Share this page
shi ya faɗa kan matasanyaranshi guda biyar ko wanne da duniyar da ya faɗa, murmushi ya saki tare da faɗin "wa zekaranta mun a cikin ku?" Yayi magana tare da ɗaga littafin sama, kallon shi suka yi kafinkowannenzj ya kauda kai, "please baby's" yace murya a hankali, "sorry Yaya bama cikin wannanyanayin" Farisat tace tare da kallon shi, "in na ce Anty ce tace ku karanta mana fa?" Yace idonshi akan su, zube mai ido suka yi cike da son gano wasa yake ko gaske, ganin irin kallon da yakemusu yasa Sadam da Yasmin saurin tashi sukai inda yake, "ni zan karanta" Sadamyace taredason amsa, "ni ce Yaya" Yasmin tace tare da kai na ta hannun, murmushi ya saki ganin yandaInsuda Farisat suka zuba mai ido, "Yaya ni zan karanta" Nafisat tace a sanyaye, "duk ku tsaya" yacetare da riƙo hannun Yasmin, shagwaɓe fuska tayi tare da kallon shi, "arrijalu?" Yace tare dakallon ta, "kawwamuna alannisa'i" tace tare da tura baki, dariya Sadam ya saki tare da faɗin"tojeki zauna" ba musu ta koma inda ta tashi, "kai ma ka nemi waje ka zauna" Yaya yace taredaƙarisawa tsakanin Farisat da Insu ya zauna tare da riƙo hannayen su.... Zama a tsakiyan Yasmin da Nafisat yayi tare da kallon bangon littafin a natse, "MUGUNTSOKA" yace cike da mamaki, ɗago kai yayi ya kalli Yaya mamaki be bar saman fuskan shi ba, murmushi ya sakin mai tare da kallon Insu da ke kallon shi, "karanta mana" yace ba tare da ya kalli sauranda yake jin kaifin idanun su akan shi ba, jinjina kai yayi tare da gyara zama ya buɗe littafinanatse, "sunana Insiyyah, Insiyyah Sa'eed, na rubuta labarin nan ne dan ku ƴaƴana" Sadamyacetare da ɗago kai, "ka karanta dare nayi za kaje ka kwanta" Yaya yace ba tare da ya ɗago kai ba.... "Ni ƴar asalin garin Ɓadamayya ce, nan ne tushena, mahaifina Alhaji Sa'eed Garba, cikakkenɗanboko ne, mahaifiyata Yasmin Saleh, karatun ta be yi zurfi sosai ba, ina da brothers biyu HassandaUsaini, Allah yayi wa Usainin rasuwa tun a yarinta, ni ce ta biyu a gidan mu, ina da ƙanni ukudukan su mata, Lailah, Khadijatu, Salwa" kallon Yaya Insu tayi tare da faɗin "Anty sunantaInsiyyah ne!" Tayi tambayan cike da mamaki, jinjina mata kai yayi tare da matse hannuntadaɗanƙarfi alamun tayi shiru, "muna jinka" Farisat da ta tattaro natsuwarta gaba ɗaya ta ba shi tacetare da ware kunnuwa.... "A yanda mahaifin mu ya ba mu labari mahaifin shi ne ya zo garin Ɓadamayya neman kuɗi ammasu ƴan asalin garin Kautal ne da yake arewacin ƙasar mu, anan aka haife shi, anan ya tashi ananyayi duk wani gwagwarmayan rayuwa, mahaifin mu yana da wani amini guda ɗaya me sunaAlhaji Sadam Sahabee, tun yarinta suka tashi tare, sun ma juna sanin da ba wani wanda yasansuhaka, hatta da iyayen su, Alhaji Sadam be zurfafa ilimin boko ba, sana'an gidan su ya riƙe dashi ya taka duk wani matsayi na rayuwa, yana da mata ɗaya Hajiya Farisat Inuwa, suna da yarabakwai, babban ɗan shi Jamilu se me bi mishi A'isha, se na ukun su Sahabee, se na huɗuLubabatu, se na biyar Kamil, se na shida Yasmin se na bakwai Kausar, duk abinda ke cikingidanmu yana cikin gidan Alhaji Sadam, bangon gidan mu ɗaya, ba abinda ba ma ji daga gidajenmu, mun taso kan mu a haɗe dan iyayen mu ba su yi wasa da haɗe kawunan mu ba, ganin ƴanuwanjuna muke wa juna, yaran shi za su shigo gidan mu su yi duk abinda suke so mu ma zamushiganasu mu yi duk abinda muke so, yanda kan mu yake a haɗe mu yara haka na iyayen mu yake, baajin kan su, komai za su yi tare suke yi".... Yanda ba'a jin kan iyayen mu haka mu ma yara ba'a jin kan mu, ni da Yaya Sahabee duk dababu tazara me yawa a tsakanin mu, iyayen mu sun ce tazaran sati biyu ne, shi ya ba ni munyi matuƙarshaƙuwa yanda ba zaku iya hasasowa da misaltowa ba, yana matuƙar ji da ni ba wanda besandahaka a anguwar mu ba, zan toni faɗa amma in fita da gaskiya dan ina da Yaya Sahabee, bayadaisashshen lafiya likitoci sun sanarwa iyayen mu ya zo da raunin zuciyase dai be yi ƙarfi sosai ba, ko da yaushe yana kan magani, haka muka taso muka tadda shi, dalilin wannan laluranyasaiyayen mu ɗaukan ƙauna suka ɗaura mai, lokacin da aka ba mu labarin laluran da yake ɗaukedashi, na ƙara dage damtse akam shaƙuwar dake tsakanin mu, a hankali shaƙuwar mu ta juyezuwa amintaka me ƙarfi, lokacin da girma ya fara hararan mu, iyayen mu suka fara samumuyi baya-baya da juna, se dai mun kasa, da suka matsa Yaya Sahabee ya kwanta ciwo rurus, anansuka sallama komai suka bar mu se dai idanun su be kauce daga kan duk wani motsin muba, alokacin da muka shiga sss2 Yaya Sahabee ya sanar dani irin tarin ƙaunar da yake mun, banyi wata-wata ba na amince ni ma na bayyana mai abinda ke cikin nawa zuciyan, da kan mumukasamu iyayen mu muka faɗa musu abinda ke zukatan mu, sunyi farin ciki sosai se da sunjakunninmu akan kar mu saka wasa a karatun mu, sannan sun yanke hukuncin bayan kammala karatunmu na gaba da sakandire za'a mana aure, duk da yanayi na shekarun mu ɗaya amma ba wandayamaida hankali akan wannan, ba ƙaramin farin ciki mu ka shiga ba a lokacin, nan muka buɗebabukan shan soyayya me cike da aminci".... "Soyayya muke me tsafta da sanin yakamata, duk da shekaru da muke ciki na girma ammaYayaSahabee be taɓa mun wani kallo na daban ba bayan wanda ya sa ba mun, dai-dai da yatsanabetaɓa kamawa da wani manufa na daban ba, asalin zallan ƙauna kawai yake nuna mun, ba wandabe sheda wannan ƙauna a anguwar mu ba, muna matuƙar burge da yawan su, ni kaina mashedawannan ƙauna, muna kammala sakandiri aka nema mishi babban jami'an dake Uk ni kumaakanema min na cikin garin Ɓadamayya, ba mu so haka ba, mun so mu tafi jami'a ɗaya kamar yandamuka faro karatu tun farko, mun sha kuka, munyi fushi, munyi zuciya da abinci, daga bayadaiyayen mu suka zaunar da mu suka mana nasiha se muka zubda makaman yaƙi, da kaina nashirya mishi kayan da ze yi tafiya da shi, ranar da ze tafi na kasa fitowa ko main parlornbareinshiga gidan su, haka ya shigo har ɗakina, ina kwance a saman gado nayi rub da ciki bandakukaba abinda nake, zare takalmin dake ƙafan shi yayi ya kwanta a kusa da ni tare da ƙureni daido, ɗago kai nayi na kalleshi se na tadda hawaye ɗaya na bin ɗaya a saman kumatun shi, kukanafashe da shi tare da rungume shi, haka muka ci kukan mu muka ƙoshi babu me rarrashi, kamofuskana yayi ya saka a tafukan hannayen shi tare da faɗin "na fasa" girgiza kai nayi tare dafaɗin"na daina" murmushi ya saki tare da zaro hankicif ya fara goge mun hawaye, amsan hankicif ɗinnayi na goge mishi nashi, murmurshi ya sakin mu me yalwa tare da amsan hankicif ɗin yasumbata ya maida a aljihu, gyara zama yayi cikin nuni da abinda yake son faɗa me mahimmanci ne tare da faɗin "Insiyyah zanyi nesa dake badin naso hakan ba, se dan gina rayuwar mukamar yanda iyayen mu suka faɗa mana, zanyi matuƙar kewanki, se dai ki sani zuciyata tana taredake"jinjina mai kai kawai nayi dan na kasa iya furta komai, riƙo hannayena yayi tare da faɗin"ki riƙemun amana da dukkanin numfashin ki, na yarda dake, na san zaki iya" jinjina mai kai nayi taredagoge hawaye cike da tabbaci nace mai "zan iya, zan riƙe maka amana har zuwa numfashinanakarshe" rungume ni yayi tare da faɗin "ina matuƙar ƙaunarki, ki dinga tunawa da hakan" jinjinamai kai nayi zuciyata na samun sasauci daga wasi-wasin da take yi".... Da ƙarfin gwiwan mu muka fito, tadda iyayen mu muka yi suna zaman jiran mu, ganin yandafuskokin mu ya washe lokaci guda yasa su sakin murmushi haka muka rankaya muka tafi airport, tunda yaji an kiran sunan shi ya rungumeni ya fara rera kuka, yana kuka ina kuka, dakyar Abbayajanye shi daga jikina ya tura shi saboda warning da suka fara, yana tafiya yana waigomuhar yashige, muna tsaye a wajen jirgin su ya tashi haka muka koma gida jikkuna a mace, tunda bayantafiyan shi walwalana ya ragu, ba ni cin abinci sosai, bana zaman hira, ba yanda Abba da Momyba su yi dani ba amma na kasa sakewa, in anga walwalata Yaya Sahabee ya kira ni, se da suAbbasuka haɗa da su Daddy a maganan sannan na fara sakin jiki, Daddy shi yamun duk wani cuku- cuku na makaranta, ranar da na fara shiga haka na dawo a mugun gajiye nayi ta ma Yaya Sahabee da ya kirani ƙorafi, banda dariya ba abinda yayi ta mun, duk bayan sati ɗaya se yaturoabokan shi uku sun kawo mun ziyara, Munnir, Abubakar, da Jabir, haka za su zo muyi ta fira, sosai nake jin daɗin zuwan sun, dan suna ɗebe mun kewa, haka muka cigaba da tura rayuwa, komanmu yana tafiya yanda muke so, Yaya Sahabee ba ya taɓa shiga lecture se ya kira ni, sannanyanafitowa ze kira ni, kafin mu kwanta ze kira ni, mun ƙara shaƙuwa sosai fiye da da.... Ban taɓa zato da tsammanin rayuwar mu zata juya daga sama zuwa ƙasa ba se da muka shekaraɗaya gyam rabon mu da juna, shigowan Abdussamad Umar tsakiyan rayuwar mu shi ya daguladuk wani rayuwar da muka shinfiɗa tare da mafarkin yi ni da Yaya Sahabee" yana kai nanyadasaaya tare da sauke kaaƙƙarfan numfashi tare da kallon Yaya, suma kallon shi suke da mamaki, bece musu komai ba se murmushi me ciwo da ya saki, maida kai ga littafin Sadamyayi a natse"yashigo makarantar mu ne dan yin wani cours na shekara biyu, gaba yake damu a makarantada kuma shekaru, ɗan asalin garin Bertuwa ne, karatu ne ya kawo shi garin Ɓadamayya, munkwashi watanni uku sannu be taɓa shiga tsakanina da shi ba, ze kalle ni in kalleshi ya wucenawuce, amma ba me cewa wani sannu, na sha ba ma Yaya Sahabee labarin ji da kan shi, sedai yamun dariya tare da faɗin "in nisanci duk wani abu da ze haɗa hanyata da shi, ranar da maganayataɓa shiga tsakanin mu, ranar wata talata ne an ba mu assignment banyi ba, se lecturer yaceinfitan mishi daga class, yanda ƴan class ɗin suka bi ni da ido shi yayi matuƙar baƙanta munrai inafitowa na saki kuka a wajen, ina cikin kuka na ji muryan shi yana tambayana dalilin da ya sani kuka, dama neman kafaɗan da zan zubda hawayenanake, nan na zayyane mai komai, murmushi ya sakin mun tare da amsan littafin ya gyara zama ya fara koya mun, dama in an bamu YayaSahabee nake kira ya mun, in be free in su Munnir sun zo su mun, a lokacin Yaya Sahabeeyanaexms su kuma ba su zo ba, yana gama mun na mai godiya ya tashi ya tafi ni ma na kama hanyargida, tun daga wannan ranar muka fara gaisawa, in ya hangoni ze zo mu gaisa, saboda banadaƙawa ko ɗaya Yaya Sahabee ya hanani yin ƙawaye"... Tun daga gaisuwa muka fara fira tun ban sakin jiki har na fara, saboda Abdussamad yana dadabarun sarrafa mutun yayi magana ko be yi niyya ba, shaƙuwar mu ta fara nisa da shi, bansansanda na fara janye jiki daga Yaya Sahabee ba, in na shiga school ban gan shi ba duk se inji nadamu, bana samun sukuni se mun haɗu, kullum ina manne da waya a gida inba chartingmukebayo waya muke, Yaya Sahabee ya damu da wannan canjin da ya hankalta da shi, da gaske najanyemai sosai, na daina dukan kiran shi a ko wani lokaci, in ya turomun saƙo bana dubawa, innadubamana ba shi amsa, ya turo mun su Munnir kusan sau biyar akan batun, amsa ɗaya ne ba komai ina son maida hankali ga karatuna ne, shima in ya dame da tambaya hakan kawai nake faɗamishi, ban farga da illan da nake shirin mana ba ni da Yaya Sahabee se da saƙo ya zo dagamakarantar su na baya da lafiya an kwantar da shi a asibiti, nan hankula ya tashi"... Daddy da Momy suka tafi duba yanayin jikin na shi, kwanakin su bakwai suka dawo da kyakykyawan labari akan ya samu sauƙi har ya fara shiga school, kowa yayi farin ciki, da darenranar Momynshi ta kirani har cikin bedroom ɗinta ta tambaye ni me ne ne ya shiga tsakani nadashi? Sadda kai nayi cike da nauyinta na ce "ba komai" tayi-tayi dan taji wani abu, da naga ta damu se na ce mata, "ba komai so nake in maida hankali akan karatu, shi kuma ya kasa ganewa" nan ta goyi bayana sannan ta ce zata mai bayani yanda ze gane, godiya na mata na fito, tundagawannan rana na samu daman baje koli tsakanina da Abdussamad, duk da shi ne san labarinYayaSahabee ba, kuma ni da zan ba shi na rufe ko wacce ƙofa da ze san labarin shi, kafin ya furtaminkalman ƙauna na rigashi furtawa, na shaƙuwa ta juye zuwa soyayya, soyayya muke sha hankalinmu kwance, wayana na ƙara nake ɗagawa, sunana ya canza daga Insiyyah zuwa Insu, ta ɓangaren Yaya Sahabee kuwa ya kasa samun natsuwa, be gaji da tambayar lafiyana wajenƴanuwa, saboda na daina ɗaukan kiranshi, sannan ya kasa faɗan ma kowa hakan, mahaifiyatatafarahankalta da halin da nake ciki, zaunar da ni tayi ta mun nasiha me shiga jiki, jikina yayi sanyi sosai, ranar da kaina na kira Yaya Sahabee, duk da nasan yayi mamaki amma haka yaƙi nunawamuka gaisa babu wani sakewa daga gare ni, a ranar na ce mai ya daina kirana da ko wani sunayadinga kirana da Insu yafi daɗi, ba musu ya amsa da to, daga ranar na fara ɗaukan kiran shi sama-sama, shima muna fara magana zan nuna na gaji, daga zan kwanta, se zanyi karatu, ko zanyi wanka, uzurori dai kala-kala, tun yana iya jurewa ya kasa, kiran Munnir yayi ya zayyane mai dukhalin da muke ciki, haka Munnir ya zo wajena yayi ta mun nasiha tare da nuna mun kuskurendaabinda nake shirin yi ze jawo, idona ya rufe a lokacin, haka na daddanƙara mai baƙaƙenmaganaya bar ƙofar gidan mu hankali a tashe, ina komawa gida na dannawa number shi kira, yanaɗagawa na tari nunfashin shi da muggan kalamai, be ce mun komai ba, har na gama na katsewayan, ina ajiyewa saƙon shi ya shigo, a lokacin ba abinda nake son gani illa ya haƙura dani, amma ina dubawa sena ga saƙon ban haƙuri ne, ba ƙaramin ɓaci zuciyata tayi ba, jefar da wayannayi na zura hijab na fita, kai tsaye parlon Abba na nufa".... "Ina shiga na fashe da kukan dake mun tuƙuƙi a maƙoshi tare da isa kusa dashi na zauna, cikedaruɗu ya tambaye ni meya sani kuka, na samu abinda nake so, share hawaye nayi tare da faɗin"Abba na gaji da abinda Yaya Sahabee yake mun, kullum cikin zargina yake, yau ma haka yaturomun Munnir yayi ta farfaɗamin magana" cike da mamaki Abba ya tambayeni "zargin me? Nace"wai ina kula samari" "ai kina kulawan ne ba zargi ba ne" Momy tace rai ɓace dan ita ta gamaaminta da hankalin Yaya Sahabee, duk cikin yaran gidan su tafi shaƙuwa da shi, "ai bangaabinzargi ba ban da abin Sahabee, har yanzu kuna da lokacin fahimtar juna, in Allah ya ƙadartazakuyi aure muna farin ciki, in Allah be ƙadarta ba ba yanda zamu iya" cike da farin ciki na ɗagonakalli Abba tare da faɗin "Abba yanzu idan na kawo wani zaku ba ni!" Nayi maganan cike dafara'a, "me ze hana matuƙar ki na son shi" Abba yace min cike da murmushi, girgiza kai Momy tayi tareda faɗin "a matsayinka na Babba be kamata ka zama me karya alƙawarin ba Abban su, wani magana ka ke yi haka?" Dakatar da ita yayi tare da faɗin "babu tsarin auren dole a cikinra'ayina, yanda ban dolanta miki wajen aurena ba, ba wanda ze dolenta ɗiyata wajen auran wanda bata ra'ayi, wanda take so zata aura, in Sahabee ne ina farin ciki in kuma ba shi ba ne ba zan ƙi ba, tashi kije Insiyyah" ya idda maganan tare da kallona, tashi nayi da sauri farin ciki cike da zuciyana.... Ina fita na ja na tsaya dan na san Momy ba zata yi shiru ba, aikuwa tsayuwana ba daɗewa naji tana cewa Abba, "Abbansu kar ka manta ka ɗauwa yaron nan alƙawari" "ba alƙawarin da naɗaukan ma kowa, ko da Alhaji Sadam ya zo da batun na bashi baki biyu ne, in dai suka kammalamakaranta suka zo mana da batun har lokacin suna son junan su ina maraba, in kuma sunkawowasu ba zamu ƙi amsa ba" "amma Abban su ana barin halak ko dan kunya, kar ka bawa yarinyarnan daman ruguza rayuwar Sahabee, yaron nan ba ya da ƙarfin zuciyan fuskanta abubuwandakeyawo a ƙwaƙwalwanta" Momy tace jiki a sanyaye, "wani halas ɗin ba Yasmin, ba fa zamujadalamarin Ubangiji ba" Abba yace tare da tashi ya barta a wajen cike da jimami, na san Abbanmusosai, dan yana da tsatstsauran ra'ayi, ba kowa ke iya juya shi ba, ba kuma kowa ke iya mu'amalantan shi ba, dalilin haƙurin Daddy ya sa amintakan su ta ɗau shekaru.... Tun daga wannan rana na ƙara samun ƙarfi daga ɓangaren Abba duk da ta ɓangaren Momybasauƙi, amma in na tuna Abba na bayana se in ji zan iya fito na fito da kowa akan Abdussamad, daga nan muka cigaba da shan soyayya da Abdussamad Yaya Sahabee kuwa ya koma gefeyazuba mun ido, be gajiya da kira da turo saƙo, ni kuma bana gajiya da banzatar kiran da saƙonni, gaba ɗaya ƴan uwa sun fahimci halin da muke ciki, Yaya Hassan da Yaya Jibril suka zaunar dani suka yi ta mun nasiha akan in daina abinda nake, a lokacin na nuna musu na daina su ka yi tafarin ciki, ina tashi a wajen na watsar da batunsu na cigaba da hidiman gabana, lokaci yajasosai, Abdussamad ya kammala abinda ya kawo shi ya tattara ya koma Bertuwa, ba kaɗan ba nashigacikin tashin hankali, duk da Momy ta fahimta amma ko kallon inda nake ba tayi ba, ba mahaɗuwa da juna se waya, kullum muna tare, haka muka share Shekara biyu shakuwarmuyaƙaratumbatsa, ta kai bana jin nauyi da kunyar kowa ido su Lubabatu dake ta ƙoƙarin nunashsheni hanya suka zuba mun dan sun gane nayi nisa.... "Shekaran Yaya Sahabee biyar ya fara shirin dawowa gida, har ɗaki su Lubabatu suka zo sukafaɗamin ranar da ze ta so cike da farin ciki, nan na hurawa Abdussamad wuta akan ina sonyazoin ganshi, duk da ya nuna mun yana da uzurori dan a lokacin ya daɗe da fara'a aiki amma nadage, haka ya amsa mun, ana tafiya ɗakko shi a airport Abdussamad ya kirani akan ya ƙariso fiddokujera nayi na ajiye a dai-dai saitin da in suka doso za su gan mu, burina ya cika kuwa, dansunashigowa anguwan da mu ya fara cin karo, se dai banyi zaton ganin abinda ya aikata ba, benunama yasan damu a wajen ba ya shige gida, ban so hakan ba sam, na so ya ƙariso inda mukeyacezeyi wani magana, haka muka cigaba da hiran mu se kusan magrib Abdussamad ya tafi akanzebi motan 12am ya koma Bertuwa, ina shiga gida Momy ta kwashe ni da mari me shiga jiki taredafarfaɗamin magana marassa daɗi ta wuce, ji nake kaman in shiga gidan su Yaya Sahabee inzazzage shi saboda takaicin marin da ta mun, da daddare muna zazzaune bayan dinner sukashigo shi da Munnir da Jabir, gaishe da Momy da Abba suka yi cike da girmamawa, amsawasukayi fuskoki yalwace da fara'a, ko kallon inda suke ban yi ba, se da Momy ta dakamun tsawa, "sannun ku" kawai na ce tare da kauda kai, murmushi ya saki tare da kallona, tashi su Munnir suka yi suka fice saboda takaici dake shirin kadasu".... "Mu ɗan taka ne?" Yace tare da kallona, ganin irin kallon da Momy take mun ya sa ni tashi nabishi, tsayawa yayi ya kalleni fuska faɗaɗe da murmushi wanda kallo ɗaya zaka mai kasanbekai zuci ba tare da faɗin "kin canza, shin wai Insiyyah tace kuwa? Anya ba'a canza mun ke ba?" Yaidda maganan a raunane, dago kai nayi na kalleshi, ya ƙara cikan zati duk wani alamun girmasunnuna kan su a jikin shi, "ni ce mana, haka rayuwa ta gada" na ce tare da kauda kai, murmushi yasaki tare da faɗin, "meyasa?" "Me kenan?" Na ce cike da rashin damuwa, murmushi ya saki tareda faɗin "canjin lokaci guda haka" gyara tsayuwa nayi dan na na samu daman da nake sonsamu, cike da rashin ɗaukan abinda zuciyata take ingizani in yi da mahimmanci nace "Yaya Sahabeeban san ya zaka ji abinda zan faɗa ba yanzu amma shine gaskiya, bana jin ƙaunarka ko kaɗan, nafahimci tunda na sanka nake ba tausayin ka nake, wataƙila saboda laluran da ka ke daukedashi ne, ko kuma wani abu na daban, na samu wanda nake matuƙar so, kuma banajin zan iya rabuwada shi" nuna yake da razanannun idanu tunda na fara maganan har na dasa aya, murmushi kawai ya saki tare da faɗin "je ki kwanta dare yayi sosai" wucewa nayi hankali kwance na barshi dabinada ido, wanna ganin da sauran yaran gidan suka mun ni da Abdussamad ya ja kace na ce, bayan kwana biyu da dawowan Yaya Sahabee Daddy ya tuntuɓi Abba akan batun tsaida ranar aurenmu, ba wani jan zance ya taso shi suka shigo har parlor, tunda Abba yasa Momy ta kira ni hankalintayayi mugun tashi, tana shigowa ta gargaɗe ni sosai akan kar in sake in furta wani abu, banƙi mata ba, ina shiga na zauna kusa da Abba, bayanin dalilin neman da suka mun yayi mun, ɗagokai nayi na kalli Daddy ganin irin kallon da yake mun ya sani saurin sadda kai tare da faɗin "inadawanda nake so" na faɗi kalman a sauƙaƙe se dai ban san ze ruguza farin cikin jama'a da damaba.... Murmushi kawai Daddy ya sakin ma Abba ya tashi ya sallame mu ya fice, ba abinda Abba yahasaso, fitan Daddy ke da wuya Momy da ta gama jin komai ta fito fuska shaɓe-shaɓe da hawaye, kallon Abba tayi cike da takaici tare da faɗin "kayi babban kuskure Abban su, san na ka zekai kaga aikata danasani a sauran rayuwarka" juyowa tayi gareni tare da faɗin "yayi miki kyau, kincikaɗiya ta gari, lallai yau na tabbatar da wacce na haifa" tana kai nan ta juya ta bar wajen, kallonaAbba yayi tare da faɗin "ki sanarwa wanda ki ke so ina son ganin iyayen shi" wannan magananshi ya mantar da ni wani damuwa da nake hasashen faruwan shi.... Munyi kwanan farin ciki ni da Abdussamad da na sanarwar saƙon Abba, se dai isan Daddy damaganan gidan shi ya haddasa faruwan abubuwa da yawa, Yaya Sahabee ya yanke jiki ya faɗi ahospital ya kwana be san halin da yake ciki ba, hankulan ƴan gida ya tashi ba wanda ya samuisasshen barci, tanan gida kuwa Momy ma ba ta samu isashshen barci ba, Abba kuwa lafiyayakwanta dan iya gaskiyan shi ya bayyana, da safe muka sami labarin abinda ke faruwa, hankalinMomy yayi masifar tashi, na jimanta abinda ya faru da shi amma albishirin da Abdussamadyayi mun na zuwan da Yayan babanshi ze yi ya mantar dani damuwan halin da Yaya Sahabee yakeciki, kwanan shi bakwai Momy ta matsa akan se munje tare na gaida shi, ko da muka isa muntaddashi zaune Momy na bashi abinci, ba ta nuna mun ko wani canji ba, Yaya Sahabee kuwa tundayakalleni yake zubda hawaye, tashi suka yi suka fice suka bar mu tare, juyawa nayi zan fice yayi saurin cafko hannuna tare da fashewa da kuka, ya kasa magana duk da yanda laɓbanshi damaƙogoronshi, ganin ina shirin zare hannuna ya sa shi faɗin "kar ki mun haka Insiyyah, kar ki mun haka, ina matuƙar ƙaunarki, dan Allah ki tausayamun, zan iya rasa farin cikina in ki ka nisance ni" juyowa nayi da mamaki na kalleshi, rai ɓace nace "au farin cikin ka kawai zakarasa?Na ɗauka rayuwarka zaka rasa" sakin baki da ido yayi yana kallona, murmushin takaici nasaki tare da faɗin "ni in na aureka rasa nawa farin cikin zanyi, na ce maka bana sanka, ba zaniyaauren wanda nake kan-kan da shi a shekaru ba, ka haƙura mana, wannan abun fa duk be kai yanda kake ɗauka ba" nayi maganan rai ɓace tare da nufar ƙofa, da sauri ya sakko ya biyoni

Chapter 5 of 109