Share this page
ta mata mekyaucike da kulawa, a sume suka dawo musu da ita daren jiya suka yasarta a ƙofar gida suka tattarasuka yi tafiyan su, ba ta farfaɗo ba se yanzu.... Zame jikinta tayi fuska jaga-jaga da hawaye da majina, "me ya faru a can?" Shila tace taredakallonta ganin ta ɗan samu natsuwa, fashewa da wani kukan tayi tare da rumtse ido tanametuno aika-aikan da Kainuwa ya aikata ma Ziza, "yi magana mana" wacce ke tsaye akanta tacecike da ƙosawa, "sun kashe Ziza, sun cire mata ƙafafu gaba ɗaya" tace murya na rawa, zareidosuka yi a tsorace tare da saurin matsawa baya, fashewa da wani kukan tayi tuna yanda jini kemalala a wajen da yanda Ziza ke asa-asan wahala, shi ko namijin sun mishi kaca-kaca da jiki batainda ba su sare shi ba" ta kuma cewa tsigan jikinta na tashi tare da kanannaɗewa waje guda... "Na shiga ukuna ni Maryama, sare ƙafa kuma! Me Zizan ta musu da zafi haka?" Shila tace cikedafirgici, girgiza kai tayi tare da faɗin "wai ta musu ƙarya bakinta ɗaya da Sa'adatu" tace cikinrishinkuka, "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, Sa'adatu ta zama annoba bala'i a waje, ba mu ga tazamaba, Jamcy, Zinariya Shuwa Ɗan ladi ku zo muje can" Shila tace tare da miƙewa, "a'a kar fa musa kan mu a abinda ba mu san farkon shi da ƙarshen shi ba" Ɗan ladi yace a tsorace, "mu ne dolensua wannan ƙadamin da suke ciki" tace tare da ficewa, bin bayanta suka yi jiki a sanyaye... "Zan wuce wajen aiki yanzu tunda ga Hajiya in za su wuce se ku rankaya tare" Farisat tacetaredakallon su Suwaiba, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "eh zamu je can gidan ma" "to shikenan" tace tare kallon Iƙilima dake bin ta a baya, "Anty Iƙilima da magana ne?" Tace da kulawa, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "saurayin Sadiya ne dama yake hanya na ce ko za ki tsayaku gaisa?" Buɗe baki tayi da mamaki tare da faɗin "Sadiya dama mun yi ɗan uwa ne babulabari!"Murmushi Sadiya dake zaune gefen Yasmin dake sakin murmushin farin cikin jin maganantasaki tare da sadda kai, "ah ma sha Allah, ga labarin bayarwa" Babiya tace cike da farin ciki.... "Allah ya tabbatar da alheri, ke ma ya kawo miki na ki me hankali da natsuwa" Baba Mari tacecike da farin ciki, "amen" suka amsa gaba ɗayansu muryoyi cike da farin ciki, "to in dai ba zejimaba, ina da program ƙarfe 2 kin ga yanzu 12 ta kusa gashi zan shirya zan nazarci maudu'in" taiddamaganan cike da kulawa, "ya dai ce yana hanya ya kusa isowa" tace tare da juyawa inda Sadiyake zaune.... "To Allah ya kawo shi" tace tare da zaro wayanta dake neman agaji, ganin me kiran ya sataɗagawa da sauri tare da faɗin "na'am sir" shirun daƙiku tayi kafin tace "ina hanya ne sir" shirutakuma kafin tace "in sha Allah gani nan sir" tana kai nan ta zare wayan tare da faɗin "an yankatatashi, Anty Iƙilima a miƙa mun saƙon gaisuwana gare shi zamu haɗu gaba in sha Allah, ogayayi kiran gaggawa" tana kai nan ta fice da sauri tare da ƙoƙarin maida wayan a jaka.... "Allah ya tsare" Iƙilima tace fuska cike da murmushi, "ai ta fice ba ta jiki ba, garin ne kamanmaba lafiya" ƙanwar Baba da ba ta daɗe da isowa ba tace tare da kallon Iƙilima, "to ba lafiya kuma!"Babiya tace da mamaki, "wallahi matasa ne gungu-gungu riƙe da alluna a hannu suna wai zanga-zanga" tace cike da damuwa, kallonta suka yi da mamaki, "tabbas anyi haka mun ga tsiraruakanhanya" Jummai tace cike da mamaki, "to me kuma aka musu, mutanen mu da ƙin tsoronmahalicci, me ne ne bawan Allahn nan ya rage mu da shi? Ai wannan gwamna da Allahyabamuse san barka" Babiya tace cike da damuwa.... "A'a Inna ba akan gwamna suke abun ba, akan shugaban ƙasa ne wai" tace tare da gyara zama, "to! Kuma dai, Allah na tuba ai mu zamu ce bana kwalliya ta biya kuɗin sabulu, wato in daɗi yama jama'a yawa fa se su sangarce, shi ɗin kuma me yayi musu?" "akan harin da aka kai mai satinda ya wuce a hanyar shi na zuwa nan Bertuwa halartan bikin ɗan gwamna, kin san ba'a bayyanakomai game da shi ba, a she sun mai mummunan illa se jiya batun ya fito shine fa matasa sukatattara suka nufi government house dan neman izinin fitowa zanga-zanga akan bi ma adalinshugabansu adalci" ta idda maganan cike da san fahimtar da ita.... "Eh ba shakka wallahi da gaskiyan su, kuma ina goyan bayansu ɗari bisa ɗari akan wannanzanga-zangan, Allah ya ba su sa'a, ai mutanen nan ba sa da tsoron Allah" ta idda maganan kamanbatasan me ya kwantar da SSB ba, murmushi Yasmin ta saki tare da zaro wayanta dake ringingganinShureim ne ya sata ɗagawa a natse ta ɗaga mai sallama, amsawa yayi a hanzarce tare da faɗin"ki shirya zan zo mu koma gida yanzu, dan anjima garin nan ze hargitse" "lafiya!" Tace a ɗantsorace, "matasa ne za su fara zanga-zanga anjima da ƙarfe 1, yanzu Daddy ya ba su izininyi" "subhanallah" tace tare da kallon Babiya dake tambayanta lafiya, "kin ji?" Yace da ɗan ƙarfi, "eh"tace tare da sauke wayan, "lafiya Yasmin me kuma ya faru!" Jummai tace cike da damuwa.... "Zanga-zangan ne ya tabbata" tace tare da danna number Habibu yana ɗagawa tace "zokaɗauki su Hajiya" tana kai nan ta zare wayan... Danna number HDn school ɗin su Umar tayi yana ɗagawa ta gaishe shi tare da tambayanshi halin da school ɗin ke ciki, "yanzu zamu sallami ɗalibai" yace a natse, "okay dan Allah a riƙeUmarAbdussamad za mu turo a ɗauke shi yanzu" "to ku hanzarta" yace tare da katse kiran, "ke Yasminkin samu a duhu" Babiya tace cike da damuwa, "Hajiya ba komai Daddy ne ya ba su damanyinzanga-zangan shine Habbubi yace yakamata mu koma gida, kin san akwai ƴan jiran wannandaman su aikata abinda suke so" "ƙwarai kuwa ƴan ta da tarzoma na gefe da gaskiyan shi" tacetare da fara tattara kaya, saurin ɗaga kiran da Habibu ya mata tayi tare da faɗin "ka iso neHabibu?" "Eh gani a ƙofar gidan" yace cike da natsuwa, "to bari su fito dan Allah in ka ajiyesukaɗakko Umar na ce musu su ajiye shi za'a zo a ɗauke shi" tayi maganan cike da damuwa a muryanta, murmushi ya saki tare da faɗin "gani tare da shi lokacin da ki ka kiran ina hanyar school ɗin su ne" wani nagartaccen murmushi ta saki tare da faɗin "Allah ya saka da alheri Habibu, Allah ya kula maka da na ka bari su fito" tana kai nan ta sauke wayan tare da kallonBabiya "suna waje suna jiranku" tace tare da kallon wayanta da ya ɗau ruri, "to ku mu hoɓɓasa, Iƙilima Allah ya ƙara dangana, ina ganin se nan da ranar bakwai kuma" ɗaga wayan tayi takaraakunni, "to Hajiya Allah ya saka da alheri ya ƙara zumunci" Sadiya da Iƙilima suka ce cike dajindaɗi.... "Gani nan" tace a hankali tare da miƙewa, "ku muje mu sauke ku a hospital" Yasmin tace taredazare wayan a kunninta idon ta akan su Halima dake ƙoƙarin miƙewa, jinjina mata kai sukayi dakulawa, juyawa ga su Sadiya tayi fuska ɗauke da murmushi tare da faɗin "za mu yi waya, danAllah ban da damuwa, idan anyi waya da ɗan uwan na mu a gaida mana da shi yau dai Allahbeƙaddaro haɗuwan mu ba" jinjina mata kai suka yi cike da yabawa da karamcin su, "ku muje" tacetare da gyara zaman glass ɗin dake saman fuskanta suka rankaya gaba ɗaya, suna fita ta nufi motan su Babiya ganin duk sun samu waje ya sata shafa kan Umar tare da faɗin "tunda kasamutime yau ka yi muraji'an haddanka da ga izifi biyar zuwa goma" jinjina mata kai yayi fuska yalwace da murmushi, "se munyi waya Hajiya, Anty Suwaiba mun gode Allah ya huta gajiya" jinjina mata kai suka yi cike da jin daɗi, "Habibu ina ga ka fara sauke Baba Mari a gida tukunsekuwuce can" tayi maganan idonta ta akan Habibu.... "Ai suma waƴan nan duk gidajen su za'a sauke su, ana cikin wannan yanayi ina za su? Yausheakasan ranar da abun ze lafa" Babiya tace idonta akan Yasmin, jinjina mata kai tayi tare da faɗin"shikenan se na kira" "to ki gaida Muhammad ɗin duk da mun gaisa ɗazu da ku ka zo" Babiyataceda ƙarfi murmushi ta saki tare da jinjina mata kai saboda juyawa da tayi.... A hanzarce ta faka mota a parking lot ɗin dake katafaren wajen, tana fitowa wani ma'aikaci yaiso wajen da sauri ya amshi jakan hannunta tare da mata sannu da zuwa, wuce wa ciki tayi dasauri ya dafa mata baya, shiga lefter tayi ta danna number inda take son zuwa, suna isa ƙofanyabuɗe suka fito, ma'aikata ne zazzaune a saman kujeru gaban su da computer kowa na aikindakegaban shi, duk inda ta gitta se an gaidata, amsawa take cike da haba-haba fuska ɗauke damurmushi, tura ƙofan glass ɗin da ake hango ciki tangararan tayi ta shiga baki ɗauke da sallama, wuce wa saman haɗaɗɗen kujeran dake fuskantan ƙofan tayi ta zauna bismillah ɗauke a bakinta.... Ajiye mata jakan yayi a girmame tare da ƙara mata sannu da zuwa, murmushi ta sakin mai cikeda kulawa, juyawa yayi ta fice a natse, jawo file ɗin da aka ajiye mata tayi ta buɗe a natsetabazaidanu, turo ƙofan wani kamilin dattijo yayi tare da faɗin "Farisat" ɗago kai tayi fuska ɗaukedamurmushi tare da faɗin "sorry sir cinkoso ne a hanyar wallahi amma ina ba da haƙuri" "okaytasoki ji maudu'inki na yau" da mamaki ta miƙe tare da faɗin "an canza ne?" "Eh muje" yace taredanuna mata hanya hannunshi riƙe da ƙofan ficewa tayi ya kullo office ɗin suka nufi ɗakintsaretsare.... Suna shiga taja kujera ta zauna, zamanta babu wuya samari uku da manyan mata biyar wandazasu iya kai 40 a haihuwa suka shigo, gaidasu tayi a girmame ta ƙara tattaro natsuwanta danfuskantar abinda ya tara su a wajen da kyau, gyara murya wanda ya kirawota yayi tare dafaɗin"mun tashi da wani al'amari me matuƙar ɗaukan hankali yau a ƙasa gaba ɗaya dan ba zanceagarin Bertuwa kawai ba, wakilan mu na sauran jahohi sun tabbatar mana da abun ya shafi har inda suke, dalilin da yasa muka canza maudu'inki na shirin (me ke faruwa a ƙasata) kenanakansakin da maza ke yi ya koma kan abinda ke faruwa, mun jiyo a majiya me ƙarfi akan zanga-zangamatasa suka fita akan harin da aka kaiwa me girma shugaban ƙasa akan hanyarshi ta zuwawannan gari na mu dan halartan bikin ɗan governor Sharifudden Muhammad... A wan can lokacin ba'a bayyana da shi a motan ba, an dai tabbatar da mahaifiyar shi ta ji raunikaita ma ba'a yarda an bayyana halin da take ciki ba, se dai jiya wani bawan Allah ya wallafawani bidiyo a shafinshi akan wannan harin ya shafi shugaban ƙasa kuma anyi mai babban rauni anrufe hakan ne dan kar hankulan ƴan ƙasa ya tashi, kun ji dalilin, yanzu haka me girma governorya bawa matasa daman su fito ƙwansu da ƙwarƙwatan su su nemi adalci ga shugabansuadali wanda adalcinshi ya kewaye su, sannan ya hana duk wani jami'i fito da makami dan hantarakokyara garesu se dan kare su, mun tattara miki rahotannin ki na da lokaci dan nazarta kafinlokaci ya cika" ya idda maganan idon shi akan Farisat, sauke numfashi a hankali tayi cike da mamakinjin wani zancen kafin ta jinjina kai a hankali, "mun san zaki iya Farisat, ki tabbatar shirinyaɗauki hankalin al'umma daughter" ɗaya daga cikin matan da suka shigo tace cike da ƙarfafa gwiwa, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "in sha Allah" tura mata duk wani rahotanni da sukaharhaɗa suka yi tare da miƙewa suka fice, tattara takardun tayi ta fice dan komawa officeɗinta.... Suna tsayawa a ƙofan hospital ɗin Halima da Nafi suka sauka, ƙasa da glass ɗin gefenta Yasmintayi tare da faɗin "ku ƙara gaidamun Yaya Sudais da jiki" jinjina mata kai suka yi tare da musugodiya suka wuce, jan motan drivern sojan yayi suka ɗau hanya, "akwai matsala fa" Shureimyacetare da riƙo hannunta, "Allah ya raba mu da ita me ya faru!" Tace da damuwa, "be kamataDaddyya ba su dama ba, yakamata a ce ya kwantar musu da hankali ne yanzu wannan daman dayabasu ba mu san me ze iya haifarwa ba, wasu in sun fito yin zanga-zangan lumana wa su ba shi neazuciyoyin su ba" ya idda maganan da damuwa, jinjina kai tayi tare da faɗin "ko ya hana suHabbubi ba za su hanu ba, sun ɓara ne, dama suna ta neman hanya se yanzu hanyar ya buɗe, hanawan da ze yi wataƙila ya shafi mutumcin shi a wajen su, kallon da suke mai ya canza kalakaga me aka yi kenan? Hukuncin da ya yanke shine dai-dai, jami'ai su fita su kula da kyau kar ɓatagari su ɓata musu kyakkyawan ƙudirinki su, jinjina mata kai yayi cike da gamsuwa tare darungumota, "oh Allah" tace tare da ɗago wayanta dake hannunta da sauri, number Sahabeetalaluba ta dannawa kira.... Yana ɗagawa tace "kana ina?" "Yanzu na shiga gida" yace a hankali, "to kar ka sake ka ce zakafitako bakin gate" tace a dake, "oh Umma in yi me?" Yace kaman ze saki kuka, "na dai faɗa makaka ce to kawai" "to Umma in sha Allah, amma da ina son zuwa gidan Mommy ne anjima" "tanawajenaiki" tace a natse, "in ta dawo" yace a hankali cike da magiya, "ka je" tace tare da zare wayan, murmushi Shureim ya saki tare da faɗin "manya" murmushi ta saki tare da kara wayan a kunni, ana ɗagawa tace "kana ina Uncle?" "Office amma yanzu nake son komawa gida" muryanSadamya bayyana ras, "okay ka hanzarta Uncle wajen babu daɗi" "okay in sha Allah" yace da kulawa, zare wayan tayi ta katse ta danna number Salman.... Se da ya kusa tsinkewa ya ɗaga tare da faɗin "sorry matan Mejor ina duba patient ne" "babudamuwa, ba kasan me garin ke ciki ba ne halan?" Ta je fa mai tambayan tare da riƙe hannunShureim dake yawo a jikinta, "wallahi na ji wai zanga-zanga ko?" "Au ka ma ji ka ke hospital haryanzu!" Tace da mamaki, "yanzu zan koma gida" yace tare da sakin murmushi, "to ka hanzartaitadai matar taka na office" "ai sune kanun labarai se ta dawo zamu ji yanda ake ciki" murmushi tasaki tare da faɗin "kafin ta dawo ma in kana so zaka ji a meke faruwa a ƙasata" "haka ne fa" yacetare da sakin murmushi, "to ka hanzarta dai ɗan Allah" tace da kulawa, "yanzu in sha Allah" yacecike da jin daɗin kulawanta.... Zare wayan tayi a natse ta fara neman number, amshe wayan Shureim yayi tare da faɗin"yaisahaka" "Amen da Hamid zan kira in ji ko sun fita school" tace a marairaice, "no suna gida" yacecike da jin daɗin kulawan da ta nuna a gare su, "su Mihna fa?" Ta jefa mai tambaya tare dakwanciya a saman ƙirjin shi, "waƴan nan fararen kurayen ne za su ji wannan labarin su tsaya" yace tare da sakin ƙaramar dariya, "kai ma ai haka ka ke" tace tare da sakin murmushi, murmushi ya saki tare da faɗin "ke ma kuma ba" yayi maganan tare da mintsilinta a baya, zabura tayi tareda sakin dariya..... A ɗan tsorace suka tura ƙaramin ƙofan dake jikin gate ɗin dake ƙofar gidan suka shiga, sedasuka zo ƙofar gidan sannan tsoro ya diran musu a zuciya, a hankali suka shiga ciki, suka isabakinƙofan da ze sa da su da parlorn zuciyoyinsu ya tsananta bugu, shahada Ɗan ladi yayi ya turayaafka ciki, dafa mai baya suka yi a ɗan tsorace, ihu Ɗan ladi ya saki tare da sauri juyawa, karoyaci da Shila dake ƙoƙarin shigewa, saurin riƙota yayi tare da faɗin "mu tafi daga nan Shila akwai babban matsala" "Ɗan ladi ba wata matsala" tace murya na rawa, kauce mata hanya yayi idonshi a rumtse, zubewa a wajen tayi saboda wani mugun jiri da ya dibeta, kuka sauran suka saki tareda ɓame bakin su da tafukan hannayesu, Ziza ne kwance cikin jini ƙafafunta rabe da gan-ganjikinta ta sanƙare da alamu ta jima da mutuwa, se Abdull dake yashe kusa da ita jina-jina.... "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un me suka musu haka!"Zinariya tace cike da ruɗu, "kar ki taramana jama'a Zinariya, wannan shine ƙarshen maci amana, ta zo duniya a banza ta tafi a hofi, kudubi irin ƙarshen da tayi duk ta dalilin biye ma Sa'adatu da tayi, ba kalan jan kunnin da banmataba, na faɗa mata Sa'adatu ba kalan wacce ake shigewa ba ne, na jima ina faɗa mata tayi nesadaita amma tayi fir ta murje ido, ni Shila na zama abar takun saƙa a wajenta to ga inda rashinjinmagana ya kaita, duk wacce take shirin kai kanta inda Allah be kaita ba ya isheta izina ga faruwan wannan, Ɗan ladi, kira su Gambo su zo a tattarasu a haƙa rami a zuba su, ni wannaɗinma ban san ko waye ba" Shila tace tare da kafe Abdull da ido, zare ido Zinariya tayi tare dafaɗin"yana numfashi!" Kafe shi da ido suka yi cike da tsoro, ganin da gaske yana jan numfashi daƙyarya sa Ɗan ladi kinkiman shi ya fice da shi da sauri.... Dafa mai baya Shila tayi a hanzarce, tana isa yana ƙoƙarin shiga driving side, "idan ka kaishi indaka ke tunani suka tambayeka meya same shi me zaka ce musu?" Ta jefa mai tambayan daƙarfi, tsayawa cak yayi zuciya shi na tsananta bugu, "ka dinga abu da tunani Ɗan ladi in ba hakabaseka saka kan ka a uku" tace tare da ƙarisawa kusa da motan, "duba jikin shi ba waya?" tacetaredagyara tsayuwa, fara bincikawa yayi a hanzarce, yana cin karo da waya ya fiɗɗo tare da faɗinakwai, duba number da yayi maganan da shi a ƙarshe ka kira" tace tare da kallon shi, ba musuyaduba ya danna kira... Miƙa mai hannu tayi a natse, miƙa mata yayi tare da bin ta da ido, ana ɗagawa ta buɗe baki dazumman magana muryan Sa'adatu da ya doki kunninta ya taka mata burki "Abdull kana soinyi blocking ɗinka ko? Na ce maka kar ka kira ni se in ni na neme ka da kaina, zan dinga kirankainna samu time" tayi maganan muryanta na bayyana takaicin da ta ji, murmushi Shila ta saki tareda faɗin "lallai Sa'adatu" "what! Shila! Me ya kai wayan shi hannunki?" Ta jefa mata tambayan ƙarshe muryanta a kausashe, "kwantar da hankalin ki, aikin Allah ya kawo wayan hannuna, kinkashe Ziza hankalin ki ya kwanta, shima wataƙila ba ze kai labari ba" ta idda maganan muryababu wani damuwa... "Me ki ke nufi! Ba me wayan wayanshi" Tace a ruɗe, waƴanda ki ka san suna nemanki tuntuni jiyaAllah ya ba su nasaran isa ga abokiyar cin mushenki kuma sun mata kisan wulaƙanci, shimawannna ɗin da wuya ya kai se dai buwayan mahalicci" ta idda maganan muryanta na canzawa, "me! Ziza ta mutu! Ki na nufin Yaya Sarari ya kasheta!" Ta jero tambayoyin a ruɗe "koma wayeyakasheta ke ce silar mutuwanta, wallahi hakkin ran Ziza kawai ba ze barki ki rayu lafiya ba, yarinya tana zaman-zamanta ki ka shiga jikinta ki ka ɓata mata tunani daga ƙarshe kumatamutu ta silarki" tana kai nan ta katse kiran ta jefar da wayan a gefe... "Ya zamu yi da shi?" Ɗan ladi yace cike da damuwa, kallon yanda yake jan numfashi tayi kafintace "asibitin dole za'a se dai bakin mu ya kasance ɗaya mun tsinceshi ne a saman titi cikinhalinda yake ciki, maida mai wayan shi inda ka gani, in ya so su sa nemi inda ahalin shi suke" taiddamaganan tare da juyawa ta inda su Zinariya suke tsaye.... "Ku koma ciki Gambo ze zo shida zugan shi za su kwasheta su binneta" ta idda maganantaredaƙoƙarin shiga mota, "haka za'a binneta ba'a mata wanka da sallah ba!" Jamcy tace tare dagogehawaye, "wa ki ka taɓa ganin amma wannan gatan inbya mutu a cikin ku? Wanka kan mukanƙoƙarta, amma sallah wa muke da shi fa ze sallace mu? Ita ko wankan ma ba yiwuwa ze yi ba, dan a yanda taken nan wa se iya mata wanka? Ko zaki iya?" Ta idda maganan tare da kallonta, girgiza kai tayi da sauri hankali a tashe, "to kin gani kenan, ni ma ba iyawa zanyi ba, zuciyanmusulunci ne ma ya sa ni nemo masu binneta amma in ba haka ba kallon inda gawanta yakebayi zanyi ba, ba wanda be san abinda ta shuka min a cikin ku ba" ta idda maganan tare da shigewamotan Ɗan ladi ya ja suka bar wajen, juyawa suka yi suka koma ciki jikkuna a mace.... Tunda lecturer ya fara ba su darasi babu wanda ya motsa da nufin fita se da 2:00pmdai-dai tabuga, yamutsa fuska tayi tare da miƙe ƙafafunta da suka yi tsami, "sorry mu mun saba" Nachmatace tare da sakin mata murmushi, harara ta dallamata ta miƙe a hankali ta ɗau jakanta tagoyasuka fice a natse, kai tsaye masjid suka yi suna idar da sallah suka wuce restaurant, suna shigasuka hangi Hisham zaune shi da Mairah dake ta cin indomien da yasa aka haɗa mata, murmushi Nachma ta sakin mata tare da jan kujera ta zauna, zama Insu tayi cike da gajiya, "Ami" tacetareda ƙoƙarin kamota... "Wash Mairah nayi matuƙar gajiya" tace kaman zata saka kuka, kwaɓe fuska tayi tare da saddakai ƙasa, miƙa mata hannu tayi a hankali saurin kamawa tayi tare da sakin murmushi, faɗama'aikatan abinda za'a kawo musu Nachma tayi a gajiye Hisham kuma ya cigaba da ba Mairahindomien, jan kujera Labib yayi ya zauna tare da faɗin "guys akwai damuwa fa"... "Wacce kala?" Nachma tace tare da janye wayanta saboda abincin da ma'aikaciyan restaurant ɗin ta zo ajiyewa, "zanga-zanga ake yi a ƙasan" yace tare da buɗe wanda aka ajiye mai a gabanshi, "zanga-zanga! Name kenan!" Nachma tace da mamaki, "akan mr president mana, matasasuncesuna son sanin halin da yake ciki, tsayin lokaci ba su gan shi ko a hoto ba, sannan an tabbatar harin nan da aka kai a hanyarsu ta zuwa Bertuwa har da shi ta sama" ya idda maganan cikedatabbaci, kallon Insu da kaman ba ta san me yake cewa ba Hisham yayi tare da faɗin "Allahmeiko" "wallahi sun mun dai-dai, ni fa tunda aka ce SSB shi ya ci zaɓe ban ƙara ganin shi ko ahotoba bare kuma a hoto me motsi, wataƙila akwai wani abu da suka mai ne ƴan iska ƴaƴantiti, wallahi da a gida nake se na fita anyi dani" ya idda maganan cike da gaskiyan shi, murmushi Insuta saki tare da faɗin "kana zagi ƴarka na kallonka" murmushi ya saki tare da faɗin "sorry Mairahƴancin ku muke san nema muku, dan gaba ku ji daɗin ƙasar" dariya suka saki gaba ɗayansutareda kallon shi.... "Wallahi ku daina dariya mutanen nan babu Allah a ransu, ko din yanda ya shinfiɗo aiki a ƙasannan daga hawan shi ba za su ƙyaleshi ba wallahi, gaskiyan wanda ya wallafa maganan ankai mai harin ne da yace "ƴan iska duk mun san ku mun san a inda ku ke rayuwa, kun cuce mu kunɓata mana rayuwa iyayen mu na kuka na Allah ya wadai da yanda muka maida kawunan mu nankosune sanadi, sun killace na ku sun kare su da ga dukkanin wani rayuwa na banza, shi ya jawomuajiki ya nuna mana mu ma ƴaƴane ya hana mu shan ko paracetamol da sunan shaye-shayeyasaan kama masu siyarwa sannan ya nema mana abubuwan yi shine ku ke neman hanyar cutar dashi wallahi duk wanda yayi gigin taɓa lafiyarshi a cikin ku se mu babbakashi da ran shi" yaiddamaganan tare da kallon yanda suke bin shi da ido, "yaushe aka yi haka!" Hishamyace da mamaki, "bari ka gani" yace tare da zaro waya, buɗewa yayi ya tafi kan videon da ya sauke daga tiktokyakunna ya miƙa musu, kallon bayanin cika aiki suka yi daga farko har ƙarshe, sauke numfashi Insutayi tare da faɗin "kaman na san fuskan" ... "Ze iya yuwuwa" Hisham yace tare da miƙa ma Labib wayan, " a gaskiya akwai matsala kuwa" Nachma tace jiki a sanyaye, "har maganan Dadynka se da na gani" Labib yace tare da kallonHisham, "Daddy!" Yace da mamaki, dariya ya saki tare da faɗin "eh ya ba wa matasan garinshi cikakken dama na zanga-zangan lumana akan neman sanin halin da shugaban ƙasa ke ciki" "ohAllah" Hisham yace tare da kallon Insu, dariya ta saki tare da zaro wayanta dake ruri, ɗagawatayi a zumuɗe ta kara a kunni tare da faɗin "baby!" "Baby Insu" ita ma tace

Chapter 77 of 109