fiye san kallo suke ba" "na taɓaka da alheri ɗan uwa to wallahi SSBne" zare ido yayi tare da faɗin "wanne a ciki!" "Wanda dai kake jin labarin shi, shine zargi maakeɗan shi aka ɗaurawa aure da Insiyyah ta mu, a she Amina na da dangantaka da shi" "ɗanshi!" Suka ce gaba ɗayan su baku na a haɗe, "ku dai zauna kuna luguden leɓe mara amfani, har ki nawani ƙafafa akan ba dai ɗanki ba, me ɗanki ya ke da? Waya san shi? Waya sani?" "amma YayaAli
a ina ka ji labarin nan?" Lurwanu yace tare da gyara zama, "zamu fito daga masjid bayananɗauraauren, kasan shi ya fara fita" "eh shine gaskiya" Balarabe yace tare da kallon shi, "to
muƙarrabanshi suna fita ni ma na fice kasan na barku a ciki, to ɗaya daga ciki naji yana wayayana cewa "ku hanzarta SSB ya shiga mota" da na kalli numbobin motan se na ga sunan" "taɓɗinjam Allah me iko" Jummai tace tare da kama haɓa, "Hajiyan Allah miƙe muje kin ji, bar marassanayi su cigaba da zaman banza, kuma wallahi ko waccen ku ta kama na ta wajen kafin indawo, dan kulle gidan ma zanyi, duk me san ganinta ya bi ta can" "to Babiya se dai mu ce saduwar
alheri, dan ba zan je yara na mun kallon uku saura kwata ba" Gude tace tare da kauda kai, bawanda yace mata komai se miƙewa da Balarabe yayi ya ɗakko mata hijabinta ya miƙa matatareda faɗin "bar kayan daga baya na haɗo miki yanzu dai muje tukun" ba musu ta amsa ta miƙetasaka suka fice....
Suna idda ficewa Suwaiba tace "ni fa duk jikina ya mace wai me Yaya Ali yake cewa ne?" Tayi
naganan tare da kallon su, tsaki Gude ta saki tare da faɗin "sumbatu yake, kin san in ya korayazuƙa jikin shi ba ya faɗa mai dai-dai, amma in banda rainin hankali ina za su ga SSB bare har ɗanshi, yaran da ba wanda ya taɓa ganin su, shima dan shaharar da yayi ne ba yanda ya iya yakebayyana fuskan shi, ke ni fa ban yarda shi ba ne ma, kawai ya sha wanda yafi ƙarfin ƙwaƙwalwanshi ne ya zo yana wani sakin zance" "in ma shine muna fata, in ba shi ba ne Allah yasa na gari ne, amma in shine ai mun washe" Jummai tace tare da kallon su, fuska yalwace da murmurshi, "kun
washe ko sun washe! Ƙannin uwarta na raye uwarce ta mutu, ke ance miki in sun samunmanuna sun sanki za su yi? Ki ma daina wannan mafarkin dan se dai kiji a labari, ku tashi mutafi
dan wannan wawan in ya kurɓa ƙwaƙwalwan shi ba faɗa mai dai-dai take ba, tsaf ze iya shukamana rashin arziƙi, in ta dawo ma zo" Gude tace tare da miƙewa, "in ta mutu dai ma sanar dakeki
mata addu'a, amma ta tafi kenan" Balarabe da ya dawo ɗaukan ma Babiya wayan da ta matayace tare da ɗauka ya fice, "jirani Balarabe muje tare" Jummai tace tare da tashi da sauri tabi shi, bin ta da ido suka yi cike da takaici....
Bin na'uran dake temaka mata wajen jawo numfashi suka yi da ido tare da fashewa da kukametsuma zuciya, jawo su Yaya da ƙirjin shi ke sama da ƙasa yayi tare da faɗin "shiii ku mata addu'a" buɗe baki Farisat tayi da ƙyar tare da faɗin "ita ma tafiya za tayi ta bar mu ko Yaya? ShikenanInsu za ta bi Anty" ta idda maganan cikin rishin kuka, ƙanƙame su yayi tare da sakin hawayendayake ta dannewa, haka suka yi ta riskan kuka ba wanda yake hana ɗan uwan shi, se da sukatabbatar sun ƙoshi dan kan su sannan suka tsahirta tare da zama jigum-jigum....
"Salman yakamata ka zo ku tafi, Baba Mari Sa'adatu ku zo ku bi shi" kallon Farisat yayi taredafaɗin "kuma ku zo ku bi su, gobe da school" girgiza kai tayi idonta na tara ruwan hawaye, "a'abana son gardama, zo ku tafi" yace tare da ɗago su, fashewa da kuka Farisat tay tare da faɗin"Yaya ka bar mu dan Allah" "meke faruwa?" Babiya da ta shigo da zugan ƴaƴanta tace taredakallon su, da mamaki Yaya ya miƙe ya bata wajen zama tare da faɗin "sannu da zuwa Hajiya"
"yawwa ya me jikin?" "Alhamdulillah da sauƙi" yace a hankali, "da sauƙi suke ta riskan kukahaka?" Tace tare da kallon Farisat, "gida ne ba sa son komawa kuma suna da makaranta gobe"
"to ai se su share waje su zauna tunda za su ba ta lafiya ne" tace tare da banka musu hararatakauda kai ....
Ba shi hannu Ali yayi tare da faɗin "ya jikin na ta?" "Da sauƙi Alhamdulillah" "tana ta ina ne?" Yace tare da kallon shi, nuna mai da hannu yayi tare da ba wa Lurwanu hannu" ba shi yayi taredamai kallon ka kwantar da hankalin ka, murmushi ya sakin mai tare da jinjina mai kai, "YayaAbdussamad ya me jikin?" Jummai tace cike da kulawa, "Alhamdulillah Jummai ya yaran?"
"Alhamdulillah suna lafiya, Allah ya ƙara mata lafiya" "amen-amen" yace cike da jin daɗinzuwansu, "wai me ya tada ciwon haka bayan na san ya daina tashi" Babiya tace tare da kallon shi....
"Tafiyan su Salwa ne ya tado shi, naje rakasu Salman ya kira ni ya sanar dani abinda ya faru"
"suma ai be kamata su tafi yanzu ba, kwana bakwai da rasuwa su tattara su koma, ina lefinwatako arba'in lokacin sun fara sabawa da rashin, zaman sun ai ze kwantar musu da hankali" Babiyatace tare da nuna zallan rashin jin daɗinta, sunkuyar da kai Balarabe yayi saboda dauriyandakesan kuɓuce mai, saboda yanda fuskokin su Yaya ya cika da mamakin Babiya, "tafiyan ne basuyoshi da shiri ba, ga shi sun bar yara a can, shiyasa na ce su koma yau, in ya so in sun kimtsa sesuzo mu samu lokaci a nan ɗin" "to da gaskiyanka, Allah ya kai su lafiya, ya jiƙan waƴanda sukarigaye mu, ita kuma ya bata lafiya" "amen ya rabbal alamen" Yaya yace zuciya cike da farinciki, "bari in zo in wuce anjima zan dawo, dawowana kenan daga Tamguro ko gida ban isa ba" Ali yacetare da kallon Yaya, jinjina mai kai yayi tare da faɗin "nagode Allah ya kai mu anjiman" "amen" yace tare da juyawa, "bari mu zo ka ajiye mu a gida" Lurwanu yace tare da kallon Balarabe" toYaya bari mu wuce" Jummai tace tare da kallon shi, jinjina mata kai yayi cike da yabawa dakaramcinta tare da faɗin "nagode Jummai"....
"Yanzu Yaya kai ɗaya zamu bari anan? ni ba zani ko ina ba ina tare da kai" Yasmin tace taredasakin hawaye, "ke dai wannan yarinya akwai fi'ili da kankanba, Abdussamad tashi kuje zanzaunada ita" Babiya tace tare da kauda kai, a mamakance ya juyo ya zuba mata ido cike da sontabbatarwa, murmushi Lurwanu ya saki tare da dafa kafaɗan shi, waigowa yayi ya kalleshi tareda sakin hawaye, girgiza mai kai yayi cike da tausayawa, da sauri Farisat dake kusa da Babiyatarungumeta tare da fashewa da kuka, rungumeta Yasmin da Nafisat suma sukayi suna na sukukan, barin su tayi suka koka duk da sabon yanayin da kukan ke haifar mata, janye jiki sukayi anatse Farisat ta kalleta tare da faɗin "mun gode Hajiya Allah ya saka da alheri" harara ta banka
mata tare da faɗin "tashi ku tafi bana son san a sani" miƙewa suka yi a natse suka bi bayanSalman da ya fice shi da Sadam da idon shi ke radaɗi da su Sa'adatu, buɗe baki Yaya yayi dazumman magana Babiya tayi saurin dakatar shi da faɗin "kaje ka samu ka huta kar ka dawomunnan se gobe" jinjina mata kai yayi ya juya da sauri tare da sakin hawayen da yake ta riƙewayafice, kallon Balarabe tayi tare da faɗin "ka haɗo kayan nan ka kawo mun yau, na sanka da
mantuwa, kar kace mun kamanta" "a'a Hajiya daga nan can zanyi, zan zo in taya ki hira inshaAllah" jinjina mai kai tayi ya juya ya fice....
Comment fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
ِبسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~ Created and written
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Eight
Tura ƙofan fafaɗeɗen office ɗin yayi baki ɗauke da sallama tare da ja ya tsaya, "ƙariso manaMalam Ibrahim" Abubakar dake zaune a kan sofan dake office ɗin yace fuska yalwace da
murmushi, ba musu ya ƙarisa tare da ba shi hannu fuska yalwace da murmushi, musabahasukayi cikin mutunta juna ya juya ta inda Jabir yake ya ba shi, cike da zolaya ya miƙa mai na shi....
Ƙarisawa kujeran dake gaban danƙareren table ɗin dake gaban SSB yayi tare da bawa Munnir
hannu, ba shi na shi yayi tare da faɗin "har ka huta kenan Malam Ibrahim?" Murmushi ya saki
tare da sosa ƙyeya cike da jin nauyi yace "oga Munnir gajiya ai ya ƙare, tun jiya fa nake hutuwa" murmushi ya sakin mai tare da faɗin "haka ne, to ya hanyan?" "Alhamdulillah" yace a girmame, "to ma sha Allah" yace tare da sakin hannun shi da yake riƙe da shi ƙam-ƙam, ƙarisawa gaSSByayi ya ba shi hannu a girmame, miƙa mai na shi yayi ba tare da yace komai ba" janye hannunshi
yayi a ladabce tare da faɗin "ranka ya daɗe na same ku lafiya?" "Alhamdulillah" yace ba taredaya kalleshi ba saboda duba takardun dake gabashin da yake....
"Ibrahim ya ƙarin haƙuri kuma? Se mu kaji mutuwa bakatatan" Abubakar yace tare da kallonshi
fuska na bayyana alhini, murmushi ya saki tare da faɗin "Alhamdulillah oga Abubukar, uwar ɗaki
na Allah ya amshi abin shi" "ciwo tayi ne?" Yace cike da alhini, girgiza kai yayi tare da faɗin"babuciwon da ta yi, ana gobe zata rasu se da ta halarci court, Alhamdulillah kuma ta samu nasara"
"subhanallah" Jabir yace tare da maida hankalin shi akan Ibrahim, "ranar kuwa lafiya-lafiya, bamuji wani abu saɓanin wanda muka saba ji ba, yara sunje makaranta lafiya, ita ta fito har indamuke zaune tace inje in dawo da manyan, ƙananun kuwa dama school bus ne ke kai su yamaidosu, sun yi duk abinda suka saba yi, muna zaune ni da me gadi ta fito ita da yaran biyu tacezamuje hospital dama tana da ciki kuma ta shiga watan haihuwa, da ƙafarta ta taka har bakinbabbangate, babu wani alaman ciwo, suna tafe suna hira, ko da muka isa hospital da kanta ta fitobabuwani alamun rashin lafiya har suka shiga ciki, abinda ze baku mamaki, yaran duk sun fitozasuyi
na su waje, ɗaya har ta tafi, ɗayance ba ta samu tafiya ba tana shirin fita daga hospital ɗinseganin Dr muka yi a rikice yana faɗin "Hajiya ba lafiya" ya idda bayanin jiki a sanyaye, tundayafara kora bayani SSB ya dagata daga abinda yake ya zuba mai kunnuwa, su Jabir kuwa gabaɗayajikin su yayi sanyi bin shi kawai suke da ido....
"Ya subhanallah, wato ba ma ciwo tayi ba!" Jabir yace cike da alhini, "lafiyanta lau" yace taredagoge hawaye, "se haƙuri Ibrahim, muna mata fatan dacewa" Munnir yace cikin muryan rarrashi, fashewa da kuka me ciwo yayi tare da faɗin "in sha Allah oga Munnir, wallahi uwar ɗakinamacece me sanin mutumci da darajan ɗan adam, duk da ba ta da sakewa da mutane, ammabatada wulaƙanci, bata yarda ko kallon banza ƴaƴanta su mana ba" ya idda maganan tare da sharehawaye, "Allah ya jaddada rahma gareta" suka ce baku na a haɗe, "amen ya Allah" yace a
sanyaye, "ka koma bakin aikin ka" SSB yace ba tare da ya ɗago ba" "ina godiya ranka yadaɗe" yace tare da sallaman su ya fice, sauke ajiyan zuciya me sauti Jabir yayi tare da faɗin "shikenanfa rayuwar, ba ragi ba ƙari, wai Insiyyah ta tafi gashi kamar ba ta zo ba" "a'a wani irin kamanbatazo ba? Bayan ta bar baya, ai wanda be bar baya ba shi ake cewa ya tafi kamar be zo ba" Abubukaryace tare da gyara zama....
Tura ƙofar ward ɗin tayi tare da kutsa kai ciki, ɗago kai Babiya da Ali da Balarabe da ke zaunesuna taɓa hira suka yi tare da zube mata ido, murmushi ta saki tare da faɗin "sannu da zuwaYayaAli, Yaya Balarabe ka dawo?" Murmushi Ali ya saki tare da faɗin "yanzu nake tambayanHajiyatace kun tafi makaranta" murmushi ta saki tare da jan kujera ta zauna, "oh ni Nafisatu na gaboni, yanzu ke wannna yarinyar ba zaki natsu ba? ɗazu-ɗazun nan fa ki ka zo da zaki tafi makaranta, yanzu kuma gashi kin dawo, anya kin je makarantar nan ma kuwa?" Babiya tace tare da kamahaɓa..... Murmushi ta saki tare da faɗin "naje submitted ɗin assignment kawai aka yi ba ma da lectureyau" "to me ki ka ce kenan?" Babiya tace tare da kama haɓa, murmushi Balarabe ya saki taredafaɗin "yau ba sa da darasi, aikin da aka ba su suka kai" "to! Saboda aikin gidan suka sa yarawahala haka?" Babiya tace tare da kama haɓa cike da mamaki, "jami'an kenan Hajiyan Allah" Ali
yace tare da sakin dariya, "wannna makaranta kuwa akwai gantalalliyar makaranta, ba sabari
ranar da za'ayi darasin su kai ba, to tashi tun kafin drivern na ku ya gaji da jira ku tafi, ki jeki ci
abinci ku yi shirin makaranta, ina ma sauran ne?" "Suna makaranta ai makarantar mu ba ɗayabane da su, ta can za su wuce, ni kuma na taho da uniform ɗina zan wuce ta nan" Farisat tacetareda gyara zama, "to je ki sallame shi kar yayi ta zaman jira tunda ke kin samu wajen zuwa, dukdashi ma gashi ga kaman shi ne, yaro ba um yake ba bare um-um" "wai wa! Ibrahim?" Farisat taceda mamaki "ni ina zan riƙe sunan shi, yaro ba sanin yakamata ko kaɗan tare da shi, in idonbawaze zazzago saboda kallo ba ze ce ko uffan ba" tayi maganan cike da takaicin Ibrahim.... Murmushi ta saki tare da faɗin "ai tare da shi su Anty Lailah suka tafi jiya" "ya tafi kuma! Tolafiyadai ko? Ko rashin ta idon naku ku ka nuna mai da ya ga uwarku ta mutu ya ajiye aikin?" Babiyatace cike da al'ajabi, tura baki gaba tayi cike da rashin jin daɗi tace "mu ba ma wa kowa rashinkunya, ba abinda muka mishi, kawai tafiya yayi, yaushe ma Anty da Yaya za su bari a ma wani
rashin kunya" ta idda maganan cike da rashin jin daɗi, "se ƴaƴana da ku ka rainawa wayauwatosuke barinku ku karta musu rashin ta ido" Babiya tace a ƙufule, "ba abinda muke musu suma"
tace tare da kauda kai, "rufe min baki kar in gwabjeki, ina nan ku ka taru gaba ɗayanku kukazage yar mahaifinku Gude a gaban uwar ta ku, ba tace komai ba ta fice tana kuka, Suwaibatazodan jin ba'asi ku ka ɗora akanta, saboda ƙin gaskiya kuma ɗan uwan su ya dawo ku ka shiryamai
magana ya hau ya zauna, duk haka be muku ba, ku ka tura folisawa suka kama su har gidajensu, aka zubda musu da mutumci a tsakiyan anguwa, se da ku ka tabbatar sun gama wulaƙantaacansannan aka sallame su" ta idda maganan a harzuƙe, "Hajiya dan Allah me ye na ta do wannanmaganan a nan kuma?" Balarabe yace cike da rashin jin daɗi....
"Bar ni Balarabe in na tuna wannan cin zarafin da Amina ta mun ko ina cikin farin ciki se baƙinciki ya riske ni, wannan abu yayi mugun dukana, ban ɗauka tsaman da ke tsakaninmu da Aminaze sa ta iya miƙa mun ƴaƴan ga hukuma ba" ta idda maganan tare da goge hawaye, "danAllahHajiyan Allah ki bar zancen ya wuce, koma me ya faru ya wuce tunda sun fito ita kuma yanzubata, mu yafe abinda ya wuce mu gyara hannuwa dan amsan wanda ze zo" Ali yace cikin muryanrarrashi, "ya wuce Allah ya kyauta gaba tace tare da kallon Farisat dake share hawaye, "menenekuma na kukan?" Tace tare da kafeta da ido, "daina Farisat komai ya wuce" Balarabe yacecikedararrashi, girgiza kai tayi tare da faɗin "a'a Yaya Balarabe be wuce ba tunda yana nan a zuciyarta, Hajiya ba ki san abinda ya faru ba, kawai an je an faɗa miki ƙarya da gaskiya ne, ke kuma ki kazokina ta zagin Anty akan rashin sani, bari in faɗamiki asalin abinda ya faru" ta tsahirta taredagoge hawayen da ya gangaro mata....
"Ina tuhumar da aka wa mijin Anty Gude, wanda har aka shiga court a kai?" Tace tare da kallonAli, "na handama da babakere da yayi akan tallafin da aka kai makarantar da yake jagoranci?" Balarabe yace tare da kallon ta, "shi, akan dalilin ne yasa Anty Gude zuwa gida wajen Antyakanta tsayawa mijinta, dan tasan in ta tsaya mai ze samu nasara, ita kuma Anty tace ba zata tsayawaƙarya ba, nan tayi ta zuba mata baƙaƙen maganganu ba wanda ya tanka mata daga mu har Anty, bayan ta fita abun yayi ta ma Anty ciwo, dan abinda yafi baƙanta mata shine da ta zo gabanmutana maganan a goyi bayan zalunci, nan muka bar zance ba wanda ya tada ko da Yaya ya dawo, bayan zuwa da suka yi suka sayi lauya ya tsaya musu har yayi free se ta dawo gidan mu tadasacin mutumci a inda ta tsaya, har ta na cewa Anty "jinin tsiya ce wacce ba ta gaji arziƙi ba, ƴar
baƙin ciki ta Allah ba tata ba, ga shi mijinta yayi free" Anty ba ta ce mata ko sannu ba, nantadinga zuba ruwan tijara, na tashi zanyi magana Anty ta hanani, Sadam ya tashi ta hana shi, nanta dawo kan mu ta fara aibanta mu, ganin yanda zuciyar mu ya ɓaci yasa Anty umurtan mudamukoma ɗakunan mu, tattara komatsan mu muka yi zamu tafi ta cafko ni zata dukan Anty tajanyeni, dukan da ta kawo mun ya sauka a jikin Anty nan zuciyan Insu ya ɓaci ta birkice mata, tayi tafarfaɗa mata maganganu san ranta ita ma, ganin abun na gab da ɓaci dan mu ma mun faramaida mata magana, yasa Anty roƙonta akan ta fice daga gidan, bayan fitan ta Anty tayi tamanafaɗa tare da nuna mana matsayinta a wajen mu, Insu zata ja ta mareta tace ta ɓace mata aido, tunda muka ta so ba mu taɓa ganin Anty ta duki Insu ba se a wannan lokacin....
Tafiyanta ba daɗewa Anty Suwaiba ta zo da zugan ƴaƴanta maza wai sun zo dukan mu, rufemuaɗaki Anty tayi tace musu ba wanda ze taɓe mu dan bata ga dalilin dukan ba, nan suka yi tazubarashin mutumci a tsakar gida, se da suka tabbatar za'a kira musu securitys sannan suka tafi, koda Yaya ya dawo ba ta faɗa mai ba, ni da Sadam muka kora mai duk abinda ya faru, a hakanmase da tayi mana faɗa, zuciyan Yaya ya ɓaci yayi ta mata faɗa akan dalilin da yasa ba ta tankamusu ba, murmushi kawai ta saki tare da faɗin "in na tanka ai se mu taru mu zama ɗaya, gundada ban tankan ba ze fi alheri" mu har mun manta da maganan kawai se gaki kin shigo ki nakukakina na ki kumfar bakin, se da ki ka zo sannan muka san an kama su, wallahi Anty ba ta saakamakowa ba, bayan yafiyanki hankalinta yayi mugun tashi, mun san in ɗaya daga cikin su AntyGudesuka zo gidanmu se Anty tayi kuka, amma bata yi a gaban mu se ta tafi side ɗin Yaya, ammaranar a gaban mu take kuka tana faɗin "wallahi bata sa kowa ya kama su ba, munyi kuka, munyi
takaicin samun ku a matsayin dangin mu, ko da muka fara Allah ya waida da dangantakandamuka haɗa da ku se cewa tayi kar ta ƙara jin wannan furucin ya fito daga bakin ɗayan mu, munazaune a cikin wannan yanayin, Yaya da ya fita ya shigo da hanzari ya ce ta ɗakko hijab suje, bamusu ta ɗauka suka fita, ko da muka bi su se muka tadda Ibrahim ya shiga mazaunin driver yajasun fita, munyi mamaki dan Ibrahim be jan Yaya Anty kawai yake ja, se yau na gano dalilindayasa ya bi su, sannan na gano wanda ya sa aka kama su" ta idda maganan tare da kafe sudaidokaman yanda suka kafeta....
"Waye!" Balarabe yace tare da kallon ta, "kawun mu dake Ɓadamayya ne" tace a hankali taredagoge fuska, "Hassan yake ma ko Husaini?" Ali yace tare da kallon ta, girgiza kai tayi tare dafaɗin"ba shi ba ne" "haba Ali wannan bawan Allahn hankali ne da shi, nan fa ya zo lokacin da
mahaifiyarta ta rasu yayi ta zuba mata rashin arziƙi a gaban mutane, wannan yaushe ze iyataɓuka abin arziƙi" Babiya tace jiki a sanyaye, "ni kaman ma be zo da rasuwan nan ba ko?" Yacetare da kallon Farisat, jinjina mai kai tayi tare da faɗin "be zo ba" "to ya sha zaman shi, Allahdai
ya yafe mata" Babiya tace tare da gyara zama, "amen" Farisat tace cike da sanyi....
"Kinji ko Hajiyan Allah, shiyasa na ce miki Gude ba dan ke take wannan buɗe muryan ba, kinji danmijinta take, dan ba'a goyawa ƙarya baya ba, dan Allah kiji wani san rai irin na su, matannantunda ta zo baku ja ta a jiki ba, ba ku so ta ba, sannan laluranki ya taso kinje wajenta, abintakaicin ma kin je dan ɓata mata gobenta, a gaban ƴaƴanta ki je mata da harkan zanba cikinaminci, wato duk wani tarbiyya da take ma ƴaƴanta ta riguza musu a lokaci guda, haba tsakani
da Allah me mutanen nan ke so ne wai?" Ali yace tare da sakin numfashi me huci, "san rai dazuciya ne kawai ba wani abuba, sun san in suka zo suka tsarata tana hawa kai ta zauna neshiyasasuke wasa da tunaninta" Balarabe yace tare da kallon Babiya, "Allah ya gafarta mana dai, itakanta duniyar nawa take, yau mu ne gobe wasun mu, duk wanda yayi me kyau dan kanshi, tundasun ce wannan ɗabi'ar suka ɗaurawa kawunansu da girmansu da shekarunsu, se suje suyi tayi, ranar nadama mara amfani na nan zuwa ya riskesu, ga yara nan sun tara da jikoki, ita sharri ƴaraike ce, a kwana a tashi za ta dawo wawanda ya aiketa da sakamako, tsakanina da Amina dai
Allah ne kawai se mana alƙalanci dan dai mun zuba rayuwa" ta idda maganan a sanyaye, "inshaAllah ba komai Hajiya, Anty Amina ba ta da riƙo, ko me aka mata anan take zubdawa ta kamaharkokin gabanta" Balarabe yace cike da tabbaci, "to Allah ya sa hakan Balarabe" Babiya tacezuciya ba daɗi....
Gyara zama Munnir yayi tare da ajiye mai takardan hannun shi a gaban shi tare da faɗin"inkasamu lokaci ka duba wannan" jinjina mai kai yayi tare da faɗin "Jabir ya ku ka yi da magananaudigan nan?" Tasowa Jabir yayi yaja kujeran da ke kusa da wanda Munnir ke zaune ya zaunatare da faɗin "gaskiya audigan be da quality, ba ze mana abinda muke so ba, shiyasa bantura
maka ba, amma mun samu labarin irin wanda muke nema yafi a yankin Indiya da Afghanistan, inzaka mana magana da mr Aditiya ina ganin in sha Allah zamu samu" jinjina mai kai yayi taredakaudawa daga saman fuskan shi, "a tura mai da saƙon zama da za muyi da shi na rabin awaranarwednesday" yace cike da kame girma, "ok in sha Allah" yace tare da miƙewa ya koma indayataso, "Abubakar fa ya samu ƙaruwan twins jiya" Munnir yace tare da sakin murmushi, ɗagokai
yayi tare da kallon shi da mamaki, "a'a ba ruwana shi zaka ma wannan kallon" Munnir yacetareda nuna mai Abubukar, dariya ya ƙyalƙyace da shi tare da faɗin "to irin wannan kallon tuhumahaka" yayi maganan tare da isa kusa da Munir, dariya Jabir ya saki tare da faɗin "malamatsagaita iyali dai, a roƙi Ubangiji ya sawa waƴanda aka samu albaraka" "gaskiya ne, abindakezuciyata kenan" Abubakar yace tare da kallon shi, "nawa kenan?" Munnir yace tare da kamahaɓa, "bakwai, se waƴan nan biyun ka ga tara kenan" "wai Allah ya wa zuri'a albarka" yace tare dakame bakin shi, "ai ba da wasa ba ya zazzaga" Jabir da ya ƙariso wajen yace tare da kai mai dukaa baya....
Yaron nan ya shekara biyu kuwa?" SSB yace tare da kallon shi, "eh yayi" yace tare da sakinmurmushi, jinjina mai kai yayi tare da kallon shi, ganin ya kauda kai ya sa shi fahimtar ba zeƙaracewa komai ba, tattara takardun gaban shi yayi ya maida gefe, ya ja kujeran da yake kai bayaanatse tare da miƙewa baki ɗauke da sunan Allah, wucewa gaba yayi suka dafa mai baya agirmame....
"Ku dai ku cigaba da musu biyayya iyayenku ne, bakwa da kamar su, da mahaifin ku da suuwaɗaya uba ɗaya ne, duk ni na haifesu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 109