Share this page
ya faɗa mana, na ta ya murna Allah ya ƙaramai lafiya" "amen, isowan mu muka ji batun farfaɗowan" Lailah tace cike da farin ciki" "mashaAllah, wallahi haka yace mana" tace ita ma na ta muryan cike da farin ciki... "Ya haƙurin wannan bawan Allah kuma?" Tace cike da alhini, "Alhamdulillah Baba sa'i yayi" tacea hankali, "Allah ya gafarta mai, in kuna tare da yaran se ku haɗa mu mu musu gaisuwa" tacecike da dattako, "in sha Allah, zan iya magana da Uncle ɗin?" Ta jefa mata tambayan cike dafata, "be jima da farkawa ba, sannan doctor yace yana buƙatar cikakken hutu, mu jira ko zuwa gobeseku gaisa ko?" Ta idda maganan a natse, "to shikenan Hajiya na kusa in gaidata?" "Eh gata" tacetare da miƙa ma Hajiya.... Gaisawa suka yi cike da taya juna farin ciki tare da mata gaisuwa, suna gamawa ta miƙa maA'isha, nan suka dinga miƙa ma juna ta na taya su murna suna mata gaisuwa ana mayar maLailah tace "to se na kira ki" "to Anty Lailah" tace tare da katse kiran, "ku tashi mu yi dinner suLailah za su wuce yanzu dare yayi" A'isha tace tare da miƙewa, "bari mu ƙara duba shi da jikin" Khadijatu tace tare ds miƙewa tayi ɗakin, "Yasmin ce ma su Maude su zo su gaida shi" Hajiyatacetare da miƙewa.... Suna shiga suka tadda mazan zazzaune tare da shi, kallon su yayi a natse ya sauke ido ba taredayace komai ba, "wannan idon na ka akwai sauran barci, ka samu ka ƙara rumtsawa" Hassanyaceda kulawa, murmushi ya sakin mai ba tare da ya yi yunƙurin furta komai ba, shigowa nurses biyusuka yi tare da sanar musu doctor na shigowa, ba shi hanya suka yi ya shigo a natse, murmushi ya sakin ma SSB tare da faɗin "congratulations Mr president" ɗago kai yayi ya kalleshi a natsetare da jinjina mai kai, ciro wata na'ura yayi a jakan da ya shigo da shi tare da fara mai gwaje- gwaje, shigowa SSG yayi a natse idon shi akan SSB murmurshi ya sakin mai tare da ƙure shi daido, sadda kai yayi fuskan shi faɗaɗe da murmushi.... Murmushi Jabir da ya ga komai yayi tare da kauda kai, sallama Yasmin tayi ta shigo su Lawizadafe a bayanta, gaishe shi suka yi cike da farin cikin ganin shi, murmushi ya sakin musu taredajinjina musu kai, kallon Ibrahim yayi tare da kallon yarinyar dake saɓe a kafaɗan Lawiza, murmushi ya sakin mai tare da faɗin "an samu ƙaruwan mace" jinjina mai kai yayi tare da lumsheido, duk abinda yake yi dauriya ce kawai amma shi kaɗai yasan yanda yake ji a jikin shi, "Insiyyahaka samu" Jabir yace a hankali tare da dafa hannun shi dake kusa da shi, da mamaki ya buɗeidotare da zube mai su.... Ganin irin kallon da yake mai ya sa shi sakin murmushi tare da jinjina mai kai, maida dubanshi ga Lawiza yayi ya ƙure yarinyar da ido, "kai mai ita ya ganta" Hajiya tace fuska yalwace da murmushi, ba musu Lawiza ta ba ma Ibrahim da ya nufo wajen yarinyar suka rankaya ita da sauranma'aikata suka fice.... Ƙarisawa yayi a hankali ya shinfiɗeta a gefen shi, murmushi ya saki idon shi akan fuskanyarinyar, kallon shi kawai suke cike da tausayawa, kallon Lailah Hassan yayi tare da mata magana daido, juyawa tayi da zumman ficewa muryan doctor ya dakatar da ita, "a ɗan ba shi space ya samuyahuta yana buƙatan hutun nan sosai" jinjina mai kai suka yi cike da gamsuwa, juyawa ga SSBdaidon shi ke kan Insiyyah ƙarama yayi tare da faɗin "kaci wani abu kuwa yallaɓai?" Yayi mai tambayan a girmame, jinjina mai kai yayi ba tare da ya kauda idonshi daga gareta ba, "teakawai ya sha" Lubabatu tace tare da kallon shi, "wannan ma ya isa, dama so ake wani abu ko kaɗanyashiga cikin" yana kai nan ya zaro kayan aiki, nurses ɗin da suka matsa gefe suka ƙariso, dantemaka mai "zamu saka maka drip ne da allurori dan kaji ƙarfin jikin naka sosai" yace mai cikedagirmamawa, jinjija mai kai yayi tare da gyara zama.... Suna tsatstsaye aka gama mai komai, ko cikakkun mintuna goma be ɗauka ba barci yayi gabadashi, gyara mai blanket Jabir yayi suka tattaro suka fito, kai tsaye dining suka wuce, suna zamaHajiya ta ce ma Elizer ta je ta kira su Nafisat, ba musu ta wuce ɗakunan su, ba su jima ba sukadawo tare.... "Hajiya a kira Insu ne?" Lawiza dake tsaye gefen kujeran da Insu ke zama tace cike da ladabi, ɗago kai tayi ta sakin mata murmushi me faɗi tare da faɗin "kira ta" ba musu ta nufi telephoneɗin dake parlorn, danna number ɗakin tayi ta gyara tsayuwa tare da karawa a kunni, cikinbarcinda ya fara fizganta ta jiyo ƙaran wayan, miƙewa daƙyar tayi ta nufi wajen, tana dagawa muryanLawiza ya doki kunninta, "dinner ya kammala" tace cike da fatan ta sakko, jinjina kai tayi kamanta na ganinta tare da faɗin "I'm coming" a hankali, jinjina kai tayi ta sauke wayan, komawagefenwajen tayi ta tsaya dan jiran sakkowanta.... Ba ta jima da komawa ba ƙaran sautin takalminta ya shiga kunnuwan su, idon su akan wajentabayyana, ƙarisawa wajen a natse tayi ta ja kujera ta zauna tare da kare hamma da hannunta, "badai kin fara barci ba!" Fadila tace tare da kallonta, harara ta zabga mata tare da kauda kai, murmushi ta saki tare da faɗin "a gaida kasa" zaran plate Lawiza tayi ta fara kiciniyar sakamataabinci, "kaɗan zaki saka a ƙoshe nake" tace a natse tare da kallon ta, jinjina mata kai tayi tacigaba da ƙoƙarin zubawa, tana gamawa ta ajiye mata ta ja gefe, "zauna mana" tace tare dakallon ta, da mamaki ta kalleta, dan ta manta da maganan da ta mata da safe, ganin irinkallonda take mata ya sata jan kujera ta zauna a natse, "ki sakawa kan ki abinci" tace tare da ɗaukancokali ta saka a na gabanta ta ɗibi kaɗan takai baki.... "Mairah tayi barci ne?" Salwa tace da kulawa, jinjina kai tayi tare da faɗin "jikinta ne ke sonmotsawa" "subhanallah, in sha Allah ba ze motsa ba, addu'an da na dinga yi kenan wallahi" Khadijatu tace cike da rashin jin daɗi, "na so hasaso hakan, dan yinin yau barci ta dinga yi sannankowa yace zo zuwa take ta lafe kamar wata mage" Lailah tace cike da rashin jin daɗi, ba abindaInsu tace se zaran tissue da tayi ta goge baki tare da faɗin "zan kwanta kaina ciwo yake, gashi gobe 7 muke da class" tana kai nan ta ja kujera ta miƙe.... Jinjina mata kai suka yi cike da jin ba daɗi akan halin da Mairahn ke ciki, "gobe tare zamufita, kina da lecture 7:20 kar ki makara" tayi maganan idonta akan Nafisat da tayi zugumdanjinlabarin abinda ke shirin samun Mairahn, jinjina mata kai tayi a girmame, "Uncle ya farka" Nabilatace idonta akan ta, juyowa daga yunƙurin barin wajen da take tayi cike da mamaki tare dakallonta, jinjina mata kai tayi cike da tabbaci, guntun murmushi ta saki tare da faɗin "Allahyaƙara mai lafiya" tana kai nan ta juya ga su Lailah tare da faɗin "Allah ya maidaku gida lafiya" tanaidda faɗi ta bar wajen, murmushi Jabir ya saki tare da faɗin mulkin ya motsa" murmushi Abubakar ya saki tare da faɗin "kasan muƙamin na manya ne, sarauniyar dakiya ai ba wasaba" dariya suka saki tare da kallon shi.... "Wani ciwo Mairah ke fama da shi!" Kamil da zantukan su ya tsayawa a zuci yace tare da kallonLailah, murmurshi ta saki tare da faɗin "gado tayi, tana ɗauke da raunin zuciya" zare ido sukayi gaba ɗayansu tare da kallon ta, jinjina musu kai tayi cike da tabbaci, "tana kan treatment inshaAllah babu damuwa" Hassan yace tare da kallon su, "Allah me iko" Hajiya tace cike da ta'ajibi, "yakamata a kira doctor ya duba ta" Alhaji Jamil yace tare da kallon su, "hakan yakamata" Jabiryace cike da damuwa.... Murmushi Khadijatu ta saki tare da faɗin "tana kan magani kuma na tabbata da sauƙi tundakuka ga Insu a natse" murmurshi suka saki saboda yanda ta idda zance, "Allah ya ba su ikoncinyejarabawa" Hajiya tace a natse, miƙewa Nafisat tayi ta sallame su ta wuce ɗakinta a natse, miƙewa Sa'eed yayi Jamil yace "zauna Abba yanzu zamu tafi" ba musu ya koma ya zauna, "mumayakamata muyi hoɓɓasa" Salwa tace tare da miƙewa, ba musu suka mimmiƙe, "Hassan kai munanan ko?" Hajiya tace tare da kallon shi, murmushi Alhaji Jamil ya saki tare da faɗin "zantafi daɗan nan naki fa yau" "to Allah ya kiyaye abinda gobe ma rana ne" Hajiya tace tare da sakinmurmushi.... Haka duk suka mimmiƙe suka sallameta suka fice dan tafiya, su Hajiya ba su dawo cikingidabase da motocin su suka fice, dawowa suka yi fuskoki cike da farin ciki wucewa ɗakunan susukayi ko wacce ta nemi makwanci.... Ka tabbata nan ne gidan?" Kainuwa yace tare da kallon Ɗan kuka, jinjina mai kai yayi taredafaɗin "wannan zancen ba ƙarya, na sha ganinta a ƙofar gidan" "bismillah mazaje a shiga dukwanda ya kawo taurin kai a ƙaddamar mai" Kainuwa yace tare da kallon gugun shiryayyunmatasan dake tsaye a gefe, ba musu suka afka ba tare da sun damu da nema ma mutanenciki amincin ubangiji ba, a tsorace ƴan mata da samarin dake cike a tsakar gidan suka fara darewasaboda ba su yi shigan lafiya ba, ma su ihu na ihu ma su ufewa ɗaka da kulle ƙofa nayi.... "Shiru ƴan iska!" Ɗan kuka yace cikin daka musu tsawa, cif suka yi tare da zare ido waje, ƙaremusu kallo yayi ɗaya bayan ɗaya kafin yace "ina shugabanku?" "Tana ciki" ɗaya a ciki tacejiki naɓari tare da nuna ɗakin Shila dake a rufe, "kirawo ta" yace tare da baza mata jajayen idanunshi, da sauri ta wuce tare da fara bugun ƙofar da ƙarfi.... Shigowa Kainuwa da Sarari suka yi fuskoki a muttuke, nan zuciyoyin su ya fara tsinkewa dandadamansu sun san fuskokin, buɗe ƙofan Shila dake ɗaure da zani a ƙirji tayi tare da faɗin"lafiya?"Dan tana tsaka da aikata masha'a bugun ya isketa, nuna mata Ɗan kuka dake tsaye idonshi akansu tayi tare da faɗin "nemanki suke yi" "in musu uban me! ban san iskanci da bara'uba, akanmema zaku faɗo mun gida ba tare da neman izini ba?" Tun kafin ta kai ga rufe baki ɗaya a ciki yayi kanta a fusace ya mata fincika ɗaya ya watsar a gefe tare da zaro adda a fusace ya ɗaga ahanzarce, zare ido Shila tayi cike da tsoro ta fasa ƙara me sauti ganin yana shirin sare mataƙafafu, muƙarrabanta ma ihun suka saki a tsorace, "kull na gaban goshin" Sarari yace taredatakawa a natse ya riƙo addan, sauke wani ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya yayi tare da hamɓaretayajuyaya koma bayan Sarari.... Duƙawa yayi akanta tare da faɗin "tambaya muka zo yi, amsa ɗaya zaki ba mu, ki ka sake ƙaryaya ratsa tsakani zamu aika ki inda ba'a dawowa" jinjina kai tayi da sauri tare da haɗiye kakkauranyawu, miƙewa yayi ya matsa gefe, ƙarisawa wajen Kainuwa yayi tare da faɗin "ina Sa'adatu!" Yajefa mata tambayan idon shi akan ta, girgiza kai tayi a firgice tare da faɗin "ba ta gidan nanwallahi, ta daɗe da barin gidan nan, tana can Yarban, amma ance ta dawo tana nan garinsedai ba ta zo nan ba, amma akwai ƙawarta Ziza tare suke ko yaushe ita zata sani" ta idda magananabirkice, kallon sakanni ya mata ya juya ga Sarari juyawa yayi ya fice ba tare da yace komai ba.... Juyawa ga Shila yayi tare da faɗin "tana ina?" "Tana Seminoye wannan ta san gidan" ta iddamaganan tare da nuna budurwan dake kusa da ita, kallon sakanni ya mata kafin yace, "zamumuka tadda ƙarya ki ka mana wallahi se kin san kin yi, dan ba ma shiri da maƙaryaci" jinjinakai tayi da sauri tare da haɗiye yawu da ƙyar, "na gaban goshi ku tsaya kai da mazaje biyar zamuleƙacan" jinjina mai kai yayi ba tare da yace mai komai ba idon shi akan su, "muje" yace tare dakallonwacce aka ce ta sani, da sauri ta fice ba ko takalmi bare a je ga hijab, juyawa sauran suka yi sukadafa musu baya, "ku tattara kan ku waje guda" na gaban goshi yace tare da banka musuharara, da sauri suka tattara waje guda zuciyoyinsu na bugu da ƙarfi da ƙarfi... "Saboda ku gantalallu ne ku kwashi jiki ku je can ku tare saboda ga ƙanin uwarku ko na ubankuya mutu ko" Gude tace a harzuƙe tare da kallon Nafi da Halima, "dan Allah Gude faɗan nanyaisahaka, tun ɗazu ki ke abu guda ki samu ke ma ki huta mana, kuma fa a asibiti muke, ki yi haƙuri inmun koma gida se ki musu" Daddy yace cike da gajiya da jin mitan da take, "Daddyn su abinnedacin rai, yaran nan fa barinsu na yi tare da shi, amma dake ba mutumci ne da su ba, haka sukakama hanya suka tafi na su wajen suka bar shi shi ɗaya, ba dadin Allah ya jefo ni da wuri badahaka ze cigaba da zama" ta idda maganan a ƙufule.... Murmushi Abdallah da Nafi'u dake ɗakin suka saki tare da kallon su Nafi dake rakuɓe wajeguda, "nace miki ni nace su je" Sudais yace cike da ƙosawa, "ai ko dan ka ɗauki lefin zaka ce haka, memuka haɗa da mamacin da za su je can su wuni zungur haka? Suma waƴanda suka bin kalandangi ne ba dangi Iya babu na Baba" ta idda maganan cike da takaici, knocking ɗin ƙofar akayi ahankali, "shigo" Daddy dake ganin ƙarshen ƙorafi da mita ya zo yace tare da zuba ma ƙofanido, turo ƙofan sojan dake ɗauke da basket yayi tare da shiga a natse, da mamaki suka bi shi daido, miƙa ma Daddy hannu yayi da girmamawa ya gaishe shi, amsawa yayi a mutumce cike da rashinsanayya, ajiye basket ɗin yayi tare da miƙa ma Sudais hannu tare da mai sannu da jiki, amsawayayi idon shi akan shi, haka ya gaggaisa da sauran kafin yace "matar Mejor MShureimmetaaikoni da shi, tace na amso wanda aka kawo da safe" bin shi da kallon rashin fahimta suka yi, dasauri Nafi da ta gane wa yake nufi ta nufi basket ɗin ta ɗakko, ganin an sake abincin da yayi sauratamiƙa mai tare da faɗin "ka gaidata da aiki" jinjina mata kai yayi ya sallame su ya fice.... "Wa ce!" Gude tace da mamaki, "Yasmin ne" tace a hankali, "Yasmin!" Tace da ɗokacin mamaki, "eh" tace tare da zaran plate, "Yaya Sudais in zubo ne?" Tace a natse, "eh zubo mana ga suAbdallah nan za su ci suma" yace a natse, girgiza kai Nafi'u yayi tare da faɗin "a'a wallahi Alhamdulillah" "ba zaka ci abincin zumunci ba?" Yace mai cike da mamaki, murmushi ya saki batare da yace komai ba, zuba musu tayi ta miƙa musu, ba musu suka gyara zama suka shigakwasan girkin Yasmin da tayi bayan komawansu.... "Lallai Yasmin ta kyauta" Daddy yace fuska yalwace da murmurshi, "ai tace in dai Yaya Sudaiszedinga ci ba zata gaji da girko mai ba har se ya gaji da kan shi" Halima tace tare da sakin murmushi, shiru Gude tayi tana mamakin sanin yakamatan su, yaranta uku reras ne a gidanaureamma ba wacce tayi tunanin ko dafo ruwa ta kawo musu amma ga Yasmin wanda a shekarusungirmemata nesa ba kusa ba tayi wannan tunanin, "Mommy in zubo miki ne?" Nafi tace a natse, girgiza mata kai tayi tare da faɗin "ba yanzu ba" "Daddy kai fa?" Tace tare da kallonshi, "zubomun kaɗan in taɓa na albarka, Allah ya saka mata da alheri" "amen suka ce tare da fara zubamai.... "Bismillah" Ziza tace tare da ajiye ma Abdull lemun da ta tsiyaya mai a cup, jinjina kai yayi batare da yayi wani yunƙuri na ɗauka ba, komawa tayi ta zauna a inda ta tashi tare da faɗin"naji damuwa a muryanka lokacin da ka kira ni, Allah yasa dai lafiya?" Ta idda tambayan idontaakanshi, furzar da huci yayi cike da damuwa ya kalleta tare da faɗin "na fara gajiya da gafara sabangaƙaho ba Ziza, ban san me ƙawarki ke shirin maidani ba, mun gama magana akan ta daina komai zamu yi aure mu mallaki juna mu rayu cikin aminci amma ta na shirin juyar da farin cikindamuke hange ya koma hasashe".. Ya idda maganan cike da damuwa, murmushi ta saki dan ta san dama maganan da ya kawoshi kenan, gyara zama tayi tare da faɗin "ba ka kai Sa'adatu ƙwaɗayi da muradin ganin kunmallaki juna ba, komai take yi dan kai take, a yanda na san Sa'adatu in tana son mutumtana sanshi neda dukkanin rayuwarta ba da zuciya kawai ba, kar ka damu kan ka game da wani abu da kagani, dan komai dan kai take da farin cikin ku na nan gaba" jinjina mata kai yayi tare da faɗin"banƙi ba, amma Ziza yanda take tafiyar da ni ne, abin yana bani mamaki, ɗazu fa in kinga yanda tamunmagana akan in buɗe mata gida se abin ya baki mamaki, yanda ki ka san tana magana da wani yaronta, sannan haka ta tafi ta barni babu wani gamsashshen bayani, a haka rayuwa za tayi tsayi kuwa? Ke kin san babu faɗi tashin da banyi ba akan ganin na mallaketa, na ƙi zaɓin iyayenanacedole se ita, babu fushin da iyayena ba su nuna ba amma na murje idona na ce se ita har Allahyasa suka yarda suka nema mun ita, in suka ji wannan shiriritan me ki ke ganin za su ce? Wallahi dazuciya ɗaya nake santa ba din wani abu da ta mallaka ko take da shi ba" ya idda magananasanyaye... Sauke huci tayi tare da gyara zama cike da son kwantar mai da hankali tace "duk na sandahakaAbdull, se dai ita ma da wannan zuciyan da ka ke santa take sanka, son kare lafiyanka da rayuwarka take shiyasa ta maka haka dan kayi nisa da ita, wallahi zan iya rantse maka akanSa'adatu tafi ƙaunarka, dan komanta kai ne a gaba kafin kanta, dole yasa ta nisanceka yanzudankare ka inba haka ba mutanen da suke san cutar da ita za su iya cutar" bammm" ƙarar bugoƙofan parlorn da aka yi ya hana ta iddasa abinda take son iddawa, a razane suka miƙe taredabaza ma waƴanda uka shigo ido, Sarari da Kainuwa da Ɗan kuka ne tsaye a bakin ƙofar sebudurwan da suka taho da ita raɓe jiki na ɓari.... Jarumtar dakiya Ziza ta arowa kanta duk da bugun da zuciyanta ke yi ta kauda kai tare dafaɗin"bayin Allah lafiya kuwa?" Wani bahagon bugu Ɗan kuka da ba ta lura da zuwan shi ba ya sakinmata a baki, zubewa a wajen tayi saboda wani ɗan banzan raɗaɗi da ya ziyarceta wanda yafirgitatunaninta ya motsa ƙwaƙwalwanta, kama bakin tayi da sauri jin wani abu na biyo shi, ɗagohannun tayi da sauri ganin jini ya sata ja baya da sauri ba tare da ta iya fasa ihun dake ciyozuciyanta ba, "dan uwarki mu ki ke ma tambayan yara!" Yace a tsawace.... Girgiza kai tayi tare da cigaba da ja baya da sauri ido a waje, "ina Sa'adatu!" Yace a tsawacetareda bin ta, girgiza kai tayi tare da faɗin "ban san inda take ba" wani bugun ya ƙara kai mataagefen kunni wanda ya ɗauke jinta na wasu sakanni, haɗiye yawun tsoro Abdull da cikinshi ya karta yayi tare da bin su da ido, "wallahi ban sani ba" tace da ƙarfi tare da sakin ƙaƙƙarfanƙara, "wato ke shegiya ko, zaki kawo mana kafiya muna da maganin irin ku" yace tare da juyawayaleƙa waje, kiran yara biyu dake farfajiyan gidan yayi tare da komowa ciki, "Sarari kubtemakakuzauna, ku ba mu minti biyu za tayi magana yanzu" yace tare da nuna musu kujera, a tsoracetaɗago saboda jin sunan da ya kira ta ba za ma wanda taga yake kallo a girmame, ba mususukazauna tare da baza ido, juyawa yayi ya kalli yaran da suka shigo tare da faɗin "ku ci munubantahar se ta kasa motsi" yana kai aya suka nufeta gadan-gadan, miƙewa tayi a zabure tayi hanyar bedroom ɗinta, jawota ɗaya yayi ya hurgar, "wash Allah" tace saboda kanta da ya bugu a hannunkujera one seater, far mata suka yi kaman zakunan da ke matuƙar jin yunwa suka ci karodanama, haka suka haɗa mata zoɓo da dinja, se da suka tabbatar ba ta da wani ƙarfin motsawabare ta gudu sannan Kainuwa ya dakatar da su.... Miƙewa yayi ya nufeta, saurin matsawa Abdull da fitsari ke bin ƙafafun shi yayi tare da mannuwada bango, duƙawa yayi akanta tare da faɗin "kin sani ko har yanzu baki sani ba?" Jinjina kai tayi da ƙyar tare da motsa laɓɓa a wahalce tare da faɗin "Yarban" "tana Yarban?" Yace idon shi akanta.... Jinjina kai tayi da ƙyar, "yaushe ta tafi!" Yace a tsawace, "12" tace a hankali, murmushi Sarari yasaki tare da kallon Kainuwa dake kallon shi, "yi mata hukunci dai-dai da lefinta, ta san komai" yana kai nan ya miƙe, "bani adda" Kainuwa yace tare da miƙa ma Ɗan kuka hannu, da sauri yazarota a bayan shi ya miƙa mai, kuka ta saki me cike da razani tare da faɗin "wallahi ba ruwanaban san me ta muku ba, tace kawai za ta tafi can ne na rakata airport, wannan ne saurayindazata aura, har iyayenshi sun je wajen iyayen da ta nema ta biya su sunyi maganan aurensu" tsayawa cak Sarari yayi dan jin sumbatun da take, dan ta fice a cikin hankalinta tunda ta yi idobiyu da zabgegen addan da Ɗan kuka ya zaro.... Juyowa yayi a natse ya nuna Abdull da hawaye suka wanke ma fuska tare da faɗin "Ɗankukahukuntashi, gobe in ya tashi neman mace ya nemi ƴar arziƙi irin albarka" yana kai nan ya fice, wani razanan nan ƙara Abdull ya saki lokacin da Ɗan kuka yayi kan shi tare da zubewa a wajen.... "Amma raba muku kujeran umra aka yi yau a wajen aiki ko Lumunde?" Cika aiki dake zauneidonshi akan Lamunde da bakinta ya kasa rufuwa yace tare da sakin murmushi, murmushi ta saki cike da mantuwa tace "dole in yi farin ciki Shagari, yau Allah ya tashi ƙafaɗun uban marasauba" "wa kenan?" Yace idon shi akanta, "Alhaji Sahabee mana shugaba ƙasar mu" tace cike da rashindamuwa, da mamaki ya kalleta tare da faɗin "dama be da lafiya ne!" Kallon sakanni ta mai cikeda tuno a inda take maganan kafin tace "um" zabura yayi tare da faɗin "me ke damun shi! Kar dai wannan harin har da shi aka kai ma wa!" Shiru tayi ba tare da tace komai ba, "Lamunde ki yi munmagana mana!" yace a ƙufule, "ban san shashanci Shagari ni ka kewa tsawan!" Tayi magananahasale dan son barin zancen.... "Yi haƙuri amma bani amsata" yace cike da son jin amsa, "ba ya da lafiya tsayin lokaci ammayauya farfaɗo Alhamdulillah" tace tare da miƙewa, "wato se da suka cutar da shi, ƴan banza ƴaƴaniska duk mun san su, kuma za su girbi abinda suka shuka da hannayensu" yayi magananaharzuƙe tare da miƙewa ya fice, sauke numfashi Lumunde tayi tare da faɗin "inda zaku ci munmutuncin wannan ja'iran da ta yi shirin sabautamun rayuwa da na fi jin daɗi.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Fourty nine Sakkowa tayi saɓe da Mairah da ta cin ma ado me burgewa, shirye take tsaf cikin shirintafiyamakaranta, sanye take da wata doguwar riga ash golden wanda yayi mata matuƙar kyau, babyhijab ash colour sanyea jikinta baya goye da jaka sunyi matuƙar kyau se zuba ƙamshi sukekamana sace su a ɓoye.... Murmushi Nafisat dake shirye cikin nata shirin tafiya makarantan ta saki daga inda take hangosutare da miƙewa ta nufe su da sauri, ba ma Mairah hannu tayi tare da sakin mata murmushi, saurin kauda kai tayi tare da ƙanƙame Insu, "ba kiji da kyau ba ne" Insu tace tare da ƙoƙarinsauketa, kuka ta saki da ƙarfi tare da ƙwaƙwumeta, da mamaki ta kalleta tun tashin su taketawani manne mata daƙyar ta barta ta shirya.... "Kin shirya ko?" Tace tare da kallon Nafisat, murmushi Hajiya da ta doso wajen ta saki taredafaɗin "ai Nafisat tun shida take zaman jiran fitowan ki a wajen nan" "ta kyauta ai gunda tazamaɗaliba ta gari" tace tare da sakin murmushi, "ya kwanan takwaran? Babu wani damuwa ko!" Hajiya tace cike da kulawa, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "se rigima da take ji da shi, kuntashi lafiya Hajiya ya ƙafan?" "Barta tayi lokaci

Chapter 75 of 109