Share this page
Allah Anty Insu ga Sahabee, haka ta gaisadasu gaba ɗaya cike da nuna musu zallan kulawa,"ba wa Sa'adatu Umar" Yasmin tace tare dakallonSa'adatu dake saman dining a zaune.... Yana bata ta ajiye a gefe tare da cigaba da cin abinci ta, jin tana ta zuba zance ya sata kashekiran, ganin ta sake kira yasata kiran Sa'eed ta ba shi wayan ya maidawa Yaya nan suka buɗe babukanhira, suna cikin kwasan shafta Salman da Sadam suka shigo, "ga Insu" Yaya yace tare da baSalman wayan.... Amsa yayi fuska yalwace da murmushi tare da kara wayan a kunni ya zauna "me kan ƙwa-ƙwa" yace tare da sakin murmushi, "na'am me kan giginya" tace tare da sakin dariya, dariya ya saki tare da miƙewa ya koma kusa Babiya dake ta sharan hawaye, "Aku sarkin zance ya can ɗin?" Yace tare da sakin murmushi, "Alhamdulillah komai normal se kewan ku" "ai muna kusa dake, kar ki ji komai" yace fuska cike da murmushi, "ina Yaya Sadam?" Tace murya na bayyana farincikin da take ciki, miƙa mai yayi murmushi be bar saman fuskan shi ba, jin tana mai-maitainayake ya sa shi faɗin "gani" ihu ta saki tare da faɗin "Yaya Sadam i miss you" "miss you toobabyInsu, ya su Hajiya?" Yace a natse, "suna lafiya" tace tare da gyara zama, "ki tabbatar saƙongaisauwa na ya isa kunninta" "nayi alƙawari" tace tare da sakin murmushi miƙawa Yaya yayi anatse, amsa yayi ya miƙe ya wuce side ɗin shi.... Miƙewa Sa'adatu tayi dan nufin komawa ɗakinta, "kin sha maganin ko?" Babiya tace idontaakanta, "eh Hajiya na sha" tace tare da ƙoƙarin barin wajen, "kin je school yau?" Salman yace idonshi akan ta, sadda kai da sauri tayi tare da faɗin "eh naje amma ban daɗe ba, saboda assignment nakai" jinjina kai yayi tare da kauda ido a kanta, "ina zaki ana hira?" Yasmin tace tare da kallonta, "ina son duba assignment ɗin yau ne" tace tare da sakin murmushi, "okay to, kar dai ki ƙi barci dawuri na sanki" tace cike da kulawa, murmushi ta saki tare da barin wajen.... Ba ta kammala waya da Yaya ba se 12:45am hamma ta saki ta sauka ta maƙala wayan a caji tashige toilet, ba ta jima ba ta fito da alamun ruwa ta watsa, ciro kayan barcinta me laushi dakauri tayi ta saka, hula me raga ta zura a kai, dakko coolern farfesun da Baba Mari ta mata tayi tazauna dirshan a ƙasa gefen gado inda carpet ya ma wajen ƙawa ta fara ci a natse, se da taji cikinta yayi dam-dam ta miƙe ta warwari tissue ta goge baki da hannu ta jefe a dustbin, buɗemadai-daicin fridge ɗin dake gefe tayi ta dakko ruwa ta ɓalle murfi ta kafa baki.... Saukewa tayi ta ajiye raguwan a saman bedroom table ɗin dake kusa da flat screen tvndakebango ta wuce inda ta ajiye ƙaramin jakanta, dakkowa tayi ta zage ta ciro takardan da Yayayasaka mata a hannu time ɗin da suke magana a airport ta haye gado ta ja blanket har wuyatadanna madannin dake saman kan gadon kaɗan wutan dakin ya ɗauke, murmushi ta saki taredadanna fitillan dake saman durowan dake gefen gadon, madai-daicin haske ne ya bayyanawandakana gani kasan na barci ne.... Warware takardan tayi a a natse tare da kafe idonta akai, "Insiyyah wannan na ki ne" murmurshi ta saki lokacin da ta karanta a bayyane tare da gyara zama, "kin daɗe ki na tambaya na meyasana ke son ki karanci law bayan ke likita ki ke san zama kaman Dr Hisham, kin san dalilin?" Girgizakai tayi kamar me magana da wani tare da sakin murmushi, "saboda Yaya Sahabee ne" "ohAllahAnty komai saboda Uncle, yaushe za mu fara abu dan kan mu?" Ta idda tambayan idonta nakallon sama, sauke idon tayi ta maida ga takardan tare da cigaba da karantawa, "a duniyayanason yaga mace na wannan aikin, hakan na matuƙar burgeshi da ba shi sha'awa, shine wandayadage akan law zan karanta, yana yawan ce min "Insiyyah za ki zama shahararriyar barrister matuƙar ina tare da ke, zan sa duniya ta san wacece barrister Insiyyah" murmurshi Insutasaki tare da jijjiga kai, "na san yanzu haka ki na sakin murmushi, ni ma a dai-dai wajen nan murmushi nake... Dariya Insu ta saki tare da faɗin "i know" "yana ce mun "ni zan kai ki aiki ranar farko, in riƙehannunki har cikin office ɗin ki in zaunar dake a kan kujeranki in sumbaci goshin ki da laɓɓanki in ce miki fatan alheri" rumtse ido Insu tayi tare da faɗin "Allah yasa Yaya be karanta nanba" tana kai nan ta maida hankali akan takardan... "Kina tashi zan dauke ki na koma dake gida na miki wanka na baki abinci ki ci na kwantar dakena miki tausa har se kin yi barci" a lokacin ba abinda nake iya ce mai se dai in yi murmushi, kinsan wani abu Insu?" "A'a faɗamin Anty" tace tare da goge hawaye tare da maida hankali gatakardan... "Ya cika batutuwan shi da dama, Yaya Sahabee yasa na shahara, shiyasa hakan, duk wani matsayi da na taka a aikina ta sanadin shi ne, duk da ya nisance ni a zahiri be nisance ni a baɗini ba, ya tsayamun a dukkan matsololin da suka taso mun daga wajen aiki, Insu ya sa na sanu, yasana shahara kamar yanda yake faɗamin kullum, kin san wani abun farin ciki?" girgiza kai tayi tareda goge hawaye.... "Na ganshi Insu duk da ganin a cikin jama'a ne, amma na gaidashi ya amsa, wannan shineabudayafi komai faranta mun bayan duk abun da yawue, ya sakin murmushi duk da ban san a inayatsaya ba" goge hawaye tayi tare da gyara kwanciya idonta akan takardan.... "Ya cika mun buri akan aikina, ya cika alƙawari da ya ɗaukan mun, se dai burin shi na ya rakani ranar da zan fara aiki be cika ba, burin mafarkan shi ba su tabbata ba, a ranar da muka haɗunahangi rauni da karaya a idanun shi Insu, na san zaki ce meyasa nake faɗa miki ko?" Jinjinakai tayi tare da jan majina.... "Saboda ke nake so ki cika mishi wannan burikan Insu, ke nake so ki maida mafarkan shi zahiri, ki tabbatar mai da cikan wannan burin, burikan da yake da shi akan matarshi da yawa, ya tsarairin rayuwar da yake son yi da ita fiye da yanda zaki hasaso, ba komai a ciki se aminci, in dai bazaki ƙosa ba zaki fahimci abinda na rubuta miki a wannan takardan, Yaya Sahabee a tsarin shi bawane ga mace, miji ne gareta, abokinta, Yayanta, amininta" sauke numfashi tayi tare da faɗin"dukda sanin hakan da ki ka yi Anty meyasa ki ka guje shi?" Ta jefa tambayan tare da kallon samanɗakin... Likitanci shine abinda yakaranta, kuma har yanzu yana aiki a babban asibitin shi dake ƙasar London, ki natsu da kyau wajen mu'amalantar shi, ba ya san garaje, ba yasan rashin natsuwa, baya san rawar kai, yana san a yi ta magana yana saurara ko da ba ze ce komai ba, yana soninyayi ƙawalliya a yaba, yana son matarshi ta ci da shi abinci da hannayenta, yana son tsan-tsankulawa" murmushi ta sakin ganin rubutun takardan ya kare tare da faɗin "oh ni Insu jikansarauniya Nafisat waye ke son jin abinda nake so da wanda ba na so ni kuma? Ke ne Anty koUncle ne?" Tayi maganan tare da girgiza kai, ninke takardan tayi ta zura a ƙasan pillor ta kai kanta a jikin pillor tare da fara karanto azkhair ɗin barci..... Zaune suke a daining area kowa na cin abinci hankali kwance, kallon kujeran Insu Yaya yayi tareda sakin murmushi, murmushi Balarabe ya saki tare da faɗin "a gaskiya anyi rashi a gidannan, daInsu baby na nan da yanzu kunnuwan mu na aiki" dariya gaba ɗayan su suka saki cike da kewanta, nan kowa ya fara furta albarkacin bakin shi akan zantuttukan da take musu, ɗaure fuska Sa'adatu tayi tare da ƙara ƙaimi wajen cin abincin dake gabanta.... Sallama Salman yayi tare da ƙarisawa inda suke, "to ga magajinta nan se ka zauna Salmanu" Babiya tace fuska cike da murmushi, murmushi ya saki tare da jan kujeran ya zauna miƙewaNafisat tayi ta zari plate ta fara saka mai abinci, gaishesu yayi a natse, amsawa suka yi da sakewa, gaishe shi su Farisat suka yi a girmame, amsawa yayi fuska a sake, "Yaya Salman mutuminkafaya kai bango" Yasmin tace tare da miƙa mai wayanta dake gefenta, murmushi ya saki taredaamsa ya fara duba saƙonnin da Morata ya turo, murmushi ya saki tare da miƙa mata, cikedafahimtar shi yace "wannan sonki yake" ... Taɓe baki tayi tare da faɗin "be ji da kyau ba, ai ban shirya wasa da kwanciyar hankali na ba" "meki ke nufi!" Balarabe yace tare da kama haɓa, "Yaya Balarabe bana so, ba zan taɓa son kowaba" tace hankali kwance, "subhanallahi Yasmin ki na cikin hayyacin ki kuwa? Tukun na ma, kinsanabinda ki ke cewa?" Babiya tace fuska cike da mamaki.... "Na sani Hajiya so mugun wasa ne, wanda ya tarwatsamun kwanciyar hankali tun kan inzoduniya, yayi wasa da hankali da natsuwan iyayena, ba zan yarda ya kawo ziyara a rayuwataba, dan shine babban gan-gancin da zanyi" ta idda maganan cikin tabbatar da kalamanta, saukenumfashi Yaya yayi tare da sakin guntun murmurshi ya maida idon shi ga abincin gabanshi.... "Abdussamad ka na jin yarinyar nan fa" Babiya tace jiki a sake, "to Hajiya me ze mata? ra'ayintane fa" Balarabe ya tari numfashinta da faɗin haka, "kai kauce mun a ido, se a barta tayi ta zamaba aure kenan, tunda a garin gaɓa-gaɓa muke" tace murya cike da takaicin maganar shi, dariyaya saki tare da faɗin "wa yace ba zata yi aure ba? Soyayya tace ba za tayi ba" yayi maganancikeda dariya.... "Ai rashin soyayya aure ne Balarabe, in ba soyayya ta ya za'a yi zaman auren?" tace tare dakallonshi, "to ke kin ji Yasmin baby se ki zubda makaman ki ki rungumi soyayya" yace tare da kallonta, "har abada Yaya Balarabe" tace cike da tabbaci, "Hajiya to ki cire rai akan wannan jikan taki zatayi aure, dan in dai ta cigaba da wannan ikirarin cikin da Anty Hafsa(matan Lurwanu) zatahaifama se tayi ko yayi aure ta na zaune" Sadam yace tare da kallon ta ... "A uzubillahi da batun ka Sadam" Babiya tace a harzuƙe, dariya ya ƙyalƙyace da shi tare dafaɗin"to ai haka take nufi Hajiya, buɗe miki batun na yi yanda zaki gane" "in sha Allah za tayi aurentaa shekarun ƙuruciya" tace cike da fata, jawo wayanta da ƙaran message ya shigo Sa'adatutayi, ganin abinda saƙon ya ƙumsa ya sata ajiyewa ta ɗan ƙara zama kaɗan ta miƙe a natse ta wuceɗakinta... Bata jima ba ta fito shirye cikin shiga na ke ce raini, less ne dakakken da yaji aikin ƙwararrentelansu, ta zuba ɗauri na kalla a ƙara, takalmi me tudu sanye a ƙafafunta se jaka da ta saɓaakafaɗa, "wow se ina haka Sa'adatu?" Yasmin tace cike da yabawa da kyawun da tayi, murmushi ta saki ganin yanda duk suka zuba mata ido, tare da faɗin "school za ni" jinjina mata kai tayi tareda fadin "bari in miki video kin yi matuƙar kyau" jinjina kai tayi tare da gyara tsayuwa.... "Yau ku na da lecture ne?" Salman yace tare da zube mata ido, "eh" tace a hankali kai a ƙasa, "kenan Rahma ta fara ƙin school, tace yau ba kwada lecture" yace idon shi ƙyamakanta, "nobalecture yau, akwai test ɗin da nake son gyarawa ne" "oh" yace tare da kauda kan shi daga gareta, sauke numfashi tayi a hankali tare da kallon Sadam dake cewa "ki jira Rufa'i ya dawo kai suNafisat se ya kai ki" "a'a bari zan hau napep" tace da sauri tare da ficewa, kallon SalmanFarisat tayi tare da mai alamun menene?, "Akwai wani abu da take ɓoyewa, zan bincika, in na tabbatarzan faɗa miki" jinjina mai kai tayi jiki a sanyaye tare da bin inda ta fice da ido ... Tunda ta iddar da sallahn asuba ta fara jera kayanta a wedrobe, tana gamawa ta koma samanmirror nan ma jera mayukan da take amfani da su tayi, wajen takalma tace ta jera, saukenumfashi tayi da ƙarfi tare da bin ɗakin da ido, murmushi ta saki tare da zaro jakunkunantata jera a inda aka tanada dan su, ɗakko hotunan da suka yi da Anty da su Farisat tayi ta fara maƙalasu a bangon kudu na dakin, se da suka mamaye kusan rabin bangon, murmushi ta saki tare da ƙarewa hotunan kallo, daga wanda take ita ɗaya se wanda take da Anty se wandasukegaba ɗayan su, sosai hotunan suka ƙara ƙawata dakin, zaro babban ciki tayi wanda suka yi selfieranar da Anty za ta rasu, fuskokinsu dake yalwace da murmushi me cike da na garta ya cikafafaɗeɗen allon hoton, ajiyewa tayi a saman gado ta wuce toilet.... Wanka ta yi shaf-shaf ta fito, shiryawa cikin wata arniyar abaya da ta ci kuɗi tayi, fuskannanbabu ɗigon komai banda mai, turare kuwa anyi ɓarin shi yanda yakamata, ɗaukan hotontayi tafice a natse, tana sauka daga matakalan benen masu kula da tsaftace side ɗin suka ƙarisodasauri suka ɗurƙusa tare da gaidata, murmushi ta saki tare da amsawa hankalinta akan fitillundasuka sakko da su suna gogewa, "akwai wani abu da ki ke buƙata ne Ma?" Babban cikin suyacecike da ladabi, murmushi ta saki tare da faɗin "ya sunan ka?"... "Feita Ma" yace a ladabce, "to Feita so nake a manna mun allan hoton nan a bangon parlournnan" tace tare da miƙa mai hoton, da sauri ya amsa tare da faɗin "a wanne za'a saka?" "Sakaanan, yanda duk wanda ya shigo ze fara arba da shi" tace tare da nuna bangon da take so, "toMa" yace tare da fita dan kwaso kayan aiki, juyawa sama tayi a natse.... "Zan samu sakwara?" Sudais dake kwance yace tare da kallon Gude dake zaune nesa da shi, murmushi ta saki jiki na ɓari tare da faɗin "me ze hana, in shi ka ke son ci yanzu se in kira Nafisatu ta yo maka" ta idda maganan cike da farin cikin maganan da ya mata, dan tun jiyadasuka dawo da batun rashin sa'a ya daina mata magana, "ni ba na son na kowa na ki nake so" yacefuska a ɗaure, "to kwantar da hankalin ka, ba ri in kira Sala ta zo ta zauna da kai se in je inyomaka" tayi maganan tare da zaro waya, "wai Momy ni ƙaramin yaro ne da za ki dinga wani nemanme zama da ni? Ba fa na son abinda ki ke mun, in har se wata ta zo ta zauna da ni ne ki bar shi ba na so" yayi maganan zuciya ɓace, "kai Sudais ka cika ɗaukan zafi a abinda be kai ya komoba, yanzu ina lefin ta zo ta zauna da kai kafin in dawo? Dan fa tsaron lafiyarka ne, kar bayana wani abun ya taso maka" tayi maganan cike da rarrashi, "ba wani abu da ze taso mun, in zaki jekawai ki je" yace a daƙile, "to shikenan kwantar da hankalin ka, bari in tafi, ka kula dan Allah kanajinwani abu ka kira ni" tace da kulawa, jinjina mata kai yayi ba tare da yace komai ba.... Kai tsaye ta na fita daga babban gate ta tari me napep, ba a inda ya sauke ta se a kofar asibiti, bashi haƙƙinshi tayi ta taka a natse ta shige, tana gab da ƙarisawa ward ɗin da za ta ta hangoGudeta fito a hanzarce, saurin raɓewa tayi ta wuce sannan ta fito ta shige ward ɗin... Tsayawa tayi kawai tana bin shi da ido, tsaki yaja tare da faɗin "kin san bana son kallo ko?" "Meyasa ka ke son sabautani ne Sudais? Meyasa ka ke son cuzguna mun ne? Me na rasa dakowacce ɗiya mace take da? Me ye ban iya ba? Me zaka nema a wajen wata wanda ba na dashi?"Ta idda maganan a raunane tare da sakin hawayen da suka kawo idonta, tsaki yaja tare dafaɗin"dan wannan na kira ki ne? Meyasa kin cika son dawo da abinda ya wuce ne? Zo ki gamsar dani".... Ya idda maganan tare da miƙa mata hannu, "ba zan iya jurewa ba ne Sudais, zan iya cutar dakaina in cutar da duk wacce ka faurtawa kalman so ko da ba ta maido maka ba" tayi maganancike da tabbaci, bin ta kawai yayi da ido hannu a sake, ganin yanda take kuka ya sa shi faɗin"indai ba zaki cutar da ni ba ai dai-dai ne" kama hannun tayi tare da faɗin "ba zan yarda ko ƙunbarkaya taɓu a ta dalilina ba, ƙaunarka nake da dukkanin zuciyata" ta idda maganan tare da karahannjnshi a saitin ƙirjinta ... "Ko na auri Insu ba zamu rabu ba, muna tare" yace bakin shi a dai-dai saitin wuyanta, ƙankameshi tayi da ƙarfi saboda lasan da ya kai ma wajen tare da faɗin "meyasa ni ba zaka aure ni ba?" Ɗagokai yayi ya kalleta tare da faɗin "Momy ba zata taɓa amincewa ba" "ba ka sanar da ita irinƙaunarda muke wa juna ba ne?" Tace tare da zura idanunta a na shi, "duk ƙaunar da nake miki, bekai rabin wanda nake ma Insu ba, da ƙaunarta na ta so, saboda shirmen da su Momy ke ma mahaifiyarta ya sa ni ƙin furtawa, amma yanzu na yi alwashin yaƙi da kowa dan mallakanta" yaidda magana tare da jinginata da ƙirjin shi yana ƙoƙarin zage zip ɗin rigarta.... Janye jiki tayi da sauri, tare da faɗin "baka isa ba, ba wacce zata mallake ka se ni, komai nakamallakina ne, wallahi Insu ba zata rabani da kai ba" tacd tare da ƙanƙameshi, tureta yayi daƙarfi zuciya a ɓace tare da faɗin "tashi ki je" yayi maganan fuska a ɗaure tare da nuna mata ƙofa, faɗawa jikin shi tayi tare da faɗin "ka dube ni da idanun adalci ka mun adalci, ba zan iya rayuwababu kai ba, kai nake so, Insu ba zata taɓa sonka ba, ta fisu kafiya gaba ɗayansu, na yi matasaninda baka mata ba" tayi maganan cikin rishin kuka, ƙoƙarin tureta yake amma taƙi ba shi damanhakan, "kai ka nuna mun komai, kai ka sa na yaga duk wani rigar mutunci da Anty ta sanyamun, kai ka saba mun da sanka da kanka, kai ka koya mun shan duk wani abu da kake sha, se danaiyakomai sannan ka ke son janye jikin ka barni, ba zan bari hakan ta faru ba, zaka sa na yi kisankai" ta idda magana tare da fara tura mai saƙonnin da ta san ba ya iya jurewa, nan da nan ta burkitashi ya fara sakin sumbatu, "ina sonki, se dai ba za su bari mu mallaki juna ba, zanaureki, zan mallaka miki kaina gaba ɗaya" ire-iren irin waƴan nan zantuka ya dinga saki, ita kuwaɗaukan su take tana adanawa a inda ido be isa gani ba, tare da alwashin fito na fito da komawaye, har da Anty in ta kasance a raye, dan za ta ɓoye ƙaunar da take mata a baɗini ta fiddoƙiyayya a zahiri.... Gyara ɗakin tayi yanda yakamata ta koma saman sofa ta zauna tare da kunna tv tashanBollywood ta nemo ta saka, murmushi ta saki saboda ganin suna maimaita filmɗin series naASHIQ ANA, gyara zama tayi tare da baza ido, dan ba kaɗan ba Chiki da Yash suke burgeta, tayi nisa a kallo ta ji waya na neman a gaji tashi tayi ta ɗaga tare da sauraran wanda ya kira, "Maankammala shirya table" taji sauka natsatstsan murya a kunninta, "okay ina sakkowa" tace taredaajiyewa ta koma saman sofa, se da episode ɗin sannan ta fice... Tana sauka ta hangi Lawuza tsaye cikin uniform ɗinta, murmushi ta saki tare da faɗin "ba dai tsayuwan jira na ki ke ba?" Murmushi ta saki cike da mamakin ƙanƙantar ta, duk da Maudetadawo tace musu ba matar gidan ba ce, amma dai tayi mamaki, "bismillah Ma" tace tare danunamata daining area ba musu ta ƙarisa, saurin jan mata kujera tayi ta zauna tare da fara sakamataabinci, sosai ta ci abincin dan ba ƙaramin daɗi ya mata ba, tana ajiye cokali tayi saurin warwarantissue ta ajiye mata, "nagode Anty ya sunan ki?" Tace idonta a saman fuskantaz murmushi tasaki tare da faɗin "Lawuza" "to Anty Lawuza nagode" tace tare da miƙewa, ƙarisawa inda hotondaaka maƙala yake tayi bin yanda ya zauna daram tayi da ido tare da ja baya kaɗan "wow" tacetareda komawa gaban hoton ta ɗago wayanta dake hannunta ta ɗauki kanta a jikin hoton, kallonLawuza da ta zuba mata ido tayi tare da faɗin.... "Munyi kama ko?" Jinjina mata kai tayi tare da faɗin "sosai Ma" murmushi ta saki tare da faɗin"ho Anty kinji abinda Anty Lawuza tace "wai munyi kama" murmushi Lawuza ta saki tare dabinta da ido, "Anty tace a miki godiya" tace tare da sakin murmushi ta wuce matakala, murmushi Lawuza ta saki tare da fara tattara abubuwan da tayi amfanin da su... "A haka zaki tafi ba zaki watsa ruwa ba?" Sudais yace tare da kallon ta, "eh in na koma gidazanwatsa" tace tare da ƙarisowa kusa da shi ta sakin mai sumba a laɓɓa tare da faɗin "ina matuƙansonka" jinjina kai yayi ba din abinda tace ya shige shi ba tare da miƙa mata ledan da ya zaro"allura ne, Allah yasa kan ki ya ɗauka" yace tare da bin ta da ido, amsa tayi tare da faɗin"indai kan ka ya ɗauka nawa ma ze ɗauka, danni ni da kai ɗan Juma ne da ɗan Jummai" dariya yasaki tare da fadin "in na samun dama zan ne me ki gobe" jinjija mai kai tayi ta juya da zummanficewa, turo ƙofan Gude tayi baƙi dauke da sallama.... Da mamaki ta bi ta da ido, tana niyyan magana Sudais yace "nagode ki je kawai" ba musutafice, juyo da dubanta kan shi tayi tare da faɗin "dama baka rabu da yarinyar nan ba Sudais!" Tajefamai tambayan kaman za ta tashi sama, "kin ganni a inda take ne? Ina ce nan ta zo ta sameni, tazo gaidani zan ƙi amsawa ne, dan Allah ki daina saurin yanke hukunci da abinda idon ki yagani" sauke ajiyan zuciya tayi tare da faɗin "wannan ƴa akwai jarababbiya, ko da yake duk kai kajadaka sakin mata fuska, zan wa tukkun hanci" tana kai nan ta ajiye basket ɗin da ta jero mai sakwaya da miya tare da faɗin "in zuba maka?" "A'a se zuwa anjima" yace tare da kauda kai.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 ِبسم الله الرحمن الرحيم ~~~~~~~~~~~~~~ Created and written By Yardajjiya👩 💻 Page. Fourteen Tana fita ta tari me napep ta haye suka kama hanya, a titin anguwarsu ta sauka, tana biyanshi haƙƙin shi ta shige gidan dake bakin titin ta gefen dama.... Gaida matan dake zaune kan tabarma tana ɗinka zube a wani babban rigan shadda dake hannunta tayi, amsawa tayi kadaran kadahan tare da bin ta da ido, "Harira na nan Mama?" Taceagirmame "tana ciki" tace idonta akan ta, miƙewa tayi ta shige ɗakin... Buɗe ido wacce ke zaune tana ɗinki irin na Mama dake waje tayi tare da faɗin "yaushe a garin?Dama kina ƙasan?" Harara ta watsa mata tare da faɗin "kyace haka mana tunda kin fini baki" dariya ta saki tare da miƙewa ta ajiye shaddan da take ɗinkawa a saman gado tare da zarotabarma ta shinfiɗa mata.... Tana zama tace "yau dai na ce bari in zo in ganki, tunda ke kin yadani, rabanki da zuwa gidatungaisuwar Anty" "anguwar ta ku ce se an shirya zuwa, shiyasa amma ai ban yanke dake ta wayaba" "eh nan kam ki na tabuƙawa" tace tare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da wucewata ɗibo mata ruwa ta ajiye mata.... Zaune take tana ƙanƙare ƙunbunan ƙafafunta, tunda ta koma ciki ta tadda filmɗin da sukasakabe mata ba ta kashe tvn ta jawo kayan gyara ƙunba ta fara gyarawa, jin telephone ya ɗaururi yasata miƙewa ta ɗaga, "Ma akwai baƙuwa a ƙasa" zare wayan tayi jin na can ya ajiye cike damamaki tare da tattara karikitan gyaran ƙumban ta maida ta fice.... "Tana gab da iddasa sauka ta hangi Hajiya tsaye idonta ƙyam akan hoton su dake manne aparlourn, tana iddasa sauka ta sakin mata murmushi tare da faɗin "sannu da zuwa Hajiya" juyowa Hajiya da hankalinta kacokan ke ga hoto tayi tare da buɗe mata hannu, "zo Insiyya" tacearaunane, dan ganin hoton ba ƙaramin rauni ya tada mata ba.... Da sauri ta isa ta shige jikinta, matseta tayi tare da faɗin "Allah ya gafartawa Insiyya, lallai anyi rashi" murmushi Insu ta saki tare da faɗin "amen" janta tayi a natse suka ƙarisa inda jerunrantststsun kujerun parlourn suke, zaunar

Chapter 18 of 109