma cikin mota ya zauna....
Suna shiga side ɗin idonta yayi arba da wani ni'imtaccen parlour wanda yayi mugun tsoratata, "wai nan duka a duniya ne? Ko kuma dai mutuwa tayi ta shiga aljanna" tace a ƙasan zuciyatareda haɗiye yawu kakkaura, "a ƙasa zaki zauna ko a sama?" Hajiya tace cike da kulawa, "sama" tacea hankali, "okay tom muje" tace tare da riƙe hannunta suka fara taka matakalan dake ɗaukanido, matse hannun Hajiya tayi da ƙarfi lokacin da suka bayyana a parlourm sama dan a wajennantakasa riƙe tsoronta, wani ni'imtaccen parlour ne wanda ya ninninka na ƙasa haɗuwa, gaba ɗayabangwayen glass ne masu ɗaukan ido, murmushi Hajiya ta saki tare da buɗe ɗaya daga cikinbedrooms ɗin dake saman suka shige, "ma sha Allah" tace lokacin da tayi arba da amintattunkayan da suka ƙawata bedroom ɗin, murmurshi Hajiya ta saki tare da faɗin "ba kowa ke hayowanan ba se masu saftacewa kawai a ka yarje su hayo, shi kan shi me gidan ba ko da yausheyakehayowa ba, ki kula za'a hayo miki da kayan ki, ki watsa ruwa ki gabatar da sallah, se ki sakkoki ci
abinci" jinjina mata kai tayi tare da bin ta da ido, murmushi ta sakin mata tare da shafa kantatafice, sauke ajiyan zuciya tayi tare da faɗin "oh Allah wannan kaman gidan aljanu" tana kai nantamiƙe ta nufi ƙofan da ta hanga, tana turawa ta saki ihu tare da yo baya da sauri, dan kantatagani
tsaye babu wani shamaki "na shiga uku wannan ai ya wuce burgewa ya koma tsoratarwa" tacetare da shigewa a hankali tana baza ido..... Hajiya na idda sauka daga matakalan ta tadda Maude tsaye cikin uniform ɗin aiki, murmushi tasakin mata tare da faɗin "akwai baƙuwa a sama, a kula da ita yanda yakamata ba ta da ban-banci
da uban gidanku wajen girmamawa, a kula da ita sosai, kar ayi wasa da lamarin da ya shafeta" taidda maganan fuska yalwace da murmushi, jinjina kai Maude tayi cike da girmama tace "toranki
ya daɗe" "a kwashi kayanta a shigar mata da shi ciki" tace tare da juyawa ta fice daga parlourn, bin ta da ido Maude tayi har ta fice kafin ta sauke numfashi tare da jan tsaki, "tunda kunsanbanamiji ba ne mata maza ne meye na ɓata kuɗaɗen ku kuna mishi aure, Allah ya kyauta dai, suma
iyayen yaran kwaɗayayyu ne dake amincewa, yanda ku ka kawota haka za ku zo ku ɗauketa" tayi
maganan tare da ficewa daga side ɗin.....
A dai-dai ƙofar gidan Ali ya taka burkin motan, sakkowa suka yi gaba dayan su, komawa dakai
kaɗan Salman yayi ya dakko yellown leda me girma suka shige da sallama a baki, da sauri matandake wanke tsaki ta miƙe baki washe tare da faɗin "maraba lale da ɗiyoyin albarka, idankukenan? Na ɗauka kun manta da Baban na ku ai" tayi magana fuska cike da murmushi, shagwaɓefuska Yasmin tayi tare da faɗin "Baba Tinene kin san ba zamu manta da shi ba, busy mukayi akantafiyan Insu amma yanzu komai normal" murmushi ta saki tare da faɗin "wasa nake Yasmin, ai
kuna ƙoƙari ma, yau kuma Insu an tafi" jinjina mata kai tayi ido na ta ra ruwan hawaye, "kull
banda kuka, Allah na sane da ita, ze dafa mata" tace cike da tuno karamci da dattako na
mahaifiyar su, "in sha Allah Baba Tinene" suka ce bakuna a haɗe, "ku ƙarisa ciki yanzu ya tashi
daga barci" tace idonta na yawo akan su, "to" suka ce tare da sa kai ciki, "sannun ku SalmandaSadam" tace fuska na yalwatuwa da murmushi, murmushi suka sakin mata tare da bin bayansuFarisat....
Suna shiga suka tadda shi kishingiɗe idon shi akan ƙofa, murmushi ya sakin musu me faɗi taredayunƙurin miƙewa zaune, da sauri Farisat da Yasmin suka ƙarisa tare da temaka mai, murmurshi
ya sakin musu tare da faɗin "daga ina haka irin wannan ado ƴan arziƙi?" Murmushi Sadamyasaki
tare da faɗin "kai ma ka gane su kenan Yaya Ali, ba sa kwalliya se za su fita" ɓata fuska sukayi
cike da jin haushin maganarshi, "kar ku ɓata kwalliyan ku, ku rabu da Sadamneman zanceyake, ai kowa ya san a ko ina haskawa ku ke ƴan albarka" Ali yace cike da farin cikin ganin su, gwaloYasmin ta mishi tare da faɗin "Yaya Ali ya ƙafan?" Tayi tambayan cike da kulawa, murmushi yasaki tare da faɗin "Alhamdulillah Yasmin ƙafa tana ta sauƙi, yau har jam'in sallah gaba ɗayanasamu" yayi maganan fuska yalwace da murmushi, "ma sha Allah" suka ce bakuna a haɗe, fuskoki
na bayyana farin cikin da zukatan su suka shiga da jin zancen na shi, murmushi Baba Tinenetasaki tare da faɗin "ai ƙafa Alhamdulillah yanzu kam, ana ta ganin haske" "ma sha Allah Baba
Tinene, a cigaba da shafa mai wannan maganin, sannan kar yace ze dinga tafiya haka ba sanda, ko da yake bari in muka koma gida zan ba Yaya Balarabe ya kawo mai sandan wajen Hajiyatundayanzu ba ta dogarawa" Farisat tace cike da kulawa, jinjina mata kai Baba Tinene tayi fuskayalwace da fara'a, "bari mu zo mu wuce, Hajiya tace kar mu kai magrib a waje, ranar abokai nabikin Yaya Annur muka je shine muka ce bari mu biyo mu gaidaka" Yasmin tace idonta akanAli, jinjina kai yayi cike da jindaɗi tare da faɗin "nagode muku Allah ya muku albarka, Insiyyahtatafi
ko?" "Eh ta tafi, tace a ce ma Baba Tinene ta kula da kai kaman yanda zata kula da jaririnɗanta" Sadam yace tare da kallon shi, kwashewa da dariya suka yi gaba ɗayan su cike da jindaɗi, "nasantana samun natsuwa zan ji kira, in sha Allah na warke lodin can zan fara, dan in dinga zuwainaganinta" yace zuciya na karyewa, "aiko da ka kyauta" Baba Tinene tace cike da jin daɗi, ajiyeledan dake gefen shi a gefen Ali Salman yayi tare da miƙewa, "oh Salman baka gajiya?" BabaTinene tace cike da yaba sanin yakamatan shi, murmushi kawai ya saki be ce komai ba, "Allahyasaka da alheri Salman" Ali yace tare da kallon shi, "amen" su Nafisat suka ce cike da jindaɗi, "bari
in ɗakko muku magani ku kaiwa Hajiya, dama ina ta tunanin me kaiwa" Baba Tinene tacetaredanufar ƙofa da sauri, "na shawaran ne?" Yasmin tace da ƙarfi tare da bin bayanta, "shine, taceSa'adatu ce ke fama da shi" "haka ne" tace tare da iddasa ficewa, sallaman Ali suka kuma sukafice a natse....
Yana hangota ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofa ta shige, komawa gaba yayi ya zauna taredabadriver umurni, suna ficewa daga gidan ya gyara zama tare da faɗin "Hajiya ba zan miki
katsalandan ba ne, amma se nake ganin kaman be kamata ta zauna anan ba" murmushi Hajiyatasaki me faɗi tare da faɗin "nan yafi dacewa da ta zauna Munnir, me zata mana a can ɗin? Kokamanta ikon shi ce ita?" Tayi maganan a sukunance, girgiza kai yayi tare da faɗin "haka ne" "kar kadamu akan hakan, da ma na so mu zauna da ita na kwana biyu ne a can, mu ɗan fahimci juna, tomasu gida sun buɗe baki kaga ba se ta tafi inda yafi can-canta ba, ku dai yanzu aiki ya sama, kuyi
ƙoƙarin ganin komai ya tafi yanda yakamata" "in sha Allah Hajiya" yace a girmame, "yawwainanema ma Lubabatu alfarman zuwa Ethiopia bikin Arfat in dai babu damuwa" "babu komai HajiyaAllah ya kai mu, tace watan gobe ne ko?" "Eh haka suka ce, na so su dawo nan ayi bikin ma, toiyayen mijin sun ƙi amincewa" "da nan da can ɗin duk ɗaya ne Hajiya, fatan mu Allah ya zaunar
da su lafiya" "amen-amen" tace da kulawa....
Side ɗin ma'aikata ta wuce kai tsaye, tana shiga tace "an ƙara yanka mana kazan wahala, firgewada hannayen mu ya zama dole" "me ya faru Baba Maude?" Wata matashiyar budurwa tacecikeda son jin abinda ke faruwa, "wata ƴar wahalan aka kawo, masu kula da kitchen su hanzartasudafa mata abinci me sauƙin dahuwa, ke kuma Lawuza aikin ki ya ƙaru, zaki dinga kula da dukwani abu da take so, ki tashi ki je ki shigar da kayanta sama, lokacin tashin ki ya koma shidanayamma" "Baba Maude shida kuma!" Tace cike da mamaki, "eh shida, in ba zaki iya ba se ki ajiyeaikin gaba ɗaya ki tafiyanki, dubunki na waje na neman gurbin aikin waƴanda ke da kwalayendigiri" ta idda maganan tare da nufar ɗakinta, har ta kai jiki ta juyo tare da faɗin "kai tsayekujera a ƙaramin dining na ƙasa ku sanar da ita" "kar a jira ki?" Ɗaya daga cikin madafan tacetareda kallon ta, "me zan muku?" Tace tare da shigewa, sauke numfashi Lawuza tayi tare da nufar
ƙofar ficewa daga side ɗin cike da jimanta lokacin da aka ƙara mata....
"Wannan yaro dai be gajiya Baban Sani" Baba Tinene tace tare da ɗaukan gasashshen cinyar kazata kai baki, "ke dai bari Tinene, Allah ne ya kawo mu lokacin hutawa, shiyasa aka ce fa kar kamayaro mugunta, dan baka san wa ze ci gajiyan shi ba nan gaba, yanzu da yaran nan na riƙesudawani abu a zuciyana za su ko kalli inda nake a wannan hali da na faɗa me?" "Wallahi ba zasukallah ba, shiyasa ko da su Gude suke wannan haukan a lokacin nan na ce maka karka saurari
furucin su, dan za su saka ka nadama a gaba" "haka ne Tinene, Allah dai ya saka da alheri" yacetare da gyara zama ya kai wani naman baki, "ai Amina Amina mutumce, wannan mata Allahkaɗai ze saka mata" yace cike da rauni, "hmm Baban Sani ni zan faɗa maka wace wannanmatan, ka ga lokacin da Hajiya ta sako ni gaba babu me tausana se ita, in na je gidanta ina farfaɗamatayanda muka yi da ita se in ga ko a jikinta, ina gama faɗa mata zata fara mun nasiha da
nunashsheni hanya, tana jaddadamun kalman haƙuri da kauda kai, a lokacin bana iya hangoakwai ranar da Hajiya zata mun magana me daɗi, amma yanzu gashi komai ya wuce, wai ni daHajiya ne zamu zauna muyi magana na fahimta yanzu" ta idda maganan tare da girgiza kai, "ai
anyi rashi" Ali yace tare da jinjina kai, kwaɗo sallaman da su Gude suka yi ne ya katse musuzancen, miƙewa Baba Tinene tayi tare da faɗin "wa'alaikumussalam waye?" Ta idda maganantare da ficewa daga ɗakin....
Sakin baki da ido tayi tare da faɗin "to! Ku ce manyan baki ne damu yau, sannu ku da zuwa"
"yawwa" suka ce a daƙile, "yana nan kuwa?" Gude tace cike da basarwa, "ina zeje yana famadakan shi? Ku ƙarisa yana ciki" tayi maganan tare da ɗaukan buta ta wanke hannunta, wucewasuka yi ba tare da sun kuma cewa komai ba, suna shiga Gude ta buɗe ido tare da faɗin "ahlallai
Ali kana sha'anin ka, kaza a wannan damunan! kuma a wannan lokacin?" murmushi Suwaibatasaki tare da faɗin "Anty Gude ai ba sa jin damunan nan, Yaya Ali barka da wannan lokaci" ɗagokai yayi tare da faɗin "barka" "wallahi Ali ka yi mugun ba ni mamaki, a ce a kwantar da Sudaisyaukimanin sati uku amma baka ba labarin ka, kowa yaje ya dubashi banda kai, a haka kuma kukecewa a haɗa kai" Gude tace cike da jin zafi, kallo me cike da ɓacin rai da takaici ya bita da shi, "Allah sarki Gude a she na ka ya kwanta ciwo a kasa zuwa gaishe shi da ciwo, to ai masuƙafakezuwa, shi da ke kwance yau kimanin wata biyu ba ya da ƙafan zuwa ko ina ya za'ayi yaje yagaisheshi" Baba Tinene tace cike da takaici, da mamaki Suwaiba tace "wai tun wannan accident ɗindaLurwanu yace yayi be warke ba!" "Hmm" Baba Tinene tace dan tasan har in tace zata ba taamsa, ba zata furta me daɗi ba, tunda ya fara jinya ba wacce ta zo a cikin su se Jummai, tana maMunari
uzuri saboda ba a garin take ba, mijinta kuma kowa ya sheda me kulle ne, amma har labarinzuwan Habiba duba ƴarta suka ji, se dai ta kasa zuwa duba ɗan uwanta, "wallahi Yaya Ali bamuɗauka abun babba ba ne har haka, ni duk a zatona irin wanda ka saba yi ne kwana biyu ka cigabada harkokin ka" Suwaiba tace cike da jin ba daɗi, guntun murmurshi ya saki tare da kaudakai....
"Sannu ya jikin?" Tace da kulawa, "Alhamdulillahi" yace cike da rashin garaje, "to Allah yaƙaralafiya" "amen" yace a taƙaice, "kin zo kin mana tsegege a ka, dan Allah ba mu waje mu ganadaɗan uwan mu" Gude tace tare da bankawa Baba Tinene harara, komai ba ta ce mata ba seficewada tayi, "sannu Ali lallai kaji jiki, wata biyu a zaune" Gude tace cike da nuna damuwa, "Alhamdulillah ai, sauƙi ya samu" yace tare da kai nama baki "ma sha Allah haka muke sonji, shima Sudais na can na fama da zama da kwanciya" tace tare da gyara zama, "Allah ya ba shi
lafiya" yace cike da gajiya da ganin su, "ma sha Allah a she kuma yau Insiyyah ta tafi makaranta?"Tace cike da son bugun cikin shi, "ni ma haka na ji" yace a taƙaice, "au ji ma ka yi ba faɗa makaakayi ba? Lallai lamarin na ƙara gaba" Suwaiba tace tare da gyara zama, "to ya magananaurendaaka ce an ɗaura?" Gude tace idonta akan shi, "ya za'ayi in sani? Tare nake da su" yace taredakauda kai, "anya da wannan auren kuwa Yaya Ali? Kusan shekara da watanni da ɗaurawa ammayarinya ta kasa tarewa, wannan wani irin aure ne?" Suwaiba tace tare da kallon shi, ɗagowayayi
ya zuba musu ido cike da mamaki, ganin haka yasa Gude gyara zama dan duk a tunaninta
maganan su ne ya fara tasiri a zuciyan shi, "yanzu lamarin Abdussamad daga shi se Babiya, bawanda su ke sakawa a ciki, yanzu kai ma da kai tsaye akan abubuwan da ya shafe su watsi sukai
da kai a ƙarshe, tunda gashi har abu ze faru se dai kaji ba ka da darajan a kira a faɗa maka, Ali muƴan uwanka ne, kuma duk yanda muka kai ga lalacewa ba zamu manta da zamtowan mujini
guda ba, dole in wani abu ya taso mu haɗa kai dan cimma buri, Sudais na can gadon asibiti yanamaimaita mun sunan Insiyyah, duk da a baya ba wacce nafi tsana a yaran Abdussamad samadaita amma dole in zubda makamaina dan samawa Sudais farin ciki, ina kyautata zaton ya sametaze natsu ya daina duk wani abu da yake" ta idda maganan cike da fata, banda mai-maita
hasbunallahu wa ni'imal wakil babu abinda Ali da yawu ya gagareshi haɗiyewa yake, binsukawai yake da kallo me cike da tsoro da firgici....
"Yaya Ali Yaya Abdussamad yace duk hukuncin da ku ka yanke akan ƴaƴan shi dai-dai ne, danAllah ka nuna goyon bayanka akan a bawa Sudais Insiyyah, Sudais ɗanka ne shima kamanyandaSani da ƴan uwan shi suke a gareka, yaron nan tun tuni yake dakon son yarinyar nan" Suwaibatace murya a marairaice, "ita kuma Insiyyah fa?" Yace idon shi na yawo a saman fuskokinsu, "bamu gane ba?" Suwaiba tace a ɗan tsorace dan wutan bala'in da ta hango a idanun shi ba nawasaba ne "ita kuma Insiyyah mecece a gare ni!" Yace a kausashe, "ƴa" Suwaiba tace a tsorace, jinjinakai yayi tare da sakin murmushin takaici, "wato ga wawa kun zo wasa da hankalin shi ko?, Shi
Sudais ɗana ne, dan son da nake mai se in ɗau Insiyyah in ba shi saboda yayi farin ciki, ita kumata dawwama cikin baƙin ciki saboda ita ba ƴa ta ba ce, "ta dawwama cikin mutuwa dai BabanSani menene maraban dambe da faɗa, ai da makashi da mashayi ba su da ban-banci, danyanabuguwa se abinda hali yayi" Baba Tinene dake tsaye a bakin ƙofa tace cike da takaici....
"Me kike son cewa ne Tinene! Kar ki yarda ki yi kuskuren aibanta mun ɗa a gabana" Gudetaceakausashe, "tunda ya kawo tallan kanshi gidan Tinene se abinda ya gani, ƙarya aka mai ba ɗanshaye-shayen ba ne? Baban Sani wallahi ka yarda da wannan shirmen marabanka da makashi
babu ban-bancin" Tinene tace tare da sa kai ta wuce, "Yaya Ali ka fahimce mu, wallahi Sudaisbaze cutar da ita ba, dan yana matuƙar ƙaunanta" Suwaiba tace cike da lalama, "ki na da ɗiyamaceda tayi saura ai, me ze hana ki ba shi ita" yace idon shi akan ta, zare ido tayi tare da faɗin"ai beceyana sonta ba ne" ta idda maganan cike da fargaba, "yi mishi tura takaici mana, dan wallahi indai
ina shaƙan numfashi Sudais ba ze taɓa mallakan ɗaya daga cikin ƴaƴayenmu ba, ba na
Abdussamad ba, ba nawa ba, ba na Lurwanu ba na Balarabe ba, kuji da kyau, ku har kuna dabakin magana shashashu marasa hankali da sanin yakamata, to Insiyyah tayi mai tazarandabaze taɓa iya taddata ba, ba ita kawai ba da duk sauran ƴan uwanta, in wannan wawancinyakawoku to ku tattara ku fice mun daga gida, dan shedanin da ke zuciyoyin ku na daɗe da nemantsari
da shi, sannan ku nemawa ɗan ku magani da alama abubuwan da yake sha sun fara taɓa mishi
ƙwaƙwalwa" "Ali mu ka ke ciwa mutumci haka!" Gude tace da mamaki, "ba zaki fahimci komabasaboda ke shaɗaniyace, wanda yayi nisa ba ya jin kira, shiyasa ke ma ki ka kasa ji" "Anty Gudemuje dan Allah ba ze fahimci komai ba" Suwaiba tace tare da riƙota, "sake ni Suwaiba, sakeni inga ƙarshen rashin kunyar Ali yau" Gude tace tare da fizge jiki, "saketa munafuka, saketa
zantukan da taji be isheta ba ne neman ƙari take" "dan Allah Yaya Ali ka yi shiru, Anty Gudemuje" Suwaiba tace duk a dame, "ke se munafurci ya yi ajalin ki Suwaiba" da mamaki ta kalleshi
tare da faɗin "munafurcin me nayi!" "Aike suffanki ma kawai na munafukan farko ne" yacetareda banka mata kallon ƙyama, "Tinene zo ki tattarasu su fice mun a gida dan na gaji da ganinsu" yace da ƙarfi, "a zo a wuce dan Allah tunda ba'a samu shiga ba" Baba Tinene tace tare da gyaratsayuwa....
Fizge jiki Gude tayi daga riƙon da Suwaiba ta mata tayi kan Baba Tinene da huruji, cafkotaSuwaiba tayi tare da faɗin "Anty Gude dan Allah ki koma cikin hankalin ki" "barni in ci ubantaSuwaiba, inga wanda ya tsaya mata" tace a fusace, "to ke barta mana, ƙyaleta ta ga gatanaaBertuwa, wallahi da se kin yi danashinan taɓa ƙumbata ma ba jikina ba, marasa hankali datunani, ku zo ku fice mana daga gida ko ina taro shiryayyun anguwa su muku rakiya" ta iddamaganan da ƙarfi, da sauri Suwaiba ta ja Gude suka fice tana fizge-fizge, "mutanen nanbazasushiryu ba" tace tare da jan tsaki ta koma ga aikinta, sauke numfashi yayi cike da takaici taredajawo ruwa ya kafa kai....
Tana shiga ta ɗau wayanta dake yashe a saman gado ta lalibi number ta danna kira, ana ɗagawatace "an kawo sabuwa" "ya akayi haka?" Ta can ɓangaren aka ce da ƙarfi, razani na fita dagamuryan, "ban sani ba ranka ya daɗe ina zaune kawai aka kira ni" tace a ɗan kiɗime, "waya kawota?" "Hajiya ce" tace a hankali, "kin san abinda ya dace ai" "eh na sani" tace a girmame, sauke
wayan tayi jin an yanke kiran ta can tare da faɗin "Maude kinga ta kan ki, wannan mutuminbabarinki ki zauna lafiya ze ba, Hajiya kuma ba daina jawo miki aiki za tayi ba" tana kai nantaɗauwayan da ake communicating a cikin gidan ta ja number ta kara a kunni, a na ɗagawa tace"inanshirya abinci a sanar dani tukun" tana kai nan ta sauke wayan ta shige bathroom....
Tsaki wani dattijo dake zaune a damfareriyar kushin ɗin da ta isa ta kawo ya saki tare da ajiyewaya a gefen shi, "kai da wa kuma?" Wata farar dattijuwa tace tare da miƙa mai tea cupdaketururi, "Maude ce, wannan matan ba ta san wani aiki ma muka bata ba" yace cike da takaici, murmushi ta saki tare da faɗin "calm down Honey, abun duk be kai kana ɓata rai haka ba, inbazata iya ba se a bawa wata" "no sweetheart ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 109