"ina sauraren ki" kwaɓe fuska tayi tare da faɗin "be ɗauke ba fa" "me!" Taceda mamaki, "jinin mana" tace a hankali, dariya Insu ta saki cike da nishaɗi, "ke fa daɗina dakekenan, in cikin wani hali kuma kina mun dariya" tace kaman zata saki kuka, "oh sorry babywallahi abun ne ya ban dariya, to se me kenan?" Tace tare da sakin murmushi, "inda na sanmafita zan neme ki ne?" Tace cike da takaici, "oh Allah na ce ki yi sorry mana" "naji" tace adaƙile....
"To shi ya sani ne?" Tace cikin murya serious, "a'a kuma se wani rawar jiki yake, gashi yaceintashi in yo alwala muyi sallahn da ake yi" tace kaman zata saki kuka, "to ai ba wani abu bane, ki
faɗa mai bakya da tsarki shikenan" tace cike da gaskiyanta "oh Allah Insu ba zan iya ba, wallahi
nauyi nake ji" tace kaman zata tsaga ihu, danne dariya Insu tayi tare da faɗin "to alwalanzaki yi
ki yi sallahn?" Tace muryanta da mamaki, "haba ya za'ayi in yi se kace ban da hankali" taceitamada mamaki, "to kin gani dole dai ya sani" tace tare da sakin murmushi, "oh Allah wannanwani
irin abun kunya ne" tace kaman zata saki kuka, "kinga baby ki bar wani fargaba, uncle Shureimmijinki yake yanzu, sirrinki, ba wani hijabi a tsakanin ku yanzu, ki sanar da shi halin da ki keciki
ba wani abu ba ne, da ilimin shi ze fahimce ki" tace cike da son ƙarfafa ta.....
jinjina kai tayi tare da faɗin "Allah yasa in iya Insu, ki taya ni addu'a" "shikenan zanyi, ki gaidamun uncle Shureim" tace tare da sakin dariyan da take ta dannewa ta kashe kiran, girgizakai
tayi ta wuce ƙofa, tana fita daga side ɗin ta nufi ɗakin Babiya ganin tayi barci su Suwaiba maduksunyi ya sata juyawa tayi ɗakinta, tana shiga ta tadda Nachma kwance tana ta sharar barci, ajiye
wayoyin hannunta a saman dressing mirror tayi ta saki murmushi ganin Nachma na ta sharar
barci hankali kwnace ta wuce bathroom, ba ta jima ba ta fito ɗaure da towel da alamunwankatayo, wardrobe ta wuce ta ciro kayan barci riga da wando masu taushi ta saka wuce wa samangado tayi ta zauna ta ɗakko madai-daicin roban dake bedside drower.... Ɗaukan maganin dake ciki tayi ta dau bottle ɗin ruwan dake ajiye a saman wajen ta kafa baki, tana gama sha ta ajiye ta haye da ƙafafunta ta ja blanket ta rufe ƙafafu tare da jingina da jikinkan gadon, lumshe ido tayi tare da karanto addu'an barci, ba ta jima ba barci yayi nasarankawomata ziyara, tarban girma ta mai cike da gajiyan da ke nuƙurƙusanta....
Sauke wayan tayi a hankali tare da faɗin "Ya Rahim ka temake ni" murmurshi Shureimya saki
tare da takowa a hankali ya isa kusa da ita, duk zancen da ta tattauna da Insu ba wanda beshigakunnin shi ba, "kun gama?" Yace a natse, jinjina kai tayi ta miƙa mai wayan a natse kai a ƙasa, amsa yayi ya ajiye a gefe tare da faɗin "ba ta kuka ko?" "Tana yi ɓoyewa take" tace a hankali, murmushi ya saki tare da faɗin "zata daina" jinina mai kai tayi a hankali ba tare da ta ɗagoba, miƙa mata hannu yayi tare da faɗin "taso muje" fiddo ido tayi tare da ƙara ƙasa da kai, "lafiya!" Yace murya da mamaki, "am am baa ba bana da tsa tsar tsarki" tace murya na rawa, murmushi yasaki tare da duƙawa a hankali ya ɗago kanta da kulawa....
Ya riƙe fuskanta a tafin hannun shi cike da tsan-tsan kulawa yace "me ki ke tunani ne gamedani
precious! Saboda kina jini ba zan taɓa ki ba? Ba zan rungumeki ba? Ban zan sumbaceki ba?" Tsahirtawa kaɗan yayi tare da sakin murmushi me tarin ma'anoni saboda ganin yanda takebinfuskan shi da idanuwanta da suka canza launin, girgiza kai yayi tare da faɗin "ke matata ce, sirrina, zan iya miki duk wannan abinda na lissafa ba tare da nayi tunanin yin komai dakebaprecious, kar ki taɓa tunanin zan buƙaci wannan abun, ba dan shi na ƙaunace ki ba, dankarankan ki na ƙaunace ki, ki adana shi da kyau kar ki sake ki bani se lokacin da ki ka ga ya dacezanjira ba tare da ƙosawa ba, tashi mu je ki rage kayan jikin ki ki watsa ruwa" ya idda maganantareda sakin fuskan ya yunƙura da nufin tashi, jawo shi tayi da sauri ta rungume ƙaƙamtare dasaka
kanta a ƙirjin shi, "I'm sorry" tace a hankali.... Murmushi ya saki tare da shafa kanta zuwa bayanta, "Muhammad Shureimda dukkaninzuciyanshi yake ƙaunar ki, ki saka wannan a zuciyarki" jinjina kai tayi idonta na tsirar ruwan hawayetareda faɗin "i know" murmushi ya saki ya ɗagota tare da lakuto hawayen dake biyo kuncinta yaɓatafuska, murmushi ta saki tare da faɗin "sorry" ta daga hannu da nufin gogewa, kama hannunyayi
da sauri tare da faɗin "wannan aiki na ne ba na ki ba" murmushi ta saki cike da jin kunya, sakahaɓar jallabiyan da ya sako yayi ya goge mata hawaye cike da ƙauna tare da faɗin "kar inƙaragani, in ba haka ba kuma zan taya ki" ƙaramar dariya ta saki tare da bin shi da ido, "tashi mujeki
tsaftace jikin ki, Allah yasa be ɓata miki jiki ba!" Yayi maganan tare da fiddo ido waje.... Murmushi ta saki tare da kauda kai, "oh Allah" yace cike da alamun samun sasauci, kallonshi tayi
tare da faɗin "ya ɓata" zare ido yayi tare da shagwaɓe fuska ya kalleta cike da ɗan tsarguwayace"please precious ba na so" dariya ta saki tare da faɗin "to tsaya anan in je in canza tunda bakason" hararan wasa ya banka mata tare da faɗin "ban yarda ba" dariya ta saki me ƙaraminsauti
tare da faɗin "to se yaya kenan?" "Se inyi haƙuri" yace tare da kamata ya wuce da ita a natsesukayi bedroom ɗinta da ya gaji da haɗuwa... Bin bedroom ɗin da ido tayi cike da burgeta da yayi, murmushi ya saki tare da zagayowa tabayanta ya rungumota kaɗan tare da faɗin "yayi kyau?" Jinjina kai tayi tare da sakin murmushi, "dama na tabbatar da ze miki kyau" yace a dai-dai saitin kunninta tare da saka hannu a natseyayi ƙasa da zif ɗin gown ɗin jiknta, kame jiki tayi da sauri dan ba tayi zaton hakan ba, murmushi
ya saki ya idda ƙasa da shi ya duƙa a hankali ya zame tare da faɗin "cire" ɗaga ƙafafunta tayi anatse ta cire daga tsakiyan gown ɗin, ta ja gefe cike da matsanancin kunya, dan daga ita sebesda dogon wando skin tight....
Miƙewa yayi a natse ya tattaro gown ɗin ya ajiye a gefen sofa tare da faɗin "muje" da mamaki takalleshi, murmushi ya saki ba tare da ya kalleta ba ya riƙo hannunta ya wuce toilet da ita, haɗamata ruwa me sauƙin zafi yayi a bathtub cike da bada umurni yace "kar ki daɗe" yana kai nanyafice, sauke ƙaƙƙarfan numfashi tayi cike da samun sassauci tare da kauda ido daga bakinƙofanta maida ga ruwan, a hankali ta cire sauran kayan da ya rage a jikinta ta shiga ruwan a natse, lumshe ido tayi cike da jin daɗin ruwan tare da sakin ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya....
Se da ta daɗe a ciki kafin ta saɓawa kanta sabulu, tana fitowa daga bathtub ɗin ta ja ƙaramintowel ta goge jikinta, rataya shi a mazaunin shi tayi taja babba ta ɗaura a jikinta ta fice a hankali, tana sako ƙafa a bedroom ɗin ta tadda shi zaune saman sofa hannun shi riƙe da waya yanadaƙila, tsayawa cakntayi tare da sadda kai jiki na ɗan ɓari, guntun murmurshi ya saki tare da ajiyewayan a gefe ya miƙe a natse ya ɗaukan kayan barcin da ya ciro mata ya nufeta hankali kwance...
Zagayawa ta bayanta yayi ya ja towel ɗin a natse yayi ƙasa, zare ido gaba ɗaya waje tayi jiki natsananta ɓari, daga kan rigan yayi ya zura mata, ya ɗan saki tare da zagayowa ta gabanta yaɗagahannun damanta a natse ya zura hannun rigan, yana iddasa sakawa ta saki sassanyan ajiyanzuciya a hankali, murmushi ya saki tare da faɗin "matsoraciya" murmushi ta saki cike da kunyatare da sadda kai....
"Baki saka abokin na ki ba" yace a natse tare da nuna mata pat da ya ajiye a gefen dressingmirror, kauda kai tayi cike da nauyi tare da faɗin "ba zan saka ba" guntun murmushi ya saki tareda faɗin "ni dai kar a ɓatani" murmushi ta saki tare da gyara tsayuwa, riƙe hannunta yayi yakaitagaban dressing mirror ya ja stool ya zaunar da ita tare da faɗin "da gaskiyana precious Allahbana son abun nan ya taɓe ni" yayi maganan kaman ze saki kuka, murmushi ta saki tare dajinjinamai kai....
A natse tayi shafe-shafen da za tayi ta na gamawa ta miƙe a natse jan stool ɗin yayi ta ficedagatsakiyanshi tare da faɗin "muje ki ci abinci" girgiza kai tayi tare da faɗin "na ƙoshi" "no baki ƙoshi
ba, ina fa lura dake ko a wajen dinner baki ci komai ba" murmushi ta saki ba tare da tace komai
ba, "please precious muje ki ci" jinjina kai tayi cike da natsuwarta, murmushi ya saki tare dakama hannunta suka fice a natse.... Da kan shi ya ci da ita ya shayar da ita cike da tsan-tsan ƙauna yana me godewa Ubangijinshi daya nuna mai wannan rana, suna gamawa ya miƙe dan tattara abinda suka yi amfani da shi, miƙewa tayi a natse ta fara tattarawa tare da faɗin "bari in taya ka" "to" yace tare da bintadamurmushi, tattarasu tayi ta kai kitchen, ba ta fito ba se da ta tsaftace su tas ta maida sumazauninsu, a inda ta bar shi ta taddashi, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "yanzu nakeshirin biyo ki" murmushi ta saki tare da faɗin "se gashi na hutashshe ka" dariya ya saki cikedanishaɗi tare da miƙewa ya ja hannunta a natse suka wuce part ɗin shi da ya kusa firgitata sabodahaɗuwa, ba su tsaya anan ba kai tsaye ya wuce da ita bedroom ɗin shi, anan ta kuma tsarkakeikoda buwayan mahaliccinta, iya tsaruwa ɗakin ya tsaru, murmushi ya saki tare da faɗin "yayi minkyau" "ni ma" tace a hankali, "to mu yi canje" yace fuskan shi faɗaɗe da murmushi, murmushi tasaki tare da girgiza kai, ɗaukanta yayi caraf ya saka a ƙirji ya nufi tamfatsetsen gadon da yacinyerabin bagon da aka saka shi, lumshe ido tayi lokacin da ta ji ta a ƙirjin shi, tana cikin amsanyanayin da hakan ya zo mata da shi ta jita cikin wani tattausan abu, buɗe ido tayi ta kalli indatake, ware ido tayi tare da taɓan katifan da ya shinfiɗeta a kai.. Kwanciya yayi ta bayanta ya jawota jikin shi sosai ya ja musu duvet ya kashe haske ya kunnadumlight ya fara karanto addu'a a natse, tofesu yayi cike da gamsuwa ya lumshe ido, wasuzafafan hawayen farin ciki suka gangaro mai, jin abu me ɗumi ya sauka a kuncinta ya satasakahannu a natse ta shafo, da mamaki tayi ƙoƙarin juyowa danneta yayi da ɗan ƙarfi, "auch" taceahankali, "sorry" yace tare da sasautawa, "Habbubi kuka ka ke!" Tace da mamaki, jinjina kai yayi
tare da faɗin "na farin ciki ne precious" jinjina kai tayi cike da gamsuwa ta lumshe ido, a hakawani daddaɗan barci ya kawo musu ziyara, ba wanda ya tantance lokacin da ɗayansu yayi....
Murmushi ta saki idonta akan Nachma dake tsaye gefenta tare da faɗin "thank you friend" murmushi ta sakin mata tare da faɗin "again!" Murmushi me faɗi ta kuma saki tare da faɗin"nayi
matuƙar farin ciki da zuwanki" "i know ni ma nayi farin ciki da ganin ahalin ki, mutanen kirki, masu dattako, na daɗe ina son sanin inda ki ka ɗakko dattakon ki se da na zo na fahimta" tayi
maganan fuskanta na bayyana farin cikin da tayi da kasancewa da su, murmushi ta saki taredafaɗin "se yaushe kenan?".... Harara ta balla mata tare da faɗin "wannan ai tambayarki ce" ƙaramar dariya ta saki taredafaɗin "very soon zamu kawo sister Hasinat can in sha Allah zan shigo Insoul mu gaisa" murmushi
ta saki tare da faɗin "muna nan muna zuba ido, duk da dama kun kusa ziyarto mu" ta iddamaganan murmushi be bar saman fuskanta ba, "mu zo muyi me kuma!" Tace da mamaki...
"Au boyfriend ɗin na ki be sanar da ke ba?" Tace tare da sakin murmushi, juyawa ta inda Hishamke tsaye da Labib tayi tare da faɗin "boyfriend me ke faruwa?" Takowa a natse yayi ya ƙarisoindasuke tare da faɗin "Insoul ne ta nemi ɗaliban ƙarshen shekara na ko wani reshe da su zo sukokacikin tushe su ƙarishe ƙarshen semestern su a cikinta" ya idda maganan idon shi akan ta, dazallan mamaki tace "yaushe wannan zancen kuma ya fito!" "Shekaran jiya ne, sha'afa ma nayi
ban sanar miki ba" "lallai mutanen nan suna son ƙure hakurin mu fa" tace cike da takaici, murmushi Nachma da Labib suka saki tare da bin ta da ido, tsaki ta saki tare da zaro wayantadake neman agaji ganin me kiran ya sata ɗagawa ta kara a kunni....
"Ina ga fa Antyn Lailah watan da zamu shiga zamu Kautal" Farisat tace ma Lailah dake tsayegefen su Insu tare da sakin murmushi, "meyasa wai ke Farisat ki na son abinda za'ayi ta maganane! Me zaki je ki yo a wannan yanayi da ki ke ciki! Ba zaki jira ki haihu ba?" Tace cike da damuwa, kwaɓe fuska tayi tare da faɗin "wallahi na daɗe banje ba fa" "to ki jira ki haihu se ki je dukinda
zaki ba wanda ze hanaki" Khadijatu tace tare da kallon ta, "ban da ma abinki ina ce ɗazutakoma, ba daɗin Yaya ba ma yace se ta koma da ku na nan tare tunda ita ma kamar ke take, bakwadalissafi wajen aikata abu" Lailah tace tare da kauda kai daga gareta ta maida ga Yaya daketasakin murmushi shi da mazajensu ....
"Yaya in Allah ya kai mu yara suka samu hutu muna son zuwa Nigeria dan ganin inda YayaHassan ke rayuwa da iyalin shi, matar nata ƙorafi akan ba mu taɓa zuwa ba shi ma na sanshirukawai yayi" ta idda maganan a girmame, jinjina kai yayi cike da fahimta tare da faɗin "nayi
tunanin haka ni ma, se dai kin san kana na ka Allah na na shi, amma tunda har ku ka yi hankalintuna hakan in sha Allah ba wani abun damuwa ba ne, amma ina roƙon da ku bar shi har Allahyasauki Farisat lafiya, kun ga se ku je gaba ɗayanku" jinjina kai tayi cike da gamsuwa, murmushi
Farisat ta saki tare da kallon su cike da jin daɗi....
"To Allah ya nuna mana Yaya, na ce ma Yasmin kar tayi gaggawan komawa kan aiki ta jiratagane kan gidanta tukun, wataƙila ta maka maganan" tace da girmamawa, murmushi ya saki tareda faɗin "hakan yayi" murmushi ta saki tare da faɗin "ya maganan zuwan Nafisat ɗin Yaya?" murmushi ya saki tare da faɗin "za mu jira jin ko za su ba ta gurbin abinda take so a makarantarin sun bata in sha Allah zata dawo nan tayi karatu" murmushi suka saki cike da jin daɗi, "toAllahya nuna mana Yaya" suka ce bakuna a haɗe, jinjina kai yayi tare da faɗin "idan na natsu zanmagana da ku akan batun da muka tattauna da brother Hassan" "to Yaya" suka ce baku naahaɗe, "to ku hanzarto, sunan ku ya fito" Sadam da ya iso wajen yace tare da kallon su, murmushi
Salman dake dafe a bayan shi ya saki tare da faɗin "an fara kiran sunaye" kwalkwal da idoNafisat tayi cike da kewan su da za tayi....
"Sallama Yasmin dake zaune gefen Shureim ta sakin mata a zumuɗe, amsawa tayi tare dafaɗin"Amarya ƴar ƙamshi irin wannan murya haka" murmushi ta saki tare da faɗin "kin taso ne?"
"Zuwa ina!" Tace da mamaki, "ɗazu Mommy da suka zo tace "zaki zo da la'asar" "a'a ba dani akayi
haka ba" "kar mu yi haka dake baby Insu" tace kamar zata saki kuka, dariya Insu ta saki taredakallon Nachma dake mata alama da za ta tafi" rumgumeta tayi cike da kewa tare da faɗin"zaki
ga magana na ko zuwa anjima" jinjina mata kai tayi ta wuce, ɗaga ma Labib hannu tayi cikedamurmushi, murmushi ya saki mata ya wuce a natse...
"Um hum kin yi shiru" tace tare da takawa tayi inda su Lailah suke shirin wuce wa dan jirgi ɗayaza su bi da su Nachma, "to ai ke nake jira" tace murya a marairaice, "wallah ba inda zan zoni
yanzu haka ma mun yi rakiya airport ne" tace tare da rungumar Lailah, hitting ɗin bayantatayi
cike da kewanta da za tayi tare da faɗin "ki kula da shan magani" jinjina mata kai tayi ta zamejikinta a natse ta rungumi Khadijatu, "zanyi kewanki daughter" tace cike da tabbaci, jininamatakai tayi tare da faɗin "ni ma" "na sani" tace tare da sakin mata murmushi, ƙarisawa kusa damazajen su tayi fuska faɗaɗe da murmushi tare da faɗin "Allah ya kai ku lafiya, ya bada ladanzumunci" "amen" suka ce cike da jin daɗi suka juya suka wuce,....
"Wai yanzu za su tafi!" Muryan Yasmin ya doki kunnuwanta da mamaki, murmushi ta saki taredafaɗin "sun tafi ma" "wayyo Allah shine ba su faɗamin ba" tace tare da sakin hawaye da sukacikamata ido daga can, rungumota Shureim yayi da tsan-tsan kulawa tare da bin ta da ido....
"To in sun faɗa mikin me ze canza da rashin faɗen?" Insu tace da mamaki, "ai da ko zuwa seinyi
in ga tafiyan su" tace a hankali, "mun ganin miki" tace tare da sakin murmushi, "muje" Sadamyace tare da kamo hannunta suka nufi barin wajen, "yanzu Nachma ma ta tafi kenam?" Tacetareda kallon Shureim dake mata alamun me ne ne da ido, "ai ba wanda yayi saura daga musehalinmu a gidan" tace tare da sakin murmushi, "Habbubi kowa ya tafi" tace kaman zata saki kuka, kwantar da kanta a kirjinshi yayi tare da faɗin "sorry" "au" Insu tace tare da sakin murmushi....
"To yaushe zaki zo?" Tace a hankali, "ba rana ki yi biyayyan aure baby" tace tare da sakindariya, "Insu!" Tace kamar zata fashe da kuka, amsan wayan Shureim yayi tare da faɗin "kar muyi haka
dake lovely sister" murmushi me faɗi ta saki wanda suka jiyo sautin shi tare da shigewa motadaHisham ya buɗe mata a natse tare da faɗin "ai mun yi ma ango ka sha mai" murmushi ya saki tareda faɗin "baki kyauta ba dai" "na sani" tace tare da sauke wayan fuska faɗaɗe da murmushi....
Zaune suke zagaye da Hajiya da ke kwance sanɓal ƙafan hagu da hannun hagu nannaɗe dabandeji, sauke numfashi Alhaji Jamil da girma ya ƙara kamawa ya saki da ƙarfi tare da faɗin"kai
jama'a" "hmmm mutanen nan fa ba Allah a ransu" Kausar tace cike da damuwa, "in sha Allahaniyarsu se ta koma musu" Abubakar yace cike da damuwa....
"Sun ɗauka SSB na motan ne fa" Alhaji Munnir yace tare da kallon su, "ni ma abinda na hasasokenan" A'isha tace idonta akan Hajiya, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "to ko ma dai mesuke tunanin yi be faru ba tunda gani da lafiyata" "wani lafiya kuma Hajiya dubi fa halindaki keciki" Jabir da tun ɗazu be ce komai ba yace murya ba daɗi, "a'a Jabir ai ba su idda manufarsuba" tace cike da dattakonta, "ai wallahi Hajiya yakamata su fuskanci hukunci akan kuskurendasukaaikata" Yasmin tace a zaffafe, "auta ban son wawta da rashin lissafi" Hajiya tace tare da kallonta....
"Jabir bana son a fidda maganan nan, dan ze taso da abubuwa da yawa ne, kuma na sankusanhakan, in su mata ne ba sa da lissafi ko maza ne yakamata ku fisu hange me ka je ka zo, sosukemu buɗe baki, kuma muna buɗewa zamu zama wawaye, dan wuƙa zamu ɗauka mu daɓawakanmu da kan mu" ta idda magana idonta ma yawo a fuskokin su, buɗe baki Alhaji Jamil yayi daniyyan magana...
shiru yayi saboda abinda ake haskawa a tv, dinnern bikin Yasmin ne, zuba ido suka yi gabaɗayansu a tvn saboda fuskan Insu da aka hasko a lokacin da take bayanin waye Amarya daAngo, bin fuskanta da ke ɗauke da yalwataccen murmushi suka yi da mamaki, "hmm" Lubabatutacecike da tsaban takaici, murmushi Hajiya ta saki lokacin da aka nunota tana taka rawa, "ƙaramana volume Lawisa" Kamil yace a dake saboda bayanin sa ƴar jaridan ke yi, ba musu Lawisadake bin fuskan Insu da ido ta dau tv control ta ƙara volume, tare da ba za nata kunnuwan....
"Ɗiyar president kenan wacce ta ɓace ɓat bayan hari da aka kai mata a hanyar dawowantadagamakaranta, da yawan jama'a na cewa an fiddata ƙasan dan kare rayuwarta ne, se ga ta anhangota kwatsam a bikin yaron governorn jahar Bertuwa inda ta bayyana ma manema labarai
Amaryan ƴar uwace mafi soyuwa a gareta, muna ma Amarya da Ango fatan alher" ɗif akaɗaukefuskan me bayanin, numfashi yawancin su suka saki cike da mamaki....
"Ki na nan ki na fama da ciwo a ta dalilin zuwa inda suke, su suna can suna rayuwarsu, sunmantada halittan ki da iyalin ki a duniya, sannan har yanzu cewa ki ke kar ayi maganan, wai Hajiyaharyaushe ne zamu yi ta dakon wannan kayan ne a kawunan mu! Ya ci ai mu sauke haka" Lubabatutayi maganan a zafafe, "Luba!" Alhaji Jamil yace a tsawace, miƙewa tayi a fusace ta bar wajenkamar zata tashi sama, bin ta da ido suka yi cike da karaya... Murmushi Hajiya ta saki tare da lumshe ido, sauke ajiyan zuciya A'isha tayi tare da faɗin"HajiyaLuba fa tana da gaskiya, bakya ganin yakamata a fidda zancen nan?" Murmushi ta saki bataredata buɗe ido ba tare da girgiza kai, "Hajiya!" Tace murya a raunane, buɗe ido tayi fuskan nanyalwace da murmushi tare da faɗin "wani tabbaci ke gare ku akan ba ta samawa kanta rayuwarda take hangowa ba?" Shiru tayi cike da nazari, jin ba wanda yace komai yasata sakin murmushi
tare da faɗin "a haka ƙaddaran ta zo, ku yi haƙuri ku rungumeta da hannu biyu, kar mu shigarayuwar wa ƴanda ba su san da rubutaccen labarin ba" jinjina kai suka yi cike da gamsuwajikkuna a mace....
Tana shiga bedroom ɗin Hajiya ta zauna a saman sofa zuciya na tafarfasa, so take ta dainajinabinda ke ta so mata se dai kalaman Hajiya na ƙara ta'azzara abun, zare ɗan kwali tayi ta ajiyeagefe tare da ɗaga kai sama, tsayin sakanni ta ɗauka kafin ta sakko da shi a hankali ta ɗauki
wayanta da ta ajiye a gefenta ta danna number ta kara a kunni, ana ɗagawa tace "ga labari zanbaki me zafi, se dai kar ku sake sunana ya fito" tayi maganan a dake, shirun daƙiku tayi daalamun na can take saurara kafin tace "zan turo miki lokacin da ya dace" tana kai nan ta saukewayan tare da rumtse ido, "ki yi haƙuri Hajiya, ba zan iya jure cigaba da kallon damuwoyi asamanfuskokin ku ba, zanyi ne dan kawo ƙarshen komai, ki min afwa, na saɓa umurnin ki a karonabarkatai" tana kai nan ta miƙe ta ɗau ɗan kwalinta ta fice a natse....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fourty three
Buɗe ƙofan bedroom ɗinta tayi ta fito shirye tsaf cikin wani dakakken lace da yayi matuƙar
amsanta ɗinki gown waya kare a kunninta, "dan Allah baby kar ki sa in rikice yanzu fitowanadaga bedroom, in ki ka saka haƙuri yanzu zaki gan mu" ta idda maganan tare da tura ƙofanbedroom ɗin Nafisat....
"Ba ze yuwu ba" tace a natse tare da ma Nafisat dake shirye cikin wata dakakkiyar shaddawandaaka Bazawa nuna me siket alamun ta fito ta juya ta fice, "wai baby meyasa ki ke son mu yi tamai-maita magana guda ne?" Tace tare da zaro wayan ta saka a speaker ta ajiye a hannun kujeratazauna tare da ajiye takalmanta dake riƙe a hannunta ta fara sakawa, "please Insu wallahi
Habbubi na son ganinta ne" muryan Yasmin ya bayyana rangaɗaɗau...
"To mu yi wani abu guda mana" Insu tace hankalinta akan saka takalmin da take, "inaji" taceazumuɗe, "me ze hana ki ma uncle Shureim magana ya kira Yaya Salman, tunda tana yardadaYaya Sadam kin ga se mu taho da ita, amma ke kin san yanzu aka je ma ɗakkota Mommy babadaita zata yi ba, haka zata yi ta jero mana ƙabliyya da ba'adiyya" ta idda maganan tare da miƙewaanatse saboda kammala sakawa da tayi ta ɗau wayan tare da ma Nafisat alamun ta shige suje, bamusu ta shige gaba....
"Okay bari in faɗa mai, dan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 63 Chapter of 109