Share this page
Muryan Yaya ya dira a kunnuwantacike da kaushi, ba ita da ya jefawa tambayan ba hatta da su Babiya se da suka razana, juyowatayi a hankali tare da sadda kai cike da ɗan tsoro tace "ba mu gama exmas ɗin da wuri ba ne, bayannan kuma na biya gida na yi ma Mama barka da dawowa, ta dawo tin satin da ya wuce bansamuzuwa ba" ta idda maganan cike da ladabi.... "Daga ina ki ke?" Ya kuma je fa mata tambayan idon shi na yawo akan fuskanta, "daga makaranta" tace a hankali, "ƙarya ki ke maƙaryaciya" Salman yace a harzuƙe tare da zaburakaman ze kai mata bugu, girgiza kai tayi tare da faɗin "wallahi daga can nake Yaya Salman, bansan me Rahma ta faɗa maka ba, amma daga can nake" bin ta yake da kallon tsana da ƙyamatunda ta fara maganan, har ta kai aya, "na ce miki tace mun wani abu ne?" Yace zuciya a mugunɓace, girgiza kai tayi tare da ɗan ja baya kaɗan, "me ke faruwa ne Salmanu? Kun samu a dubu, itaSa'adatun ba makaranta take ba? Yau fa tace suna sa jarabawa tun safe ta fice" Babiya tacetareda nufo su.... Girgiza kai tayi tare da saurin faɗin "wallahi can na je Hajiya, ban san me na ma Rahma batakefaɗa mai irin waƴan nan maganganun, haka kwanaki tace mai bana zuwa school yayi ta bincikana, yau ma gashi ta faɗa mai wani abun" ta idda maganan jiki a sanyaye, ta cikin zuciya kuwabanda tsinemai ba abinda take.... "Salmanu ai da zuwa kayi ka ganewa idonka da ze fi, zato ba daɗi ne da shi ba ko me kyaunebaremara kyau" Babiya tace tare da kallon shi, jin Babiya ta yi maganan yasa ta juyawa ga Yayamurya a sanyaye tare da faɗin "Yaya wallahi na je school, yau fa shine kaɗai daman da nakedashi na cika burin Anty a kaina, meze sa in yi wasa da wannan dama" gigitaccen marin da yakwasheta da shi ne ya kasa ba ta daman idda abinda take son cewa, a razane suka mimmiƙetareda zube mai ido, kama kumatun tayi a matuƙar razane tare da kallon shi, "Yaya!" Farisat tacetareda ƙarisowa wajen da sauri, riƙe shi tayi tare da faɗin "Yaya" saboda yanda jikin shi ke ɓari.... "Meke faruwa ne wai?" Balarabe yace tare da kallon Salman, "wannan yarinyar da ku ke gani munafukace ta ƙarshen ƙarshe, shegiyace wacce ba ta gaji arziƙi ba, ba tun yau take manawasada hankali ba, ta daɗe da maidamu shashashu, ba makarantar da take zuwa, duk in ta fitanansheƙe ayanta kawai take, a idanun mu babu mumina kamanta, a bayan mu babu sheɗaniyar datakaita, yawon barikin ta kawai take tare da fakewa da school".... Ya idda maganan azabure, girgiza kai tayi kuka na ƙwace mata tare da faɗin "wallahi Yayabahaka ba ne, wallahi Hajiya ban san akan abinda yake magana ba, wallahi ku yarda dani, tayazanfara aikata haka bayan ceto rayuwata da faɗawa harkan da Anty tayi, ni wacce iriyar butulucedazan butulce mata har haka, Farisat ke ma kin san ba zan aikata ba, Yasmin" ta idda maganancikin rishin kuka... Tsaki Habiba ta saki dan tasan wannan ranar na tafe, amma ba tayi zaton shi da wuri hakaba, kallonta Suwaiba tayi tare da faɗin "ba fa wani kukan munafurci da zaki tsaya kina mana, ki faɗi gaskiya kawai" "haba Anty Suwaiba kar ƙiyayyan da ki ke mun ta kai ki da jifana da mugunɗabi'airin wannan mana, ko na rasa nayi na zaɓi wannan abun da ya maƙalamun, Hajiya wallahi bansan akan me yake magana ba, kalli yanda yasa Yaya yau ya ɗaura hannun shi a fuska na, abindabe taɓa yi ba tunda Allah ya haɗa mu" "subhanallahi kun rikita mu" Babiya tace cike da gajiyawa.... Na miki sharri ko? Kuma kin je makaranta ko?" Salman yace tare da kafeta da ido, jinjina kai tayi tare da sadda kai ƙasa, "okay Hajiya dubi wacce taje makaranta yau, wannan wacece!" Ya iddamaganan a harzuƙe tare da miƙa ma Babiya wayan, amsa tayi jiki na ɓari tare da kallonSa'adatuda ta shige SD hotel, "subhanallahi Sa'adatu ce" tace da mamaki, "ba anan mamakin ya ƙareba" yace tare da amsan wayan ya kunna mata wani" "lahaula wala ƙuwwata illa billah" tace jiki naɓari, amsan waƴan Balarabe yayi tare da kafe wayan da ido, miƙa ma Salman wayan yayi taredakallonta zuciya a mugun ɓace yace "draman ya isa haka, zaki faɗa mana abinda ya kai wajennanne ko se kin ci uban jikin ki?" "Wannan da ka ke gani ta wuce duk tunaninka, daina ma matabarazana, asalin munafukace da kake ganinta" Salman yace tare da juyawa ta inda suke tsaitsaye ya rattafo musu komai, banda salati ba abinda suke, "wannan kawai ku ka sani, ba kusanshaye-shayen da take yi ba" Baba Mari tace cike da ƙunan zuciya.... "Shaye-shaye Mari!" Babiya tace cike da kaɗuwa, zuba mata ido suka yi dan jin bayani, "tabbasshaye-shaye, duk wannan barcin da take yawan yi kina cewa shawarace, ba shi ba ne, kayanmaye take ɗirka ta yi ta barci, ba yanda banyi da ita akan ta daina ba amma taƙi" tace jiki amace, fashewa da kuka Yasmin da Farisat da Nafisat suka yi a tare, da gudu Farisat tayi inda taketareda girgizata da ƙarfi, cikin matsanancin kuka tace "Sa'adatu me ki ka wa kan ki? Me Anty tamiki da ta cancanci wannan sakayyan daga gare ki? Me ya shiga kan ki har ki ka aikata waƴannanmunanan ɗabi'un?" Tureta da ƙarfi tayi tare da faɗin "kar ki tarwatsa mun kai da hayaniyamana, me ta mun da har ki ke tambayata? Suna ta nema kuma ta samu, se me? Rayuwata ba na ɗayadaga cikin ƴaƴanta ba ne, na taɓa cewa ɗayan ku ta kaucewa tarbiyyan da ta ba ta? Wannanrayuwatace, ba wanda ke da daman shiga a cikin ku" ta idda maganan murya na nuna zallanɓacin ran da ta shiga.... Da ɗinbin mamaki suka bi ta da ido, "Sa'adatu!" Yasmin tace hawaye na kwarara a idonta, ƙaramin tsaki taja tare da kauda kai, "kin san me ki ke faɗa kuwa? Anty ki ke jifa da irin wannan kalaman? Anty fa, matan da ta tsamoki daga ƙunan rana ta kawo ki inuwa, wacce ta damƙamiki sabon rayuwa me cike da ƴanci, wacce ta rungumeki matsayin ɗiya me cikakken ƴanci kamar yanda ta rungumi na ta, ta hanaki kuka ko na second guda, yau ita ki ke kira da ta temakeki nedan tayi suna? Wani suna ki ke nufi?".... "Lallai yau na ɗanɗani zafi da raɗaɗin butulci, a she haka yake? Yau rana ta farko da na yi farinciki da tafiyan da Anty tayi ta barmu saboda ba ta ga wannan baƙar rana me baƙin duhuwaba, natabbata da ta riski wannan rana da se tayi fatan mutuwa kafin zuwan shi" ta idda maganancikinrishin kuka.... "Ya isa haka" Suwaiba tace tare da rungumota, kuka akan wanda be san daraja da kimanhawayemasu daraja ba babu amfani, ku daina wannan kukan haka dan butulci a jininta yake tundakukaga haka gadan shi tayi, babu ɗigon kunya ko kaɗan a idanunta" ta idda maganan tare da sharemata hawaye, "to dama ai kunyar mara kunya a sara, ku kunyar ne da ku har da ku ke ikirarinbana da shi, da da sauran kunya a idanun ku yatsanku ba zaku bari ya tako gidan nan ba barekuda kan ku, bayan kun gama zagin mamallakiyan gidan da aibantata da wulaƙantata bayanmutuwarta ga ku zazzaune a gidanta hankali kwance, tabbas na ga waƴanda ke da kunyakuwa" Sa'adatu tace cike da ƙunan zuci tare da watsa ma Suwaiba razanannun idanunta da sukari neda ɓacin rai.... "Ke ba wannan shirmen muka tambaye ki ba, ina ki ka je?" Balarabe yace tare da kafeta daido, "kayya Balarabe kai ma akwai dawo da hannun agogo baya, ina ce nan yanzu Salman ya gamafaɗa mana ina take zuwa, inda ta ga dama take zuwa da sunan makaranta ta bar Yaya Abdussamad yana dakon biyan kudi, wallahi kin cuci Amina, kin yaudareta, alhakinta kaɗai bazebarki ki rayu cikin aminci ba" Habiba tace cike da takaici, "juyawa inda take tayi a fusace taredafaɗin kuna ta mai-maita na ci amananta wai ni na gayyato ta rayuwana ne? Ko bata shigorayuwata ba zan rayu irin rayuwar da nake so da fata, ita ta kawo kanta dan neman daukaka, danhaka kar wanda ya ƙara cewa na butulce mata ko na yaudareta ko na ci amananta" bata kai da rufe baki ba Sadam da ya iso wajen a fusace ya sauke mata marika biyu masu ratsa ƙwaƙwalwa, cikin matsanancin ɓacin rai ya nuna ta da yatsa jiki na ɓari yace "ke dan uwarki ki iya bakinki"... "Ki san irin kalaman da zaki dinga furtawa mahaifiyarmu, sun ce miki batulun ba ki amsa sunanki ba ne?, Ke ai kin wuce butulu kawai, azzaluma, maha'inciya, ma zanbiya, maƙaryaciya ce kegabaɗaya, yau inda kalman da suka fi wannan ki cancanci fiye da su, tirr da MUGUWAR TSOKARdakedashe a ƙirjinki, tirr da MUGUWAR TSOKAR da ya mantar dake halarci da wacce mi ke niyyar butulcewa ta miki, tirr da MUGUWAR TSOKAR da ta rufe miki alheran da aka miki ta bayyanamiki sharri dake tattare da ke, me ba mutum ba ce dabbace, ta dawa wacce jahilci ya ma ƙawanya" ya idda maganan rai a ɓace idanu sun kaɗa sunyi jazur, "ni ka mara Sadam!" Tayi maganan tare da kafe shi da ido, nufarta yayi gadan-gadan tare da ƙoƙarin zare belt, da sauri Farisat da Yasmin suka riƙe shi, suna kuka.... Goge hawaye Babiya tayi tare da faɗin "Sa'adatu wani irin tabo ki ka wa kan ki haka? Ina miki kallon me hankali da natsuwa da sanin yakamata Sa'adatu, wani furuci ki ke furtawa ga Aminada ta rungume ki matsayin ɗiya ta baki dukkan yardanta?" "Hajiya ban nemi duk abinda ki kaanbato daga wajenta ba, ita tayo karanbanin sawo kanta a rayuwana" tayi maganan cike dajinzafin marin da Sadam ya mata, kallonta suke da dukkanin mamakin su.... Girgiza kai Yasmin tayi tare da faɗin "wannan ba kalamanki ba ne Sa'adatu, wannan ba halayenki ba ne, ba ke ba ce Sa'adatu, an canza mana ke, me ki ka sha ne haka?, Matar da ta zame miki uwata zame miki uba, ta baki gatan da kike yabawa kullum, ta miƙa miki iyalanta matsayin iyalanki, ta rungumeki a ƙirji dan kiji ɗumin uwa yau ita ce ki ke jifa da waƴan nan kalaman? Sa'adatuAnty fa, Anty ce yau ta zama maƙiyiyan ki har ki ke jifanta da muggan kalamai haka?" Tayi maganan tare da ƙarisawa kusa da ita tare da kafeta da idon dake zuban hawaye, kalloncikinidonta tayi kai tsaye tare da faɗin "ban nemi dukkan wannan ba" lumshe ido Yaya dake binsudaidanu yayi tare da faɗin.... "Ban san inda na gaza ba, ban san kuma ta inda Amina ta gaza miki ba, abinda na sani shinedakyakykyawan zuciya muka amshe ki, muka mutuntaki a idanun duniya, muka darajtaki, bazancemiki ba mu can-canci wannan butulcin ba, saboda kasantuwar mu na ƴan adamgaba dayanmu, wataƙila akwai wani abu da ke ɓoye wanda ba musan da shi ba, Allah ya jiƙan Amina ba tashigalamarin ki dan neman suna ko ɗaukakan da ki ka ce ba, ta shiga ne dan nema miki adalci, takawoki gidanta ne dan kar kaɗaici yayi sanadiyyan rasa rayuwarki, se dai yau gaki kin tsaya a tsakiyaninda ta rayu dake kina faffaɗan maganganun da ranki yake so ba tare da kyakykyawan tunani ba, mun gode Sa'adatu, mun gode da dukkanin wani sakayyan da ki ka nuna mana yau, wandazaki nuna mana gobe ma mun gode"... Ya idda maganan tare da goge hawayen da ya zubo mai, kuka gaba ɗayan su suke, hatta Umar kuka yake dan sabon abu ne a wajen su, abinda ba su taɓa ji da gani ba ne ya riskesu, juyawatayi da nufin shigewa ɗaki, "ba zan iya cigaba da rayuwa dake ba, bayan duk wannan abun da yafaru"Yaya yace a dake, juyowa tayi fuska faɗaɗe da murmushi tare da faɗin "bana jin na ce ina dawani abun yi a gidanka bayan duk abinda ya faru" tana kai nan ta juya ta shige ciki, fashewa da kukasuFarisat suka yi me tsananin ƙuna zuciya na tafarfasa.... "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa ahalifni hairan min ha, Yayame ke shirin faruwa damu ne? Antyn ta tafi, Ibrahim ya tafi, Insu tayi nisa damu, yau ga Sa'adatuna ikirarin tafiya ta bar mu, ubangiji in lefi muka maka ka yafemu mun tuba ba zamu sakeba, Anty na yawan ce mana, familynmu a cike take, mun cika mun zama family guda, ga ta gaYayaga Sa'adatu ga Baba Mari ga Ibrahim ga Baba Kalla ga Farisat ga ni, ga Insu ga Yaya SadamgaYaya Salman ga Nafisat ga Sahabee ga Sa'eed ga Umar, se dai yau kowa na kama gabanshi, yauSa'adatu za ta tafi, gobe Farisat ne da Yaya Salman, jibi ban san waye ba" Yasmin tace cikinrishinkuka, jawota Habiba tayi tare da faɗin "har yanzu family a cike take, dama ita ba ɗaya dagacikinmu ba ce, barta ta tafi Yasmin, Allah ze cigaba da wanzar da farin ciki a saman fuskokinku" rungume ta tsam-tsam tayi tare da fashewa da raunataccen kuka.... Ita fa tsakani da Allah ta manta fa zaman jiran dawowan wani take, in za ta faɗi gaskiya tamantada a gidan shi ma take zaune, dan rayuwarta take kai tsaye babu wani tunani komai, ganinyandaMaude ta ƙureta da ido ya sata zare ido tare da washe fuska, cike da yanayinta tace "da gaskeBaba Maude!" Ta jefa mata tambayan tare da nufar inda take, "a'a tsaya daga nan kar ki kusantoni" Maude tace tare da kauda fuska, murmushi Lawiza ta saki tare da faɗin "ba'a take miki dawowa ze yi" kwaɓe fuska tayi idonta akan Maude tare da faɗin "Baba Maude ya da haka?Harna fara hasaso yanda zan danni snacks ɗin Anty amarya" "ai se ki danna tunda ba kya ci ne" Maude tace tare da ƙoƙarin barin wajen, dariya ta saki tare da faɗin "Baba Maude wannannamusamman ne ai, snacks ɗin amare har wani garɗi-garɗi zaki ji yana yi" ko ci kan ki ba ta cemataba ta fice.... Dariya Lawiza ta saki tare da faɗin "Allah ya shiryeki" "yaushe ze dawo? Kin fa ce yau zaki zomunda Iman ɗi na" tayi maganan cike da taɓara, murmushi ta saki tare da faɗin "ita ma se na cinzuwan take, na ce ta bari in sun ɗau hutu zan kawota ta miki weekend" "wow da kin kyauta" tacetare da zama saman one seater, "dama kin san Uncle ze dawo ne?" "Eh jiya Daddyn Zarahyafaɗamin" "wato ya sani na tambaye shi yace be sani ba, Allah ya shiryi Abban Iman" tayi maganantare da kauda kai.... Murmushi Lawiza ta saki tare da faɗin "wataƙila yana san shammatanki ne, kin san ganinshammata a fuskanta wanda aka shammata da daɗi" "ai ya kyauta yaushe ze dawo?" Taceanatse, "yau" tace tare da kallon ƙofan da aka turo, "yau dai! Amma meyasa banji ana sanarwaba?" "An sanar sosai kuwa, ke ki na kallon news ne?" taɓe baki tayi tare da faɗin "da yaushezasuiso?" "Sun iso" tace idonta akan Maude da Lamunde da suka shigo da sauri, "what!" Tace taredakallonta, ganin idonta ya tafi wani waje ya sata bin saitin idon tana saukewa a bakin ƙofa Hajiyadake riƙe da hannun shi tana shigowa.... "Oh Allah!" Tace tare da zare ido, dan haiban shi da take hanga a tv be kai rabin na zahiriyyaba, haɗiye wani yawu me kauri tayi lokacin da idon shi ya faɗa kan hoton ta da Anty, sumanwuccingadi yayi lokacin da idon shi ya faɗa kan hoton, banda bugu da ƙarfi babu abinda zuciyanshi keyi da tsintsinkewa, nan da nan bakin shi ya bushe, ya nemi yawu ya rasa, kallon inda ya bazawaidogaba ɗayansu ƴan rakiyan suka yi, zare ido su Lubabatu suka yi da ɗokacin mamaki.... "Zaki iya Insu zaki iya, Uncle ne zaki iya" tace a ƙasan maƙoshi tare da nufar wajen da sauri, bawanda ya hankalta da isowanta tana isa ta shige jikin shi ta ƙanƙameshi tare da kwantar dakanta a ƙirjin shi, lumshe ido yayi a hankali ba tare da yasan yayi hakan ba, "you're welcomeUncle" tace cikin soft voice tare da ƙanƙameshi so tight.... Comments fans🙏🥰 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Twenty three Ba ze iya manta irin wannan rungumar ba, rungumace irin wanda a wajen mutun ɗaya ya taɓasamu, daga shi be ƙara samun ko makamancin shi ba, se yau da aka ƙara mai irinta sak babanbanci, abu biyu ne ya zo mai aka, imma Insiyyat ce ta dawo duniya ta dawo gare shi, immamafarki yake me mahimmancin gaske, in dai wannan abun yanayin ya kasance mafarki neAllahkar ya bashi ikon farkawa har abada.... Saukan muryanta na marabtanshi da tayi ya maidoshi cikin hayyacin shi, da mugun mamaki Lubabatu ta zare ido tare da baje musu, ba ita kaɗai ba, saura ma duk kallon abinda ke faruwasuke ido waje, murmushi Hajiya ta saki tare da jana hannun shi a hankali, buɗe ido yayi taredasaukewa akanta duk da be ga fuskanta ba ya fahimci ba Insiyyat ɗin shi ba ce, mamaki yakewacece da wannan ƙarfin halin, yasan kaf jikokin gidan da ƴaƴa ba wanda ze iya wannanƙarfinhalin, motsa ta yayi a hankali, sakin shi tayi a natse ta ja baya tare da ɗago kai fuska cike da murmushi, kallon second guda ya mata ya fahimci wacce ya kauda kai, "what!" Yasmin tacetareda kallon A'isha, murmushi ta saki tare da nufar Alhaji Jamil da sauri ta rungumeshi tare dafaɗin"Uncle Jamil" murmurshi ya saki tare da shafa kanta a natse cike da kulawa, janye jikinta tayi tare da ƙarisawa wajen Kamil cike da murmushi tace uncle Kamil ina ta son ganinka ammakayi wuyan gani" ta idda maganan tare da tsayuwa kusa da shi, murmushi ya saki tare da faɗin"togani, kina lafiya?" "Eh Alhamdulillah uncle Munnir sannu da zuwa" "yawwa Insu" yace a natse.... Murmushi ta saki tare da faɗin "kai ma Insun?" Murmushi ya saki ba tare da yace komai ba, "barka da yammaci sir" tace tare da kallon Abubakar, harara ya dallamata tare da kauda kai, murmushi ta saki tare da kallon Jabir dake tsaye kusa da SSB dake jiran iso, "uncle Jabir newannan ko?" Tace tare da nuna shi, "ke ai kin san kowa, ba'a gabatar miki da su" Abubukar yacetare da wuce wa inda SSB ke tsaye, "mu ƙarisa ciki" yace cike da girmamawa, "oh Allah mylovelygrandma I really miss you" tace tare da rungume Hajiya, murmurshi ta saki cike da farinciki tariƙe hannunta suka nufi parlor, wuce wa ciki mazan suka yi su kuma mata suka baje anan... Tana shiga ta soma tattaro kayanta zuciya na tafarfasa, ba ƙaramin dukanta kalaman susukayi ba se dai ta musu uzuri, sun ci arziƙi da albarkacin Anty da take ji fiye da iyayen da suka kawotaduniya a zuciyanta, dan ta bata rayuwar da iyayenta suka gagara ba ta, tana gama zura waƴandatake buƙata ta zage zip ɗin ta dauki jakanta da wayanta ta jawo ta fito, bin ta kawai suka yi daidohar ta isa bakin kofa, tana saka ƙafa da zumman fita Yasmin ta miƙe tare da faɗin "dakata" tsayawa cak tayi ba tare da ta juyo ba, takawa tayi har gabanta ta ɗago hannu a natse ta miƙamata tare da faɗin "pass" duk zuba mata ido suka yi, ko wa yasan irin ƙaunar da ta nuna mataagidan.... Sauke numfashi me ɗumi tayi ta saki hannun dake riƙe da akwati ta zage jakanta ta ciro tamiƙamata, amsa tayi ta juya ta koma inda ta tashi ba tare da tace mata ko ci kan ki ba, haka ta jaakwatin ta fice daga gidan, suna tabbatar da fitan ta suka saki marayan kuka cike da tausayinkan su, "ya isa haka, haba dan Allah, ita yakamata tayi wannan kukan ba ku ba" Suwaiba tace tare da kallon su... Taka burki yayi a bakin babban gate tare da kashe kiran da ya ƙara shigo wayanshi a karonabarkatai, kallon shi Gude tayi da mamaki tare da faɗin "ka ɗauka mana, kasan wani amfani kiranyake da" "zanje can yanzu jirana suke, sauka kawai" yace ba tare da ya kalleta ba, "kai ka jiyo, karfe 10 nayi ka zo ka ɗauke ni inyi na gida" tayi maganan tare dw yunƙurin fita, "kai Momywallahi kina ban mamaki, yanzu nan da gida ba zaki iya taren napep ko ki taka a ƙafa ba, inananina gida?" "Ni dai na faɗa maka" tace fuska a ɗaure, "gaskiya ina da abubuwan yi a darennan, bazan samu daman zuwa ba" "wallahi se ka zo Sudais, baka isa ba, yamma na yi ba samun napepake a anguwan nan ba, dan haka na faɗa maka ka zo" "shikenan jeki" yace ba tare da ya kalletaba, buɗe murfin tayi ta sauka tare da buɗe jaka ta zaro waya, a guje ya juya ya bar wajen, yanaɓacewa ganinta ya taka burki tare da jawo waya ya danna number ya kara a kunni..... "Ina ka yada wayan ina ta kira?" Muryan Sa'adatu ya bayyana rangaɗaɗau, "wai ke wacce irinjarababbiya ce ne? Na faɗa miki in ki ka kira ni sau ɗaya ki ka ga ban ɗaga ba, kar ki sake kirainauzuri ne, in na gama zan neme ki, sannan saboda rashin hankali bayan kin gama jeramunwannankiran sannan in kira ki tsaya jeromun korafi, dama bakya da dalilin kiran ne ki ka dame ni dakira?" ya idda maganan cike da ɓacin rai, "ina son ganinka ne" tace a hankali, "kina nufinhar yanzu ba ki koma gida ba har yanzu ki na wannan wajen?" Yace rai ɓace, "duk wannan tambayoyin ba gamsar da kai za su yi ba, ka zo coffe shop ɗin da muke haɗuwa ina jirankayanzu"tace tare da katse kiran, tsaki ya ja bayan ya sauke wayan tare da ma motan key ya ɗau hanya.... "Hajiya dama nan ki ka kawo yarinyar nan!" Luba da ta kasa zama tace murya na bayyana irinbaƙin cikin da zuciyanta ya shiga, "ga tabbaci kin gani ai" Hajiya tace tare da riƙo hannunInsudake bin su da ido ta zaunar kusa da ita, "Hajiya meyasa za ki yi haka? Meyasa zaki kawo tagidannan? Wai kin mance wacece uwarta ne? Insiyyat ce fa, wacce ta zaɓi jefa ɗanki cikin tashinhankali dan tayi farin ciki, wanda ta zaɓi kashe shi dan ita ta rayu" Lubabatu tace zuciya amatuƙar ɓace, ƙirjinta na sama da ƙasa, sakin baki Maude da Lamunde suka yi tare da binsudaido, Lawiza kuwa nan da nan jikinta ya ɗau rawa... "Bana son shashancin banza anan Luba, kin san a ina muke dai ko? To ki bar maganan nan" Hajiya tace na ta zuciyan na ɓaci, "hmm shikenan" tace zuciya a maƙoshi, "Hajiya Luba fa nadagaskiya, ban ga dalilin da ze zaunar da yarinyar nan a gidan nan ba" A'isha tace tare da kallonHajiya, "subhanallahi wai ban ce ku yi shiru ba ne?" Tace tare da watsa musu kallon gargaɗi, kallon Maude da ke gefenta tayi tare da faɗin "Maude a shirya dining roomzamu yi dinner gabaɗayan mu tare" Hajiya tace a dake, jinjina mata kai tayi ba din ta so ba, Lamunde ta ma maganasuka juyawa dan nufar wajen, saukan muryan Lubabatu da ya doki kunnuwansu ne ya sa sutsayawa can tare da ba za kunni.... "Wai Hajiya me ki ke ɓoye mana ne game da yarinyar nan? Ko dai akwai wani abu da ba mukai gasani ba ne? Babu haɗin yarinyar nan da mu bare har ya kaita da raɓan SSB, abun takaici mawai acikin gidan shi take rayuwa" kallon Lamunde Maude tayi tare da taɓe baki, "ita ko ke da haɗi dagidan, kar ki manta Insiyyat ita ce mahaifiyarta, kuma kin fi kowa sanin wacece Insiyyat a wajenme gidan, tunda kun ce ba zata zauna a gidan ku ba shiyasa na kawota inda ba kwada ikonmataiyaka da shi dan gidan ubanta ne, ikonta ne" Hajiya ta idda maganan a kausashen, shiru duksukayi saboda ganin yanda zuciyanta yayi mugun ɓaci, zare ido Maude da Lamunde suka yi taredakallon juna, da sauri suka yi dining room jiki na ɓari, "muje ki ci abinci" Lawiza tace tare dakallonInsu dake zaune kaman ba ta wajen.... "Barta zamu yi dinner tare" Hajiya tace da kulawa, "okay shikenan, Allah ya maidaku gida lafiya" tace a ladabce tare da sakin ma Insu murmurshi, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "ki gaidaIman da Abulkhair, ki mai sannu da jiki" jinjina mata kai tayi ta juya ta fice a ɗan hanzarce, dasauri Maude dake leƙe ta cikin dining room

Chapter 30 of 109