me faɗi tare da faɗin "gobe ne in sha Allah, jibi 7 muke da lecture" jinjinamata kai tayi cike da gamsuwa, "kin san suna tsakiyan semester ne, se da uzuri, jiya ma kafinLabib ya taso se da ya shiga class" jinjina mai kai tayi cike da fahimta ta juya tare da faɗin"ƙarfenawa za su tashi" "4 ne" yace da ɗan ƙarfi, "okay Allah ya kai mu" tace tare da shigewa gabansusuka nufi cikin gida saboda an shige da amarya tun ɗazu.... Da sallama suka shiga general parlor, bin su Farisat dake zazzaune fuska cike da alhini tayi daido tare da ƙarisawa kusa da Sha'awanatu ta zauna tare da faɗin "lafiya?" "Lafiya lau" taceasanyaye, "ina Yasmin ɗin?" "Yanzu suka kaita side ɗin Kawu Abdussamad" jinjina kai tayi sabodagane inda alhininsu ya samo asali tare da miƙewa a natse cike da kulawa ta kalli Nachma taredafaɗin "muje ki watsa ruwa ki kwanta" ba musu ta miƙe dan dama abinda take son yi kenan, "bari
in tafi gida zan shigo da safe" Ziyada tace tare da miƙewa....
"Ba zaki bari a kai amarya a dawo ba?" Farisat tace idonta akanta, "ba zan iya ba gaskiya, danbanshirya ganin rauni a saman fuskokin ku ba" tace kaman zata saki kuka, murmushi Insu ta saki
tare da faɗin "haba yanzu ai mun girma" "a'a gaskiya se da safe" tace tare da nufar ƙofanfitadasauri, murmushi Insu ta saki tare da girgiza kai ta wuce ciki Nachma ta dafa mata baya.... Ciro kayan barci doguwar riga cotton me laushi tayi ta ajiye mata a gefenta tare da faɗin"ki
shiga ki watsa ruwan, please bari in zo" jinjina mata kai tayi tare da bin ta da ido har ta fice, kai
tsaye inda first aid box ɗin su yake tayi, curo paracetamol tayi ta wuce fridge ta ɗakko ruwamarasanyi ta nufi parlorn a natse, tana zama Lailah da Suwaiba da Jummai suka fito da Yasmindaketa sharɓan kuka a natse, wuce wa ɗakin Babiya suka yi da ita, ba su daɗe ba suka fito Babiyabiyea bayansu tana sharar hawaye, ƙofa suka nufa da ita kai tsaye, dan sun san suka tsayawa wani
tsaron za'a samu ga su Yaya na jiransu, da sauri Insu ta miƙe tare da faɗin "bari ta sha magani" tayi maganan tare da nufarsu a natse i....
Tsayawa suka yi tare da baza mata ido, kana ganin yanda take tafiyan kasan dakiya ne kawai, tana isa Yasmin ta faɗa jikinta tare da fashewa da raunataccen kuka me tsuma zuciyan mesaurare, guntun murmushi ta saki wanda ta jiyo sautin kayanta tare da zameta a hankali cikedadakiya tace "kar ki sani kuka mana babu me rarrashi" murmushi suka saki zukata na rauni, "hanzarta Insu su Yaya na jiranta" Khadijatu tace da kulawa, jinjina mata kai tayi a natse taɓalloparacetamol ɗin ta miƙa mata, amsa tayi hannu na rawa ta kai baki, murmushi ta saki taredabuɗe bottle ɗin ruwan ta mata alamun ta buɗe baki, buɗewa tayi a natse, zuba mata ruwantayi
da kulawa, haɗiye maganin tayi tare da baza mata ido, riƙo hannunta tayi a natse suka fice.... Fashewa da kuka Nafisat da su Sahabee suka yi cike da tausayinta kansu, miƙewa Farisat tayi tadafa musu baya da sauri dan ta kasa dakiyan ƙin fitan, suna fita suka tadda Yaya da su Ali daHassan tsai-tsaye da alamun jiran fitowanta suke, murmushi ta sakin ma Yaya tare da mai kallonina za ta shiga, saurin ƙarisawa wajen Balarabe yayi ya buɗe mata ƙofan baya, saka ta tayi anatse tana dai-daita zama ta riƙo hannunta ta matse da ɗan ƙarfi tare da faɗin "fatan rayuwamecike da aminci ƴar uwata zamu yi kewa" ta idda maganan murya na rawa, fashewa da kukamecike da rashin madafa Yasmin tayi tare da damƙe hannun Insu dake cikin nata, kuka Farisat tasaki jiki na ɓari ta rungumo Insu, janye hannun Insu dake cikin na Yasmin Lurwanu yayi zuciyana
rauni tare da ma Yaya iso, murmushi ya saki ya shige a natse, buɗe ƙofan can ɓangarenBalarabeyayi Hassan ya shiga suka kulle motan, shigewa mazaunin driver Lurwanu yayi Ali dake tashararhawaye ya shiga gefen shi, key ya ma motan ya nufi gate ɗin da Baba Kalla ya wangale sukaficea natse....
Se a lokacin kuka ya kuɓucewa Insu, zamewa tayi a hankali ta yi ƙasa tana kuka me gunji, nansuLailah suka fara nasu dan yanayin da take kukan dole in dai da ɗigon imani a zuciya a zubdamatada hawaye, da gudu Farisat ta koma cikin gida dan ta kasa jurewa jin kukan, kamota Balarabeyayi a natse tare da faɗin "shii daina kuka, kukan ki shi ze tada hankalinta kin san ba ta ƙaunar ji
ko kaɗan" murmushi ta saki tare da saka hannu ta goge hawayen cikin rawar murya tace "zatayi
farin ciki ko?" "In sha Allah" yace tare da danne hawayen da suka cika mai ido, kamota Lailahtayi
tare da faɗin "kin manta ke ki ka yarda da ta aure shi saboda fahimtar ze riƙe miki ita da amana, ki kwantar da hankalin ki Insu Yasmin za ta kasance cikin aminci tare da Shureim" jinjina kai tayi
ta goge hawaye tare da faɗin "bana da haufi game da riƙon da ze mata, kukan ma ban sannamenake ba, be kamata in yi shi ba, ji nake kawai yana zuwa" ta idda maganan a raunane... Bin ta suka yi da duba me cike da tausayawa, share mata hawayen Lailah tayi tare da faɗin"nasabo ne, dole dama ki yi, se dai ya isa haka kar ya cutar da ke" jinjina mata kai tayi tare da janhanci suka rankaya suka nufi cikin parlor, suna shiga suka tadda Farisat ta haɗa kan su Nafisat
waje ɗaya suna ta rera kuka me ban tausayi, "oh Allah Farisat me yasa bakya girma ne wai?" Khadijatu tace cike da takaici, ɗago kai tayi tare da faɗin "Anty Khadijatu sabo ne dole muyi" "toya isa haka dan Allah, ke da zaki ƙarfafasu ke kuma ke raunatasu, ku yi shiru Yasmin ba nisatayi
da ku ba, tana kusa da ku" tace cikin muryan rarrashi, jan hanci Nafisat tayi tare da faɗin"inaAmmi?" "Gata nan" Shafa'atu tace cikin sanyin jiki tare da nuna Insu dake zaune idonta akansu.... Da sauri ta miƙe tayi inda take tana isa ta faɗa jikinta tare da sakin kuka, "shii ya isa" tacecikinshaƙaƙƙen muryarta tare da hitting bayanta a hankali, tashi saura suka yi suka koma kusadaitacike da neman kafaɗan koka damuwan su, tattarasu tayi gaba ɗaya ta rungume tana rarrashinsu
da kalamai masu sanyaya zuciya.... Har general parlor dake side ɗinta da aka ƙawata da kayan more rayuwa su Yaya suka kaita, sunaisa ya zaro waya ya kira Shureim, ko cikakken mintuna biyar be ƙara ba ya iso, gaidasu yayi agirmame ya ja baki ya tsuke tare da sadda kai ƙasa, murmurshi Hassan ya saki tare da faɗin"Muhammad ga Yasmin nan mun ka wo maka" jinjina kai yayi a natse, "amana muka baka kamaryanda muka bata naka amanan, ku riƙe juna tsakani da Allah, ku rufe asirin juna ku adana, kar
muji kar mu gani, kasan zama da mace se da haƙuri, ka ɗaura ɗammaran haƙuri zaka yi rayuwaraure me tarin ma'ana" jinjina kai yayi cike da gamsuwa... Gyara zama Ali yayi tare da faɗin "zo mu zauna zo mu saɓa ne, a duk lokacin da zama ya haɗakada wani to dole se ka kai zuciya nesa dan in ya faranta maka yau gobe ze iya baƙanta maka, wataƙila a sannin shi wataƙila kuma ba'a sanin shi ba, musamman zama na aure, haƙurindamuketa ce muku ku yi shine tsanin da ze kai ku ga rayuwar farin ciki, Manzon tsira(s.a.w) yasanar mana da wacece mace, ya kuma sanar mana da rauninta sannan ya sanar mana jarumtar
ta, ka ɗau maganan fiyayyen halinta ka yi aiki da shi in sha Allahu ba zaka yi dama a rayuwar dazaku fara ba" jinjina kai ya kuma zuciyan shi na rauni....
"Yasmin!" Yaya yace a natse, "na'am" tace da disashshiyar murya laɓɓa na rawa, "gamu a gidanki
mun kawo ki, tun awannin da suka shuɗe ki ka tashi daga ƙasana ki koma ƙasan mijinki, yanzuMuhammad shine gatanki, shine garkuwanki shine kuma jaruminki, ki tabbata duk wani abuwanda ze nema mai farin cikin kin yi shi in dai be saɓawa tafarkin mahalicci ba, "aljannar ki tanaƙarƙashin ƙafarshi ne, ki bi shi fiye da yanda ki ka bi ni, zanyi farin ciki da hakan" jinjina kai tayi
hawaye na tsere a saman fuskanta, juyawa ga Shureim yayi tare da faɗin "zanyi farin ciki
matuƙar ka sanar dani wani kuskure na ta dan in kawo gyara a cik, duk da na san wacece ita"
jinjina kai yayi a natse tare da faɗin "in sha Allah" "to ma sha Allah, Lurwanu rufe mana zamandaaddu'a" Yaya yace cike da kama girman shi, ba musu Lurwanu ya ɗaga hannu, haka ya ɗaulokaci
yana kwarara ma ango da amarya addu'an zaman lafiya, daga ƙarshe ya rufe da kaffaratul
majalis" miƙewa Yaya yayi a natse tare da faɗin "to Allah ya ba mu alheri" yana kai nan yayi ƙofa,
suna idda ficewa ta fashe da ƙaƙƙarfan kuka tare da curewa waje guda, miƙewa Shureimyayi dasauri ya fice dan yi musu rakiya.... Godiya su Annur dake tsaye a farfajiyan gidan suka musu tare da fatan sauka lafiya, suna ficewaShureim ya sauke ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya tare da shafa saman fuskanshi da tafukan hannayenshi, dafa shi Annur yayi tare da faɗin "what?" Ɗago kai yayi ya kalleshi tare da faɗin "nothing"
"please kar ka damu komai ya kammalu yanzu Yasmin na gidanka, taka ce" guntun murmushi yasaki tare da faɗin "jimanta yanda zata rayu da ni nake, zuciyanta na ga ahalinta kasan hakan" yayi maganan kaman ze saki kuka "na sani, se dai kar ka manta tana kuma sanka, wani ɓangarena zuciyarta tare yake da kai, ko wacce mace tana son ahalinta ake rabata da su, haka aureyagada, ka cigaba da ƙoƙarin ɗauke mata wannan kewan, zata manta da wannan tunanin kushinfiɗa rayuwa me tarin ma'anoni" jinjina mai kai yayi cike da gamsuwa tare da faɗin "kumushiga please" "no dama mun tsaya ganin isowanta ne, zamu tafi yanzu, se mun dawo ganinɗaki"
"a'a kar mu yi haka da ku" yace tare da kafe Annur da ido, murmushi ya saki tare da faɗin"bazamu shiga ba, lokacin ka ne yanzu ka je ka rarrashi abinka, na san tana can tana kukanbaroInsuda ta yi" huci ya saki tare da tuna kukan da ta saki da su Yaya suka fice....
"Wallahi abun ba sauƙi, musamman su da suka shaƙu sosai" Laɗifa tace cike da tausayawa, "insha Allah komai ze wuce, malam koma ciki" Annur yace tare da kallon Shureimdake binsudaido, ba musu ya basu hannu suka yi sallama ya juya ya koma ciki jiki a mace, "Allah sarki Insuwallahi ita kawai nake tausayawa" Mardiyya matan Zubair tace murya a raunane, "tana daƙarfafa kai, zata jure" Khalid yace tare da riƙo hannun matan shi yayi mota, haka suka shishshigesuka nufi gate, suna ficewa me gadi ya kulle ƙofan....
Suna zaune a wajen su Yaya suka shigo jikkuna a sanyaye, "har kun dawo Yaya?" Salwa taceidona tara ruwan hawaye, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "kun kai wa mazajen ku abinci
kuwa?" Jinjina kai tayi tare da faɗin "eh" "ku shirya gobe zaku wuce tare da su" "gobe Yaya!" Tacecike da rashin jin daɗi, "eh gunda ku koma kar yara su yi ta asaran karatu" jinjina kai tayi batare
da tace komai ba, "Sarah ke ma ki shirya gobe da safe zamu wuce" Hassan yace da kulawa, jinjinakai tayi jiki a mace....
Juyawa yayi a natse ya shige side ɗin shi, "bawan Allah ta so mu wuce" Lurwanu yace taredakallon Balarabe saboda gida ɗaya suke, "to Nafisat ce musu su fito" Balarabe yace tare damiƙewa, miƙewa tayi a natse ta wuce kiran matayensu dake ɗakin Babiya, juyawa Ali yayi yarufamata baya jiki a mace, ƙarisowa ciki Hassan yayi ya zauna kusa da Farisat tare da riƙo hannunta, fashewa da kuka tayi tare da faɗin "shikenan kowa ze tafi kenan?" Murmushi ya saki taredafaɗin "makarantar yara yasa hakan, amma suna samun hutu za su tatttaro yaran su zo suzaunadaku har se kun gaji da su sannan za su komo" murmushi ta saki tare da faɗin "ba zamu taɓagajiya da su ba" murmushi ya saki tare da faɗin "to shikenan" yana kai nan ya miƙe tare dakiranSarah da ke ta share hawaye suka nufi side ɗin baƙi inda aka sauke mazajen su Salwa....
"Allah sarki Umman Mairah an tafi kuma" Farisat tace tare da goge hawaye, "to ya za'ayi macenkenan" Suwaiba tace tare da kallon ta, "wallahi ji nake kaman mafarki" tace cike da gaskiyanta, "au ke ma da ki ka tafi mafarkin kenan?" Lailah tace tare da banka mata harara, murmushi tasaki tare da faɗin "wallahi Anty Lailah haka nake gani" miƙewa Insu tayi a natse ta tattarasuSahabee tayi ɗakinsu da su, bin ta suka yi da ido cike da tausayawa, zaro waya Farisat tayi taredadanna number Hasinat tana ɗagawa tace "ki kawo mun Mairah anan zan kwana" amsawa tayi da"to", tana sauke wayan Khadijatu tace "a gidanki zaki kwana, ta kawo miki ita ki tattara ki tafi
gidanki" kwaɓe fuska tayi cike da rashin jin dadin, "ki fashe amma ba zaki ƙara kwana a gidannan ba, banda rashin hankali ma ga baki ga hanci ki dinga kwaso jiki wai kwana, to kin gamadaga yau" tana idda zayyana bayanin ta miƙe ta fice dan zuwa wajen mijinta....
"Se da ta tabbatar sun kwakwkwanta sannan ta kashe musu hasken ɗakin ta fito ta rufe musuƙofa, ta nufi ɗakin Nafisat, tana shiga ta taddata kwance tana ta sakin sheshsheka tare daajiyanzuciya, murmushi ta saki tare da ƙarisawa a natse, zama a saman bedside drower tayi taredafaɗin "to menene na kukan Hajiya Nafisat?" Ɗago kai tayi da sauri ganin itance ya sata fashewa
da kuka me rauni tare da faɗin "shikenan haka zaku yi ta tafiya ku bar mu" murmushi ta sakinmata tare da ɗagota a natse cike da muryan rarrashi tace "wayace miki sun barmu ne? Sunanantare da mu bakya ganin Mommy kusan kullum tana nan gidan?" Jinjina kai tayi tare da gogehawaye, "to ita ma muna tare da ita" "ke ma muna tare dake?" Tace tare da kafeta da idondahawaye ya ƙi daina tsiyaya a cikin shi, guntun murmushi ta saki tare da faɗin "ba inda zani nabarku, ina tare da ku" jinjina kai tayi tare da sakin murmushi me haɗe da zuwan hawaye, murmushi ta sakin mata tare da rungumo kanta ta saka a ƙirjinta tare da ɗaura haɓarta asamankan tace "kune ƙarfin gwiwata, ku ne bangon jinginata, kune kafaɗan koke damuwoyina inazani
in barku, ba na da wajen zuwa" ta idda maganan hawaye na gangarowa a kuncinta, "munamatuƙar sonki" Nafisat tace murya na rawa, jinjina kai tayi tare da goge hawayen ta ɗagotatareda saka hannayenta ta riƙo fuskanta cike da kulawa tace "Nafisat in tana kuka ba ta kyau, murmushi yafi kyawu a saman fuskanta, daina kuka muna tare ba inda zamu mu barku" tayi
maganan fuska ɗauke da murmushi, murmushi ta saki me faɗi tare da faɗin "ke ce uwar muinbaki a kusa damu ba musan yaya zamu yi ba, ke ce wacce ta maye mana gurbin mahaifiyandamuka rasa a lokacin da muke matuƙar buƙatan ta a kusa damu, ya zamu yi in baki?" Ta iddamagana kuka na kuɓuce mata, lumshe ido tayi tare da miƙewa a natse ta fice.... Ba ta jima ba ta dawo riƙe da paracetamol da ruwa, ɓalla mata tayi ta ba ta, amsa tayi ta sakaabaki tsiyaya mata ruwa tayi ta miƙa mata, sha tayi ta miƙa mata kofin, "ki yi alwala ki yi sallahkoraka'a biyu ne kafin ki kwanta, ki tabbata kin kashe wuta" tayi maganan idonta ƙyamakanta, jinjina mata kai tayi ta miƙe a natse ta wuce toilet, tana shigewa ta juya ta fice jiki a mugunsanyaye, kai tsaye parlorn ta wuce, tana shiga ta tadda Salman da Sadam da Farisat da sauranmahalarta biki na zazzaune, miƙewa Sadam yayi ya riƙota tare da kafeta da ido, cike da zargi
yace "kuka!" Murmushi ta saki tare da girgiza mai kai, rungumeta yayi tare da faɗin "bandakuka, ba mu yi alƙawarin haka ba" ya idda maganan tare da hitting bayanta a hankali, ɗaga kai samatayi tare da maida hawayen da suka cika mata ido....
Zare ta yayi tare da faɗin "amarya fa ta bar wayanta a wajena" yayi maganan tare da fiddowayanYasmin ƙirar iPhone 16 pro, murmushi ta saki tare da ɗaga hannu ta amsa a hankali tare dafaɗin"ka manta ne, gobe in su Anty Lailah za su kafin su wuce se su kai mata" "ina za su!" Salmandayamiƙe ya ɗau Mairah da tayi barci ya saɓa a kafaɗa yace da mamaki, "gobe za su tafi" tace anatsetare da wuce wa kitchen, "da wuri haka?" Yace tare da kallon Sadam, "yanzu na ji maganan" yace
tare da wuce wa ɗakin shi, "muje my Jannah Yaya ne yace su tafi an katsewa yara school, kagakuma jibi Monday" jinjina kai tayi cike da gamsuwa ya riƙo hannunta suka fice......
Tana shiga ta kunna gas ta ɗaura tukunya, tana dakko kayan haɗa shayi ta ajiye ta saki wani
marayan kuka, kuka tayi sosai tafasan da ruwan yayi ne ya ankarar da ita halin da take ciki, gogehawaye ta yi ta fara zuba kayan haɗin, jiran mintoci tayi tana tabbatar da nunan shi ta sakeamadadincin buta ta daura a saman madaidaicin trey ta saka cup's biyu ta ɗauka ta fito, ganinbakowa a parkorn ya sata wuce wa side ɗin Yaya a natse.... Da sallama a saman laɓɓa ta shiga, ganin baya parlorn yasa ta nufar bedroomɗin shi, knockingtayi a natse, "come in" muryan shi ya iso kunninta a disashe, murɗawa tayi ta tura a hankali, tanashiga ta tadda shi zaune saman sofa hoton su gaba daya riƙe a hannun shi, murmushi ta saki tareda ƙarisawa ciki, ajiye treyn tayi a saman table ɗin dake gaban shi ta zauna kusa dashi a natse.... Murmushi ta sakin mai tare da faɗin "ba mutuwa tayi ba, tana raye har yanzu" murmushi yasaki
tare da lumshe ido hawayen da suka cika idon suka sakko, "o'o Yaya kuka kuma?" Tace taredanarke fuska, murmushi ya kuma saki tare da rungumota ya ƙanƙame sosai, kuka ta saki meƙarfi, ba abinda ya iya ce mata dan shi ma kukan yake, se da suka ɗau mintoci a haka kafin ya saketatare da fara goge mata hawaye, "Farisat ta tafi jiya, Yasmin ta tafi yau, gobe ke c, jibi kumaNafisat, shikenan gimbiyoyina sun girma, sun zama tsintsaye" ya idda maganan tare da sakinmurmushi, murmushi ta saki tare da faɗin "sun girma amma suna nan a matsayin gimbiyoyinYaya, ba wanda ya isa ƙwace wannan matsayin naka ne kai ɗaya" murmushi ya saki tare dajinjina kai, miƙewa tayi a natse ta fara tsiyaya mai tean, tana bashi ya amsa tare da faɗin"thankyou dear" murmushi ta saki tare da komawa ta zauna tare da faɗin "kun baro ta lafiya?"...
Murmushi ya saki tare da faɗin "lafiya lau, ban ɗauka zata iya kai tsayin lokaci haka ba ta kirani
ba, murmurshi Insu ta saki tare da ɗago mai wayanta tare da faɗin "yana hannun Yaya Sadamyanzu ya bani" murmushi ya saki tare da faɗin "ko da nace" ƙaramar dariya ta saki tare dafaɗin"ai da yanzu duk mun banu da kira" ƙaran ringing ɗin wayanta ya sata ɗagowa ta kalla da
mamaki ta kalli Yaya tare da nuna mai me kiran fuska cike da murmushi, jinjina kai yayi nashi
fuska cike da murmushi, ɗagawa tayi ta kara a kunni a natse.....
Ta ɓangaren Shureim kuwa ciki ya wuce kai tsaye yana shiga ya hangeta zaune jiki cukuikuyewaje guda a inda ya barta tana ta sakin jerarrun ajiyan zuciya, kulle ƙofan yayi a natse ya ƙarisociki a hankali, zaunawa a gefenta yayi tare da kiran sunanta a hankali, ɗago kai tayi da sauri, ganin shine yasata kwaɓe fuska tare da shirin sakin wani kukan, "dan Allah ki yi haƙuri ki dainakukan nan haka kar ya cutar dake" yace kaman ze saki kuka....
"Ni gida na ke son komawa" tace tare da sakin hawaye, fiddo ido waje yayi tare da faɗin"kinfasazama da ni precious! Kin manta ke ki ka ce kin shirya rayuwa dani?" Ya idda maganan kamanzesaki kuka, sadda kai tayi tare da fara cuɗa yatsun hannunta waje guda, matsawa kusa da itayayi
a hankali tare da faɗin "please ki daina furta wannan kalaman, kin san ze cutar dani" "to Insunasan kuka take, za tayi kewana" tace tare da fashewa da kuka, sauke numfashi me ƙarfi yayi tareda faɗin "na sani amma ba zata ji daɗin wannan kalman da ki ke furtawa ba, kin san tafi kowaƙaunar san ganin mu waje guda ko? yana daga cikin burikanta" ya idda magana idon shi acikinnata, jinjina kai tayi cike da fahimta, "yawwa daina please" yace tare da rungumarta a hankali yalumshe ido, zare ido tayi a tsorace tare da dan matse jikinta waje ɗaya.... Murmushi ya saki tare da ɗago kai ya sumbaci goshinta tare da kallon fuskanta da ta saddaƙasa, "ina matuƙar ƙaunarki, ban san da wani suna zan kira wannan rana ba, duk wani suna da nabashi se inji martabanshi ya wuce hakan, yau gani ga ke ƙarƙashin inuwa guda, igiya ɗaya yaɗaure
mu, wai ke ɗin dai kin zama mallakina precious, wai ke tawa ce yanzu" ya idda maganantaredaƙara rungumarta cike da ɗin bin farin ciki.... Ɗan janye jiki tayi a hankali, saurin sakinta yayi tare da faɗin "sorry, tashi mu yi sallah mugodema Ubangiji da ya nuna mana wannan rana me matuƙar daraja, ya cika mana muradin mudamuka daɗe muna mafarkin ganin cikan shi" yayi maganan cike da zumuɗi, "ina son waya" taceahankali, "waya! Me zaki yi dashi!" Yace da mamaki tare da komawa ya zauna daga yunƙurintashin da yake, "zanyi magana da Insu ne" tace a hankali, duba agogon dake ɗaure a tsintsiyar
hannun shi yayi, ganin 12:30am ya sa shi faɗin "dare yayi sosai fa" "ina son magana da ita ne" tace a hankali, "okay tom" yace tare da zaro wayan shi ya miƙa mata tare da faɗin "ina na ki?"
"Yana wajen Yaya Sadam" tace a hankali, jinjina kai yayi ya miƙe a natse ya wuce part ɗinshi tareda faɗin "bari in yo alwala kafin ki gama" jinjina kai tayi a hankali, ta buɗe wayan, kyakykyawangani tayi da hotonta da tayi ranar Arebian night, murmushi ta saki tare da wuce wa contact kai
tsaye, searching ɗin sunan Insu tayi, ganin be ba ta sunan da ta saka ba, ya sata ficewa ta wuceɓangaren kira, number ta fara jerawa nan take ya bayyana mata sunan da yayi saving da shi
(lovely sister) murmushi ta saki tare da danna number ta kara a kunni....
Sallama Insu ta yi a hankali amsawa Yasmin tayi murya a disashe, da mamaki tace "baby!"
"Na'am" tace a sanyaye, "lafiya!" Tace tare da kallon Yaya da ya kafeta da ido, "lafiya lau, kinatakuka ko?" Tace murya a raunane, murmushi ta saki me yalwa wanda sautin shi ya kai matahar
can tare da faɗin "kamar wata ƙaramar yarinya, ba kukan da nayi" tayi maganan tare da maidahawayen da suke son zubowa, "ban yarda ba, yanzu haka shi ma ki ke yi" dariya ta saki meyalwatare da faɗin "shi dai ki ke, amma ni banyi kuka ba" "su Yaya sun dawo lafiya?" Tace a hankali, "ehgani ga shi" tace tare da sakin murmushi ta zaro wayan ta saka a speaker, "Yaya!" Tace a raunane, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "Yasmin" fashewa da kuka tayi cike da rashin madafa....
"Oh Allah dama kiran mu ki ka yi ka yi ta mana kuka?" Yace tare da kama haba, girgiza kai tayi
kaman yana ganinta tare da saka hannu a saman bakinta, "to ya isa haka, kin fa girma yanzu"
yace dw kulawa, girgiza kai tayi tare da faɗin "ah ah Yaya har yanzu ni babynka ce" dariyayasaki
me yalwa tare da faɗin "har yanzu ke babyn Yaya ne" murmushi ta saki tare da jinjina kai, murmushi Insu ta saki tare da faɗin "ke baby ba ma son taɓara fa" tayi maganan tare da sakindariya, "ai Yaya na nayi ma wa" tace tare da balla mata harara kaman ta na ganinta, "to kar dai
idon ya faɗi" tace tare da sakin murmushi cikin hasaso yanayin da take ciki ....
"Bari mu yi magana" tace a hankali, "okay" tace tare da cire speakern ta tashi a natse ta maYayase da safe ta fice a hankali, da murmushi ya bita cike da ɗin bin ƙauna, tana fita ta tsaya aparlornside ɗin tare da faɗin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 62 Chapter of 109