tare da taɓa ta, ganin tayi barci yasata faɗin "kasan Anty" kallon junasukayi ko wacce ta kauda kai ba tare da tace komai ba....
Sallama wani matashi ɗan kimanin shekaru 30 da haihuwa yayi a madai-daicin tsakar gidanBabiya da Yaya ya gina mata tare da kutsa kai, sallama wacce ke tafe a bayan shi tayi cikinshigata mutumci madaidaicin basket riƙe a hannunta, kai tsaye inda Babiya da take zaune a samantabarma suka nufa, yana zama ya nuna ma wacce suka shigo tare kusa da shi tare da kallonBabiya da ke kallon shi yace "Hajiya a she kun dawo?" "Eh mun dawo, masu gida sun fatattakemu ba dole mu tattaro tsummokaran rayuwarmu mu dawo inda muka fi wayau ba, kai wallahi
Abdussamad be yi sa'an ƴaƴa ba" ta idda maganan cike da takaicin su Yasmin, "ban gane baHajiya! su wa ɗin suka kore ku!" Yace da mamaki, tsaki taja tare da faɗin "kayya Lurwanunemanjan zance ka ke Suwaiba yi mai bayani" buɗe baki Suwaiba tayi za ta fara bayani ya dakatar daitada faɗin "dallah rufe mun baki, Hajiya karfa ki dinga ɗaukan zantukan mutanen nan fa" yaiddamaganan tare da kallon Babiya, "tunda mun zama gamau dole kace karta ɗauki maganar mu, toAllah yasa a gabanta komai ya faru" Gude tace cike da takaici, ƙwarai kuwa a gabana ne Lurwanu, wallahi yaran nan a tsakiyan jama'a suka mana tijara ba abinda suka manta ba su faɗa manaba, kai har fa gori suka mana wai Abdussamad ba shine da wannan gidan ba uwar su ne da shi" Babiya ta idda maganan tare da kama haɓa....
"An zo wajen, wato zuwa ku ka yi ku ka barbaɗa halin na ku, wai yaushe zaku fahimci kungirmane, wannan mummunan ɗabi'an tun da fararan sahu ku ke gashi girma ya riske ku amma kunkasa dainawa, menene amfanin tashin tashinan bayan wacce ku ke buɗewa murya da shatatamata tijaran Allah ya amshi abin shi? dasawa za kuyi akan ƴaƴan ɗan uwanku saboda bakwadatunani? Wai ni yau ina son jin abinda baiwar Allahn nan ta muku ku ke wannan adawandaitahaka ma tukun" ya idda maganan rai ɓace, "ba ta girmama mana uwa" Suwaiba tace tare dakauda kai, "dalla rufe mana baki, ke girmama uwar taki ki ke? In ana maganan girmama iyayezaku saka baki ne, nan zata muku magana ku dinga ɗaga mata murya kuna daddanƙara matamagana san ranku kaman ku ku ka haifeta ba ita ta haifeku ba, tsakani da Allah Hajiya kuntaɓafaɗa in faɗa da Anty Amina?" Yace tare da kallon Babiya, "duk me ne ne na wannan maganganunhaka Lurwanu bar maganan" Babiya tace cikin son a bar batun, "a'a Hajiya ai sun tsokanoyakamata a basu amsa, wannan matar harta koma ga mahakiccinta ba ta taɓa maida mukudaduk wani baƙar magana da ku ke faɗa mata ba bare ta maidawa Hajiya, sannan saboda rashinhankali kun zo kun miƙe ƙafa kuna faɗin bata girmama muku uwa, ke ba ki ji nauyin faɗinhakanba ma" juyawa ga Babiya yayi tare da faɗin "tsakani da Allah Hajiya abinda ki ka yi be kamataba""me kuma nayi Lurwanu?" Babiya tace tare da kama haɓa, "gaskiya ne Hajiya in ba mu faɗamiki
ba ba wanda ze faɗa miki, zaman makokin nan yakamata a ce ki zauna har ayi addu'an bakwai
tukun, in ma dawowan zaki yi se ki dawo, amma daga uku se ki tattaro ki dawo, kin san YayaAbdussamad ba ze ji daɗi ba" "to ya zanyi ne Lurwanu sun ce in fitan musu daga gida na uwar sune" Babiya tace a sanyaye, "ai wannna yarinyar Yasmin ba ta da hali ko kaɗan yanda ki ka gaAmina haka take" Gude tace rai ɓace, "a'a Anty Gude baki san wacce ta biyo Amina ba ma ashe, ai kinga wannan Insiyyan tafi ko waccen su iya rashin ta ido, dan tana cikin halin firgici neammada ita ta buɗe baki a wajen nan da kin fahimci wacce tayi gado" "wai me ku ke yi ne anan? Gidanmakoki ku ka zo, kuma kun dawo se ku tattara ku koma inda ku ka fito" Lurwanu yace cikedatakaici, "ai seka jamu, ka wani kwaso mata zagai-zagai ka zo, ance maka ko ina ake zuwa damacene" Gude tace rai ɓa ce, dariya Suwaiba ta saki tare da faɗin "na raji ne, kin san ana tsakiyanabun, ki bari ya bi jiki" "to ku tsaya, wallahi tun wuri ku cire idanunku akan matata, shirme da
haukanku da Yaya Abdussamad ya ɗauka ba ɗauka zanyi ba" yayi maganan da kausassashshenmurya....
Juyawa ga Babiya yayi tare da faɗin "kinga irin abun ko? Indai za ki cigaba da ɗaukan zantukansu wallahi se sun rabaki da ɗanki me temakon ki, haba Hajiya menene Yaya Abdussamadbemiki
ba a rayuwa? Gaba ɗaya cikin mu tara da ki ka haifa ba wanda ya miki abinda ya miki, dukcikinmu ba wani ƙunbiya-ƙunbiya ya fi mu biyayya gare ki, shin ya ze ji a lokacin da ya fahimci bakyasan yaran shi, ko tsanan da ki ka wa mahaifiyarsu ya dawo kan su, kaman fa mu ne wani kenuna
mana ƙiyayya ƙiri-ƙiri kina gani ya zaki ji?" Yace idon shi akan ta, "zanji ba daɗi mana" Babiyatace murya a sanyaye "to ina tabbatar miki yanda za kiji haka Yaya Abdussamad ze ji, ze mafi jinzafi dan mahaifiyar shi ne ta tsani jinin shi, ki bar ɗaukan zantukan da ba su da tushe da makama, ki dinga yanke hukunci da abinda ki ka gani a zahiri" "to shi wannan abinda suka aikata baazahirin ta gani ba!" Gude tace tare da banka mai harara, "wallahi Hajiya na san in nayi rantsuwaba zan yi kaffara ba, kafin yaran nan su tanka su se da suka ƙure hakurin su, ba yanda za'ayi aceduk cikin masu zaman makoki su rasa waƴanda za su ci wa mutumci se ku, yaran nan fa dahankalin su, da tunaninsu, ba kara zube suke ba, kuma ko koran za su yi na san ba dai sukoreki
ba, se dai in su tunda ba su kama girman su ba, ace banda zubda girma yaran da ku ka haifakukajuya ku tsaya kuna ja'in ja da su, wannan wani irin abin kunya ne" ya idda maganan cike datakaici....
"Ai gunda ka zauna a gaban matar ka kana ƙare mana tanaji, gunda ka nuna mata ba mudadaraja da kima a idanun ka" Gude tace a harzuƙe, buɗe baki yayi zeyi magana Babiya da kalamanshi suka shigeta tace "bar su Lurwanu dan Allah kar kace komai, "shashasha mara saninciwonkai, kai yanzu me ka yi? Ai duk lalacewan mu gaba muke da kai, amma ka zo a gaban matarkakana aibanta mu da walaƙanta mu" Suwaiba tace cikin harzuƙa, "Hajiya bari mu tafi, damabayanidar da sallahn la'asar ne na leƙa cikin gidan aka ce mun ai kin dawo gida, shiyasa na ce bari inleƙo nan ɗin, ga abinci nan na san ba lallai sun dafa ba" "ba mu dafan ba, se ka zo ka dafa" Suwaiba dake jiran ya furta tace rai ɓace, "to dama me ku ka iya mata banda neman lalatamatatunani, gashi nan na girka tunda na sa wanda na isa da ita ta girka" yayi maganan hankali
kwance, "na ce Lurwanu ka yi shiru ko" Babiya tace tare da kallon shi, "shikenan Hajiya nayi shiru, gaisheta mu tafi" yace tare da kallon matar shi, "wawa shashasha" Gude tace cike da hargowa, "shin Gude ba zaki yi shiru ba ne? Shi na ce yayi ya yi ku meyasa ba za ku yi ba?" Babiya tacetareda kallon ta, "yama za'ayi ki ce in yi shiru Babiya bayan ki na jin yana farfaɗan mana maganandayaga dama, waye shi? me akai aka yi shi, ba ya ci da ni ba ya sha dani ba zan tsaya yana farfaɗanmin maganganun banza ba, ke da yake ciyarwa se ki yi ta lallaɓashi" tace cike da ɓacin rai, "toni
yana ci da ni kuma yana sha da ni ba ki yi ƙarya ba, se dai ba dan yana ci da ni na ce ku yi shiruba, dan bana son jin kuna cigaba da cacan bakin ne, yanzu matarshi ce ya ɗakko ya kawo ammakonauyinta ba kuji ba ku ke zubda girma" "ruwanshi Babiya kema ki ka ganta, ni ban lura ya zodawata aba ba ma" Suwaiba tace na ta zuciyan a dugunzume, sakin baki matan Lurwanu tayi tanakallon su, murmushi Lurwanu ya saki tare da faɗin "to Hajiya ga masu girmamaki nan, waƴandasuka tsani wata dan ba ta girmamaki, su yanzu me suke kenan?" Jinjina kai Babiya tayi taredafaɗin "da gaskiyanka Lurwanu duk tsayin shekarun da muka ɗauka tare da Amina ba ta tabadaga ido dan rama abin da nake mata ko da da kallon banza ba, amma yau ga ƴaƴan cikinasuna
tsaye a kaina a gaban sarakuwata suna farfaɗamin magana" "karki damu, kar ma ki sa abinaranki, inda sabo ai kin saba, menene wani abu sabo daga ciki? daɗin abun sun haifa, kumakomekayi se an maka" "kaima zaka haifa kuma duk abinda kayi za'a maka" Gude tace tare da jantsaki, "Allah ya tabbatar Allah ya so, dana more, Hajiya su tattara su koma gidajen su, babu me ci dakea cikin su, ba za su zo su cinyake abinda ƴaƴanki suka kawo miki ba" yana kai nan ya juya, gaidaBabiya matarshi da jikinta yake rawa tayi a ɗarare, amsawa tayi da kulawa, juyawa tayi dazumman gaidasu ko wacce ta ja tsaki ta kauda kai, "tashi muje, ai kin gaida wacce yakamata, itace farillan waƴan nan duk nafilfili ne se kinga dama" yace a natse tare da riƙo hannunta sukafice.....
"Kina dai gani a gabanki, ya nunawa matarshi rashin darajta mu da mutumta mu, ya za'ayi taganmu da gashi, da zamu tsaneta kuma se a ce bama da ɗabi'a me kyau" Gude tace da ƙarfi, ɗaukanbaske din da matar Lurwanu ta ajiye mata a kusa da ita Babiya tayi ta wuce ɗaki ba tare datacemusu komai ba, kallon juna suka yi da mamaki tare da bin bayanta....
Drivernta na daidaita parking a parking lot ɗin gidan ta buɗe ta fito, tadda Maude tayi tsayefuska yalwace da murmushi, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "Maude ya gida ya famadaaiki?" "Alhamdulillah Hajiya ya ƙafa?" "Alhamdulillah ƙafa da sauƙi, tunda na dawo ganinlikitabe ƙara tashi ba" "ma sha Allah, Allah ya ƙara lafiya me albarka" tace cike da farin ciki, "amenMaude a haɗo mai abinci yanzu ki kawo mun" "ai ban kwashe ba Hajiya" tace a girmame, "tokinkyauta bari in ƙarisa ciki" "to a fito lafiya Hajiya" tace tare da juyawa tayi side ɗin su Hajiyakumatayi side ɗin shi....
Da sallama ta shiga parlorn, amsawa me alhakin gyara parlorn yayi tare da duƙawa har ƙasayagaidata, amsawa tayi a mutumce ta nemi waje ta zauna, "yallaɓan ya shiga ciki ko a mishi
magana ne?" yace cike da ladabi, "kar ka damu, jeka abunka" tace tare da zaro waya, dannakiratayi ta kara a kunni, be daɗe yana ringing ba aka ɗaga, "ina jiranka a parlorn" kawai tace taredazare wayan ta katse kiran, be jima ba ya fito sanye cikin kayan barci me taushi da laushi, kallontayayi da idanun shi da suka canza launi cike da mamaki, yana shirin zama ta miƙe tare da faɗin"muje daining" ba musu ya dafa mata baya, suna isa taja mai kujera ya zauna ta zari platetasakamai malmalan tuwo da miyan ɗanyen kuɓewa da yaji nama, ajiye mai cokali tayi a gefe dantasan be cin tuwo da hannu, ɗauka yayi a natse ya fara ci baki ɗauke da bismillah, bin shi kawai
take yi da kallon tausayi, tasan daurewa kawai yake amma shi kaɗai yasan me yake ji, ita kantada ke amsa sunan uwa gareta mutuwan ya daketa bare kuma shi ne amsa sunaye da yawa, sedayaci rabi da kwata na malmalan sannan ya ja jiki a natse, ruwa ta zuba mai ta miƙa mishi, amsayayi ya kai baki, "kasha magani?" Tace da kulawa, jinjina mata kai yayi tare da ajiye kofinyajakujeran baya ya miƙe, miƙewa tayi ta dafa mai baya, a parlor suka yada zango,....
Gyara zama tayi cike da dattakonta tace "ina me baka haƙuri akan hukuncin da na yanke kai
tsaye ba tare da na tuntuɓeka ba, haka abin ya zo, ba na da daman ƙiyawa dan zuciyata bazatataɓa zama lafiya ba indai na ƙi amsa wannan alfarma da aka nema daga gare ni" jinjina kai yayi
ba tare da yace mata komai ba, gyara zama tayi tare da faɗin "Sahabee Insiyya ta mutu dagaske, ta tafi kaman yanda wanda suka tafi suka tafi, kar ka cigaba da yaudaran kan ka, komai yaƙare, dama na faɗa maka wataƙila Allah be ƙadadara rayuwarku kai da ita a ƙarƙashin inuwanaureguda ba ne, ta tafi da ciwon kansar jini" zamewa ƙasa yayi jikin shi na kyarma, so yake ya fasheda kuka me ƙarfi wanda ze amsa garuruwa da ƙauyukan ƙasar Ɓadamayo, amma ya kasa, bandarawa ba abinda jikin shi ke yi, tashi Hajiya tayi a hankali ta ƙarisa kusa da shi tare da kamoshi, ƙanƙameta yayi tare da sakin marayan kuka, kuka yayi sosai wanda raban da yayi irin shi tunranar da Daddy ya zo mai da batun tace ba zata aure shi ba, "ka yafe mata, ta ɗau tsayinshekarutana azabtuwa da dakon nadama da danasani, yafiyanka take nema Sahabee" Hajiya tacetaredagoge mai hawayen da suka gangaro, janye jikin shi yayi a natse tare da faɗin "na daɗe da sanar
da ita na yafe mata" "ba ta gamsu ba ne, wataƙila kai ma baka gamsu da yafiyan da ka mataba" guntun murmushi ya saki tare da faɗin "na yafe mata" "Allah yasa hakan, se abu na biyudayakawo ni" tace tare da miƙewa ta koma inda ta ajiye jakanta, miƙewa yayi ya koma samankujera, miƙa mai takardan da ta ciro daga jaka tayi a natse, amsa yayi a natse ya buɗe....
Yana gama karanta abinda takardan ya ƙumsa ya ajiye a teburin gaban shi tare da faɗin"bansanme mutanen nan suke nufi da ni ba, na faɗa musu bana da sha'awan abun nan ko kaɗan" yayi
maganan cike da takaici, "yakamata ka zurfafa tunaninka akan batun, kana da sauran lokaci dazaka yi tunani yanda yakamata, da farko ni ma ban amince musu ba, se dai bayan tafiyansudabani lokaci da suka yi akan nayi tunani, se na hangi fa'idan hakan, Sahabee a ƙasan nantalakanafuskantar matsayin rayuwa, takai talaka na iya ɗaukan guba ya kashe kan shi dan halinmatsi, abinci yayi tsada ta kai talaka ba ta iya siye" tun da ta fara maganan ya kafeta da ido har sedatakai aya, fesar da numfashi yayi a hankali tare da faɗin "Hajiya mu ma abin mu duba kanmune, harka ta mulki ba ta da sauƙi, ba mu santa ba daga nesa muke hangen ta, muka ce zamujefakanmu ciki kai tsaye zamu iya illata rayuwarmu ba tare da mun sani ba, mutanen nan sun iya romanbaka, ba zan yarda ayi amfani da ni bisa rashin sani a cutar da mutum ko guda ɗaya ba" yayi
maganan cike da tabbaci, murmushi ta saki tare da faɗin "kaga abinda na hanga kenan, dalilindayasa na amince kenan, kana da daman karantar abun a natse tunda da saura kafin me ci yasauka, kusan shekaru biyu ya rage mai, kafin cikan lokacin na san zaka nemi sani akan abun, fatanadai
ka amince" jinjina mata kai yayi tare da faɗin "zan nazarci lamarin" "shikenan" tace tare damiƙewa, saɓa jakanta tayi tare da juyowa a natse tace "Baban yarinyar nan ya nemi alfarmantazauna da su ta kammala sakandire tukun" lumshe ido yayi ba tare da yace komai ba, ba tadamuda yacen ba juyawa tayi ta kama hanya, miƙewa yayi a natse ya dafa mata baya, har parkinglot
ya rakata, sallama suka yi ya ja baya kaɗan, dan su wuce, suna ficewa ya juyo ya koma ciki.....
Yanayin da suka fito da safe ba wanda be ji daɗin shi ba daga kan Yaya su Lailah da sauranmaƙofta masu zuwa ta'aziyya, haka aka cigaba da amsan makokin Anty cike da kewanta, yautagama gobe addu'an bakwai zaune suke a general parlor gaba ɗayan su, ta waje kuwa suBabaMari ne ana ta haya-haya da aikin soye-soye da ƙulle-ƙulle, gobe ku shirya zaku tafi school" Yasmin tace ma su Nafisat dake zaune a gefe, ɓata fuska tayi tare da faɗin "an ba mu styleɗinkitso" tayi maganan cike da rashin jin daɗi, "se dai su miki haƙuri a wannan satin kam" Farisat
tace tare da kallon ta, "an faɗa musu abinda ya sameta ma fa" Yasmin tace tare da jawo Umar
jikinta, sallama Mami da su Safinat suka yi a parlorn, amsawa suka yi idon su akan su, murmushi
Mami ta saki tare da faɗin "Alhamdulillah, ba ƙaramin daɗi nake ji ba da na ganku haka" tayi
maganan tare da zama kusa da Sahabee, murmushi suka sakin mata ba tare da sun ce komai ba, "ina Insu?" Tace tare da kallon Farisat, "tana ɗakinta" tace kadaran kadahan, "lafiya dai ko?" Tacetare da kallon ta, "lafiya lau ina ga sallah taje yi" "to ma sha Allah, ma sha Allah" tace cikeda
farin ciki, murmushi Khadijatu ta saki tare da faɗin "Alhamdulillah ai ƴan albarka ne masujinmagana" "gaskiya ne wannan" Mami tace zuciya cike da farin ciki, fitowa Insu tayi a natsetasamu waje ta zauna tare da ɗaga mata gaisuwa a natse, amsawa tayi da kulawa, "Insu Yasminsister Farisat ya ƙarin haƙuri?" Rahma tace tare da kallon su, "Alhamdulillah" suka ce baki ahaɗe, "Allah ya gafartawa Anty" tace tare da gyara zama, "amen" suka ce cike da jindaɗin addu'an, haka suka gaggaisa da juna a mutunce, miƙewa Mami tayi dan zuwa taya su Baba Mari aiki, miƙewa su Safinat suka yi tare da dafa mata baya.....
Shigowa Sadam yayi a natse tare da faɗin "gasu can" miƙewa Yasmin tayi ta jawo hannunSahabee a natse suka fice kai tsaye side ɗin baƙi suka nufa, tana shiga ta tadda su cike daparlorn, neman waje tayi a gefe ta duƙa, tare da gaida su, gyara zama Shureim yayi tare da faɗin"yaƙarinhaƙuri?" "Alhamdulillah" tace kai a duƙe, "Allah ya gafarta mata" suka ce baki a haɗe, "amen" tace a hankali, "ga members ɗin Aminan juna nan sun zo muku ta'aziyya gaba ɗayan su" Annur
yace idon shi akan ta, "mun gode Allah ya saka da alheri ya bada lada" tace murya na rawa, "amen dan Allah ƙanwata kar ki yi kuka" yace tare da kallon wacce ke zaune kusa da shi, miƙewatayi tare da ma sauran alama, ɗakko babban kulan da suka zuba waina da fanken da suka yi sukasassaka aledan dake dauke da sunan group ɗin suka ajiye a gabanta, ɗakko katan-katanɗinlemu da ruwa suka yi suka ajiye, murmushi Zubair ya saki tare da faɗin "daga Aminan junaAllahya kai ladan gareta" fashewa da kuka tayi tare da cukuikuye kanta a hijabin jikinta, gaba ɗayashiru suka yi tare da zuba mata ido....
Sallama Sadam da ya sanarwa su Yaya da su Lailah dake shirin tafiya suka yi, da sauri Farisat taƙarisa tare da faɗin "me ya faru!" Murmushi Yaya ya saki ya gewaye kayan ya shige ciki a natse, gaisawa suka fara da shi a mutumce, bayanin komai Yasmin ta ma Farisat, share hawaye tayi taɗago tare da faɗin "mun gode Allah ya saka da alheri, Sahabee jeka kira Sa'adatu da su Hasinasukwashe" da sauri ya tashi ya fice, gyara zama Sagir yayi tare da faɗin "anyi addu'an ne?" "Ehtunasuba aka yi" Salwa tace cike da yaba sanin yakamatan su, "Allah ya jaddada rahma gareta"
"amen ya rabbal alamen" suka ce baku na a haɗe, ɗaga hannu Shureim yayi tare da faɗin"bari
mu mata addu'a" nan kowa ya ɗaga na shi, tunda ya sadda kai yake zubo addu'o'i nagartattuwanda kana ji kasan anginu da ilimin mahammadiyya, se da ya ɗau kusan mintina a shirinkafinya ƙarƙare da nema mata aljannar mahaliccinta, shafawa suka yi zukata na faɗaɗuwa da yalwa, "to zamu zo mu wuce" Annur yace tare da miƙewa, godiya suka musu sosai Farisat da Yasminsuka bi su dan rakiya...
"Nagode sosai" Yasmin tace a hankali, murmushi Annur ya saki tare da faɗin "ba na ce miki babugodiya a tsakanin mu n8a ƙanwata?" Jinjina kai tayi tare da faɗin "kayi haƙuri" murmurshi yasaki
tare da faɗin "ba komai, ga Antyn ki in sha Allah" yayi maganan tare da nuna mata Laɗifa daketsaye kusa da shi, ɗago kai tayi ta kalleta tare da sakin mata guntun murmushi, murmushi tasakin mata tare da bata hannu a natse, "Laɗifa" tace idonta akan fuskanta, "Yasmin" Yasmintacea sanyaye tare da bata nata hannun, "to sister se mun ƙara zagayowa" Zubair yace tare dakallonFarisat ya saki murmushi, murmushi ta sakin mai tare da faɗin "Allah ya baku iko mun godesosai" dawowa kusa da Farisat Yasmin tayi tare da bin su da ido, haka suka shishshige motocinsusuka ɗau hanya, suna juyawa da nufin komawa ciki muryan Salman ya doki kunnuwan su....
"Kushi" yace a hankali, duk da ba su gane wa aka kira da sunan ba amma fahimtar mamallakinmuryan ya sa su juyowa a natse, murmurshi ya sakin musu tare da ƙarisowa a natse, "dagainakuke?" Yace tare da kallon Farisat da ta kauda kai daga kallon shi, "rakiya muka yo" Yasmintacetare da kallon shi, "sune ƴan Aminan junan?" Yace a natse, "eh sune" tace tare da juyawa tashige, murmushi ya saki tare da matsawa kusa da Farisat kaɗan, "Kushi" yace ƙasa-ƙasa, ɗago kai tayi
ta mai kallan sakanni ta kauda da sauri, murmushi ya saki tare da faɗin "kin rame sosai" "hmm" kawai ta ce a hankali, "please Kushi mu yawaita yin mata addu'a" yace cike da magiya, "munayi" tace a hankali, "Allah ze amsa, in sha Allah Anty tana cikin aminci" "in sha Allah" tace cikedajindaɗi, "mu shiga ciki na tsaidaki a waje" jinjina kai tayi tare da juyawa ta tura ƙofan suka shige, suna shiga idon su ya faɗa kan su Lailah da suka fiffito da akwatuna....
"Anty Lailah ba dai yau za ku tafi ba!" Salman yace cike da mamaki, kauda kai tayi idanuntanatara ruwan hawaye, "ni ma yanzu tambayan da na gama musu a ciki kenan" Baba Mari tacecikeda sanyi, "Anty Lailah tafiya za ku yi da gaske!" Farisat tace tare da isa kusa da su, kamo
hannunta Khadijatu tayi tare da faɗin "zamu dawo nan kusa Farisat, Yaya ne yace yakamatamutafi yau, mu ma ba mu so tafiyan ba" kallon Yaya dake tsaye riƙe da hannun Insu Farisat daYasmin suka yi cike da tambayoyi, "kar ku damu, za su dawo nan kusa idan suka kimtso, wannan5yafiyan ya zo musu ba tare da shiri ba, sun baro yara a can, idan suka kimtso zuwa su zokoshekara suyi damu" jinjina mai kai suka yi cike da gamsuwa, ɗago wayanta dake ringingSalwatayi tare da goge hawaye ta ɗaga ta kara a kunni, "gani nan" tace tare da sauke wayan ta
rungume Insu "zan dawo kar ku yi kuka da yawa" tace murya na rawa, tana sakinta ta shafakanUmar ta fice da sauri, saboda ba ta so su karya mata zuciya, ga mijinta na waje na jiran
futowanta....
Ƙarisowa Ibrahim dake janye da akwatin kayan shi yayi tare da kallon su Lailah da kulawayace"ku mu je, 5 jirgin ze tashi, huɗu da rabi ya wuce" "Ibrahim kaima tafiya zaka yi!" Yasmintacemurya a karye, jinjina kai yayi a hankali fuska kadaran kadahan, "saka number na kar ka mantadamu dan Allah" Yasmin tace tare da karanto mai number hawaye na zarya a saman fuskanta, kallon Insu yayi tare da faɗin "muna nan muna jiran zuwanki" ba abinda ta iya ce mai se binshi
da ido da tayi, "shikenan mu kuma kowa tafiya ze yi ya bar mu, Anty ta tafi kowa ma ze tafi, BabaMari dan Allah kar ki tafi ki bar mu" Farisat tace cikin rishin kuka tare da rungumo Baba Mari, kuka Baba Mari ta saki tare da faɗin "ina tare da ku ba inda zani" jawo Sa'adatu dake sharɓankuka a gefen su tayi tare da faɗin "Sa'adatu dan Allah kar ki ce zaki tafi kema" "mutuwa zerabani daku, amma da raina da lafiya na ba zan gujeku ba" Sa'adatu tace murya na rawa, kuka sukegaba ɗayansu ba wanda be koka ba, hatta Salman ya kasa control ɗin na shi hawayen, "kumuje" Yaya da ya goge na shi hawayen yace tare da nuna musu mota, haka suka shishshige jikkunaamace, motan su na fita a gidan Insu ta zube, ba wanda ya kula suna can suna kuka me taɓazuciya, Sadam da ya jiyo dan kama mata hannu su koma ciki ya tadda ta a zube, ihu ya saki da ƙarfi tareda yin kanta, nan kowa ya juyo, mummunan ganin da suka yi ne ya ƙafar da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 109