2023 as a requirement of law" tun kafin ya ɓame baki Insu da SSBsukasaki
kuka me ƙarfi a tare, bajewa a wajen Insu tayi kukanta na tsananta, saurin rungumeshi Alhaji
Jamil yayi yana zubda na shi hawayen, nan kowa ya fashe da kuka mara sauti cike da farinciki, banda sharar hawaye ba abinda suke... Ta gidan Yaya ma kuka ne ya ƙwacewa su Farisat har Yaya se da zubda hawayen farin ciki, jawowaya Yasmin tayi ta danna number Insu jiki na ɓari, ringing biyu Lawiza da taje dan ɗagotataɗaga tare da ɗaga mata sallama, tana shirin jefa mata tambaya tace "yi haƙuri ba ta yanayindazata iya amsa call" "okay na gane please tasha maganinta kafin ta kwanta" "in sha Allah" tacetare da sauke wayan, miƙewa zumbur tayi kamar wacce aka kira ta yi inda hotonsu yake...
"Ba na faɗa miki se yi nasara ba? Ba na ce miki shine me nasaran nan ba Anty? Dubi" tacetaredanuna tv, "ji abinda yake cewa, yace Uncle shine yayi nasara, Anty yau na fahimci akan mutuminnan da ki ke yawan ce mana sa'a na tare da shi a ko ina, shine, Uncle ne, Uncle ɗina shine daƙasata yau" ta idda maganan tare da duƙewa a wajen ta saki raunataccen kuka, banda bin ta daidobaabinda suke suna kuka, kamo hannunta Lawiza tayi cikin na ta kukan ta rungumeta tare dabugun bayanta a hankali, "kai ta ɗaki" Hajiya tace a hankali, jinjina kai tayi ta wuce da ita upstairs....
Juyawa ga Jabir da duk suka rufu akan SSB suna rarrashi tayi tare da faɗin "kai shi ɗaki Jabir" tayi maganan hawaye na tsirara a saman fuskanta, miƙewa yayi a natse ya kamo shi sukawuce, "Alhamdulillah" tace a natse tare da wuce wa ga sujuddushshukri a natse, ta daɗe tana maubangijinta kirari da godiya kafin ta ɗago ta goge hawaye ta miƙe ta wuce ɗaya daga cikinɗakunan da ke ƙasa.... Ƴan ƙasa sun cika da murna da farin ciki, da yawan su ba su rumtsa a wannan daren ba, sunfito
tsakiyan gari suna nuna zallan farin cikin su tare da jaddada kalman ɗan Ɓadamayya shinedaƙasa, ba wanda yayi yunƙurin hanasu, tun daga lokacin suka fahimci akuyan ɗaure ta samusake, ta ɓangaren SSB kuwa raya daren nan yayi a gaban mahaliccin shi yana me kuka da roƙonyabashi wuyan ɗaukan nauyin da ya ɗora mai.... Da wannan farin ciki jama'a gari da ƴan uwa da abokan SSB suka wayi gari, duk wanda kakai idogareshi farin ciki ne ze fara maka sallama, sakkowa tayi a natse, sanye take da palazzo orangecolour, da t-shirt milk me hoton dog a gaba, orange ɗin jacket ta ɗaura a sama me tsayi dataushi
wanda ya kai ankle ɗinta, madaidaicin jaka me suffan mage saɓe a bayanta taja igiyan samasosai yanda jakan yayi ƙasa sosai, siniker orange sanye a ƙafanta, tayi masifar kyau fuskannanda ta ƙawata da baby hijab orange yayi fayau da shi da alamun kumburi a fuskan, tana iddasauka ta wuce dining room inda ta jiyo motsin su, "har kin tashi?" Hajiya tace da kulawa, jinjinakai tayi tare da ƙarisawa kusa da ita cike da girmamawa tace "barka da safiya Hajiya kintashi
lafiya?" "Alhamdulillah Insiyyah" tace cike da kulawa, ɗago kai yayi ya zube mata ido sabodaambatanta ta cikakken sunanta da Hajiya ta yi, murmushi ta saki tare da faɗin good morninguncle's and Auntie's" "morning Insu" wasun su suka ce wasu kuwa maida kai ga abincindakegaban su suka yi, murmushi ta saki tare da juyawa da nufin barin wajen....
"Ah-ah ina kuma zaki? Zo zauna ki ci abinci" Hajiya tace tare da kallon ta, girgiza kai tayi taredafaɗin "I'm okay" da mamaki ya zube mata ido jin abinda tace dan a iya zaman da yayi da itayafahimci ba ta wasa da ciki sam, "baki ci komai ba fa" Lawiza tace da tsan-tsan kulawa, murmurshi
ta sakin mata cike da jin daɗin kulan da ta nuna gareta tare da faɗin "ina azumi ne" "azumi! Yaufa friday" Kamil yace da mamaki, saura kuwa duk tsayawa suka yi da ga cin abincin da sukeyi
suka zuba mata ido, jinjina kai tayi tare da faɗin "eh uncle Kamil, na yi ma ubangijina alƙawari indai yasa Uncle ya ci zaɓe zan azumci wata ɗungum" tayi maganan cike da yanayinta, zareidogaba ɗayansu suka yi da ɗinbin mamaki, guntun murmushi SSB dake bin ta da ido ya saki, yanasane da jiya kwana sallah tayi yau kuma ta tashi da azumi, "shine yau ki ka fara?" Alhaji Munnir
yace da tsan-tsan kulawa, jinjina kai tayi tare da sakin murmushi, "ma sha Allah Allah ya baki
ikon azumta cikin ƙoshin lafiya" yace tare da kauda kai ya maida ga abincin shi, "muje DaddynIman na waje yana jiranki" Lawiza tace tare da riƙo hannunta da tsan-tsan kulawa...
Murmushi ta saki tare da juyawa da nufin barin wajen, "Innsouu" kalman da ya taka mata wani
kyakykyawan burki kenan daga yunƙurin barin wajen da take, juyawa tayi a matuƙar razanedanganin da gaske muryan wanda taji ne ya kirata ko kuma kunninta ne ya jiyo mata ba dai-dai ba, ilai kuwa shine zaune ya baza mata ido yayinda sauran jama'an wajen suka baza mai ido amamakance, murmushi ta saki idonta akan shi tare da faɗin "na'am Uncle kira na ka yi?" Jinjinakai yayi tare da miƙewa a natse ya buɗe hannayen shi a hankali tare da faɗin "come" ƙaramar
dariya ta saki me tafe da hawaye tare da yin inda yake a guje, shigewa jikin shi tayi ta ƙanƙameshi tare da sakin kuka me ƙaramin sauti, murmushi ya saki tare da saka hannayen shi biyuyarumgumeta, lokaci na farko da ya maida mata martanin runguma kamar yanda take mai, "congratulations" yace a hankali a dai-dai saitin kunninta, dariya ta saki tare da janye cikinta, binta yayi da ido a natse.... Girgiza kai tayi ta ɗaga kai sama alamun son tsaida hawayen da suke zubin mata take, sakkodakan tayi tare da sakin murmushi wanda ya ƙara fiddo asalin wacece ita, kallon shi tayi a natsetare da miƙa mai hannu idonta a saman fuskan shi, murmushi ya saki ya miƙa mata na shi sukadamƙe da ƙarfi gaba ɗayan su, murmushi ta saki tare da faɗin "I'm very very happy UncleI
wishing you all the best, may almighty Allah help you to handle the situation, may god blessandsuccess be with you" ta idda jero addu'o'in tare da shigewa jikin shi, banda furta amen babuabinda su Jabir ke yi cike da jindaɗi, shigo gogan zuba mata ido kawai yayi dan ya kasa iyafurtako kalma ɗaya, tana shigewa jikin shi ya lumshe ido tare da furta "shii is okay" Jan hanci tayi tareda zare jikinta a natse ta zari tissue ta juya ta fice da sauri.... Bin ta da ido yayi har ta idda ficewa, jan kujeran da ya miƙe yayi ya koma ya zauna a natse, ƙaramar dariya Hajiya ta saki tare da goge hawaye cike da farin ciki tace "oh Insiyyah ba dai
wawta ba, me ne ne na kukan kuma yanzu?" Ta idda maganan tare da goge hawaye, murmushi
Jabir ya saki tare da faɗin "da zaki tambayeta ce miki za tayi farin cikin ne yayi mata yawatarasaya zata yi shiyasa ta saka kuka" dariya duk suka saki tare da kallon shi, "tana da wawta sedai
kuma tana da hankali" A'isha tace a natse, "wannan ai dabanne ma A'isha, yarinyar nantunaninta ba na masu shekarunta ba ne, nazarinta da sanin yakamatan ta ya wuce na masuhankali" Jabir yace idon shi akan ta, "gaskiya na hangi wannan ma, jiya fa na haura dan kai maSSB magani na ɗauka ɗakin da take yake wallahi ganin yarinyar nan nayi zaune dirshansamanpraymat tana kwararo addu'o'i masu ratsa zuciya, nayi matuƙar mamaki" murmushi suka sakin
mata ba tare da sun ce komai ba....
"Kai Anty A'isha akwai ki da zuzuta abinda be kai ya kawo ba" Lubabatu tace tare da kaudafuska, "haba Luba ki dinga ganin komai da idon da ya dace mana, yayinda yarinyar nan ke zaunedirshantana roƙan aminci da kwanciyar hankali akan abinda ɗan uwanki ke harare ke kwance ki kebaki
san inda ki ke ba ma, sannan saboda rashin son gaskiya ki buɗe baki ki ce ina zuzuta abindabekai ya kawo ba, in dai haka ne kuwa na zuzuta kuma zan cigaba da zuzutawa" ta idda maganatare da jan kujeran da take kai baya ta miƙe cike da ɓacin rai ta bar wajen, "to menene kumaabun harzuƙa anan dan Allah?" Lubabatu tace tare da kama haɓa, mimmiƙewa suka yi ba wandaya ce ko uffan, dan sun san ko suncen ba gamsuwa za tayi ba....
"Momcy leƙa ki ce musu zan tafi wallahi" Balarabe yace tare da kallon Nafisat dake zaunekusada Babiya, murmushi ta saki tare da miƙewa a natse ta wuce hanyar bedroom's ɗin su, tanakai
jiki Yasmin ta fito cikin shiga me matuƙar ɗaukan hankali da burgewa, murmurshi ta sakinmatatare da faɗin "wow kin ga yanda ki ka kashe kala kuwa!" Dariya ta saki tare da rungumotacikedajindaɗi tace "kin fi ni kyau ai" dariya ta saki tare da faɗin "wane ni Yaya Balarabe yace ze yi
tafiyar shi" zare ido tayi tare da faɗin "wayyo Anty Farisat ta fito ne?" "Ai saƙon wa dukkankune"tace tare da wuce wa ɗakin Farisat....
"Ina zaku je kuma?" Babiya tace idonta kyam a saman fuskan Balarabe, "ba dai har kin mantaba!" Yace da mamaki tare da baza mata ido, harara ta zabga mai tare da faɗin "in zaka faɗamunka faɗa bana son yawan tambaya mara amfani, in na sani me ze sani tambayan" "gaskiya Hajiyayakamata mu kaiwa hospital ziyara, jiya fa nake faɗamiki general meeting da za'ayi na member'sɗin Aminan juna" ya idda maganan cike da mamaki, "oh tabbas anyi haka, to amma ai bakacemun yau ba ne, ka ce dai za'ayi meeting akan yanda za'a tsara shagalin bikin Farisatu" dariyaHabiba da ta shigo ta saki tare da faɗin "ai kuwa kai ne yakamata ka kaiwa hospital ziyarabaHajiya ba, kana yaron ka da kai ka fara mantuwa ina kuma ga girma ya cimmaka" "faɗa mai dai" Babiya tace tare da gyara zama...
"Na fa faɗa mata, se dai in bata fahimta ba ne" yace tare da miƙewa saboda shigowan da Yasmintayi, "ina take?" Yace tare da kallon ta, murmushi ta saki tare da faɗin "tana zuwa yanzu" "mujeta same mu a mota, 12 aka ce kowa ya tabbatar ya same shi a can, gamu a 12:11" ya idda
maganan tare da jan hannunta suka nufi ƙofa, shigowa parlorn da sauri Farisat tayi tare dafaɗin"gani nan Yaya Balarabe Anty Habiba se mun dawo, Hajiya a mana addu'a, in Yaya ya dawobamudawo ba a ce mai akwai saƙo da na ajiye mai a bedroom ɗin shi" jinjina mata kai suka yi taredabin su da murmushi har suka fice.... Tunda ta shiga school take tarban ƴan taya murna, ba ta samu daman samun hutu ba se dabarrister Umar ya shigo class ɗin, shima se da ya taya ta sannan ya fara gabatar da abindayakawo shi, ba su samu daman fita ba se da 1 ta buga, fitowa suka yi a gajiye suka yi masjidsunafitowa ta nufi library Nachma ta nufi restaurant, tana cikin nazari akan assignment ɗin wani
shari'a da aka basu Khalim ya ja kujera ya zauna, ɗago kai tayi ta kalleshi babu wani mamaki asaman fuskanta tare da kauda kai ta maida ga littafin hannunta, "congrats" yace a natse, ɗagokai tayi ta sakin mai murmushi tare da faɗin "thank you" "ba komai, nayi farin ciki sosai daUnclene ya ci, na san jama'an ƙasa za su yi farin ciki da kasantuwar shi shugaba a gare su, sannanzasuji daɗin mulkin shi, dan ina da tabbacin ze ɗaukesu kamar yanda ya ɗauke ki" ya idda magananidon shi na yawo a saman fuskanta, nagartaccen murmushi ta saki cike da jin daɗi tare dafaɗin"ina da yaƙini akan hakan" jinjina kai yayi tare da faɗin "zamu iya cin abinci tare?" Girgiza kai tayi
tare da faɗin "ina azumi" "wow! A wannan ranar?" Yace da mamaki, murmushi ta saki taredafaɗin "yeah" "okay to ki zauna anan kar ki ce zaki fita cikin ranar nan" murmushi ta saki taredafaɗin "okay sir" murmushi ya saki tare da juyawa ya fice....
"Na taya murna" Annur yace cike da farin ciki, tare da zube mata ido "thanks" Yasmin tacetareda sakin mai murmushi, "Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da ya ɗaura mai" "amen YayanainaAmir?" "Yana wajen Momyn shi ba ku haɗu ba ne?" "Banganshi a wajenta ba" tace a natse, "inaganin yana wajen takwaran shi, muje ki ganshi" taye tare da kafe ta da ido, "ayye, no na damuwabarshi ya mori lokacin shi" tace a natse ba tare da ta kalleshi ba "Allah yasa yanda Uncle yaci
Daddy ma ya ci" murmushi ta saki tare da jinjina kai tare da faɗin "amen, in dai shine alherinjahar mu" murmushi ya saki tare da faɗin "in sha Allah shine ƙanwata, Daddy yana da zuciyantemako, muna fata wannan zuciyan na shi ta mai jagorancin wajen kyautata mana" "amen" taceanatse tare da juyawa ga Farisat dake ta zuba surutu da wata me suna Batula, "to Anty sututuzo
mu tafi kar Yaya Balarabe ya tafi ya bar mu" "jeki ya ganki gani nan" tace hankalinta akanmaganar da suke... Murmushi Annur ya saki tare da faɗin "to muje se ta kai aya tukun, dole lokaci zuwa lokaci mudinga zuwa gaida brother Salman dan ba ƙaramin aiki zamu haɗa shi da shi ba" murmushi tasaki
tare da fara takawa a natse, "har yanzu ƙoƙon barar mu a miƙe yake ƙanwata, a dube mubadanmu ba, ba dan halin mu ba a saka mana ko ba yawa" Annur yace cike da magiya da fata taredajaya tsaya idon shi akan ta, murmushin gefen baki ta saki tare da faɗin "Yayana ba na sonwannanmaganan ta dinga shiga tsakanin mu, please ka bar shi ya wuce kamar yanda ya wuce a wajena, ba na da wani kataɓus a ta nan" tayi maganan fuska kadaran kadahan, "ƙanwata anya yandanaɗauke ki haka ki ka ɗauke ni kuwa?" Yace tare da zube mata ido, jinjina kai tayi tare da faɗin"fiyeda zaton duk me zato" girgiza kai yayi tare da faɗin "a'a ƙanwata, ba na ganin hakan, inda kinɗauke ni yanda ki ke faɗa da kin fahimci ba zan iya tallata miki abinda ze cutar da ko ƙumbanki
ba, ƙanwata Shureim na matsanancin sonki, ze kula da ke, ze tsaya miki a duk sanda ki kebuƙata, ze kasance a bayanki a ko wani lokaci, meyasa ba zaki fahimci abinda nake hango miki ba ne?Meyasa ba zaki buɗe zuciyanki yanda yakamata ki gane me take so ba ne? Ki na da buƙatanwanda ze kula miki da ita, kuma ba wanda ze iya wannan se Shureim, bance miki ba wani namiji
da ze iya ba, se dai Shureim na daga cikin waƴan da za su iya, ki je ki yi tunani yanda yakamata, kafiya da taurin kai ba mafitan da ze baki" yana kai nan ya juya ya wuce ya bar ta tsaye a wajen... Bin shi da ido tayi cike da zallan mamakin yanda ya wuce ya barta, a tsayin rayuwar da sukayi dashi hakan be taɓa faruwa a tsakanin su ba, "mamakin me ki ke? Fiye da hakan ma ze iya faruwa" Farisat tace tare da jan hannunta suka nufi mota.... Wasa farin girki... Comments fans🙏🥰
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Thirty one
"Mtswww oh Allah duk sun bi sun dame mu da abu guda" Yasmin dake zaune riƙe da wayatanadaƙila tace tare da ɗago kai cike da takaici, "ke da wa?" Habiba dake zaune a two seater's Farisatkwance a saman cinyoyinta tana sosa mata kai tace tare da ɗago kai ta kalleta...
"Su Yaya Annur mana, tunda mutumin nan ya ci zaɓe mu kuma muka shiga uku ba ranar dabazasu turo video's ɗin shi da hotuna ba" tace kaman za ta saki kuka, "wa kenan!" Habiba tacedamamaki idonta a saman fuskanta, "professor Sharifudden Muhammad mana" tace tare dakaudakai, "au shi yaci zaɓen!" Tace da mamaki tare da kama haɓa, "au ba ki sani ba dama!" Balarabedashigowan shi kenan ya tadda zancen yace tare da zama kusa da Yasmin...
"Wallahi ban sani ba, kai ni ko zaɓen ban fita ba, murnan na Uncle ɗin su ya mantar da ni akwai
zaɓen da ya rage" dariya ya saki tare da faɗin "aiko ya buge maza ya fice da nasara, fari mefarinaniya ba, baya goya marayu da masu uba, me gaskiya uban marasa gaskiya, ka ga dokinƙarfemebugunka shine da jinya" ya idda kirarin cike da farin ciki, "kai ma sha Allah bana dai mu shar, daga governor har president Allah ya ba mu nagari" Habiba tace cike da farin ciki, "a'a AntyHabiba ki jira dai tukun, kar daga ganin sarkin fawa ki yi tunanin miyanki za tayi zaƙi" Yasmintace idonta akanta "bar wan nan maganan Yasmin ai juma'ar da za tayi kyawu tun daga larabaake ganeta, shi kuwa talatarshi ma tayi kyawu" Habiba tace cike da tabbaci dariya suka saki tareda kallon ta...
"Wallahi ku bar dariya gaskiya ne, mutumin nan haka siddin matsalakan babu siɗiɗi babusaɗaɗa, ba dangi Iya babu na Baba ya kyautata bare kuma yanzu da Allah ya ɗaurashi akaragandayazama uba ga kowa, ai muna mai fatan nasara tare da fatan cika alƙawura" "amen Anty Habiba" Farisat tace tare da miƙewa ta maida hulanta saman kai, "me kuma yau aka saka a groupɗinnaji
kina ta mita?" Balarabe yace tare da kallon Yasmin, "godiya ya ma jama'amAminan juna, shinefabrother Zubair ya turo tare da umurtan kowa ya yi statut" Farisat tace idonta akan shi, "ahtoai
dai-dai ne" yace tare da zaro wayanshi, "ke yanzu ki ka gani ai mu da zafi-zafi mu ka doki ƙarfenmu ba mu bari ya huce ba, dan ya huce ba ze bugu yanda ake so ba" Farisat ta kuma cewa idonta
akan Yamsin, "ai na ga kin yi statut har da turowa cikin group" Yasmin tace cike da takaici, "tomeza ta tsaya jira? Ni ma ga na wa nan tafe, ke ma hanzarta yi, ai bawan Allahn nan ya can-canci
fiye da haka" Balarabe yace tare da kallon ta...
"Taɓ ɗin ai kun wakilce ni" tace tare da kauda kai, "kaman Yaya dalla kar ki kawo mana fi'ili jeki
yi" Balarabe yace tare da banka mata harara, "wallahi Yaya Balarabe ba zan iya ba" tace kamanza ta saka ihu, "me ki ke nufi kenan!" Farisat tace fuska a ɗaure, sadda kai tayi ganin yandatakebin ta da ido cike da ɓacin rai, "ba dake nake ba!" Tace a tsawace, "da ni ne" tace murya ƙasa- ƙasa, "ina lura da ko murna ba ki taya su ba ranar da suka turo labarin ya ci zaɓe, sannanyaubawan Allah ya nuna farin cikin shi gare mu ba tare da kallon matsayinmu ba, kowa na farinciki
yana statut ke kin tsaya ki na wawanci, to bari kiji dole ki mutumta duk wata doka ta wannangida, dan yace ya na sonki ba shine ze baki daman wulaƙanta shi ko wulaƙanta iyayen shi ba, kuma wallahi ki gaggauta yin statut ɗin nan yanzu sannan ki je ki taya shi murna kar in sassaɓamiki, banda rashin hankali ina ce nan ya yi ta taya mu murna ranar da aka tabbatar da Uncleyaci
zaɓe, amma ke dake baki da hankali kin zauna ki na jiran a ce miki ki yi" tayi maganan zuciyaɓace tare da miƙewa ta bar wajen... Murmushi Habiba ta saki ganin Yasmin ta kasa ɗago kai tare da miƙewa ta koma kusa da ita, tanataɓa ta ta fashe da kuka tare da faɗin "ni bana son shi" "ka da Allah ya baki ikon san shi, nanbaso ko ƙi ke aiki ba, matsayinki ta membern gida aka baki umurnin bin doka da oder ba ruwanmuda wani rashin son shi da ki ke" Balarabe yace na shi zuciyan a wuya, "yi shirun ki, ban da abinki
Yasmin me ya haɗa taya murna da so, tunda kin ce bakya son shi ai ba me dolanta miki, kedai ki
bi umurnin gida, "ni ba zan iya mai magana ba" tace tare da goge hawaye, "ki tafi cikin groupki
ɗau abinda Annur ya turo ki yi fatan alheri hakan kaɗai ya wadatar, ko ƙiyayya zamu yi muyi danAllah, kar muyi dan san ran mu" Balarabe yace tare da tashi ya bar wajen, "daina kuka, kingagashi kin harzuƙa Farisat, duk da a tsukinnan na ga abu kaɗan ke harzuƙata" Habiba tacecikedakulawa, murmushi ta saki tare da faɗin "ba ta son barin gida ne"....
Dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "wannan kuwa dolenta, dan ma Allah ya dubeta yasaakusa da gida zata zauna, inda a wani anguwar yayi gini ai da abun se ya fi taɓa ta, amma gatagagida ko ihu me ƙarfi mu kayi za ta iya jin mu" murmushi ta saki tare da bin ta da ido, "mazaamshi
wayan ki yi abinda ya kamata" tace tare da miƙa mata wayan, amsa tayi a sanyaye... Danna horn yake da ƙarfi tare da tunkarar su gadan-gadan, juyawa suka yi dan ganin ko sunakan hanya ne, ganin ba sa kan hanya ya sa Abdallah jan tsaki tare da kallon na kusa dashi, yanashirin magana Sudais ya ƙariso tare da yunƙurin hawa kan su da mota, da sauri suka matsatareda watsa mai ido cike da ɓacin rai, ɓalle murfin motan yayi ya sakko dare da sakin dariya mesauti, tsaki Abdalla ya ja me sauti tare da faɗin "wannan wani irin rashin hankali ne Sudais?Indaka taka mu fa?" "Yi haƙuri iyalin zuuu kai sam ba ka san wasa ba" "ina ka taɓa ganin anyi wasadarai?" Yace a harzuƙe, "oh sorry tun daga nesa na hangoku na ce bari mu buga wasa da waƴannanmutanen" ya idda maganan tare da ba ma na kusa da Abdallah hannu, ba shi na shi yayi taredafaɗin "kwana biyu ka ɓoye abun ka"...
"Wallahi ina nan ba ku neme ni ba ne" "kai ma ai ba neman jama'a kake ba" yace tare da zarehannun shi, miƙawa Abdallah yayi tare da faɗin "mutumin kana sha'aninka fa irin wannanajiyetunbi haka" "kwanciyar hankali na samu, kasan ba abinda be sawa" Abdallah yace cike da
takaicin shi dake nuƙurƙusanshi "wannan gaskiya ne mutumina, Allah ya ba mu i na ka, yainazaki haka? ku zo in sauke ku a gida dan gida nayi" "ah-ah tsaye kagan mu fa ba tafiya mukeba, akwai wajen wanda muka zo ne" "oh to shikenan, maida wuƙan se kun shigo arean" yace taredayunƙurin wuce wa...
"Oh Sudais dama ina son taya ka murna, a she Farisat kuma aure ya gabato, ɗazu ta tura muncard Allah ya sanya alheri" wanda ke tsaye kusa da Abdallah yace idon shi akan fuskan Sudaisdamamakin shi ta kasa ɓoyuwa, "ba dai baka san za tayi aure ba!" Yace tare da kama haɓa, "tundaka ga haka ai be sanin ba ne, Allah dai ya nuna mana, in sha Allah zamu je ɗaurin aure" Abdallahyace tare da juya kai daga ɓangaren da Sudais ke tsaye, juyawa yayi ya nufi motan shi da mamaki, "Farisat ce za tayi aure?" Yace cike da mamaki, "to meyasa Momy ba ta faɗa mun ba?" Ya ƙarajefawa kan shi wani tambayan, ganin ba amsa ze samu ba ya sa shi ajiye batun a gefe ya jamotanya nufi gida....
"Dan Allah dubi yanda duk ya soma lalacewa" murmushi Abdallah ya saki tare da faɗin "habaNafi'u baka kalleshi da kyau ba ne halan? Ai ba somawa yayi ba lalacewa yayi, kai da hakaSudaisyake? Dubi yanda yayi baƙi yayi rama, yana magana kamar wani mace" Abdallah yace cikedatakaici, "Allah ya ganar da shi gaskiya muje" Nafi'u yace cike da jimanta lamarin, "amen, ai Allahya temaki yarinyar nan da ya fidda mata son shi a zuciya da wuri" Abdallah yace tare da faratakawa a natse suka ɗau hanyar gida....
Zaune suke cike da babban parlor ana hira ana dararraku, kallo ɗaya zaka musu ka fahimci
shaƙuwa da farin ciki ya musu ƙawanya, murmushi Shureim dake riƙe da waya a hannu yasaki
tare da ɗago kai ya dube su, "what!" Matashiyar dattijuwan dake zaune kusa da kamilallandattijo tace tare da kallon shi, gaba ɗaya zuba mai ido suka yi dan jin dalilin da ya saka shi sakinfafaɗeɗen murmushi haka, murmushi ya kuma saki tare da gyara zama a hankali, "muna tayamurna Allah ya ba shi wuyan ɗauka nauyin da ya ɗaura mishi, yayi riƙo da hannunshi wajenkyautatawa al'ummar shi, ya hanashi kamuwa da ƙwaɗayin mulki, ya dafa mishi wajen cikaalƙawuran da ya ɗauka, Allah ya jiɓanci lamarin shi na zahiri da na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 42 Chapter of 109