Share this page
"Ibrahim kaji abinda na ce?" "Eh" yace a dake, jinjina kai yayi tare da juyawa ya fara taka matakalan, "Uncle!" Tace da dukkaninƙarfin da ya rage mata, tsayawa cak yayi ƙirjin shi na tsananta bugu, "i want stay with" tayi maganan a rarrabe tare da tsaywa cak ba tare da ta ƙarisa abinda take son faɗi ba sabodawani abu da ya danne ƙirjinta ya wuce maƙogoronta kai tsaye, jin tayi shiru ya sa Hajiya kallonta, ganin yanda take sakin numfarfashi tare da lumshe ido ya sata faɗin "Jamilu!" Kafin Alhaji Jamil ya samu zarafin amsawa wani mugun tari ya taso mata, da ƙarfi ta fiddoshi, tare da faɗin"you" tatafi luwww ta baya, saurin tarota A'isha tayi cike da zallan mamaki ganin Hajiya ta saketaafirgice tare da kallon inda Hajiya ke kallo a razane, "jini!" Tace idonta na bin gudajin jinindakewajen, a firgice ya juyo tare da bin jinin da ido, kuka Ibrahim ya saki tare da juyawa da sauri yayi ƙofa, "Ibrahim!" Jabir da ya gama firgicewa yace tare da kallon Ibrahim da ya tsaya cak bataredaya juyo ba... A guje Alhaji Jamil yayi sama dan kiran doctor dake can yana bincike, takawa yayi har indayaketare da faɗin "ina zaka!" Kuka ya fashe da shi tare da faɗawa jikin shi, se a lokacin Lawiza tafarfaɗo da ga suman tsaye da ta yi tun sanda ta ga tarin jinin da Insu tayi, fashewa da razanannan kuka tayi tare da ƙarisawa ta ta amsheta daga hannun A'isha ta nufi ƙofa da ita tare dafaɗin"ba zaki mutu ba, Insu ba zaki mutu ba, za ki cika burikan ki, za ki cika muradanki" "Lawizakawota" A'isha tace saboda sakkowan da Alhaji Jamil yayi da doctor, tare da dumfaranta, SSBkuwaƙamewa a waje guda yayi banda bin su da ido a matuƙar firgice babu abinda yake, amsotasukayi suka shinfiɗar da ita, nan doctor da ya koma ya kwaso kayan aiki ya duƙufa a kanta, bandakukaba abinda su Fadila ke yi, hatta Nabila se da ta koka, se da ya ɗau kusan 20 minute's yana ƙoƙarin gano abinda gmya haddasa mata hakan kafin ya miƙe cike da firgice ya kalli SSB da ya bazamai ido daga nesa tare da faɗin "I'm very sorry sir extremely heart attack ne" "what!" Yace a firgicetare da fara takowa a natse idon shi ƙyam a saman fuskanta, su Jabir ma gaba ɗaya sumantsayesuka yi ba wanda ya samu zarafin magana... Kallon Ibrahim da ya kauda kai SSB yayi a natse, jinjina mai kai yayi tare da faɗin "dashi akahaifeta, firgici da fargaban da Hajiya tayi ta fama da shi tun daga haihuwa zuwa girma ita maHajiya Amina ta ɗanɗana, ta raineta cike da firgici da fargaban wata rana za ta iya barinta, sedai kash ta rigata wanda ba haka ta so ba, se dai kan ta tafi ta damƙata a hannun wanda ta sanzekula mata da ita fiye da yanda za ta kula da ita" ya idda maganan cikin rishin kuka" tunda yafaramaganan yake bin shi da rikitattun idanun shi da tsoro ya cika, be samu zarafin kaudawa basedaya dasa aya, maida duban shi ga Hajiya yayi a firgice, girgiza kai tayi cikin rishin kuka taredafaɗin "ban sani ba, ba su faɗa mun ba" lumshe ido yayi ya buɗe akan Insu dake shinfiɗe kamangawa, takawa ya fara kamar me tsoron wani yaji sautin takun har ya isa gabanta, duƙewa agabanta yayi cike da rauni ya ɗago hannunta ya riƙe, jin bata damƙe ƙaƙamkamar yanda tasababa ya sa shi sakin hawayen da suka cika mai idon tare da faɗin "damƙe mana, me ki ke jira!" Yaidda maganan tare da kwanciya a saman fuskanta ya saki kuka mara sauti.... Nan hankula suka yi mummunan tashi, kuka yake me cike da rauni wanda ke bayyana wasurufaffun saƙuna wanda ba kowa ze iya fahimtar inda suka nufa ba, takawa Hajiya tayi a hankali ta riƙo hannun shi tare da faɗin "Sahabee" ɗagowa yayi da sauri ya rumgumeta tare da sakinmarayan kuka, "ita ma zan rasata, yanda ta tafi ta barni ita ma tafiya za tayi ta barni, ba nadasa'a a rayuwarnan, me ke shirin faruwa ne?, Meyasa ba ta jira ko sau ɗaya na faɗa mata irinzafinda na ji a zuciyata da ta bar ni ba! ita ma wannan ɗin za ta tafi, shikenan komai ya ƙare makaSahabee ba ka da sa'a a wannan rayuwa you lose everything" ya idda maganan da ƙarfi kukanakuɓuce mai, girgiza kai Hajiya tayi tare da faɗin "ba zata mutu ba, tana tare da kai, zata rayuwatare da kai, ba zata gujeka ba, za ta tsaya a bayanka" janye jiki yayi da nufin komawa kanta, saurin riƙoshi tayi tare da faɗin "kabar shi yayi aikin shi" kallon doctor dake tsaye a gefe cikedamamaki yayi ya lumshe ido cike da magiya.... Jinjina kai yayi tare da gyara murya cikin muryan rarrashi yace "I'm very sorry Mr president alamu ya nuna matakin ƙarshe take, sannan kuma ba wani treatment da ta ke yi, ba na dawani abun yi, se dai kuma in za'a gwada" se kuma yayi shiru, "what!" Ibrahim yace da mamaki taredakallon doctor, ganin irin kallon da doctorn ke mai na neman ƙarin bayani ya sa shi faɗin"anatreatment sosai ma" "to anan dai be nuna ba" yace cike da tabbaci, zaro waya yayi da sauri aaljihu tare da danna number Dr Hisham hannu na ɓari.... Bin shi kawai suka yi da ido ganin yanda duk ya rikice, yana ɗagawa ya zaro ya saka a speaker tare da sai-saita muryanshi cike da girmamawa yace "Dr Hisham barka da wannan lokacin" "yawwa malam Ibrahim barka dai ya gida ya iyalan?" "Alhamdulillah" yace a natse, "ma shaAllahina my patient? My rigima, my ciwon kaina" ya idda maganan cike da murmushi, murmushi yasaki cike da ƙarfin hali tare da faɗin "tana lafiya, dama maganinta ne ya ƙare na ce bari inkiraintambaya a ina kake samu anan" yayi maganan a natse, "eh anyi haka a wannan watan kozeƙare, ai nan kusa da ku ne SSB pharmacy anan nake samo mata" "to shikenan nagode sosai doctor" yace tare da sauke wayan, kallon doctor yayi tare da faɗin "kaji ko? Tana kan treatment, "I'msorry nan be nuna mana hakan ba, da tana kan treatment yanda yakamata da ba ta kasanceawannan yanayin yanzu ba" yace cike da tabbaci.... "Please doctor duk ba wannan ba yanzu dai ya za'ayi" Jabir ya datsi yunƙurin Ibrahim, "abugudane, se dai kuma babu tabbaci akan shi, ina ga mr president ma ya fahimci me nake nufi" yaiddamagana idon shi akan SSB da ya sadda kai, "me yake nufi Sahabee!" Hajiya tace a rikice "alluracese dai ɗayan biyu ne Hajiya imma ta farfaɗo imma kuma Allah ya amshi abin shi" doctor yaceidon shi akan Hajiya, girgiza kai tayi da sauri tare da faɗin "a'a gaskiya kar a mata, a barta haka, ku mata dabarunku na likitoci" goge hawayen da ya gangaro mai yayi a natse ya kalli doctor tareda faɗin "a kawo" "a'a" Alhaji Munnir yace a rikice, "zata tashi, akwai abubuwan da take soncikawa, zata farfaɗo" SSB yace da ƙarfi tare da ɗaga ido ya watsa musu jajayen idanunshi dasukaƙi komawa dai-dai har lokacin, tsitt suka yi tare da bin shi da ido.... "Wai me ke faruwa ne Hajiya!" A'isha tace a rikice, "to kema kenan kin gaji ina kuma gamu" Lubabatu tace idonta akan Hajiya, "me ki ke son sani?" Hajiya tace idonta akan A'isha, "zantukanku ne ke rikita mu, menene ya sa SSB ke zantuka haka akan Insu?" "Saboda matar shi ce, akwai igiyoyin da ya haɗe su waje guda" Hajiya tace cike da tabbaci, kallonta suka yi kaman wawayecike da zallan mamaki, "mata!" Maude tace a rikice, "ƙwarai Maude matar shi ce" Jabir yacecikeda na shi tabbacin.... "Ita kuma ta sani!" A'isha tace da mamaki, "eh me ze hanata sani?" Alhaji Jamil yace cike daƙosawa, jinjina kai tayi ba tare da ta kuma cewa komai ba, sauke nannauyan numfashi Lubabatutayi tare da sakin murmushin takaici, "wato mu aka rainawa hankali" tace a ƙasan zuci, taredabin su da ido a zahiri, Maude kuwa banda mai-maita salati da sallallami babu abinda takecikedatsoro, "ai halan ya halaku baki na da furtawa wani wannan kalman" tace idonta ƙyamakanfuskan Insu, su Fadila kuwa mamaki kusan kashesu a tsaye yayi, Lawiza ma hakan take, danbatataɓa sanin zancen auren ba, Ibrahim be taɓa gigin faɗa mata ba, duk ɗaukanta Insu ta zokaratune kamar yanda yace mata, bin shi da ido tayi tare da faɗin "ka kyauta" cikin body language.... Haka suka zauna jigum-jigum dan jiran dawowan doctor, kowa da abinda yake tunani, SSBdai nazaune kan Insu a saman cinyoyin shi ya zuba mata ido cike da fatan ta farfaɗo a wannanlokaci batare da wani abu ya shiga jikinta ba, a haka doctor ya dawo ya taddasu, fiddo kayan aiki yayi yahaɗa alluran ya ja ya nufeta a natse, dakatar da shi SSB yayi ya amsa a hankali ya zame kantayamiƙe tare da durƙusawa a gabanta buga alluran da ƙarfi yayi a saitin zuciyanta baki ɗaukedabismillah, banda tsitstsinkewa ba abinda zukatansu ke yi, wani ƙaƙƙarfan numfashi taja daƙarfi ta sauke tare da zabura kamar zata tashi tare da faɗin "Uncle!" Da ƙarfi tare da komawa takwanta kamar ba ita tayi maganan ba, murmushi ne ya kuɓuce mai tare da faɗin "sorry" ahankali.... Comments fans🙏🥰 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Thirty four Tunda suka samu suka fice daga babban ƙofar white house ko wacce yayi ta kanta, sabodatsaban ruɗu Jabiida a ƙafa ta ɗau hanya tana yi tana waiwaye dan kar ya zo an biyota, se datayi tafiyan da ba za ta iya ƙiyasta nisan shi ba sannan ta tsaida me napep ɗin da ya zo wuce watahaye tare da faɗa mai inda ze kaita.... Suna ƙarisowa anguwar ya nufi wuce gidan, da sauri security's da jami'an tsaro suka tsaidashi saboda motan haya ba ya wuce ƙofar gidan ba kuma ya tsayuwa a ƙofar gidan, hayaniyansuneya maidota cikin hayyacinta, da saura ta dira ta wuce ba tare da tayi wani yunƙuri dan biyanshi haƙƙin shi ba, da sauri ya diro ko bi ta maganganun da suke be yi ba tare da yunƙurin binta, kojuyowa ba tayi ba ta shige gate ɗin da aka buɗe mata dan daga veil har jaka da takalmi batasaninda ta hurgar ba, "malam ja abarka ka bar nan" ɗaya daga cikin jami'an tsaron yace cike dabadaumurni, komawa yayi tare da jan "Allah ya isa" a ƙasan zuci ya ja napep ɗin shi ya bar wajencikeda takaicin hana shi haƙƙin shi da aka yi.... A firgice ta faɗa parlor tare da wuri-wurin neman inda zata hango Mommy, ganin bata a parlornya sa ta nufurar bedroom ɗinta a guje, tana ƙoƙarin tura ƙofa Mommy ta buɗe ta fito, sakinbaki da ido tayi akanta tana bin ta da kallo me cike da tsoro, fashewa da kuka tayi tare da faɗin"Mommy mun shiga uku za su kashe mu gaba ɗayan mu" ta idda maganan tare da faɗawajikinMommy jiki na mugun ɓari, zaro ta tayi da ɗokacin mamaki tare da faɗin "suwa! Daga ina ki ke! Me ke tsami haka a jikin ki?" Share hawayen da ke zuba kaman an buɗe fanfo tayi tare da faɗin"daga can gidan" harara ta banka mata tare da faɗin "ba na ce ki bar gidan da sassafe ba! Meyatsaida ki?" Tace a ƙufule, "sun hanani ne" tace tare da goge hawaye... "To yanzu ya aka yi!" Tace idonta zube akanta, "sun gane komai, sun fahimci ke ne ki ka saasakamagani" tace a rikice, "what! Waya faɗa musu!" Tace cike da firgice, "wallahi ba ni ba ne, itacetafaɗa da kan ta dan cameran tsaro ya haskota tana zuba maganin" "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, se aka yi yaya!" Tace tare da goge zufa, "shine tace ke ne" "na shiga uku, ba kumaki ƙaryata ba!" "Ba zan iya ba Mommy na rikice" tace tare da fashewa da kuka, zubewa a wajenMommy tayi cike da firgici.... "Me ke faruwa?" Former president dake tsaye a bayan su yace tare da bin su da kallo me cikedanazari a natse idon shi na yawo akan su, saurin miƙewa Mommy tayi tare da faɗin "nothingseyanzu ku ka gama meeting ɗin?" Watsa mata ido yayi ba tare da yace komai ba tare da juyaakalan duba da tambayar ga Jabiida, dake ta zare ido, buɗe baki tayi cikin rawar murya taredafaɗin "Mommy ce" "wuce ki tafi ɗakin ki" Mommy tace cikin muryan ba da umurni, juyawadadubanshi kanta yayi tare da watsa mata kallo me cike da gargaɗi, maidawa ga Jabiida yayi tareda kafeta da ido, "ita ce ta saka wannan matar wacce ke aiki tare da SSB saka mishi magani atea" nan ta rattafo mai komai a ruɗe dan gani take shi kaɗai ne ze ba su mafita, da ɗin binmamaki ya ɗago ido a rikice ya zube ma Mommy tare da faɗin "abinda ta faɗa gaskiya ne!" Yaidda tambayan zuciyanshi na tsitstsinkewa, jinjina kai tayi a tsorace tare da faɗin "nayi hakannedan in sama maka abinda ka daɗe kana kwaɗayin samu" "shut up useless, ki na da hankali kuwaMaryam! Shikenan kin tarwatsa mun duk wani daman da nake hanga, shikenan kin rusa munmafarkin da na daɗe ina yi, kin tarwatsa mu da kan ki, kin cuce ni, meyasa yawancin ku matadaƙiƙai ne? Bakwa lissafi in zaku aikata abu, ni na saka ki!" ya jefa mata tambayan a fusace, girgiza kai tayi da sauri jiki na ɓari.... "Na ce miki ina buƙatar wani temako daga gare ki ne!" Ya kuma je fa mata tambayan na shi jikinna ƙyarma, girgiza kai ta kuma a matuƙar tsorace, "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un kin kashemugaba ɗayan mu, kin tarwatsa mana goben mu da duk tanadin da muka mata" ya idda maganancikin mugun ɓacin rai... "Darling ban yi hakan dan kowa ba se dan kai" tace baki na ɓari, juyowa yayi a fusace taredafaɗin "wallahi ki ka ƙara cewa tak se na sassaɓa miki, har ki na da bakin da zaki mun magana?Bayan wulaƙanta rayuwarmu da ki kayi, ki ɗau wuƙa da kan ki ki daɓa mana a maƙoshi sabodarashin hankali sannan ki buɗe baki ki ce zaki ba mu haƙuri, ku ɓacewa ganina!" Ya idda magananda ƙarfi a tsawace, simi-simi suka wuce jiki na ɓari, suna gab da ficewa daga wajen tambayanshi ya doki kunnuwansu, "ya san wanda ya aikata?" "Eh, amma yace kar wanda ya ɗau mataki" Jabiida tace jiki na ƙyarma tare da jinjina kai, rumtse ido yayi cike da baƙin cikin da ke hanƙorohar maƙogoron shi, suna ficewa ya wuce bedroom da sauri kamar ze ci ta baki, banda ɓari babuabinda jikin shi keyi, zaro waya yayi ya lalubo number saurin yanje hannun shi daga yunƙurindannawa da yake shirin yi yayi tare da faɗawa wani tunani na daban, tsaki yaj ya hurgar dawayan a saman gado ya nufi toilet da sauri dan ba ƙaramin kartawa cikin shi ke yi ba.... Lamunde "A ƙafa ta nufi anguwarsu dan ba ta cikin hayyacinta sam, hurga ƙafa kawai take duk indaAllahya bata iko, yanda take bugun madai-daicin gate ɗin gidan kaɗai ya isa sanarda me saurarebatacikin hayyacinta, ana buɗewa ta bangaje wanda ya buɗen ta shige ciki a guje, da mamaki matashin saurayin da ya buɗe ya fita tsakar anguwan ya bi da ido, ganin ba wani abu saboyasashi komawa ciki da sauri ya kulle gate ɗin yayi ciki.... A sittin ta faɗa parlorn ko kula da matasa biyun dake zaune suna kallo ba tayi ba ta jefar dawayanta da ta ciro a lalita ta wuce bedroom ɗinta a guje saboda sakin zawayin da ta fara, dazallan mamaki suka mimmiƙe suka bi ta da ido, shigowa wanda ya buɗe mata gate yayi taredafaɗin "ina take?" "Ta shige ciki" ɗaya daga ciki yace tare da kallon shi, "kaman ba ta cikinnatsuwanta ko?" yace da ɗokacin mamaki, "wannan ba natsuwa ba kaɗai har dwhankali, wandake tsaye a cije yace cikin muryan shiryayu tare da yunƙurin wuce wa, ƙarar da wayan da tajefarya ɗauka ne ya sa shi juyowa tare da ɗaukan wayan, ganin Madam na yawo a saman screenɗinya sa shi ɗagawa ya saka a speaker ba tare da yace komai ba.... Ana ɗagawa Mommy dake fatan a ɗaga ta miƙe zumbur tare da faɗin "to ƴar iska wacce batagaji arziƙi ba, har ni zan sakaki aiki ki wulaƙanta sannan ki bi shi da adon tonon silili, to bari ki ji wallahi wani abu ya taso bayan wannan furucin na ki se na waɗanɗana rayuwarki, se na shayar dake ruwan tashin hankali wanda ze kashe miki ƙishirruwan ƙwaɗayin ki gaba ɗaya" ta iddamaganan zuciya a matuƙar hasale, zare ido gaba dayan su suka yi tare da bin junansu da kallonme ɗauke da ɗumbin mamaki, wani mugun tsawa wanda ke riƙe da wayan ya sakin mata wandase da ya kusan kadasu daga ita har Jabiida dake tsaye jiki na ƙyarma.... "Dan wanda yayi sanadiyyan zuwanki duniya Uwata ki kewa gargaɗi haka!, uwar Cika aiki yauwata ƴar iska ke wa barazana haka!, zan zo gare ki, ki tsimayeni, bari ta fito ta ba ni address ɗinki se na tabbatar harshenki be ƙara furta kalman barazana ga kowa ba" ya idda magana taredakashe kiran ya hurgar da wayan gefe yana fidda numfashi me cike da ɓacin rai.... "Lamunde!" Matashin da ya buɗe mata gate yace tare da baza mata ido, juyawa gaba ɗayansusuka yi tare da baza mata ido, "wacece wannan da ta kira ki? Ita ce ta saki fita hayyacinki haka!" Cika aiki yace idon shi ƙyam akanta, fashewa da raunataccen kuka tayi ta zube a wajen taredafaɗin "na shiga uku, ku zo mu tattara mu bar garin nan" ta idda maganan cikin rishin kuka, dasauri suka isa kusa da ita tare da tambayanta abinda ke faruwa, nan ta labarta musu komai, cikeda takaici Cika aiki yace "wallahi aka zo neman ki se na nuna inda ki ke, me bawan Allahnanyamiki? Duk wani kyautatawa ya miki a rayuwa, amma ki rasa sakayyan da zaki mai se na sonkashe shi, ke da hannunki ki ka zuba mai maganin da ze iya sanadiyyan rayuwar shi?" ya iddamaganan kamar ze haɗiyi zuciya dan baƙin ciki.... "Rufe mun suka yi, ba su faɗamin gaskiya ba" Lamunde tace cikin rishin kuka, "dama ai dukwanda ya hau motan ƙwaɗayi a tashan wulaƙanci take sauke shi, yanzu wa gari ya waya? Ki nazaunen ki cikin rufin asirin aikin ki kin hangi matakin da Allah be kai ki ba kin haura, ga ƙarshennan kin gani da gaggawa, tunda ƙwaɗayin rayuwar da muka bari me cike da ƙunci ki ke manasemu cigaba" ɗayan da be ce komai ba tun ɗazu yace cike da takaici.... "Wallahi yaudarata suka yi" tace tare da ɗago idon da suka tasa ta zube musu, "ki fa daina maganan yaudara Lamunde, ba fa ƙaramar yarinya bace ke" Cika aiki yace rai ɓace, "kuyi minafwa, na tuba" tace a raunane, "ita wannan ɗin waye?" Yace tare da kallonta, "matar former president ce" tace a hankali, "ki ce shegun ne, dama ina so su shigo hannu, bari zan cafkesunankusa" yace tare da miƙewa ya fice, bin shi kawai Lamunde tayi da ido cike da fargaba, dantasanwaye ɗan nata.... Mommy na zare wayan Jabiida ta fashe da razanan nan kukan shikenan mun gama yawo, tsawaMommy ta daka mata tare da faɗin "wuce ki tsaftace jikin ki, kin isheni da tsami, da sauri tawucebedroom ɗinta dan se a lokacin ta tuna da ta zawaye jikinta, tana shigewa Mommy ta zaunasaman one seater tare da faɗin "an yanka ta tashi" .... Tsaye suke a wajen jiran matafiya, ko wacce ka kalli fuskanta yalwace yake da murmushi mecikeda farin ciki da zaƙuwan ganin Insu "gasu can" Nafisat tace tare da nuna musu su Lailahdaketafe da zugan ƴaƴansu, nan da nan fuskokin su ya ƙara yalwata da murmurshi, suna ƙarisowasuka fara rungumarsu cike da kewa, zame jiki Yasmin tayi daga jikin Khadijatu tare da faɗin"aina ta tsaya?" Ta jefa mata tambayan tare da fara baza ido dan ganin ta inda za ra ɓullo.... Farisat da Nafisat ma kafeta da ido suka yi cike da son jin amsa, "waye?" Tace tare da zubamataido "Insu" tace a hankali, "oh bar tuna mun da wannan ɓacin ran ba mu zo tare da ita ba" Lailahtace cike da gajiyan da ta ɗebo tare da kallon Farisat da ta saki ido da baki tana kallonta cikedamamaki, "ina motan?" "Yana parking space ku muje" tace jiki a sanyaye, tattara yaransusukayi suka wuce cike da gajiyan da suka kwaso, kallon Yasmin da jikinta yayi mugun sanyi Farisat tayi tare da faɗin "kar ki damu, muje" jinjina kai tayi tare da maida facemask ɗinta ta dafa musubayaa natse.... "Muje Nafisat" Farisat tace tare da nuna mata hanya, sauke ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya tayi tawucekamar wacce ba ta san taka ƙasa, juyawa ta inda tun tsayuwan su ta hange shi tayi tare dasakinmai murmushi, murmushi ya sakin mata ya tako a natse ya yo inda take, "me amarya ke yi anan?Allah dai yasa kin nemi izini" yace tare da sakin dariya, dariya ta saki cike da danne damuwar data shiga tare da faɗin "har yanzu a gidan Yaya nake fa, ku jira nan da kwanaki" "a'a me akewandaya rage kuma ba muyi ba? Malama sadaƙar ki fara biyayya" yace tare da bin ta da ido, dariyatasaki tare da faɗin "me ka zo yi anan?" "Wallahi brother na na zo tarba, yau ze dawo daga school" "oh ma sha Allah, mu ma Auntie's ɗin mu muka zo tarba" "na gansu, a ce ina musu maraba" murmushi ta saki tare da faɗin "Allah ya tinasar da ni, dan wallahi zan iya mantawa"... Tayi maganan murmushi yalwace a saman fuskanta, "dako mun samu saɓani, jeki kar sugaji dajiranki, na ga mutuniyar kamar a wuya take" murmushi ta saki tare da faɗin "okay a miƙa munsaƙon gaisuwan bangajiyan jiya ga su Yaya Annur, wallahi na manta ban kira su ba" "tundakintuna se ki kira, in sha Allah zamu samu mu shigo anjiman" "Allah ya yarda" tace tare da juyawatamaida na ta facemask ɗin ta wuce, cike da mamaki Mihna da ta zo sanar da shi wanda sukejirayafito ta bi ta da ido se da ta ɓacewa ganinta sannan ta dawo da shi kan Shureimda murmushinsaman fuskan shi ya kasa ɓacewa.... "Brother ita ce ko!" Tace cikin ɗan tantama, kauda kai yayi ba tare da yace mata komai ba, "please brother ita ce ko!" Ta kuma cewa kaman za tq saki kuka, "no sister ɗinta ce" "wowsunamatuƙar kama, ita ce wanda ka ce za tayi aure?" "Yes Aku" yace tare da saƙala hannun shi awuyanta ya jawota da ɗan ƙarfi, "ouch, brother da zafi fa" tace kamar za ta saki kuka, "hukuncinwanda ya cika tambaya mara dalili ne, ina Minha?" "Tana tare da brother Hisham" tace taredajan jikinta, zare hannun shi yayi a hankali tare da faɗin "au ya fito ma baki faɗamin ba sabodatsaban son jin ƙwam!" Dariya ta saki tare da faɗin "to ai shi na zo faɗa maka" "to muje" yacetareda jan hannunta suka yi inda su Minha suke.... Da sauri Hisham da ya hango zuwan shi ya taho ya shige jikin shi tare da faɗin "i really miss youbrother mie" ya idda maganan tare da ƙanƙameshi, murmushi ya saki tare da faɗin "na fika" dariya ya saki ya janye jikin shi a natse tare da faɗin "anya!" "Eh mana, kana ganin yanda kamulka ki ba, ni kuma kalleni kamar a hure ni na faɗi, ai ana ganin mu ansan wanda yayi kewa" ya idda maganan tare da jawo shi ya rungume, dariya ya saki tare da faɗin "oh Allah kana nanfanatafi bare in ce baka nan, ai nafi haka lokacin" "to shikenan muje Mommynka na can ta ƙosataganka" dariya ya saki tare da faɗin "ni ma" ya yi maganan idon shi na yawo a farfajiyan wajen, "akwai wanda ka ke nema ne!" Shureim yace tare da kafe shi da ido, zare ido yayi tare da faɗin"no" ta cikin zuciya kuwa banda fatan ya ga Insu ta ɓullo ba abinda yake, jirgin 7 ze biyo, ammasaboda ita ya maidata na 12 amma shiru ba ta, "ku muje" yace tare da kallon su Mihna.... Da sauri suka riƙo hannun shi cike da san idda zance Mihna tace "brother yayi budurwa" tayi maganan ƙasa-ƙasa tare da zare ido, dariya ya saki tare da kallon yanda take ta zare ido kamar wacce ta wa sarki ƙarya, "to dole se

Chapter 47 of 109