Share this page
Baza ido suka yi cike da mamaki ganin Khalim na taka rawa shi da wata kyakykyawan budurwawacce zata iya kai 24, yana ganin su ya saki murmushi tare da fita daga filin ya yo inda suke, murmushi Nachma ta saki tare da faɗin "ashe ka iya rawa?" "Ina koyo" yace tare da kafa kai aruwan da be ankara da wanda ta ba shi ba, "hi Insu" wani matashin saurayi ɗan shekaru 22dahaihuwa yace tare da kallon ta.... Kallon shi tayi da mamaki tare da faɗin "a ina ka san sunana!" Murmushi ya saki tare da faɗin"ranar registration ne" murmurshi Nachma ta saki tare da faɗin "aiko na gane ka, kana wajen" murmushi ya saki tare da faɗin "ina gefe, Insu kin burge ni sosai, kin burge Babana ma" guntunmurmushi ta saki tare da kauda kai, "sunana Hisham, zamu iya zama abokai?" Yace cike dakulawa fuska faɗaɗe da murmushi, bin shi da kallo me cike da mamaki tayi, ita fa ba ta taɓazaton akwai me sunan nan ba bayan Dr Hisham, girgiza kai tayi tare da faɗin "ba na abotadamaza" "to ɗan uwa please" yace cike da magiya, "na san duk fuskokin ƴan uwana, amma banwayi na ka ba" tana kai nan ta wuce ta barshi sake da baki, murmushi Nachma da ta ɗan fara fahimtanta ta saki tare da kallon Hisham cike da basarwa tace "me ka zaɓa?" "Kiɗa" yace fuskakadaran kadahan.... "Ina take?" Khalim da ya sauke bottle ɗin ruwa yace tare da kallon Nachma, nuna mai indamakaɗa ke ta kiɗa tayi a natse, murmurshi ya saki saboda hangota da yayi tare da nufar wajen, tsaki wacce ta ba shi ruwan tayi tare da wuce wa inda wacce ke rawa da shi ke tsayuwanjiranshi... "Wani course ka zaɓa?" Nachma tace idonta akan Hisham, murmushi ya saki tare da faɗin"civil law" murmushi ta saki tare da jiniija mai kai, "a wani gari ki ke?" Yace da kulawa, murmushi tasaki tare da faɗin "Yarban" "akwai sister na dake aure a can" yace fuska faɗaɗe da murmushi, "kaifa?" Tace tare da gyara tsayuwa, "Bertuwa" yace a natse, "wow garin ku ɗaya da Insu" tacedamamaki, zare ido yayi tare da faɗin "da gaske!" "Yeah, ƴar Bertuwa ce ita ma" "ma sha Allahwani course ta ke karanta?" "Course ɗin mu ɗaya" tace tare da maida hankali ga inda take ... "Me ki ka zaɓa? Ba dai kiɗa ba?" Yace tare da bin ta da ido fuska faɗaɗe da murmushi, kallonsakanni ta mai tare da faɗin "akwai matsala ne?" "No amma zan so ki koyi rawa, dan ze fi dacewadake" murmushi ta saki tare da kauda kai.... "Wacece ita?" Wacce ke tsayuwan jiran shi tace tare da kallon ƴar former governor da ta ƙarisakusa da ita, ɗaga kafaɗa tayi cike da rashin jin daɗi tare da faɗin "I don't know, amma ita cewacce na faɗa muku ta yi ta farfaɗan maganganun nan a Office ɗin registerer" jinjina kai tayi tare da faɗin muje" tana kai nan ta nufi inda Insu ke tsaye da Khalim... "Hi l'm Minakshi future wife ɗin shi" tayi maganan tare da nuna Khalim da hannu, kallonsakanni Insu ta ma hannun tare da faɗin "Insu" tayi maganan a taƙaice, "wow na so sunan ki gaskiya, ba lefi ya mun daɗi, ƴar sarkin Yarban ga coursin sister na ƴa former governorn jahar Yarban, ƙanwar my soul, zan iya sanin wacece ke?" Bin wanda ta nuna tayi da ido kafin ta kauda kai tareda faɗin "ai na faɗa miki" "Minakshi" Khalim yace tare da mata alamun ta wuce da ido... "Meyasa? So nake mu san juna, na ji labarin kun san juna sosai" "oh god ba na son rigima" yacekaman ze saki kuka, murmushi Insu ta saki tare da raɓesu da nufin barin wajen, "mijin da zanaura ne shi, ki tabbatar kin ba da tazara me yawa a tsakanin ku dan bana buƙatan wani alaƙayashiga tsakanin ki da shi, ko da na gaisuwa ne" Minakshi tace idonta ƙyam a bayan Insu.... Kallon Nachma da ta zuba mata ido tayi, murmushi ta sakin mata tare da juya mata ido, murmushi ta saki tare da bin ta da ido, juyawa tayi a natse cike da rashin ɗaukan abinda tacedamahimmanci tare da faɗin "shi za ki ma wannan gargaɗin, ba na maida hannun kyauta a duksanda aka miƙo mun" tana kai nan ta raɓesu, "wannan yarinyar ƴar rainin wayauce, ba na faɗamiki maganganun da ta dinga faɗawa Daddn mu ba ranar nan" Sunaina tace cike da ɓacinrai, "Sunaina!" Khalim yace tare da banka mata harara, "no brother ka fa ji maganganun da tayi tafaɗan ma Daddy" tace kamar za ta saki kuka, riƙota yayi tare da faɗin "is okay, bar maganan"... "Taɓe baki Insu tayi tare da faɗin ina ne wajen raye-rayen tunda ance dole muyi" murmushi Khalim ya saki tare da faɗin "oh dama shi ki ka zaɓa? Okay muje gayi can" "no my soul ba zatashiga group ɗin mu ba gaskiya" Minakshi tace tare da ɓata fuska, "oh Dear ba na son rigimafa" murmurshi Insu dake bin su da ido ta saki tare da faɗin "wai wa za'a koya wa ne?" "Ke" Nachmada ta ƙariso wajen tace tare da sakin murmushi.... "A'a ku barshi na hutashshe ku, da iyawata nake tafe" tayi maganan tare da juyawa ga Minakshi da ke cewa "au ke a haka nan kin iya kenan?" "Tabbaci ki ke son gani?" Tace a dake idontaƙyama saman fuskanta, "zan so hakan" tace ita ma a dake, "to a ba mu waje" tace tare da sakinguntunmurmurshi idonta na yawo a saman fuskanta, juyawa Minakshi tayi tare da ba su umurninsufitadaga filin, nan da nan kowa ya fice, "no Insu bar wannan batun" Khalim yace dan sanin waceceMinakshi a rawa, "my soul" Minakshi tace tare da shagwaɓe fuska, "music" tace tare da nunakaman ba ta ji abinda yace ba, ana sakin waƙa Minakshi tayi wani tsalle ta faɗa filin, da gasketaiya rawa ba ƙarya, yanda take juya jiki da tsalle-tsalle, da juye-juye ya isa sheda ma me kallogwanancewanta.... Ihu sauran students suke suna tafi, se da ta kusan kai mintuna ashirin ta na yi kafin ta tsagaitatare da ficewa tana sakin numfarfashi, wani nagartaccen murmushi Insu dake bin ta da idotasaki tare da ciro jakanta ta miƙa ma Nachma, fara cire maɓallan abayanta tayi a natse, tanacirewa ta miƙa mata, duƙawa tayi a natse ta cire takalmin ƙafarta ta ajiye a gefe, warwareveil ɗin kanta tayi ta miƙa ma Nachma, "wow" Nachma tace saboda arba da tayi da baƙin gashintadake kame da ribom, se ɗaukan ido baƙin yake da alamun yana samun kula na musamman, gyarazaman t-shirt ɗin jikinta tayi ta wuce filin a natse.... "Music" tace tare da kallon wanda ke tsaye a gaban manya-manyan sifiku, music ya saki metsuma zuciyan me saurare, a slow ta yi ƙasa kamar mara lakka, a hanzarce ta ɗago tare dajuyaƙugunta tayi baya da dukkanin ƙarfinta, "subhanallah" Nachma tace cike da razani, ihu sauranstudents suka saki dan ba kaɗan ba salon ya burgesu, yanda take juya jiki da lanƙwasawa, dayanda take juyi da tsalle kaman za ta tashi sama shi ya ɗau hankulan masu kallo, nan ruwantafi ya tashi, Insu da tunaninta ya koma Bertuwa kuwa ƙara ƙaimi da azama tayi, yanda kasanbabuƙashi a jikinta tana gamawa ta fice tare da amsan ruwan da Hisham ya miƙa mata "thanks" tacetare da amsan abayanta ta maida, takalminta ta zura ta saɓa jaka tare da faɗin "4:57pmmuje" tana kai nan tayi ƙofan barin wajen, bin ta Nachma tayi tare da faɗin "wow dama haka ki kaiyarawa!" Murmushi ta saki tare da juyowa cike da yanayinta ta sauke ido akan Minakshi taredafaɗin "kar ki ƙara gan-ganci gwada gasa da ni, za ki ji kunya, juya dubanta ga sauran studentsdake tsai-tsaye tayi tare da faɗin "duk me son shiga group ɗina ƙofa abuɗe take, white dancer'sza su ba su wuta" tana kai nan ta juya suka fice, da sauri Khalim ya bi su.... Murmushi Hisham ya saki tare da faɗin "yanda Abba yace haka take" murmushi wacce ketsayekusa da shi tayi tare da faɗin "tun ranar registration na san za'a sha fama" dariya ya saki taremata alamun su wuce, ƙwafa Minakshi ta saki tare da ɗaukan bottle ɗin ruwa ta kafa kai.... Tun daga nesa ta hango Ibrahim dake tsaye, murmushi ta saki tare da kallon Nachma cikedakulawa tace "koma gayi can ya zo ma" "no muje in raka ki" tace tare da sakin mata murmurshi, bamusu suka ƙarisa, murmushi ta sakin mai tare da faɗin "ba dai ka daɗe ba?" "Ba sosai ba" yacetare da amsan jakanta ya cire ID card ɗinta ya miƙa mata, "oh na manta ma da shi" tace taredasakin murmushi, "dama za ki manta ai" yace tare da banka mata harara, dariya ta saki taredafaɗin "ga friend ɗin da nayi yau, Nachma" tayi maganan tare da nuna mishi Nachma daketasakinmurmushi.... Murmushi ya saki tare da faɗin "sannu Nachma" "yawwa Yaya kana lafiya?" "Alhamdulillah" yaceda kulawa, "ga abokinta Yaya ba ta faɗa maka ba Khalim" Khalim da ya ƙariso wajen yacetaredaba shi hannu, ba shi na shi yayi da kulawa tare da sakin murmushi... "To banda wasa a maida hankali sosai please" yace tare da bin fuskokin su da ido, "in sha Allah" suka ce bakuna a haɗe, "muje ko" yace tare da mata alaman ta shige, da sauri ta shige taredaamsan jakanta, sallama ta musu ya shige driving side, yana shiga ya ma motan key suka bar wajen, murmushi Nachma ta saki tare da juyawa, "oh tafiya za ki yi ki barni?" Yace tare dabinbayanta murmurshi ta saki ba tare da ta juyo ba.... Suna ficewa daga makarantar ta gyara zama tare da faɗin "Ibrahim yakamata in iya drivingfa" murmushi ya saki tare da faɗin "har yanzu ba ki iya ba?" Kwaɓe fuska tayi tare da faɗin "ai nahaƙura da koya ne, dan Yaya Salman da Sadam ba su iya koyawa yanda yakamata ba, ranar nansaura kaɗan Farisat ta buge wata tsohuwa, da ƙyar ta kauce mata, se masifa suke mata, Sadamhar da bugunta a kai" dariya ya saki tare da faɗin "bari weekend se mu dinga bi ta" "ho ni" tacetare da sakin ƙara ta ɗaga hannu.... Murmushi ta saki tare da faɗin "bi dai a hankali, in kin maida hankali a kai wata huɗu ne kiniya" "ai kafin lokacin ma zan iya in sha Allah" tace cike da gamsuwa da kanta, "sister Lailah ta kirani ɗazu" yace a natse idon shi akan hanya, "me tace?" Tayi tambayan tare da ba shi natsuwarta.... "Salwa ta shigo jiya da yamma" zare ido tayi tare da faɗin "ko zamu biya ta can ne?" "No ki jiraƙarshen bayanin mana" "okay ina jinka" tace tare da gyara zama, "jikin uncle ɗin mijin na tayayi tsanani da yawa, sun ɗaukeshi da safe sun koma can" "har da Anty Salwan?" Tace jiki a mace, "ehhar da ita" yace tare da kallon ta, ɓata fuska tayi tare da banka hararan da ba wanda yasantayi, murmushi ya saki tare da faɗin "tace ita kanta ba ta ji daɗi ba, a baki haƙuri" "to su ba za suzobane?" ta mai tambayan cike da rashin jin daɗi, "bata dai ce mun ga ranar zuwan su ba, ammainzan baki shawara ki ɗauka kar ki takura musu akan zuwa, ki barsu duk sanda suka ga za suiyazuwa su zo" jinjina mai kai tayi cike da gamsuwa.... After one year Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Twenty one "Subhanallahi ka fahimce ni mana Sudais" Sa'adatu dake tsaye a bakin ƙofar class ɗin sukaredawaya a kunni tace kaman za ta saki kuka.... "Ba na da matsala da fahimtar da ni da ki ke son yi, na riga da na faɗa miki, se ki zaɓi wandayafi daraja tsakanin ni da exams ɗin" muryan Sudais ya bayyana rangaɗaɗau cike da kaushi a ƙarshenmaganarshi, "ka fa san wannan shine ƙarshen dama da school ta ba ni, sannan Yaya ma yasani, Sudais in ban zana jarabawarnan ba korata za su yi" ta idda maganan cike da damuwa... "Se me in sun kore ki? Me ne ne dama karatun ze amfana miki? Ke bari ma fa kiji in dai har ni ki ke fatan aura ba wani aiki da zaki yi a gidana, dan wallahi akan wannan se dai mu haƙura dajuna" zare ido tayi kaman yana ganinta tare da faɗin "dan Allah me ya kawo wannan kalmankuma?" "Ke ki ka kawo ta, ina jiranki yanzu akwai wani banzan magani da Habib ya ba ni nashagab yake da zawata ni" "am zan zo yanzu" tace a hankali, "ba zaki zo ba, wallahi ki kai ƙasada10to 15 minute's to ki san wajen wanda zaki zo" yana kai nan ya kashe kiran ɗif.... Zaro wayan tayi jiki a mace tare da bin wayan da ido kaman wanda ke neman wani abu, saukenumfashi me ƙarfi tayi ta koma cikin class, tana shiga waƴanda za su kula da su suka shigo, ɗaukan jakanta tayi ta rataya a kafaɗa tare da nufar ƙofa, da sauri Rahma ta miƙe ta bi bayanta.... "Sa'adatu, Sa'adatu" tace da ƙarfi, tsayawa cak tayi tare da juyowa fuska a ɗan ɗaure, "inazaki za'a fara exams yanzu!" Tace cike da mamaki, "ji nayi kaina na juyawa" tace tare da yamutsafuska, "Sa'adatu kin san mahimmancin exams ɗin nan kuwa? Shine fa wanda ze tabbatar dakeacikakkiyan ma'aikaciyar lafiya" "kinga Rahma koma ke ki fita da abinda ki ke son fita, ce miki nayi fa kaina ke masifar ciwo, dan me zaki zo tsakiyan kaina kina min ihu, koma ke ki zana ki fitadaabinda ki ke son fita, dan Allah kar ki nemi tarwatsamun kai" tana kai nan ta juya ta bar wajendasauri, bin ta da ido kawai tayi ta na jimanta al'amarin na ta, ganin ba juyowa za tayi ba ya sataɗaga kafaɗa ta juya ta koma ciki... Murmushi Yasmin dake zaune gefen Farisat riƙe da baby boy dake cikin shiga na alfarma tasaki tare da faɗin "wato abun ba wuya Allah ya shiryeki takwaran Anty" murmushi wacce ke zauneagefe cikin gun-gun jama'a ta saki tare da faɗin "da gaske fa maganata Yasmin, ana aurensehaihuwa yanzu, dubi dai yaushe aka yi auren ga shi yau mun dawo suna" murmushi Farisat tasaki tare da faɗin "wallahi da gaskiyan ki Anty na, abun ba wuya, na Hajiya tace yanzu kamantuntuɓe ake da cikin daga bakin ƙofa" dariya suka saki gaba ɗayan su tare da bin ta da ido, "kyaceba wuya mana, ai kina gab, zaki mana bayani ne" Laɗifa dake zaune cikin shiga na alfarmatacetare da banka mata harara... Ƙaramar dariya mara sauti ta saki tare da faɗin "ai mu ba haihu, munyi ma da wajewa" "ahlallai kuwa, wato kun yi da wajewa" humen leader tace tare da sakin dariya, "wallahi sister Sadiyabazan iya haihuwa ba, na tsorata da wannan lamarin, Anty ta zo haihuwa ta rasu, Zuwaira mahaka, ba wacce ta kai ga haihuwa, ta ya zan yarda da wani ciki" ta idda maganan cike da bayyanatabbacin ta, murmushi vice humen leader ta saki tare da faɗin "to ya amince?" "Ya ze yi ai dolene" tace tare da kauda kai, dariya suka kwashe da shi tare da bin ta da ido.... "Ku ba na son ɗiban albarka" tace tare da banka musu harara, murmurshi Yasmin ta saki taredafaɗin "ni zan so fa in zo haihuwa in mutu, ina son ganin Anty" tace a natse, bin su da ido akwai suka yi cike da jajantawa, leƙowa parlorn Annur yayi tare da yafuto Yasmin... "Ni wannan ƙafa na ka Ali ya fara ba ni tsoro, ƙafa se ana murna ya warke kana shiga tashayadawo ɗanye, anya maganan Gude na jifanka aka yi ba gaskiya ba ne kuwa?" Babiya dake zauneasaman tabarman da Baba Tinene ta shinfiɗa musu ita da Suwaiba da Habiba da Balarabe tacecike da nuna zallan tausayawanta, murmushi ya saki tare da faɗin "to gamu nan dai Hajiyamunata faɗawa Allah, Allah shiyasan me ke ɓoye mu ba mu isa sani ba" "haka ne, amma ni da zakaji shawarata da ba ka tsayawa na asibitin nan kawai ba, ke Tinene ina kawunkin nan da ke badamagani?" "Yana nan" tace a hankali, "ai da kin kai shi sun gani ko da temakon da za su ba shi, base Abdussamad ko ƴaƴan shi sun ji ba, lafiyan Allah ayi a gama, amma a ce rayuwa a hakazeyuwu, in ka fita wajen sana'a kuma se cuta ya miƙe"... Ta idda maganan cike da jimantawa, "in sha Allah Hajiya zamu je ko zuwa gobe da safe ne" "toAllah ya yarda, na sanka Ali dan Allah in an amso maganin nan ka sha, wannan tsirface-tsirfacenduk a ajiye a gefe, Allah ya yaye maka abinda ke damunka, ya maka albarka" "amen-amenyacecike da jin daɗi, "to ku kuma ku mu koma gida kafin yaran nan su riga mu" tace tare da kallonsuSuwaiba, "to Yaya Ali Allah ya ƙara lafiya" suka ce da kulawa, "amen nagode sosai, Allahyabar zumunci" "amen" suka ce jikkuna a mace.... Miƙewa Balarabe da ya kawosu yayi tare da miƙa ma Ali hannu cike da kulawa yace "to malaminbari mu lallaɓa mu koma, Allah ya sa ya zamo kaffara" "amen" yace tare da miƙa mai na shi hannu, murmushi Baba Tinene ta saki tare da faɗin "ango me jiran gado" "na'amuwar gidamecapasity, ya aka yi ne" ya jefa mata tambayan tare da sakin ƙayataccen murmushi, "oh ni TineneBala ba kunya ba tsoron Allah ka ke amsawa" kallon ku ji ni da wannan mata ya musu taredafaɗin "ah to kunyar wa zanji anan? Hajiya ko su Suwaiba?" "A'a bar zancen kar ka goge munhadda" tace tare da sakin ƙaramar dariya.... "Kin kyauta ma kan ki da ki ka yi shiru, Hajiya muje" Suwaiba tace tare da nufa ƙofa danbaringida, har bakin mota Tinene da Ali suka raka su, sallaman juna suka yi suka kaman hanyar gida, su kuma suka koma.... Jakanta dake maƙale a gefe ta ɗauka ta saka a baya tare da kallon matasan samari da ƴanmatandake ta faman bitan rawar da ta koya musu tare da faɗin "a cigaba da bi ta" "to su ka ce taredasakin mata murmurshi, juyawa tayi ta fice daga wajen, kai tsaye restaurant ta nufa, tana shigatahango Khalim da Minakshi da Sunaina suna zaune su suna cin abinci shi yana zaune waya riƙeahannun shi, jan kujera tayi ta zauna tare da zaro waya ta danna number ta kara a kunni.... "Kina ina ne?" Tace tare da tattaro natsuwa dan jin amsan da zata ba ta daga can, "okay pleaseki hanzarta yunwa nake ji sosai" tace tare da sakin hamma..... "Gani nan" tace tare da sakin ƙaramar dariya, sauke wayan tayi a natse tare da kafe Hishamdaido, murmushi ya saki tare da goge hawayen da suka zubo mai, "please ka zama namiji mana, kadaina kuka, zan faɗawa Insun in sha Allah amma maganan wai ka haƙura da school be ta soba" tace cike da tausayawa, jiniina mata kai yayi tare da goge hawaye ba din yaji ze canza shawaranda ya yanke ba, miƙewa tayi ta fice daga Coffe shop ɗin,.... Jan kujeran dake gefenta Khalim yayi tare da faɗin "Malama yau dai ke ce da biyan bill" dagokai tayi ta watsa mai harara tare da faɗin "ba kaji da kyau ba ne" "wallahi ke ce bari Nachma tazokiji" "me za'aji?" Nachma tace tare da jan kujera ta zauna, "yawwa Nachma wa ke da biyanbill yau?" "Ita" tace tare da sakin dariyan hararan da Insu ta banka mata, "wallahi ke ce, ranar Monday ni, jiya Khalim yau ke" tace murmushi be bar saman fuskanta ba, amsan littafindaakamiƙo musu tayi tare da faɗin "ba kuji da kyau ba ne, account ɗina yayi asalin lowku ɗaunaannabawa".... "Ai me sauƙi ne zamu iya binki ba shi" Khalim yace tare da amsan littafin a hannunta, "wallahi baku isa ba, ba me bi na bashi, ina zaune ƙalau ku sani mafarke-mafarke marasa fai'da" tacetaredawatsa musu harara, dariya suka saki tare da bin ta da ido, "shikenan se ki biya" yace idonshi akanta, "na ji" tace tare da tsiyaya ruwa ta kai baki.... "Wallahi da baka zo ba tafiya zanyi, na ce maka akwai abinda zanyi me mahimmaci ammakashanya ni" Salman yace tare da kallon wanda ke zaune a kujeran me zaman banza, hararayazabga mai tare da faɗin "yanzu me ne ne na jan zancen? Ba gashi na iso ba, manta dan Allah" harara ya zabga mai tare da faɗin "yanzu ya ake ciki? Can zamu wuce?" Yace tare da kallonSalman, jinjika mai kai yayi tare da kallon shi, "okay muje ɗin kawai?" Yace tare da kallonshi, "zamu bi ya ta wani waje mu ɗakko su se mu wuce can" "abinda yakamata ke nan" yace taredasaka belt.... "Wai me ma ya kawo ka nan ne?" Yace tare da juya akalan motan zuwa hanyar fita, "wallahi nazoganin vice chancellorn makarantar ne, ban ƙarisa ma abinda ya kai ni ba kayi ta kira, hakanannasallame shi na fito" "oh kace duk kiran da nake maka kana min ƙaryan ga ka nan kana ma zaunene" yace tare da dai-daita motan akan hanyar da ze sa dasu da gate, da mamaki yabi Sa'adatudata gittasu da sauri da ido... "Wacece wannan? Kaman Sa'adatu" yace tare da ƙure ta da ido, kallon Sa'adatu dake ƙoƙarinficewa daga gate na kusa da shi yayi tare da faɗin "kasanta ne?" Yayi mai tambayan cike damamaki, kallon sakanni ya mai ya kauda kai tare da faɗin "sister na ce" "wannan ɗin!" Yacemamakin shi na bayyanuwa, "eh menene?" Yace tare da kallon shi, "no ba komai, ban taɓasaninhakan ba ne, ko da yake ba cika son a san wani na ka kake ba, da yaya ma na san Farisat sedanahaɗa da sallahn dare" murmurshi ya saki idon shi akan Sa'adatu cike da mamaki.... Ficewa suka yi daga gate ɗin har ya ɗau hanya ya tuna Rahma tace mai suna da final exams yau, kuma yasan class ɗinsu ɗaya, taka burki yayi tare da zaro wayanshi idon shi akan mirror motan, danna number Rahma yayi ya kara a kunni, tana ɗagawa yace "kina ina?" "Class" tace dagacan, "me ki ke yi?" "Yanzu zamu fara exams lafiya kuwa?" Tace cike da tsarguwa, "yanzu kuma! tomeya fiddo Sa'adatu kenan?" "Tace wai kanta ke ciwo, nayi-nayi ta zauna taƙi, kuma wallahi indai tafaɗi a wannan exams ɗin koranta za su yi" tayi maganan cike da rashin jin daɗi, "okay" yacetareda sauke wayan a hanzarce ya taka motan ya juyo da sauri ganin ta shige napep, "meya faru?" Nakusa da shi yace tare da kallon shi, "Usman akwai matsala, na daɗe ina zargin wani abu, inagaranar tabbatar da gaskiya ne ya zo" yana maganan hankalin shi gaba ɗaya akan number napepɗin da Sa'adatu ta shige... "Ka sani a duhu" yace da mamaki, "shii please kar ka ƙara cewa komai tukun" yace tare dakallonshi, komai be kuma cewa ba, se maida hankali ga hanya da yayi, tafiyan kusan mintina 20sukayi, taka burki yayi nesa da inda me napep ɗin ya taka na shi, fitowa tayi ta ba shi haƙƙin shi tashigeda sauri, fitowa yayi cike da mamaki tare da bin inda ta shiga da ido, "SD hotel!" Yace zuciyanshi na ƙaryata abinda idanuwan shi suka gani.... "Salman wai me ne ne?" Usman yace tare da dafa shi, "mu shiga Usman" yace tare da rufemotanya nufi ciki a hanzarce, dafa mai baya Usman yayi cike da mamaki... Miƙa ma Farisat babyn tayi ta miƙe a natse ta fice, tana fita ta hangoshi zaune a farar kujeranroba dake madai-daicin garden ɗin gidan, murmushi ta saki tare da ƙarisawa ta ja na kusadashi ta zauna, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "ƙanwata idon ki kenan?" Fiddo ido waje tayi tare da faɗin "Allah yasa ba lefi nayi ba?" "Hmm Yasmin ki na ba ni mamaki" yace tare da gyarazama.... "Please Yayana in wani lefi na yi dan Allah ka faɗa min, wallahi wannan zantukan fargabasukesani" tace kaman zata saki ihu, kafeta da ido yayi cike da nazarin kalamanta kafin yace "meyasaki ke nuna kaman ba ki san komai ba? Yasmin meyasa za ki yi watsi da dukkanin wani alamadaShureim ya nuna miki? Na san kin san me yake nufi a dukkanin wani motsin shi, na san kinfahimci inda ya nufa a dukkanin furucin shi, meyasa ba zaki amince mai ba? Yasmin na sanShureim tun ban gama sanin kaina ba, mutum ne me hankali, mutumci, natsuwa, kamala, sanindaraja da kiman kowa".... "A ɗan zaman da ku ka yi damu a group na san kun fahimci haka, duk saboda kyakykyawanzuciyan shi group ɗin Aminan juna ya kai

Chapter 27 of 109