tare da faɗin "love you uncle Jamil" murmushi ya sakin mata tare da miƙewayabar wajen, tashi Kamil yayi ya dafa mai baya....
"Har kin gama Hajiya?" Tace tare da miƙewa, "eh" tace tare da sakin mata murmushi, "ni manaƙoshi" tace tare da ƙoƙarin fita daga gefen kujeran, "a'a zauna ki gama ci a natse ina nan, batafiya zan yi ba" girgiza kai tayi tare da faɗin "na ƙoshi ne" "a'a ai ba abinda ki ka ci zauna ki ci inanan parlor" tace da kulawa, murmushi ta saki tare da komawa ta zauna a natse ta cigaba daci...
"Dama kasan nan aka kawo yarinyar nan sannan na tambaye ka ka ce baka sani ba, wai mekake
nufi da ni ne Munnir?" Lubabatu tace cike da takaicin da ta kasa haɗiyewa, ɗago kai Alhaji
Munnir yayi ya kalleta ba tare da yace komai ba ya zari tissue ya miƙe, "ai dole ka miƙe tundakasan ba ka da gaskiya, na faɗa maka ba tun yau ba ka fita da kan ka a duk wani abu da yashafeni da ahalina, ka tsaya iya matsayinka na ma'aikacin SSB kamar yanda sauran suke, kar kadingakatsalandar a wannan fannin" ta yi maganan da ƙarfi, wanda sautin ya iske su SSB dake parlor
suna taɓa hira sama-sama.... Rumtse ido yayi tare da faɗin "bani zaki ma wannan gargaɗin ba, Hajiya zaki ma wa ita ta sakani, umaurninta na ci ka, kuma ko yanzu ta ƙara ba ni umurni zan bi shi ina me biyayya" ya iddamaganan a natse, "to ka cigaba da bi, tunda ka zama me mataccen zuciya, ko da yake da mazuciyan na ka a mace take, tunda kana zaune a ƙarƙashin mace se abinda ahalinta suka ɗaukasuka baka" ta idda maganan cike da rufewan ido, "Luba" A'isha tace cike da rashin jin daɗinmaganan da ta furta, "ƙyaleni Anty A'isha shi ya jawo wa kan shi komai, na faɗa mai ya cireidonshi da hannun shi a abun da ya shafe ni yaƙi, ya shiryawa jin abinda yafi haka ma matuƙar bazeyanje jikin shi ba" tayi maganan murya cike da ɓacin rai, "Lubabatu" Alhaji Jamil yace muryaakausashe, saurin ja baya tayi dan ta san halin shi sarai ze iya kai mata bugu... Murmushi Alhaji Munnir ya saki inda sabo ya saba, dan ya ji fiye da haka daga bakinta, "tafiyazaka yi kenan ba zaka fahimtar da ita kuskuren furucinta ba?" Insu tace tare da ɗago kai tabazamai ido, murmushi ya kuma saki tare da mata alamun kar ta ƙara furta komai, "sorry uncleMunnir, wanda ta haifeni ta raine ni tace kar in raina na gaba dani, sannan kar in bari a ci
mutumcin na, miji gaba yake da mata ko a addinan ce, ko ita ke fita aiki take dawowa ta ci dakai
baka can-canci wannan cin fuskan a tsakiyan mutane ba" ta idda maganan tare da miƙewatsayeta juya ga Lubabatu da ke tsaye tana sakin huci kamar zakanyan dake jin matsanancin yunwa, tare da faɗin "gyara kalamanki Anty Luba, uncle Munnir ba miƙe ƙafa yayi ɗan uwanki na bashi
kuɗi yana ci dake ba kamar yanda ki ke tunani, bautuwan mishi yake ba dare ba rana, da
guminshi yake ci dake, lokutanshi da lafiyanshi da iliminshi ɗan uwanki ke amfana, ba a
ƙarƙashin ki yake ba kamar yanda ki ke ikirari, sannan har in uncle Munnir a ƙarƙashin ki yaketouncle Jamil da Kamil ma a ƙarƙashin ki suke, dan duk ma'aikata Uncle ne" ta idda magananidonta ƙyam akan ta, "ke dan uwarki ni kike faɗawa wannan maganan!" Tace a harzuƙe taredayin inda take gadan-gadan, ko gezau ƙiyawa tayi tana tsaye idonta na bin fuskanta da kallo, dasauri Ibrahim da ya ratso wajen ya janyeta tare da faɗin "dan Allah ki yi haƙuri" yayi maganan
tare da juyawa ya lalli Insu da tayi ko gezau, murmushi Jabir dake kusa da SSB da zantukanLubabatu ya taso da su ya saki tare da bin ta da ido....
"Ai ba ƙarya tayi ba, mu ma in haka ne duk ci ma zaune ne, dan gaba ɗayan mu a ƙarƙashinshi
muke" Alhaji Jamil yace tare da watsa mata kallo me cike da gargaɗi...
"Goya mata baya kenan kayi Yaya Jamil?" Tace rai ɓace, "dalla ba ma son hayaniya anan" Kamil
da ke tsaye gefe yace tare da watsa mata kallon gargaɗi, "wato yau duk kun manta da waceceuwar yarinyar nan, har ku ke hanani hukuntata, wallahi ba zan iya manta tabon da ta manana, kuma wallahi se yarinyar nan ta ci ubanta, Hajiya kin ga abinda nake hango mana tun ranar dayarinyar nan ta sakko garin nan ko? duk inda Insiyyat ko jininta suka raɓa se sun tarwatsa, yanzudubi yanda yarinyar nan ta tsaya a gabana tana zubamun ruwan rashin kunya a gaban mutane" ta idda maganan a zafafe, "rashin kunya ya wuce wanda ki ka yi? Ki tashi kina ɗaga muryaakanmijinki na sunna, wanda ke tsaye akan duk wani abu da ya shafeki ya shafi ahalinki" Hajiyatacerai ɓa ce, "ba na so Hajiya, ba na son shi cikin sabgogina, wallahi bana buƙata, ya cire kanshi dahannun shi, banga amfanin sako shi ciki da ki ke yi ba, menene damuwan shi in ya faɗa minananaka sauke yarinyar nan? Me yake tsoron ya faru? Tambayanshi nayi akan ina ku ka kaita secemin yayi be sani ba" ta idda maganan cike da zafi....
"Ni ma hana shi faɗawa ko waccen ku, ko ban isa ba ne?" "Ba danke yayi shiru ba Hajiya, kobaki
hana shi ba ba ze faɗa ba, saboda kar a ɗagawa ɗiyar Antyn tsohuwar budurwanshi Khadijatuhankali, dole ya rufe, wai shin ma me muka haɗa da sune!, Maƙoftaka ne na iyayen mu, sunkuma mutu, kowa ya kama gabanshi, kuna ɓata lokacin ku da soyayanku, da kulawankugaɗiyarmayaudariya, maha'inciya, wanda ta gaji butulci, butulci a jininsu yake, duk yanda ku ka kai dakyautata mata watarana se ta butulce muku, dan sun tsotsa a wajen uwarsu....
Rumtse ido Insu tayi jikinta nan da nan ya ɗau ɓari, "inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" Ibrahimyace a ƙasan zuci tare da kallon Insu da ta rumtse ido, "Luba, meyasa ba matakin bari ne wai?" A'isha tace murya a ɓace, "barni in tuna musu abinda suka manta Anty A'isha, me Insiyyat tamuku? Tarwatsaku tayi ta kashe ku ta binneku da rayukan ku, ta tafi ta bar ku cikin matsanancinbuƙatan kasantuwarta a kusa da ku, duk wannan be isheku izina ba, kun rungumi ɗiyarta
matsayin ɗaya daga cikin ku, har kai kana rufe min inda ku ka kaita saboda manufarka na kanka, to ga kunan gata in dai butulci ne gadon shi tayi, zata bayyana muku shi in muna da rai" taiddamaganan zuciya na tafarfasa, sakin baki duk suka yi suna mata kallo me cike da ban mamaki, "tana can ta gina rayuwarta ta na gudanar da shi yanda take buƙata, sannan saboda cika siffofinmunafuka da take son yi ta turo ɗiyarta dan farin cikin da ta hanga kuna yi ta ƙara tarwatsawa....
"Correction!" Tace da ƙarfi tare da ƙarisawa kusa da ita, cikin matsanancin ɓacin rai tace "gyarakalaman ki akan mahaifiyata, bana juran gugar zana akanta bare kalman ɓatanci, ke kinsanwacece ita da har ki ke furta wannan kalaman akanta? Antyn ta fiki ta fi duk zuri'arki, tundabata iya walaƙanta wanda ke ƙarƙashinta bare kuma wanda take ƙarƙashin shi, sannan maganadaki ke akan uncle Munnir ya so Anty Khadijatu yaso, ai so ba ƙarya ba ne, kamar yanda ke mawanin shi ki ka so ba shi ba" ta idda maganan a harzuƙe, tare da baza mata razanannun idanuntada suka jima da canza launi, da mugun mamaki suka bita da ido, a razane Lubabatu ta watsamataido....
"Ƙarya nayi? baki so uncle Hassan ba? Har yanzu san shi ki ke tunda har ki ke wulaƙanta uncleMunnir, son ma so wani aikin banza, gwara shi da ya so an maido mai da so, ke ko dakonwahalakawai ki ke, har kina da bakin kiran Anty azzaluma bayan ke ce cikakkiyar azzaluma, kintarwatsatarayyanshi da wanda yake so bayan kin sheda irin san da su ke ma juna, da sanin ki ki ka
tarwatsa saboda wanda ki ke so be maido miki da son ba, saboda rashin adalci irin na ki kumaki
ka kasa kyautata mai, ki ka dinga muskuna mai akan lefin da be da masaniyan wanda ya aikata, duk da kin san ke ce katafilan da ta ruguza farin cikin shi baki na shi daman samun natsuwar damaza ke samu a gidajen su baz kin kasa kyautata mai, baki bar wacce zata kyautata mai taaureshi ba sannan ki zo ki na buɗa baki ki na faɗin Anty ta ruguza rayuwarku? Karya ne ba ta ruguza
rayuwar ɗaya daga cikin ku ba....
"Ke ce ki ka ruguza farin cikin uncle Munnir da na Anty Khadijatu da na ki da na duk wandakeraɓe dake, akan mutumin da be san ma ki na yi ba, da uncle Hassan na son ki da be tafi yaƙyaleki
ba, da ya tsaya dan cikan muradin ku kamar yanda uncle Munnir yayi kafin ki kunno kai a
rayuwarshi, ki iya bakin ki akan Anty, rayuwar da tayi tsakaninta da Uncle be shafeki ba, basusako ki a ciki ba, ba wanda ya buƙaci bakin ki, su ta shafa, kar ki fake da ɗaukan fansa ki tozartamun uwa" ta idda maganan zuciya a wuya, tana rufe baki Lubabatu da ta gama firgita da irinkalaman da take zarowa ta kwasheta da wani gigitaccen mari, wanda ba ta san ta ina ta samuƙarfin kai shi ba, a razane Insu ta ɗago kai ta zube mata ido cike da tsan-tsan mamaki, marinyazo mata bakatatan, ba ta san da zuwan shi ba se saukan shi da ta ji, juyawa tayi da zummanneman abun da zata naƙasata idonta ya faɗa kan na SSB dake tsaye rungume da hannu, tsagawani rikitaccen kuka tayi wanda ya amsa ilahirin side ɗin tare da nufarshi a guje ta shige jikinshi
tare da ƙanƙame shi, "Insu!" Ibrahima da se a lokacin ya dawo daga suman wucin gadin damarinda aka saukema Insu ya haddasa mai, rumtse ido SSB da ihun na ta ke cika mai duniyar jinshi
yayi ba tare da ya iya ko motsi ba, a razane Alhaji Munnir ke bin Lubabatu da ido cike da zallanmamaki.....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Twenty four
Bin gidan da suka shiga kawai take da ido, cike da ƙyanƙyami, gida ne babban me ɗakuna rututua zube, kallo ɗaya zaka mai ka gane gida ne irin na mata masu zaman kan su..... Ganin yanda take wani baya-baya ya sashi juyawa fuska a muttuke tare da faɗin "shige mana" ba
abinda tace mai se shigewa gaban shi da tayi ta ja ta tsaya, guntun tsaki ya saki tare da cirowayanshi ya danna kira ya kara a kunni, a na ɗagawa yace "gamu" be jira amsan da za'a bashi baya sauke wayan ya katse ya mai da aljihu.... Ba su jima da tsayuwa ba wata hamshaƙiyar ƙwanƙwararriyar ƴar bariki wacce zata iya kai 45dahauhu ta fito sanye da bubun atamfa, kallon shi tayi tare da faɗin "har kun ƙariso?" "Eh" yaceadake tare da kallon ta, "wannan ne baƙuwar?" Ta kuma cewa tare da ƙare ma Sa'adatu daketsaye ba um ba um-um kallo....
"Eh ita ce, "ah lallai ba lefi, kai duk kamun na ka da mutunci" tace tare da sakin murmushinƴanbariki, "ina makullin me Shila?" Yace tare da kallon Sa'adatu da ta ƙi cewa ko uffan, "saurinmeka ke, ke baiwar Allah daga wani jahan ya rakito ki?" Ta idda maganan tare da jefa mata tambaya, "a nan" tace tare da kauda kai, "ka ce ƴar gari ne ma, to ina fata ba auren dole ta gudanmawaba, dan wallahi rantsuwa nayi ba ƴar iskan yarinyar da zata ƙi ma auren dole ta zo in ba ta masauki, dan an ɗanɗanamun raɗaɗin zanba cikin aminci" "no ba aure ba ne" yace tare da amsa makullinda ta miƙo mai lokacin da take rattafa zance, "to shikenan, Allah ya ba mu ikon ƙaruwa dajuna, ga ɗakin can, wanda Bala ya ɗaukan ma wannan shegiyan gantalalliyar da ta kasa tsayuwawajeɗaya har se da ta jajibowa kanta maƙale mata manne mata ne" ta idda maganan tare da juyawata wuce ɗakinta... Buɗe ƙofan yayi a hankali ya shige, zaro wayanshi dake ruri yayi tare da kallon sunan dakeyawoa saman screen ɗin "Momy" yace kaman ze saki kuka, kashewa yayi ya maida aljihu, "shigomana"yace kamar wanda aka zaganwa iyaye, taɓe baki tayi ta shige a natse, babu abinda babuaciki dai -dai na me zaman kai....
"Shikenan ga masauki nan kin samu, please ba na son wani shirmen kuma" yayi maganantaredazaro waya ganin ita ne dai ya sa shi ja tsaki ya kashe ya maida aljihu, "da ka ɗauka ai" taceadake, idonta akan shi, "babu abinda ya shafeki da wannan waje ki ka nema gashi nan na baki" yanakai
nan ya juya ta nufi ƙofa kaman ze tashi sama, kyaɓe baki tayi tare da faɗin "abinci yunwa nakeji, sannan please ka haɗo da wannan alluran ina masifan kewan shi" tayi maganan tare da
kwanciya a saman madaidaicin gadon, ko ci kan ki be ce mata ba bare tayi zaton samunamsa....
"Luba! Wani gan-ganci ne wannan!" Hajiya tace murya a matuƙar kausashe, buɗe baki tayi dazumman magana Alhaji Jamil ya kwasheta da marika biyu ma su ratsa jiki, "zo ki bar nankar inillataki" yace a zafafe tare da nuna mata ƙofa, zareta yake ƙoƙarin yi daga jikin shi amma taƙi
yarda da hakan, banda kuka ba abinda take da iya ƙarfinta, runtse ido yayi ya kalli Maudedatunihun da Insu ta sakii na farko suka bazamo ciki, da sauri ta isa kusa dashi ta riƙo hannuntacikedakulawa tare da fadin....
"Yi shiru Insu, daina kukan haka" sakin shi tayi ta faɗa jikin Maude tare da sakin wani marayankuka, buɗe baki yayi a natse tare da faɗin "yaushe ka zama lusari har haka ban sani ba?" Yajefatambayan idonshi ƙyam akan Alhaji Munnir da idanun shi suka juye lokaci guda, guntunmurmushi ya saki tare da kauda kai "duk ranar da ta kuma maka gan-ganci irin wannankaɓallata ni na baka umurni" yace a natse tare da riƙo hannun shi, "me ki ke jira ne?" Hajiya tacemurya a kausashe, "Allah ya baka haƙuri" tace hankali a mugun tashe, ba abinda yace se ficewada suka yi, kamo Insu dake jikin Maude Hajiya tayi ta ja kujera ta zaunar da ita....
"Ba ki gama cin abincin ba ma" tace tare da matso da plate ɗin kusa dasu sosai, ɗibowa tayi tanufi bakinta da shi, kuka ta ɓarke da shi me ƙuna, zamewa tayi tare da faɗin "Anty" kama kai
Ibrahim yayi cike da rashin jin daɗi ya fice, bin shi da ido Maude tayi cike da mamakin rashinɓoyedamuwan shi da yayi...
"Daina kukan mana Insu jarumace ke fa, taso muje" Abubakar yace cike da kulawa, miƙewatayi
tare da bin bayan shi ido na shatatan ruwan hawaye, suna shiga parlor ta wuce inda hotonsuyake a guje, tana isa ta ɓarke da kuka tare da faɗin "Anty" ta rungume hoton, cikin gunjinkukatace "Anty kinga Anty Luba ta mare ni ban mata komai ba, kuma ke ce ki ke ce mana muzama
masu faɗin gaskiya a ko ina muka tsinci kan mu, dan na faɗa mata gaskiya akan abinda tamauncle Munnir be dace ba, shine ta zage ki" tsahirtawa tayi ta sharɓi kukanta sosai kafin tacigabada faɗin "dan nace kar ta ƙara zaginki shine ta mareni duba Anty" tayi magana tare da nunakumatunta da hannu, dubi zafi yake mun kuma na san yayi ja ya kumbura" ta idda maganantareda duƙewa a wajen cikin matsanancin kuka, da sauri Hajiya da hawaye ke bin kuncinta ta ƙarisata kamota tare da rumgumeta cikin muryan rarrashi tace "daina kuka Allah ba azzaluminbayinshi ba ne ze saka miki" tana kai nan ta ɗagota suka yo ciki...
Tunda suka shigo parlorn ya fahimci da ita aka shigo ganin tayi wajen hoton da ya girgiza ganinshi tun ɗazu ya sa shi kafe ta da ido ta ƙasan ido, tana fara rattafo zantukan yaji wani sanyi naratsa kasusuwan shi, su Alhaji Munnir ma gaba daya jikkunansu ne yayi sanyi.... Zaunar da ita tayi ta zauna a kusa da ita, goge hawaye tayi tare da kallon Abubakar cike dayanayinta tace "uncle Abubakar yau mun kai ma deputy chancellor admin ziyara" ta idda
maganan tare da sakin faffaɗan murmushi, bin ta da ido suka yi da mamaki, kauda kai SSByayi
dan ya fahimci ba ta riƙo ne, "me ya kai ku?" Yace tare da kallon ta, gyara zama tayi tare darattafo mai abinda ya faru, "wannan mutumin na daɗe da saka mai ayan tambaya" Kamil yacetare da kauda kai, "wallahi uncle Kamil se ka ga yanda yake ta share zufa, kaman wanda akajefaa gidan bread, su Nachma na ta ƙumshe dariya" ta idda maganan tare da ƙyalƙyacewa da dariya, murmushi suka saki gaba ɗayan su idon su akan fuskanta....
"To tunda Kum fahimci waye shi ai yakamata a yanka mai ticket tunda ba ya da gaskiya" Hajiyatace tare da kallon Alhaji Jamil, "mun fahimci waye shi ai ba tun yau ba, ɗaga mai ƙafa mukesaboda yana da abubuwa da makaranta ke ƙaruwa da shi, ba dadin haka ba ai da yanzu anmantada ya taɓa kasancewa a school ɗin, Abubukar yace tare da kallon ta, "to ai shikenan ammaajamai kunni" "zamu yi ƙoƙarin hakan" "uncle Abubukar babu amfanin rayuwa da wanda be shiryarayuwa da kai ba, tunda aka ce ga doka da odern makaranta kamata yayi kowa ya bi, ai gabaɗayansu a ƙarƙashin makaranta suke, shine fa ya bamu rantsuwa na zamu yi karatu da gaskiyaranar da muka fara ɗaukan lecture, basa ba ma malamai wannan rantsuwan ne?" Tayi tambayan
idonta akan Abubukar....
"Ba wanda be yi ba" yace tare da gyara zama, "to ka ga sun ci amanar aikin su, duk wanda yaci
amanan aikin shi be kamata ya cigaba da aikin ba, ni fa in ni ce me school ɗin nan ka ga
registarer, students affair, examination office deputy chancellor admin duk se na yi wajedasuna kawo wasu, suna ɓatawa makaranta sunanta, suna ɓata tarbiyya ƴaƴan makaranta, yanzukaga wannan abinda ya faru na Hisham Sharifudden ko rantsuwa nayi ba na jin zanyi kaffaraakanbiyan su aka yi suka aikata hakan, na Hisham ɗin ne ya fito ba musan na wa suka tauyewahaƙƙi
da wannan gurɓataccen tunanin na su ba, sannan wanann courses ɗin namu gaskiya da amanayake buƙata, tun a karatu ba'a nuna mana shi ba, ya kake ganin in mun kammala mun faraaiki?Ko wa ze yi abinda ranshi ke so ne, tunda munga ana yi, sanna abinda na gaba yayi shifa nabayaze yi, kuma fa uncle Abubukar kana ganin su kasan bakunan su ɗaya, wai ni za su wa barazananakallesu na watsa musu kallon ban ma san kuna yi ba" ta idda maganan cike da yanayinta taredasakin murmushi, murmushi ya saki tare da faɗin "sannun ki da aiki" "bari in je in yi sallah" tacetare da miƙewa da sauri tayi up stairs... Dago kai yayi a natse tare da kallon Abubukar, murmushi ya saki tare da faɗin "ina hankalcedasu, zamu tsananta bincike" miƙewa yayi saboda idda amsa kiran sallah da ya yi tare da faɗin"abinda ya dace zaka yi ba tsananta bincike ba" jinjina kai yayi cike da girmamawa, "bari mujemasjid" yace tare da kallon Hajiya, "to ina ga kafin ku dawo zamu wuce, dan na san zakujiraisha'i" Hajiya tace da kulawa, jinjina mata kai yayi a natse ya fice suka dafa mai baya, miƙewatayi
ta shige ɗaya daga cikin ɗakunan parlor, alwala ta daura tana fitowa ta tadda su Lubabatuzazaune, wuce wa gefen da praymat ke shinfiɗe tayi tana dai-dai tsayuwa ta juyo ta kallesutareda faɗin "ku hanzarta muna idar da sallah zamu tafi" jinjina kai suka yi jikkuna a mace ... Yana fita ya tadda Shila tsaye a bakin ƙofar ɗakinta, ƙarisawa yayi tare da faɗin "na tura miki
kuɗin" "na gani" tace tare da gyara tsayuwan ɗan kwalin kanta, "a ba ta komai da ya kamata, zanshigo zuwa gobe, please ku yi hankali da ita mahaukaciya ce, ƙwayan da take sha yafi ƙarfinƙwaƙwalwan" ya idda maganan cike da takaici, dariya ta saki tare da faɗin "in ita mahaukaciyacemu tuburan ne, dama duk wanda ya bar gidan iyaye ya fito duniya ai cikakken taɓaɓɓe ne, mudaita kuma zamu ne ta tadda muje mu" ta idda maganan tare da taɓe baki, "duk ba wannanba, ki
dai kula" "kar ka damu, kana sane da Ziza a satin nan za ta dawo ko?" Tayi mai tambayanidontaƙyam a nashi, tsaki yaja cike da rashin madafa tare da faɗin "na sani" yayi maganan tare dafiddowayanshi dake neman a gaji, ganin Momy na yawo a saman screen ɗin ya sa shi faɗin "ohAllahMomy za ki kashe ni" ya idda maganan tare da ɗaga kiran ya kara a kunni....
"Duk inda ka ke ka zo gida yanzu ina son ganinka" tayi maganan a kausashe tare katse kiran, tsaki ya saki tare da maida wayan a aljihu ya sallameta ya fice, komawa ɗakinta tayi ta ɗauwayata aika ma Sa'adatu abinci....
"Tashi ki je kiyi sallah" Yaya da ya fito daga bedroom ɗinshi a shirye tsaf dan zuwa masjidyacetare da kallon Yasmin dake kwance a two seater's, mikewa tayi a natse ta nufi ƙofa, "Yasmin" yace idon shi akan ta, juyowa tayi a natse tare da zube mai ido, "kar Insu ta ji wannan maganan" yace a natse, jinjina mai kai tayi ta fice jiki a mace, tana shiga side ɗin Anty ta tadda Suwaibatsaye cikin shirin komawa gida, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "tafiya?" "Eh Yasmin" "dada din da school gobe ba da na biki mun kwana" tace fuska kadaran kadahan, dariya Suwaibatasaki tare da fadin "akwai weekend se in zuba ido" dariya ta saki tare da faɗin "ranar munadazuwa gidan marayu"....
"Sannun ku da aikin lada, Allah dai ya biya ku, satin da ya wuce muna zaune muna kallonlabarai
a CST tv aka yi ta nuna jamma'an ku a gidan tsofaffi sun kai musu temako da ziyara, nayi tabazaido dan ganin ku, Kabir yace ze iya yuwuwa ba ƙungiyarku ba ne" murmushi ta saki tare dafaɗin"na mune, amma bandamu aka je ba" "kai wannan ƙungiya na ƙoƙari wallahi, Balarabe ka gairinkayan arziƙin da suka kai musu kuwa? Ga shi su na ta kula da su har da waƴanda suka ba suabinci a baki da magani" "ai ƙungiyar ta fara amsa suna a ƙasan nan na mu, har register tayi fadagwamnati" "to kun ji ko, wallahi irin wajen nan yakamata yara su dinga shiga, kai ma bansanabinda ya hanaka shiga ba" "ah zan shiga ina da wannan burin, in sha Allah kin ma ƙara munƙaimi, Yasmin a san yanda za'ayi dani" murmurshi ta saki tare da faɗin, "zan ma Yaya Annur
magana ya baka form" tayi maganan tare da wuce wa, "yawwa ko kefa" yace tare da kallonSuwaiba dake ta sakin murmushi "muje in sauke ki in wuce sabgan gabana" "to me sabga" tace
tare da sakin murmushi tayi waje.... Bedroom ɗin Babiya ta leƙa ganin ta kabbarta sallah ya sata wuce wa na Sadamganin ba kowaaciki ya yasa ta fito dan tanada tabbacin akan ya tafi masjid ne, kullowa tayi ta nufi na Farisat tana shiga ta taddata kwance kife da ciki, "an kira sallah" tace a natse, ɗago kai tayi tare da bintada ido, murmushi ta sakin mata tare da faɗin "ki ƙarfafa kan ki, kar ki sa ran wani ze tsayadakelokacin da ki ke buƙatan temako, ki ɗauka ba ki taɓa saninta ba kamar yanda ta nuna ba tasanki
ba, ki shafeta a littafin rayuwarki zaki rayu cikin aminci" tana kai nan ta sa kai ta fice taredagoge hawaye, miƙewa tayi jiki a mace tayi toilet... Kofar ɗakin Nafisat ta tura tana shiga ta tadda tana ƙoƙarin saka hijab dan gabatar da sallah, "inkin idar ki tisa haddanki sosai kar ki tashi se kin yi isha'i" tace da kulawa, "to" tace a natsetaredazura hijabin, ficewa tayi ta wuce bedroom ɗinta dan ta san Sadam ya tattara su Sahabee sunwuce tare, toilet ta wuce kai tsaye tana shiga ta tuɓe ta ɗaura towel ta haɗa ruwa me sauƙinzafi
ta shige, ruwan na fara ratsata ta saki kuka mara sauti tare da haɗa kanta da gwiwa, ba abindatake tunawa se irin rayuwar da suka yi da ita, se da tabbatar ta ƙoshi dan kanta sannan tatsagaita ta fara saɓa sabulu....
Tana fitowa ta zura doguwar riga a saman bra da fant ta zura hijab ta fuskanci gabas ta kabbartasallah, ba
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 109