ta amsa, "kin kyauta Nafisat, wallahi
ban zace ki da haka ba" zare ido Nafisat tayi tare da miƙewa da sauri ta nufi wajen ta duƙayandaza ta iya ganinta....
"Mairahn Mommy muna baki abinci ko?" Tace idonta akan ta tare da sakin mata murmushi "eh" tace tare da sakin murmushi, "to kin ji ko?" Tace tare da kallon Farisat, "dalla rufe min baki, ai bazata taɓa muku ƙarya ba, ba kwa mata wanka bakwa bata abinci, dubi duk yanda ta rametayi
baƙi, akwai Allah" ta idda magananta cike da gaskiyanta....
"Yanzu maganan ta da komai eh ne zaki ɗauka? Ki na ji fa aka ce ana mata tace eh" Insu tacetareda sakin mata murmushi, "ai maganan farko shi ne abin ɗauka dan ba ta yanda za ta mukuƙarya" "to me ƴa" tace a natse, "ku dai sa Allah a ranku, ba dai kya mata tsawan nan ko?" Tacecike da gargaɗi, "a'a bana yi" tace cike da murmushi, "ta na yi sister Farisat, yanzu ma se datamaketa" Asma tace da ƙarfi, zare ido Insu tayi tare da mata kallon kin kasheni....
"Insu duka kuma! Yanzu ba zaki ji tsoron mahaliccinki ki tausaya mata ba, kin san ba isasshenlafiya gareta kamar ko wani yaro ba, shine zaki dinga dukanta" ta idda maganan murya narawaalamun gab take ta sakin kuka, kallon Insu suka yi da mamaki, kauda kai tayi tare da faɗin"toza'a kiyaye, "yayi miki kyau" tace cike da rashin jin daɗin, "ina Hajiya Nafisatu?" Tace a natse, yanzu suka fita, ni ma ban jima da shigowa ba" tace a natse, "oh ya jikin naki?" "Wallahi nawarware, tace dai in rage motsi me ƙarfi ne, amma yanzu ba komai" "please ki kiyaye ina Hajiyataje da safe haka?" Ta idda magana tare da jefa mata tambaya....
"Yanzu ne safen ko! Abinda 12 ta kusa" tace tare da sakin hamma, "to mutumin na kusa kenan" tace tare da sakin dariya, "wallahi ke dai bari tun ɗazu nake jin zuwanshi, sun tafi asibiti ne" damamaki tace "asibiti! Yin me!" "Sudais ne ba lafiya" "oh Yaa Rahman, ƙafan dai!" Tace cikedatausayawa, "wallahi shi fa, bana ya mai me kankat, wai cirewa za'ayi" ta idda maganan taredakare hamma, "Yaa subhanallah, cirewa kuma!" "Eh da wannan ruwan azaban da yake sha inƙafarta motsa ai gunda a cire wataƙila ya samu sassauci, kuma a yanda Hajiya tace sunce in dai ba'acire ba zata harbi ɗayan, kinga me aka yi kenan, ai da ayi ba wan ba ƙani gunda ayi rashinguda, ya rage zafi in yana ganin gudan, girban abinda ya shuka yake, lokacin da yake rashin jinwayebemai magana akan ya bari ba? Har daina kula iyayenmu maza yayi dan suna faɗa mai gaskiya, iyayenshi kuma suka mara mai baya, yanzu wa gari ya waya? Ba ga su can suna ife-ifa ba, damaza su yi su kaɗai ne da ma wani matsala, amma sun tashi hankalin baiwar Allah se kin ga yandata bar gidan nan a kiɗime" ta idda maganan cike da takaici....
Sauke numfashi Insu tayi tare da faɗin "meyasa baki bi su ba?" "Inje in yi me!" Tace da mamaki asaman fuskanta "haba Farisat kar haushi da takaici ya hanaki sauke haƙƙin mahaliccinki mana, shi fa yace mu yi zumuncin nan, wannan bawan Allahn ɗan uwanki ne, dolenki ne" "a'a wallahi badolena ba ne, dolena uwarshi ce, shi ko in na ga dama ne inyi zumuncin da shi in na ga haguinƙiyi" tace hankali kwance, girgiza mata kai tayi tare da amsan wayan a hannun Mairah yandazata fi ganinta da kyau tare da faɗin "wallahi dolenki ne, ɗan uwanki ne, yafi zama dolenki akanyaranki, ɗan uwanki yana cikin wannan halin ki miƙe ƙafa haka, be kamata ba, a kullumAntyumurninta akanmu shine mu riƙe zumunci mu ƙarfafashi wa kowa, kowa na mu ne, ko mutumyace shi ba na mu ba ne, mu nuna mai shi na mu ne, gaba ze fahimta, ko kin manta da kalamantane?" Ta idda maganan cike da muryan rarrashi....
"Ban manta ba Insu, amma ki ga fa abinda mahaifiyarshi ta mana, nayi aure ba ta zo ba, mukahaihu ba ta zo ba, ko albarkacin rasa yaron da nayi ya ci a ce ta zo mun jaje, amma ta ƙi zuwa" taidda maganan cike da ɗin bin takaici, murmurshi Insu ta saki tare da faɗin "uwace ai, tanadadaman miki fiye da hakan kuma dole ki bita ba tare da ƙulli ko kaɗan ba, ki zama ɗiya ta gari mebiyayya Farisat, in ta ƙi zuwa bikin ki da haihuwa, ba gashi ta zo bikin Abar ƙaunarmu Yasminba, da ita aka rakata har ɗakinta wannan ma abin a gode mata ne" jinjina kai tayi tare da faɗin"shikenan zan kira Habibu yanzu ya zo ya kai ni na duba shi, se dai ba zan daɗe ba" "hakanmamuke da godiya, ai ke ce wakiliyan mu anan, tunda duk munyi nisa, Yasmin kuma be kamatatadinga fita yanzu ba da na kirata na ce taje ke ki huta" "a'a barta se ta yi wata guda gaskiya, shimaƁadamayyan dan ba mu san da tafiyanta ba ne wallahi da ba zata ba" tace tare da sakinhamma, "to ki dai rintsa kaɗan kafin ki tafi, ko kuma ki yi barcin in su Uncle sun dawo da ga school sekujetare suma su gaidashi da jikin tunda ba su da islamiyya yau" "to shikenan" tace tare da katsekiran.... Murmushi Hajiya ta sakin mata cike da jinjina sanin yakamatan ta, sauke Mairah daga jikintatayi
tare da miƙa mata wayan cike da son mata dabara tace "mammy na magana je ki yi maganadaita, wuce wa tayi da sauri Nafisat ta miƙe ta dafa mata baya, "karfa ta yarda wayan" A'ishataceaɗan tsorace, "ba zata yarda ba, ba ta yarda waya" Nafisat tace tare da sakin murmushi ta ɗagatata rungume ta zauna ta zaunar da ita a jiki....
"Yanzu se ta fita ba tare da ta nemi izinin mijinta ba!" Asma tace da mamaki, idon ta akanInsu, "waye?" Insu da ba ta gane inda maganan ya dosa ba tace idon ta ana ta, "sister Farisat" taceanatse, murmushi ta saki tare da faɗin "ai inda yakamata ne, kuma tunda ki ka ji haka bayadamatsala in taje ne" "taɓ ɗin jam" tace cike da mamaki, "Me ya faru?" Tace tare da kallonta, "bakomai" tace a hankali, "ah-ah da komai mana, ita ta saba ko ina zata se ta kira Abdullaɗif tatambayeshi se in ya yarda zata in be yarda ba kuma ta haƙura, shine take ganin abun a bauɗe" Nabila tace cike da takaicin Asman...
Da mamaki Insu ta kalleta tare da faɗin "ki na nufin wai a yanzu haka se kin tambayeshi ki kezuwa waje!" "To ya zanyi? Mazan ne gani suke in ba ka bi umurnin su a gidanku ba ko sunkai kagidansu ba za ka bi ba" tace kaman zata saki kuka, "sannu" Insu tace cike da mamaki, "wallahi beyarda inje ko ina se na faɗa mai, in ko na je be sani na da ga baya ya sani se munyi faɗa" takumacewa a sanyaye, "Allah ya baki ladan niyya, ban iya wannan tambaye-tambayen ba ma koagidanmu bare a gidan miji, ai bawan Allah ɗau amana ka bani ba zanci ba, da ilimi na da saninYakamata na ba zan yi wasa da igiyoyin da ke kaina ba, duk da wasu matan suke ɓata wasu, amma gaskiya ya tsawwala da yawa, kuma ke ki ka ba shi wannan daman, yanzu dai in Allahyasaki ka shige mu cire ran ganin ki a inda muke nan kusa dan yanda ake wannan ikon tun yanzunasan yana mallakan ki kuma shikenan, arziƙi ze ci uban na da" ta idda magana tare da kallontacike da mamakinta.... Dariya Fadila da Nabila suka saki su Kausar na taya su da murmushi, "haba wallahi ba ze rabani
da iyayena ba, wannan ma gan-ganci ne" tace cike da tabbaci, "a'a bakya da tabbacin hakandaina tabbatar mana malama, yanda ya dama haka zaki shanye, dama haka auren yake ammaagaskiya ke kin bada dama da yawa" ta yi magana cike da gaskiyanta, "yanzu ke kina nufininzaki
fita wani waje ba zaki tambayi Uncle SSB ba kenan!" Tace idonta akan ta, guntun murmushi tasaki tare da faɗin "meze hanani tambaya? Kawai dai yanda ki ke tambayar shi a gidankunebekamata ba, shi ze ba shi lasisin yi miki komai, iyayenki ke da wannan hakkin ba shi ba, shi seyamallake ki wannan nauyin ze hau kan shi, kinga kin nuna mai ya fi su ƙarfin faɗa ki ji tunkantafiyar ku ta yi nisa, shine abinda ya bani mamaki, amma a gidan shi ki tambayeshi kafinki fitashine dai-dai, ita kanta Farisat da ki ka ji nace taje kai tsaye mijinta ya amince mata duk gurindayakamata in tafiya ya tashi taje ya lamunce mata, saboda ba ko da yaushe in abun ujiya yatasoza ta iya samun shi a waya ba, kuma wajen da na roƙeta zuwa ya dace ne, in ba haka ba ai setatambayeshi ita ma dole, amma ke ma dai ki zama mace" ta idda maganan cike da gajiya dazance....
"Rabu da ita Insu ba zata gane ba, ba tun yau muke nuna mata rashin dacewan hakan ba ammaba ta gani, tunda har an zo gangara lafiya ai ba amfanin maganan ma" Fadila tace cike da son
barin maganan, murmushi Insu ta saki tare da jinjina mata kai, "oyoyo Anty Lailah" Nafisat tacecike da farin ciki tare da miƙewa zumbur ta ajiye Mairah ta nufesu cike da farin cikin ganinsutarungumesu....
"Sannun ku da zuwa" Hajiya tace musu fuska yalwace da farin cikin ganinsu, murmushi LailahdaKhadijatu suka saki tare da amsawa cike da girmamawa tare da janye Nafisat daga jikinsusukariƙe mata hannu, "ya ƙafan Hajiya?" Lailah tace tare da kallonta cike da kulawa, "ah ƙafa yayi
sauƙi Lailah, ana ta gashi" "ma sha Allah Allah ya ƙara lafiya" suka ce tare da neman wajenzamasuka zauna, "yau dai muka ce bari mu zo mu ga yanayin jikkunan na ku" Lailah tace cike dagirmamawa fuska yalwace da murmushi, "ma sha Allah lallai kun kyauta Allah ya saka daalheri
ya sa muku a mizani" Hajiya tace cike da farin ciki, "amen" suka ce cike da jin daɗi, nan sukashigagaggaisawa da su A'isha dake ta sakin musu murmushi, murmushi Insu ta saki tare da faɗin"jiyana kira wayanki Anty Khadijatu be wuce ba" "network ne wallahi, kwanan nan haka ake tacewaana kirana be wuce wa" tace cike da rashin jin daɗi.... Murmushi ta saki tare da faɗin "na ɗauka kin yi kuɗi kin daina ɗaukan wayan talakawa ne" taidda maganan tare da sakin ƙaramar dariya, "kin ci gidanku Insu, kin taɓa ganin uwar da tayi kuɗi
ta yada ɗiyoyinta?" Tayi maganan tare da watsa mata daƙuwa, girgiza kai tayi tare da rufebaki
da tafin hannunta, "ai se da muka yi gulmanki da Anty Salwa, tace ita ma tayi ta kiran ki bewucewa" "dama na san ai se kunyi" tace tare da sakin murmushi, "wallahi mun sha hira jiya, tacezatazo gobe in Allah ya kai mu" "eh haka tace ma Anty Lailah zata zo, tana son haɗuwa da YayadaYaya Hassan ne, na ce ta haƙura tunda wan can satin ta zo kin san uwar mijin nan na ta dasakaido, to taƙi ji tace se ta zo, su kuma Yaya se gata ma sannan za su zo, har maganan yara namataamma tayi fin firin fir, ta murje ido" tayi maganan cike da damuwa.... Dariya Insu ta saki tare da faɗin "ta ƙuna ne, ku ƙaleta wataƙila da abinda take son yi kafinzuwanna su ne, da ina ce ku da kan ku takaici ku ke da rashin san zuwan na ta, ta gaji da biye musuneta fahimci gaskiya, in dai uncle Yusuf ya barta ta zo kawai, in Kakan ba zata iya riƙe su ba su
zauna a gidan da yarinyar aikinta mana ba shikenan ba" "ke ma so ki ke ki zama Salwa da Farisatwajen rashin hankali yanzu ko?" Lailah tace tare da kallon ta, dariya ta saki tare da faɗin"kutashi mu ƙarisa dining ku sha ruwa" "a'a kawo shi nan duk a ƙoshe muke" "to Hajiya kinji wai
abincin gidanki ba daɗi" Insu tace tare da kallon Hajiya, murmushi ta saki tare da faɗin "nagidanki dai ƴar nema, ai ta yaki zama muke" "oh Allah ni fa so nayi ki buɗe musu ido" tacekamarzata saki kuka, "a'a za su ci ai suma sun san ba zan yarda da gan-gancin nan ba" tace tare damiƙewa a natse ta nufi ɗakinta, saurin tashi Yasmin tayi ta dafa mata baya, mimmiƙewa sukayi adabarance suka bar wajen.... Murmushi Khadijatu ta saki tare da kallon ta cike da kulawa tace "babu wani matsalan ko?" Girgiza mata kai tayi a natse cike da jin daɗin kulawanta "ta wajen Yaya Sahabee fa akwai wani
cigaba ne!" Tace cike da fargaban jin amsa, numfashi ta sauke a hankali tare da faɗin "har yanzudai" "Yaa subhanallah, Allah ka tashi bawanka cikin aminci" tace a hankali cike da tausayinshi, "amen" suka ce bakuna a haɗe tare da sakin mata murmushi, "zamu je ku ganshi ne?" Tacetareda kallon shi, "ana zuwa ne?" Lailah tace cike da mamaki....
"Eh a ƙofa ake tsayawa amma" tace fuska ɗauke da murmushi, kallon Mairah tayi cike da
tausayawa tare da faɗin "Allah sarki ba abinda ta sani" murmushi Nafisat ta saki tare da faɗin"ina su Amatullah?" "Tana can gidansu, jiya Abbansu yaje gidan ya haɗamu ta waya" "tayi wayane?" Tace a zumuɗe, "a'a na Kakan ne" "oh Allah ki bani number ma lallaɓa a tanan kafintayi nata" tace tare da kallon ta, "ai ina ganin makarantar da ki ka samu ze neman mata" zare idotayi azumuɗe tare da faɗin "da gaske Anty Lailah!" "To jiya dai ya fara maganan, kin san shi be maidahankali wajen bayanin da ze gamsar, amma dai yace yana ganin can za tayi" "ma sha Allah! Allahya yarda" tace cike da fata...
"Amin ba kun gan ku a haɗe ba ku ce zaku ƙi maida hankali, wallahi kuna wasa a farkonzango
za'a raba muku makaranta" Khadijatu tacr cike da tabbaci, girgiza kai Nafisat tayi tare da faɗin"ba wannan maganan in sha Allah Anty Khadijatu, zamu ba da mamaki" "Allah ya sa" tacetaredakauda kai....
"Amshi nan riƙe wannan" Lailah tace tare da miƙa ma Insu ledan dake cike da robobin danbunnama, "oh Allah my lovely Anty Lailah" tace tare da amsa cike da farin ciki, zaro roba ɗayatayi tabuɗe ta zari tissue ta ɗibi kaɗan takai baki, lumshe ido tayi tare da faɗin "wow! Gaskiya wannanna musamman ne" dariya suka saki tare da bin ta da ido, da sauri Mairah ta ƙarisa kusa daitatare da miƙa mata wayan hannunta, amsa tayi ta ajiye a gefe tare da cigaba da cin danbunanatse, kwaɓe fuska tayi tare da kallon Nafisat, murmushi ta saki tare da faɗin "Ammi zataci nefa"...
"Me ɗin!" Tace da mamaki, "danbun" tace tare da sakin dariya, "dama ta iya ci ne!" Tace damamaki, "to ai se kin bata zamu sani" Khadijatu tace tare da ɗiban kaɗan ta kai mata baki, miƙamata hannu tayi alamun ta ɗauketa, dariya suka saki tare da bin yanda take mamulan bakindaido, "lallai Mairah ashe ke ke ƙarewa Mommy na ta" Nafisat tace fuska cike da murmushi, "kebaki ga yanda ta amince da Khadijatu kai tsaye babu wani musu ba" Lailah tace fuska yalwacedamurmushi....
"Duniya ce ta samu" Khadijatu tace tare da ɗiban wani ta kai mata baki, "ina Babana?" Lailahtacetare da kallon Insu, "yana ɗakin shi yana muraji'a" tace hankalinta akan danbun gabanta, "inYayaya zo za su wuce tare ko?" Tace idonta akanta, "da wuya" tace a natse, "yawwa please a barshi
anan, na san in kin mai magana ze amince" Khadijatu tace cike da fata, "zamu gani Allahyasayayarda" tace a natse baki cike da danbun, janye roban tayi da sauri ganin se hambaɗa ma Mairahsuke ita kuma tana ta hambaɗa, "kai Insu ga fa sunan da yawa" Khadijatu tace tare da kallonta....
"Ya isheta haka Anty Khadijatu, kar ya burgar mata da ciki, tunda be burgar miki ba ita mabazeburgar mata ba, dan gado tayi, bani abu nan" tace tare da amsa ta cigaba da bata, "oh Allah!" tace da mamaki tare da bin yanda take da hambaɗa mata da ido, murmushi suka saki na suidonakan Mairah dake ta cin danbun hankali kwance....
Se da ta tabbatar babu sauran ko burbuɗe a roban tace ma Nafisat ta ɗauketa ta wanke matajiki, saboda ɓata jikinta da tayi, ba musu ta ɗauketa suka nufi ɗakinta, miƙewa suka yi suka nufi ɗakinda SSB yake, cike da jimami suka baro wajen, dan ganin babu wani canji da ya samu da ganindasuka mai na farko "wallahi tun wan can ganin da na mai nake mafarkin shi" Lailah tace cikedadamuwa, "Allah dai ya tashi kafaɗunshi" Khadijatu tace da damuwa, murmushi Insu ta saki tareda kallon su, "ku tashi muje please ku taɓa ko kaɗanne ba daɗi ku ƙi cin wani abu" "kin dai matsane Insu amma wallahi a ƙoshe muke, kin yi magana da Yasmin?" Lailah tace tare da miƙewa, miƙewa tayi tare da faɗin "kwana biyu da suka wuce, amma jiya nayi magana da uncle Shureimakan su je hospital su duba jikin Baban Sa'adatu shi da Yaya Sadam da Salman" "subhanallahi
jikin ya ƙara motsawa ne!" Tace cike da alhini, "ai tun lokacin bikin Yasmin be koma dai-dai ba, jiya Anty Iƙilima ta kira ni duk a rikice ta sanar mun ta ɗauka ma ina Bertuwa ne, na dai batahaƙuri akan bana Bertuwa shine na ce su suje su wakilce mu" "kin kyauta, Allah ya ba shi lafiya, dama su je har da matayensu ai" tace cike da tausayawa....
"To wataƙila nan gaba, amma Yaya Salman ya tabbatar mun da yau za su duba shi" tayi maganantare da jan mata kujera, zama tayi tare da faɗin "Allah dai ya ba su lafiya gaba ɗayansu" "amen, oh kinga ma Farisat zata je hospital ɗin ai da na faɗa mata ta je ɓangaren da yake ta dubashi" tace cike da ganin hakan shine dai-dai, "to ita kuma lafiya?" "Eh Yaya Sudais ne ƙafarshi tamotsa" "oh shima, Yaa Allah" suka ce baki a haɗe, "wallahi ance se an yanke ƙafan" "subhanallahi, shima fa wannan yaron ya ga jarabawa" Lailah tace da damuwa, "wallahi suna can hospital"
"Allah yasa ayi lafiya" suka ce cike da jajintawa, "amen" tace tare da fara zuba musu abinci anatse....
Suna kammalawa suka tattaro suka dawo parlor, nan suka buɗe babukan hira, biyu na bugawasuka tashi suka nufi ɗakin Nafisat dan gabatar da sallah, suna idarwa suka kikkimtsa dankomawa gida, har dakin Hajiya suka shiga dan sallamarta, "ba dai tun yanzu za ku tafi ba!" Taceda mamaki, murmushi suka saki ba tare da sun ce mata komai ba, "ai da kun bari rana tayi sanyi, zuwa la'asar se ku koma" "mu ma za mu so hakan Hajiya, se dai yara na hanyar dawowa dagamakaranta" Lailah tace a girmame, "ah lallai kun fini gaskiya, to Allah ya ba ku ladan da yakebawa mazumunta, na ji matuƙar farin ciki da ganinku" murmushi suka saki cike da jin daɗi sukamiƙe, "Insiyyah kin faɗa musu maganan sha'anin Asma ko?" Hajiya tace tare da kallon Insu, "ehna faɗa musu, gobe ma mother's day" ta idda maganan tare da kallon su, ba abinda suka cesemurmushi ta suka saki...
"Lailah yaranki nawa ne kuwa?" A'isha dake ta bin su da ido fuska yalwace da murmushi taceidonta akan Lailah da ta saki murmushi, "biyar ne" tace a natse, "ma sha Allah Khadijatufa?" Taƙara jefa tambayan idonta akan su, "yawan yaranta ɗaya da Anty Amina su takwas ne" Lailahtace tare da sakin murmushi, "ikon Allah, kuma kin rigata aure ko?" Tace da mamaki, girgizakai
tayi murmushi be bar saman fuskanta ba tare da faɗin "rana guda ne aka yi, se dai ita ta rigani
haihuwa, ana biyu muka jera" "ma sha Allah Allah ya albarkace su" suka ce fuskoki faɗaɗedamurmushi, "amen" suka ce a natse suka tashi suka fice tare da rakiyan su.... Suna shiga mota Insu ta ɗan shigar da kanta kaɗan tare da faɗin "amma zaku zo mother's daygoben ko?" "Da wuya Insu dama ba mu riga mun zo ba ne muka ji maganan da se mu tsahirtasegoben mu fito gaba ɗaya, amma mun zo yau gobe kuma mu dawo" Lailah tace tare da kallonta, "yakamata ku je wajen, ba se mun zo tanan ba, ku wuce event's centern kawai kai tsaye, kumasun ce se four ma za a fara, kunga ko five ne se ku koma kun dai je sun ganku" ta idda maganancike da ganin hakan shine dai-dai, "shikenan Allah ya kai mu, Babana yaushe zaka zo munkwanabiyu?" Khadijatu tace tare da sakin ma Sa'eed da be daɗe da isowa wajen ba murmushi, "inshaAllah zan zo" yace a natse, "Allah ya yarda" tace cike da ƙauna, "Nafisat ke ba zan tambayeki ba, in dai na gaji da zuba ido zan zo da kaina in cicciɓeki" tace tare da sakin murmushi, murmushi tasaki tare da jinjina mata kai, kallon Mairah dake hannun Nafisat tayi tare da faɗin "ita wannaninda danbu ina ganin zamu shekara ma tare" dariya suka saki cike da nishaɗi, ja baya Insutayi tareda sakin musu murmushi, ƙara sallaman juna suka yi driver ya ja su suka ɗau hanya, ba sukomaciki ba se da suka ɓacewa ganin su....
"Farisat!" Suwaiba dake zaune kusa da Jummai tace tare da bin Farisat da ta shigo ita da
Sahabee da Umar da ido cike da mamaki, murmushi ta sakin mata tare da ƙarisawa inda suke, tashi tayi ta ba ta waje tare da faɗin "zauna ai ban zata zaki zo ba, Hajiya tace bakyajin daɗi tundaku ka dawo daga Ɓadamayya, ina ta son zuwa duba ki Allah be amince ba, dan ni ma kwanakinnan jikin yaƙi daɗi sam" "subhanallahi Allah ya ƙara lafiya" tace tare da gaida Jummai daketasakin musu murmushi... Gaidasu su Sahabee suka yi cike da mutumtawa, "Sahabee kana jin Sa'eed kuwa?" Jummai tacetare da sakin mai murmushi, murmushi ya saki tare da jinjina mata kai, "ai na ce ma Hajiyabawanda aka ma wannan giɓin se Sahabee, sune kullum a tare kamar Hassan da Hussaini, inkingaguda to zaki ga guda tafe a baya" tayi maganan fuska faɗaɗe da murmushi, murmushi Farisat tasaki tare da faɗin "aikuwa yana can yana shan na Ɓadamayya, ina Hajiyan?" "Suna can gefenɗakin aikin ita da Anty Gude da sauran yaran" "to Allah yasa ayi a sa'a, Yaya be iso ba ne?" "Yaiso, ai gaba ɗayan su ma sun iso, suna ta can baya tare da Daddyn Sudais ɗin" Suwaiba ta kumacewatare da kallon ta, jinjina mata kai tayi tare da faɗin "bari mu ƙarisa can ɗin" ko kafin su kai gabata amsa Salman da Shureim da Sadam sun shigo a natse bakuna ɗauke da sallama.... Da mamaki ta bi su da ido, "sannun ku da zuwa" Suwaiba tace cike da farin cikin ganinsutaredanufar inda kujeru suke, bin ta Sahabee da Umar suka yi dan taya ta, "waya faɗa muku!" Farisat
tace tare da kallon su, murmushi Shureim ya saki tare da ma Suwaiba da ta ajiye mai kujeranroba godiya ya amsa, shafa kan Umar da ya miƙa mai na hannun shi Salman yayi cike da jindaɗi
tare da faɗin "Insu ce ta kira mu yanzu muna gab da ficewa ta sanar mana, shine muka juyo"
"dama kun zo hospital ɗin ne!" Tace tare da kallon su, "oh na mance ban faɗa miki ba, jiya akakwantar da Babansu Sa'adatu, Insu ta kira ta nemi alfarman muje mu gaidashi da jiki, na ɗaukama kunyi maganan" girgiza kai tayi tare da faɗin "ina ga ta sha'afa ne, ko ɗazu munyi wayadaita, ya jikin na shi?" "Tabbas se dai sha'afa Insu ba dai son raya zumunci ba" Jummai tace cikedaalfahari da ita....
"To se dai mu ce Alhamdulillah, dan gaskiya jikin nan na shi ba za'a ce komai ba, Allah ne dai meyi, muna roƙan mai samun lafiya" yace cike da tuna halin da suka tadda shi, "subhanallah, Yayaya sani kuwa?" Tace cike da damuwa, "eh ita Yayar nan na su tace ya je jiya ya duba shi" "ohAllah, Allah ya ba shi lafiya" tace cike da jimantawa, "to ita ɗiyar tashi ta sani kuwa?" Suwaiba tacetareda kallon su....
"Daƙyar dan ba ko alamunta a wajen" Sadam dake daƙilar waya yace tare da ɗago kai ya kalleta, "kai wannan ɗiya anyi mara sa'a a duniya, ubanta na wannan mawuyacin halin ta kasa zuwadubashi" Jummai tace cike da zallan mamaki, murmushi Shureim ya saki tare da faɗin "to Anty ai keki
ke ganin mata hakan, ita fa gan-gan sheɗan ya gama buɗe mata kunni"
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 70 Chapter of 109