Share this page
yayi zuciya na wasi-wasi, ba wanda yacewani abu a cikin su har se da ya kammala cinye tuwon shi tsaf sannan ya buɗe baki a natsecikeda kame girman da Allah ya ba shi yace "ka tafi da wayan a canzo wata a maida mata dukabindake ciki can, a sa ma wannan ɗin screen ka dawo mun da shi" yana idda maganan ya miƙe anatseya fice, tunda ya fara bayanin Ibrahim ya ba shi dukkanin natsuwan shi be samu damansaukeajiyan zuciya ba se da ya fice, sauke ajiyan zuciya me ƙarfi yayi tare da bin shi da ido.... Hajiya Insu na fita ta yada zango a two seater's, tana zama Yasmin ta ɗaga kiran, "baby" tacedaƙarfi, "baby Insu sim ki ka canza!" Tace da mamaki, "a'a ba sim ɗina ba ne, na Uncle ne, dazuwayata ta ci screen wallahi a school" tayi maganan cike da takaici, "oh Allah sorry ba daɗi, ammayakamata ki kyara, tun ɗazu Anty Farisat ke neman ki" "na san za ta neme ni, sun amso result ɗinne?" "Eh mana" tace tare da sakin murmushi, "haba! Nawa da nawa?" Tace a zumuɗe, "tagwayenalheri ne, AA da AA" tayi maganan cike da farin ciki, "na taɓa ki da alheri baby! Da gaske ki kewai!" Tace tare da miƙewa zunbur cike da ɗin bin farin ciki, "wallahi" tace na ta farin cikinnabayyanuwa.... "Hu hu hu, wayyo Allah daɗi, ya Yaya Salman yayi kuwa?" "Ya ze yi kuwa?, Kafin dai a fiddoresultɗin daga shi har ita ciwon jin sanyi ne ya riske su" dariya Insu ta saki me yalwa tare da karebaki, "wallahi gaba ɗaya banda rawar ɗari ba abinda suke, ke haƙwaransu har haɗewa fa suke, doctorna miƙo result aka kasa samun me amsa se da Yaya Sadam ya amsa ya buɗe yana faɗinsakamako duniyar zukatansu ta washe da haske me cike da farin ciki da annashuwa" "wowinasuke?" Tace a zumuɗe "yanzu Yaya Salman ya fita, Anty Farisat ta shiga toilet watsa ruwa, YayaSadam sun tafi tare, Nafisat na karatun exams, Antyn Habiba ta kwanta kanta na ciwo ta shamagani, Hajiya tana bitan karatu, su Sahabee sun manta ma sunyi barci, ni kuma gani ina tayaYaya hira" dariya ta saki me faɗi tare da faɗin "Allah ya shiryaki baby amsa ɗaya ya koma dubu" dariya ta saki tare da faɗin.... "Wai yanda zaki fi ganewa ne" "ina Sa'adatu? Banji ita kuma me take ba" shirun daƙiku tayi kafinta saki murmushin da sautin shi ya riski kunnuwan Insu tare da faɗin "ai ba ita ɗaya ba nebaki ji ba akwai Baba Mari a kwai Yaya Balarabe" "haka ne" tace tare da gyara riƙon wayan, "BabaMari ta tafi gida kin san dare yayi tsayi, Yaya Balarabe ya tafi zance, Sa'adatu ta je gaida Mamantatadawo" "oh da ba ta nan ne?" Tace cike da rashin damuwa, "eh ta koma garinsu jinya" "to Allahyaƙara mata lafiya" "amen, ga Yayan" tace tare da ba Yaya dake ta bin ta da ido wayan.... "My Yaya!" tace da ƙarfi, murmushi ya saki tare da faɗin "baby Insu ya karatun?" "Alhamdulillahya fara ɗaukan zafi" murmushi ya saki tare da faɗin "ki cigaba da jajircewa da dagiya duk zafindaze ɗauka ba ze taɓa ƙonaki ba" murmushi ta saki tare da faɗin "in sha Allah Yaya" "Allahyamukualbarka" yace cike da tsan-tsan kulawa.... "Amen Yaya an tsaida ranar ne?" "Eh in sha Allah nan da watanni huɗu zuwa biyar masuzuwa" yace a natse, ihu ta saki cike da farin ciki tare da miƙewa ta fara taka rawa me haɗe da tsalle, dai -dai nan SSB ya fito a natse, ba ta kula da shi ba se tiƙan rawarta take cike da matsanancinfarincikin da ta shiga lokaci guda, tsayawa cak yayi yana bin ta da ido buɗe, murmurshi Yaya yasaki tare da faɗin "to ya isa haka" tsahirtawa tayi tare da sauke numfarfashi me haɗe da haki.... "Kina shan maganin ki kuwa?" Yace cike da kulawa, jinjina kai tayi kaman yana ganinta taredafaɗin "eh Yaya" "wannan hakin fa?" Yace tare da sauraran amsa, "ban sani ba, haka yake muninnayi sauri ko gudu ko rawa" tayi maganan cike da rashin damuwa, "ki cigaba da shan maganinki akan lokaci" yace cike da bata umurni" jinjina kai tayi tare da faɗin "to Yaya" "da kyau ɗiyar kirki"yace sautin murmushin shi na sauka a kunnuwanta.... Shagwaɓe fuska tayi tare da faɗin "Yaya my phone" "zan tura miki kuɗi se ki canza screenɗinnasan bakyason rabuwa da wayan nan" murmurshi ta saki cike da farin ciki tare da faɗin "Allahƙara arziƙi da wadatan zuci Yaya" "amen" yace tare da miƙa ma Yasmin wayan.... Nayi hoton result ɗin ko in turo miki ne?" "Eh turo mun, zan samu na haskaka statut ɗina" dariyaYasmin ta saki tare da faɗin "auf na manta wayan ta zama akwala a she" ɓata fuska tayi taredafaɗin "zan haɗaki da Anty" "sorry" tace tare da danne dariyar ta, ɗago kai tayi da zummanmagana idonta ya sauka akan shi da sauri ta isa gareshi tare da faɗin "Uncle kana whattapp chart?" Ɗago kai yayi da zallan mamaki ya kalleta, narke fuska tayi alamun magiya, "ke ki nayi?"Ibrahim da ya fito yace tare da zabga mata harara... Tura baki gaba tayi tare da faɗin "eh mana" "to ke kenan ma" yace tare dw banka mata harara, "to ai shi babba ne, kuma yawancin manya ba sa yi" "to shi yana yi" yace tare da juyawa yasallame shi cike da girmamawa ya fice, murguɗa mai baki tayi tare da bin shi da harara, murmushi SSB dake hankalce da ita ya saki tare da ƙarisawa saman one seater ya zauna, "Uncleka ji ka nayi?" Tace kaman zata tsaga ihu, jinjina mata kai yayi a natse, murmushi ta saki taredamaida wayan kunni cike da yanayinta tace "ki yi saving ɗin number nan na Uncle ne se ki turomun a ciki in na gyara phone ɗin zan cire" sai-saita kanta daga dariyar da take ɓaɓɓaka tayi tareda faɗin "okay, ki gaidamun da Uncle tare da Ibrahim" "Uncle ze ji, amma banda Ibrahim" tacetare da sauke wayan, zama tayi a ƙasa kan capet kusa da ƙafarshi tare da faɗin "Uncle result ɗingwajin genotype ɗin su Anty Farisat ya fito, gaba ɗayan su A'A, mun kusa shan biki" ta iddamaganan cike da farin ciki idonta akan fuskanshi, jinjina mata kai yayi ba tare da yace komai ba.... Miƙa mai wayan tayi tare da faɗin "Uncle sa number na, Yasmin za ta turo da result ɗin a wayanka in na gyara waya se ka turo mun" "saka" yace a natse, murmushi ta saki tare da farajeranumber, "wani suna zan sa maka?" Tace tare da kallon shi fuska washe da murmushi, ganinbeyi ko wani motsi dan faɗa ba yasata faɗin "bari in rubuta maka baby Insu za ka fi ganewa, sunandaAnty da Yaya da su Yasmin ke kira na da shi kenan" ta idda maganan tare da rattafa mai sunan, miƙa mai tayi tare da sakin murmushi, sa hannu yayi ya amsa a natse ya ajiye a kusa da shi.... Haka suka cigaba da zama ba wanda ya ƙara yunƙurin cewa wani abu, jin shiru-shirun yayi yawaya sata miƙewa tare da faɗin "Uncle in haɗo maka tea?" Ɗago kai yayi ya kalleta tare da kaudakai, murmushi ta saki tare da faɗin "to bari in sa maka news kafin in haɗo" ta idda maganantareda kunna tv ta wuce kitchen da sauri, sauke numfashi yayi a hankali tare da lumshe ido, batawani jima ba ta dawo riƙe da treyn dake ɗauke da madai-daicin butan shayi me ɗaukanidodacup's ɗin shi, ajiyewa tayi a saman center table, zaran tissue tayi ta ɗago cup daya ta tsiyayamai ta saka a madadincin plate ɗin shi ta miƙa mai, ba musu ya amsa tare da gyara zama ya farashaanatse, komawa gefen shi tayi ta zauna zuciya cike da farin ciki.... Se da ya shanye cup's uku sannan ya ce ya ishe shi, murmushi ta saki tare da kwashewa takai dining room ta ajiye, tana fitowa ta tadda shi yana ƙoƙarin hayewa stairs, da sauri ta bi shi tareda faɗin "Uncle ka fara jin barci ne?" Ta idda tambayan tare da riƙo hannun shi suka taka stairsɗin a tare, be yi yunƙurin ba ta amsa ba be kuma yi yunƙurin ƙwace hannun shi ba, dan yasanbaze iya ba, haka suka cigaba da takawa a natse har suka haura, suna zuwa dai-dai ƙofan bedroomɗinta ta tsaya tare da faɗin "Uncle nan ne bedroom ɗi na" kallon ƙofar yayi kaman be taɓasaninda wanzuwan ɗakin a wajen ba, sakin hannunshi tayi tare da shigewa jikin shi a natse, goodnightUncle" tace tare da zare jikinta ta ja gefe, ba abinda ya iya cewa se nufar bedroomɗin shi dayayi, yana shigewa ta juya a guje tayi down stairs, kai tsaye wajen hoton su ta wuce.... Kissing ɗin kumatun Anty tayi tare da faɗin "good night Anty" ta na barin wajen tayi diningroom, kai tsaye inda ta zauna tayi ganin ba phone ɗin da ta bari a wajen ya sa ta fara dube-dube, ganinda gaske ba ya wajen ya sa ta tunanin ko Ibrahim ya ɗauka, fitowa tayi ta wuce sama cikedawasi -wasin me ze mata da waya in ya ɗauka... Kiran sallahn farko ta farka, toilet ta wuce kai tsaye, tana fitowa ta kabbarta raka'atanul fijr, tanaidarwa ta ɗaura subhi, ba ta samu tashi daga kan praymat ba se da rana ya fito ras, miƙewatayi ta maida Alƙur'anin hannunta inda ta dakko, naɗe praymat ɗin tayi ta buɗe ƙofa ta fice a natseba tare da ta cire hijabin da tayi sallah da shi ba, kai tsaye ƙofar bedroom ɗin da take kyautatazaton bedroom ɗin shi ne tayi, tana shirin knocking idonta ya faɗa kan door bell din dake ɗaukanido, kai hannu tayi ta danna a natse.... Dawo wan shi kenan daga masjid ya zauna saman sofa ya jiyo ƙaran door bell da mamaki yakunna na'uran dake bayyana mai me buƙatan ganin shi, fuskanta ne ya bayya tangararan, tanatsaye cikin hijab ɗin da yayi mugun amsanta, kafe ta da ido yayi cike da mamakin abinda yakawota.... Ta ɓangaren Insu kuwa ba ta gaji da dannawa ba, kuma ba ta ƙosa da jira ba, ta yi kusa 20minute's tana aikin abu ɗaya, kaman ance ta kalli saman madannin tana kai idonta ta hangi camera maƙale a adon da aka zagaye wajen da shi, murmushi ta saki tare da ƙure wajendaido, "Uncle kana gani na ko? Please ƙafafuna sun fara zafi ka buɗe mun" tace cike da shagwaɓa, beji me tace ba, se dai yana kallon yanda take ta motsa baki da fuska har ta kai aya, sauke ajiyanzuciya me ɗan sauti yayi ya miƙe a natse ya nufi ƙofan.... Yana buɗewa ta saki murmushi tare da nufan shi da sauri ta faɗa jikin shi, rumtse ido yayi taredajanyeta da sauri, ɗago kai tayi ta kalleshi tare da faɗin "kaji zafi ne Uncle?" Kauda kai yayi taredafaɗin "ki dinga natsuwa" zare ido tayi cike da jin haushin abinda yace tare da tura baki gaba, "good morning Uncle" tace a hankali tare da sadda kai ƙasa, juyowa yayi ya kalleta tare dafaɗin"morning" juyawa tayi kan nan a ƙasa ta nufi ƙofa ba tare da ta kuma cewa wani abu ba, tanagabda ficewa ta jiyo soft voice ɗin shi a natse ya doki kunnuwanta "sorry" zare ido tayi tare dajuyowa da sauri fuska washe da murmushi... Da sauri ta nufe shi tare da rungumeshi ƙam-ƙam "sorry Uncle" tace a natse, ɗaga kai samayayi tare da maida hawayen da suka cika mai ido, janye jikinta tayi tare da bin ɗakin da ido, ba ƙaramin haɗuwa dakin yayi ba, babu wani hayaniyan kaya abubuwa kaɗan ne daga gadosedrower dake gefe se bed table dake dauke da madai-daicin trey dake ɗauke da ruwa da cup's, sesofa, murmushi ta saki tare da kallon shi, ganin ita yake kallo ya sa ta faɗin "ɗakin ka yayi kyauUncle" guntun murmushi ya saki tare da wuce wa saman sofa ya zauna, zare ido tayi lokaci nafarko da ta ga murmushi a saman fuskan shi, "subhanallah murmushi yana maka kyau, kadingayi" tace a ƙasan zuciya idonta akan shi.. Saurin kauda kai tayi ta maida dubanta ga wani madai-daicin ƙofa dake gefe, cike da yanayintata kalleshi tare da faɗin "Uncle in gani?" Ɗago kai yayi ya zuba ma inda ta nuna da hannuido, jinbe ce komai ba ya sata faɗin "thank you" ta nufa wajen a natse ta tura ƙofan a hankali ta shige.... "Subhanallah tace lokacin da ido ta ya faɗa kan jerin takalman dake saƙalƙale, yanda kasanwani shago se da takalma ta shiga, juyawa inda jerin kaya suke tayi nan ta fahimci dressing roomtashigo, ba abinda babu na kayan sakawa se wanda be mallaka ba, takawa tayi a natse ta shigeciki, wani madai-daicin waje da a ka killace ta leƙa, "wow" tace lokacin da idonta ya faɗa kanwani fitinannen dressing mirror, an jera kai duk wani abun buƙata, kallon gegen shi tayi wani showglass ne da ke ɗauke da wasu gitinannun parfume's murmushi ta saki tare da shigewa ciki saboda ƙofa da ta hango, tana turawa idonta yayi kyakykyawa gani da bathroom, "subhanallah" tace tare da sa kai ciki baƙi ɗauke da addu'a, "an shirya wa duniya, toilet ne harda tv!" Tacetareda kama haɓa, kai hannu kan wani madai-daicin wardrobe me ƙofan glass tayi, tana buɗewaidonta ya faɗa kan jerin rigunan wanka da huluma da towels, jinjija kai tayi tare da ci gabadabaza ido, ganin abun gani ba ƙarewa ze yi ba ya sata tattaro ƙafafunta ta fito a natse.... Tana fitowa asalin bedroom ɗin ta tadda shi zaune a inda ta bar shi, murmushi ta saki taredafaɗin "bye Uncle" ba abinda yace har ta fice, miƙewa yayi ya shige ciki dan shiga toilet,,, kai tsayeɗakinta ta koma, tana shiga tace "anya waƴan nan suna tunanin mutuwa ma kuwa! Toilet mawajen fidda ƙazanta ba a barshi haka ba" ta idda maganan tare da hayewa gado ta ja bargo... Ba ita tasan halin da duniya ke ciki ba se da 12:30 ta buga, sakkowa tayi tare da rufe hammadahannun damanta ta shige toilet, watsa ruwa tayi ta ɗauro alwala saboda kiran sallah da akayi tana cikin toilet, tana fitowa ta kabbarta sallah, tana idarwa ta ja stool ta zauna ta fara shafamai, tana gamawa ta zari tissue ta goge fuska ta hurgashi cikin dustbin ta nufi wardrobe doguwar riga ta zura light green bayan bra da pant da ta saka, baby hijab light green ta zura ta ficeanatse, tana sauka ta hango Hajiya da zugan iyalanta, murmushi ta saki tare da nufarta kai tsayekolurada su SSB dake zaune gefenta ba tayi ba.... "Kin tashi?" Tace da kulawa, jinjina kai tayi tare da faɗin "na sha barci, yau babu lecture" jinjinamata kai tayi cike da ƙauna, ɗagowa tayi da nufin tashi daga jikinta idonta ya faɗa kan SSBdasuAlhaji Jamil, murmurshi ta saki tare da faɗin "Uncle Jamil!" Murmushi ya sakin mata taredafaɗin "ganin ki ya dawo?" Ƙaramar dariya ta saki tare da faɗin "da gaske ban ganku ba lokacindana shigo" murmushi ya saki tare da kauda kai, "in kwanan ku?" Tace cike da girmamawa, "Alhamdulillah" suka ce baku na a haɗe, juyawa ga su A'isha tayi tare da faɗin "Anty's ina kwana"amsawa suka yi a daƙile cike da rashin jin daɗin kulasun da tayi... "Uncle Kamil na ajiye maka saƙon abota jiya a facebook baka duba ba" murmushi ya saki taredafaɗin "ai na fi sati ban hau app ɗin nan ba" "kai ma baka damu da su ba ko?" Tace tare da nufar inda yake, "gaskiya, in kin ganni a wajen nan na je duba halin da ƙasa ke ciki ne" murmushi tasaki tare da faɗin "kaman Anty, haka take, ba ta damu da hawa ko wanne ba kuma kusankullumdatan ta a buɗe" murmushi ya saki tare da bin ta da ido, dan yanda take maganan zaka fahimci tayi matuƙar kewa, murmushi ta saki tare da faɗin "yaranka nawa uncle Kamil?" "Biyu" yacetareda kallon ta, "wow amma baka yi aure da wuri ba?" Dariya ya saki saboda yanda tayi tambayantare da faɗin "nayi" "kin ci abinci kuwa?" Abubakar yace tare da kallon ta, "a'a" tace tare dagirgiza kai, "to je ki ci" yace da ɗin bin kulawa, murmushi ta saki tare da miƙewa ta wuce anatse.... Tsaki Lubabatu ta ja tare da faɗin "yakamata Hajiya ki koya mata tarbiyya dan ina ganinuwar bata ba ta gamsashshe ba, a ce yarinyar haka babu natsuwa babu sanin girmama na gaba, danAllah dubi fa yanda ta zauna tana jera ma Kamil tambayoyi se ka ce wata babbar mace" "sangarci ne kawai ya mata yawa" A'isha tace tare da sakin murmushi, "wallahi wannan ba sangarci bane, rashin tarbiyya ne kawai" Lubabatu tace a ɗan zafafe, ba wanda yace ko uffan a cikin suHajiya, haka suka yi kiɗinsu suka yi rawar su... Insu da bata san me suke tattaunawa ba kuwa abincinta ta ci a natse tana fitowa Lawiza nashigowa, da sauri ta isa gareta ta rungume tare da faɗin "nayi missing ɗin ki over, ya jikin Abulkhair?" "Ya warware yau har ya tafi school" "ma sha Allah, ya Iman?" "Tace a gaisheki" "inaamsawa ace mata ta dinga samun albarka please" murmushin yanda tayi maganan Lawizatasaki tare da bin ta da ido, "serious fa" tace tare da nufar gefen da su Hajiya ke zaune suna bintada ido.... Tana shirin zama Hajiya tace "jeki shirya kar mu ɓata lokaci" da mamaki ta kalleta tare dafaɗin"anguwa zamu!" "Eh maza hanzarta" "to" tace tare da nufar up stairs da gudu, "bi a hankali dai" Hajiya tace fuska cike da murmushi, "Lawiza ya me jikin?" Hajiya tace da kulawa, "AlhamdulillahHajiya" tace tare da raɓewa ta fice.... "Hajiya ba dai kina nufin da yarinyar nan za'a wajen nan ba?" Yasmin tace da mamaki, "wai kumeyasa bakwa tauna magana in zaku fiddota ne? Ke yanzu kinga yakamata ki mata irin wannantambayan?" Kamil yace murya a kausashe, "ƙyaleta Kamil, ai sun haifu, cikakken ɗa shikenunawa iyayen shi ya girma ya kawo ƙarfi" Hajiya tace ba tare da nuna wani alamu na jinhaushi ko wani abu makamancin wannan ba... "Allah ya baki haƙuri Hajiya, amma se nake ganin kaman wajen nan be kamata aje da yaraba, wallahi tun jiya Samha ke mun nacin son zuwa na ce ba zata ba" A'isha tace tare da gyara zama, "ai da baki hanata ba, me ze hana su zuwa kuwa?" Hajiya tace tare da gyara zama, miƙewaJabiryayi tare da faɗin "ina ganin zamu jira ku a mota" "ai se mun gabatar da la'asar tukun Jabir" Hajiya tace da kulawa, "to hakan yayi bari mu je in kun fito se ku sanar" "to shikenan" tacefuskayalwace da fara'a.... Tana komawa ta faɗa toilet wanka ta ƙara sheƙawa ta fito a hanzarce, jan stool tayi ta zaunatareda matso da kayan make up gaba, tsara simple make up tayi me cike da burgewa babu wani hayaniya tattare da shi, amma fa yana ɗaukan idon wanda ya kai idonshi kai, miƙewa tayi tanufi wardrobe, bin jerin kayanta tayi da ido cike da neman wanda ze tafi dai-dai da kwalliyanta, zaro wani dakakken lace tayi golden milk, gown ce wacce tayi masifar tsaruwa, murmushi ta saki taregyara zaman ƴan ciki ta ɗaura lace ɗin a sama, "subhanallah" tace tare da ɗaukan nostril meadon heart ta saka, hijab ta zaro ta kabbarta sallah, tana idarwa ta kashe ɗaurin gaban goshi, cikashe adonta tayi da earing da jewelry da agogo da awarwaro masu ɗaukan ido, body spray'stakwaso ta feshe jikinta da su, nan da nan ta fara fidda ƙamshi me sanyi... Takalmi me faɗin tsini ta dakko da jaka golden milk, madaidaicin veil ta ciro ta yafa a samankashima golden milk, da sauri ta fice dan jin kiran da Hajiya ke kwaɗa mata, tana sakkowa Hajiyatace "ma sha Allah" murmushi ta saki tare da faɗin "na bata muku lokaci" "a'a muje, yanzusukadawo daga masjid suma" Jinjina kai tayi ba tare da tace komai ba ta dafa mata baya, suna fitowasuka tadda su tsai-tsaye, da sauri tayi inda ta hango Ibrahim, da kallon ƙasan ido ya bi ta, dantunfitowan su ya sauke idonshi a kanta... "Abban Iman jiya baka ga wayata ba a dining room!" Tace cike da fargaban kar yace be gani ba, saka hannu a aljihu yayi ta ciro waya ƙirar iphone ya miƙa mata, cike da mamaki ta fidda idowajetare da faɗin "iphone 16 promax!" Murmushi ya saki tare da faɗin "eh" "kunyi magana da Yayane?" Tace da mamaki, "no SSB ne yace a baki" da ɗumbin mamaki ta juya ta zuba mai ido, kafintace "to ina wan can wayan?" "Me kuna zaki da ita?" "Abban Iman akwai abubuwana masumahimmanci a ciki fa" tace kaman za ta saki kuka, "kin duba wannan ɗin baki gansu ba ne?" Yaceidon shi akan ta.... Girgiza kai tayi tare da kunnawa, murmushi ta saki lokacin da idonta yayi arba da hotontaitadaAnty, gyara tsayuwa tayi ta fara dubawa, "je ki shiga mota jiran mu ake" yace tare da nunamatamota, jinjina kai tayi ta juya motan da ta ga Hajiya ta shiga, kusa da ita ta shige tare da cigabadabincikan wayan, ba abinda ke wan can da babu a wannan, murmushi ta saki tare da saka wayanajaka ta ba ma titi hankali.... Kai tsaye white house suka yi wato villa, tunda suka doshi wajen suke cin karo da jami'antsaro, suna ƙarisawa ciki police suka musu ƙawanya, nan suka bubbuɗe musu mota suka sakko, dasauri ta fara rarratsa mutane, se da ta isa kusa dashi sannan ta sauke numfashi tare da kamahaɓan hannun rigarsni, tunda ta iso wajen ya fahimci na ta gab da shi, se dai be ba ta wani alamun da zata fahimci hakan ba, "bismillah yallaɓai" ɗaya daga cikin police ɗin yace taredanuna musu hanya, jinjina kai yayi ya fara takawa a natse, yana ajiye ƙafa take ajiye nata, yanaɗagawa take ɗaga nata, murmushi Hajiya da ke bin su da ido ta saki zuciya na hasaso abindabegamsu da shi ba.... "Thank you Uncle" tace a natse murya ƙasa-ƙasa, ba abinda yace mata se wajen zama da akanuna musu na alfarma, yana zama ta zauna a kusa dashi, murmushi Alhaji Munnir ya saki taredakallon Jabir dake cewa "a ƙarshe SSB ya samu cingwam"... "Mr president shin har yanzu kana kan ƙudirinka?" Father dake zaune ta can sama yana hangensu SSB yace tare da kallon mr president, "Father ina ganin be kamata muna ta dawo da maganabaya ba, muyi fatan alheri kawai" mr president yace tare da miƙewa ya nufi barin wajen, saurinbin bayan shi masu ba shi tsaro suka yi cike da biyayya, murmushin yaro yaro ne Father yasaki tare da kallon sauran mabiya, "akwai wani ƙudiri na kai da kai da yake son cikawa, se dai besanze yi wasa da daman da ya shigo hannun shi ba ne" kallon shi suka yi cike da nazarin maganganun shi, "ku tashi muje" yace tare da miƙewa ya bi inda mr president ya bi.... Kai tsaye ya isa inda Hajiya ke zaune ya ɗurƙusa har ƙasa ya gaidata, murmushi Hajiya ta saki cike da yaba karamcin shi tare da shafa kan shi a natse, ba ma su SSB hannu yayi a mutumcesuka gaisa, komawa sama yayi fuska faɗaɗe da murmushi, bin shi kawai suke da ido cike danazarin abubuwan da su ka hanga tattare da shi, yana zama me magana da yawun president yamiƙe ya isa inda aka tanada dan gabatar da bayani, nan ya jero zantukan shi akan fidda SSB matsayin ɗaya daga cikin ƴan takaran da jama'iyya me ci tayi, da kuma buƙatan SSB ya fitoyayi jawabi a gaban ƴan jam'iyya tare da ƴan jarida dake ta kashe musu ruwan hotuna da video's.... Kallon shi Alhaji Jamil yayi tare da faɗin "tashi mana" lumshe ido yayi a natse ya miƙe, ta kubiyuyayi ya tsaya cak tare da buɗe hannun shi ta baya, da sauri Insu dake biye da shi da ido ta mikecike da farin ciki ta kama hannun, murmushi Hajiya da su Abubakar suka saki, takaici kuwayahana ƴan matan Hajiya ko kallon su, cike da takunshi na ƙosassu kuma lafiyayyun mazajeyahaye wajen, suna hawa ya saki hannunta a natse ya ƙarisa wajen da aka mai iso, banda sakinmurmushi ba abinda take, masu ɗaukan rahoto kuwa ba su yi ƙasa a gwiwa wajen fidda matafitinannu hotuna ba, masu video's ma ba a barsu a baya ba, dai-daita zaman microphone ɗinyayi a natse, kai a ƙasa ya bude baki tare da ɗaga musu sallama, "na ji daɗi har da wannan jama'iyyame ci a yanzu ta ga dacewan cewa in zamo ɗaya daga cikin ahalinta, ina

Chapter 35 of 109