bar wajen...
Sauke numfashi me sauti Maude da ke tsaye ta na bin su da ido tayi cike da mamaki tare dafaɗin"wannan mutumin akwai ɗan banzar rawar ƙafa, daga ganin ƴarinya se wani ɓashe baki yake, Allah na tuba ko maza sun ƙare a duniya iyayenta barinta za suyi ta aureka, matarka fa
hadimanta ne" tayi maganan tare da shigewa ciki dan marabtan Insu...
Zaune ta taddata Feita ya ajiye mata ruwa, da sauri ta ƙarisa tare da faɗin "maraba da dawowaInsu" murmurshi ta saki tare da ɗago kai cike da yanayinta tace "maraba da shigowa BabaMaude, ya gajiyan aiki?" Murmushi ta saki tare da faɗin "ke za'a tambaya gajiya Insu, ke da ki ka shawowannan rana" murmushi ta saki tare da faɗin "a'a Baba Maude wani rana kuma, abinda a motanake" "haka ne, Hajiya ta kira ɗazu babu jimawa take tambayan ko kin dawo? Na ce tukunnadai
wata ƙila ba ki gama abinda ya kai ki ba ne, tace to! amma oga Abubukar ya tabbatar matadakun gama abinda za kuyi tun 4" ta idda maganan idonta na yawo a saman fuskan Insu, murmurshi Insu ta saki tare da faɗin "mun biya shan ice cream ne, dan yau an yi rana sosai, kai
Baba Maude mutumin nan yana da kirki sosai" tayi maganan tare da miƙewa...
Sakin baki Maude tayi tare da bin ta da ido, murmushi ta saki tare da nufar stair ta fara takawa, "ai yana da kirki kam kullum matar shi na faɗan kirkin shi" tace da sauri, danne dariya Insutayi
tare da juyowa ta ɗaura mamaki a saman fuskanta cikin nuna zallan mamaki tace "mata! Damayayi aure ne! A haka kaman be taɓa aure ba" ta idda maganan tare da kama haɓa, murmushi
Maude ta saki tare da faɗin "ai Lawuza matar shi ce, tana matuƙar ƙaunarshi da kishin shi" tayi
naganan idonta ƙyam a saman fuskan Insu...
"Anty Lawuza da na sani?" tace ido waje, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "ita dai, har sa yaransuuku" jinjina mata kai tayi ta juya fuska ta sakin dariya mara sauti...
"A shirya daining ne?" Tace zuciya ƙal, "no" tace tare da fara taka stair's a natse, tana shigewaɗaki ta cire takalmi ta zare veil ta ajiye jaka ta saki dariya me sauti tare da zama a samansofa... Murmurshi Maude ta saki tare da faɗin "namiji dai ba kunya gare shi ba, yanzu banda rashinkunya na namiji matarka na kusa ka rufe ido kana ta rawan ƙafa akan ƴar cikin ka, wannandanawa tafi ƴarka ta fari, ita kuma ta ga kyakykyawa ta ruɗe se wani washe baki take, to da matarshi"tana kai nan ta juya ta fice.... Kusan tare su Yasmin suka shiga asibitin da Yaya da Balarabe, suna shiga suka tadda suzazzauneko wa da abinda ya ɗauke mai hankali, "ta haihu?" Yasmin tace cike da fargaba, kallon susukayi
cike da mamaki, "kun dawo?" Babiya tace tare da nuna musu kusa da ita, suna niyyan zamanurseta fito, ba ta natsuwan su suka yi gaba ɗaya, "Zuwaira Hamidu" tace tare da kallonsu....
Jinjina mata kai suka yi ƙiraza na bugawa, "ku yi haƙuri Allah ya amshi abin shi" tana kai nantakoma ciki, sakin baki suka yi gaba ɗayan su suka zuba ma inda ta bi ido, ihun da Habiba ta saki neya dawo da su cikin hayyacin su, nan fa masu kuka suka fara, Yasmin da Farisat kuwa rasamameke faruwa suka yi, dan kai tsaye ƙwaƙwalwalensu suka daina aiki....
Jawo su Yaya yayi ya rungume, cike da rarrashi, dan shi kan shi ba ƙaramin rauni zuciyanshi tayi
ba, danne kuka kawai yake, "shikenan Babiya Zuwaira ta mutu" Habiba tace cikin gunjinkuka, jawota Babiya tayi tare da fadin "kar ki yi kuka, yi mata addu'a" girgiza kai tayi tare da faɗin"ni
nayi sanadiyyan mutuwarta, ni ce silar mutuwarta Babiya, ina ma ni mutuwar ta ɗauka baitaba, ina ma ina da daman goge abinda ya faru, ina ma da a mafarki wannan abun ya faru, ina mainada tsumman goye ƙaddara da na goge na Zuwaira ta koma ga ubangijinta a tsarkakakka" taiddamaganan muryanta na sarƙewa, "ba ke ba ne Habiba, ba ke ba ne, Allah ya ƙaddara komai tunkafin ta zo duniya" girgiza kai tayi tare da faɗin, "da na tsawata mata lokacin da take rashinji dahakan be faru da ita ba" tayi maganan da ƙarfi tare da sakin kuka, yanda take kuka yasa suYasmin ɓarkewa da kuka da ƙarfi, dan mutuwan Anty ne ya dawo musu sabo, gani suke kamanalokacin ake sanar da su mutuwarta...
"Balarabe je ka ji me ta haihu ne? Sannan ka jiyo mana abinda za su buƙata kafin su ba mugawar, Abdussamad daure ka ƙarfafa zuciyarka, kwashe su ku tafi gida, muna bayan ku" Babiya tacetare da kallon shi, ko kafin yace wani abu Jummai ta shigo ita da babban ƴarta a ruɗe, ganinhalin da suke ciki ya sa faɗin "me suka ce?" Tayi tambayan cike da fargaba, "Zuwairatu ta tafi
Jummai" Babiya tace cike da danne na ta raunin" zubewa a wajen tayi tare da fashewa da kuka....
"Allah sarki Zuwaira a she ajalinki ki ka ƙumsa, Allah sarki a she maganan da ki ke yawanmai- maita min na ba zaki haifi cikin jikin ki ba gaskiya ne, Allah ya gafarta miki, Allah ya amshi tubanda ki ka yi dan shi, Allah ya amshi shahadarki" ta idda maganan cikin rishin kuka...
"Haƙuri za mu yi dan dole ne a gare mu, ku tashi mu tafi gida, sun ce ba ta kai ga haihuwa ba, sannan ba abinda za mu biya za'a saka ta a mota mu tafi" Balarabe yace cikin sanyin da yariskeshi, haka suka tattara suka yi gida zuciyoyi a mugun raunane....
Comments fans 🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Eighteen
"A ƙara ne?" Lawuza dake duƙe gaban Ibrahim tana zuba mai abinci tace tare da kallon shi, girgiza kai yayi tare da faɗin "ya isa" ajiye coolern tayi ta ɗakko madai-daicin bowl ɗin da tazubamiya ta ajiye mai... Matsawa gefe inda su Fatima ke zazzaune suna cin abinci tayi ta zauna tare da kallon Ummadake mata magana, "kin san ban jima da cin danbun da Magajiya ta aiko mun ba, cikin a cikeyakese shan ruwa da nake ta yi" ta idda naganan tare da sakin ƙaramar gyatsa...
"Ai shi dama dambu sai da ruwa kusa" Umma tace tare da kallon ta, "Ummi na ƙoshi" Imantacetare da miƙewa ta dawo kusa da Lawuza, "me ki ka ci kenan Aminatu?" Umma tace tare dakamahaɓa, "na lura kwanan nan ba ta son cin abinci sam, kullum se ta dawo da lunch ɗinta da yawa" Lawuza tace tare da shafa fuskan Iman da ke zaune a jikinta, miƙa mata hannu Ibrahimyayi tareda faɗin "zo Anty" da sauri ta tashi tayi inda yake...
"Meyasa bakyason cin abinci?" Yace tare da kwantar da kanta a ƙirjin shi, "ba komai Daddy" tacecike da yarinta, "a'a da komai, ko ki na so in daina kai ki park ranar Sunday?" Girgiza kai tayi tareda shagwaɓe fuska, "to in ki na son a dinga fita dake ki dinga cin abinci, in ba haka ba, zanfitadasu Anty Zarah ke mu barki gadin gida" "zan dinga ci" tace kamar za ta saki kuka, "to ma zaki jeki
cinye abincin ki, bari in gani ko ki na son zuwa" ya idda maganan tare da ɗagata, da sauri tawuceinda abincinta yake ta fara ci.... Dariya Sahabee da suke kira da Abulkhair ya saki tare da kallonta, murmushi Lawuza ta saki tare
da faɗin "Allah ya shirya ki Iman kina jin yunwa amma ba zaki ci abinci ba" "ke ki ka saba matadakayan ƙwalama, shiyasa take ƙin cin abinci" Ibrahim yace tare da bismillah ya fara cin abincinshi, "ni kuma Daddyn Zarah! Haba ai baka ce haka ba kuwa, kowa yasan kai ke ba ta kayan zaƙi" Lawuza tace tare da kallon shi... Komai be ce mata ba se cin abincinshi da yake hankali kwance, "ke Lawuza yau ya ki ka ƙaredamutuniyarki?" Umma tace tare da kallon ta, murmushi ta saki tare da faɗin "ai Insu ce tacezaniya tafiya, tana tambayan ina zani na ce mata izini aka ban, haka ta bi ni da ido har na fice" "ja'irada ta hana ki mana, da alama wannan sabuwar uwar ɗakin na ki tana da girki ba kamansauranba" "wallahi tana da shi Umma, ƙaramar yarinya ce dai amma akwai hankali da girmama manya, ba ta la'akari da aiki muke a ƙarƙashinta fa, kowa ja take a jiki, kwananta biyu kenan yau, ammaduk mun saba da ita, a gaskiya ba ta da wuyan sabo" Lawuza ta idda maganan cike da tunokaramcin Insun, "ma sha Allah, to ga irin waƴanda ake so, amma kya haɗa da waccan da tatafi
me shegen ƙorafi" "ai ba sa da haɗi ma Umma" tace tare da gyara zama...
"Yawwa Daddyn Zarah dama ka santa ne?" Tace idonta akan Ibrahim da ya ajiye cokali ya jagefe, yasan da ma se tayi mai wannan tambayan dan yanda ta kalleshi lokacin da za ta ba Insuruwayafahimci kallon me ne ne, jinjina mata kai yayi ba tare da yace komai ba, "a ina!" Tace fuskacikeda mamaki, "Bertuwa" yace a natse, "tsaya-tsaya Daddyn Zarah kar dai a gidan su ka yi aiki!" Tace ido waje, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "ƴar Anty ce" buɗe ido tayi cikin tsan-tsanmamaki tare da faɗin "Anty! Dama Insu ƴarta ce? Ka na nufin hoton nan da Insu ta sa aka sakaageneral parlor ɗin SSB Anty ce da ita!" Ta idda tambayoyin cike da san amsa...
"Ban san wani hoto ba ne, amma dai Insu ƴar ta ce ta huɗu" "wani hoto ne su biyu kamanselfiesuka yi, sun saki murmushi me faɗi gaba ɗayan su" tace cike da son fahimtar da shi, tundatafarakwatancen ya gane wani hoto take nufi, ɗakko wayashi a natse yayi ya buɗe ya faɗa whattapp, kan Profil ɗin Sadam yaje kai tsaye, "wannan ne?" Yace tare da miƙa mata wayan, amsa tayi cikeda zumuɗi, "wallahi shine Daddyn Zarah, shine aka mai da shi babba" tace fuska cike da ta'ajibi, "wannan hoton ranar da za ta rasu suka yi, shiyasa suke son hoton sosai, gaba ɗayansu shi suka
ɗaura a profil ɗin su, akwai ma wanda suka yi da su Farisat ina da shi, na ɗauka da Yasmintasakaa statut" yace tare da amsan wayan shi ya ajiye a gefe...
"Allah sarki, a she ga a inda Insu ta gaji karamci, dole ta san mutumci da darajan mutane, ashegada tayi, Allah ya gafarta miki Anty, Allah be nufa zamu ga juna a zahiri ba, amma ya nufazanrayu da ɗiyarki waje guda, Allah ya jaddada rahma gare ki, wallahi Umma na daɗe ina mamakinyanda yarinyar ke hidiman gabanta ba ruwanta da wani ɗagawa da jiji da kai irin na yaranmanya" ta idda maganan tare da kallon Umma, "ai duk wani batun mamaki ya ƙare Lawuzatundakinji nonon wa ta tsotsa yanzu" Umma tace tare da gyara zama, "haka ne Umma, Anty ai itacejarumata, duk da ba ta sanni ba a zahiri ni ma ban santa ba, amma wayan da muka yi sauɗayadaita lokacin da na haifi Iman ya sanar da ni wacece ita"... Murmushi Ibrahim ya saki tare da faɗin "duk yaranta haka suke, ta musu tarbiyya irin wandakowacce uwa yakamata ta ma ƴarta ko ɗanta, ba za su sha wiya wajen zama da ko wasu mutaneba, yanda ki ka ga Insu haka sauran ƴan uwanta suke, se dai ita ta ɗan sha ban-ban da su ta wani
ɓangaren, dan ta na da zolaya, ta na da son barkwanci, ta na da surutu, tana da shashantar damutum, sabanin su, dan su ba su cika wannan abubuwan ba.... Amma girmamawa mutumtawa, darajtawa, wannan na su ne gaba ɗaya" ya idda maganantareda tuna rayuwar da yayi da su a baya, "sun huta, ka ga duk da ta tafi ta barsu ba za su rasamajingina ba, ko dan wannan kyawawan halayyan na su, za'a so su" Umma tace cike da jinjinajajircewan Anty, "gaskiya ne, ko mu kwana biyun nan da tayi damu zamu ba da wannna shedan" Lawuza tace tare da kallon shi, "se dai fa tana da abu guda" yace tare da sakin murmushi, "menene shi Daddyn Zarah!" Lawuza tace tare da kafe shi da ido ...
"Ba ta barin ba shi, duk wanda ya ci bashinta dole ya biya ko waye shi" yace tare da miƙewazaune sosai, "bangane bashi n8a?" Tace tare da kallon shi, murmushi Umma ta saki tare dafaɗin"ba ta barin ta kwana, dan ba ta juran me tsami" "oh Allah Umma kin daɗa shigar dani" tacekamar za ta saki kuka, dariya Ibrahim ya saki tare da faɗin "ita sha yanzu magani yanzu ne, batabarin ɗigon datti ko kaɗan a zuciyanta, in har za ka taɓi Anty ko Yaya ko sister's ɗinta ko
brother's ɗin ta to zaka amshi hukunci dai-dai da abinda ka yi, dan wallahi ko me za'a ce matabaza ta tsahirta ba se ta dire abinda ta ɗauka" "a hakan!" Lawuza tace tare da buɗe ido, "sosai
kuwa"...
"In zaki shekara dubu in ana yi da ita baki taɓo waƴan nan ba, to ba zaki taɓa sanin tana dazafinnan ba, akwai wani abu da ya taɓa faruwa da Yayar mahaifinsu da ita se da na tsorata ganinyanda yarinyar nan ta birkice a second guda, tana da zafi a wannan fanni" ya idda maganantareda kauda kai, "wato a yita ta ƙare ce" Umma tace tare da sauke numfashi, "aiko ita ce, to kai bawame ze kai ka taɓo mata su, tunda kasan ba ta so, a zauna lami lafiya, a rabu salin alim" Lawuzatace tare da sakin murmushi, murmushi Ibrahim ya saki tare da faɗin "shine kawai, Zarahtashi ki
je ki gyara muku shinfiɗa" miƙewa Zarah tayi ta wuce ciki a ladabce, "Daddy ka ga" Imantacetare da ɗaga plate ɗin da ta cinye abincin ciki, murmushi ya saki tare da faɗin "lallai Imantashirya zuwa shan ice cream" dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da rufe fuska, "ƴar nema da ki tsayaƙwaɗayi" Umma tace tare da sakin murmushi, "za ku ɓata kuwa da Insu" Ibrahimyace taredamiƙewa, "a'a a'a me ya kai ni ni kuma" tace tare da kallon shi, dariya ya saki tare da faɗin"takwaran Anty ce fa" ya idda maganan tare da shigewa ciki, "auf na yi shiru" tace tare da rufebaki, dariya Lawuza ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "a to, ni dai ba ruwana" ....
Tunda suka koma gida ko waccen su ta samu daman baje kuka yanda take so, babu me iyararrashin wani, me ƙarfin halin a cikin su Babiya ce, ita ma ta na yi tana sharan hawaye, maƙoftasun shigo sosai sun musu kara, ko da aka shiryata barinta a kayi a ɗakin Babiya dan dole tayi
kwanan keso, su Yasmin sunyi kuka, kukan su zamewa biyu yayi, suna tuna Anty ga kumaZuwaira da suka fara sabawa da ita daga jiya zuwa yau, Sa'adatu kuwa tunda aka shigo dagawanta fito cike da alhini ta gani ta koka kaɗan kar a ce ba ta koka ba ta tashi tayi ɗakinta ba wandaya ƙara ganin dan ƙafarta, haka suka kwana cike da damuwa ba wanda ya samu rumtsawaacikingidan se su Umar da barci ya sata, Sa'adatu kuwa ta zarƙamawa kanta allura ta baje ba tasanhalin da duniyar ma ke ciki ba...
INSU
Se da ta dara san ranta ta miƙe tare da faɗin "Allah yasa kar gulma yayi alajinki Baba Maude" sakin wani dariyan tayi ta yi toilet da sauri, haɗa ruwa me ɗumi a bathtub ta shige tare dalumshe ido, ta daɗe sosai kafin ta saɓa sabulu, fitowa tayi ɗaure da towel, jan stool tayi tazaunaa gaban dressing mirror ta matso lotion's ɗin da take shafawa ta fara shafawa a natse, tanagamawa ta miƙe ta wuce wardrobe, kayan barci ta ɗauka riga da dogon wando masu taushi, tanasakawa ta shafa body spray ta zaro hula ta saka, ta haye gado, kashe wutan dakin tayi ta kunnadumlight ta ɗau waya ta hau facebook, se da ta gaji dan kanta ta kashe datan ta shafa addu'anbarci ta ja blanket ta juya kwanciya (asuba ta gari Insun mu🤗)... Bertuwa
Tun da asuba gida ya fara ɗaukan harama, jama'a shigowa suke suna ta'aziyya, kafin 10 tacikamutanen Dimau sun iso mota uku, cikin gida matan suka shigo suna kuka me taɓa zuciya, yayinda maza suka ɗau butoci dan ɗaura alwala, dama isowan su kawai ake jira, dan Habibatanemi alfarman a bari mahaifinta ya iso ya sami sallatarta, ba wani ɓata lokaci aka sallacetaakaɗauketa aka kaita gidanta na gaskiya(se dai mu ce Allah ya yafewa Zuwaira, da yawan mumunaaikata lefuka irin wannan, wajen zubda ciki ko haihuwa mu mutu, me muka tanada dankarekanwunanmu a gaban mahaliccin mu, ƴan uwa mu gyara ita zina Ubangijin mu da kan shi yaceyaharamtata, dan me zamu saɓa ma wanda ya ba mu lafiya ba tare da ko sisin mu ba, ita fa zinadamuke ji da gani, ƴar aike ce, wallahi watan watarana se ta dawo ko akan ƴaƴan mu ko akanjikokin mu, Allah ya tsare mu ya tsare mana iyalan mu daga faɗawa jarabawa ta zina, Allahyatsarkake mu ya tsarkake mana zukatan mu🤲)... Ana dawo wa kaita Hamidu mahaifinta ya nemi Ali da ya dogaro ya zo ya neman musu izinin
shiga yin ma su Babiya ta'aziyya, babu wani jan zance ya tarkato su suka yo ciki... Gaishe da Babiya yayi da girmamawa tare da mata ta'aziyya, "haƙuri na mune mu duka Hamidu, Allah ya amshi Zuwairatu, Allah ya yafe mata kurakurenta, ya amshi tubanta, mu duka munsheda tuban da tayi kafin rasuwarta" Babiya tace tare da kwance haɓar zani ta fara sharanƙwalla, "Allah ya yafe mata" suka ce bakuna a haɗe, "amen" tace tare da fyace majina....
"Ku je ganinan" yace tare da kallon ƴan uwanshi da ke zaune jigum-jigum, ba musu suka tashi
suka fice, kallon Habiba yayi tare da faɗin "ya ƙarin haƙurin mu?" "Alhamdulillah" tace dadisashshiyar muryanta, "Allah ya gafarta mata" yace a natse, "amen" tace a hankali, zarofarar
takarda yayi a aljihun tazarcen jikinshi tare da faɗin "gashi" ba wani fargaba ta saka hannubiyuta amsa, juyawa ga Babiya yayi tare da faɗin "Hajiya kimin afwa, ba na yi hakan dan in tozartaki
ba ne, ko in nuna gazawa ga ƙaddarata ba, na yi hakan ne dan samun maslahan mu gaba ɗaya, bazan iya cigaba da zama da Habiba ba bayan duk abubuwan da suka faru, Habiba ta yi munabubuwa da dama, wansa faɗensu ma ze iya taso wani matsalan, ta mun tabon da har inkomagamahaliccina ba ze ɓace ba"...
"Na sawwaƙe mata igiya ɗaya daga cikin sauran biyun da suka rage, Allah ya ƙara mana haƙuri" ya idda maganan tare da goge hawaye yana me tuna badaƙalar da suka sha da ita, sadda kai
Habiba tayi tare da danne kukan dake son kuɓuce mata, "ba zanga lefinka ba Hamidu, danni dakaina na sheda haƙurin ka, Allah yasa hakan shi yafi muku alheri, a ƙara haƙuri, ita kuma
Zuwairatu ka yafe mata ka mata addu'a" Babiya tace murya na rawa, "wallahi na daɗe da yafemata Hajiya, addu'a kuwa kullum akan yin shi muke" "to Allah ya muku albarka ya raya zuri'a" tace a dake, "amen-amen zamu wuce yanzu" yace tare da miƙewa...
"Yanzu kuma!" Tace da mamaki, "eh in sha Allah" yace cikin na shi dakiyan, "to harda su
Sha'awanatun za ku tafi?" Tayi maganan idonta akan shi, "a'a suna nan se anyi bakwai" "toshikenan, mun gode Hamidu a gaida manyan" Jinjina kai yayi ya fice a natse, tashi Ali dakejin
kamar yayi ta ball da Habiba yayi ya dafa mai baya, sallama suka kuma suka wuce shi kumayadawo ciki....
Yana dawowa Babiya tace "kiramun Abdussamad a sashin shi" jinjina kai yayi ya wuce sideɗinYaya, be jima ba suka dawo tare suna shirin zama Suwaiba ta shigo fuska shaɓe-shaɓe dahawaye, cikin rishin kuka tace "har nayi lalacewan da Zuwaira za ta mutu ta kwana har a kaitagidanta na ƙarshe ba'a faɗa min ba? Yanzu tsakani da Allah duk yanda na zama masiba zesamuɗan uwana in kasa jajanta mai ne, wallahi banji daɗi ba, a ce ba wanda ze iya ɗaga waya yakirani
ya sanar da ni, se yanzu yaron maƙoftan mu ya shigo yake sanar da ni, har sun kaita ma, dabezoba da ba zan sani ba kenan, haba tsakanin ku da Allah kun kyauta mun?" Ta idda maganancikingunjin kuka...
"Malama ɗan dakata mana da draman nan haka, ba'a faɗa miki ba, ba kuma za'a faɗa ba, konangaba wata ko wani a cikin mu ya faɗi ya mutu, wallahi ba me kiran ki ya sanar miki, ubanmezaki
zo ki yi mana anan? Ina ce tun jiya da take fama da ciwon Jummai ta amshi wayana ta kiraki
muna tsaye a asibiti ki ka ce da ciwon kai ki ka tashi, au wato dama jira ki ke ta mutu se ki zo" Lurwanu yace murya a kausashe, fashewa da wani kukan tayi tare da faɗin "wallahi tallahi banada lafiya jiyan nan Lurwanu"...
"Lokacin da Jummai ta kirani ina kwance shan maganina babu daɗewa, amma wallahi bansamusukuni ba, se addu'a nake mata, ko da Anty Gude ta kirani ta na mun maganan Jummai tasametasuna haɗa kaya an sallame su akan batun an kawo Zuwaira asibiti tace ba za ta je ta dubatabadan ba taje ta duba Sudais ba se da na nuna mata hakan be dace ba, inda ina da lafiyan zuwawallahi zanje Lurwanu, ina Jummai?" Tace tare da ba za ido tana nemanta, ko kula da yandasukashiga shock da jin abinda Gude tace ba tayi ba...
"Yawwa Jummai jiya ban kira ki ki ka ce mun ya lafa tana gidan Yaya Abdussamad ke kindawo
gida ba?" Tace cike da son kare kanta, "eh anyi haka" tace a dake, "kaji ko Lurwanu, wallahi nakira ta akan jin ya ake ciki, in kuna asibitin in lallaɓa inje, se tace mun ya ma lafa mata har kunkoma gida, kaji dalilina, wallahi ko yanzu a kwance nake yaron ya shigo yake faɗamin na zaburo, ina tafe kaina na sarawa yanda kasan ze faɗi" ta idda maganan hawaye ɗaya na bin ɗaya.... Kamota Farisat da duk jikin su yayi sanyi tayi ta zaunar da ita, tare da faɗin "wani magani ki kasha?" "Paracetamol ne" tace tare da goge hawaye" "Nafisat jeki ɓallo mata sudrex ze saukainsha Allah" tace tare da miƙewa tsaye, "to kinga mugun halin ki yasa ba wanda ya miki uzuri, daace kun kyautata zukatanku, ba wanda ze ƙi amsan uzuri ki" Ali yace rai ɓa ce" jinjina kai tayi cikeda gamsuwa...
"Wallahi Allah ne be nufa zani gidanta ba jiyan nan da na fita nan, da nayi niyyan zuwa inzubamata ruwan tijara ne se na ga dare yayi" Lurwanu yace tare da zama saman one seater, miƙamata magani da ruwa Nafisat tayi da girmamawa ta koma gefe, sha tayi ta jingina da jikinkujera, "Abdussamad gashi dai Hamidu ya bawa Habiba takarda tare da saki ɗaya" Babiya tace taredaɗaukan takardan dake jikin Habiba ta miƙa mishi...
Jiki a mace ya amsa ya fara duba ba, "saki!" Balarabe yace a rikice, "saki, yanda kajin dai, ai yayi
ƙoƙari, in wani ne ba ma za'a kawo wannan lokacin ba" tace cike da takaici, "wallahi bangalefinshi ba, dama ai yakamata ya samu ƴanci daga mulkin kama karyan da ake mai, yanzu kingaindarashin hankalin ki ya kai ki, in ana faɗa muku gaskiya ku yi ta ɗaɗɗaga kai ana takura muku, yauga inda ƙarshen takura ya kai ki, aya ne babba Allah ya saukar miki, in kina da rabo ki gyaraki
rungumi ƙaddaranki da hannu biyu, in baki da rabo kuma se ki cigaba daga inda ki ka tsaya, duniyan faɗi ne da ita, zaki gaji ki haƙura" Ali yace zuciya a mugun ɓace.... Banda kuka ba abinda take, ko iya ɗago kai ba tayi, ita kanta shedace akan irin haƙurin dayayi daita, ta kaishi bango ne shiyasa ya yanke mata wannan hukunci, "to ba abinda zan iya cewayanzu, dan me faruwa ta faru, tunda har ya iya yanke wannan hukuncin a dai-dai wannan ƙadaminbaze
ji haƙuri ko ban baki ba, se ki rungumi ƙaddara, sannan ki tuba ki roƙi Ubangiji gafaran zunubanki, mun san shi gafurun ne, kuma afuwun ne, sannan rahimum ne, Allah ya kyauta gaba" Yayayacecike da rashin jindaɗi....
"To ba abun cewa dama yanzu se hakan, Allah ya ganar daku gaba ɗayan ku, wallahi in bakuhankalta dan Allah ba, duniya zata hankaltar daku, abun takaicin ita se lokaci ya ƙure takeankararwa" Babiya tace jdonta na yawo akan su, faɗowa parlorn Gude
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 109