Share this page
da faɗin "please ce mata ta zo mutane na can na zaman jiranta" "wayyo Allah Yaya Salman ban san komawa ciki" tace kamar za ta saki kuka, "please tun ɗazu nakekirannumberta ba ta ɗaga ba" "wannan ta san ma inda ta je fa wayan ne bari in kira ta" tace taredajuyawa ta koma ciki.... Tana shiga ta ja ta tsaya a ƙofar parlorn tare da fadin "mijinki na kiran ki" miƙewa tayi da sauri tafice tare da faɗin "sun dawo kenan?" Murmushi ta saki tare da kallon Yasmin da jikinta yayi mugun sanyi tare da faɗin "ji wani gurguwar tambaya" "Allah ya shiryeki, ina ki ka maƙalayarinyar?" Laɗifa tace tare da sakin murmushi, "tana wajen fathern ta" tace tare da sakinmurmushi ta juya ta fice rw sauri.... Da sallama ta shiga parlorn Ummi, murmushi ta saki ganin yanda jama'a suka cika fanƙal taredaɗaga musu gaisuwa, amsawa suka dinga cike da yabawa, "wayyo Ummi na ya ki ka wuni dazirga-zirga?" Tace cike da kulawa tare da duƙawa gefenta, murmushi Ummi ta saki tare da faɗin"Alhamdulillah ya na ku zirga-zirgan?" "Ba daɗi Ummi kaina har ya fara ciwo" "sorry ki samuki kwanta ki huta ko na awa ɗaya ne ze daina" tace da kulawa, "in sha Allah Ummi na, bari ingaisada abokan Uncle" tace tare da miƙewa.... "Sannu amaratu" Rahma da ta fito tace tare da sakin dariya, "Antn Amarya ba" tace tare datayata dariyan, "sannu da ƙoƙari Mommyn Mubin" tace tare da rungumeta, "sannun mu dai kekedasannu" tace cike da yaba mata, zare jikinta tayi tare da faɗin "ina baby Mubin?" "Yana barci" "yahuta, ina me cikin nan?" "Gani Safinat tace tare da banka mata harara.... "Sorry Mrs Adam ya jikin? Baki wahala sosai ba ko?" "No ba wani wahala, Allah dai ya nunamananaki kamar yanda mu ka ga na Yasmin" "amen to ki na haihuwa ki danna allura dan rakashewazamu yi, kinga in da ciki kamar haka ba dama" murmushi Safinat ta saki tare da faɗin "kinkawo shawara baby Insu" dariya ta saki tare da faɗin "ai gaskiyane kawai a hanaki raƙashewa yandayakamata, Mommyn Mubin an raba wannan abun ko?" Murmushi ta saki tare da faɗin "kowayasamu" "sauran da ya rage da yawa ne?" "Eh da yawa ba lefi" "okay an rabawa na cikin gidane?" "Ba duka ba" "okay, a cire ma abokan Uncle da Sa'eed da Umar da ƙawayen Nafisat, saura kumakin san yanda zaki yi da shi" tana kai nan ta wuce.. Har ta fara taka stairs ta juyo tare da faɗin "ina Amaryar me jiran gado ne?" Dariya Safinat tasaki tare da faɗin "Allah ya shiryeki tana can saman" "ai wallahi na ƙosa mu tattara ta mu miƙataƁadamayya kowa ya huta" "kin kyauta Insu wato ke ma kina cikin masu farin cikin nisandazatayi daga gefena ko?" Ummi tace tare da kallonta.... Zare ido tayi tare da faɗin "na isa Ummi ni murnan da nake na samun matsayi da tayi ne, ganaɗayanmu fa ba wacce tabar Bertuwa se ita zata tsallaka har capital ai dole in yi murna" taiddamaganan tare da sakin dariya ta haye da sauri, murmushi Ummi ta saki tare da bin ta da ido,.. Haka suka ƙarisa yinin bikin cikin hidima da jama'a, suna idar da magrib suka fara shirintafiyadinner, ana idar da isha'i motocin tafiya suka iso anguwan, shigowa Sadamyayi da sauri taredafaɗin "ina Insu! Insu! Insu!" "Oh Allah yau ko za'a bar Insu ta huta kuwa?" Suwaiba tace cikedadamuwa, "ai tunda tace sunanta amara ita da hutu se Amarya ta isa gidanta lafiya" Sadamyacetare da sakin murmushi, "tana can tana shiryawa" tace tare da ƙoƙarin wucewa, "dan Allahcemusu su fito se fa da aka ce ban da african time" yace cike da damuwa, "oh Allah mun gamashiryawa fa" Insu dake riƙe da hannun Yasmin dake cikin shiga na musamman tace tare dasakinmurmushi, "ma sha Allah, Allah ya kauda mugun ido akan ku" Suwaiba tace cike da farincikinburgeta da suka yi, "amen" Insu tace tare da gyara zama ƙaramin jakan dake kafaɗanta, "mujeina Nachma?" Tace tare da baza ido, "gata nan" Ziyada dake cikin ankon dinner tace tare danunaNachma dake gefenta, "to ku muje, yakamata wasu motocin su fara gaba, ina Nafisat ne?" Taidda maganan tare da baza ido, "sun fita" Suwaiba tace tare da kallon ta.... Suna fita ta kai Yasmin har jikin motan da za su tafi a ciki ta saki hannunta ta wuce wajensauranmotocin dan yi ma masu zuwa magana akan su shishshiga, "bismillah" Shureimdake sanyedakakin shi da yayi masifar amsan shi yace tare da nuna mata ƙofan motan, ƙasa da kai tayi tamatsa tare da faɗin "ina Insun ta zo mu tafi tare" buɗe ido yayi da mamaki tare da faɗin"tsoronaki ke ji ne!" Girgiza kai tayi tare da faɗin "Insu zan jira" ƙarisowa wajen Annur yayi tare da faɗin"ku shiga mana lokaci na wuce wa"... "Ƙanwarka ce fa taƙi da alama tsoro na fara bata" yace tare da sakin murmushi, ganin irinkallonda yake mai ya sa shi faɗin "se Insu ta zo" dariya Annur ya saki tare da faɗin "ikon Allah yaukuma, to wataƙila ba ta taɓa ganinka da kaki ba ne ko ƙanwata?" "Ta taɓa mana da ita aka zo bikinƙaringirma" yace a hankali, matsawa inda take yayi fuska ɗauke da murmushi tare da faɗin "ƙanwatashige mu tafi, Insu zata biyo mu" girgiza kai tayi tare da faɗin "anan zamu tafi tare" buɗe baki yayi da zumman magana Shureim ya tari numfashin shi da faɗin "kirawo ta" fuska ɗaukedamurmushi, wuce wa yayi fuska ƙumshe da dariya, bin ta kawai yayi da ido cike da mamaki.... "Ku shishshiga dan Allah time na tafiya" Insu tace tare da nunnuna musu mazaunin da ba kowa, "ƙawayenki za su ne?" Tace tare da kallon Nafisat dake cikin nata ankon dinnern, "eh biyuzasu" "to ga mota su zo su shiga" tace tare da kallon ta, yafuto su tayi suka ƙariso suka shiga, "muhaɗua can" tace tare da wucewa, "sistern ki na da kirki sosai" ɗaya a ciki tace tare da kallon Nafisat, murmushi ta saki tare da faɗin "matsayinta ya wuce na sister a waje na, uwace" jinjina matakai suka yi cike da gamsuwa.... "Ku shiga muje" tace tare da kallon Nachma da Ziyada, shigewa suka yi a natse, buɗe ƙofangana tayi da zumman shiga, tsayawa tayi sakace da baki tana bin Labib dake zaune da ido, murmushi ya saki tare da faɗin "kaina bi sa wuya" "wai dama tare ku ka zo!" Tace tare da kallon Nachmadaita ka take bin shi da kallon mamaki, girgiza kai tayi tare da faɗin "yanzu na ganshi" "be daɗedaisowa ba, na ce ya bari in mun zo tafiya dinner kwa gaisa" Hisham yace tare da kallon ta, "kakyauta" tace tare da banka mai harara.... Murmushi ya saki tare da faɗin "yanzu kuma me nayi?" Ƙarisowan Annur wajen ya dakatar daitadaga ba shi amsan da take ƙoƙarin yi, "lafiya!" Tace da mamaki, "amarya taki hawa mota" yacetare da sakin murmushi, "what!" Tace idonta akan shi, "yeah tace se kin je" dariya ta saki taredafaɗin "oh Allah Yasmin kuma yarinya ta zama" tana kai nan ta rufe ƙofan tare da faɗin "inazuwaboyfriend" ta wuce da sauri, tana isa Yasmin dake tsaye kai a ƙasa ta ɗago tare da riƙo hannuntaido sunyi ƙwal-ƙwal alamun gab take da fashewa, murmushi ta saki tare da faɗin "haba jarumarAnty, shiga mana jama'a na jiran shigarki ne fa" "mu tafi anan tare" tace tare da sakin hawaye, "a'a tare da Yaya Annur da sister Laɗifa zaku tafi, ni zan bi boyfriend da su Ziyada, maza shigajarumar Yaya" ta idda maganan tare da kama hannunta ta nufi ƙofan motan da ita, shiga tayi aɗarare, murmushi Shureim ya saki tare da bin bayanta, "ku hanzarta gamu nan bayan ku, sisterLaɗifa jeki hau" tace tare da kallon Laɗifa, "wallahi abun ba sauƙi Insu, ni kaina a ranar nawaseda natsorata" tace cike da tausayawa, "haba dan Allah ku zama jarumai, kuna auren sojoji kunawani abu kaman lusarai" tace tare da sakin murmushi, "Allah ya nuna mun ranar naki Insu" tacetare da kama haɓa.... "Irin su ne zaki ji su gum, ba baki se ido" Farisat da ta gama kashe kala tace tare da kallonLaɗifa, da mamaki Insu ta kalleta saboda ganin Mairah da aka gama ɗaukan mata wankan ƙarshesaɓeakafaɗanta, tana ƙarisawa kusa da ita tace "amma ba da ita zaki wajen nan ba ko!" "Da ita nemana, wa zan barmawa ita?" Tace cike da gaskiyanta... "Haba Farisat wajen nan ne zaki da ita! Dare ne fa, sannan wajennan za'ayi kiɗe-kiɗe, matsayinki na uwa me son inganta tarbiyyan yarinyarki me ze kai ki kaita wannan wajen?" Ta idda maganan cike da mamakin ƙarfin halin Farisat, "to wa zan bar mawa, ku za ku, su Hasinat za su" "inaceUmmi na gida ba zata ba!" tace da mamaki "eh tana gida" "to ki barta tare da ita" tace taredawuce wa, bin f8a tayi da ido cike da juya zantukanta a zuci, "ki kaita Insu ta fi mu gaskiya" Salmanda ya iso wajen yace tare da kallonta, "se dai ka kaita da kan ka, amma in ni na kainta ba zatayarda ta zauna ba" tace tare da kallon shi, "kawo ta" yace tare da miƙa hannu, ba shi ita tayi tareda faɗin "ta ma yi barci" jinjina kai yayi ya saɓata ya wuce da ita, kallon Insu dake tsaye kusadaita Lailah tayi tare da bugun kafaɗunta ta sakin mata murmushi tare da mata alamun kinkyauta, murmushi ta sakin mata ta wuce motan Hisham da suke zaman jiranta.... Zaro hanky yayi a hankali yayi ya nufi fuskanta da shi a natse, saurin ja baya tayi tare da kallonshi, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "bana so" sadda kai tayi cike da fargaba, ita fa tundaaka ce an ɗaura auren ƙirjinta ke bugu, matsawa kusa da ita sosai yayi tare da ƙasa da muryacike da rarrashi yace "please bana son wannan tsoron da nake gani a idanunki" jinjina kai tayi anatse ba tare da ta ɗago ba, "ɗago" yace a hankali, ɗagowa tayi a natse saka hanky yayi yagogemata hawaye da suka ɓata mata fuska tare ra jawota a hankali cikin ƙasa da murya yace "faɗamin me ya tsorataki ko dai shiga na ne?" Girgiza kai tayi a hankali, kamo hannunta yayi tareda faɗin "to faɗamin" "su Yaya Annur suna kallon ka" tace kamar zata saki kuka, ƙaramar dariyaya saki tare da ɗago kai ya kalle su.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Fourty one Motansu na fakawa ta zare belt ɗin jikinta ta buɗe murfin ƙofar ɓangarenta ta fita tare dafaɗin"ku hanzarto dan Allah, Ziyada ki shigar da Nachma da Labib ciki" ta idda maganan tare dawucewa motan su Shureim, tana isa ta tadda ya sakko Yasmin na ƙoƙarin sakkowa, wuce wa tayi dasauri tare da zaro wayanta dake neman a gaji ta kara a kunni.... Miƙa mata hannu yayi cike da kulawa tare da kafeta da ido fuskanshi na fidda sihirtaccenmurmushi, kauda kai tayi da sauri ta dafa gefen ƙofan motan ta sauka a natse, murmushi yasaki me faɗi tare da faɗin "Annur ƙanwarka fa kunyarka take ji" murmushi Annur da isowan shi wajenkenan ya saki tare da faɗin "ƙanwata daina jin kunyata dan Allah, rungumi mijinki farinciki zanyi" yayi maganan tare da kallonta, murmushi ta saki tare da sadda kai, matsawa kusa daitasosai yayi tare da faɗin "kin dai ji abinda yace ko?" Jinjina kai tayi ba tare da ta ɗago ba, "inaInsun ta shiga kuma?" Annur yace tare da baza ido, "yanzu ta wuce kuwa" Laɗifa dake tsayeakusa da shi tace tare da baza nata idon .. "Tattaro mutanen Aminan juna su matso kusa" yace tare da kallon ta da kulawa, jinjina mai kai tayi ta wuce ta inda suke tsai-tsaye cikin ankon su na musamman.... "Eh event's centern da aka yi Arabian night ne dan Allah ki hanzarta Anty Jamila, duk aniso" shirun daƙiƙu tayi tare da faɗin "to shikenan, bari in ɗau kira" tana kai nan ta sauke wayantakatse kiran ta ɗau wanda ke shigowa, "kuna ta ina?" Tace tare da juyawa ta fara wawwaigawa, "okay kune a napep ɗin da ya tsaya yanzu?" tayi maganan idonta akan napep ɗin, shirindaƙiƙutayi tare da faɗin "okay gani nan" tana kai nan ta sauke wayan ta nufi wajen... Tana ƙarisawa Iƙilima da Sadiya suka fito, murmushi ta sakin musu tare da rungume Iƙilima, "sannun ku da zuwa Anty Iƙilima" tace cike da farin ciki tare da zare jikinta ta rungume Sadiya, murmushi Iƙilima ta saki tare da faɗin "Allah yasa ba mu makaraba" janye jiki a jikin Sadiyatayi tare da faɗin "isowan mu kenan, ban zata zaku zo ba ma" murmushi Sadiya ta saki tare dafaɗin"mun so zuwa yinin biki ɗazu jikin Baba ne ya motsa shiyasa ba mu zo ba" "oh Allah ya jikinnashi!" Tace da kulawa.... "Alhamdulillah yanzu da sauƙi dan da kan shi ya matsa ma se mun zo, da mun ce ba zamuzoba" "ayye Allah ya yaye mai wannan ciwo, ku ƙarisa ga Farisat can" tace tare da nuna musu indatakea, jinjina kai suka yi suka wuce inda take, juyawa tayi da niyyan wuce wa muryan Sudais yatakamata burki... Juyawa tayi mamaki ɗauke a saman fuska tare da faɗin "Yaya Sudais kaima ka zo!" Ta jefamai tambayan cike da mamakin ganin shi a wajen, murmushi ya saki tare da faɗin "eh ko be kamatain zo ba ne Insu?" Yayi maganan a natse cike da kulawa, "no yakamata, ai kai yafi kamata madaka zo saboda kasantuwarka na Yaya ga amarya" tace cike da murmushi, murmushi ya saki tareda faɗin "nagode Insu" "ba komai kaje ta can yakamata ku shiga kafin amarya da ango sushiga" jinjina mata kai yayi cike da gamsuwa ya juya ya wuce cike da farin cikin yanda ta mai maganadakulawa, da ido ta bi shi tana mamakin irin kallon da yake bin ta da shi... "Kar dai ni ki ke tsayuwan jira?" Muryan Jamila ya doki kunnuwanta, ɗago ido tayi ta kalletatareda sakin murmushi me faɗi, "in na jiraki ai ban yi aibu ba Anty Jamila, barka da zuwa" tayi maganan tare da rungumarta, "da oga fa muke tafe" tace tare da zare jikinta, "oh uncle Ahmadina yake?" Tace tare da baza ido, "gayi can yana dai-daita parking" tace fuska cike da murmushi, "okay to bari ya ƙariso mu je ko" tace tare da riƙo hannunta.... "Mommyn Mairah" Iƙilima da suka isa inda Farisat ke tsaye tana magana da wasu friend's ɗintatace fuska yalwace da murmushi, juyowa tayi fuska faɗaɗe da murmushi tare da faɗin "IƙilimaSadiya!" Murmushi suka saki cike da farin cikin tarban da ta musu, tare da faɗin "ina Mairah?" "Tana gida wajen Ummi, barkan ku da zuwa, lokaci yaja ba zamu tsaya dogon gaisuwa ba, kuzoku shige, in an tashi ma gaggaisa" tace da kulawa murya na nuna zallan farin cikin zuwandasuka yi, jinjina kai suka yi cike da murmushi suka nufi inda ta nuna musu.... "Uncle Ahmad kama hannun matarka ku shige duk suna ciki, mu na bayanku mu ma yanzu" Insutace fuska yalwace da murmushi tare da kallon Ahmad mijin Jamila, murmushi ya sakinmatatare da kama hannun Jamila da ta haɗe cikin a kone dinner suka shige, juyawa tayi a natsetareda faɗin "ina Nafisat?" Ta jefa tambayan tare da kallon Ziyada da ta ƙariso wajen a lokacin, "tashiga kai jama'a ciki, ga ma ta can ta fito" tace tare da nuna mata Nafisat da ta nufo su, "okayshikenan, kin shigar da su ko?" Tace tare da kafeta da ido, jinjina kai tayi tare da faɗin "ehwhitedancer's ma sun iso bayan wuce wan ki duk na shigar da su" "ma sha allah ina boyfriend?" "Yanawajen Ango yanzu su Mihna suka iso da zugan ƴan uwa da abokan arziƙi" "okay koma ciki danAllah ki tsaya da su" tace tare da jan hannun Nafisat da ta ƙariso wajen ta wuce inda su Shureimke tsayuwan jiran zuwanta..... "Wow! Sister Insu kamar ke ce amaryan" Minha tace tare da sakin murmushi, murmushi tasakinmata tare da faɗin "to waya sani ma ko ni ce, har yanzu ba'a gama tantance wacece ba" tacecikeda yanayinta, dariya suka saki tare da kallon ta, "ke fa muke jira baiwar Allah lokaci na tawucewa" Zubair dake sanye cikin kakikshi yace tare da kallon ta, "wayyo Allah bro Zubair tsorokakeban a wannan kakin baka ga tun ɗazu na kasa haɗa ido da kai ba" tace kaman za ta saki kuka, "murmushi ya saki tare da girgiza kai dan ya san halinta ne ya motsa akan shi, "okay pleaseamotsa, waƴanda ba sa cikin tawagan shigan amarya da ango su shige ciki" tayi magana taredajuyawa ga motan da ya faka da ɗan a gafe sauti na tashi.... Buɗe motan aka yi cike da wani salo, sako ƙafa na ciki tayi ta fito tare da wanke fuskokinsudamurmushi, "Sa'adatu!" Farisat tace da mamaki, "Anty Sa'adatu Nafisat tace tare da zare ido, Sa'adatu ne cikin wani arnen lace black and white wanda yayi fasifar amshenta, fuskannanyaci make up yanda ya kamata ba abinda ta manta ba ta ƙawata adonta da shi ba tunda ga kanɗankunni awarwaro, sarƙa, idon nan yaci gashin ido, kai ma an ƙara mai ya bazu a baya, veil ratayeakafaɗa jakan dake ɗaukan ido akan shi, takalmin nan kuwa ɗogogo a sama saboda tsabantsini, tayi haske na ban mamaki ta yi ƙiba banda ɗaukan ido ba abinda take.... Rufe motan tayi ta taka a natse ta isa inda suke tsai-tsaye, murmushi ta ƙara ƙawata fuskantadashi ta ƙarisawa kusa da Yasmin ta ɗan rungumota tare da faɗin "Allah yasa kin yi maraba dazuwa na" ta idda maganan tare da zare jiki fuska yalwace da murmushi me tarin ma'anoni, ɗaurefuska Shureim da su Annur suka yi ta mau, dan kallo ɗaya suka mata suka gane wacece.... Guntun murmurshi Yasmin ta saki tare da bin ta da ido, "sannun ku fa" tace ma saura taredaɗaga yatsu biyu, "Allah me iko dama kina garin nan!" Farisat tace da mamaki, murmushi tasakinmata tare da faɗin "bana nan, zuwa nake in abu me mahimmanci ya taso, kaman dai wannan, kinsan Yasmin ta musammance a wajena, ko ba gayyata zan zo" guntun murmushi ta saki taredakauda kai, "Mihna tattarasu ku shiga" Insu da tunda ta mata kallo guda ta kauda kai tace taredakallon Mihna, "to" tace tare da tattara sauran dan kai su ciki.... "Nafisat kin zama ƴan mata ko?" Sa'adatu tace tare da kallon Nafisat, murmushi ta saki batareda tace komai ba, "Nafisat ku je ki kaita ciki" Farisat tace tare da kallonta, "to" tace tare danufarta, "ki hanzarta" Insu tace a dake, jinjina kai tayi suka wuce, "dan Allah ya zamu yi dajournalist's ɗin nan ne! Abu goma sa ashirin ga police a gefe, ga sojoji a gafe sannan ga ƴanjarida a gefe guda, kai jama'a" Insu tace kaman zata saki kuka, "ga kuma Lawyer's a gefe ba" Farisat tace tare da banka mata harara, dariya Hisham ya saki tare da faɗin "haƙuri ya mukaiya, abun na su ne ai" "kai jama'a" tace tare da juyawa ga Yasmin... "Ya haka ku tsaya yanda yakamata mana" tace da mamaki tare da zuba musu ido, kauda kai Yasmin tayi kaman zata saki kuka, "lafiya kuwa!" Tace tare da kama haɓa, murmushi Annur yasaki tare da faɗin "kunya wai take ji" "kunya! Taɓ ɗin jam, sannu ustaza Yasmin, kunyar wazaki ji anan, ni ko boyfriend ko su Yaya Annur, ko kuma Mommy ne?" Tace idonta ƙyamakan ta, "wataMommyn! Ai duk ɗaya ne in dai Mommy ne" Hisham yace tare da sakin dariyar hararan daFarisatta maka mai, "malama kama mijinki da kyau mu shige, kina wani tsayawa kunya-kunya gobe farkawa zaki yi da batun auren ƙiyayya aka yi muku a media" tayi maganan tare da riƙo hannuntata saka ana Shureim, dariya suka saki gaba ɗayansu, "wallahi ba wasa ba, yanzu idon kowaakansu yake, ƙofa kaɗan za su bada kaji ana tattaunawa a can" tace tare da banka ma Yasminharara, murmushi ta saki tare da zare hannun a hankali ta maida kan hannun uniformɗinshi ta riƙeanatse, kallo ta yayi tare da sakin mata murmushi, murmushi ta sakin mai tare da sadda kai, "ah! ah harkan na smile ne" Insu tace tare da sakin ƙaramar dariya.... Ta cikin wajen taron ma'aikata ba su yi sakaci da shirya jama'an dake ciki ba cikin ƙwarewansunasanin makaman aiki, haka waje ya ƙawata dan tsarin ya tafi da shirin da aka ma wajen, babuhayaniya ko kaɗan saboda kasantuwar manyan ƙasa da suka halarci wajen se sauti dake tashi ahankali wanda ke isar da saƙon abinda ya tarasu a wajen.... Daddy da Mommy da ƴan uwan su duk sun samu halarta, abokan aiki da na rayuwa duk sunhalarci wajen, ta ɓangaren Yaya ma ba wanda be je ba se Babiya da ƴan uwanta, su Salwadamajazensu ma duk sun halarta, sanar da shigowan Ango da Amarya MC yayi cike da ƙwarewaaaikin shi, zuba ido suka yi gaba ɗayansu zumunɗin kowa na bayyana, Nafisat da su Mihna da Hasinat ne suka fara bayyana, taku suke ɗai-ɗai a natse fuskoki yalwaceda murmushi.... Suna kaucewa, zugan su Farisat ya bayyana, a jere suke ita da Salman dake riƙe da hannuntacikeda so da ƙauna a gefenta Rahma da mijinta ne se Safinat da na ta mijin, suma ba ƙaraminburgewa suka yi ba, bayansu sojoji aka zuba waƴan da suka ƙara ƙawata tsarin, suna kaucewaInsu dake tsakiyan Hisham da Sadam da suka haɗu suka haɗe suka bayyana a bayansu, "wow!" Suka ce cike da farin ciki dan ba ƙaramin burgesu suka yi ba.... Suna kaucewa Amarya da Ango suka bayyana, banda fidda walwali ba abinda suke, tafi sukafaracike da farin cikin ganin yanda suka yi dace da juna, banda murmushi ba abinda suke saki, kai tsaye aka nufi inda aka tanadar musu, se dai ba'a ba su izinin zama ba, su Annur da matayensunesuka bayya abayansu, sanye suke da uniform ɗinsu matayensu kuma sanye cikin ankondinnernda aka fidda musu, "ma sha Allah" Daddy yace fuska yalwace da murmushi, suna kaucewasauranjama'an Aminan juna suka bayyana reras, nan da nan aka ba kowa wajen zama.... "Ma sha Allah, a gaskiya wannan salo ya tafi da ni gaba ɗaya" MC yace tare da sakin murmushi, murmushi suka sassaki tare da baza mai ido, juyawa ga amarya da Ango yayi tare da faɗin"bari mu ga wanda ze fi tsada tsakanin amaryarmu da Angonmu, wannan abu ne na in baka yi bani waje, ga dai amarya da Ango a tsaye, ba kuma za su zauna ba se mun ji wanda yafi tsada acikinsu, a motsa, kar ƙafafu su sassage, ƴan uwa a fiddo da masu gidan rana a siya ƙwalliyar angodaamarya" ya idda maganan tare da sakin murmushi cike da nishaɗi.... zare ido Yasmin tayi tare da kallon Insu da ke zaune kujeran dake gefenta ita da Hisham, murmushi Annur dake zaune shi da Laɗifa dake kujeran dake gefen da Shureimyake ya saki tareda ɗaga hannu, "to jama'a babban abokin Ango ze buɗe mana kasuwan" MC yace tare da sakinmurmushi, da sauri yaron MC ya kai mai microphone ya koma wajen tsayiwan shi ya tsaya.... Gyara murya yayi tare da faɗin "na siya kwalliyar amarya million 2" yana kai nan ya ajiye microphone ya saki murmushi saboda hararan da Shureim ya banka mai" "ma sha Allah, babbanabokin Ango ya siya kwalliyar amarya million biyu ku tafa mai" nan ruwan tafi ya tashi, ɗagahannu Salman yayi da sauri aka kai mai microphone "na siya ƙwalliyar ango million 3" "wowYayaga amarya ya siya ƙwalliyar ango million 3" MC yace tare da jan 3 da tsayi, tafi a ka saki cikedanishaɗi, ɗaga hannu Salwa tayi da sauri aka kai mata, murmushi ta saki tare da fadin "matsayinmu na iyaye ga amarya mun siya ƙwalliyar Ango dubu million biyar" nan kowa ya fara siyabanda murmushi ba abinda suke saki, kallon Hisham Insu tayi tare da mai maganan sakanni ta mai daido ga inda Zubair ke faɗin na su shi da su Khalid, miƙewa Hisham yayi ya amshi microphonehannu riƙe da farar takarda ya nufi gaban wajen tare da faɗin.... "Mahaifiyar Ango ta siya ƙwalliyar Amarya million biyar, Mahaifin Ango ya siya ƙwalliyar Amarya million biyar, ƙannin Ango Mihna da Minha sun siya ƙwalliyar Amarya 1million, ƙanninAngo maza again Hamid da Amin sun siya ƙwalliyar Amarya 2 million, ƙanin ango Hishamni kenan na siya ƙwalliyar 3 million, iyayen amarya sun siya ƙwalliyar ango million 12, sister's ɗinAmarya sun siya ƙwalliyar Ango 5 million, brothers ɗin amarya sun siya a 3 million" yana kai nanya ajiye microphone ɗin ya koma ya zauna" tafi suka ɗauka cike

Chapter 60 of 109