ta fito ta bi ta....
"Lawiza, Lawiza" tace tare da ƙara sauri saboda ganin tana gab da shigewa side ɗin su, juyowatayi da mamaki ta bi ta da ido, tana ƙarisawa ta saki murmushi tare da faɗin "lokacin tashinki
yayi ko?" "Eh har ya wuce ma, sauri nake na bar Abulkhair kwance ba lafiya" "ai da kin faɗamatun ɗazu da kin koma, ciwo ai ya kori komai" Maude tace cike da nuna tsan-tsan kulawa, murmurshi ta saki tare da faɗin "ba komai ai" ta shige ciki da sauri, canzo kaya tayi ta fitodaaɗan hanzarce, cike da mamaki ta bi Maude da Lamunde da ta iso bayan shigewanta da kallomecike da mamaki.... Murmushi suka sakin mata ba tare da sun ce komai ba, murmushi ita ma ta saki tare da yunƙuringittasu, "a she yaro kuma be ji daɗi ba?" Lamunde tace fuska na bayyana alhini, "wallahi BabaLamunde" tace tare da wuce wa da sauri ta nufi parking space ɗin ma'aikatan gidan, da sauri
suka dafa mata baya, juyowa tayi da mamaki tare da faɗin "Baba Maude lafiya kuwa?" Jawotatayi da sauri tare da tare da faɗin "ke dama a she kin san yarinyar nan ƴar yallaɓaice ki kaƙyalemu mu ka yi ta haukan mu na rashin sani!" Tayi maganan cike da tsoro, kallo me cikedarashin fahimta ta mata tare da faɗin "bangane ba" "oh Lawiza, kin fa san akan wacce mukemagana, Insu a she ɗiyar yallaɓaice?" Bin su da ido tayi cike da mamaki, kafin ta sauke numfashi
tare da faɗin "oh ba ga shi yanzu kun ji ba" "Allah ya so mu ba wani mugun hali da muka taɓanuna mata, ke kuma Lawiza ba haka ake ba, da ki ka sani ai se ki kora mana bayani, yanzudaacewani abu mara daɗi ya taɓa shiga tsakanin mu ya zamu yi kenan?" "Baba Maude ba ku tambayaba ne ai" tace cike da ƙosawa, "to ai shikenan, su nawa ne a wajen Mamanta?" "Ita ɗaya ce" taceaƙage, "Allah sarki a ina take?" "A Bertuwa ne, ta ma rasu, shiyasa ta dawo nan da zama" tanakai
nan ta wuce inda ta hango Ibrahim da sauri.... Sakkowa a mota yayi tare da faɗin "zaki tafiya ne?" Jinjina mai kai tayi tare da gyara zamanjakanta, "jira in ma SSB maraba se mu tafi" "a'a sauri nake, yanzu muka yi magana da UmmataceAbulkhair na ta kiran sunana, wai in zo yana son ganina, SSB kuma be sakko ba" murmushi yasaki tare da faɗin "shine hankalin ki yayi gida?" "Eh mana" tace tare da sakin murmushi, "toshikenan, ina bayanki, SSB na fitowa zan taho" yace cike da kulawa, "okay se ka dawo, danAllahka ce mai ina mai maraba" tana kai nan ta wuce tare da ƙwalawa ihu kira.... Bin su da ido suka yi har ta bar inda yake ta shige mota suna ficewa Lamunde taja tsaki tareda
sauke numfashi cike da takaici tace "ba na faɗa miki yarinyar nan munafuka ba ce, to gashi nanyanzu kin gani kin sheda, ta fa san komai ta bar mu munata lalube a cikin duhu bayan tanadaingantaccen battery a torchlight ɗin da ke hannunta, nafi zargin wan can munafukin mijinnatane ya hanata fidda maganan" ta idda maganan cike da takaicin Lawiza da Ibrahimda ba susantana yi ba, bin ta da ido Maude tayi zuciya na hanƙoro tare da faɗin, "je ki duba mutanancansungama tsaftace kitchen ne" tana kai nan ta juya ta shige side ɗin su, wuce wa Lamunde tayi
takaicin Lawiza tamƙam a zuciyanta....
Tana shiga ɗakinta ta danna ma ƙofan key ta wuce ƙurya tare da zaro wayanta dake lalitatadanna number ta kara a kunninta,,,, miƙa mishi wayan da se kira me mahimmanci ke shigaciki
wanda ke tsaye a gefen shi yayi tare da faɗin "mr president ana magana a waya, excuse ɗinwaƴanda ke zazzaune a gabanshi yayi tare da karawa a kunni, zaunawa tayi a hanzarce jinanɗaya tare da faɗin "yallaɓai kana lafiya?" "Alhamdulillah Maude lafiya ki ka kira a wannanlokacin?".... Murmushi ta saki kaman yana ganinta tare da faɗin "yallaɓai albishirne da ni me matuƙar daɗi"
"okay riƙe waya ina zuwa" yace tare da miƙewa a natse ya fice daga office ɗin ya ya shiga officeɗin sirri, zaunawa yayi a saman sofan dake gefe tare da faɗin "ina jinki" a natse, gyara muryatayi
tare da faɗin "yallaɓai ba juya ba ne, yana haihuwa, wannan yarinyar da ka san labarinta ƴar shi
ce" shiru yayi cike da zallan mamaki tare da faɗin "a ina ki ka ji?" "Yanzu haka ne daɗe da
shigowa ba" "na sani" yace a dake, to su Hajiya da suka zo marabtan shi ne suke maganan, sedai
a yanda na fuskanta ƴan uwanshi ba sa san yarinyar da mahaifiyarta, amma Hajiya na matuƙar
sonta"....
Cire hula yayi ya ajiye a gefe tare da faɗin "su ne suka tabbatar da ɗiyar shi ce?" "Eh Hajiyadabakinta ta furta, sannan da alamu duk sun sani, dan duk shiru suka yi, sannan nayi wani bincike"
"ina jinki" yace tare da sakin murmushi, "yarintar ita ɗaya yake da, mahaifiyar ma ita ɗayatahaifa, a Bertuwa ta taso tare da mahaifiyata, ina ga yallaɓai ya sake ta tun yarinyar na ƙaramane, se bayan mutuwan mahaifiyar aka dawo da ita dangi" "good job Maude, nayi matuƙar farinciki
da jin wannan labarin" yace cike da farin ciki, murmushi ta saki tare da faɗin "na san zaka ji
yallaɓai shiyasa na hanzarta faɗa maka, "ki cigaba da aikin ki yanda yakamata zamu yi maganainna koma gida" jinjina kai tayi ta sauke cike da farin ciki.... Nagartaccen murmushi ya saki tare da miƙewa ya fice, kai tsaye office ɗin shi ya koma, murmushi ya saki tare da faɗin "amun afwa father, "bq damuwa mr president, ina ganinyakamata mu zo mu wuce yanzu, sannan kuma ka ƙara nazari akan hukunci da ka yanke" murmushi ya saki tare da faɗin "hukuncin da na yanke ban yanke shi kai tsaye na se da nayi
dogon nazari a kai, shigowan shi wannan rafiyan, ba ƙaramin nasara ze bawa wannan jam'iyyarba, zamu ƙara dafe madafan iko da ƙarfin mu" murmushi vice president ya saki tare da faɗin"ni
kaina na hangi hakan, dan makaho a harkan, ƴan jagoran kuma mune" "wannan haka yake" mr
president yace tare da sakin dariya, "to shikenan, zamu saurareka zuwa jibin" father yacetaredamiƙa mai hannu, "in sha Allah" yace tare da ba shi nashi hannu suka yi musabaha suka tashi sukafice.... Maida wayan lalita tayi tare da faɗin "ba shikenan ba, da muna nan muna ta kwaɗa mai juyaashe bawan Allah da lafiyar shi, gaskiya Lawiza zurfin cikin ki yayi yawa, yanzu duk kin sandawaƴan nan batu ki ka rufe mun, to menene ribarki da adanawan? Haba biri yayi kama da mutum, a she shiyasa take nuna rashin damuwa da yanda yarinyar ke shishshigewa mijinta, ai doleki
danne duk wani kishi ki kwashi roman demukuraɗiyan arziƙi, to ko ni na samu wannan damanwasa zan da shi, Allah dai ya kauta" ta idda maganan tare da nufar ƙofa ta fice a hanzarce....
Sallama Nafisat da aka tura shigo da Gude tayi ta wuce inda ta tashi ta zauna, "lafiyankudai! Wakuma ya mutu yau?" Gude tace tare da ƙarisowa ciki ta nemi kusa da Suwaiba ta zauna, "wannanwani irin tambaya ne haka?" Balarabe yace murya ba daɗi, "a'a kai kama kan ka, ba da kai nayi
magana ba, meke faruwa ne?" Ta idda maganan tare da jefa musu tambaya, "ai iftila'i ne yafaɗamana yau ɗin nan Gude, Allah ne be yi za'ayi dake ba, yanzu Sa'adatu ta wanke mu ta wankeAmina gatanta tas ta tattara nata yi nata ta fice" Babiya tace cike da jimanta abinda ya faru, "to
fa, ita Sa'adatun ta zagi Aminan? Lallai kam, to Allah ya kyauta, ai gunda da ba'ayi ina nanba, Allah ne ya ga abinda ya gani ya sa ban fara yo nan da farko ba, da na ce zan biyo in ɗaukeki
Habiba mu leƙawa Hajiya Zainab biki, se Sudais ya ɓata min lokaci ban fita da wuri ba kawai nacemu wuce can kai tsaye, se yanzu na ce ya sauke ni a nan in gaida ku" Gude ta rattafo bayanintareda bin su da ido....
"Hmm Allah ya kyauta" Habiba tace tare da kauda kai, "to me ya faru har ta yanke hukuncintafiya ta bar rumfar da ta fake dan gudun bugun rana?, Ai dama na san wannan ranar na nanzuwa, ai tunda Amina ta nuna fifiko tsakanin mu da yarinyar nan na san in dai ɗan wani tarunguma se ta yi kuka da idanunta wataran, ɗan wani guntun kashi, Allah ma yasa ba ta duniyanme afkuwan ta afku, da tana nan abun ze fi bada kala" ta idda maganan ko a jikinta, da mamaki
suka baza mata ido...
"Gude meyasa ki ke da saurin juya batu zuwa wani abu daban ne? A wannan maganan kumameya sako Amina a ciki? Ina yanzu na gama faɗa miki ko ita ba ta bari ba, yakamata fa ki fahimci
Amina ba ta duniya yanzu, duk wani shirme ki zubda" Babiya tace rai ɓace, "ai shikenanmeyarinyar tayi?" Tace tare da kallon Suwaiba, gyara zama ta juda da dubanta gareta tare darattafo mata komai a natse... Yana jan kujeran dake kusa da nata yace "me ki ke yi anan?" Yayi maganan tare da zaunawa, sauke numfashi tayi tare da kafe shi da ido, "wai lafiya? Kin kira ni bakya da na faɗi ne kome?Inafa da abubuwan yi" yace tare da ajiye wayan shi a gabanshi, "na bar gida" tace a dake, ɗagokai
yayi ya zuba mata ido cike da mamaki tare da faɗin "ban gane kin bar gida ba? Kaman yayakenan?" "Kaman yanda ka ji dai hakan na ce na bar gida" tace idonta ƙyamakanshi, "akanmekenan?" Yace tare da kafeta da ido, sauke numfashi tayi tare da faɗin "sun fahimci komai" "komai!Ki na nufin har tarayyana dake!" Yace a rikice, "eh" tace tare da kauda kai, zare ido yayi taredamiƙewa a rikice cikin kiɗima me haɗe da fargaba yace "ya a ka yi ki ka bari suka sani!" Ya jefamata tambayan zuciya na tsintsinkewa, "ban sani ba ni ma, amma ina zaton Salman ne, danshi
ke yawan samun ido" "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, yanzu fa na sauke momy a can" yacetare
da zama cikin ɗin bin fargaba ya kama kai.....
"Numfashi ta sauke a natsa tare da faɗin "ni duk ba wannan ba, wajen da zan zauna za ka nemanmun, dama ai yakamata su san da soyayyan mu" ta idda maganan ko a jikinta, ɗago kai yayi azafafe tare da faɗin "su san da soyayyan mu? To wannan wawancin da ki ka aikata nesantamuzeyi in baki sani ba shashasha, kawo ƙarshen tarayyan mu ze yi, ke kwata-kwata ba kya abudalissafi, duk abinda ya zo zuciyanki aiwatarwa ki ke na kyakykyawan tunani" ya idda maganancikeda ƙunan zuci, "ba wannan mutumin a doron duniya wallahi, mutuwa ce kawai zata shiga tsakani
na da mallakar ka, dan ita ma ta zama wajibi ne akan mu, amma matuƙar kana shaƙar numfashi
da fesarwa ina yi wallahi ba wacce ta isa mallakarka se ni ɗaya" ta idda maganan a zafafezuciyaa matuƙar harzuƙe, tsaki ya ja me sauti tare da faɗin "kar ki kawo mun shirme anan, ba kyadogon tunani kafin ki furta magana, duk abinda ya zo ƙwaƙwalwanki zuciyanki tayi na'amdashi
shine dai-dai"...
"Ƙwarai kuwa shine dai-dai, dan kai da kanka ka san irin matsanancin son da nake maka, bekamata ma hakan ya dame ka ko ya baka mamaki ba" sauke numfashi yayi ba tare da yacematakomai ba, "ina zan sauka?" Tace tare da kafe shi da ido, "ban sani ba, lokacin da ki ka yankehukuncin barin mafakar ki kin faɗa mun ne? Ko baki yi tunanin inda zaki sauka ba ne ki kabarocan?" "Banyi ba, dan na san wajen sauka ba ze gagareka samamun ba" "ba na da inda zaki sauka"yace tare da ɗaukan wayan shi da makullin mota ya juya da nufin barin wajen.... Riƙoshi tayi a hanzarce tare da faɗin "ba ka isa ba, wallahi baka isa ba Sudais, soyayyandanakemaka ba ze sa in baka daman walaƙantani ba, dole in taka maka burki in ka zo wuce iyakar ka, dan waye nayi duk abinda nayi? Dan kai ne, sannan saboda ka mai sheni ƴar iska ka ce ba kadawajen sauke ni to wallah ko ɗakin jatumarka ne se ka fiddata ka ba ni na zauna" ta idda maganana matuƙar zafafe, fidda ido waje yayi yana bin ta da ido cike da ɗin bin mamaki....
Leƙowa Kamil yayi tare da faɗin "Hajiya ya sakko" yana kai nan ya juya, "ku tashi muje" Hajiyadata miƙe tace riƙe da hannun Insu, miƙewa suka yi gaba ɗayan su suka nufi dining room, sunashiga ta saki murmushi tare da jan kujeran kusa da Abubukar ta zauna, "uncle Abubakar wai menayi ne kake ta harara na?" Tace kaman zata saki kuka, murmushi Hajiya ta saki tare da zamakusa da SSB da ke zaune idon shi akan waya, "ina Mauden tayi kuma?" Hajiya tace cike damamaki, maida dubanta ga Hajiya Insu tayi tare da faɗin ta fita ba jimawa" tayi maganananatse, murmushi Alhaji Jamil ya saki tare da faɗin "Maude me abun mamaki" murmushi Insu ta saki
tare da jan kujeran baya kaɗan ta miƙe tare da faɗin "me za tayi?" "A'a bar shi je ki zauna" Hajiyatace da kulawa, murmushi ta saki tare da faɗin "to" tayi maganan tare da zaran tissue tayi indaSSB ke zaune hankalin shi gaba ɗaya na wayan hannun shi...
"Uncle me zaka ci?" Tace cike da yanayinta, tare da kara kunninta a saitin bakin shi, murmushi
mazan suka saki tare da bin ta da ido, matan kuwa ba wacce ta kalli wajen dan tsaban takaici, jinbe ce komai ba kuma ba ya da niyyan faɗi yasata dagowa tare da jawo food flaks, shinkafadai- dai ta zuba a plate ɗin dake ajiye a gaban shi, madaidaici bowl ta ɗakko ta zuba mai miyanhantada ƙamshin shi ya baɗe wajen, cup tea ta ɗakko ta haɗa mai tea me kauri ta ajiye, banda bintadaido ba abinda suke, komanta a natse tayi ba garaje ba hayaniyan da suke hangota da shi...
"Hajiya me zaki ci?" Tace tare da sakin mata murmushi, "akwai tuwo?" Tace cike da murmushi, "bari in duba" tace tare da fara bubbuɗewa jerin coolers ɗin dake baje a tsakiyan center tableɗin, "akwai" tace tare da zaran tissue ta ɗakko malmala ɗaya ta saka mata, miyan ganye da yaji agushi da tsokoki ta zuba mata tare da zuba mata ruwa a kofin gabanta ta koma wajen zamantatazauna, murmushi Alhaji Jamil ya saki tare da faɗin "sannu da aiki" zare ido tayi tare da faɗin"sorry uncle Jamil" tayi maganan tare da ƙoƙarin miƙewa, "a'a yi zamanki, zanyi servingɗinkai
na" yace da kulawa, murmushi ta saki tare da komawa ta zauna... Ajiye wayan hannunshi yayi a natse ya ɗau cokali ya zura a plate ɗin, ɗagowa yayi ya kallesucikeda kulawa, sauke kai yayi tare da faɗin "banga Ibrahim ba" "kasan shi wataƙila ya na canwaje" Hajiya tace da kulawa, jan kujera baya Kamil yayi ya fice, be jima ba se gashi sun shigo tare, jankujera yayi ya zauna ba tare da yace komai ba, nan kowa ya fara ƙoƙarin serving ɗin kanshi, jellof macronin da yaji kifi ta saka ma kanta ta zuba ruwa ta gyara zama ta fara ci a natse....
"Me ki ke son ce mun ne Suwaiba! Kina nufin da Sudais suke sheƙe ayan da ku ke magana?" Gudetace a rikice tare da kallonta ido waje, "to haka dai mu ka ji" tace tare da kallon ta, "ƙarya newannan, wallahi ko ita ce autar mata a duniyan nan na san Sudais ba ze taɓa ɗaga ido ya kalletaba bare har wani abu ya ratsa tsakanin su, yaron da ba ko wacce mace yake ma kalla a matsayinmace ba, shi ki ke son ce mun ya biyewa shashashan nan suna shashanci?" Tayi magananrai aɓace, "Anty Gude ba fa ni na ce ba, Yaya Abdussamad ne suka dawo da batun kuma yarinyabataƙaryata ba, "wannan haɗin baki ne kawai na maƙiya, an gama mai bi ta da ƙullin shaye-shayeyanzu kuma an koma na zina, wanann wani irin ƴan uwa ne haka Allah ya ba ni?" Ta idda maganatare da fashewa da kuka...
"Au shima wannan batun kin juyar dashi ta wani ɓangaren kenan? Shikenan sharri aka mai, danAllah ku bar maganan haka" Balarabe yace tare da kallon Suwaiba, "wallahi ba za'a bar maganannan ba, yanzu ma aka farata ƙazafin zina ga ɗana kuma daga wajen ƴan uwana, haba ai wanannabu ba zan taɓa iya mantawa da shi ba" "ba ya da daraja da kima da mutumcin da za mumai
sharri, abinda ga aikata mu ka ji kuma muka gani, ɗanki baya gaban mu bare har mu mai ƙazafi
Gude, ba matsalan mu ba ne in ya kasance bunsuru ƙarshen barbara kenan, su ma da sukafaɗamiki na su yi shawara da ni ba ne da ba za su faɗa miki ba, kuma ina da tabbaci akan basunfaɗamiki dan farin ciki ko wani abu makamancin wanda ki ke hasashe ba ne, sun faɗa miki ne danki
tashi tsaye wajen tseratar da ɗanki kamar yanda ki ke ikirari daga ruɗun duniyan da ya faɗa"..... Yaya da ya fito tun fara banbamin Gude yace tare da ƙarisawa kusa da ita ya miƙa mata wayanshi tare da faɗin "ga sheda in kina buƙata, ban ajiye shi dan komai ba se dan ke na san zaki
buƙace shi" ya idda maganan tare da kunna mata videon da manager ya tura mai akan wasunesuka biya su akan su ɗaukan musu sexy ko na waye, se dai kafin su tura musu sun rufe
fuskokinsu, amma wanda suka tura mai fuskokin a bayyane yake...
Jiki na ɓari take kallo, ihu ta saki lokacin da me afkuwa ta afku tare da sakin wayan, da sauri
Balarabe ya taro tare da faɗin, "shirmen banza, in ana faɗa miki gaskiya akan ƴaƴanki ki rufeidoki fututtuke ki ce sharri aka musu, ke me salahan ƴaƴa, yanzu ma wannan sharrin ne ai" yayi
maganan tare da miƙa ma Yaya wayanshi, yana amsa ya goge, dan dama baya da niyyanbarinshi
a cikin wayan....
"Na shiga uku, na lalace, Allah ka saka mun, Allah ka ma Amina abun da ta mun, Allah ya isatsakanina da ke Amina, duk ke ki ka jawo mun wannan bala'in, ke ce silar faɗawan Sudais awannan hanyar, wallahi ba zan taɓa yafe miki ba, se Ubangiji ya mana shari'a ni da ke" ta iddamaganan cikin rishin kuka, sakin baki kawai suka yi suna bin ta da ido cike da mamaki ba taredasun ce komai ba, miƙewa Farisat tayi cikin rishin kuka tayi ɗakinta a guje, "miƙewa Sadamyayi afusace ya fara zare belt ɗin jikin shi, saurin riƙoshi Habiba tayi tare da girgiza mai kai, bandaɓari
babu abinda jikin shi ke yi, hawaye na bin kuncin shi, laɓɓan shi na ɓari amma ya kasa magana...
"Wannan wani irin magana ne Gude!" Babiya tace tare da kafeta da ido, "Babiya kar ki yi ƙoƙarinkare Amina a wannan karon, da Amina ba ta kawo mana baƙar kilakin nan ba da ba ta yandaSudais ze haɗu da ita har wani alaƙa irin wannan ya shiga tsakanin shi da ita, Amina ce ta ɗakkomana wannan jaraban ta kawo ma cikin dangi, wallahi ita ce silar lalacewan tarbiyyan Sudais, wallahi in yafe wannan kaɗai ze sa Amina shiga aljanna ba zata taɓa shigan shi ba, wallahi bazantaɓa yafe mata ba" "ka da Allah yasa ki yafe mata, ke ma ki yi fatan zunuban da ki ka kwasaAllahya yafe miki su, kar ki ƙara kuma kuskuren kiran sunan mahaifiyar mu ki faɗi wani kalma naashsha akanta, in mun jure tana da rai ba zamu jure ba ta da shi ba" Yasmin tace zuciya a wuya, da mamaki ta bi ta da ido tare da faɗin "ni ki ke faɗawa waƴan nan maganganun! Abdussamadagabanka ɗiyarka ke jifana da muggan kalamai haka ba tare da ka tsawata mata ba!" Ta iddamaganan tare da kallon Yaya, "ba abinda zance mata" yace tare da juyawa ya shige side ɗinshi
ba tare da yace komai ba....
"Yau kin tiƙeshi, kin kai haƙurin shi ƙarshe, kullum ana nunashsheki da ki iya bakin ki wajenfiddo
magana amma bakya iyawa, ko ƴaƴanki ba za su tsaya ɗaya daga cikin mu na zagin ki a gabansusu yi shiru ba, sannan ke kin tsaya a gabansu ki na zagin musu uwa da aibantata, wai meyasamuke rufe ido a duk san da gaskiya ta kawo mana ziyara ne?" Balarabe yace rai ɓace, "ta bar gidannan" Sadam yace da ƙarfi tare da fizge jikin shi a hannun Habiba ya nufeta, "fita gidan nan" yakuma cewa murya a kausashe tare da ƙoƙarin zare belt, zare ido tayi tare da faɗin "duka nazakayi?" Finciko belt ɗin daga jikin shi yayi zuciya a wuya yayi kanta a fusace, da sauri Balarabeyariƙoshi tare da rungumeshi ƙam-ƙam...
"Jeki Gude, dan Allah ki bar mu mu rayu lafiya, ke kenan, duk in kin zo kafin ki tafi se zuciyoyinjama'a ya ɓaci, na yafe miki zuwa dubanin, wallahi na yafe miki, tunda alheri ba ze kawo ki ba" Babiya tace rai ɓace, fashewa da kuka tayi me ciwo tare da ɗaukan jakanta ta saɓa ta ficeafusace....
"Kawo shi nan" Habiba tace tare da miƙa ma Balarabe hannu, ba musu ya kai shi kusa da itayazaunar da shi, banda sauke ajiyan zuciya ba abinda yake, miƙewa Suwaiba tayi da sauri danɗibomai ruwa, da sauri Yasmin ta shige side ɗin Yaya dan ba zata iya zama anan ba, wani
matsanancin kewan Anty ne ya riske ta.... Kafeta da ido yayi cikin ɗin bin mamaki tare da faɗin "kin san me ki ke faɗa kuwa?" "Na sani, inasane da abinda na ce, bansha ƙwayan ba tukun, duk abinda ka ke ji da shi Sudais na takakanamurje, wallahi ko da uwarka ka ke kwana yau se ka neman mun wajen da zan zauna, kai nesilarkomawana ruwa, se da ka tabbatar ka gama tarwatsa rayuwata Sannan zaka zame ka barni, tobari kaji yanda muka faro daga farko se mun kai ƙarshe, se da na gama haddace duk wani
darasinka sannan ka ke shirin yayeni bayan kasan da sauran wani ilimi da zan buƙata, ina zaunena lafiya a sabon rayuwar da ya kawo mun gayyata har gida, ban ne me ka ciki ba ka kutsokanka, na zubda duk wani ɗabi'un banza da nake da shi a lokacin, ina gudanar da rayuwa me tsaftaagidan Barr Amina, ka tarwatsa komai ka riƙe hannuna muka taka fara taka ruwa da dukkaninwani kulawanka se da muka shiga tsakiya zaka zare hannunka ka barni in lume, to ba ka isaba,
tare zamu nitse, komai ta fanjama famjam" tayi maganan zuciya na tafarfasa, "cika munriga" yace idon shi akan ta, ba musu ta cika mai na ta idon akan shi, tsaki yaja me sauti ya ja kujerayazauna tare da danna number ya kara a kunni, a na ɗagawa yace "a kwai ɗaki a gidan nanne?" Sauraran amsan da aka ba shi ta can yayi kafin yace "okay" sauke wayan yayi tare da jankujeranya miƙe fuska ɗaure yace "muje" yana idda faɗi ya juya ya fice kaman ze tashi sama, taɓe baki
tayi ta miƙe ta ja akwatin ta dake ta bayan kujeran da take kai ta dafa mai baya.... Zaran tissue yayi ya goge baki ya ja kujeran baya ya miƙe a natse, zare ido waje Insu dakesatankallon shi tayi tare da faɗin "Uncle har ka ƙoshi? Ai ba ka ci da yawa ba" lumshe ido yayi zuciyanshi na tsintsinkewa, dan muryanta na tuna mai da abubuwa masu tarin yawa, murmushi Jabir yasaki tare da miƙewa a natse, "muje" yace a hankali tare da wuce shi, bin bayan shi yayi a natsesuka yi cikin parlor, kwaɓe fuska tayi tare da kallon Ibrahim, murmushi ya saki tare da tashi yabi
bayan su, murmushi Hajiya ta sakin mata tare da mata alamun tayi haƙuri da ido....
Juyawa ga Abubakar tayi tare da kwaɓe mai fuska, harara ya banka mata ya janye ido, jankujerayayi ya miƙe a natse, murmurshi Hajiya ta saki tare da faɗin "Abubakar me Insu ta maka hakane?Na ga se hararanta ka ke" murmushi ya saki tare da faɗin "Hajiya wannan daughter na mubaji
take ba" yayi maganan tare da sakin murmurshi, murmushi ta saki tare da faɗin "to a mataafwa""shi muke tayi Hajiya har da uzuri muke haɗawa, amma na kusan tattara ta da matsalolintainkai
gaban brother Jamil" ya idda maganan tare da wuce wa parlor, kwaɓe fuska tayi tare da kallonAlhaji Jamil dake sakin murmurshi, "rabu da shi, in ya miƙo ma ajiyewa a gefe zamu yi" dariyataƙyalƙyace da shi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 31 Chapter of 109