Share this page
Mairah ta tsana shine kace zo ki abu kaza, wallahi wahala za ta sha ba abinda ya shafen" tace tare da miƙewa, "tafiyan ya tashi kenan?" Farisat tacetare da kallon ta, "lokaci ya gabato, gashi tun ɗazu Nafsii ke kira na" tayi maganan tare dajuyawainda yara ƴan kimanin shekaru 7 ke zaune, "ku tashi ku kwaso tarkacenku" tace a dake, bamususuka miƙe suka fice side ɗin da sauri, "baby miƙe" tace ma yarinya ƴar kimanin shekaru huɗudake gefen Nafisat, miƙewa tayi tare da nufanta.... "Ba zaki leƙa Suhailat ɗin ba ne?" Yasmin tace idanta akan ta, "in mata me? An ɗaura munkawota, ta riƙe mijinta da kyau shine komanta anan, uwa, uba, wa, aboki, a toh" ta idda maganancikeda mayyance, dariya Sadam dake bin ta da ido ya saki tare da girgiza kai, "to shi Sadamɗinfa?" Samir yace murya cike da murmushi, "ai ya san komai tunda da tunanin shi yayi auren, dukabinda zamu faɗa tishine akan abinda ya sani, ya ɗauki tarihin rayuwar Yaya da Anty kacokanyadasa a gidanshi ze ga alfanun koyi da magabata, sannan kowa ya san Suhailat yarinya ce baruwanta, wallahi in muka ji muka gani to shine" dariya suka kwashe da shi tare da bin ta daido.... Murmurshi Yaya ya saki tare da yafutota, murmurshi ta saki tare da ƙarisawa inda yake, riƙohannunta yayi cike da ƙauna tare da ɗago kai ya bi su da ido, "Umar jeka kira uncle da ɗiyarka" yace fuskanshi akan Umar da ruwan samartaka ya fara wankewa, ba musu ya tashi ya ficeanatse, be jima ba ya dawo tare da su, kauda kai da sauri Mairah da ta tasa sosai tayi cike dafargaban kallon da Insu ta watsa mata.... Zama kusa da Nafisat Sahabee da ya zama cikakken saurayi yayi tare da amsan ɗiyarta dakejikinta, sauke numfashi Yaya yayi idan shi akan su tare da faɗin "alhamdulillah, ina miƙa godiyana ga mahaliccina da ya nuna min wannan rana, rana me matuƙar mahimmaci a gareni, ga ku ko wannen ku ya fuskanci rayuwa, wasun ku da zuri'a wasun ku na kan hanya, bani kaɗai na so ganin wannan rana ba, se dai banyi baƙin ciki dan ni kaɗai na gani ba, Allah ya muku albarka, ya albarkaci zuri'ar ku!" Ya idda jero addu'o'in fuskan shi na yalwatuwa da murmushi, "amin" suka ce bakuna a haɗe na su fuskokin yalwace da murmushi.... "Rashin Anty a cikin mu babban giɓi ne da babu me iya cike gurbin, ba zamu daina zubda hawayen rashinta da addu'a a gareta ba har se ranar da muka tafi inda taje, Allah ya gafartamata, ya rahamsheta, ya sa tana kyakykyawan mako ma, jigon mu dake raye Allah ya ƙaramai lafiya, ya wadatashi da abinda lafiya za taci ta sha, Allah ya ƙara mai tsawon rai me albarkadaamfani, ba zamu ƙi roƙon ya nuna mai jikokin jikokin mu ba ko mu ba mu gani ba" dariya sukakwashe da shi idan su akan Insu da ta kame fuska, "sosai kuwa ko ba haka ba lovely Yaya?" Tacetare da kallon shi, murmushi ya saki tare da jinjina mata kai, "yawwa, Allah ya jiƙan magabatanmu ya yafe musu kura kuransu, malam Sa'eed a rufa mana zaman da addu'a" ta idda maganantare da ɗaga hannu.... Gyara zama Sa'eed dake bin ko wannen su da ido yayi ya fara rattafo addu'o'in nema musualherin mahalicci da albarka, da aminci, yana dasa aya suka shafa suka mimmiƙe dan musurakiya.... "Shiga Aamir" tace tare da kallon Sa'eed dake tsaye a gefen Sadam babba, shigewa yayi dasauri, "ina Aiimar?" Tace tare da buɗe ido a wajen, "gani Ammi" yace a hanzarce, "shige" tace a natse, shigewa yayi da sauri, "baby shiga kusa da Yaya Aiimar" ba musu ta shige, ina Farhat (Amina, ɗiyar Nafisat ta farko tun yaye aka bar mata ita) "gata" Mairah tace a ɗan tsorace, "zo ki shige" bamusu ta shige, ja gefe tayi tare da kallon drivern cike da bada umurni tace "banda gudu" jinjinakai yayi ya nufi mazaunin shi.... "Ita Mairah ba da ita za'a koma ba!" Gude tace tare da kama haɓa, "Anty Gude ki ce ma Halimaina jiran kiranta dan Allah" tace tare da wuce wa gefen da su Lailah ke tsaye, "Insu me yehakan?" Khadijat tace tare da baza mata ido, "Anty Khadijat ƴa fa na bata ta riƙe mun sabodaraini ta bawa wata ta wuce!" Tace a zafafe, "yi haƙuri tayi laifi, kar ki ce zaki yi fushi da ita, kinfasan fushin uwa akan ƴaƴanta babu kyau" "hmm" tace cike da takaici, "wuce ki bata haƙuri" Salwa tace tare da kallon ta, ba musu ta wuto jiki a mace, duƙawa tayi har ƙasa tare da faɗin"kiyi haƙuri Ammi ba zan ƙara ba" "Allah yasa" tace tare da jan hannun Sa'eed suka wuce motandakegaban na su Aamir, tana shiga ya dafa mata baya, wuce wa motan su Mairah tayi tare da ɗagamasu little hannu ɗaga mata na su suka yi cike da kewa, ƙarisawa jikin motan su Insu su Farisat suka yi cike da kewanta da za su yi suka miƙa mata hannu, kamawa take a natse fuskantanabinfuskokin su da kallo me cike da ƙauna, "a ba shi dai haƙuri, Anty ba ta yi lefin da za'ayi fushi daitahar haka ba" Yasmin tace tare da danne dariyar da ke san kuɓuce mata, harara ta banka matatare da faɗin "wa kenan!" "Shi ɗan shagwaɓan mana" zare hannunta dake cikin nata tayi taredafaɗin "Umma ki daina sa ido wallahi" dariya suka saki tare da janye jiki daga jikin motan... "Sa'eed ina jiran saƙon nan fa" Sahabee yace da ƙarfi, jinjina mai kai yayi fuska faɗaɗe da murmurshi, hannu suka ɗaga musu gaba ki ɗayansu har suka fice daga gidan, murmushi Yayadasuka ɓacewa ganin shi ya saki tare da maida duban shi kan su Farisat da ke ta tattara yaradankomawa ciki tare da faɗin "na ganin miki, alhamdulillah ala kulli hal" "muje ciki Yaya" muryanYasmin ya katse mai yanayin da yake ciki, sauke idan shi a saman fuskanta dake cike da murmushin ƙauna yayi tare da miƙa mata hannu ta kama suka juya dan komawa cikin gida..... Suna fitowa farfajiyan tashi da saukan jiragen garin suka tadda jerin gwanon motoci da masubada kariya tsaye suna jiran su, babu wani ɓata lokaci suka shishshige suka ɗaki hanyar gida.... A hanzarce yaran da suka ƙosa su yi tozali da abun ƙaunarsu suka fiffito suka yi ciki a guje, sakkowa Insu dake saɓe da Nur tayi tare da ƙoƙarin gyara zaman jakan dake kafaɗanta, kai hannu Mairah tayi a ɗarare tare da faɗin "kawo ta Ammi!" Miƙa mata ita tayi ba tare da takalleta ba ta wuce, murmurshi Sa'eed ya saki tare da jan kunninta, "auh uncle Sa'eed da zafi fa!" Tacekamar zata saki kuka, "ai ke ce daughter ba ji ki ke ba" shagwaɓe fuska tayi tare da kallonshi amarairaice, dariya ya saki tare da jan hannunta suka shige ciki.... Da hoton Hajiya dake manne a bangon general parlor ta gabas suka fara cin karo, a hanzarcema'aikata suka fiffito dan tarban su, "yawwa sannun ku, a shirya dinner mr president ze yi dinnertare damu" Insu tace tare da miƙawa wacce ta kawo hannu jakanta ta wuce sama a natse, fitowaAnisa da ta zama cikakkiyar budurwa tayi daga ɗaya daga cikin ɗakunan ƙasa tare da faɗin"yanzu fa Anty Suhailat ke tambayan kun iso" tayi maganan cike da mamakin ganinsu, murmushi Mairah ta saki tare da faɗin "ta kira ki ne?" "Eh mana, Aiimar ku zo ku watsa ruwa Farhat wutonan, ina baby?" Tace cike da kulawa, "gani nan Anty Aniy" tace tare da nufarta a guje, ɗaukantatayi ta ɗaga sama tare da faɗin "iyye ƴan Bertuwa, na ɗauka a can za'a barki" maƙye kafaɗatayi tare da faɗin "ni a wajen Abie za'a barni" dariya suka saki tare da bin ta da ido.... "Ke ki ma Nur bari in ma baby da Farhat, ku kuma ku wuce ku wanko kan ku" tace tare daƙoƙarin juyawa, "a'a Anty Aniy dan Allah ki ma Nur se in ma su babyn" Mairah tace cike dafata, "kin san ba yarda za tayi ba, gunda ke ɗin ma tana iya yarda ni kuwa se ta tara mun al'ummanƁadamayya akai" tace tare da juyawa ta wuce riƙe da hannayensu, shagwaɓe fuska tayi taredakallon Nur da ta lafe a ƙirjinta.... Murmurshi Sa'eed ya saki tare da miƙewa ya saka wayan shi a aljihu, bari zamu yi waya, ki cemata na wuce" yayi maganan tare da juyawa ya fice, jinjina kai tayi ta wuce bedroomɗinta, sabosa su Aiimar duk sun wuce na su.... Zazzaune suke a kujerun da ya ma general parlorn ƙawanya, cikin shiga na alfarma, bandawalwali da zuba ƙamshi ba abinda suke idanun su akan ƙofan shigowa alamun akwai wandasuketsammanin gani, da sallama ɗauke a baki ya shigo su Jabir dafe a bayanshi, girma ya ƙarakamashi haiba da kamala sun ninku.... A guje Aiimar da Aamir da baby da Farhat suka yi kan shi tare da ihun farin cikin ganin shi, buɗemusu hannu yayi cike da farin cikin ganinsu tare da rungumesu ya matse su, ɗago kai yayi yazuba ma Insu da ta miƙe ta nufo su ido, tana ƙarisowa ta sakin mai murmurshi tare da faɗin"toasaki Abie haka ko" sakin su yayi suka koma gefenshi suka tsatstsaya.... "An gaji an dawo kenan?" Jabir yace tare da sinne dariya, "uncle Jabir yaushe muka fara hakadakai!" Tace tare da kama haɓa, "auh na manta ne" yace tare da sakin murmushi, murmushi Abubakar ya saki me faɗi ganin Mairah na nufo su tare da miƙa mata hannu, kamawa tayi taredafaɗin "uncle's sannan ku da zuwa" murmushi suka saki cike da ƙauna kowa na nuna zallanfarincikin ganinta da yayi.... "Muje an shirya dinner, ko zaka watsa ruwa tukun?" Insu tace da kulawa, girgiza mata kai yayi tare da kama hannunta suka wuce ciki, kai tsaye dining area suka nufa, a natse ta haɗa mai abinci Anisa da Mairah suka haɗawa su Jabir suka haɗawa ƙanninsu da kan su, abinci sukaci anatse, cike da shaƙuwa da ƙaunan juna, suna kammalawa suka dawo cikin parlor saboda hakanya zame musu tamkar al'ada gare su.... "Ɗazu Kamil ke cewa in ba ki dawo ba ze je ya taso kawunan yaranshi" Alhaji Munnir yacetareda sakin murmushi, tura baki tayi tare da faɗin "yaran shi a ina, ni kaɗai ce ƴar shi" "a'a kingirmaki yi haƙuri ki koma ƙanwa" Jabir yace tare da kallon ta, "ba fa zan yarda ba" tace tare da sakinmurmushi, "Mairah!" SSB da idan shi ke kanta tun ɗazu yana nazartan ta yace tare da ƙarabazamata ido, saurin tattaro natsuwa ta kuma tare da faɗin "na'am Abie!" "Lafiya ko?" Yace cikedatuhuma, jinjina kai da sauri tayi tare da faɗin "eh Abie, ya aiki?" Murmurshi ya saki tare dajuyawaya kalli Insu, kauda kai tayi da sauri, murmushi Jabir ya saki tare da miƙewa, miƙewa suAlhaji Munnir suka yi suka sallame shi suka fice.... "Ku muje ku kwanta" Anisa tace tare da miƙewa, kamo hannun SSB da Insu suka yi kamar koyaushe in zasu tafi kwanciya tare da faɗin "Abie Ammi se da safe, Allah ya tasheku lafiya, yasakuna daga cikin bayin Allah salahai, ya sa ku tashi kuna masu cikakkun imani, Allah ya ba kualjanna ya kare ku daga wuta, se da safe" murmushi suka saki cike da ƙaunarsu tare da shafakawunansu zukata ƙal tare da faɗin "kar ku manta da alwala da addu'a" jinjina kai suka yi sukabi Anisa da ta musu se da safe ta wuce.... Miƙewa Mairah tayi a natse tare da faɗin "Abie se da safe Ammi se da safe, Allah ya haɗakudaalherin duniya da lahira, ya kare ku ya kare zukatan ku, ya yalwata farin ciki a rayuwarku, yakareku da ga sharrin dukkan abin ƙi, in kwana da Nur ne?" "Amin" SSB yace tare da yafuto ta, ƙarisawa inda yake tayi a natse kamo kanta yayi ya sumbaci goshinta ya juya ya sumbaci goshinNur tare da faɗin "Allah ya yalwata farin ciki a rayuwarki da na ƴan uwanki" "amin" tace cikedafarin cikin addu'an na shi tare da alfaharin samun su a matsayin iyaye, ganin ta ja ta tsayaalamun jiran jin abinda Insu zata ce take ya sata faɗin "amin, Allah ya baku abinda ku ka roƙamana, in zaki iya ba" murmushi ta saki tare da juyawa ta wuce saɓe da Nur.... Murmurshi SSB ya saki tare da jawota kusa da shi sosai, cike da rarrashi yace "me Hajiya Farisat ta kuma aikata yau?" Kaman jira take tace "Nafsii yarinyar nan babu tausayin ƴan uwantaazuciyanta, ace Mairah ta na jin Nur na kuka amma ko inda take ba ta kalla ba" murmurshi yasaki tare da faɗin "ki daina ɗaukan abu da zafi har haka Gorgeous, har yanzu Mairah yarinya ce, duka- duka yanzu take cika 10 year's, kuma kema kin san tana iya bakin ƙoƙarinta akan yarannantunkafin takai haka, rigiman na nan ne ya sa ki harzuƙa tare da tunanin hakan" ya idda maganantare da matsa cikinta kaɗan, ɓata fuska tayi tare da faɗin "ni dai bana da komai" dariya mesauti ya saki tare da faɗin "auh da gaske!" "Eh" tace tare da kamo hannun shi.... "To shikenan in ya bayyana ai zamu ga bakin faɗin "bani da komai" murmurshi ta saki taredafaɗin "kaji matan Hisham wai ta ƙara haihuwa!" "To me zata jira?" Yace tare da gyara zama, "habaNafsii shekara uku fa! Yara biyu" murmushi ya saki tare da faɗin "to ba wasa suka je yi ba, gaantynki na nan matan uncle ɗinki ma ta sauke ba jimawa Kausar ke faɗa mun" "wai AntynIƙilima!" "A'a Hasinat ko?" "Auh dama cikin na ta ya isa haihuwa ne!" Tace tare da kama haɓa.... "To gashi nan dai ta haihu" yace a natse, "tab ai ko ita ma Anty Iƙilima na hanya, dan banzatazamu je mu dawo bata haihu ba me ta samu?" "Baby boy" "oh a gaida uwar maza" tace tare dasakinmurmushi.... Murmushi ta saki tare da faɗin "kin ga ai sayi su gama su barki a hanya" tura baki tayi taredafaɗin "da wuya ne fa Nafsii!" "To zamu huta in muka kawo wannan" yace tare da rungumota, murmushi ta saki tare da faɗin "yawwa ɗaya tamkar da dubu" tayi maganan tare da ƙanƙameshi, dariya ya saki tare da miƙewa da ita a jikin shi cike da ɗinbin farin cikin dawowan su lafiyayace"muje a cuɗani" dariya ta saki tare da faɗin "ina sonka!" Murmushi ya saki tare da faɗin "i know" "um um ni ban yarda ba se ka faɗa" tace a taɓare "ina sonkiii!" Yace da ƙarfi, "i know" tacedaƙarfi, dariya suka tintsire da shi cike da so da ƙaunan juna.... Tammat bi hamdilillah... Anan na kawo ƙarshen littafina me suna Muguwar Tsoka, ina godiya ga mahaliccina da yabani iko da daman farawa da gamawa lafiya, Allah ya yafe mun kura-kuraina na ciki, ladan kumayasaka mun a mizani, Allah ya ba masoya da makarantan shi ikon amfanuwa da daidan da keciki akasin shi kuma ya hanesu ɗauka🙏🙏🙏 Ina ma masoya albishir da sabbin littafaina da za su zo a cikin wannan shekara da muke ciki, GAYYAH, JARUMAR AZABA (BA JININ SA BA CE BOOK 2) WUTA DA HANKALI, ku biyo Yaardaɗoacikin duniyar nishaɗantarwa, faɗakarwar, da ilmantarwa, Yaardaɗo taku ce masoya 🙏🙏🙏 Comments fans🙏🥰 An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 109 of 109