damƙe hannun cikin karayanzuci tace "in sha Allah, Farisat ƴa ce a gare mu" jinjina kai tayi ta juya da sauri ta shige mota, dasauri Baba Mari da ta tsaya sake mata farfesun da ta mata a cooler ta ƙarisowa wajen, miƙamatatayi tare da faɗin "Allah ya kai ki lafiya" tana kai nan ta juya da sauri tare da sakin kuka mesauti, rufe ƙofan Sadam yayi ya buɗe gaba ya shige, ɗaya musu hannu Baba Kalla kawai yake kai aduƙeya kasa ɗagowa, jan motocin suka yi a natse sukai airport....
Suna shiga wajen jira suka fara jin sanarwan da ake akan jirgin ya kusa tashi ana nemanfasinjanta, kallonta Yaya yayi tare da riƙo hannunta a hankali ya saka mata wani takarda yadamƙe, ɗago kai tayi ta kalleshi ido na cika da ƙwalla, girgiza mata kai yayi tare da buɗe baki
cikin murya me nuni da zallan abinda za'a ce me matuƙar mahimmanci ne yace "duk sandaki kashiga damuwa ki ɗauki littafin mahaliccin ki zaki ji natsuwa da kwanciyar hankali ya riskeki, duksanda ki ka nemi shawara ki kira Yaya yana da lokacin ki, na san za ki iya Insu, zaki cika burinmahaifiyar ku da ta ɗau tsayin shekara 23 tana son cikawa, ahalin ki suna goyon bayanki, bazamu gajiya wajen ƙarfafa miki gwiwa ba" jinjina kai tayi hawaye na shatato mata, "wa cezantsokana yanzu? Insiyyah zaki nesa damu, kar ki yi sakaci da addu'a, duk inda ki ka tsinci kanki
kar ki sare ko ki ji kaman Ubangijinki baya tare da ke, yana tare da ke, Insiyyah, aure yanagaba-gaba cikin sinnonin ma'aiki kar ki wasa da shi, ki riƙe tsafta, ki kyautata zuciya ki rayu da kowalafiya, shi fara'a da mutuntawa yana jawo maka soyayyan maƙiyi" jinjina kai tayi tare da
rumgumeta....
Sarauniya Nafisat zanyi matuƙar kewanki" tace murya na rawa, "zanyi na ki ni ma Insiyyah" Babiya tace na ta muryan na rawa, janye jikinta tayi ta ja majina tare da goge hawaye, kallonSahabee da Sa'eed da Umar dake sharɓan kuka tayi tare da faɗin "kar ku yi wasa da karatu, kudage wajen maida hankali, kar inji ɗaya daga cikin ku be ci jarabawa ba zamu ɓata, ko kunasonin ɓata daku?" Girgiza kai suka yi ido be daina zuban hawaye ba, "to ku dage" tace a hankali
hawaye na bin kuncinta, jinjina kai suka yi tare da shigewa jikinta, "Allah ya muku albarka" tacemurya na rawa, janye su Yasmin da hawaye ɗaya ke bin ɗaya a saman fuskanta tayi tare darungume su, kallon Salman da ya kauda kai gefe tayi tare da faɗin "kaii me kan giginya" juyowayayi idon nan ya kaɗe yayi jazur tare da sakin guntun murmurshi, "me kan kwakwa" yace ahankali, "kar tayi kuka ko na sakan guda, ka tabbatar farin ciki ya cigaba da wanzuwa a samanfuskanta, ka wanke mun zuciyanta da kwanciyar hankali me cike da haske" tayi magananidontadake shatatan hawaye na yawo a saman fuskan shi, yatsanta manuniya na kan Farisat da tahaɗakai da ƙirjin Sadam, jinjina mata kai yayi tare da faɗin "na miki alƙawari" jinjina kai tayi taredasakin murmurshi ta shige jikin Sadam, "zaki iya, ki buge ko wani daliɓi ki fita da sunan ki, Antytace zaki iya ki tabbatar ma duniya da zaki iya" yace a hankali dai-dai saitin kunninta, jinjinakai
tayi tare da faɗin "in kayi kewata ka kalli sama zaka hangoni ina maka murmushi" sakinhawayeyayi tare da faɗin "tanan ki ke hango Anty?" Jinjina kai tayi tare da faɗin "ta ko ina haska idanunatake" jinjina kai yayi tare da matseta da ƙarfi, ganin sun ɗau lokaci a haka yasa Yaya jawotaahankali, tare da faɗin "ana neman ki" lumshe ido tayi hawaye masu zafi suka gangaro, buɗewaYasmin da Farisat da Nafisat hannu tayi tare da faɗin "ku zo" da gudu suka isa suka rumgumetatare da fashewa da kuka a tare, kuka suke me taɓa zuciya su Babiya dake bin su da ido dagagefesuna ta ya su, "zan tabbata a kewan ku" tace a murya na kyerma, "zamu tabbata a kewanki" sukace tare da ƙara ƙanƙameta, jin ana ta kiran sunanta ya sa Farisat jan jiki tare da faɗin "kar ki yi
wasa da abinci, maganin ki ki sha akan ka'ida, ki dinga barin wayanki a kusa dake" ta idda
maganan murya na rawa tare da saurin ja gefe, "kar ki wasa da caji, kar ki saka damuwankomai, in kina jin ganin mu ki kira mu" Yasmin tace tare da share mata hawaye, murmushi ta saki tareda riko hannunta dake saman fuskanta, tare da faɗin "zamu rayu" cafke maganan suka yi gabaɗayan su baki a haɗe tare da cigaba da faɗin "rayuwa me cike da farin ciki, zamu danne
damuwoyin mu a ƙasan zuciya mu wanzar da farin ciki a saman fuskokin mu, zamu saka kowafarin ciki ko da mu ɗin ba ma maraba da shi" suna kai ƙarshe suka saki dariya me cike da dakiya, ɗago waya Insu tayi tare da faɗin "one selfie" da sauri suka ƙariso bayanta duk suka ƙure
cameran da ido, "smile" tace tare da murmusawa, washe bakuna suka yi cike da ƙarfin hali, ɗaukan su tayi tare da faɗin "happy family, ina alfahari da ku" sauke wayan tayi ta maida ajaka, ta mayar baya taja akwatin da zata iya ja, sauran kayan ma'aikata suka kwasa, da sauri ta nufi
hanyar da ze sadata da wajen bincike tare da faɗin "zanyi kewan ku guys" tana kai nan ta ɗagamusu hannu ba tare da ta juyo ba ta shige, kuka suka saki cike da zugin da zuciyan su ke yi, dasauri suka isa gaban glass ɗin dake bayyana filin jirgin....
Saka akwatinan ta a inda yakamata tayi ta nuna musu ticket ɗin ta suka bincike ta, wuce watayi
ta ɗau kayanta ta wuce filin jirgin, tana fitowa suka ganta, banda ɗaga mata hannu ba abindasuke, haka suka bita da ido har ta haye motan da ze kai ta inda jirgin yake, tana sauka ta jawokayanta, ba wa masu kula da jera kayan a jirgi tayi ta shige jirgi a hankali, lumshe ido Yayayayi
hawayen da suka cika mai ido suka sakko....
"Tana shiga ta saki murmushi tare da fara duba site ɗin ta, kwaɓe fuska tayi tare da kallonAbubakar dake zaune dogare da ƙafa ya rufe hanyar da za ta bi ta wuce site ɗin, "excuse meuncle" tace tare da ƙure shi da ido, saurin janye wayan dake kunnin shi yayi tare da baza mataido, rass ƙirjin shi ya buga, murmushi ta saki tare da ɗago numbern site ɗin ta nuna mai, "my site" tace tare da nuna mai site ɗin da hannu, "oh I'm sorry" yace tare da saurin janye ƙafafunshi, shigewa tayi tare da sakin murmushi, "Insiyyah" yace a mugun mamakance, "yes magana kake?"tace tare da juyowa ta kalle shi, "no" yace tare da sakin murmushin yaƙe, zama tayi tare dafaɗin"wash nayi kewan ku guys" "me ki ka ce?" Yace idon shi akan ta, a firgice ta juyo inda yaketaredazare ido, "na ji kaman kin yi magana" yace cike da mamakin kaman da yake gani.... Murmushi ta saki tare da faɗin "da family na nake, na yi kewan su uncle, tunda muke ba mutaɓanesa da juna na kwana ɗaya ba, yau gashi zanyi nesa da su" ta idda maganan tare da sakinmurmushi, "sorry" yace a hankali, "oh uncle ya kaman jikin ka yayi sanyi, ilimi zan je nema" murmushi ya saki tare da faɗin "belt" yayi maganan tare da nuna mata belt ɗin gefenta dansunsanar a saka tana ta zuba ba ta ji ba" fidda ido waje tayi tare da faɗin "oh" murmurshi ya saki tareda girgiza kai, jin jirgin na ƙoƙarin tashi ya sa ta rumtse ido ƙirjinta na bugawa, ƙanƙame jiki tayi
tare da fara karanto duk addu'an da ya zo bakinta....
Jirgi na dai-daita a sararin samaniya Abubukar dake ta kallonta ya saki murmushi tare dafaɗin"buɗe idon ya gama dai-daita, buɗe ido tayi a hankali cike da tsoro, jin komai normal yasatasakinmurmurshi tare da saurin kauda kai daga gareshi, dariya ya saki tare da faɗin "shine hawanki nafarko?" Jinjina kai tayi tare da haɗiye yawun tsoro, "oh ko ya Sarauniya Nafisat tayi lokacindajirgi ke diran tashi" "magana ki ka yi?" Yace tare da kallon ta, murmushi ta saki tare da faɗin"daKakata" tace tare da sakin mai murmushi, murmushi ya saki tare da faɗin "da ita ku ke ne?" "Notime ɗin da za su tafi Saudi nake magana, na santa da tsoron tsiya, Allah yasa cikinta be burgeba" ta idda maganan tare da ƙyalƙyacewa da dariya, dariya ya saki tare da bin ta da ido.....
Jirgi na tashi suka bi shi da ɗaga hannaye, juyowa Yaya yayi ya jawo su suka fita daga wajen, jawo wayanta daga jaka Yasmin tayi tare da shigewa bayan motan Salman ta ja ƙofan, ɗagawayan tayi ta kara a kunni tare da faɗin "Yayana" "kuna ina Yasmin?" muryan Annur ya doki
kunnuwanta, zare ido tayi tare da kama kai, alamun menene Farisat ta mata da hannu, "kinmanta ma ko?" Yace cike da rashin jin daɗi, girgiza kai tayi kaman yana ganinta tare da faɗin"a'aYayana ina tune, mun raka Insu airport ne, yanzu haka muna hanyan gida, in sha Allah ba dajimawa ba zamu zo" ta idda maganan cike da tabbaci, "oh yau ne za ta tafi school ko?" Yaceanatse, "eh tama tafi" tace a hankali, "meyasa baki faɗa min ba da na zo nayi rakiya" dariyatasaki
tare da faɗin "ka rufa mana asiri kar Anty Laɗifa ta zane mu, Yayana kana ango me ze kai kawannan aikin" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "a'a ƙanwata, ƴar uwata fa zan raka kokuncire ni a dangi ne ban sani ba?" yayi maganar cike da zolaya, "a'a kana cikinsu tsundum" tacecike da jin daɗi, "to shikenan nagode sosai Allah ya sauketa lafiya, ku hanzarta banda africantime" "in sha Allah" tace tare da sauke wayan, "me ya faru?" Farisat tace tare da kafeta daido, "ashe yau ne friends day ɗin Yaya Annur" tace tare da rumtse ido, zare ido waje Farisat tayi taredafaɗin "what!" "Wallahi" tace tare da buɗe ido ta zubr mata, "taɓ lallai da ba mu je ba, wannanshegiyar humen leadern ta ci gidan mu" murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "Yaya Annur baze bari muƙi sani ba" tana kai nan ta sauke numfashi tare da lumshe ido...
"Ya mutumin ki" Farisat tace tare da kallon ta, buɗe ido tayi tare da faɗin "mutumin nanwataƙilaaljani ne, lamarin shi ya fara tsorata ni, yaƙi faɗin sunan shi garin shi anguwarshi, se dai kumaduk inda naje idan shi na kai" ta idda maganan cike da damuwa, "ba wani aljani, kar ki sakamaranki hakan, mutum ne wataƙila ma wanda ki ka sani sosai tunda ki ka ga haka" Sadamdayajuyo fuskan shi ta inda suke yace tare da mata alamun karta damu da ido, "ai lamarin ne dabantsoro Sadam, har fa candyn ya sani, munje bikin wani ɗan Aminan juna ya sani, hoton da mukayi
a can ma yana da su" murmushi Salman ya saki tare da faɗin "ku kuma matsorata ko, ki banzaci
lamarin shi Yasmin ze bayyana miki kan shi" jinjina kai tayi tare da faɗin "shawara me kyau" murmushi ya saki tare da miƙawa securitys pass ɗin shi, suna miƙa mai 8ta ja suka yi ciki, saurinbuɗe gate Baba Kalla da jikin shi ke a mace yayi tare da bin su da ido, "Sa'adatu ta dawo kuwaBaba Kalla?" Yasmin da ta sakko tace tare da kallon shi" "eh fitan ku ba jimawa ta shigo" yacetare da bin ta da kallon tausayawa, yasan tafi gaba ɗayansu shaƙuwa da Insu za tafisu jigata....
"Amma zaka jira mu ko?" Farisat tace tare da kallon Salman da ya sakko, "ya na iya Kushi, dolena" yace fuska a shagwaɓe, murmurshi ta saki tare da faɗin "ba zamu jima ba, yanzu zamufito"
jinjina mata kai yayi ta wuce da sauri tayi inda Yaya yake tsaye shi da su Babiya, "Yaya yaufriends day ɗin Yaya Annur" tace a ladabce, juyowa ta inda take yayi tare da faɗin "haka lokacinya gabato?" "Eh yanzu ya kira ya sanar" tace a natse, "to Allah ya tabbatar da alheri, zakune?"
"Eh members ɗin Aminan juna duk za su, in dai ka amince mu ma se muje" ta idda maganancikeda fata, murmushi ya saki tare da riƙo hannunta suka fara takawa, "ban da wasan da be daceba, banda hotuna marasa tarbiyya, ku nuna kalan na ku tarbiyyan a wajen" jinjina kai tayi taredafaɗin "in sha Allah" murmurshi ya saki tare da faɗin "zan turawa Salman kuɗi a account ɗinshi yacire ya ba ku, tunda ke sun kulle miki na ki, se ki mai magana ma kuje a buɗe miki wani" jinjinakai tayi cike da jin daɗi tace "Allah ya ƙara imani da wadata Yaya, ya jiƙan Anty ya sa ta huta"
"amen" yace fuska yalwace da murmurshi, kallon Nafisat dake tahowa ita da su Sahabee tayi
tare da faɗin "ki shirya muje tare" zare ido tayi tare da saurin taddata suka jera suka shigeciki....
Tura ƙofan ɗakinta tayi tare da shiga baki ɗauke da sallama, saurin tura abinda Yasmin batagane ko me ne ne ba Sa'adatu tayi a ƙasan fili tare da ɗagowa ta kalleta fuska ɗauke da
murmushin yaƙe, "ki na lafiya kuwa Sa'adatu?" Tace tare da duƙawa a gabanta ta riƙo
hannayenta, murmurshi ta saki tare da ɗaga kai, "yau Insu za ta tafi baki tsaya kunyi sallamaba, gashi har mun dawo daga rakata" tayi maganan a sanyaye kwaɓe fuska Sa'adatu tayi taredafaɗin "assignment ɗin mr Gushwan na kai, yau za'ayi submitting kin san halin shi, shiyasa nakai"jinjina mata kai tayi tare da faɗin "hakan da ki ka yi shine dai-dai, tace a ce miki za tayi kewanki"murmurshi ta saki nan da nan idonta ya cika da ruwan hawaye tare da jinjina kai, "kar ki yi kukaSa'adatu in sha Allah zata kasance cikin aminci" jinjina kai tayi tare da share hawaye, "zamujeshagalin abokai na bikin Yaya Annur, in zaki ki shiryo muje" tayi naganan tare da tashi, girgizakai
tayi da sauri tare da faɗin "kaina ciwo yake sister Yasmin so nake in sha magani in kwanta" "okayba matsala ki duba first aid za ki samu medik 55" jinjina mata kai tayi tare da bin ta da idohar tafice, sauke ajiyan zuciya me ƙarfi tayi tare da miƙewa ta dannawa ƙofan key ta dawo ta zaunatare da sauke numfashi a hankali, ɗaga filon tayi ta jawo ledan da ta tura lokacin da Yasmintashigo, buɗewa tayi a hankali ta ciro madai-daicin kwalban dake ciki, buɗewa tayi ta zazzagi
ƙwayoyin da ba ta san adadin su ba ta afa a baki tare da rumtse iso ta haɗiye duka....
Jingina da kan gadon tayi a hankali saboda hawa network da tayi kai tsaye, lumshe ido tayi
hawayen da suka cika a ciki suka biyo kuncinta, buɗe bakin dake kyarma tayi tare da faɗin"Antyki yafe ni, na kasa jurewa ne, banyi hakan da tozarta karamcinki ba, kar ki ɗauke ni a me mantaalheri, ba zan iya jurewa ba ne Anty, ba na da ƙarfin zuciya kaman ke, ba zan iya jurewa ba, bazan iya ɗauka ba, yayi min nauyi Anty, ina son shi son shi nake da dukkanin zuciyata Anty" taiddamaganan cikin sumbatu tare da zamewa ta kife a wajen....
"Kallon juna suka yi fuskokin su na yalwatuwa da murmurshi, kaya iri ɗaya suka saka hattadatakalmi iri ɗaya ne, ba ƙaramin kyau suka yi ba, "munyi kewan ki beb" Yasmin tace tare dagogehawayen da ya zubo mata, dan ƙarya ne ɗayan su ta yi ƙawalliya ba ta ce mata "kinyi kyauba" murmushi Nafisat ta saki tare da faɗin "kunyi kyau my Antys" murmushi suka saki tare dafaɗin"kin yi kyau me kyau" dariya ta ƙyalƙyace da shi tare da gyara zaman jakan da ta saɓa a ƙafaɗa
suka fice, suna shiga main parlor Balarabe shi da su Gude na shigowa, ko kallon inda sukebasuyi
ba se kallon Yaya da Babiya da ke bin su da ido cike da yabawa da shigan da suka yi, "zamutafi
Yaya, Hajiya mun fito" suka ce bakuna a haɗe, "kar a manta da addu'an fita gida da shiga mota, ku kula sosai, sannan kar a kira magrib kuna wajen" Babiya tace idonta akan su, jinjina matakai
suka yi cike da gamsuwa, "ina za'a haka?" Balarabe yace tare da zama kusa da Sahabee, "friendsday" Farisat tace tare da yin ƙofa, "ku jira na zo na ajiye ku" yace tare da yunƙurin miƙewa, "kahuta Yaya Balarabe Yaya Salman da Sadam za su kai mu" Farisat tace da ɗan sauti tare daiddasaficewa "okay ku kula, banda sakin fuska ga waƴanda ba su dace ba" yace tare da kallon Gudedata kafe su da ido, "in sha Allah" Yasmin tace a ladabce, "ba ku gaida iyayen ku ba" Yaya yaceanatse, "barkan ku da zuwa" Nafisat tace tare da bin bayan Yasmin da ta kusa ficewa danbamataji abinda Yayan yace ba.....
"Jummai yau an tuna da mu ne?" Babiya tace tare da kallonta cike da kulawa, murmushi Jummai
ta saki tare da faɗin "Hajiya ai muna tune dake, zuwan ne ba ko da yaushe muke samundamaba"jinjina kai tayi tare da faɗin "haka ne, in kuna zaune lafiya ma ai hakan ya wadatar tunda dawayaza'a dinga jin lafiyan juna ta nan" murmushi ta saki tare da faɗin "haka ne Hajiya" "to ya itaZuwairan da jiki?" "Alhamdulillah tana nan tana ta turawa" "to Allah ya raba lafiya, yasa daganan ta fahimci rayuwa" "ta fahimci rayuwa ma wallahi Hajiya, gaba ɗaya tayi sanyi, alamominnadama sun gama bayyana a ɗabi'unta" Jummai tace cike da tabbaci, "to ai haka ake so Jummai
Allah ya sa silan shiryuwanta kenan" "amen" suka ce bakuna a haɗe, gyara zama Suwaibatayi
tare da faɗin "mun same ku lafiya Hajiya?" "Alhamdulillah Suwaiba ya gida da yara da megidan?" Babiya tace kadaran kadahan, "Alhamdulillah suna a gaidaki" "ina amsawa" tace taredagyara zama, "mun same ku lafiya?" Gude tace idonta akan Babiya da ta yi mugun sanjawa, "Alhamdulillah ya me jikin?" "Alhamdulillah yana ta samun sauƙi" tace tare da gyara zama, "toAllah ya ba shi lafiya, shekaran jiya na je ni da su Farisat sun gaida shi, na ga jikin na shi dasauƙi
ba kaman lokacin da aka kai shi ba" "eh Alhamdulillah lafiya na samuwa a hankali" "ai hakadamalafiya yake a sannu a sannu yake zuwa, ciwo ne ke shiga farar ɗaya" Babiya tace tare da kallonta, "haka ne" suka ce a sanyaye.... Gyara zama Gude tayi tare da faɗin "Hajiya Abdussamad akwai abinda ya kawo mu wajenku, agaskiya mun san abinda muke aikatawa be kamata ba sannan be dace ba, muna masu nemanyafiyanku, ku yafe mana, sannan in sha Allahu hakan ba ze sake faruwa ba" tunda ta fara
maganan suke bin ta da ido har ta kai aya, sauke numfashi a natse Babiya tayi tare da faɗin"toai
abinda muke fata da burin gani kenan, Allah ya ƙara haɗa kawunan ku" "amen" Yaya da Balarabedake bin su da ido suka ce baki a haɗe, "muna fata Hajiya za ki manta komai" Suwaiba tacetareda kallon ta, "murmushi Babiya ta saki tare da faɗin "ai ban riƙe ku ba, komai ya wuce, fatanadama be wuce ku fahimci gaskiya ba" "Allah ya daɗa kyautawa, ina Sa'adatu ta zo ta zubominabinci" Balarabe yace dan be gamsu da zancen na su ba, "ka tashi kaje ka zubo da kan ka, Mari takai saman dining tun da ta gama, Sa'adatu kwana biyu ba wani isashshen lafiya ne da ita ba, nama cewa Tinene ta aiko mun da maganin shawara Mari ta dafa mata tasha, kaman shi kedamunta, ba ta da aiki se na yawan barci" ta idda maganan tare da banka mai harara...
Dariya ya saki tare da faɗin "ba wani shawara lalaci ne kawai irin na ta, Sa'adatu ba ta ƙi tayi tabarci daga safe har yamma ba" yana kai nan ya miƙe, "am akwai wani magana da Anty Gudekesan yi da ku Hajiya" Jummai tace tare da kallon Babiya, "to muna ji" tace tare da kallon Gude, "dama akan maganar da Suwaiba ta taɓa yi akan Farisat na son Sudais ne, shine na ce na amincea yi maganan yanzu" tace tare da kallon Yaya da Babiya, "wannan maganan ai ya daɗe da zamatarihi" Balarabe yace tare da zama ya fara cin abincin da ya zubo, gyara zama Babiya tayi taredafaɗin "ai yace be santa, yarinya har ta haƙura ta kawo wani, yanzu haka da baikon shi akanta"
"Hajiya Sudais ya tabbar mana da yana son Farisat, zan iya cewa ma wannan rashin lafiyandayake yi har da dalilin hakan, tunda ita ma yarinyar na son shi ina ganin in an ba wan canhaƙuri
ba komai ba ne, gida be ƙoshi ba ba'a ɗauka a kai dawa ba" Gude tace tare da kafe Babiya daido, "kinga malama kar ki kawo mana zantukan ki na san rai, lokacin da take haukan ƙaunanshi inaceke ki ka ce kin hana shi kallon ko inda take, ta haƙura ta dangana ta kawo wani ana mukubatunanyi musu baiko kuna kawo mana wani shirme, ko ba kusan nema cikin nema haramun bane" Balarabe yace rai ɓa ce, "a'a daina ta da jijiyan wuya Balarabe, maganan ai be kai haka ba, somuke a fahimci juna" Jummai tace tare da dafa shi, "haba Jummai wannan ai wawanci ne, watolokacin da Farisat take dakon son shi ba ta da gatan da za'a tsaya mata ta aure shi, se shi dakeyana da gata yaje ya sha abinda ya fi ƙarfin ƙwaƙwalwanshi ya birkitashi sannan ki zo ki namanawani zance dalilin santa ne ya kwantar da shi, to wallahi wanda Farisat ke so zamu bata" yakuma cewa zuciya ɓa ce, "Balarabe wannan maganan ba da kai a ke yi ba, sannan duk a indakaji
zancen ƙwaƙwalwan shi ya taɓu ƙarya ne, sharri ne kawai na magauta, kuma wannan abuitakanta Hajiya ta daɗe da nuna kwaɗayin son ayi shi, dalilin da yasa da ya furta yana sonta mukakwaso jiki dan a gyara komai a bawa sheɗan kunya, sannan baka da ƙarfin yanke hukunci akanwannan batun, uban ƴa shike da wannan powern" Suwaiba tace tare da kauda kai, "okay to" yacetare da cigaba da cin abincin shi....
"Gude Suwaiba Jummai ku tashi ku tattara ku fice mun daga nan, in dai wannan batun ya kawoku to ku sani ba zan taɓa goya baya ba" Babiya tace tare da miƙewa ta bar su a zaune, kallonsuSahabee dake ta zare ido Yaya yayi tare da faɗin "ku je ɗaki ku yi muraji'a" da sauri suka tashi
suka wuce, "Abdussamad na san kana da burin aurawa ƴarka mijin da take so, Farisat ta daɗedafurta Sudais take so, dan a lokacin Allah be yi zamu ɗau batun da wani mahimmaci ba ne" Gudetace idonta akan shi, murmushi ya saki tare da jinjina kai, miƙewa yayi a natse tare da faɗin"dukwanda ta zaɓa matsayin miji shi zan ɓata, sannan Balarabe da Lurwanu da Ali suna da powernyanke hukunci a dukkanin rayuwar ƴaƴana ba ni kaɗai ba, ba zan ba wa Sudais auren Farisat basaboda ba shi ta zaɓa matsayin miji ba" yana kai nan ya wuce side ɗin shi, murmushi Balarabeyasaki tare da ajiye plate ɗin hannun shi ya miƙe, "ku tabbatar kun fice kafin Hajiya ta fito danhakan ba ze muku kyau ba" yana kai nan ya shige ɗakin shi, canzo kaya yayi zuwa kayanƙwalloya nufi ƙofa har ze fita ya juyo ya nufi ɗakin su Sahabee tura ƙofan yayi tare da faɗin "ina Insu?"
"Ta tafi" Sa'eed yace tare da narke fuska, "ina!" Yace tare da shigewa ciki, "can, ba mu daɗedarakata airport ba" Sahabee yace tare da goge hawaye, "meyasa ba ku kiran ba" yace cike darashin jin daɗin, "Anty Farisat na ta kiran wayanka baka ɗaga ba, shine Hajiya tace "mu tafi kawai
tunda jirgin ya kusa tashi" "oh Allah my Insu" yace cike da rashin jin daɗi tare da zaro wayanshi, ganin kusan kira bakwai da tayi ya sa shi cire wayan a silent ya maida aljihu, "bari in na dawotraining zan kira ta vid call musha hira" yace tare da sakin musu murmushi, murmushinfarincini
suka saki tare da mishi Allah ya kiyaye suka cigaba da muraji'a....
"Yanzu Yaya Salman haka zaka barta ta shiga wajen nan?" Yasmin tace tare da danne bakintadatafin hannun dama, "to gama" Farisat tace tare da banka mata harara, "ba wani gama, ai gaskiyane, ba dadin mutumcin shi da nake gani baa da ba inda zaki" Salman yace tare da kallonta, "yanzu Yaya Salman yarda da abinda tace kayi!" Farisat tace tare da zare ido, "to ba dole ba, kawai ki je ayi ta kalle mishi ke" Yasmin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 109