miƙa mata ita tayi tare da faɗin "ido biyu na taddata, taƙi
yarda da ko Anty Hasinat yau" "oh my farin ciki na, rayuwata, sanyin idaniyata waya taɓa ki
Mommy ne ko" ta idda maganan tare da kwantar da kanta a saman ƙirjinta, shafa samangoshinta tayi tare da faɗin "kanta be dai yi ciwo ba ko? Da yawa tayi kukan? Meyasa tundatafarka ba'a kawo ta ba?" "Ni kuma ina zan sani, shiga nayi na taddata tana kukan" Nafisat taceagajiye ,"oh Allah" tace tare da ɗagota ta share mata busassun hawayen da suke shinfiɗe asamankumatun ta....
Sakin ido da baki kawai suka yi suna bin ta da ido cike da zallan mamaki, "da Mommy tasanzaki
farka da wuri ki nemeta haka da ba ta barki a can ba" tace cike da rashin jin daɗi, "oh Farisat
bakya kunyar ƴar fari!" Laɗifa tace tare da kama haɓa, "wacece ƴar farin? Ai ba ita ba ce ɗiyar
fari na, se da nayi misscarage kafin ita ko kin manta ne, kinga ai ta biyu ce" tace tare da kallonta, "duk da haka dai ita ki ka fara gani yakamata ki dinga alkunya, ki bar su Yasmin su nuna ƙaunan""a'a ai mu nuna gaba ɗaya, a 200 da wani abu muke fa ba'a 100 ba, ko Anty ba ta cuceni dawani
kunya ba bare ni kuma in cuci tawa, ba wannan maganan tace cike da tabbaci....
"Yau na ga abu" tace tare da kama haɓa, "kinga kaɗan" Insu da ta fito cikin shiga kalar na sudayayi masifar amsanta tace tare da sakin murmushi, "wow baby Insu irin wannan burgewa haka!" Yasmin tace tare da sakin mata murmushi, "ya ku ka ga babyn!" Tace tare da ware hannu, "tafi
haɗuwa ɗaukan wanka" suka ce baki a haɗe, farr da ido tayi ta zube musu tare da faɗin "kucenafito a amaryata" "ba ƙarya" suka ce tare da sakin murmushi, murmushi ta saki tare da ƙarisawakusa da su...
"A gaskiya Farisat ki rage, wallahi little ko a gaban Daddyn shi bana iya mai wani abun" tacetareda kallon ta, "kina ɓata bakin ki ne sister Laɗifa, to ita da Daddyn yarinyar duk zamu ne tatiddamuje mu, ba me faɗawa wani gaskiya" Insu tace tare da kallon ta, "lallai waƴan nan sunmato" tace tare da sakin murmushi, "murus kuwa" Insu tace tare da gyara zaman jakan da ta saɓa, "seku yi" Farisat tace cike da takaici, "yanzu Nafin Anty Gude ta tambayeni ke na ce kina ɗakinki" Nafisat tace tare da kallon Yasmin, "sun zo ne!" Tace da mamaki, "Eh har da ita ma da YayaSudais" tace a natse, "ah lallai Yasmin ke me sa'ace" Farisat tace tare da kama baki, "ku jama'aku
tsaya" wacce ke kusa da Laɗifa tace tare da kallon su.... Zuba mata ido suka yi cike da mamaki, "wai ina agreement ɗin da Farisat tace mana sunyi ne!" Tace tare da kama haɓa, "gayi nan a hannunta ga wani nan a ciki" Insu tace hankali kwance" kwashewa da dariya suka yi tare da bin Farisat da ta ɗaure fuska da ido, "eh mana" Insu taceasukunance, "wallahi zan ɓata miki rai Insu" tace murya a ɓace, "to Allah ya baki haƙuri Mommy" tace tare da sakin murmushi, "shiyasa nace ban da cika baki" Laɗifa tace tare da kallon ta, murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "aikin agreement ta gani, "kar ki furta komai sister
Yasmin" wacce ke zaune kusa da ita tace tare da kallon ta, "a'a ita ba tayi agreement ba, kodukshekara zata haihu ba damuwa" Insu tace tare da sakin murmushi...
"Ƙyalesu daughter fita zabgansu" Momcy tace tare da kallon ta, "ai ban san ma suna yi ba Momcyna" tace cike da takaici, "tana shan nono har yanzu ne?" Tace da kulawa, murmushi ta saki tareda girgiza kai "ba ta sha" tace a natse idonta akan kyakykyawan fuska Mairah, "meyasa ki kayayeta! Ai da kin barta ta cigaba da sha in ta cika watannin yayen se ki yayeta, amma yanzuzatayi ta fama da laulayin ciwuka kala-kala ne, nono garkuwane a jikin yara, in an ciresu ba taredasun isa yaye ba se ki ga suna ta ciwuka suna lallacewa, saboda sun rasa garkuwan nan, mutanenmu da ba su san kan abin ba se ki ji suna faɗin "sun sha ciki" wacce ke zaune tace cike da
damuwa, "wallahi bani na yayeta ba Doctor Muwaddah da kanta ta yaye kanta, kusan watashidada ya wuce, kin san tayi baƙon dauro, to tun daga lokacin ta daina amsa, lokacin ma bandakomai" "oh to shikenan ai, tunda da kanta ta yaye kanta, lallai Mairah, kin hango zuwanɗanƘanine ki ka ba shi waje ya wataya ko?" Ta idda maganan tare da shafo kanta, murmushi Farisatta saki tare da faɗin "aikuwa" dariya Yasmin da su Laɗifa suka saki...
"Meye!" Tace fuska a ɗaure, "wallahi mamaki ki ke ban" Laɗifa tace tare da kama haɓa, tsaki tajatare da faɗin "ai se ki yi ta yi" "ta fa saba, ku ma daina mamaki" Insu tace tare da buɗe jakandakekafaɗanta ta ciro wayanta dake neman agaji, ganin me kira yasata saurin ɗagawa ta kara akunni, "an ɗaura" yace da ƙarfi, tsalle ta daka tare da zaro wayan ta saka a speaker hannu na ɓari tace"me ka ce!" "An ɗaura" ya kuma cewa da ƙarfi tare da sakin dariya....
Rawa ta fara takawa tana juyi tare da sakin murmushi, lumshe ido Yasmin tayi ƙirjinta nabugawa, "ta zama ta zama ta zama" tace da ƙarfi, "ta zama" Hisham yace da ƙarfi daga can, "tazama ɗakko riga" "ta zama" "ta zama ɗakko wando" "ta zama" ta zama ɗakko hula" "ta zama" "tazama bani ruwan nan" "ta zama" "ta zama bani abinci" "ta zama" haka suka dinga mata
shaƙiyanci ita kuma se murmushi take saki tare da goge hawaye, "wayyo daɗi baby ta zamamallakin uncle Shureim yau Alhamdulillah" tace tare da kashe kiran ta wuce gefenta da sauri tazauna....
"Oh baby an girma" tace tare da sakin dariya, duka ta kai mata tare da sakin murmushi ta gogehawaye, "oh zata naƙasani in shiga ɗari ba ɗaya, ta samu ta shiga da komanta ni in shiga datangarɗa" "Allah ya shiryeki Insu" Momcy tace tare da sakin murmushi, "wallahi Momcy dagaskiyata" tace tare da ɗagowa, "yanzu fa ko cewa yayi Yasmin zo mu tafi, hakanan zaki tashi ki
bi shi fa Allah sarki" Insu tace tare da kama haɓa, "ai ke ma zaki iya ce mata" Farisat tace taredamiƙewa ta saɓa Mairah da ta fara barci, "ko in ɗakko miki zanin goyo ne?" Insu tace cike dashaƙiyanci, "ban nema ba" tace tare da ficewa, "Allah ya shiryeki Insu" Laɗifa tace tare da sakinmurmushi, "so take ta ƙure haƙurinta" Momcy tace tare da sakin murmurshi, "in ba haka akewadaughtern nan na ki ba Momcy ba zata gane tana wani abun ba" tace tare da miƙewa....
"Ina Uncle?" Tace tare da kallon Nafisat dake tsaye tana sakin murmushi, "ya tafi ɗaurinaure"
"oh a she fa sune masu bada auren, in ya dawo ki ce ya zo ina nemanshi faka-faka" "to" tacetareda juyawa ta ficewa, juyawa da dubanta kan su tayi tare da faɗin "me ku ke da buƙata mutanenkirki?" "Ba komai" suka ce bakuna a haɗe, "ku dai ku faɗa banda fulaku" tace idonta akansu, dariya suka saki cike da yaba karamcinta, "to ku mu fita parlor musha iska, a ɗan tattaɓa
hotunan nan na zamani ma daga nan" tace tare da kama hannun Yasmin suka nufi ƙofa....
Da sallama suka shiga ɗakin Babiya dake maƙil da mutane, amsawa Babiya tayi idonta akanGude tare da faɗin "Usaina ke-ke ta tambayan Gude tun ɗazu ga ta ta iso" murmushi dattijuwanda ta kira da Usaina tayi tare da faɗin "haba uban amarya se yanzu ya iso, mu da ke matsayinkakannin har mun rigaki isowa" murmushin yaƙe Gude ta saki tare da ƙarisawa gefenta taduƙata ɗaga mata gaisuwa, "wallahi Alhamdulillah sha'ani kuma ya taso?" "Eh wallahi" to Allahyazaunar da su lafiya, yanda duk ku ke zaune ɗakunan ku cikin rufin asiri Allah ya zaunar daitamalafiya kar mu ji kar mu gani" "amen" suka ce ita da sauran jama'an dake ɗakin....
Juyawa ga Babiya tayi tare da faɗin "kin tashi lafiya Hajiya?" "Alhamdulillah ya Sudais da jiki?"
"Ya ji sauƙi se dai yanzu da zamu fito na ga yana ɗingisa ƙafa" "to! Aiko ku dangana ga masanadawuri" tace cike da ɗan firgici, "eh in sha Allah zuwa gobe ko jibi in dai be daina ba zamu koma" "tohakan yayi, wannan ciwon ƙafa dai Allah ya kawo mai iyakar shi, a ce abu yaƙi ci yaƙi cinyewa, Ali
dai ya rabu da na shi da ƙyar, shima in sha Allah ze rabu da shi, jarabawa ne Allah ya ba shi ikoncinyewa" "amen" Habiba tace tare da kallon Gude a natse tace "bari in leƙa wajen aikin canmahalarta ɗaurin aure gab suke da dawowa, in kin kammala ki same ni a baya" jinjina matakai
tayi ta juya ta fice...
Shigowa parlorn Nafisat tayi da friend's ɗinta, da mamaki Insu dake duƙe tana magana daLailahta kalleta tare da faɗin "daga ina ki ke?" "Na je shigo da friend's ɗina ne" ta yi maganan a ladabcetare da nuna su, "auh sun iso?" Tace tare da miƙewa, jinjina kai tayi tare da sakin murmushi, "sassannunku da zuwa, sannun ku, ƙariso da su su gaida su Anty Lailah" tace tare da nunamusuinda Lailah da su Khadijatu ke zaune, ba musu ta musu iso har wajen, suna gama gaidasutacekai
su side ɗin Yaya har yanzu Uncle be dawo ba ne?" "Sun dawo yanzu na ganshi a waje na mai
magana" "okay je ki kai su su samu su huta", sannun ku da zuwa" tace cike da kulawa, wucewada su tayi cike da jin daɗin kulan da ta nuna musu....
Juyowa tayi ta kalli Shafa'atu tare da faɗin "dan Allah Shafa'atu jeki kai musu ruwa da lemu, ki
ɗauki me sauƙin sanyine" jinjina mata kai tayi ta miƙe ta wuce gefen da deep prezern gidanyake, haɗa duk wani abinda yakamata tayi ta wuce kai musu, juyawa ga Munari dake kwance saman
three seater's tayi tare da faɗin "Anty Munari a temaka musu da abun taɓawa, "akwai sauranfried rice ɗin nan kuwa?" "Akwai" tace tare da miƙewa, a saka musu kaɗan kar a cika, a haɗamusu da cowslow, a buɗe pride meat ɗin nan a zuba musu isashshe a kai musu dan Allahyanzu"
"okay" tace tare da miƙewa ta fice, juyawa tayi da niyya ficewa Farisat ta shigo goye da Mairah, "baƙin Nafisat sun iso ki je side ɗin Yaya ku gaisa" tace da kulawa, "okay an kai musu abinci?" "Ehyanzu za'a kai" tace tare da yunƙurin wuce wa, har ta kai ƙofa ta juyo tare da faɗin "yawwa" saurin katse mata hanzari Lailah tayi da faɗin....
"Wai Farisat bance kar in ƙara ganin kin goya yarinyar nan ba ne! Meyasa bakya tausayinkanki
ne? Duk yawan yaran dake gidan nan ba zaki iya ba ɗaya ya goyata ba se ke" Marairaice fuskatayi tare da faɗin "wallahi Anty Lailah ba zata yarda su ɗauketa ba" "to waya koya mata hakan?Aike ce ki ka koya mata, ina Nafisat ta zo ta goyata tunda tana yarda da ita" Lailah tace rai ɓace, "sakkota" tace cike da bada umurni, sakkota tayi ba din ta so ba, "Anty Lailah Nafisat tanataredafriend's ɗinta, kuma wallahi ta goyata ba zata bari ta samu natsuwa da su ba, ba'a goyata azaunase dai a tsaya" Insu tace cike da damuwa, "ai abinda ku ka shuka ne ku ke girba" tace taredabamka mata harara, "akai musu ne?" Munari da ta shigo tace tare da kallon Insu, "eh Anty
Munari" tace cike da jin daɗi.....
"Ki kira mun Nafisat in kin shiga Munari" Lailah tace cike da bada umurni, amsawa tayi tashige, shiganta ba daɗewa Nafisat ta fito a natse....
"Zo ki amsheta ki goyata" Lailah tace tare da kallon ta, ba musu ta ƙariso tare da miƙa matahannu, maƙye kafaɗa tayi tare da ɓata fuska, "jeki Ummi" Farisat tace tare da san miƙata kukatatsala tare da ƙanƙameta, murmushi Nafisat ta saki tare da bin ta da ido, ɗago kai Farisat tayi tareda faɗin "taƙi" tayi maganan kaman zata tsala ihu, dariya jama'an parlor suka saki cike damamaki, "ba wani ƙi ki bata ita ki samu waje ki natsu, ke ko tausayin kan ki bakya yi" "to yazanmata Anty Lailah!" Tace ido na tara ruwan hawaye, "a wannan hali Insu kaɗai zata amshetatanatsu, amma kuka zata yi ta yi in Nafisat ta amsheta" Habiba tace cike da tabbaci, kwaɓe fuskaInsu tayi tare da kallon Habiba dake sakin mata murmushi...
Juyawa tayi ta amsa sallaman Sahabee da ya shigo tare da faɗin "Uncle tun ɗazu fa nake zamanjiranka" murmushi ya saki tare da faɗin "gani Ammi ba mu daɗe da dawowa ba ne" "yawwaaikenka zanyi muje ka ji yanda saƙon ze kaya" tace tare da riƙo hannun shi, murmushi ya saki taredajuyawa, "Insu amshi yarinyar nan" Lailah tace a dake....
Juyowa tayi tare da ɓata fuska cike da rashin jin daɗin tace "Anty Lailah" "shiru ki yi abindanace" ta kuma cewa a dake, miƙa hannu tayi tare da faɗin "kawota" ƙarisawa kusa da ita Farisat tayi
ta miƙa mata ita, fashewa da kuka Mairah tayi ta damƙe hannun rigar Farisat da iya ƙarfinta, "ai
gunda kar ki zo dan zaki gaya ma jikin ki ne" tace a hankali, zare ido Farisat tayi tare da ɗagowatace "Anty Lailah wai zata gayawa jikinta ne" "in ta gadama ta kasheta ƙarshen ta faɗawajikintamiƙa mata" "amsheta" tace ba din ta so ba, janyeta tayi da ƙarfi zata buɗe baki da niyyankukatace "cif shanye shi" tayi maganan tare da zaro mata ido, gum da baki tayi tare da kallonFarisat, "ki aika ma friend's ɗin Nafisat snacks please" tace tare da saɓa ta a kafaɗa....
"Ammi friend's ɗin mu sun zo fa, suna waje" Sahabee yace tare da kallon Insu, "shine kayi shiru?Ina sister Hasinat?" Tace tare da ware ido a parlorn, "ga wata" tace tare da miƙewa, "pleasekujeda Uncle abokanan shi sun zo masaukin su na parlorn sama na gidan Ummi, ki duba in akwai
abinda ba'a kai ba se ki faɗa min" jinjina kai tayi tare da faɗin "muje Uncle" "to friend's ɗinSa'eedda Umar sun iso suma" "okay su na su masaukin a nan yake, in kun fita kace su shigo da suciki, sister Hasinat ki ce ma Antyn Rahma a fiddo da gift's ɗin nan a fara raba musu tunda sunawajen"tace tare da sakin musu murmushi, murmushi suka sakin mata cike da jin daɗi suka fice...
Suna fita Hisham ya doko sallama, murmushi ta saki tare da amsawa cike da sakewa, "inasisterin-law!" Yace cike da zumuɗi, "gata nan" Laɗifa tace tare da nuna ta fuska ɗauke da murmushi, sallama wacce ta tsaya cire takalmi tayi ta shigo a natse zare ido Insu tayi cike da mamaki tareda faɗin "rigiji gabji cashi da tirƙashi, wa ido na ke gani kaman Nachma baby!" harara me haɗedamurmushi Nachma ta sakin mata tare da kauda kai, "wow! Irin wannan bazata haka! Boyfriendse na yi maka rashin kirki" tace fuska yalwace da murmushi, "i want to surprise you ne fa
girlfriend" yace tare da wuce wa inda Yasmin ke zaune ya zauna a gefenta tare da tankwasheƙafa....
"Zo ki rungume ni mana" tace tare da sakin mata murmushi, "banyi niyya ba" tace tare da sakinmurmushi, "zo ki zauna Nachma sannu da hanya" Farisat tace da kulawa tare da nuna matawajen zama, murmushi ta saki tare da isa wajen ta zauna, "wato ni ki ka watsawa ƙasa a idoko!" Tace tare da kama haɓa, jama'a ku juyo nan ga best friend ɗina nan ta zo taya mu murna" tacetare da sakin murmushi, nan a ka shiga mata barka da zuwa, tana amsawa cike da farincikintarban da ta samu daga gare su, "ga amarya Yasmin" tace tare nuna mata Yasmin dake tasakinmurmushi, murmushi ta sakin mata cike da farin cikin ganinta, "ma sha Allah ta fiki kyau" tacetare da banka mata harara, "na sani" tace tare da sakin murmushi...
"Ga Farisat baby" tace tare da nuna mata Farisat, murmushi ta saki tare da faɗin MommynMairah ko ai na santa a hoto" da mamaki tace waya tura miki!" Murmushi ta saki tare da faɗin"Hisham, ba ranar da zamu yi waya be kawo zancen baby Mairah da Mommynta ba" tayi
maganan fuska ɗauke da murmushi, murmushi Farisat ta saki tare da faɗin "ga abin arziƙi ganatsiya" murmushi ya saki tare da kauda kai, "yanzu zaka ƙara samun fada" Insu tace tare dasakinmurmushi, "ina baby Mairah?" Tace tare da kallon Farisat...
"Gata nan" tace tare da nuna kafaɗan Insu, "wow ita ce nan?" Tace tare da miƙa ma Insuhannu, zarota tayi ta miƙa ta kuka ta tsaga tare da rumtse ido, "oh Allah ƙiwiya take?" Tace tare dajanyehannu da sauri, "ai wannan da ki ka gani se dai kallo daga nesa" Hisham yace tare da sakinmurmushi.... Girgizata ta fara tare da faɗin "ni ma dan na fi ƙarfin ta ne" "goyata mana" Salwa da ta shigotace
tare da kallon ta, "goyo kuma Anty Salwa!" Hisham yace tare da miƙewa cike da mamaki, "ehmana za tafi yin shiru" "ba wannan maganan" Insu tace tare da wuce wa gefen fridge, treytazarata saka ruwa da lemu ta kawo gaban Nachma ta ajiye, "Mommy a haɗa mata tarba mana" tacetare da kallon Farisat, miƙewa tayi a natse ta wuce haɗo mata abinci, "ku! na fa manta, angwayena waje suna neman iso dan su gaida iyayen amarya" Hisham yace tare da kallon Insu, "tosushigo ai gamu" tace cike da manyance, murmushi Nachma ta saki tare da kauda kai, ba abindatacanza a yanayinta, ƙarisawa kusa da ita tayi ta zauna tare da faɗin "ya Insoul?" "Meye naki natambaya ke da ki ka tafi ba ko sallama, gwara shi wannan ya mana sallama" tace tare da nunaHisham, murmushi ya saki tare da faɗin "in nayi kaman ta yi ne" "yawwa faɗa mata dai boyfriend"tace tare da sakin murmushi... Shigowa Umar da Sa'eed da zugan abokanansu suka yi, miƙewa tayi da sauri cike da farinciki tafara tarban su, kallon Sa'eed tayi tare da faɗin "ku kai su garden" jinjina mata kai suka yi cikedafahimta suka nufi ƙofa da ze sadasu da can, "sister's dan Allah bari in ci arziƙi" tace tare dakallonHalima da Nafi, miƙewa suka yi fuskoki cike da murmushi, "yawwa dan Allah ku ba abokananƙannin kun nan kulawa yanda yakamata, akwai ruwa da lemu a fridge, ku je wajen Anty Suwaibazata nuna muku abincika ku zaɓi wanda ku ka ga ya dace" jinjina mata kai suka yi cike da fahimtasuka fice, sauke numfashi tayi ta koma ta zauna.... Murmushi Nachma ta saki tare da faɗin "sannu" murmushi ta saki tare da faɗin "ina jinki" "Insoul
na nan lafiya, komai yana tafiya yanda yakamata, cigaba na ta zuwa mana a ko wani lokaci, naƙasu ɗaya ke gareta ba ki ba Hisham, zaƙwaƙwuran ɗalibai wanda take ji da su" murmushi tasaki
tare da faɗin "na san za tayi waƴanda suka fi mu ma" "gaskiya har yanzu bangani ba, watakiladai nan gaba" tace tare da ma Farisat da ta ajiye trey a gabanta godiya, "sannu me ciki" Hishamyace tare da guntse baki, "wai dama haka ka ke Hisham!" Laɗifa tace da mamaki, "ai yafi haka, shi da ita Hassan ne da Husaina, abinda ɗaya yayi ɗayan in ya zo mai-mai ze yi" Farisat tacecikeda takaici, "to ina lefi ya kira ki da baiwarki" Insu tace tare da kama haɓa, "Allah ya nuna munlokacin na ki, za ki fahimci baki da wayau" tace tare da komawa ta zauna....
Dariya suka saki cike da shaƙiyanci, "bismillah ci abinci" Insu tace tare da ɗaukan plate, "kaɗankar ki cika" tace tare da kallonta, harara ta dalla mata tare da faɗin "ko ba kaɗan ba" "kar dai ki
zageni" tace tare da sakin murmushi, serving ɗinta tayi ta miƙa mata ba musu ta amsa ta faraci anatse, "ni ko ya labarin su Minakshi?" Insu tace tare da sakin murmushi tare da buɗe lemutatsiyaya mata, "suna nan a class ɗin da ku ka barsu, suna faɗi a wannan shekaran shikenansunbar Insoul har abada" tace tare da kallon su, "wayyo Allah, su kuma ya rayuwarsu da haka!" tacecike da rashin jin daɗi, "to ya za su yi, haka su kuma na su ƙaddaran ya zo" tace tare da sakinmurmushi, "to ogan fa?" Tace a hankali, "gyace a hankali mana tunda kin kusa haukata ɗanmutane, wallahi bawan Allahn nan ya jigata, shekara biyu be dawo school ba se wannanshekaran, se dai komai normal ya maida hankali sosai yanzu" kwaɓe fuska tayi tare da faɗin"wayyo abin ba daɗi" "kyace haka mana" tace tare da sakin murmushi, "to ya za tayi in ba tacehaka ba?, Allah be ƙaddara komai ba" Hisham yace tare da kallon ta, "ai dama kai duk abindatace eh ne" tace tare da hararan shi, dariya ya saki tare da kauda kai....
Shigowa Sadam yayi da sauri tare da faɗin "baƙi za su shigo kuɗan ragu" "wow! Haka ka haɗebanganka kafin ka tafi ba" Insu tace tare da miƙewa ta isa inda yake, murmushi ya saki tare dafaɗin"ba yanzu ba Insu, bari mu sallami baƙi tukun" "haba waƴan nan ƴan gida ne ai" tace taredasakin murmushi, sallama suka yi suka shigo a natse, tun shigowansu idon Shureimdake aƙasaya sauka akan Yasmin da tun da suka yo sallama ta sadda kai, ba ƙaramin kyau ta mishi ba, "ango, ango ka sha ƙamshi" Insu tace cike da iya shege, murmushi ya saki ba tare da ya ɗago ba, kallonYasmin tayi tare da faɗin "to amarya ki ke ƴar ƙamshi" dariya jama'an parlorn suka saki gabaɗayansu, "Insu bar nan" Salwa tace tare da miƙewa, tattare doguwar rigan jikinta tayi zatagudu, da sauri Shureim da ke kallonta yace "Mairah" ɗago kai Farisat tayi da sauri tare da faɗin"Insu!"
"Oh Allah ba yadata zanyi ba" tace tare da kallonta.... Kauda kai tayi cike da samun sassauci, gaida su Lailah suka yi a ka kira Babiya da su Gudesukagaidasu sannan suka tattara suka tafi dan suna son isa wajen walima akan lokaci, miƙewaInsutayi tare da faɗin "boyfriend bari in zo zanga Yaya kaɗan" "okay mu ma tafiya zamu yi yanzuMommy ta ƙosa ta isa can gashi ina son leƙa wajen walimar nan" yace tare da miƙewa, "banganeba" tace da mamaki, murmushi ya saki tare da faɗin "ita zan kai can" "a'a kar muyi haka" tacedamamaki, "aiko se munyi" yace tare da sakin murmushi, "ba inda zata malam" tace tare da
kallonshi, "wallahi Mommy na jiran isanta, ta san da zuwanta" harara ta banka mai tare dakauda
kai, "sorry girlfriend na miki alƙawarin dawo da ita da wuri" "ka tabbata ta dawo kafin tafiyanmudinner anan zata shirya" tace tare da kafe shi da ido, "okay" yace tare da miƙa ma Mairahhannu, "zo muje wajen Mommy" laƙe kafaɗa tayi tare da kwaɓe fuska, "a'a ba se kin yi kuka ba, mujeNachma" yace tare da wuce wa, bin bayan su tayi cike da rashin jin daɗin tafiyan Nachman... Motanshi na fita ta wuce inda ta hango Yaya da Hassan cikin jama'a suna ta gaisuwa, tanaisataraɓe gefe tare da sakin musu murmushi, murmushi Hassan ya saki tare da ƙarisowa inda taketamiƙa ma Mairah hannu, "ai wannan sarauniyar ƙiwiyan ba yarda za ta yi ba" Yaya da ya isoyacetare da sakin murmushi, "kin huta ke ki ka yi asaran zankaɗeɗen miji" yace tare da sakinmurmushi, murmushi Insu ta saki tare da komawa gefen Yaya a natse, murmushi ya sakinmatacike da kulawa ya bi ta da ido, "ba su zo ba ko?" Tace a hankali, jinjina mata kai yayi cike dadamuwa, murmushi ta saki tare da faɗin "na sani, side ɗin baƙi a shirye yake ku ƙarisa da sucan"bin ta da ido yayi tare da jinjina mata kai tare da sakin mata murmushi...
"Bari in sanarwa Anty Lailah da kun iso" tace a dake, "uncle Hassan ku ƙarisa can please, jama'anna ku su shishshiga" ta idda maganan tare da juyawa, "na sanarwa Lailah da isowan mu" Hassanyace tare da kallon ta, juyowa tayi ta sakin mai murmushi tare da faɗin "to ku ƙarisa kafinsuiso, kar su yi ta tsayuwa a waje, bari in leƙa gidan Ummi mu gaisa da abokan Uncle" tayi maganantare da wuce wa, da ido suka bita kowa da abinda yake ji akanta....
Ja baya tayi da sauri daga kai jiki da tayi dan fita gate ɗin gidan saboda Salman da ya kawojiki, "yawwa Insu ina Kushi?" Kallon shi tayi da mamaki tare da faɗin "tana ciki" tace tare da miƙamai
Mairah da tun da ta gan shi take miƙa hannu da kwaɓe fuska.... Amsanta yayi ya tare
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 59 Chapter of 109