Share this page
idanta akan shi, "uncle Kamil da nasani!" Yace cike da san tabbaci, jinjina mai kai tayi duk da ba ta san wa yake nufi ba, da sauri yaisa gare shi ya rungume shi tare da faɗin "sannu da zuwa uncle Kamil" "kai zamu wa sannuSamir" yace cike da gazgata karamci da sanin yakamatan shi da Insu ke faɗa musu, "yakamatamu wuce gida, kar mu jawo hankulan jama'a kan mu, Anty Gude ku je da shi" Yaya yace taredakallonta, "a'a Yaya gidan Anty zani, a can zan sauka, ba zan iya zama ba tare da na ganta ba" yacea zumuɗe tare da jan hannun Saminu suka nufi Yaya, bin shi kawai suka yi da ido jikkuna nasanyi, yana isa inda yake ya saki hannun Saminu ya kama na Sahabee suka wuce inda jerun motocinyake, kamo hannu Umar Insu tayi tare da goge hawayen da suka zubo mata ta kalli Yaya, jinjinamata kai yayi cike da ƙarfafa gwiwa, sauke numfashi tayi tare da faɗin "uncle Kamil muje, waƴansu su zo mu je a can" tayi maganan tare da wuce wa inda motocin da suka zo ɗaukansusuke, haka suka nufi motoci jikkuna a mace.... Fitowa Sadiya tayi kare da waya a kunni cike da mamaki a saman fuskanta ta nufin barinsashin, kusan karo ta kusan yi da Mama da ta kawo jiki, saurin ja baya tayi tare da zare wayan ta katsekiran, "a'a lafiya Sadiya! Saurin me ki ke haka?" Tace cike da mamaki, "wai Anty Iƙilima netacegata a cikin asibitin nan!" Tayi maganan mamaki be bar saman fuskanta ba, "Iƙilima ta zone!" Tace ita ma cike da mamaki, "haka tace amma ban sani ba ko zolayata take" "to je ki duboammayanzu na wuto farfajiyan wajen banganta ba, duk da na biya gaida ɗan wajen Zainaba a sashinyara" tace tare da gyara zaman basket ɗin dake hannunta, "kawo in shiga da shi Mama" tacetareda kai hannu da zumman amsa, "a'a jeki ɗubota kar ya zo da gaske ne" tace cike da kulawa, jinjina mata kai tayi ta raɓeta a natse ta fice, da zallan mamaki ta bi ta da ido.... Tana fita farfajiyan ta hangeta can tsaye da alamun ita take jira, zare ido tayi tare da nufartaaguje, tana zuwa ta faɗa jikinta tare da sakin ihun murna, murmushi ta saki tare da faɗin"aasibiti muke fa" "manta Anty Iƙilima farin cikin ganinki ne, sannu da zuwa, ke ɗaya ki ka zo? Ina ki kabar Abban?" Ta jefa mata tambayoyin cike da ƙaguwan jin amsa, murmushi ta saki tare dafaɗin"yana tare da Daddyn su, ba daɗewa zan ba gobe zan koma" "hakan yayi mu isa ciki" tayi maganan tare da amsan jakanta ta ja hannunta.... Tura ƙofan tayi a zumuɗe tare da faɗin "Harira wallahi ita ce, Mama Anty Iƙilimance da gaske" miƙewa Harira tayi zunbur tare da sakin ihu, wani banzan tsuka Sa'adatu dake zaune tanabinsuda ido ta saki tare da ma Iƙilima kallon sama da ƙasa ta kauda kai, murmushi Mama ta saki cikeda farin cikin ganinta tare da faɗin "sannu da zuwa Iƙilima"... Murmushi ta saki tare da faɗin "sannu Mama" "ƙariso ciki" Harira tace tare da riƙota, ba musutaisa, har saman sofa ta kaita ta zaunar da ita ta jawo ruwa ta miƙa mata, "sannu da ƙoƙari Harira"tace tare da amsa, murmushi ta saki tare da komawa gefe, kallon Sa'adatu tayi cike da mamaki yanda ta nuna kaman ba ta san tana wajen ba tare da faɗin "yau mutumiyan na ku lafiya kuwa?" "Ita ta sanin ma kanta, tun jiya da daddare take wani shashshan ƙamshi, ba ta amsa maganakuma ba tayi, se harara da tsuka se ife-ife da take in barci ya ɗauketa da kiran sunan Abdull" Sadiya tace cike da rashin damuwa, "to fa!" Tace cike da mamaki, "manta da ita ba ta sanAngonna ta ya dawo ne, bari in kira Yaya Kabir in sanar mai da zuwanki" murmushi ta saki idantaakanSa'adatu.... Murmushi Harira ta saki tare da isa inda take, cike da nuna tsan-tsan kula ta riƙo hannuntatareda faɗin "ƙawa ga Antynmu da muke faɗa miki kullum tana gaishe ki ta zo duba ki" tayi maganancike da muryan rarrashi, ɗago firgitattun idanunta da suka kaɗe tayi ta watsa mata tare dasakahannu biyu ta ingijeta da ƙarfi, da sauri Iƙilima ta yarda ruwan hannunta ta tare ta cike daɗinbinmamaki me haɗe da fargaba, tana faɗawa a jikinta ta sauke wani ƙaƙƙarfan ajiyan zuciyansamun nasara..... "Kina da hankali kuwa!" Sadiya tace rai ɓace, zuba mata ido gaba ɗayansu suka yi da mamaki, ɗagowa tayi ta kallesu kallo me ɗauke da wasu abubuwan da ta barwa kanta sani tare da janƙaƙƙarfan tsaki ta kauda fuska, kallon juna suka yi da mamaki, kafin su kai ga faɗin wani abuanbugo ƙofan da ƙarfi an faɗo ciki..... Habibu na dai-daita parking ya ɓalle ƙofan dake ɓangaren da yake ya fice da sauri ya nufi cikingeneral parlor a guje tare da ƙwalawa Anty kira cike da zumuɗi, sassakkowa suka yi jikkunaamace suka dafa mai baya, yana shiga ya tsaya turus tare da bin Babiya da Baba Mari da yaradakezaune fuskoki cike da murmushi da ido, da sauri ya nufeta ya rumgumeta tare da faɗin "matar!" "Mijin" tace tare da fashewa da kuka, murmushi Baba Mari ta saki tare da faɗin "ai kuka yaƙareyanzu Hajiya tunda gashi a gabanmu" sakinta yayi ya rungume Baba Mari tare da faɗin "BabaMarin Anty!" Murmushi ta saki zuciyanta na rauni, sakinta yayi ya miƙe tare da fara waige-waige, "ina take!" Yace tare da juyawa ya kalli Yaya, murmushi ya sakin mai tare da fara takawa ahankali ya nufeshi, kafeshi da ido yayi zuciyarshi na tsitstsinkewa, yana isa ya kamoshi yarungume shi ya matse shi da kyau, yanda ba ze iya kuɓucewa ba, saki jiki yayi cike da mamaki, dan ya kasa gane dalilin wannan rumguman, "Antynka ba ta tare damu!" Yace a hankali muryanshi na seasion, wani azababben sanyi ya ji ya taso mai tun daga ƙasan ƙafa, cikinkyarmanlaɓɓa ya motsa su a hankali tare da faɗin "tana ina! Ba dai sun ɗauketa daga gare mu ba!" girgizakai yayi a hankali zuciyar shi na rauni, kafin yace "ta koma ga mahaliccinta!" Wani banzanturayamai wanda se da Ali da Lurwanu da ke kusa da su suka yi saurin kama shi, ɗago idon da sukafiffito waje cikin ƙanƙanin sakanni suka kaɗe yayi tare da watsa su a saman fukan shi cikedagargaɗi me ɗauke da tashin hankali.... Bin shi da ido kawai suke saboda yanda duk ilahirin jikin shi ke ɓari, fashewa da kuka suSuwaibasuka yi cike da tashin hankali, kallon Salman yayi a razane, saurin juyawa yayi yana sakinnashi hawayen, da sauri ya nufe shi, kamo shi yayi ya juyo da shi ya fuskance shi cike da tashinhankali yace "menene gaskiyan abinda Yaya ya faɗa yanzu! Salman Anty! Da gaske! Wai Anty!" Sekumaya tsaya cak saboda jin saukan kukan Insu, Farisat, Yasmin, Sadam, Sahabee, Umar da yayi lokaci guda, saurin juyowa yayi a razane ya zube musu idoƙirjinshi na mugun lugude, taga-taga yayi ze faɗi Balarabe da Salman suka riƙo shi, zamewa yayi yazauna daɓas tare da sakin wani rikitaccen kuka me haɗe da sumbatun da ba wanda ke shedaabinda yake faɗi.... Da zallan mamaki suka juya tare da watsawa waƴanda suka shigo idon dake cike da firgici, mutane uku ne, ko wannen su riƙe da mugun makami, kallo ɗaya zaka musu kasan ba suhaɗahanya da mutumci da imani ba, "su waye ku!" Sadiya tace cike da tsoro, wani banzan kallowandaalamu ya nuna babbansu ne ya watsa mata tare da faɗin "waye Sa'adatu anan!" Yayi tambayancike da gargaɗin ku ka kawo taurin kai zaku ji a jikin ku, "me zaku mata!" Harira tace cike daƙarfin hali.... Tsalle ɗaya yayi ya wanka mata mari tare da faɗin "ubanki zamu mata, ina take!" "Gata" Iƙilimatace tare da nuna ta, wuce wa inda take suka yi fuska babu wasa, "ina abinda ki ka sata!" Babbanyace a kausashe, ko gezau ba tayi ba bare ta tanka, se ma kauda kai da tayi cike da rashindamuwa, sa hannu yayi ya juyo da fuskanta da ƙarfi tare da daka mata tsawa, gaba ɗayansusunrazana ban da Sa'adatu da ko gezau ba tayi ba se ƙwace fuskanta da tayi da ƙarfi ta tattaradukkan ƙarfinta ta hankaɗashi tare da buga tsaki ta kauda kai, da mugun mamaki ya miƙedagafaɗuwan da yayi ya bi ta da ido.... A harzuƙe biyun da ke gefe suka yi kanta suka shaƙota cike da ɓacin rai, "dan Allah ku yi haƙuri ba ta cikin hankalinta, ta samu matsala a ƙwaƙwalwa" Mama tace murya na rawa cike da magiya, "me ke faruwa anan!" Ɗan kuka da ba wanda ya lura da shigowanshi yace idan shi akansu, zareido shugaban na su yayi tare da ja gefe, da sauri sauran suka saketa suka ja gefe, cike da mamaki ya bi su da ido, "me ku ka zo yi anan!" Ya kuma jefa musu tambayan murya ba wasa.... "Saƙo a ka turomu amsa, se dai a duhu muke Ɗan kuka, ba musan jininka ba ce" shugabansuyace cike da san kare kai, kallon banza ya watsa musu tare da faɗin "kuna wasa da mutuwa, jininSarari ce, waya turo ku!" Cike da firgici suka bi shi da ido, daka musu tsawa yayi tare da faɗin"waya turo ku!" "Rufaffen aiki ne, se dai Haƙilu ne ya biya" "ku fice" yace a tsawace, ficewasuka yi da sauri, "mun gode" Sadiya tace cike da samun sassauci, juyawa yayi ya fice ba tare da yacekomai ba, dan ya zo asibitin duba wani ɗan uwanshi ne ya ga wuce wan su, dalilin da yasa yabiyosu kenan dan ya ga inda suka nufa.... Takowa Yaya yayi ya duƙa kusa da shi cikin muryan rarrashi yace "Samir Antynku ta tafi matsayinshahidiya, ta zo haihuwa ne Allah ya amsheta, tayi dace ka daina mata kuka, addu'anka tafi buƙata a yanzu" ya idda maganan tare da rungumeshi yana sakin na shi hawayen kuka yayi kamar ba ze daina ba, yana kukan yana tuna shuɗaɗɗun abubuwa, ba abinda yafi tsaya mai arai se ganin da ya mata na ƙarshe, sauran jama'an wajen ma kuka suke, su Insu kuwa mutuwar neyadawo musu ɗanye shakaf, kuka suke me taɓa zukatan masu saurare, hatta da Kamil se dayakoka, "meyasa mutuwa zaki barni ki ɗau Anty na! Meyasa kunnuwana suka jiye mun wannanmummunan labarin, meyasa baki kawo min ziyara kafin ganin wannan ranar ba, Anty na buƙatanta rayu" yayi maganan cikin fita hayyaci, buga bayan shi Yaya yake cike da dakiya.... Ɗago kai yayi tare da kallon Yaya, ganin yanda idanumshi suka yi jajazur ya sa shi sakinmurmushi tare da faɗin "komai ya ƙare, ba abinda yayi saura, ba da nasara na dawo ba da faɗuwana dawo Yaya, ni kasashshene! Tunda har na kasa ganin ranar da Anty zata bar duniya! Samir baka da sa'a! Samir baka da nasara a rayuwa! Samir ka yi asara mafi girma" ya idda maganatareda kwanciya a ƙasa yana saki kuka me cike da nan agaji..... Saurin ɗagoshi Babiya da ta iso wajen tayi tare da faɗin "daina faɗin haka Samir daina, Aminatatafi mu mata addu'a, shi tafi buƙata" janye hannun shi yayi daga na ta, tare da faɗin "kinsanwacece ita kuwa a wajena Hajiya! Rayuwa tace! Anty uwatace! Antyn garkuwatace! Anty ƙarfingwiwatace! Tayi min abinda iyayen da suka haifen ba za su taɓa iya mun ba, ta soni, ta ƙaunaceni, ta ginani, nasaran da na dawo da shi gare ku a yau ita ce sila, ita ce, ita guda ɗaya! Batanemi wani ya temaka mata ba wajen kaini ga nasaran rayuwata ba" ya idda maganan tare da sakatafukan hannun shi a fuskan shi ya fashe da kuka me ƙarfi, kallon Yaya suka yi cike da mamaki.... Murmushi ya saki tare da faɗin "Amina ita ce ta saka hannu akan su cigaba da riƙe shi har tsayinwannan shekarun" "mene!" Suka ce da ɗokacin mamaki, jinjina musu kai yayi cike da tabbaci, "saboda me ne!" Daddyn shi yace cike da zallan mamaki, "saboda ya gina rayuwarshi kamar dai haka" yace tare da nuna shi, "Abdussamad yi mana bayani yanda zamu fahimta" Babiya tacenata mamaki ɗauke a saman fuska.... "Lokacin da aka kama Saminu Samir ya tsorata sosai, ya ƙulla abota da tunani da kuka, baburarrashin da ba ta mai ba amma abun ya shige shi sosai, damuwar shi abokin shi Saminudakecan, baya so a cutar da shi saboda shi, kuma ba ya so ya shiga hannun su, kuma yasan dolecikinbiyu a yi ɗaya, imma Saminu da baya da lefin komai ya ɗau nauyin hukuncin, imma shi ya miƙakanshi, ku ba ku da lokacin sauraranshi, ba inda yake samun mafaka se a wajenta, fahimtar hakan da tayi ya sata fara binciken mafita, zan iya rantsewa akan abincin kirki ba ta iya ci, gashi nan shine me takurata akan se ta ci" yayi maganan tare da nuna Samir dake kuka.... Taga darare da yawa ido biyu, ba ta inda ba ta nemi agaji ba, kwatsam se dabara ya zomata, tayi farin ciki sosai, duk da kasantuwar shi me wuyan ɗauka ga kowa, ta same ni da batun ta sanar dani, ni kaina na ji ba daɗi amma haka nan na ƙarfafata dan a lokacin shi ne kaɗai mafita, mafitanshine dole Saminu da yaƙi magana a sashi ya buɗe baki, wato ya faɗi asalin wanda yayi wannanbincike a kamashi, ko da ta tari Samir da maganan ya rikice ya ruɗe yace ba ze iya tafiya yabartaba, da kanta ta shawo kan shi har ya amince ta shirya ta je ga Saminu ta ba shi umurninyafaɗi asalin wanda yayi abun, Saminu ya nuna ba zai iya ba, saboda Samir amini yake a wajenshi, daƙyar da ban baki ta shawo kan shi ya amince, da saninta da yardanta aka kama Samir, tayi hakanne kuma dan ta gano, in suka kamashi akan wannan lefin, zata gabatar musu da wasu abubuwada ya binciko dangane da ƙasar wanda ze amfanesu tare da kawo musu cigaba a ƙasan, intamiƙa su garesu matsayinta na lawyershi za ta samamai rangwami daga hukuncin da zasumai, haka ko aka yi, ta miƙa komai gare su sannan ta miƙa ƙoƙon barar nema mai sassauci, babuɓatalokaci suka amince, se dai sun miƙa mata na su ƙoƙon na son kasancewa tare da shi, za subashi daman faɗaɗa tunanin shi da baiwar shi da iliminshi, ze zauna da su yayi aiki tare da su, zasuɗage zaman ƙarshen da za'ayi har bayan tsayin shekara goma sha biyu, a wannan ƙadaminkukakunno kai, ku ka so ɓata komai" ya tsahirta tare da kallon Gude da jikinta yayi mugun sanyi tareda Daddyn su.... "Kun janyeta matsayin lawyershi kun ɗaura wani, yana shirin rikita komai, ta rasa yanda zatayi ta shawo kan ku, ku fahimceta, kun ƙi tsayawa ku saurareta ta rasa madafa da abin yi, dalilindayasa ta amincewa buƙatar su kenan dan ba ta da wani mafita ba ku ba ta ko wacce dama ba, sedai ta roƙi su nuna gamsuwar bayanan lawyernku, sannan su nuna mai za su sake shi, surufedukwata ƙofan da ze zo gare su, su kuma rufe ƙofan da wani labari akan Samir ze iso kunninkowahar da ita, sannan shima su rufe duk wata ƙofa da ze ji labarin gida, sun amince dan damahakasuke so, dalilin da yasa ku ka kasa cin mishi kenan, duk shirinta ne" ya idda maganan taredabinfuskokinsu da ya cika da tsan-tsan mamaki da ido.... "Dama komai da sanin Anty! Ashe shiyasa kullum na tambayeta dangane da shi se tace mun"yana cikin amincin ubangiji ze dawo gare mu cike da tarin nasarori" Salman yace cike da jinjinahali irin na Anty, murmushi Samir ya saki tare da faɗin "ganina da ita na ƙarshe, ta ziyarceni harinda aka kaini, mun zauna gani gata, tana sakin mun murmushin ta me cike da ƙauna tace"Samirkar kai ƙawa zuciya, ka zama namiji, ka ƙarfafa zuciyanka dan gina goben ka, gina gobenmunada matuƙar mahimmaci a wajen mu da ahalin mu" na ce Anty ba lallai in jure rayuwa bakuakusana ba, tayi murmushi tace "Samir duk abinda Allah yace ze faru se ya faru, ko kana tare damukobaka tare damu, me ka ke tsoro? Ba fa ma da kilinan goge rubutaccen ƙaddaran mu" na ceAntyzaki dinga kawo mun ziyara? "Tace ka shafe tunanin Anty zata ƙara zuwa, ka mai da hankali kadawo a zakin Anty, zanyi alfahari da kai" jinjina mata kai nayi nace nayi miki alƙawari, tace"nasan zaka iya" ashe zan dawo da nasaran ba tare da tana duniya ba, a she maganan da mukayi nabankwana ne, a she idanuna ba za su sake ganinta ba" yana kai nan ya miƙe a natse ya nufi ƙofa... "Ina zaka Umaru!" Babiya tace murya na kyarma, "zan koma, zan koma inda na fito, ba zaniya zama tare da ku ba Anty ba, na dawo ne da ƙishin ruwan ganinta, wanda ganinta shi ne zemagance min shi, se dai ba ta, ba kuma zata zo ba, na tabbatar da ƙishir ruwan namshi zeajalina, ku barni in nesa da ku zan fi samun aminci" ya idda maganan cikin rishin kuka tare da cigabadatafiya.... Share hawaye Yaya yayi ya sa hannu a aljihun gefen wandon shi ya zaro waya, da sauri ya shigawajen ajiye recording ya danna hannu na rawa saboda kama handle da Samir yayi, "Samir!" Muryan Anty ya bayyana rangaɗaɗau a kunnuwansu, ba shi ba hatta saura tsayawa cak sukayi suka juyo a hanzarce suka zubawa Yaya ido.... "Suwa ye waƴan nan Sa'adatu! Me suke nema a wajenki!" Iƙilima tace cike da tashin hankalintare da nufarta gadan-gadan, saurin riƙota Mama tayi tare da faɗin "barta Iƙilima ba ta cikinhankalinta, "tana ciki Mama, tana sane da komai raina muku hankali take" tace murya ɗaukedaɓacin rai, isa kusa da ita Sadiya tayi tare da faɗin "Sa'adatu kina jina! Me suke nema! DanAllahfaɗa mana dan in suka dawo mu ba su, yau albarkacin Ɗan kuka muka ci gobe ba dole ya kasanceyana kusa ba" ta idda maganan cike da muryan rarrashi, ko kallon inda take ba tayi ba, "Sadiyaku ƙyaleta dan Allah" Mama tace cike da magiya, jinjina mata kai tayi tare da miƙewa tabar wajen, "ga abinci ku sakawa Iƙilima ta ci" "a'a Mama ba yanzu ba, na ci abinci a jirgi muna gabdasauka" "to shikenan, ya ki ka baro mutanen can?" "Suna lafiya suna a gaidaku" "muna amsawa, ina wannan yarinyar me kirkin nan?" Murmushi ta saki tare da faɗin "Insu!" Ɗago kai Sa'adatutayi ta baza musu ido, "eh ita, ai wannan yarinyar me dattakon manya ne" tace murya cikedamurmushi, murmushi ta saki tare da faɗin "aiko tare da ita muka zo".... "Tare da Insu! Tana ina!" Sadiya tace a zumuɗe, "na barota a airport, yau ne Yayan nan na suzedawo, ta zo tarban shi" "ashe yau ne! Allah sarki, wallahi da na sani da na je, ma sha Allahki cezama yayi riba" "wallahi na so tsayawa tace in zo kar in ɓata lokaci in kasa samun damanzamadaku, shiyasa na taho, amma tace anjima za su zo" "Allah ya kai mu, da Mairah ta zo?" "A'a tanacan""tare zaku koma goben?" "Eh in sha Allah" "Allah ya kai mu, wallahi har na ƙosa in ganta" "ai yarinyar ba da ga nan ba, in dai karamci da mutumci ne" Mama tace cike da yabawa da hankalinta, tsaki Sa'adatu ta ja tare da kauda kai, cike da mamaki suka bi ta da ido.... Tsayawa yayi cak zuciyar shi na sama da ƙasa da sauri da sauri, juyowa yayi kaman me gudunganin wani abu, ganin Yaya a tsaye riƙe da waya ya sa shi lumshe ido, murmushi me haɗedahawaye Yaya ya saki tare da danna recording ɗin ya cigaba, "na yi maka wannan recordingɗinneakan ƙadami biyu, in ya riske ka Anty ta rasu tana buƙatan addu'anka, in be riske ka ba, Antytarayu ta ga dawowanka ta rungumeka a ƙirjinta, bana da lafiya Samir, kalman da na kasa faɗawakowa kenan, amma kai zan faɗa maka saboda yakinina akan ka me girman gaske ne, batuncancern jinin da nake ɗauke dashi gaskiya ne, amma cikinta akwai wata gaskiyan da ba kowayasan dashi ba, ina ɗauke da matsalar zuciya wacce ta gama rauni, ban fahimta ba se da lokaci yaƙure, rauninshi ya bayyana Samir, gashi ina ɗauke da cikin ɗan uwanka, ba zan iya amincewadakisan kai ba bare in yarda a cire shi, ga ƴan uwanka nan amana, zan barsu a tsakiyan dajindabagida gaba ba gida baya, kai ne garkuwan su Samir, ga amana nan na baka, na san ba zaka barsusu zubda hawayen kewata ba, ba zaka bar damuwa ta kawo wa ɗayan su ziyara ba, ba zakabari ko kuɗa ya rabi jikin ɗayansu da nufin cutarwa ba, Allah ya maka albarka, Allah ya albarkaci rayuwarka da na ƴan uwanka, Allah ya kulamin daku, Allah ya zama gatan ku, Allah ya jiɓanci lamuranku" jin shiru alamun maganan ya ƙare ya sa shi zamewa ya zauna ƙasa daɓas taredasakin kuka wanda ke fitowa daga ƙasan zuciyarshi, ba wanda be koka da maganganun Antyawajen ba.... Su Insu kuwa kuka suke na tsan-tsan maraicin rashin ta, "zan iya Anty, zan iya, zan zame musugarkuwan da ba wanda ya isa raɓansu da sharri" yayi maganan cikin rishin kuka laɓɓanshi naɓari tare da buɗe musu hannu, da sauri suka rarrafa suka isa gareshi, tattarosu yayi ya rungumeya saki wani raunataccen kuka, haka suka yi ta kuka cike da kewan Anty, ba wanda yayi yunƙurinhana su, dan sun fahimci suna buƙatan rage nauyin ƙirazansu.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Sixty one "Na rantse maka da asssmadillazi lam yalid wa lam yuladu akuyanci suka shirya mana, kaii!" Yace cike da mamaki tare da kama baki idan shi akan mutumin dake zaune a gaban su, kodayake tambayi Walki ka ji gaskiyan batun, idonmu idan ɗan Kuka tsaye yana ƙare mana kallofa" ya idda maganan cike da tsoron abinda ze bi yo baya..... "Rufe mana baki dalla, za su san sun mana jakanci" wanda ke bin su da ido da alamu ya nunashugaba yake garesu yace yayi tare ra zaro waya ya danna kira, kaman jira ake kiran na shigaakaɗaga tare da faɗin "aiki ya kammala?".... "Ba'a fara ba, bare a kammala, kai dama kasan yarinyar jinin Sarari ce ka tura mu gareta?" "Me! Sarari! Waya faɗa muku!" Yace cike da firgice, "to tsaya ka ji, ba mu zakawa wannan tambayanba, kan me uwa da wabi za'ayi wallahi, sunanka ya fita fitt, dan na gano akuya ku ka shirya mana, dan haka ka jira shi ze iso gareka, kuma ka gaggauta turo mana raguwan kuɗin mu, in kumakanuna wayau zamu nuna maka Dila" ya idda maganan tare da zare wayan ya katse cike da ɓacinrai.... Sauke wayan shima yayi zuciyan shi na bugu tare da bin wayan da ido, kaman wanda aka marayayi firgit tare da fara nema number a hanzarce ya danna kira, ana ɗagawa yace "yarinyar nanbazata taɓu ba, ƙanwar Sarari ne, kuma sun faɗa mai sunana" "me!" Muryan wanda ya ɗaga kiranya bayyana cike da firgice, "ƙwarai yanzu Na Shehu ya kirani ya sanar mun" yayi maganancikedatashin hankali... Ka ga Haƙilu kwantar da hankalin ka, zamu san yanda zamu ɓullo wa abun, ba ze iso garekaba, ka shirya yau ka taho Yarban, in komai ya lafa se ka koma, amma ka kira su ka tambayanmunsunga yarinyar" "okay" yace cike da samun sassauci tare da zare wayan ya katse kiran ya maidawa number Na Shehu kira.... Banda fatan ya ɗaga ba abinda yake, se da ta kusa katsewa ya ɗaga, "yawwa dan Allah NaShehutsaya ka saurareni tambaya guda zan maka" "baka da wani magana dani Malam, ka turominkuɗina kawai" yace murya a kausashe, "zan turo maka yanzu kuwa" yace murya a sanyayedaalamun san samun abinda yake so, "ya fi maka" yace cike da rashin damuwa, "amma sungayarinyar a asibitin?" Ya jefa mai tambayan cike da fatan ya ba shi amsa.... "Oho wannan su zaka tambaya, ni dai inji alert yanzu in ba haka ba zaka ga jakancin da bakataɓagani ba" ya idda maganan tare da miƙa ma na kusa da shi wayan, "ina ji" yace murya ba daɗi, "yawwa Ɗan Iya kunga yarinyar kuwa!" Yace a zumuɗe, "ra'ayil aini kuwa, idan mu idanta, munganta ganin idanmu kai wani bangaza da ta mun har yanzu ƙuguna be daina zafi ba, kalantakalan ɗan uwanta, a fusace take" ƙitt ya katse kiran ba tare da ya yatsa jin zuban da yakeba, tsaki ya saki ya ciro wayan ya bawa Na Shehu tare da faɗin "wannan gayen yana shirin wasadamutuwa".... "Se ya dawo, shi ze kai ziyara can ba tare

Chapter 98 of 109