da ita tayi tare da bin bayanta ta zauna...
"Ya kwanan baƙunta?" Hajiya tace da kulawa, murmushi ta saki tare da faɗin "Alhamdulillah" cike da nauyinta, "kin tabbata ko?" Tace da kulawa, jinjija kai tayi tare da faɗin "baƙunta yaƙarena zama ƴar gida" tayi maganan fuska yalwace da murmushi, murmushi ta saki tare da faɗin
"tabbas kin zama ƴar gida, hoton yayi kyau" murmushi ta saki tare da faɗin "in wajen be kamataba se a cire Hajiya" tayi maganan a ladabce, murmurshi Hajiya ta saki tare da faɗin "a'a nanneyafi dacewa da shi, jinjina mata kai tayi cike da farin ciki....
"Kar ki cutar da iyalan matan nan Sa'adatu, alheri ta miki ba sharri ba, cutar da ɗaya dagacikiniyalanta tamkar cutar da ita ne" Harira da ta gama sauraran zantukan Sa'adatu tace tare dakallonta, guntun murmushi ta saki tare da faɗin "ba zan taɓa yafewa Insu ba, ko da ace mutanenduniya za su taru a kaina suna tofin Allah ya tsine, kin san kalaman da Sudais ke mai-maitamuna kullum kuwa? Yana sonta ko rabin son da yake mata ba ya mun, a duk sanda ya faɗin munhakaji nake ina mutuwa, numfashi gagarana shaƙa da kyau kalaman suke, duk a haka ki ce inzubaidoina kallon ta" ta idda maganan murya a kausashe.... Dafata Harira tayi tare da faɗin "ba ita tace ya so ta ba, kuma sanin kan ki ne yarinyar nanbazatataɓa son shi ba bare ta aure shi, meyasa zaki sakawa zuciyanki wani abun?" Ture hannuntadakesaman kafaɗanta da ƙarfi tayi tare da faɗin "amma shi yana sonta ai, kuma tasirin da mahaifiyarshi take da shi a wajen Hajiya ze sa ta yarda da auren, in ta amince Yaya dole ya amince, kingakomai ya ƙare min kenan, an bar ni da dakon soyayya mara madafa" ta idda magana zuciyanatafarfasa.... Girgiza kai Harira tayi tare da faɗin "duk wannna abun a zaton ki ne Sa'adatu, be za ma doleyakasance ba, ke ina da tabbaci akan ba ze taɓa faruwa ba, kina da dama da lokacin jawo zuciyanSudais gare ki" murmushin takaici ta saki tare da faɗin "wannna ba tun yau na fara ba, ba kumazan daina a yau ba" ganin ta dage yasa Harari haɗa hannaye tare da faɗin "dan girman Allahkarki cutar ma barrister Amina da iyalanta, matar nan alheri ta miki" ta idda magiyan fuskaamarairaice, miƙewa Sa'adatu tayi tare da faɗin "komai fa ya faru, ki daina ma roƙona, na sanyanzu haka Insu ta fara amsan hukuncinta dai-dai da abinda ta aikata, wallahi ko Anty da duniyata sheda karamcinta gare ni ba ta isa dakatar dani ba" tayi maganan cikin takaicin tuna kalamanda Sudais ke jifanta da shi...
"Ban gane ba, me ki ka ma yarinyar mutane!" Harira tace zuciya na tsinkewa, "kwantar dahankalin ki, ba iyalinki na taɓa ba fa" tace tare da dafata, "Sa'adatu me kika ma Insu!" Tacefuskaa ɗaure, "ba wani abu ba ne, maganinta na canza zuwa wani da ban" zare ido waje Harira tayi tareda faɗin "kaman ya!" "Oh Harira bana son tambaya mana, ki bari in komai ya faɗa za ki ji koki
gani" ta idda maganan tare da juyawa da nufin ficewa, jawota da ƙarfi tayi tare da faɗin"ki munbayani"... Kallo me cike da zargi ta mata kafin ta zare hannuta dake riƙe da nata hannun, cikin rashinɗaukan abinda zata faɗa da wani mahimmaci tace "rashin shan maganinta ze ƙara raunanazuciyanta, in raunin zuciyan ya kai matakin da ba'a so abu biyu ne ze faru, ko ta dawwamacikinazabtuwa wanda za ta fi son mutuwa da shi, ko ta mutu shikenan a rufe shafinta" ƙureta daidoHarira tayi dan ba ta fahimci komai ba, tsaki taja tare da kauda kai, "na canza mata magani" tacecikin taɓe baki, "magani!" Tace a mamakance, "eh, maganin da Dr Hisham ya kawo na canza, shine hukuncinta, zanfi son na biyun ya faru da ita, dan na rage mugun irin dake shirin tarwatsafarin cikin da nake hangowa kaina, in na kalli karamcin mahaifiyarta kuwa shima na biyunzanzaɓa mata dan sauƙaƙa mata azaban da zata sha ana ɗaya, kinga ban kasheta ba katsalandanɗinta ne ya ja mata" ta idda maganan tare da kafe Harira da ta saki baki tana bin ta da kallomecike da razani da ido...
"Anya Sa'adatu zuciya ne a ƙirjinki kuwa?" Tace cike da mamaki, "shine mana, in bashi ba netayazan ƙaunaci Sudais" tace hankali kwance, girgzai kai tayi tare da faɗin "ba shi ba ne Sa'adatu, muguwar tsoka ce me manta alheri, ke har za ki iya nufan ɗaya daga cikin ƴaƴan barrister Aminada mugunta haka? Ke da zaki tsaya da dukkanin ƙarfin ki wajen kare su, ke ce ke niyyantarwatsasu" ta idda naganan murya na rawa, "dakata Harira! ban zo dan ki tsaya kina
gaggayamun maganganun da ki ke so ba, ita ma ta temakeni ne dan tayi suna ba dan wani abuba, dan haka ki bar mai-maita mun zance ɗaya, wa ki ka ga na nufa da sharri a iyalan na ta?, Koda Farisat ke ikirarin son shi a wan can lokacin na mata ko kallon banza ne? Ban mata komai ba
dan na san baya santa, ita ko Insu sonta yake, wallahi ba zan tsaya ina ji da ganin Sudais nafurtayana son wata na ba, dame Insun ta fi ni? Na fita cika da zati da sura na cikakkiyar mace, nafitasanin me ne ne so" ta idda maganan da ƙaraji "hmm Sa'adatu kenan, idon ki ya rufe, ba lallai ki
hango abinda nake nunashsheki ba, amma na sanj ke ma kuma kin sani, cutar da Insu tamkar
cutar da kowa na cikin wannan iyalan ne, yayi miki kyau, gunda da ki ka canza mata magani ...
Tana kai nan ta jawo hijabinta ta saka suka fice, sallaman Mama da mamaki ya kusan kashewaazaune tayi suka fice, bin su kawai tayi da ido jiki na ɓari, suna fita ta kalleta tare da faɗin"zaki
shiga ki ga yanayin jikin na ta ne?" Tayi naganan idonta akanta, girgiza kai tayi tare da faɗin"sewani lokacin in na shigo, sauri nake" ba abinda tace mata se tsaida mata me napep da tayi, tanahawa ta juya ta koma cikin gida zuciya cike da saƙe-saƙe.... Gyara zama Hajiya tayi tare da riƙo hannayenta ta damƙe kaɗan, cikin magana me nuna zallannatsuwa tace "ki yi haƙuri da abinda ya faru jiya a gida, a gaskiyan magana su Lubabatunamatuƙar fushi da Insiyya, ba zan iya miki bayanin dalilin fushin ba, amma zance miki ki yi haƙuri
da duk wani abu da zaki ji ko ki gani daga gare su, na san a sannu koma ze wuce".... Murmushi ta saki tare da faɗin "ba komai Hajiya in sha Allah, suma iyayena ne, kuma dukɗiyatagari zata rungumi duk wani abu da iyayenta suka bijiro da shi matuƙar be saɓawa umurninAllahda Manzon tsira Muhammad (s,a,w) ba" ta idda naganan a sukunance, murmurshi Hajiya tasaki
tare da shafa kanta....
"Allah ya gafartawa Insiyya na san wannan duk daga gare ta ki ka ji" ta idda naganan tareda
shigar da ita jikinta, jinjina mata kai tayi ba tare da tace komai ba, ɗagota tayi a natse taredafaɗin "yau Sahabee ya koma UK, a can yake aiki, be cika zama a nan ba, yakan dai zo lokaci zuwalokaci, amma ina sa ran in ya dawo ze jima damu, kar ki ga bakya ganinshi" ta idda maganancikeda kulawa, murmushi ta saki tare da faɗin "Allah ya ba shi abinda ya je nema ya dawo da shi
lafiya" "amen, bari in kira Maude ta tattaro ma'aikatan gidan in gabatar miki da su" jinjinakai
tayi tare da faɗin "to"....
Tana shirin gitta Mama ta jiyo saukan muryanta a ɗan zafafe, "me ya kawo yarinyar nan? Banace kar in ƙara ganinta a gidan nan ba?" Ta idda maganan idanunta na yawo a saman fuskanHarira da ta juyo a zabure cike da tsoro da fargaba, jinjina kai tayi tare da faɗin "ban sanzatazoba ni ma Mama" tayi maganan murya na kyerma, "na dai faɗa miki bana son tarayyanku, tundaita ba ta gaji arziƙi ba, matar da ta inganta rayuwar ta take son butulcewa ina ta san kimadadarajan alheri, tunda har zata iya cutar da ita ba wanda ba zata iya cutarwa ba, dan haka ki jatazara sosai a tsakanin ku, dan duk wani abu da ta aikata ze iya shafan ki" jinjina kai tayi jiki amace ...
"Wallahi irinsu ke sa wasu mutanen ƙin temakon me ne man temako, ta ya zaka ɗakko mutundaga rana ka kai shi inuwa shi saboda butulu ne ya turaka ranan bayan yasan zafi da raɗaɗindaranar ke ɗauke da shi" "wallahi na hanata Mama" Harira tace a sanyaye, "to wanda yayi nisayanajin kira ne Harira? Ai sheɗan ya buga mata gangan tsiya dole ta fito tsakiyan duniya ta takarawan rashin mutumci, ke dai ki kiyaye tarayyan ku, wai ma kin faɗa mata halin da mahaifiyartake ciki kuwa?"...
"Tun ranar da ta faɗi na kirata na faɗa mata abinda ke faruwa, da Doctor ya sanar da abindayasameta shima na kira ta na sanar da ita, amma ba ta zo ba, yanzu ma da muka fita na ce zatatadubata ne tace "sauri take yi" "ƙyaleta ba ta da rabo ne a duniya, ita duniya dake jiran na ciki mabare ita da ta fi shekaru ashirin a cikinta" Mama tace cike da takaici, "Mama ina ganin zansanarda Safinat a school dan ta sanar da su abinda take ƙoƙarin aikata ma Insu" Harira tace cikeda
rauni, "kul raba kan ki da yarinyar nan, dan tunda ta iya aikata musu haka to ke abu me sauƙi neta aikata miki fiye da hakan, dan haka ki manta ma da batun" "Mama wallahi Insu kafatanintaabar tausayi ce, da heart problem aka haifeta, tun da ta taso iyayenta ke faɗi tashi akansamamata lafiya, kullum cikin shan magani take, su ba su gaji da siya ba ita ba ta gaji da shaba, maganin da take maganan ta canza Safinat tace mun da mugun tsada mahaifinta ya ke siyanmata, ba ma a samu a nan, garin, a ƙasan nan gaba ɗaya a SSB pharmacy ake samu can
Ɓadamayya, haka yake turawa har can a samo mata, sannan yanzu ta canza mata da wani daban" ta idda maganan idonta na tara ruwan hawaye, "akwai Allah Harira, ba ze barta ta cikaƙudirinta akan su ba, Allah ze dubi zuciyoyin iyayen su da ba su nufi ɗan kowa da sharri bayatemake ta, amma ke kar ki yunƙurin cewa kowa komai, dan in maganan ya fita ke za ta kawo, sannan ba musan wani mataki zata ɗauka a kan ki ba"... Sauke numfashi tayi tare da faɗin "shikenan Mama Allah ya karya ƙudirinta" "amen in shaAllahba zata cimma burinta ba" "in sha Allah" tace tare da shigewa cikin ɗaki.. . Bin su da ido Insu dake zaune kusa da Hajiya tayi cike da mamakin yawansu, banda zancenzuci
ba abinda take, "yanzu duk waƴan nan aiki suke a gidan? Allah me iko, to wani ayyuka suke?Kai
jama'a masu kuɗi suna abinda ransu ke so, banda san neman zance shi da ba zama yake bameyakai shi ɗaukan ƴan aiki haka?" Ire-iren wannan tambayoyi ta dinga jefawa kanta, ganin bawandayasan ta na yi bare ya bata amsa ta watsar da batun ta maida hankali ga Hajiya dake cewa"kukenan ko?" "Eh Hajiya se Lamunde, ta kira ta sanar ba zata samu shigowa ba saboda hatsari daɗanta yayi jiya" "subhanallahi da sauƙi dai ko?" Hajiya tace idonta akan Maude da tayi magana, "eh ta ce dai da sauƙi" "yakamata ku wakilta wasun ku suje su duba shi" "in sha Allah Hajiyazamuyi ƙoƙarin hakan"...
"Hakan yayi, Insiyyah wanann ita ce Maude shugaban ma'aikatan gida mata, matemakiyantacewacce yanzu muke magana akan ɗanta yayi hatsari, waƴan nan sune nasu aiki a cikin gidawandawani mu'amalla ze iya haɗa ki da su, kinga waƴan nan guda takwas ɗin a ɓangaren kitchensukeaiki, suke dafa duk wani abinci da za'a buƙata, wannan da ki ka gani Feita kenan shi ne shugaban
masu kula da gyaran side ɗin nan, sannan SSB ya yarda dashi sosai, ga sauran matemakanshi
nan a bayan shi, wannan ita ce" "Lawuza" Insu tace fuska yalwace da murmushi, murmushi Hajiyata saki tare da faɗin "haka ne Lawuza ita ke kula da duk wani abu da ya shafi matan SSB, itakuma wannan Lantai me kula da duk abinda ya shafi tsaftan kwanoni ga matemakanta nansuma, waƴan nan suke kula da flower's, waƴan nan gun-gun kuma sauran ɓangarorin suke tsaftacewa, ga masu wanki, ka masu guga, ga direbobi, kowa da ki ka gani anan da aikin shi" ta idda naganantare da kallon ta fuska yalwace da murmushi .... Murmushi ta saki tare da faɗin "na haɗu da wasu daga cikin su ai" tayi maganan tare da kallonMaude, ganin yanda tayi saurin sadda kai ya sata sakin murmurshi me faɗi, gyara zama Hajiyatayi tare da faɗin "tun jiya na sanarwa Maude ta faɗa muku mahimmacinta a wannan gida, jikacemafi soyuwa a gareni, ƴata da nake matuƙar so da alfahari ce ta haifeta, matsayin ɗiya takegashugaban ku, ko wannen ku ya san ta yanda ze mu'amalanceta, dole ne ko wannen ku ya
girmamata fiye da yanda za ku girmama duk wani dake wannan gidan, kar inji matsala dagagareku, dan ba zan ɗauki shashanci akan abinda ya shafeta ba" ta idda maganan idonta na yawoasaman fuskokin su, jinjina kai suka yi cike da gamsuwa, ba wanda be sha jinin jikin shi ba awajen, "kuje ke Lawuza gobe za ta tafi school ki tabbatar duk wani abu ya kammala kafin lokacinfitanta, zan saka a turo miki jadawalin lokutan zuwa" jinjina kai tayi a ladabce ta juya ta bi sauran, Maudea shirya mana lunch, da jikana zanyi" Hajiya tace tare da kallon ta, jinjina kai tayi da sauri tajuyata fice....
Tana fita kai tsaye tayi kitchen, gaya musu abinda za su girka tayi ta fice da sauri, kai tsayesideɗin su ta wuce, tana shiga ta tadda Lawuza da biyu daga cikin masu wanke-wanke, "Lawuzatashi
ki je ki haɗa musu babana an Mango juice su fara sha kafin a kammala abincin" da sauri tatashi
ta fice, kallon sauran tayi tare da faɗin "kun san abinda za ku yi ko?" jinjina mata kai suka yi sukamiƙe suka fice, se da ta tabbatar da fitan su sannan ta shige ɗakinta.... Da sallama a baki ta shiga main parlour, da gudu Umar yayi inda take tare da faɗin "Anty
Sa'adatu oyoyo" "oyoyo mekyau" tace tare da ɗaga shi sama, dariya ya ɓarke dashi cike dajindaɗi, murmushi Farisat dake zaune tana lunch ta saki tare da faɗin "har kin dawo?" "Eh wallahi" tacetare da ajiye Umar, "lallai saurayi zaki aura, kina dawowa ana cin lunch, zo zauna mu ci damabason ci ni ɗaya nake ba, Yasmin ta kwanta Sadam ya shiga school, Nafisat da su Sahabee basudawo ba, Hajiya ta ce fura za ta sha" ta idda maganan kaman za ta saki kuka.... Dariya ta saki tare da faɗin "aiko ba ki samu abokiyan ci ba, danni ma ba ci zan yanzu ba, gaUmarnan ya taya ki" "oh Sa'adatu ki temaka mana" tace tare da shagwaɓe fuska, dariya ta ƙyalƙyaceda shi tare da faɗin "ko zan ci se na watsa ruwa nayi sallah, kin ga wanda ki ka zuba ze yi sanyi"
"jeki kawai" tace tare da ɓata fuska, murmurshi ta saki tare da faɗin "dama zanje ai" tayi
maganan fuska yalwace da murmushi ta wuce ɗakinta...
"Sama ƙofan key tayi ta wuce ga wayanta kai tsaye ta ɗauka ta lalibi number ta danna kira, zamaa gefen gadonta tayi a hankali kamar me gudun wani yaji sautin zaman, ana ɗagawa tace"rankashidaɗe yau na samu tabbacin da ka ce in nemo kafin in faɗa maka, Hajiya Farisat da kantatazota sanar damu yarinyar ƴarta ne ta zo karatu a nan" "kin tabbata!" Yace cike da zaƙuwa, "natabbata ranka shidaɗe da akwai wani magana za ta faɗa, ita ma yarinyar ta sanar min da meyakawo ta jiya na faɗa maka" "shikenan, ki huta, zan neme ki" "to ranka shi daɗe godiya nakeAllahya ƙara arziƙi da wadata, Allah ya sa ka zarce" ɗiff ya katse kiran, dariya me cike da farinciki tasaki tare da ajiye wayan ta miƙe fice da sauri....
Jawo wayanta dake ringing tayi a natse ido cike da barci tare da karawa a kunni, "zo ki shigodani" taji saukan muryan Habiba a ka, da sauri ta miƙe ta bi wayan da ido, dan duk a zatontamafarki take, ganin da gaske ga kira na aiki ya sata sakin baki da ido akan wayan cike mamakindama tana da numberta, "kinji abinda na ce kuwa?" Ta jiyo sukan muryanta da ƙarfi, "eh" taceahankali tare da ajiye wayan a saman dirowan dake gefen gadonta ta kudu ta sauka a natsetaɗauveil ta fice, tana shiga parlor ta tadda Farisat na ta fama da abincin da ta zuba, "se ina?" Tacedakulawa, bakin gate" tace tare da sakin hamma...
"Baƙo?" Tace idonta akan ta, "Anty Habiba" tace a hankali tare da ficewa, bin ta tayi da idocikeda mamaki, jan kujeran da take kai tayi ta wuce ɗakin Babiya, da sallama ta shiga, murmushi
Babiya dake zaune hannu riƙe da Alƙur'an ta sakin mata tare da maida hankali ga Alƙur'anintaƙarishe ayan da ta faro ta rufe baki ɗauke da addu'a...
"Farisat lafiya kuwa?" Tace da kulawa "Anty Habiba ta kira ki ne?" Tace da kulawa, "a'a ta cetakira ne?" "A'a Yasmin dai ta je shigo da ita yanzu" "na ji wayan na ƙara ina karatu, wataƙilaitace, ɗakko mu gani" tace tare da nuna mata inda wayan yake, wucewa tayi ta ɗakko idonta akai, daalamun dubawa take, miƙa mata tayi tare da faɗin "aiko ta kira, kusan ten missed calls dai" "toina karatu a lokacin" Babiya tace tare da ajiyewa a gefe, miƙa hannu tayi ta ɗau Alƙur'anindakeriƙe a hannun Babiya tare da maidashi mazaunin shi....
"Turo ƙofan Yasmin tayi ido cike da barci tare da faɗin "Hajiya Anty Habiba ta zo" miƙewa tayi
tare da faɗin "to kema yakamata ki tashi daga barcin nan haka" "to bari in wanko ido" tacetareda wuce wa....
"Habi ke ce a garin yau?" Hajiya da ta shiga parlorn Farisat dafe a bayanta tace tare da nemanwaje ta zauna, "ni ne Hajiya, tun daren jiya Jummai ta kira ni akan tana ganin Zuwaira ta faranaƙuda shine na ce bari in zo" "naƙuda! Wata bakwai ne ina cikin ke shirin cikawa?" Hajiyataceda mamaki, "to haka ne bakwai ne a na takwas" tace jiki a sanyaye, "ikon Allah shine ita kumatakasa faɗa mana mu dake kusa da ita ta kira ki har can ta faɗa miki?" Tace cike da mamaki, "tace
ta faɗawa Lurwanu sunyi magana da shi tun jiyan" "Allah me yanda ya so, to ni dai banga
Lurwanu a gidan nan ba, be kuma kira kowa ba, ita ma banda wawta kalan na ta menene nasanarwa Lurwanu bayan tana da number na?" Hajiya tace da alamun rashin jin daɗi a muryanta, "ta ce ta kira ba ki ɗaga ba, ba kuma ta da number kowa a cikin yaran, gashi wayan ba na taba, na Baffa ne ta ci arziƙi" "to ai ta kyauta, yanzu yarinyar na ina?"...
"Suna gida" "yin me?" Farsiat tace da mamaki, "to ke ma kinga hakan be dace ba, bare ni" "ai
yanzu ba zama zamu yi ba, Farisat kira Rufa'i ya zo mu je mu kaita asibiti, ace yarinya na kangwiwa tun jiya saboda tare take da shashashu a kasa samun me kaita asibiti, kullummalamankafiya batu suke akan a daina barin yara na dogon naƙuda a gida, a dinka gaggawan kai sugamasa na... Hajiya tace tare da miƙewa ta wuce ɗaki, kallon Habiba Farisat tayi tare da faɗin "kar ki damu, insha Allah zata samu sauƙi" tana kai nan ta shige ɗakinta, bin su da ido kawai tayi da mamaki, dantana sauka gidan Jummai tayi, ganin halin da Zuwaira ke ciki ya ɗaga mata hankali, tambayanJummai tayi meyasa ba su kaita asibiti ba? Jin abinda tace yasata mata uzuri dan tasanJummai
ba ta da shi, duk sun fita abun hannu, ba ta nemi Gude ko Suwaiba ba dan tasan ba abindazasuiya mata, Ali tayi niyyan kira Jummai ta sanar da ita halin da yake ciki, Balarabe ba ya da motahaka Lurwanu, dalilin da yasa ba ta nemesu ba kenan, tun a can gidan take gwada number Hajiyadan ta nemi arziƙin mota, amma ba ta ɗaga ba, kiran Balarabe akan in yana gida ya fito gatezatacan ya shiga da ita tayi, jin yana wajen aiki yasata neman ya turo nata number ɗaya daga cikinyaran.... ba jimawa ya tura mata na Yasmin, sauke numfashi tayi tare da kallon Farisat da ta fito cikinshiga na mutumci hannu riƙe da waya, "muje Anty Habiba yana waje" tace tare da kallonta, miƙewa tayi jiki a sanyaye, "ya fito ko?" Babiya da ta fito a shirye tace tare da kallon Farisat "ehyana waje" tace tare da ƙoƙarin wucewa, "ina zaku?" Yasmin tace tare da bin su da ido, "Zuwairaƴar uwanku ce ba lafiya" Babiya tace tare da kallon Sa'adatu da ta fito a amintaccen shiga, "a'aSa'adatu kin dawo dama?" Tace fuska yalwace da murmushi, "subhanallahi ku jira ni" Yasmin
tace tare da komawa ɗakinta da sauri, "eh Hajiya na dawo ba jimawa, Allah ya bata lafiya" tayi
maganan tare da wuce wa daining area.... Da mamaki Farisat ta kalleta tare da faɗin "ba zaki ba ne?" Girgiza kai tayi tare da faɗin"zanzauna da Umar" "haka ne" tace tare da sauke numfashin samun sassauci, "ina Mari kinga kiɗimayasa ba mu faɗa mata ba" Babiya tace tare da wuce wa kitchen, fitowa Yasmin tayi suka
ɗunguma suka fice a hanzarce.....
Suna idda ficewa ta ja tsaki tare da faɗin "in muku uban me? Ni na sa tayi cikin kenan" tayi
maganan tare da jan plate ta fara zuba wa kanta abinci, murmushi Baba Mari dake jiyo komai tasaki tare da girgiza kai ta yi ɗakinta, fitowa tayi sanye da hijab ta fice da sauri... Murmushi Hajiya ta saki tare da shigewa motan da drivernta ya buɗe mata, "ki kula da kanki
sosai, na zaɓa miki driver ina da yaƙinin za ki ji daɗin tafiya da shi" murmushi Insu dake bintadaido ta saki tare da faɗin "nagode sosai Hajiya" jinjina mata kai tayi fuska faɗaɗe da murmushi, rufe mata ƙofan tayi ta ja baya kaɗan dan ba su hanyar wuce wa, suna tsaye a wajen sukaficedaga gate ɗin dake sada me shigowa da filin cikin gida, juyawa tayi a natse, ganin Lawuzatsayeya sata faɗin "body guard ki ka zama ne?" Murmushi ta saki tare da girgiza kai, "jeki hidimanki, zan kwanta yanzu" Jinjina mata kai tayi ta wuce ɓangaren su ita kuma ta shige ciki....
Comments fans 🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Fifteen
Tsatstsaye suke a waiting parlor na general hospital, ba wacce ta samu ƙwarin gwiwanzama, tunda suka kawo ta aka shige da ita labour room ba wanda ya fito bare su san halin da ake ciki....
"Oh Farisat wai ba'a nan Salman ke aiki ba?" Babiya tace tare da kallon Farisat, girgiza kai tayi
tare da faɗin "ba'a hospital ɗin nan yake aiki ba" "be ma da ƙwarewa a wannan fannin shi likitanƙwaƙwalwa ne fa Hajiya" Yasmin tace tare da kallon Babiya, "bari inje in sanarwa Anty Gudetanasashin maza, na san ba ta san muna nan ba" Jummai tace tare da ficewa....
"Ina zaki a wannan lokacin? Ko kin manta lokacin tashin ki ne?" Maude tace tare da kallonLawuza da ta canza kaya zuwa kayan da ta zo da shi, girgiza kai tayi tare da faɗin "Baba Maudezan ɗakko Iman ne a makaranta, Babanta ba ze samu daman ɗakkota ba" tayi maganancikedamagiya...
"Ke kanan kullum cikin ba da uzuri, anya Lawuza kin shirya ma aikin nan kuwa yanzu?" "DanAllah Baba Maude amun afwa, ina ɗakkota zan ajiyeta a gida in dawo, ita ma tace zata kwantakafin anjima" "shikenan ki hanzarta, in dai ta nemeki ba na da kalaman kare ki" jinjina kai tayi
tare da faɗin "nagode Baba Maude" komai Maude ba ta ce mata ba se wuce wa da tayi.... Da sauri ta fice tayi inda motocin ma'aikatan gidan suke, "Ilu muje school ɗin su Iman" tacetareda buɗe motan ta shige, tasowa wanda ta kira yayi da sauri ya shige suka fice gate ɗin da sauri....
"Shine me Jummai?" Gude dake harhaɗa kaya a waje ɗaya saboda takardan sallama da akakawomusu ba jimawa tace tare da tsayawa cak ta kafe Jummai da ido, "haba Anty Gude, Zuwairafanace miki, sannan haihuwa za tayi fa" tsaki taja tare da faɗin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 109