ta fara sassaukewa, dariya Safinat ta saki tare da faɗin "na dai taɓa jin uwar gidabanda labarin amarya" "to ga amarya me capasity anan" tace tare da buɗe akwatin da tayi ƙasadashi, "Halima je ki kira mana iyayen a parlor su leƙo su sha kallo" Rahma tace tare da nufar wajentasakko da sauran, nan suka shiga kallo suna yaba namijin ƙoƙarin da Alhaji Jamil yayi, Iƙilimadake rufe cikin mayafi kuwa ban da bugu ba abinda ƙirjinta ke yi, dan ta tsorata haƙƙun, badadinsu Farisat suka kawo mijin ba da zata iya cewa se da ta aka yi....
Sallama zugan Yasmin Kausar, Lailah da Khadijatu da su Nabila da Nafisat da dawowantadagaschool kenan ta biyo su suka yi tare da shigowa, ihu Yasmin ta saki tare da nufar su ta haɗesutarungume, ba ta masauki me kyau suka yi cike da kewanta da suka yi "yau ga lalata har da keakazo ne!" Lailah tace tare da ɗagota, shagwaɓe fuska tayi tare da faɗin "ba ki yi farin ciki da ganinaba ne! Ina can ina mafarkin ku" ta idda maganan cike da jin haushi, "ai ta dage se ta zo" Farisat
tace tare da miƙewa....
"Auh ki ce dukkan ku ne, Safinat Hasinat Rahma, am Halima da Nafi ko?" Ta idda magananidantaakan su, murmushi suka saki tare da jinjina mata kai, "ai dukkan mu ne, amarya me capasitymuka rako" Farisat tace tare da sakin murmushi, "to marabanku da zuwa, sannun ku da hanyakun shawo hanya" Kausar tace fuska cike da murmushi, "ai ba gajiya Anty Kausar, dake hawadasauka ne" Yasmin tace tare da sakin dariya, dariya suka saki gaba ɗayansu tare da kallonta, "Allah ya shirye ku" Khadijatu tace tare da bin su da ido, "wace wannan!" Farisat tace taredazareido ta kama haɓa, murmushi Nafisat ta saki tare da kauda kai, "subhanallah ba dai Hajiya
Nafisatu Bertuwa ba ne ta koma haka! Ke ce haka ki ka yi ɓul-ɓul ki ka haska gari!" Tace taredaba je mata ido, dariya mara sauti ta saki tare da sadda kai, "sun koya mata ƙauyanci dubi yandasuke tsaye cirko-cirko kaman ba wayayyu ba, da Bertuwa aka bawa Capital ba Ɓadamayyaba" Yasmin tace tare da bin su Nabila da ido.... Dariya su Rahma suka saki cike da iya shege, "Allah ya shirya ku ga abinci can a parlor kujekuci, lokaci na wucewa ance 4:00pm flight ɗin ku ze tashi ko?" Lailah tace cike da kulawa, "na sudai
Anty Lailah ai mu Ɓadamayya kwana Ɓadamayya wuni" Farisat tace tare da ficewa dan ɗibowa
Iƙilima abinci, "to! Ikon Allah" tace cike da mamaki, "Anty Lailah so muke fa mu gwangwajetareda ku, ko ba kwaso ne?" Safinat tace tare da kallon ta, "a'a wallahi Safinat muna so muna marabada ku" tace tare da sakin murmushi, "to ko ku fa" tace tare da sakin murmushi....
"Ku ƙarisa Auntie's ga amaryan can" Yasmin tace tare da riƙo hannun Nafisat, murmushi sukasaki tare da wuce wa inda ta nuna musu, "amma dai ke yau zaki koma ko?" Khadijatu taceidontaakan Yasmin, girgiza kai tayi tare da faɗin "tare da su zan koma" "Yasmin!" Tace cike da mamaki, "please Anty Khadijatu kar ki ce komai, wata ɗaya da wani abu fa nake da shi, har yanzubazaniya zuwa wani waje ba" ta idda maganan tare da jan hannun Nafisat suka wuce gefen da Iƙilimatake, ganin yanda suke gaisawa da ita fuska a rufe yasata faɗin "a'a ba mu yarda ba a buɗemanafuska" ta idda maganan tare da ɗaga mayafin da ya sauka saman fuskanta sama, "wow!" Fadilada Nabila suka ce cike da yabawa dan ba ƙaramin kyau ta musu ba, "ma sha Allah" su Kausar
suka ce cike da yabawa, "barka da zuwa Iƙilima, Allah yasa an ƙulla alheri" Lailah tace fuskacikeda murmushi, "Anty Iƙilima ina wuni?" Nafisat tace cike da girmmamawa, ɗagowa kaɗantayi
fuska ɗauke da murmushi tare da miƙa mata hannu, matsa mata tayi ta zauna a kusa da ita, "bari
mu koma can parlorn kafin sun kammala cin abincin se mu wuce can gida su gaida su Hajiyakafin su wuce" Khadijatu tace tare da wucewa, dafa mata baya suka yi fuskoki washe da
murmushi....
"Ina Insu ina Mairah da Sa'eed?" Ta jefa mata tambayan a hankali, murmushi ta saki tare dafaɗin"Ammi na school amma ance tanan zata biyo, Mairah tayi barci shiyasa ba mu zo da ita ba, Sa'eedna nan gidan" "oh Allah bar surutun nan tunda kin samu bakin ki ya buɗe ci abinci, dan malamango ya taddaki da ƙarfin ki" Farisat tace tare da ajiye plate ɗin da ta cika da abinci a gabanIƙilima, fiddo ido tayi tare da faɗin "yayi yawa" "kuma duka zaki cinye ba" tace tare da bankamata harara ta wuce, kallon Yasmin tayi cike da roƙo, murmushi ta saki tare da faɗin "ci yandazaki iya se dai kar ki mana fulaku" murmushi ta saki tare da kallon Nafisat cike da kulawatace"ɗakko spoon mu ci" kallon Yasmin tayi a natse, "jeki ɗakko" tace tare da miƙewa, "ku zamanmeku ke! ba zaku ci abincin ba ne?" Tace idonta akan Harira da Sadiya dake zaune suna magana, "zamu ci gamunan" Sadiya tace tare da yunƙurawa....
Haka kowacce ta zubawa kanta abinci ta ja gefe ta fara ɗumama ciki, zare ido Harira dakekallonSadiya dake dauriyan ƙyeta tayi tare da faɗin "amma baki da kirki" "rashin kirkin me tayi?" Safinat tace tare da kallon su, "wallahi ƙarya ta mana akan Abdullmalik be gama gini ba, yagama tuntuni" kallonta suka yi da mamaki ɗauke a saman fuska, "kinwa kan ki" Farisat tacetareda maida hankalinta ga abincin gabanta, "to dan Allah ba gashi na cika burina ba" tace cikedajindaɗi, "ƙwarai hakan kuma ba ze hana muna komawa mu miƙa ki na ki ɗakin ba" Yasmin tacetareda banka mata harara, "wallahi na ji, na yarda tunda na cika burina" tace cike da gaskiyanta, "Allah ya shiryeki" Iƙilima da ke bin ta da kallon mamaki tace tare da kauda kai, "amin" tacekoajikin, "ita ma me kawo muku rahoton munahukace, sun jame da Yaya Kabir tuntuni, danyadagese ya aurar damu ne kafin yayi aure shiyasa ba'a yi maganan ba, ta ƙosa mu ba ta wuri ta shigadaga ciki" tace tare da kai mata mangari a goshi...
"Banga lefin ki ba Harira kina da gaskiyanki" Safinat tace tare da sakin murmushi, "ai se a haɗada na ki kawai a make tunda shima ya shirya" Rahma tace cike da ganin hakan shine dai-dai, "shikenan an raba gardama ba" Yasmin tace fuska washe da murmushi, "wata wainar aketoyawane anan!" Insu da ta faɗo ɗakin tace idonta na bin fuskokin su da murmushi me ban sha'awa, tashi suka yi gaba ɗayansu a guje suka yi inda take tare da rungumeta suna ambaton sunanta..
"Oh Allah nan duk kewan Insu ku ka yi gaka!" Tace idonta na tara ruwan hawaye, "ke dai bari
baby Insu ba musan haka ki ka shige ƙalbin mu ba se da ki ka yi nisa damu" Safinat tace cikedaƙauna, murmushi ta saki tare da faɗin "wallahi ni ma nayi kewan ku over, kumatsa in ga Antyamarya" tayi maganan tare ra nufar Iƙilima dake bin ta da idon da ya cika da ruwan hawaye, "a'a, kar mu yi haka dake, ya da kuka kuma ranar farin ciki" ta idda naganan tare da kai jikinta tarumgumeta ƙam-ƙam, "ina matuƙar taya ki murna Anty Iƙilima, ki nuna tarbiyyanki da ladabi dabiyayyanki, zaki haska in sha Allah" jinjina mata kai tayi cike da gamsuwa tare da jan hanci, gogehawayen da ya zubo mata tayi tare da janye jikinta, "to bari in koma gare ku ƙawayen amarya" tace cike da yanayinta, "malama jeki zuba hatsi ki ci tukun" Farisat tace tare da banka mataharara, kama haɓa tayi tare da faɗin "haba malama ƴar jarida" tayi maganan cike da yanayinta, kwashewa da dariya suka yi idanunsu akanta....
Miƙewa Yasmin tayi ta wuce parlorn, ba ta jima ba ta dawo riƙe da plate wanda ta zuba abinci dai -dai, kamata tayi ta zaunar tare da ajiye mata abincin a gabanta, "a haka zaki ji daɗin maidayaakayin" tace fuska cike da murmushi tare da komawa insa ta tashi....
"Hala su Anty Lailah ba su ganki ba ne?" Farisat tace tare da kallon ta, "ba kowa a parlornhakana wuto" "ina ga sun je side ɗin uwargida me capasity ne" Safinat tace tare da sakin murmushi, "dan Allah daina ɓata abun mana na faɗa muku amarya me capasity ne fa yanzu" dariya sukasaki saboda yanda tayi maganan, "ina Sa'eed?" Insu tace tare da kallon Nafisat, girgiza kai tayi
tare da faɗin "banji ɗuriyarshi ba" "jeki ɗakunan dake parlorn ki duba uncle Jamil yace tunshekaran jiya ya dawo nan side ɗin" tayi maganan cike da damuwa, miƙewa Yasmin tayi taredafaɗin "bari in taya ta da zuba mai abinci" "hakan yayi" tace tare da maida hankalinta ga abincingabanta.... A'a wannan kuma yaushe ta iso!" Lailah dake ƙoƙarin shigowa ɗakin tace cike da mamaki, "lokacin kuna side ɗin Anty uwar gida me capasity" Insu tace tare da miƙewa fuska washedamurmushi ta rungumota kaɗan, "to sannu da zuwa, yakamata ku hanzarta ku yunƙuro mutafi"
"ai mu muna nan" Farisat tace cike da gaskiyanta, "auh! Kuna nan wato! "Ai se ku cigaba dazama, dalla malamai ku hoɓɓaso" Lailah tace tare da banka musu harara, "to da wa za'a barta?" Yasminda ta shigo ta ci karo da zancen tace cike da mamaki, "Sa'eed na side ɗin, sannan Yaya Jamil badaɗewa ze zo" "to Anty Lailah in ki ka mana bayani ma a sanyaye zamu gane, ku taso mutafi
gobe ma dawo jin ya aka yi" Farisat tace idonta na bin su Sadiya dake zazzaune, harara Lailahtazabga mata tare da ficewa, dariyar da su Rahma ke ta dannewa suka saki tare da kallonFarisat
da ta bi ta da kallon me kuma nayi....
"Kun tadda Sa'eed ɗin?" Insu tace tare da saɓa jakanta a baya idanta akan Yasmin da ta shigo, "eh gayi can yana cin abinci tare da Mami fa muka zo tana parlor" Yasmin tace tare da wucewaciki dan ɗaukan jakanta....
Zare ido tayi tare da faɗin "meyasa ba ku mun bayani tun ɗazu ba!" Ta idda maganan taredawucewa kusa da Iƙilima, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "zamu wuce, za su dawo gobe, nasan zuwa jibi uncle Jamil ze kawo ki gaida Hajiya zamu haɗu a can" jinjina mata kai tayi cikedakulawa, miƙewa tayi ta fice da sauri, nan suka fara sallamanta jikkuna a sanyaye, tana shigaparlorn ta wuce inda ta hango Mami da sauri tare da sakin ihun farin ciki, "Mami na!" Tacetaredafaɗawa jikin ta, murmushi ta saki tare da rumgumeta ƙam-ƙam fuska cike da murmushi, zamejikinta tayi tare da faɗin "Mami nayi kewanku, ya Daddy yake?" Yana lafiya yana gaidaki" "inaamsawa" tace cike da farin ciki, "oh ko kunya gabjejiya dake kin wani haye jikinta" Hasinat datafito shirye dan tafiya tace tare da kama haɓa.... Harara ta dalla mata tare da faɗin "ba dai zaki hau ba, wai meyasa ma ku ka zo da ita ne Mami?"
"Ke za'a barwa ita halan?" Farisat tace tare da gyara mayafin jikinta, "ita da za'a kawo nandasati
saurin me take na zuwa" tace tare da miƙewa, "ke ba wannan maganan yanzu ai" Safinat tacetare da kallon ta, kallon sakanni ta mata baki a sake kafin ta saki wani nagartaccen murmushi, "ma sha Allah, kai amma nayi farin ciki, daga ƙarshe dai autan Mami ta farka daga nannauyanbarci" tayi maganan cike da tsan-tsan farin ciki, dariya suka saki idon su akanta, "muguwadamana san irin tsanan da ki ka mai" Hasinat tace tare da banka mata harara, "wallahi na tsaneshi
kam, be burgeni sam, bari in zo" ta idda maganan tare da wuce wa ƙofar ɗakin Sa'eed, turawatayi baki ɗauke da sallama ta shiga, taddashi tayi zaune shi da Nafisat yana cin abinci, "ta somuwuce" tace idonta akan Nafisat, ba musu ta miƙe ta fice, ƙarisawa tayi ta zauna kusa da shi tareda faɗin "ya gidan?" Murmushi ya sakin mata tare da faɗin "uncle Jamil na da kirki"... Murmushi ta saki tare da faɗin "na sani shiyasa ya auro Anty Iƙilima Anty Sa'adatu dantadingadafa maka abinci ka na ci in zaka tafi makaranta, ka zama yaron kirki, ban da raini ko nunataurinkai, na sanka sosai da ladabi da biyayya ka ƙara akan wanda ka ke dashi, Allah ya maka albaraka""Amin Ammi, ina Mairah?" Yayi tambayan a sanyaye, murmushi ta saki tare da faɗin "tanagida, gobe su Momy za su taho maka da ita" murmushi ya saki cike da jin daɗi, tashi tayi ta ficejiki a
mugun sanyaye, tana kai jiki ta yi saurin ja baya saboda karo da ta kusan yi da Farisat da Yasmindake tsaye a jikin ƙofar....
"Yaa Allah!" Tace da mamaki, "muje" Yasmin tace tare da riƙo hannunta suka wuce, kallonƙofarɗakin Farisat tayi tare da dafa musu baya, suna fita suka shishshige jerin motocin da aka jeradansu, suka dau hanya tafiyan mintinan kaɗan ya iso da su White house....
"Subhanallah ina zamu shiga wai white house! Abinda muke hanga a jarida da tv da hotunayaugamu zamu shige shi" Hasinat tace cike da farin ciki, "ji ƙauyanci" Safinat tace tare da kaudakai, "a'a barta wallahi ta bayyana farin cikinta, ko ni nan cike nake da farin ciki" Rahma tace taredakallon ta, murmushi drivern dake jan su ya saki ba tare da ya nuna alamun ya ji ba, a kofar sideɗin Mr president motocin suka faka, nan da nan security's suka ƙariso suka fara temaka musu, sunan idda fitowa suka musu iso ciki, suna shiga suka tadda su gaba ɗayan su a parlon zazzaunesuka kwasan hira "Ami mammy" Mairah da ta hangosu tace tare da zamewa ta nufe su a gujecikin tafiyarta, buɗe mata hannu Farisat tayi cike da so da ƙauna, faɗawa jikinta tayi tare daƙyalƙyacewa da dariyan farin ciki.... Ɗagata tayi ta saɓa a ƙirji cike da jin daɗin yanda ba ta manta da ita ba, "ai ba ruwana daketundabaki ganni ba" Yasmin tace tare da miƙa mata hannu, kamawa tayi ta nufeta cike da kewa, "toai
ki na ta baya ne alarammiya Yasmin" Farisat tace tare da sakin dariya, zaro waya Insu tayi dasauri tare da shiga camera ta saita wayan ta fuskan Alhaji Jamil, tare da faɗin "kun gane munAngon amarya me capasity kuwa, wow! Gaskiya tun daga kan wankan shi zaku fahimci amaryartamu me capasity ne, subhanallah, irin wannan karya hula haka" dariya suka kwashe da shi tareda bin ta da ido, "a gaskiya ango ya bi ya mu" Farisat tace tare da sakin dariya, "ni fa tundanasako kaina cikin parlorn turaren ango ke sanar mun yana ciki a zaune" Yasmin tace ita macikedaiya shege, girgiza kai Lailah tayi tare fa faɗin "Allah ya ba ka yara Yaya Jamil" dariya Alhaji
Munnir ya saki tare da faɗin "ƙawaye dai, ai mu ƙawaye aka haifan mana" "aikuwa dai" Khadijatutace fuska cike da murmushi, maida wayan Insu tayi tare da faɗin "se an jima sanyi posting" taidda maganan tare da wuce wa inda yake ta zauna a kusa da shi....
"An ɗaura lafiya?" Ta jefa mai tambayan fuska cike da murmushi, jinjina mata kai yayi cikedakulawa, "Allah ya sa an ƙulla alheri uncle Jamil, ya baka ikon kwatanta adalci a tsakaninsu, danwallahi ban son ka tashi da shanyayyen ɓarin jiki" ta idda maganan cike da yanayinta, dariyasuka kwashe da shi idon su akan ta, "wallahi da gaskiya na, in ka siyan ma wannan sweet kasiyanma wan can, in ka yi wa wannan murmushi ka yi wa wan can, a to" ta idda maganan tare damiƙewa, kallon Sadiya da Harira da su Rahma Farisat tayi tare da faɗin "ku ke ta san ganinAngo, to ga uncle ɗin na mu, ɗaya tamkar da dubu, jarumin zuri'armu kaf guda ɗaya, dan shi ya zarotuta ya ɗaga ta sama, duk cikin su daga kan matsoratan farko su Alhaji Sadamzuwa kansubawanda ya iya jarumtar auren mata biyu se shi" ta idda maganan tare da sakin dariya, dariyasukakwashe da shi tare da kallon ta, "kin wa kan ki" Lailah tace tare da banka mata hararata...
"Ƙarya na yi Anty Lailah?" Tace fuska yalwace da murmushi, "ba ki yi ƙarya ba wallahi ba wannanjarumin" Insu tace tare da sakin murmushi, "oh Allah, shikenan yanzu ya buɗe mana hanyadamashine yakamata ya fara, daga shi se me bi mishi se ni" Kamil yace tare da sakin murmushi sabodaganin yanda Insu ke kallon shi, "sorry daughter" yace tare da sakin dariya, "uncle Kamil hakazamu yi da kai?" Tace fuska a ɗaure, "na yi shiru" yace tare da alamun zage bakin shi da hannu, murmushi Lailah ta saki tare da kallon su Mami cike da kulawa tace "ku sha ruwa Mami, Hajiyaga iyayen amaryan fa" murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "na gansu Lailah ina jiran suhutanemarabanku da zuwa" ta idda maganan fuska washe da murmushi, murmushi suka saki taredaamsawa cike da yaba mutumcin su...
"Wai ba dai matayenku ba su zo bikin amarya me capasity ba?" Insu tace tare da kallon Kamil, "duk sun zo suna can, kunyi saɓani ne, fitan su nan ba daɗewa ku ka shigo" "to sun wankekansu, dan duk wanda be zo ba se na ƙulla da shi" tayi maganan cike da gaskiyanta, murmushi sukasaki
tare da bin ta da ido, "uncle Jamil wannan ita ce ƙanwa Anty amaryan uwan su ɗaya ubansuɗaya, Hajiya wannan sister's ɗin mu ne yaran Antyn Yaya, ga wasu sister's ɗin na mu kumaRahma Safinat Hasinat ƙannin Yaya Salman babban yaron Anty" jinjina kai Hajiya tayi fuskacikeda murmushi, "ga Mamin mu da nake baku labari" ta kuma cewa tare da nuna Mami, "ai nawayeta, mun haɗu a bikin Farisat da gaisuwa" murmushi Mami ta saki cike da yabawa sanin
yakamatan Insu ...
"Bari in kimtsa" tace tare da juyawa da nufin wuce wa sama, karo taci da SSB da sakkowanshi
kenan cikin shiga me matuƙar burgewa, "wayyo!" tace tare da ja baya da sauri, saurin riƙotayayi
saboda ganin zata faɗi, "Nafsii!" Tace a shagwaɓe, murmushi ya sakin mata tare da kafetadaido, tura baki tayi tare da faɗin "ka tsorata ni sosai fa!" Tayi maganan a taɓare, "sorry" yace a hankali, murmushi ta sakin mai tare da muntsilan fatan hannun dake riƙe da hannunta, "auch" yacetareda saurin sakin hannun ya taɓe fuska idon shi akan wajen da ta muntsila, dariya ta saki taredawuce wa sama a guje, "zaki sakko" yace tare da sakin murmushi ya wuce gefen Jabir ya zauna, suman zaune su Lailah da su Rahma suka yi dan ba ƙaramin mamaki lamarin ya ba su ba, suRahma kuwa mamaki biyu suke, na ganinshi da suka yi face to face da kuma yanda suke zubaƙauna a gaban kowa hankalin su kwance, su Yasmin kuwa wani ni'imtaccen farin ciki ne yalulluɓe su abinda suke hasashe ya tabbata sun gani da idanun su....
"Baƙi ne damu fa" Jabir yace a hankali tare da kallon shi, kallon menene ya mai cike da mamaki, "ana ragewa" yace murya a ƙasa, banka mai harara yayi tare da juyawa ya ma su Mami barkadazuwa, murya na rawa suka fara gaidashi, "Uncle sannu da fitowa" Farisat dake rungume daMairah tace fuska cike da murmushi, nagartaccen murmushi ya sakin mafa dan se a lokacinyagansu tare da faɗin "yawwa Hajiyata ya gajiyan hanya?" "Alhamdulillah" tace cike da farinciki, jinjina mata kai yayi fuska ɗauke da murmushi, gaishe shi su Rahma suka yi cike da girmamawa, amsawa yayi cike da kamalan shi, "Mairah" yace a natse, "a'am" tace tare da ɗago kai, "kinajikinmammy ne?" Yace a natse, "eh" tace cikin magananta, "zaki bi mammy ku koma Bertuwa?" Shirutayi tare da sakin murmushi, dariya suka saki tare da faɗin "shiru ma amsa ne" murmushi yasaki
tare da kallon Yasmin cike da kulawa yace "Mommy na gajiyan ne haka?" Murmushi ta saki cikeda jin kunya....
Tunda ya fita daga asibitin yake walagigi a saman titi, ya rasa ina za shi, ya rasa me ze yi, yarasaina ze nufa, zama a gefen titi yayi yana bin jama'an dake harkokin gabansu da ido, se da yaɗauki
lokacin da be san ko nawa ba a wajen, ba kalan tunanin da beyi ba, goge hawayen da suka
gangaro mai yayi tare da zaro wayan shi dake aljihu, neman number yayi a hankali, tundayazokan number da yake nema ya tsaya cak yana bin sunan da ya sama number da ido kamar menazartan wani abu, sauke ƙaƙƙarfan numfashi yayi tare da danna number ya kara a kunni, sedaya kusa tsinkewa aka ɗaga, jin ba a ce komai ba yasa shi faɗin "kina ina?" "Gida" muryanSa'adatuya fito raɗau, "zan zo" yace a dake, "bari in turo maka address" tace tare da katse kiran....
Zare wayan yayi a hankali tare da kafe wayan da ido, kiran da ya shigo wayan ne yasa shi
dawowa cikin natsuwar shi, ganin number babu suna ya sa shi ɗagawa ya kara a kunni taredaɗaga sallama, "kana ina ne Abdull?" Muryan Shila ya doki kunnuwan shi, "waye!" Yace cikedaƙosawa, "Shila wacce ta temaka maka lokacin da ka ke neman temako, na je wajenka a asibiti
ban taddaka ba, amma na tadda Mamanka tace ba ka jima ta barin can ba" "lafiya ki ke nemana?" Yayi maganan a dake, "lafiya lau, temakon ka nake nema kamar yanda na temake ka" "meki ke so?" Ya jefa mata tambayan cike da ƙosawa, "Sa'adatu ta shigo gari, shin ta nema ka ne?"
"A'a" yace tare da ƙoƙarin zare wayan, "ka daina ƙarya mana Abdull, be maka kyau, mahaifiyarkata faɗa mana ta zo wajenka yau, duk da munji yanda ku ka rabu amma na san zata neme ka, intakira ka please ka sanar mun, ina son magana da ita ne" "okay" yace tare da zare wayan ya katsekiran, tsaki ya ja tare da shiga app din saƙonni ganin ta turo mai address ɗin ya sa shi kashewayan ya maida a aljihu tare da saka ma napep ɗin da ya zo wuce wa hannu, yana tsayawayashige tare da faɗa mai inda ze kai shi....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fifty six
Tsatstsaye suke a parking space ɗin side ɗin suna sallama da su Mami, janye Insu daga jikintaMami tayi tare da faɗin "a cigaba da dagewa kar a saka wasa a karatu, Nafisat a dage" jinjijamatakai suka yi cike da jin daɗin kulawanta a gare su, kallon Farisat tayi tare da faɗin "kar a yi aikinrashin hankali" jinjina mata kai tayi tare da sakin murmushi....
"Ni fa Mami da zaki ji ta tawa da kin tattarasu wallahi, in kuma hakan ba ze yuwu ba ki tafi daYasmin da Safinat sauran a barsu" Khadijatu tace cike da ganin hakan shine dai-dai, "amMami
shiga mota lokaci na tafiya jirgi ba ya jira, Mama Allah ya sauke ku lafiya" Insu tace cikinkatsehanzarinta tare da buɗe mata murfin mota, murmushi ta saki tare da shigewa, tana shigataƙarasallamanta ta rufe ƙofan tare da ja baya, shishshiga saura suka yi fuskoki cike da murmushi, janmotan driver yayi suka nufi barin gida, suna ɓacewa ganinsu Insu da ta bi su da ido ta saukenumfashi me sauti tare da juyowa cike da yanayinta tace "ɗazu kaman kina magana ko AntyKhadijatu!" Harara ta banka mata tare da juyawa ta koma ciki, dariya suka saki gaba ɗayansucike da jin daɗi....
"Kin burgeni baby Insu, da yanzu ta ɓaro mana aiki, dama da ƙyar ta yarda da barin mu" Yasmintace tare da juyawa, "Allah ya shiryeku" Lailah tace tare da juyawa ita da su Kausar da sukayorakiya suka koma ciki, murmushi suka saki tare da tattarawa suka nufi ciki zuciyoyi ƙal, sunashiga suka tadda su Lailah da ba su zauna ba bayan komawan su na shirin tafiya....
"To ai tare zamu tafi can ɗin" Farisat tace tare da kallon Lailah, murmushi ta sakin mata taredafaɗin "to ku tattaro karikitanku mu tafi" "ba inda zaku, nan ku ka zo dan haka a nan zakuzaunazadai mu yi muku alfarman zuwa musu yini" Kamil yace idan shi akan su, "to uncle" Farisat tacecike da ladabi, "Kamil ka bari mu tafi da wasu daga ciki sun yi yawa" Lailah tace idanta akanshi, "yaushe wannan maganan ya fito!" Yace tare da kama haɓa, murmushi ta saki tare da faɗin"tomu zamu tafi, ku se kun zo, Hajiya se Allah ya kai mu rana ita yau zamu dawo ganin amarya" "toLailah Allah ya sama zumuncin da aka raya albarka, Khadijatu ki gaida me jiki" "amin, inshaAllah ze ji" tace tare da juyawa, "Anty Lailah, zan zo ko zuwa jibi ne mu tattauna wani batudake" Kausar tace tare da miƙewa ta nufeta...
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 90 Chapter of 109