Share this page
Murmushi ta saki tare da faɗin "Allah ya kai mu" "za'a je ayi gulma kenan" Kamil yace taredasakin dariya, "kai fa wani zubin jikin ka baya faɗa maka dai-dai, wai Hajiya kin faɗa mai gabaakeda shi kuwa?" Kausar tace tare da banka mai harara, dariya suka saki cike da burgesu da sukayi, "wallahi uba nake a gare ku" yace tare da gyara zama, "gare su dai ga sunan a zube a gabanka" tace tare da nuna su Insu, "ƴan arziƙi irin albarka ba" yace fuska yalwace da murmushi, "AntyKausar in kin je kar ki manta da amso min dambu" Insu tace da ƙarfi saboda kai ƙofa da sukayi.... "Ku koya daga garesu, ku kenan kullum ƙafarku na ƙaiƙayi se kun fita ku ke jin daɗi" Alhaji Jamil yace idan shi akan su A'isha, "ai mu da su ba ɗaya ba Yaya Jamil" Lubabatu tace tare da kaudakai, "me ya raba tsakanin na ku!" Yace cike da mamaki, "to wa suke da shi a raye wanda ya zamemusu dole se sun fita sun gani? Mu kuwa uwarmu na raye, dole mu fito mu ga yanda ta kwana" tace cike da jin abinda ta faɗa ba wani abu ba ne, sakin baki su ka yi cike da mamaki idansunabin ta da kallo me cike da zallan mamaki "suna da Hajiya, ita ma uwace gare su, duk da tasuuwarba ta raye kamar yanda ki ka ce, amma ita tana raye" Yasmin Bertuwa tace fuska yalwacedamurmushi babu wani alaman ɓacin rai a fuskanta se dai a zuciya ita ta san irin ƙunan da kalamansuka mata, murmushi SSB ya saki tare da faɗin "Mommy na zo mu yi wani magana" murmushi tasaki tare da miƙewa ta nufe shi a natse, "ke da ki ka yi maganan dambu se ki ka tuna mundasaƙonki na Dimau, muje in baki ki ba mu na mu kason" Farisat tace tare da miƙewa ta ja hannunInsu, miƙewa tayi tare da faɗin "karki ɓallani fa... Kallo me cike da ɓacin rai Hajiya ta bi ta da shi tare da miƙewa cike da ba da umurni tace "ki same ni a ciki" tana kai nan ta wuce, kallon Alhaji Jamil tayi ganin irin kallon da ya mata yasatamiƙewa ta bi Hajiya da sauri, tura ƙofan a hankali tayi ta shiga baki ɗauke da sallama, tanaɗagowa da zumman yin magana maruka biyu suka ziyarci kuncinta cikin tsan-tsan ɓacinrai Hajiya dake sakin huci ta nuna ta da yatsa manuniya tare da faɗin "haukan ki da rashin ta idonki ya isheni Luba, na gaji da ji da ganin wawancinki, ki nesanta kan ki dani daga yau, bana buƙatanƙara ganinki a inda nake, wawiya shashasha ki na matsayin uwa kina zubda kima da mutumcinki a idan ɗiyoyin cikin ki, to na yafe miki zuwa inda nake dan ba abinda zuwan na ki ke haifa munsedamuwa da baƙin ciki" ta idda maganan cike da fushi, duƙawa kai tsaye tayi a saman gwiwoyintadan ta fahimci fushin da tayi ba na wasa ba ne, idanta na tsirarar ruwan hawaye tace "Hajiyakimin aikin gafara, wallahi banyi maganan da wata manufa ba, ki yi haƙuri hakan ba ze ƙarafaruwa ba"... "Yi min shiru shashasha, sau nawa ki ka kuma bayan kin ce ba zaki kuman ba? Su ɗin suneyaranahalak malak in baki sani ba ma yau ki sani, sun fiki kima da mutumci a idona dan ba sa jayayyadaumurni na, ba kuma su baƙanta mun" ta idda maganan cike da ɓaci rai, "dan Allah Hajiya ki yi haƙuri ba ta kyauta ba kam amma ki ba ta dama" A'isha da ta shigo tace jiki a sanyaye, "rufemunbaki babban banza, ke ma dama ina da cikin ki, jira nake ki kai ni bango tunda kin kawo kanki seku buɗe kunnuwan ku da kyau ku jini, wallahi duk wanda ya ƙara katsalandar a cikin wani abudaya shafi ɗaya daga cikin su se nayi mugun saɓa mai" tana kai nan ta fice ta barsu cikin tashinhankali, dan sun fahimci ta kai ƙololuwar ɓacin rai.... Miƙa mata ledan da ta ciro tayi tare da faɗin "wallahi Shafa'atu ta yi ƙoƙari" murmushi ta saki tare da faɗin "gaskiya tayi ban fa tura mata ko biyar ba" "ah! Gaskiya yakamata ki tura matakuwa, dan ze iya yuwuwa jarinta ta kwashe dan faranta miki" "zanyi hakan, ina da account ɗinAnty Habiba zan tura mata ta can se ta cire ta ba ta" "hakan yayi, ke dama wai haka wannanAntyLuban take!" Tace cike da mamaki tare da gyara zama, "shareta tayi wanda yafi wannanma, amma na san wannan karon Hajiya ba za ta ƙyaleta ba" "gaskiya yanda take bin ta da idokaɗai yaisheta hukunci, buɗe ki ba mu namu kason mu samu na hira anjima" dariya Insu ta saki taredafaɗin "bana san neman zancen ku na masu ciki" "ke ma ai ba ma da tacewa akan ki yanzu, danyanda na ga lamari na tafiya ba'a ce babu ba" zare ido tayi tare da faɗin "rufa mun asiri manaMalama ƴar jarida, ciki yanzu! A'a wallahi tsumayeshi shekaru biyar ma su zuwa" "aikuwa, baki ji da kyau ba ne, sldalla ni buɗe" ta idda naganan tare da jawo ledan.... "A'a jira in kwance" Insu tace tare da janyewa ta fara kwance ƙullin da aka ma ledan, "nayi matuƙar farin ciki da ganinku a yanda na ganku Insu, na so Anty na raye ta ga hakan da idanunta, na san za ta so ganin hakan" tayi maganan idanta na bin fuskan Insu dake sakin murmushi, "danAllah kar ki gajiya, ki ƙara dage damtse wajen nuna mai kula amanan Anty ne, ki ƙarawa kanki haƙuri akan wanda ki ke dashi, zaman tare se da kauda kai" jinjina mata kai tayi fuska faɗaɗedamurmushi tare da buɗe ledan ta ajiye a tsakiyan su tare da faɗin "ɗiba iya cin ku" "a'a ɗibanmanakar mu yi aikin hankali" dariya ta saki tare da faɗin "ke dai ɗiba, in zaki zarcewa tunani na ai dakatar dake zanyi" "auh haka abun yake?" Tace tare da kai hannu cikin ledan... "Baby's" Yasmin da ta shigo saɓe da Mairah tace tare da ƙarisawa ciki ta ajiyeta a gefenFarisat, "my Mairah na barki a can ko?" Farisat tace tare da miƙa mata Kantun Ghanan da ta ciro, "gaskiya rayuwarki da matsala baiwar Allah, wannan fa koyawa yaro ƙwaɗayi ne" Yasmintacetare da ɗaukan ɗaya ta kai baki, "ke me ki ka yi kenan?" Tace tare da banka mata harara, "auhhaɗani da ita zaki yi!" Tace cike da mamaki, "to na ji zan gyara" tace cikin son barin maganan" murmurshi Insu ta saki idanta akan su, "baby Insu in na ce banyi farin ciki matuƙa da taddakuyanda na ganku ke da Uncle ba na munafunci kaina" Yasmin tace tare da riƙo hannunta, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "na sani" "please a dage kar ayi sanya, ki cigaba da bashi zafafa kar ki bari suyi ɗumi bare sanyi" murmurshi ta sakin mata tare da jinjina kai, "ku tashi muje ga bayin Allah, mun baro su can mun zo nan mun tare" Farisat tace tare da miƙewa ɗaukedaMairah da Bitimis da Kantun Ghanan da ta ɗiba, ba musu suka miƙe suka dafa mata baya... Yana sauka daga napep ɗin ya bi number gidan da aka sauke shi da ido kamar me koyonkaratu, jan napep me napep yayi ya wuce ya yinda ya taka a hankali ya isa bakin gate ɗin, tsayinsakanni ya ɗauka yana bin gate ɗin da ido, gida ne ƙato na alfarma, daga gani ba a daɗe da kammalaginashi ba, ɗaga hannu yayi ya buga gate ɗin a natse, buɗewa wani gabjejen mutumyayi wandatsayi da ƙiba ya wadace shi, razanan nan kallo ya mishi cikin muryan shi me amo da firgitarwa yace"lafiya!" Kallon sakanni ya mai tare da kauda kai cike da rashin tsoro ya ciro waya ya dannanumberta tana ɗagawa ya saka a speaker tare da faɗin "ki mishi bayani" murmushin na sanza'ayi haka ta saki wanda ba su gagara ji ba, tare da faɗin "Timo barshi ya shigo" jinjina kai yayi kamantana ganinshi tare da ba shi hanya, shigewa yayi a natse rufe gate ɗin yayi ya juya ya shigegabadan mai iso ciki.... Suna shiga parlorn ya bi duniyan da aka narka a ciki da jdo, be yi mamaki ba dan ya san zataiyafiye da hakan, "my handsome!" Tace cike da zumuɗi ta nufeshi gadan-gadan ta rungumeshi tsam, be hanata ba sannan be ba ta gudummuwa ba, sakin shi tayi tare da jan hannun shi tayi indakujeru suke ta zaunar da shi a saman one seater tare da faɗin "na sani, na san ba zaka iya gudunaba, ba zaka iya rayuwa ba tare dani ba, na san zaka dawo gare ni Abdull, daga ƙarshe ga kataredani" ta idda maganan cike da zumuɗin ganin shi tare da rungumeshi tsam-tsam... Jin be maida mata martani ba ya sa ta janye jiki cike da mamaki tare da faɗin "Abdull kar ka damu akan komai, ina tare da kai, babu wani abu da zan bari ya kusantoka matuƙar ze iyacutarda da rayuwar ka" ta idda maganan tare da riƙo hannun shi idanta na yawo a saman fuskanshi dake sadde, "sauke numfashi yayi a hankali tare da ɗago kai ya watsa mata rinannun idanunshi da kalamanta ya ƙara birkitasu cike da tuhuma yace "dama kin san kina tare da laluran ki kakusance ni!" Ya jefa mata tambaya idan shi ƙyam a nata, kallon sakanni ta mai tare da janyehannunta ta miƙe ta juya da nufin barin wajen, "Sa'adatu!" Yace a tsawace, "eh" tace a tsawacetare da juyowa ta fuskance shi, guntun murmushi ya saki tare da faɗin "me za'a kira hakankenan?So ko ƙi!" Girgiza kai tayi a razane tare da duƙawa da sauri a gaban shi ta riƙo hannun shi... Ganin irin kallon da yake mata ya sata faɗin "so ne yasa hakan Abdull, ina matuƙar ƙaunarkakasani, ina son rayuwa da kai na har abada ka sani, tsoro ya sani aikata hakan, tsoron rasakainkagano ina ɗauke da cutan ya sani aikata hakan, tsoro nake kar ka gujeni a gaba, ban shiryawahakan ba, ba na da ƙarfin zuciyan ɗaukan hakan, shiyasa na magance faruwanshi kafin ta faru, kar ka zargeni akan abinda na aikata, kar ka mun kallon wacce ta cika son kanta da yawa, nayi alƙawarin tsaya maka, zan baka gudunmuwa a dukkanin rayuwarka, ba abinda cutan ze maka, zaka dinga shan magani mafi tsada daga campany mafi girma da daraja a duniya"... "Dubi gidan nan Abdull, kalle shi da kyau duk mallakin mu ne, zo muje in nuna maka iringirmada yawan kaddaran da muka mallaka, duk gwagwarmayan da na sha dan tarasu dan munayi, dan mu rayu cikin farin ciki na har abada" ta idda maganan tare da zare hannunta ta kamofuskan shi da kaman ze yi aman wuta ta ƙure idon shi da narkakkun idanunta, sadda kai yayi hawayen da suka cika mai ido suka zubo, ɗago kai yayi tare da faɗin "wani farin ciki ki ke maganaa kai Sa'adatu!" "Wani farin ciki ya rage mun a duniya, komai ya ƙare, kin kawo ƙarshen komai da kan ki" yayi maganan a zafafe, girgiza kai tayi a kiɗime tare da faɗin "a'a! Yanzu zamu fara rayuwa, kar kadamu kan ka, Abdull dube ni, kalleni da kyau" bin ta da ido yayi a natse, "duk raunikan nandankai aka ji mun, dan in inganta rayuwarka ne Abdull, ko kaɗan ban ji zafi ko ciwon su ba, sabodanasan dan abu mafi soyuwa a zuciyata aka ji mun su, na shirya amsan abinda yafi hakan indai akan ka ne" ɗago haɓarshi tayi a hankali cike da wutan son shi dake a zalzalan zuciyanta tace " kar kasare Abdull, Sa'adatu na tare da kai, komai ze wuce zamu rayu a duniyar mu ni da kai, cutandamuke ɗauke da shi ba ze taɓa kashe mu ba se ranar da Ubangijin mu ya yanke mana" zarehannunta daga kan fuskan shi yayi a hankali tare da kafeta da ido, ganin irin kallon da yakemataya sata faɗin "please!" "Komai ya ƙare, komai ya zo ƙarshe, ba abinda yayi saura, kin kasheAbdull da san ranki, kin tarwatsawa wanda ki ke ikirarin so da ƙauna rayuwa da san zuciyarki, mahaifiyata da ta raine ni cike da so da ƙauna tayi gwagwarmaya akai na dan ganin na zamanagari, ta hana kanta ci da sha dan inganta rayuwata yau a gabana take kuka me ƙuna wandakefitowa daga ƙasan zuciyarta saboda ni, ni Abdullmuminu, ban saka mata da komai ba se datakaici da baƙin ciki, saboda ni take wannan kukan!, Se dai a zahiri nike a baɗini ke ce!" Yaiddamaganan da ƙarfi tare da shaƙota ya miƙe a fusace ya jata da ƙarfi ya haɗa da bango taredamatseta a jikin bangon da dukkanin ƙarfin shi.... "Zaki mutu kafin ta ga mutuwata, zaki girbi abinda ki ka shuka kafin in kai ga mutuwa, ba zanbarki ki cigaba da rayuwa cikin farin ciki ba, dan ke annobace cigaba da rayuwarki ba ya daamfani" ya idda maganan cikin rishin kuka tare da ƙara matseta, banda wutsil-wutsil da ƙafafuba abinda take da buga bango dan da gaske ta shaƙu, idanunta sun firfito saboda tsabanazaba, zare ido guard ɗin da ya shigo yayi tare da nufarshi a hanzarce ya fara janye shi, se dai ya ƙi sakinta dan ba abinda yake san gani kaman mutuwanta a wannan lokacin, ganin haka ya sashi kiran sauran abokan aikin shi biyu da ke waje da sauri suka shigo nan suka mai taron dangi sukajanye shi daga gare ta da ƙyar, rufuwa akan shi suka yi suka shiga duka kamar waƴanda Allahyaaiko.... Yana sakinta ta zube a ƙasa tana sakin numfarfashi me haɗe da tari, banda murza wuya baabinda take dan ji take kaman har lokacin hannun shi na shaƙe da ita, ɗago idon da yayi zajur ɗinazaba tayi tare da sauke wa akan shi, ganin yanda suke bugun shi ya sata faɗin "ya isa haka" dakatawa suka yi cike da bin umurni tare da ja gefe, ɗago kai yayi ya kalleta da fuskan shi dasuka canzawa kamanni tare da sakin murmushi, murmushi ita ma ta saki tare da faɗin "meyabaka nishadi haka?" "Hango ƙarshen ki mana, Sa'adatu in dai ina raye mutuwa ta zame miki ƙawa, ba zan taba hutawa da farmakan ki ba har se na aika ki can" yayi maganan cike da alwashi, dariyata saki me sauti wanda ya sarƙe mata da tari, daƙyar ta samu ya lafa, ɗaure fuska tayi taredafaɗin "in baka raye fa!" Kallon sakanni ya mata tare da faɗin "ba na raye ne" dafa bango tayi ta miƙe tare da nufar ɗaya daga cikin guard ɗin, miƙa mai hannu tayi fuska a ɗaure, miƙa mataƙaton goran dake hannun shi yayi, nufar Abdull tayi gadan-gadan tana isa gare shi ta ɗagagoranda dukkanin ƙarfin da ya rage mata ta sauke mai a kai, ƙara ya saki da ƙarfi tare da zubewaawajen sumamme, dariya ta saki me ƙarfi me haɗe da zuwan ƙarfaffan kuka me sauti ta cigabadabuga mai goran a ka, banda zuban jini ba abinda kanshi yake amma ba ta fasa buga mai ba, ganinyanda kan yayi daga-daga ya sa ɗaya daga cikin guard ɗin ƙarisawa gareta da sauri ya riƙogoranda take niyyan sauke mai, ture shi tayi da ƙarfi ya faɗi tare da ɗaga goran, "ya mutu!" yacedaƙarfi, tsayawa tayi cak tare da kallon shi kamar wata wawiya, jinjina mata kai yayi tare damaidaduban shi ga Abdull da kan shi yayi jaga-jaga a kwance, maida dubanta a hankali tayi gareshi, ganin irin ɓarnan da ta mai ya sata ja baya da sauri tare da faɗi ƙasa daɓas, ta bi shi da razanannan kallo me cike da firgici, ɗago hannunta dake kyarma tayi ta ɗaura a saman bakinta dalaɓɓanke ɓari tare da fashewa da razanan nan kuka... Kuka take me ƙuna tana bin shi da idon dake shatatan zafafan ruwan hawaye, ba wanda yahanata a cikin su, zabura tayi ta yi kan shi da hanzari tare da ɗago kan shi da ake iya hangoabinda ke ta ciki, saurin jefar da kan tayi tare da ja gefe, ido a warwaje, rarrafawa tayi ta kamoƙafafun shi tare da faɗin "tashi Abdull! ta shi! Ba zan iya kasheka ba, na faɗa maka ba zaniyakashe ka ba, ina sonka, aure zamu yi mu rayu cikin farin ciki ka ƙi fahimtana, ka ƙi saurarana, kaƙi gane abinda nake cewa, tashi ka ji zan faɗa maka wani abu, kar ka tafi ka barni, kana damatuƙar mahimmaci a gareni" ta idda jero sumbatun cikin fita hayyaci, ganin irin kukandatakeyasa ɗaya daga cikin guard ɗin matsawa kusa da ita ya taɓa ta, doke hannunshi tayi tare dacirewa da sauri ta jefar gefe... "Sorry Ma'am ki matsa mu fiddashi" yace cike da rarrashi, girgiza kai tayi tare da faɗin "baindazaku kai mun shi, mijina ne! Aure zamu yi!" Ta idda maganan a ɗimauce tare da ƙwaƙumeƙafan, banko ƙofar Ɗan amanan Sarari yayi tare da ja gefe ya tsaya fuska babu sauƙi, kafin su yi yunƙurin isa gare shi Ɗan kuka da sauran muƙarraban sun faɗo, "kul!" Ɗan kuka yace taredakallon guard ɗin dake ƙoƙarin nufosu, saurin dakatawa suka yi zuciyoyi na bugu da ƙarfi sabodaSarari da Kainuwa da suka shigo da sauran yaran.... "Dan Allah ki yi haƙuri Mommyn Hafiza, abinda kwanciyar hankali be bada ba rashin sa babadawa ze yi ba, kin ga su Mommy can ma ba sa tare da duk wani yunƙurin ki, shawarata ki haƙura ki amshi ƙaddarar ki da hannu biyu, wallahi se kin so yarinyar da aka kawo za ta sankangidanki, kar ki manta fa ke ce wacce ta tsara gidan, akan tsarin ki gidan ze cigaba da tafiya, inki ka ce zaki tashi hankalin ki, ba riban da zaki samu, aure an ɗaura an kawo ta cikin gidanmeyarage? Ba wani abu da zaki yi da ze hana shi shiga inda take yau" matan Jabir tace cike da ganinhakan shine gaskiya, "hmm Hassana baki san zafi da raɗaɗin da ake ji ba ne" uwar gida mecapasity tace tare da kaɗa ƙafafu.... "Haka ne da gaskiyanki, ban san raɗaɗin da ake jiba, ko in ce ba mu sani ba ma gaba ɗayanmu, amma ba wanda ke da tabbacin watarana ba ze ɗanɗana ba, mu dai fatan mu ki yi haƙuri kuzauna lafiya" "babu wani zaman lafiya tsakanina da ita, ban san tana gidan ba ma, bare indamuda sanin ya take har maganan zaman lafiya ya shigo" tace a harzuƙe "hakan ma ta gode" matanAbubakar tace tare da sakin murmushi, "hmm gamu ga Allah dai" matan Kamil tace tare dakallon su, dariya matan Jabir ta saki tare da faɗin "ya dai Mommyn Alpha?" "To ita ta ga natama, kowa kuma yasan ba ta fi ta komai ba, hasalima se dai ta nuna mata wani abun, mu kuwa fa?Muna da tabbaci watarana za su yi, yaushe?, Wace? Duk ba me masaniya" ta idda maganancikeda tausayin kanta, "wallahi fa" matan Jabir tace tare da sakin murmushi, "ai duk Alhaji Munnir yaɓallo mana wannan ruwan muna zaune zaman mu na lafiya" matan Abubakar tace cike datakaici, sallama Alhaji Jamil yayi fuska kadaran kadahan.... Murmushi suka sakin mai cike da girmamawa, "kuna nan dama?" Yace tare da tsayuwa idanshi akan su, "eh yanzu muke shirin tafiya dama" matan Jabir tace tare da miƙewa, "to ku wucegidajenku kai tsaye tunda yamma ta kawo jiki" "to" suka ce tare da fara tattara komatsansu.... Yana tsaye a wajen suka gama shiryawa suka sallame su suka fice, se da ya tabbatar da ficewan su side ɗin gaba ɗaya ya zauna saman two seater's, miƙewa tayi zumbur kamar wacce akatsungula, murmushi ya saki tare da fadin "Malika" juyowa tayi a fusace tare da ɗaga mai hannualamun dakatar da shi... Cike da mamaki ya bi ta da ido, "kar ka ɓata yawunka wajen ce mun in zauna zaka kawo watakahaɗamu dan mana nasiha, bana da wannan lokacin, sannan ina fata kuɗin ka ya isko ka?" Guntunmurmushi ya saki tare da miƙewa cike da kamalanshi, "kar ki damu, bana da lokacin haɗakudanmuku nasiha, ba zamanki ta zo ba, babu amfanin haɗakun, sannan na ga kuɗi ina matuƙar godiyada wannan babban kyauta, gaskiya ba kowacce mace ba" yana kai nan ya juya ya fice fuskaɗauke da murmushi saboda kiraye-kirayen sallah da aka fara.... Da kallo me cike da mamaki ta bi shi, yana ɓacewa ganinta ta ja dogon tsaki tare da faɗin"namiji be da kunya sam a rayuwa, dan Allah dubi yanda yake wani magana da izza kaman be aikatakomai ba, dama Annabi (s.a.w) yace "in baka da kunya kayi duk abinda ka ga dama" sabodakaajiye ni dole in maka kyauta, banzan kuɗin yaudaran da ka turo mun na maida maka da abunka" tana kai nan ta juya ta wuce bedroom ɗin ta cike da ɗin bin takaicin shi.... "Sannu da aiki" Farisat tace ma Lawiza dake ta aikin saka musu abinci fuska cike da murmushi, murmushi ta sakin mata tare da fadin "a ci lafiya" "Anty Lawiza zauna mana" Insu tace idontaakan ta saboda ganin tana shirin barin wajen, murmushi ta saki tare da jan kujera ta zauna, "bansan yaushe Lawiza za ta saki jiki damu ba, kullum se an tuna mata zama tare damu" Hajiyatacefuska ɗauke da murmushi, murmushi kawai suka saki ba tare da sun ce komai ba.... Suna kammalawa suka tattaro suka dawo cikin parlor, tashi daga inda yake Jabir yayi ya dawokusa da SSB tare da miƙa mai file ɗin da ya ɗakko, amsa yayi tare da faɗin "na me ne ne?" "Akanwan can binciken ne da muka yi magana, na so in bari se gobe in baka a office amma se nagasaninka a yau yana da matuƙar mahimmaci" jinjina kai yayi tare da buɗewa a natse, ƙure shi daido Insu tayi zuciyanta na bugawa dan tasan maganan, yana gama nazartan shi ya rufe yamiƙamai tare da faɗin "ina ganin ka samu lawyer kawai zamu cigaba da maganan a office" jinjinakai yayi tare da faɗin "se na biyu"... "Oh Jabir na fa faɗa maka, ba na son kawo aikin office gida" "I'm sorry shima yana da mahimmanci ne" yace fuska cike da murmushi, "menene?" "Anjima baƙin da vice president yanemi alfarma za su zo, an shirya tarban a office ɗin cikin gidaa" "yaushe!" Yace cike da mamaki idan shi akan shi, "Amin afwa, anjima da ƙarfe 10pm, ganawan sirri ne a nan za'ayi" kallonsakanni ya mai tare da kauda kai, "I'm sorry na cin yayi yawa, kar su ga kaman ana ƙin sanzamanne" yayi maganan cike da magiya, "alright" yace a natse.... "Nafsii, maganan nan ne!" Insu tace a hankali tare da kamo hannun shi, jinina mata kai yayi tareda bin ta da ido, ganin yanda duk tayi fuskan tausayi ya sa shi jawota fuska yalwace da murmushi tare da faɗin "yana raye, kuma za su sake shi" zare ido tayi cike da zumuɗi ta juya ta inda suFarisat suke tare da faɗin "da gaske ne Yaya Samir ze dawo yana raye" saurin mimmiƙewasukayi suka dawo kusa da ita cike da zumuɗi tare da tambayanta a inda ta jiyo tabbaci.... Kallon su yake da mamakin irin san da suke mai, sadda kai suka yi ganin irin kallon da yakebinsuda shi cike da jin nauyi, murmushi ya saki tare da faɗin "sarauniyar zumuɗi ban gama maganabahar ki fara iddawa" murmushi Insu ta saki tare da kallon shi, "se ƙasa ta bada lawyer wandazetsaya mai ayi shari'ar ƙarshe da shi, a saƙon da suka turo mana sun ba da tabbacin yarjewadasahannun.." se kuma yayi shiru, murmushi Jabir ya saki tare da kafe shi da ido, ganin yanda sukazuba mai ido ya sa shi rufe fuskan Insu da ke kan shi ƙyar tare da faɗin "barrister Aminat na tsayin shekaru 10 da ze yi kafin a yi zaman ƙarshe, samun labarin rasuwarta da suka yi neyasa su tsahirtawa ko wani ze tuntuɓesu matsayin lawyern da ze maye gurbinta kamar yandawan can karon iyayen shi suka tura"... "Yanzu Uncle za su sake shi kenan ba tare da anyi zaman ƙarshen ba!" Yasmin tace cike daƙosawa dan jin amsa, murmushi ya sakin mata ganin yanda zalaman jin amsa ga bayyana asaman fuskanta tare da faɗin "ba ze yuwu ba Mommyna, sun dai yanke hukuncin komawadashi court ne dan ayi zaman ƙarshe, in lawyern shi yaje ma to in be je ba ya zama na su kenan, wataƙila zancen shiga court ɗin suka faɗa mai, dan yayi magana wa iyayenshi ko akwai wandazetsaya mai wata ƙila ba su fahimta ba" ya idda maganan cike da hasashe, "inna lillahi wa innailaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati wa a khalifni khairan min ha, Anty ina ki ke? YaugaYaya Samir na buƙatan ki"

Chapter 91 of 109