Share this page
ƙarfi.... Dariya Insu ta saki tare da faɗin "ka barshi ya yi ban ruwa dakyau be san ranar dawowa ba" "Allahya shiryeki Insu" yace tare da mangareta a kai, "wash Nafsii!" Tace a taɓare, "ai be wajensedai ruhi" Yasmin tace tare da rungumota, "ki kula da kan ki sannan ki kula da ɗan tayi" murmushi tasaki tare da faɗin "to ki kula da nawa ɗan tayin" "ban musa ba" tace tare da sakin dariya tasaketa, ƙara sallama suka yi da juna suka shishshige mota, "a ce ma malama ƴar jarida ina san maganada ita please jiya na kira numberta be wuce wa" jinjina mata kai Yasmin tayi tare da faɗin"inshaAllah" suna tsatstsaye har suka ɓacewa ganin su.... "Ina Mairah?" Fadila tace tare da kallon Nafisat dake jin kaman ƙasa ya tsage ta shige ta ɓuya, "tana barci" tace a hankali, dariya Nabila ta saki tare da faɗin "haba gimbiya menene na jinkunyar" fiddo ido tayi tare da wuce wa da sauri, "meye hakan! Wannan ai zaku ƙara sawa tajanyeda jama'a ne" Yasmin Ɓadamayya tace cike da tsawatarwa, "sorry Mahmah" suka ce a hankali, "toMahmah muje ki shirya mu yi rakiya, kar malam ango ya biyo sahu" Insu tace cike da yanayinta, "wannan ƴa anyi shaƙiyiyan ɗiya" Lubabatu tace tare da kama haɓa dariya suka kwashe dashi tare da wuce wa ciki da sauri..... Comments fans 🙏🥰 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. sixty five "Wow akwai wanda kayan nan ya amsa sama dake kuwa! Dubi yanda ki ka yi kyau a ciki!" Nachma dake bin Insu da ido tace tare da kai hannu ta gyara mata zaman hulan dake sanyeakanta, "ke ma ya amsheki ai Nachma" Nabila tace tare da sakin mata murmurshi... "Duk da haka sister Nabila, yanda ki ka san dan ita aka ƙirƙiri kalan kayan" tace cike da gaskiyanta, sakin dariya Nachma da Fadila da Asma suka yi tare da bin ta da ido, "auh kukunanan ana ta neman ku! Tawagan mr president fa na gab da ƙarisowa, kuma yana iso wa kunsanme za'a fara" Hisham dake sanye cikin na shi kayan kammala karatun yace tare da bin sudaido, "to bari muje wake biɗan mu" Fadila tace tare da miƙewa "jama'an Bertuwa ne" yace taredawuce wa gefen Insu da ke ta haskawa saboda matashin cikinta da ya fara tasawa.... "Da baby aka zo?" Tace tare da kallon shi, "ban kai hankalina kanta ba wataƙila Habib ya lura" yace tare da zaro wayan shi ya daddana ya miƙa mata, amsa tayi tare da baza ido, video yaɗaukashi da Mairah" taɓe baki tayi ta miƙa mai tare da faɗin "ayi ta koyawa yarinya dai rashinkunya" amsa yayi tare da faɗin "a rage hassada dai girl friend, menene na takaici dan kin gama haihuwan kyakykyawa" banka mai harara tayi tare da faɗin "in na haifa ka maida" "ai ba mazaki ƙara haifan irinta ba, sau ɗaya dama ke zuwa" ya idda maganan tare da fashewa da dariyadanyasan ya gama kunnata... "Rabu da shi Insun mu, neman magana yake" Habib yace tare da sakin murmushi, "ku fitokufaɗamata gaskiya, ku daina take gaskiya dan a so ku" Hisham yace cikin dariya, juyawa tayi ta sumfuci goran dake wajen ta jefe shi da shi, da sauri ya kauce tare da faɗin "se haƙuri, muaharka ta gaskiya bakin rai bakin fama" ɗaukan wayanta dake neman agaji tayi ta ɗaga ta karatare da banka mai harara... "Gamu nan" tace a natse tare da zare wayan, "waye?" Yace tare da miƙa mata hannu a natse, miƙa mai jakanta tayi tare da faɗin "uncle Hassan da iyalin shi ne suka zo" "wowdama ze zo?" Jinjina kai tayi tare da faɗin "tun a sunan Insu baby da muka haɗu yace za su zo" "da ki ka faɗi haka se ki ka tuna mun da ma hangi Mommy na ɗaga mata hannu ta bankamun harara" yayi maganan cikin dariya, "muje, ai har duka yau yakamata ta haɗa maka da shi" tace tare da nufar ƙofa, dafa mata baya suka yi fuskoki cike da farin ciki.... Suna fitowa ta hangi dandazon ƴan uwa ƙwansu da ƙwarkwatansu suna zazzaune ko wannefuska cike da farin ciki, haka tayi ta bin su da ido ɗaya bayan ɗaya, sauke wani ƙaƙƙarfannumfashi tayi lokacin da ta kammala kallon su tare da ɗaga kai sama, "please Ammi!" Nabilatace a raunane, girgiza kai tayi tare da ba hawayen da suka cika idonta daman gangarowa.... "Insu! Menene hakan? Ranar farin ciki da murna da dariya da shewa ne ya zo gare ki ba nakukaba, da yawan mutane sun so ganin irin wannan ranar a rayuwar su amma ba su gani ba, kekingani da ranki da lafiyanki amma ki kasa godewa Allah da ni'iman gani da ya miki? Haba girl friend ke da zaki hani ke ke yi!" Hisham yace cike da damuwa... "Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillahi bi ni'imatihi ta tummussalihat!" Tace cikinsautinkuka tare da fashewa da raunataccen kuka, saurin kamota Fadila da ta saki nata hawayentayi tare da faɗin "daina kuka, ko ba ta gani ba kin ganin mata Ammi!" Girgiza kai tayi tare da faɗin"Fadila ta so ganin wannan ranar! Tun ban fahimtar abinda take nufi take maimaita munfarincikin da za tayi a wannan ranar!" "Subhanallah" Nachma tace tare da kauda kai da sauri tafarashare hawaye, ganin yanda ta kasa tsagaita kukan ya sa Hisham faɗin "ku kamata ku komaciki kar kukan ya jawo hankulan mutane" jinjina mai kai Fadila da Nachma suka yi tare da temakamata suka koma ciki, wuce wa sauran suka yi dan neman wajen zama.... "Ina Insun?" Anty Lailah tace idanta akan Nabila, "bata gama kimtsawa ba" tace a sanyaye, "yauga shashanci, saka rigan da hulan ya zama aiki ne, ance fa yanzu tawagan Yaya Sahabee zasuiso" "zata gama yanzu" tace a hankali, miƙewa Yasmin tayi tare da faɗin "bari inje in temakamata" "to ki bi dai a hankali" murmushi ta saki cike da jin daɗin kulawan da ta nuna a gareta, kallon Shureim dake zaune da zugan amaren ƙannin shi tayi tare da mai alamun tana zuwa, jinjina mata kai yayi tare da bin ta da ido.... "Ina Umma za ta haka?" Farisat tace tare da kallon Nafisat dake rungume da little Insu a kafaɗa, ɗiyar Farisat da ta haifa wata biyu da suka wuce, "ina ga wajen Ammi zata har yanzu ba tafitoba""miƙa wa sister Rahmah ita mu leƙa" tace tare da miƙewa, ba musu ta bawa Rahama dakezauneita da su Hasinat suka nufi can.... Tana ƙarisawa ƙofar class ɗin ta jiyo saukan sheshahekanta, rumtse ido tayi da ƙarfi tare dadafaƙirji a hanzarce, "la haula wala ƙuwwata illah billah!" Ta fara maimaitawa a hankali, cikinni'imanmahalicci natsuwa ya diran mata a take, ɗaga ƙafanta da yayi mata masifar nauyi tayi da zumman shiga, "lafiya!" Farisat da suka iso wajen tace cike da mamakin sanyin da ta gani taredaita, guntun murmurshi ta saki tare da faɗin "ina little?" "Tana wajen Rahmah, me ke faruwa!" Taidda jefa mata tambayan tare da kai jiki bakin ƙofan.... Hango Insu da tayi zaune dirshan na risƙan kuka ya sa ta furta "subhanallah!" Tare da shigewadasauri, dafa mata baya suka yi a hanzarce, "yawwa gunda da ku ka zo, munyi-munyi ta yi shirutakasa!" Nachma tace cike da damuwa, "kar ki damu Nachma yakamata ki je ga baƙin ki tunɗazusuke nemanki" Yasmin tace a natse, jinjina kai tayi tare da faɗin "dan Allah friend ki dainakukannan haka" tana kai nan ta nufi ƙofa, miƙewa Fadila tayi ta dafa mata baya.... "Ya isa haka ba gashi mu mun gannin mata ba, ko baki gamsu da na mu ganin ba ne?" Farisat tace murya na rawa, girgiza kai tayi tare da faɗin "alfahari nake da ganinku gefena a wannanrana, se dai na so ta gani ta cika wannan burin" "burika da dama ba ma cika su muke tafiyaInsu, shi ɗan adam a ko da yaushe cikin buri yake da shi kuma yake tafiya, da Anty yau ta ga wannanranar to wani ɗammaran burin ganin wani abun tare da mu zata ɗaura" tace cike da rarrashi.... "Duk jama'an nan da suke waje danke suka zo, ba dan kowa ba baby Insu, farin cikin ki yakamataki nuna musu da jin daɗin halartan da suka yi taya zaki keɓance kan ki waje guda ki na kukabayan ƴan uwanta sun zo dan gane mata, share hawaye ki goge fuska muje ku gaisa" Yasmintace tare da miƙa mata hannu.... "A'a matsa kar ki ja mana magana" Farisat tace tare da kaudata, "oh Yaa Allah Mommy zaniyafa""kin ji nace ba zaki iya ba ne?" Tayi jefa mata tambayan tare da temaka ma Insu ta miƙe, dasauri Nafisat ta zari tissue ta miƙa mata, goge fuskanta ta fara a natse, "ina faɗa miki baby Insu, YayaSudais Yaya Abdallah Yaya Nafi'u, amare gaba ɗaya ba wanda aka bari a baya, ke hatta dasuMihna masu auren 3weeks sun zo" Yasmin tace dan ta ɗan sake.... "Ga sabbin shigan ciki ma sun zo baki faɗa mata ba" Farisat tace tare da kallonta "su waye?" Tacetare da baza mata ido "Sadiya da Harira" "na fa manta ance sunyi gamo!" Tace tare da sakindariya "to Anty Iƙilima da Hasinat ma fa an gamu" Insu tace tare da sakin dariya, "dan Allah!" Farisat tace cikin salon janta da zance, "wallahi haka na ji Anty Kausar na faɗan wa Hajiya" "tabAllah ya inganta, Allah ya ba anty Iƙilima namiji uncle Jamil na son ɗa namiji" "to amin, shimauncle Kamil ɗin na so, duk da yana da shi" "to ai shi yana da shi Ammi" "Mommy kogi beƙi daɗi bafa" "haka ne, ya jikin Anty Yasmin kuwa?" "Ta ji sauƙi sosai ba ku haɗu a nan ba ne?" "A'a banganta ba na dai ga su Anty A'isha da yaransu da mazajensu duka" "ta zo tana kusa da suHajiya" Yasmin tace tare da kallonta.... "Aiko bari mu koma zan je gareta, Fadila ke ce mun ciki ne da ita, na ce Allah ya inganta wai yarinyar nan tace "ba amin" ba" "akanta" Insu tace tare da kallon su, dariya Yasmin ta saki taredafaɗin "easy mana ba ta nan fa" "ai yarinyar nan mugun alkaba'inta kaɗai ya isa ya zubda cikin, kaman yanda aka yi ta ma Anty Habiba, to ta Allah ba ta su ba in sha Allah se ta haifa" "Allahyasa, ni ma a ranar nayi mata faɗa sosai akan abinda ta furta, wai wallahi kunya take ji brother Sagir ya ji labarin" "auh ita ba abin kunya tayi ba da take nane da miji kullumtana abubuwaseitada ba wanda yasan me ke faruwa a gidanta shine take jin kunyan sanarwa, in sha Allah setahaifi cikin" "Allah ya yarda, ku muje kar Anty Lailah da Salwa su biyo bayan mu" Yasmin atce taredazare ido.... Murmurshi suka saki tare da rankayawa a haɗe suka fice suna niyyan nufan inda kujerukejeretawagan mr president ya iso, nan take jami'ai suka barbazu ta ko ta ina, wuce wa inda uncleHassan ke zaune shi da su Alhaji Jamil suka yi a natse, miƙawa Insu hannu yayi a natse ta kama, yana niyyan magana ta fashe da raunataccen kuka ta faɗa jikin shi, a dai-dai nan SSBda akabuɗewa ƙofa ya sakko, ba inda ya sauke idan shi se a kanta.... "Abie!" Mairah dake zaune jikin Sa'eed tace da ƙarfi tare da nuna shi da yatsa, saurin riƙohannunta Sa'eed yayi tare da faɗin "ki na so ciji ya cije ki?" Girgiza kai tayi tare da kallonshi, "toki daina nuna Abie da yatsa" jinjina kai tayi tare da lafewa a jikin shi.... A natse ya fara takawa dan isa inda aka tanada dan shi, ji yake kaman ya nufi inda take kai tsayeya tambayeta dalilin da ya sa take kuka haka, banda dauriya ba abinda yake har ya ƙarisa wajen, jan mai kujera da sauri shugaban masu tsaro yayi ya zauna a natse tare da sauke numfashi ahankali, murmushi Abbah dake kujeran kusa da shi ta ɓangaren hagu ya sakin mai tare dakai gaisuwa a girmame, gaisawa suka yi a mutunce ya juya ɓangaren dama inda jerin su Jabir sukama kan su masauki.... "Ya isa haka mana Insu, kar ki tayar wa bawan Allah hankali a cikin jama'a, kin san ba ze yi maraba da wannan kukan naki ba" Salman yace tare da kallon ta, "na kasa dannewa ne YayaSalman, duk ga ku a tare dani, ina matuƙar farin ciki, se dai" "shiiii Allah ya gafarta mata, kukanya isa haka shekara nawa ana yi, mun san da ciwo, amma Insu kuka ba ƙauna ba ce, addu'ashineƙauna, duk sanda abu irin haka ya bijiro muku ku mata addu'a ze isa gareta, amma kuka bama zata san kuna yi ba" Ali yace cike da rarrashi, jinjina kai tayi tare da yunƙurawa a natse, temakamata yayi ta miƙe ta fara share hawayen... "Yawwa ko ke fa Insun mu har kin fi jiya da shekaran jiya kyau, amma da kawai kina shirinkiɗimamu, kin san fa kina kiɗimewa muke bi yo bayanki" Sudais yace fuska faɗaɗe da murmushi, hararata ban ka mai tare da juyawa ta fara gaida matar uncle Hassan da su Babah Lanti dake ta sakinmurmushi, "ina matan Yaya Balarabe?" Tace idanta akan Balarabe murmushi ya saki taredanuna mata inda take zaune, "ka wanke kan ka" tace tare da wuce wa inda Ummi ke zaune... "Oh Insu idanta akan wanda suka zo da wanda ba su zo ba, a gaidata" Munari tace tare da kamahaɓa, murmushi su Farisat suka saki tare da nufar wajen zaman su, lumshe ido yayi ganintasaketare da kallon Jabir dake cewa, "yaron nan fa yaƙi bada ƙofa, se ƙara shiga tsakanin su da kwanciyar hankalin su yake" murmushi ya saki tare da faɗin "dama basu da wani kwanciyar hankali da yarage musu"... "Ai gogan yaƙi bayyana kan shi har yanzu, ɗazu na ƙara samun kira akan former president naneman alfarman zama da kai, na ce ace ya jira tukun hidimomi sun maka yawa a watanninnan" murmushi SSB ya saki tare da faɗin "ze gaji ya magantu" "sosai kuwa musamman da yanzujama'an ƙasa suka fara tattauna batun a media, shekaran jiya fa yaron nan datsan gidantvnMWyayi ana tsaka da nuna film ɗin nan me dogon zango da ya ja hankulan mutane ya bayyanawani ɗauka na su, abinda ze baka mamaki muryoyin su da ya fito wan can da suka ƙaƙƙaryata yasajama'a dawo da su suka cigaba da cin kasuwan su" murmushi SSB da idan shi ya koma kanInsuya saki tare da faɗin "zamu ji abinda za su ce yanzu kuma" "ba su da bakin magana ai" "marakunya ze iya komai" yace a hankali dai-dai juyowan Insu dan neman wajen zama.... "Cikin ƴan department ɗinku zaki, ance ki iso za'a fara jawabi" Habib yace tare da nuna matahanya ba musu ta shige gaba ya dafa mata baya, "Ami!" Mairah tace cike da farin cikin ganintatare da ƙoƙarin ɗaga hannu saurin riƙe hannun Sa'eed yayi tare da rufe mata baki a hanzarce, dariya Sahabee da Umar suka danne tare da kallon Mairah da ta shagwaɓe fuska.... Suna isa ya wuce gefen ƴan department ɗinsu ita kuma ta fara biɗan wajen zama, miƙewaKhaleem dake zaune yayi a natse tare d faɗin "bismillah" ya wuce, "nagode" tace tare da zaunawa a natse, ɗago kai tayi da zumman yafuto Nafisat idanta ya faɗa kan na shi dake tsayeƙyam akan ta, tura baki tayi tare da shagwaɓe fuska, murmurshi ya sakin mata tare da mataalamun sorry da ido.... Lumshe ido tayi tare da sakin murmushin da shi ka ɗai aka mallakawa ta juya tare da sosakai, "ƴar nan kar ta sa Uncle yin abin faɗi a gaban al'umma" Farisat tace tare da kallon Yasmindakesakin murmushi, kiran vice chancellor da aka yi dan gabatar da jawabi ya sa su maida hankulaakan wajen gabatar da jawabin, a natse ya taso daga jerin inda malamai suke ya hayo wajen, isoaka mai gefen da microphone yake ya tsaya cike da kamala ya fara jawabi, "assalamu alaikumwarahmatullahi wa barakatuhu, ya ku manyan malamai masu daraja, iyaye, baƙi, da kuma kuɗalibai masu albarka, yau rana ce ta alfahari, rana ce ta cikar buri, kuma rana ce da take nunaamfanin juriya da sadaukarwanku, ya ku malamai, ku ne ginshiƙin wannan nasara, ku ne haskenda ya jagoranci waɗannan matasa cikin duhun jahilci zuwa hasken ilimi, ku ne kuka koya musuabubuwa da yawa ba dokoki kawai ba har ma da adalci" yana kai nan ya ɗan tsahirta kaɗankafinya gyara tsayiwa ya cigaba da faɗin... "Da Gaskiya da tsoron Allah, a yau kun girbin abin da kuka shuka da hannuwanku masudaraja, ga ɗalibai nan masu ilimi, masu tunani, kuma masu kishin gaskiya" numfashi ya sauke a natseyajuya ga dandazon ɗaliban tare da faɗin "ya ku ɗaliban da Allah ya nuna muku wannan rana, dayawan ku na san an fara da su ba a kawo wannan ranar da su ba, to ku da Allah nunawa kusani an yaye ku yau, ku tuna cewa zama lauya ba kawai sana’a ba ce, amana ce, kuma tsayiwa neakan tafarkin kare gaskiya, tsayawa ga marasa ƙarfi, da tabbatar da cewa adalci ya yi nasarakodakuwa yana da wahala, kada ku manta da darussan da kuka koya, domin su ne za su zama fitilarkua cikin rayuwar aikinku, ku kasance masu gaskiya ko da a lokacin da ƙarya ta yi ƙarfin danne gaskiya ne, ku tsaya tsayin daka kan adalci ko da lokacin da zalunci ya yi ƙarfi ne, a ƙarshemutunci shi ne babban kambun lauya... jinjina kai kawai suke cike da gamsuwa, juyawa ga malamai ya yayi tare da faɗin "malamai, kuci gaba da zama jagorori, ku ci gaba da gina al’umma ta hanyar ilimi, domin kowanne ɗalibi dakukakoyar ku sani wata rayuwa ce kuka canza, wata al’umma ce kuka inganta, a yau muna murna, amma kuma muna ƙara ɗaura ɗammaran gaba, Allah ya albarkaci wannan rana, ya sa ilimindaaka koya ya zama mai amfani, kuma ya ba ku ikon amfani da shi wajen inganta duniya, nagodeƙwarai, wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu" yana kai nan ya ja daga wajen, tafi suka fara cike da farin cikin jawabin da ya gabatar dan take jikkunan matasan ɗaliban yaɗauɓari.... "Ma sha Allah mun ji jawabi me ratsa zukata daga bakin me girma vice chancellor na wannanmakaranta namu me albarka, muna fata malamai da yayayyun ɗalibai da ɗaliban da ke kankaratu na wannan makaranta na mu su ji su ɗauka sannan su ɗauri ɗammaran amfani da shi, agurguje zamu yi wa babban baƙon mu iso saboda tsaikon da aka samu na rashin fara jawabandawuri, me girma shugaban ƙasa muna maka barka da isowa, sannan muna neman alfarmankazoka tofa naka albarkacin bakin" me bayanin ya dasa aya tare da ja gefe a natse cike da girmamawa.... Miƙewa SSB dake zaune kan shi sadde a ƙasa yayi a hanzarce guard's da security's suka matso, miƙewa Abubakar da Jabir suka yi suka wuce a tare.... Tunda ya miƙe ruwan camera's ke aiki akan shi, duk da damun shi da hakan yake be nuna koafuska ba, a natse suka hau wajen cike da tsaro, ƙarisawa wajen yayi tare da gyara zaman microphone ɗin ya ɗago ya watsa ma ɗaliban ido cike da tuna wasu shuɗaɗɗun abubuwa, zubamai ido suma suka yi cike da alfaharin ganin shi ido da ido, gyara murya yayi cikin natsuwanshi tare da faɗin... "Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu" amsawa suka yi da ƙarfi muryoyi cikedaƙauna, murmurshi ya saki tare da faɗin "mai girma shugaban jami’a, manyan malamai, iyaye, baƙi masu daraja, da kuma ku jaruman ɗaliban da aka yaye a yau ina miƙo jinjina a gare ku" tsahirtawa kaɗan yayi tare da gyara zaman hannun shi da ya ajiye a saman wajen kafin gacigabada cewa "yau rana ce mai girma a tarihin wannan jami’a, kuma rana ce da take nuna irinnasararda ƙasa ke samu ta hanyar ilimi, ina matuƙar farin ciki da kasancewa tare da ku a matsayinbabban baƙo domin taya ku murna a wannan lokaci na musamman, da farko, ina miƙa gaisuwatamusamman ga malamai da shuwagabannin wannan jami’a, lallai kun taka rawar gani wajenginamatasa masu ilimi, masu kishin ƙasa, masu kuma fahimtar muhimmancin adalci a cikinal’umma.... "Ya ku ɗaliban da aka yaye, kun shiga wani sabon mataki na rayuwa, a yau kun zama lauyoyi, amma ku tuna, wannan ba kawai nasara ba ce, wata babbar alhaki ce ta hau kawunanku, ƙasanasa ran ku zama masu kare gaskiya, masu tsayawa ga doka, masu taimakawa wajen tabbatar dazaman lafiya da adalci, a matsayina na shugaban ƙasa, ina kira gare ku da ku yi amfani dailiminda kuka samu wajen gina ƙasa mai ɗorewa, ku guji amfani da ilimi wajen zalunci ko sonzuciya, ku zama abin koyi ga al’umma, domin ku ne jagororin gobe, gwamnati za ta ci gaba da tallafawaharkar ilimi da kuma tabbatar da cewa ɓangaren shari’a yana samun ingantaccen ci gaba, munabuƙatar ku matasa masu ƙwazo, domin ku taimaka wajen kawo sauyi mai ma’ana a cikinƙasarmu, ina taya ku murna, ina kuma yi muku fatan alheri a dukkan matakan rayuwarku, Allah ya jagorance ku, ya ba ku hikima da juriyar aiki, ya sa ku zama masu amfani ga al’umma, nagodeƙwarai, wassalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu".... Yana dasa aya ruwan tafi ya tashi a wajen kaman za su tsaga wajen cike da farin ciki, ba shi hanya Jabir dake gefen shi yayi alamun ya wuce, da sauri me gabatar da masu jawabin yamatso tare da faɗin "afwan mr president zaka bawa ɗaliban mu masu hazaƙa da ƙwazo kyautangirmamawa" jinjina kai yayi tare da sakin murmushi, "bismillah ga wajen da aka tanadanmakanan" yace tare da nuna mai inda aka tanada na musamman dan zaman shi, ba musu suka rankayacan a natse.... "Ma sha Allah! Ma sha Allah! Mun ji jawabi da yabo da shawarwari daga bakin me girma shugaban ƙasa kuma mamallakin wannan makaranta ta mu me ɗin bin daraja wato Insoul, lallai waƴan nan jaruman ɗalibai ƴan gata ne, muna fata ku rungumi duk wata shawara da nasihadaaka baku, dan ina da yaƙinin ba za ku taɓe ba matuƙar ku ka mai dashi wani ɓangare dagacikinrayuwarku" "in sha Allah!" Suka ce da ƙarfi, "Allah ya amince" yace tare da juyawa ga jerinindajudge's ke zaune tare da faɗin... "Judge Tanimu Barau muna buƙatan ka a nan dan ba wa jaruman mu call to bar" murmushi wanda aka kira sunan shi ya saki tare da miƙewa a natse ya iso inda suke, mimmiƙewa sukayi cike da girmamawa, ɗaga hannu yayi a natse, ɗaɗɗaga na su suka yi a natse, gyara tsayiwayayi tare da faɗin “ni" ko wannen su ya ambaci sunan shi, "na rantse da sunan Allah maɗaukaki cewazan yi aikin lauya cikin gaskiya da riƙon amana, zan mutunta dokokin ƙasa, zan kare adalci, kumaba zan yi amfani da wannan sana’a wajen zalunci ko son zuciya ba, zan kiyaye sirrin wandanakewakilta, kuma zan yi aiki bisa ƙa’ida da gaskiya a kowane lokaci, Allah ya taimake ni” yanarufebaki suka fara mai-maitawa cike da ƙwazo, suna kammalawa ya saki murmushi ya koma mazaunin shi, nan iyaye suka fara share hawayen farin ciki, da ido kawai yake bin ta, duk abindaake ta kasa ɗago kai yasan aikin ta cigaba da yi.... "Ma sha Allah kafin mu kai ga miƙawa kowannen ku takaddan shedan shi na kammala Insoul zamu bawa gwarazan cikin ku kyautan girmamawa, kowannen mu ya san jajircewan su taredajarumtarsu a ɓangaren karatu, a kowani department mun ɗauki ɗalibi ɗaya, zamu fara dashari'alaw, a shari'a law muna dw barrister Maryam Ibrahim, barrister Maryam Ibrahimmuna buƙatanganin ki anan" ya idda maganan tare da zuba ma ɓangaren su ido, ba musu ta miƙe a natseta nufo wajen.... Saurin ɗaukan kyautan da aka naɗe da leda me ɗaukan ido ɗaya daga cikin malaman da sukekanwajen yayi ya miƙawa Jabir a girmame, amsa yayi a natse ya miƙawa SSB da ke sauraranAbubakar dake koro mai bayani.... Iso aka mata har inda yake, duƙawa tayi jiki na ɓari tare da miƙa mai hannu biyu, gyara yanayinfuskan shi yayi tare da miƙa mata, cike da tsoro ta amsa ta wuto, umurtan ta aka yi data yi jawabi, tana kama microphone ɗin tace "Na gode ma Allah da ya nuna mun wannan rana, na godewaiyayena da suka kawo ni Insoul dan cikan burina, sannan na godewa malaman Insoul da shuwagabanninta da suka cika mun burina" ta idda maganan murya na ɓari tare da janyejiki, damurmurshi suka bi ta gaba ɗayan su dan tsoronta ya bayyana a fili.... "Ma sha Allah mun saurari bayanin godiya daga gwarzuwan mu ta farko, yanzu zamu kirawojarumi da ya bayyana hazaƙan shi da fasahan shi daga, commercial law, barrister HishamSharifudde ya zo ya amshi kyautan girmamawan shi" rumtse ido Hisham da maganan ya dakanwa zuciya yayi dan be

Chapter 105 of 109