"haka ne kuma
Muhammad" tace a sanyaye, "ya me jikin?" Salman yace cike da girmamawa, "yana ciki tunɗazuaka shigar da shi, ba mu tadda shi ba ma gaba ɗayanmu, Anty Gude tace sumewa ya fara sukashige da shi dan azaban yayi mai yawa" "oh Allah, Allah ya ba shi lafiya" yace cike da tausayawa, "ku muje ku gaida su Anty Guden" tace da kulawa tare da kallon su, ba musu suka mimmiƙe....
"Alhamdulillah da sauƙi Salman, amma wannan kai ka ɗaɗɗagota ko?" Babiya tace tare danunaFarisat da yatsa, murmushi ya saki tare da faɗin "anan na taddata" "to anyi abun ka" tace taredakauda kai, murmushi Shureim ya saki tare da faɗin "Allah ya ƙara mai lafiya ina ga zamuwuceinsha Allah zuwa gobe ko anjima in an fito da shi zamu leƙo" "to Allah ya bada lada Muhammad, iyayen na ku na ta can baya, ku biya ku gaida su kafin ku wuce" Babiya tace fuska faɗaɗe damurmushi, jinjina mata kai suka yi cike da girmamawa suka wuce, "wai me ki ka ɗauke ni ne?" Farisat tace tare da kallon Babiya, harara ta zabga mata ta kauda kai, "ai ance ka gaida mai
gaidaka, kuma Sudais me gaidawa ne, wallahi dalilin shi ya sani zuwa wajen nan" ta idda
maganan cike da jin zafin Gude....
Bin ta kawai suka yi da ido dan sun fahimci abinda take nufi, "ina ganin ni ma tafiyan nanzamuyi, tunda ba'a fito da shi ba" Farisat tace tare da kallon Suwaiba, "dama zaman ba abinda ze ƙarabanda fargaba, zo ku wuce in an fito da shi ma ba ganin yau ba se ya farfaɗo" Suwaiba tacedakulawa, jinjina kai tayi tare da faɗin "an faɗawa Antyn Habiba da Anty Munari kuwa?" "Banjinba, a cikin mu dai ba wanda ya faɗa se dai in Anty Gude ko su Halima" ta idda maganan tare dakallonsu, girgiza kai Halima tayi tare da faɗin "ba mu faɗa ba" "bari in na koma gida zankirasu, zamu leƙa Baban na ta ne?" Ta idda maganan idonta akan su, "eh muje, ai gaida mara lafiyaladane da shi ba zamu dan ita ba dan ubangiji zamu" tace tare da juyawa da nufin fara tafiya, "wayebe da lafiyan?" Babiya tace da mamaki, bayani Jummai ta mata a natse, "to ai bakwa je kukaɗai
ba, ku mu rankaya" tace tare da miƙewa....
"Bari mu gaida su Yaya tukun" Farisat tace tare da wuce wa inda suke ita da su Sahabee, gaidasusuka yi a girmame suka ma me jiki fatan samun lafiya suka dawo suka nufi can, gaba ɗayajikkunan su sanyi yayi da ganin yanayin da yake ciki, ba ƙaramin jin jiki yake ba, "to ke Iƙilimaki
kira Sa'adatu mana, duk da ba wanda yasan gawar fari amma ta zo su gana" Babiya tace muryaasanyaye, "na kira ta Hajiya tun jiya da muka kawo shi, yanzu ma haka ban daɗe da ƙara kirantaba, amsar ɗaya ne, ba ta nan a gari tana Yarban, in ta gama abinda take za ta zo" Iƙilima tacemuryaa karye, "dan Allah Anty Iƙilima kar ku sake kiranta, tunda kun sanar mata ku barta, in tayi
hankali ta zo in kuma har yanzu ba ta yi ba ta zauna, Allah dai ya tashi kafaɗunshi" Farisat tacecike da takaici, "amen Mommy, shima haka yace ɗazu, dama shine ya damu da yana songaninta, amma tunda yaji abinda take ta cewa yace a ƙyaleta kawai" tayi maganan a sanyaye, "ohni
Nafisatu, Sa'adatu me take son zama ne!" Babiya tace cike da damuwa....
"Me ta zama dai Hajiya?" Sadiya tace cike da takaici, "wallahi me ta zama dai, ai ta riga da tazama" Farisat tace cikin na ta takaicin, "Allah dai ya kyauta ya Mairah Mommy?" Iƙilima tacetareda kallon ta "tana lafiya Anty Iƙilima, wake kwana da shi?" "Yaya Salisu ne shi da abokinshi YayaLukman, mu kuma ɗaya ta zauna ɗaya ta je tayi girki" ta idda maganan a raunane, juyawaFarisattayi ta fice da sauri tana sakin hawayen da suka cika mata ido...
Suma nan fashewa da kuka suka yi gaba ɗayansu, haka suka baro wajen cike da tausayinsu, "wannan yarinya ba zata ga dai-dai ba" Jummai tace cikin muryan kuka, "ba zata gane tsiyandata shukawa kanta ba, se wannan bawan Allahn ya tafi ba ta zo sun gana ba" Babiya tace cikedatabbaci....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
ِبسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~ Created and written
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fourty seven
Sakkowa tayi a natse hannunta riƙe da hannun Mairah da aka ci ma ado na musammanidontaakan akwatina ukun da Fadila ke tsaye kusa da su, da mamaki ta kalleta tare da faɗin "shekarazasu yi a can ne?" Dariya ta saki tare da faɗin "ina ganin ni ma na tambaya tace shine yace tahaɗakaya da yawa dan za su daɗe" "to Allah ya temaka" tace tare da shigewa parlorn.... Da gudu Mairah tayi inda Nafisat ke zaune tare da mata magana cikin yarenta da ita kaɗai kegane abinta, zama tayi a two seater's tare da gaida Alhaji Jamil da Kamil da ke zaune, amsawasuka yi a mutumce fuskokinsu na bayyana jin daɗi, "yau su uncle Jabir sun makara" tace fuskayalwace da murmushi, "waya ce miki?" Muryan Jabir ya daki kunnuwan su, zare ido tayi taredafaɗin "oh Allah" ganin sun fito daga lungun ɗakin da SSB yake...
"Zo Angel" Abubakar yace tare da miƙa mata hannu, ba musu ta ɗaga mai hannayenta biyualamun ya ɗauketa, ɗaukanta yayi cike da so da ƙauna tare da sakin mata sumba a kumatu, "my
Angel ta daɗa wayau" yace cike da jin daɗin yarda da shi da tayi, murmushi suka saki ba taredasunce komai ba, "ina Abba?"(Sa'eed) haka suke ce mai, Alhaji Jamil yace tare da kallon Nafisat, "yana ɗakin shi" tace a natse, juyawa da duban shi ga Insu yayi tare da faɗin "aji nawa yakeaschool?" "Ya kammala primary secondary ze shiga" tace a natse, "ma sha Allah karatunshi yayi
sauri" yayi maganan cike da mamaki....
"Murmushi suka saki ba tare da sunce komai ba, gyara zama yayi tare da faɗin, "Insu" cikinmuryan abinda yake son faɗa me mahimmaci ne, ɗago kai tayi ta zube mai ido a natse, "inasonɗaukan Abba idan kun amince" ya idda maganan cike da fata me haɗe da magiya, guntunmurmushi ta saki duk da sanin waye shi a gidan shi se dai sanin matarshi ba me nuna damuwagadangin shi ba ne ya sa ta kafe shi da ido cike da jin hakan ba me yuwuwa ba ne, ganin ta saddakai ya sa shi sakin murmushi tare da faɗin "kar ki damu" murmushi saki tare da faɗin "uncleJamil Sa'eed ƙanine gare ni ba ɗa ba, duk da ina da iko ta wani ɓangaren akan shi se dai har
yanzu Yaya mahaifinshi na raye, baka shi ko rashin baka shi shine ze yanke wannan hukunci bani
ba" ta idda maganan a hankali, jinjina mata kai yayi cike da fahimta tare da faɗin "na fahimceki
Insu babu damuwa" jinjina mai kai tayi tare da kauda ido daga kan shi, sauke numfashinsamunsassauci Nafisat tayi cike da fatan Allah yasa kar a yardan mai a ƙasan zuciya tare da sakinmurmushi a zahiri.... Hira suka fara jansu da shi sama-sama har Hajiya da Yasmin suka fito, "oh Insu ke ce ki kafitodasassafe haka!" Yasmin tace cike da mamaki, murmushi ta sakin mata tare da faɗin, "Asmatafiddo ni, anyi maganan tafiya 12 tace wai yace 10 za su tashi" "haka fa tafiyan ya koma, mumaduk abun be mana ba" tace cike da rashin jin daɗin, "an tashi lafiya Hajiya?" Insu tace taredakallon Hajiya cike da girmamawa, "Alhamdulillah, ya kwanan Farisatu?" Tace cike da jindaɗi, murmushi ta saki ba tare da tace komai ba, "zan ga ranar da zaki fara amsawa" Nabila tacetareda sakin murmushi, "ba ko zaki gani ba" tace tare da banka mata harara, dariya ta saki taredafaɗin "ke ba ƴar 199..wani abu ba, amma halayyanki irin na su, ai kunyar first born an dainatunzamanin su Hajiya" murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "to ita dai tayi riƙo da al'adan mubatabari zamani ya taɓan mata shi ba" ....
"Wannan wahalar da kai ne Hajiya, kuma SSB ya hankalta da hakan za a samu matsala da shi, kunsan yanda yake da yanda ya shirya rayuwar shi da iyalanshi" Jabir yace cike da tabbaci, "totabarmuku ku kununa ba shikenan ba, amma ku nuna ita ma ta nuna ai abin ze ma yarinyar yawa" Hajiya tace tare da kallon su, murmushi suka saki tare da kallon ta, "eh mana ku tashi mukaryarana ta ɗaga, ina Alhaji ƙarami?" Ta idda maganan tare da kallon su, "Nafisat jeki kira shi" Insutace tare da miƙewa, sallama Asma da Kausar da Lubabatu da suka kaita sallama da danginBabanta suka yi dan tanan za su wuce airport....
"Bari in samu ladan yau Elizer" Insu tace tare da sakin ma me aikin da ke shirin zuba ma Hajiyaabinci murmushi, murmushi ta sakin mata ita ma tare da ajiye serving spoon ɗin da ta ɗaukaasaman plate ta ja gefe, murmushi Hajiya ta sakin mata cike da ƙauna, a kullumƙaunarta daɗaratsata yake, miƙewa tayi a natse ta ƙarisa kusa da ita ta fara serving ɗinta, murmushi Jabir yasaki ganin Lawiza na serving ɗin ta ita ma, tana gama zubawa ta koma wajen zamanta ta zauna, "sannu da aiki Anty Lawiza, please zauna mu karya tare" tace tare da kallonta cike da magiya.... Girgiza kai tayi a natse fuska cike da murmushin karamcinta tace "a'a ba mu daɗe da cinabinci
ba a ƙoshe nake" "to daga yau ki daina ci a can, tare zamu dinga ci dake anan" tayi maganancikeda ba da umurni, kallon Ibrahim Lawiza tayi da mamaki, murmushi ya sakin mata tare da jinjinamata kai, murmushi ta saki tare da janyewa daga wajen ta wuce, "meyasa ba ku barta a canba?" Hajiya tace tare da kallon Kausar, "ga ta nan a gabanki Hajiya ki tambayeta, wallahi ba yandabamu yi ta zauna a can in ya so yaje ta can ya ɗauketa su wuce ba amma tayi fin firin fir tacebazatazauna ba, mu kuma ba zama ya kai mu ba muka miƙe muka fito ita ma ta dafo mana baya yazamu yi, Anty A'isha ta fara magana Anty Luba ta dakatar da ita" Kausar tayi maganan cikedatakaicin Asma dake cin abinci hankali kwance....
"Asma'u me yasa ki ke son tada ma mutane hankali ne? Kin san dangin Babanku sarai kinsanƙananun maganganunsu amma ki ke aikata abinda ze ba su daman cin ma mahaifiyarki mutumci, yanzu kin bi yo su kin dawo kin bar uwarki da jin zantuka marasa daɗi kin kyauta kenan?" Taiddamaganan a natse idonta akan Asma, sadda kai tayi ba tare da tace komai ba, "ai dama na sanse
sun yi" Kausar tace cike da damuwa, "ita ma Anty A'isha tana son wahalar da zuciyanta neakanzantukan su, yau ta fara ji? Menene ba su faɗa ba tun daga fara shagalin bikin nan zuwa yaudataro ya watse? Taji damuwa ne kawai" Lubabatu tace cike da takaicin A'ishan, "a'a Anty Lubawallahi da zafi, ke kina ganin abinda ya faru ranar dinnern nan fa, kuma wallahi ta daure, dauriyan da tayi ban yi zaton zata iya ba ma, amma tayi shiru ta bi su da ido, kuma yau ɗinmazaniya cewa suma da gaskiyansu, da ita Asma ta zauna a can ɗin, canne ma a haƙƙu da ta zaunayajeya ɗauketa su wuce ba nan ba, dan ita ma bajin magana take ba, amma da gidan mijinta
yakamata ta tafi tun jiya yau su wuce tunda zuwa cin amarcin ya zame musu wajibi" Yasmintacetare da kallon Asma...
"Ku bar maganan tunda dai ya riga da ya faru, tattauna maganan ƙara jawo ɓarcin raine kawai" Kamil yace hankalin shi akan abincin gaban shi, "gobe uwar haka su Nafisat ana jami'a" Fadilatace tare da sakin murmushi, murmushi Nafisat ta saki tare da sadda kai, "ban san nemanzanceFadila" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "wani school ne?" Abubakar yace da kulawa, "Datti
Surajo" tace a hankali, "wow! Ki ce da babbar likita nan gaba muke zaune" yace tare da sakinmurmushi, murmushi ta saki tare da ƙara sadda kai, "aikuwa dai in ta maida hankali" Insutacetare da kallon shi....
"A'a zata maida mana in sha Allah, ai goyanki ce, kuma ita ma na san tana son gina kyakykyawanrayuwa nan gaba haka ne ko Nafisat?" Ya idda maganan tare da kallon ta, jinjina kai tayi taredakai ma Mairah cup ɗin tea baki, fashewa da kuka tayi tare da janye bakinta da sauri ta ɗagaƙaramin hannunta ta kai kan laɓɓanta, "oh Yaa Allah" tace da sauri tare da ajiye cup ɗintajuyoda ita, "da zafi ne!" Tace a rikice, jinjina mata kai tayi tare da shagwaɓe fuska, "sorry Ummi ne?" Tace da kulawa, jinjina mata kai tayi idonta akan nata fuskan da take gab da fashewa da kuka, "sorry Ummi ba zata ƙara ba" tace a natse tare da hura mata laɓɓan cike da tausayawa, murmushi Alhaji Jamil ya saki tare da faɗin "to ke ma ki yi haƙuri kar ki yi kukan" dariya sukasaki
gaba dayan su tare da kallon Nafisat da duk tayi wani iri....
"Ki ci abinci kar ya hucewa" Insu tace tare da kallon ta, jinjina kai tayi ta gyara mata kwanciyaajikinta ta cigaba da cin abincin a natse, haka suka cigaba da cin abinci cike da shaƙuwa, sunagamawa suka tattara suka koma cikin parlor aka dasa daga inda aka tsaya....
Miƙewa Jabir da Alhaji Munnir suka yi a natse dan tafiya office, "Insu idan barrister sun isopleasea kira mu" Alhaji Munnir yace cike da kame kai, murmushi Insu ta saki tare da faɗin "in shaAllah, ni fa akwai abinda ke ciwo ni tuntuni amma ina tsoron furtawa" tace tare da kafe shi da ido, "faɗi
kina da mu" Alhaji Jamil yace tare da miƙewa, "to shikenan tunda zakuna na bayana, wai uncleMunnir yayi auren nan ne ko maganan ya tafi a zance?" Ta idda maganan tare da kallongefendaLubabatu ke zaune, "auh ba ki samu labari ba?" Kausar tace tare da kallon ta, "na bar magananauren dai a ƙasa" tace tare da gyara zama....
"Ai har da tsohon cikinta, dalilin da yasa ba ta zo bikin Asma ba kenan, ta shiga watan haihuwawallahi" Yasmin tace tare da kallon ta, "ikon Allah rabo ati" tace tare da sakin murmushi, "Allahya shiryeki" Jabir yace tare da yunƙurin juyawa, saurin ja baya yayi dan kawo jiki da ɗaya dagacikin nurses ɗin dake kula da SSB tayi, cike da mamaki ya bi ta da ido ganin yanda jikinta kekyarma...
"Deborah lafiya kuwa!" Hajiya tace cike da fargaba tare da miƙewa zumbur, wuce wa indaHajiyatake tayi da sauri tare da nuna mata lungun ɗakin da SSB yake da yatsa tare da faɗin "yallaɓai!"
"Meyasa me shi!" Suka ce gaba ɗayansu a rikice tare da miƙewa zumbur, "ya yi motsi, hannunshi
ya motsa" tace a rikice tare da kallon Hajiya, ko kafin su kai ga furta kalma guda da ga shockɗinda suka shiga sallaman doctor ya doki kunnuwan su, da sauri Deborah ta miƙe ta nufe shi, besamu daman furta musu komai ba ya wuce ɗakin da hanzari, wuce wan su da sakanni sallamanYaya da Hassan da Sadam da su Lailah ya doki kunnuwan su, da gudu Insu da hawaye ke zaryaasaman fuskanta ta nufe su, faɗawa jikin Yaya tayi tare da sakin kuka me ƙarfi....
Tura ƙofan ɗakin suka yi bakuna ɗauke da sallama suka shiga a natse, miƙewa Nafi tayi dasauri
tare da faɗin "sannun ku da zuwa" murmushi suka sakin mata tare da ƙarisawa gefen da jerunkujerun roba suke suka zauna a natse, juyowa Sudais da yayi mugun rama yayi tare da zuba
musu ido, "Yasmin yau harda ke aka zo duba ni?" Yace a hankali, jinjina mai kai tayi cike datausayawa, guntun murmurshi ya saki tare da faɗin "nagode Yasmin, nagode, kusan kullumFariaat se ta zo duba ni, ba ta gajiya da hidima, baka gane me sanka na gaskiya se ka faɗahalinha uwali Yasmin, dubi yanda rayuwa ta maidani, bana da ƙafa ɗaya Yasmin na zama gurgu" yaidda maganan zafafan hawaye na biyo kuncin shi....
Sakin hawayen da ya cika mata ido tayi tare da girgiza mai kai, "kabar faɗin haka Yaya Sudaisbaka zama gurgu ba, za'a saka maka ƙafa zaka cigaba da tafiya kamar da" tace murya na rawa, girgiza mata kai yayi tare da faɗin "hakan ba ze sa ni ƙin kiran kaina gurgu ba Yasmin" "danAllahka yi shiru haka" tace a sanyaye, "wallahi haka yake irin zantukan nan tun ranar da ya farfaɗo" Halima da ta fito daga toilet tace tare da kallon su, "to ku barshi yayi ta yi mana, bayan
gurguntakan se mun haɗa mai da hauka" Farisat tace tare da banka mai harara.... Murmushi ya saki tare da faɗin "shima dab nake da farawa Farisat" "to Allah ya baka sa'a tundabaka iya amsan ƙaddara a duk yanda ta zo maka ba, tun daga kan rayuwar da ka zaɓawa kankazuwa wannan halin da ka tsinci kan ka a ciki duk jarabawa ne daga mahaliccinka, so yakeyagwada ƙarfin imaninka, wannan maganganun raunana maka imani za su yi ba ƙarfafa makaba, ka cigaba da neman gafaran mahaliccinka ka kyautata zuciyanka ka tuba akan zunubankakanemi hanyan gyara kurakuranka za su fiye maka wannan sumbatun" tayi maganan cike datakaici, jinjina mata kai yayi da sauri dan ya kasa magana, "Nafi zo ɗauki wannan basket ɗinki
zuba mai abinci ya ci" "tace tare da kallon ta, "to" tace da azama tare da nufar inda basket ɗindasuka zo da shi yake da sauri....
Zubawa ta fara a natse, "kaɗan kar ki cika" yace a hankali, "ya ci wani abun ne?" Farisat tacefuska a kame, "wallahi tun jiya banda ruwan tea ba abinda ke cikin shi" tace a sanyaye, "cikaplate ɗin" tace tare da miƙewa ta wuce inda ta hangi flaks da kayan tea, haɗa mai tea mekauri
tayi ta ajiye mai a saman table ɗin da ake ajiye wa a tsakiyan gadon majinyata dan cin abinci, "bismillah ka cinye duka, zama da yunwa ƙara illata ka ze yi, ka ga yanda ka koma kamanwani
ƙwarangwal" tace tare da banka mai harara ta bar wajen, murmushi ya saki tare da miƙa maNafi
hannu, da sauri ta temaka mai ya miƙe zaune, a natse ya fara cin abinci dan ya zame mai doleci
ne amma be da apatite ko kaɗan....
Sauke numfashi Yasmin tayi a hankali tare da kauda ido daga kan shi ta maida ga Halima, "inaAnty Guden?" Tace cike da kulawa, "ba ta daɗe da tafiya gida ba, taje yin wanka" tace a natse, "nan ba toilet ne?" Tace da mamaki, "tana ƙyanƙyami" tace tare da sakin murmushi, jinjinamatakai tayi tare da kauda ido, "ya su Insu?" Tace a hankali, kallon su yayi dan jin amsan da za subata, "suna lafiya, yau ma Yaya ya tafi wajen su shi da Sadam" Farisat tace a natse, "tare da Sa'eedzasu dawo ko?" Tace cike da fata, "Ina ganin" tace tare da zaro wayanta dake neman agaji, "ɗagakiran tayi ta kara a kunni tare da faɗin "isan mu kenan, yana cin abinci bari ya kammala" shirundaƙiku tayi kafin tace "to in sha Allah" tana idda faɗi ta sauke wayan, "Safinat ce ke songaidashi"tace tare da maida wayan a inda ta zaro....
"Ya jikin nata kuwa?" Yasmin tace da kulawa, "tana nan tana fama" tayi maganan tare da sakinhamma, "tana shan wahala fa wallahi" tace cike da tausayawa, "to ya zamu yi daga ni har itaƙaddarar mu ne a hakan, shiyasa da tace tana haihuwa zata saka allura na ce banga lefintaba"
"auh baki ga lefinta ba wato!" Tace da mamaki, "wallahi ban gani ba, bakya ganin wahalandamuke sha ne? Ni ma sawa zan" tace cike da gaskiyanta, "ah magana ya ƙare ai ba zaki ga lefintaba" Yasmin tace tare da sakin murmushi....
"Alhamdulillah" Sudais da ya ci fin rabi yace tare da ajiye cup ɗin tean hannun shi, kallonFarisatHalima tayi dan jin me za tace "ɗauke ai yayi ƙoƙari" tace a natse murmurshi ta saki tare dakwashewa cike da jin daɗin yanda ya ci abincin tace "wallahi tunda abun nan ya faru be ci abinci
me yawan na yau ba" murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "to ko gobe zamu dawo" murmushi
ya saki tare da bin su da ido, "zo amshi ki ba shi" Farisat tace tare da miƙa ma Nafisat wayantadata dannawa Safinat kira, ba musu ta amsa ta kai mai, gaida shi tayi a girmame cike da kulawa, amsawa yayi a mutumce cike da jin daɗi, suna gamawa ta dawo mata da wayan, amsa tayi tamiƙe tare da faɗin "bari mu leƙa Baban Sa'adatu muga yanayin na shi jikin" duk ƙirjin Sudais ya
buga wallahi ya ma manta da ita sam se yanzu da ta ambaci sunanta, miƙewa Yasmin tayi taredafaɗin "ka kwanta ka huta Yaya Sudais anjima in ka tashi ka ƙara cin wani" murmushi ya sakinmata tare da jinjina mata kai.... Kwaɓe fuska tayi tare da faɗin "kayi alƙawari?" Jinjina mata kai yayi a natse, Halima Nafi kuzama sheda in dai be ci ba ku kira ku sanar mun gobe ba zan ƙara girkowa ba" ta idda maganantare da ɗaukan basket ɗin da za su kai ma su Iƙilima, "in dai zaki dinga girko mun ni kuma nayi
miki alƙawarin ci" yace tare da sakin mata murmushi, murmushi ta saki me faɗi tare da faɗin"nayi maka alƙawarin ƙin gajiyawa har se ranar da ka ce na daina" tayi maganan tare da sakinmai murmushi, murmushi ya sakin mata cike da jin daɗi....
"Muje mu ma mu duba shi da jikin" Halima tace tare da bin bayan su, ba wanda yayi yunƙurinhana su a cikin su har suka fice daga ɗakin, kai tsaye ɓangaren da yake suka nufa, tun daganesasu ke jiyo kururuwa, zuciyoyi a tsitstsinke suka shiga wajen, ganin Iƙilima zaune daɓas a ƙasatana kuka me cike da rauni ya sa Farisat saurin juya baya, takawa Yasmin tayi a hankali kamar
me tsoron wani yajita ta ƙarisa kusa da Sadiya da ta kife fuska a bango tana kuka, dafata tayi atsorace, juyowa tayi da sauri ganin Yasmin ne ya sata faɗawa jikinta tare da faɗin "YasminBaba!
Baba! Baba ya tafi ya bar mu kaman yanda Mama ta tafi ta barmu, shikenan mu kuma ba mudauwa ba mu da uba, ba mu da sauran gata, meyasa mutuwa ta mana haka! Meyasa ba ta haɗadamu ba? Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, shikenan mu kuma na mu ta ƙare, majinginan damukejingina mu ji sanyi ya tafi, shikenan me ƙaunan mu ya tafi, wayyo Allah na, wayyo Allahkacecemu, ka mayar da komai mafarki din ƙarfin buwayanka" ta idda maganan a mugun raunane, kukaYasmin ta saki da ƙarfi, wani kewa na shiganta, wani lokaci me tsayi ta tuna kamar dai haka....
"Mommy!" Iƙilima tace tare da miƙewa zumbur, da sauri Farisat da ɗaga ƙafa da zummanbarinwajen, da gudu ta rungumota ta baya tare da faɗin "Farsiat! Kin ji abinda suka ce mana yau! Wai
Baba shima ya tafi ya bar mu" tayi maganan murya na rawa, a tare suka saki wani ƙaƙƙarfankuka tare rungume juna....
"Se na ji kaman tace ya motsa! Wai tana nufin ɗan uwana Sahabee ne ya motsa yau!" Lubabatutace a rikice, jinjina kai Jabir yayi tare da dafa musu baya da sauri gaba ɗaya bin bayan susukayi
har da su Yaya da ba su san me ke faruwa ba, suna ƙarisawa ƙofar ɗakin suka taka burki taredazube ma ciki da suke hango komai ido, aikin su suke cike da hanzari da ƙwarewa, kallonInsuLailah tayi tare da faɗin "me ke faruwa!" "Ya motsa" tace murya a disashe, "ma sha Allah" sukacebaku na a haɗe... Se da suka kusan haɗa awa a wajen ba tare da sun gajiya ya ƙosawa da tsayuwa ba, hangodoctorna doso ƙofa ya sa su gyara tsayuwa tare da fiddo zalaman sanin halin da ake ciki a bayyane, yana fitowa ya zame facemask, murmushin yanda suka zuba mai ido ya saki tare da faɗin"Alhamdulillah, nayi mamaki sosai, numfashin shi ya dai-daita, sannan ya motsa wasu gaɓoɓi
daga jikin shi" "ma sha Allah" suka ce cike da ɗin bin farin ciki....
"Waye Insiyyah?" Yace tare da baza musu ido, nuna Insu da sauri Ibrahim yayi, murmushi yasaki
tare da faɗin "a gaskiya yana matuƙar buƙatan ki kusa dashi" yayi maganan idon shi akanta, sadda kai tayi ba tare da tace komai ba, "yanzu wani hali yake ciki?" Yaya yace idon shi akanshi, "yana cikin aminci, mun mai allura dan ya samu daman hutawa yanda yakamata, in sha Allahmuna fatan ya farka cikin ƙoshin lafiya" jinjina mai kai suka yi cike da gamsuwa, excuse ɗinkanshi yayi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 71 Chapter of 109