Share this page
yalalubo numberta ya danna kira ya sa a amsa kuwwa ya ajiye a gaban shi.... Suna shigowa anguwan suka fara danna horn, da sauri securityn gidan suka taso suka wangalegate ɗin, a guje suka tura hancinan motocin ciki, suna dai-daita parking na kusa da shi ya buɗeyasauka da sauri tare da mai alamun ya sakko, murmushi ya saki tare da mai alaman godiyadaido, ya an sauka ya dumfari hanyar da ze sada shi da cikin main parlorn tafkeken gidan, yana turaƙofan idon shi ya wanke da kyakykyawan dattijuwan dake tsaye fuska yalwace da murmushi, juyawa da sauri yayi ya kalli wanda ke bayan shi, murmurshi ya saki tare da faɗin "sun zomarabtan ka ne" juyowa yayi tare da sakin murmushi, duƙar da kai yayi tare da cire hulankanshi, shafa kan tayi cike da farin ciki tare da faɗin "Allah ya maka albarka, barka da dawowa gida" murmushi ya saki tare da ɗagowa ya kalli sauran jama'a dake tsaye a bayanta fuskokin suwashemurmushi, guntun murmurshi ya saki tare da nufar hanyar da ze sadashi da bedroomɗinshi..... "Ina me gayya me aikin?" Wata mata da ta fito daga ɗaya daga cikin ɗakunan da suka ma parlorn ƙawanya, wanda a shekaru zata iya kai 37 tace tare da kama baki "Ya shige yanzu" su ka cebaki ahaɗe, "Munnir ina sauran ku shigo mana munyi lunch" dattijuwan tace cike da kamala, murmushi Alhaji Munnir dake tsaye ya saki tare da faɗin "to Hajiya bari a musu iso" jinjina kai tayi fuskayalwace da murmushi, fitowa yayi sanye da riga da wando mara nauyi da alamun watsa ruwayayi, yana shirin zama Alhaji Munnir yace "mu ƙarisa daining ka ɗumama ciki" kallon shi yayi kaman ze ce wani abu se kuma ya fasa ya miƙe, suna shiga ɗakin da dining ɗin yake Hajiyatamiƙe tare da jan mai kujeran dake kusa da ita, cike da mamaki ya kalli Alhaji Munnir, murmurshi ya sakin mai tare da faɗin "ai har da ita" murmushi ya saki tare da zama saman kujeran a natse, "ba dai na makara ba!" Sautin me cike da kamala ya doki kunnuwan su, ɗagowa yawancinsusukayi tare da kallon wanda yayi maganan, matashin dattijo ɗan kimanin shekaru 44 da haihuwametsaye fuska yalwace da fara'a, hannun shi riƙe da kyawawan yara mace da na miji waƴandanazasu yi ƙasa da shekaru 12 ba, "gaskiya kam ka kamakara" wata me kama da shi sosai tace taredasakin dariya, "to lefin ma Munnir ne" yace tare da jan kujera ya zauna, "babban mutum, mebabban aiki se mu kaji labarin zuwanka bakatatan, kamar a mafarki" yace tare da kallonshi, guntun murmushi ya saki tare da ɗaukan cokalin da hajiya ta ajiye mishi a natse ya fara cinabincin cike da natsuwa.... Ajiye cokalin yayi a natse tare da jan kujeran baya, kallon Alhaji Munnir yayi tare da faɗin"ankai yaran can sun huta kuwa?" Jinjina mai kai yayi tare da faɗin "sun watsa ruwa, an kai musuabinci sun ci, yanzu haka suna barcin warware gajiya" jinjina kai yayi tare da faɗin "8:30pmjirginsuzetashi" jinjina mai kai yayi tare da faɗin "Allah ya kai mu".... Jawo wayanta dake neman agaji Yasmin tayi tare da kallon me kira, se a lokacin ta tuna jirantada ta saka su yi, rumtse ido tayi tare da kallon Farisat dake faɗin "ki ɗaga" jinjina kai tayi taɗagata saka a handsfree ta ajiye a gefe, sallama ya ɗaga mata a natse, amsawa tayi cikin disashshiyarmuryanta, "ƙanwata lafiya naji muryanki haka? Ko a barci na tashe ki?" Yayi maganan taredakallon yanda suka zuba mai ido, harara ya banka musu tare da kauda kai, "a'a, kuna lafiya?" Tacea natse, "Alhamdulillah shekaran jiya muna ta jiranki kuma ba ki zo ba" goge hawayen da yazubomata tayi tare da faɗin "uzurine ya ta so mun a lokacin" "wani uzuri ƙanwata? Kamar kukaki keko?" Yace cike da kulawa, fashewa da kukan da take ta dannewa tayi tare da faɗin "Anty netarasu a lokacin" kallonsu yayi tare da musu alamun kun ji ko, alamu Khalid yayi da ya cigabada magana, "Antynki?" Yace murya da alamun damuwa, jinjina kai tayi tare da faɗin "eh" "subhanallahi Allah ya yafe mata" "amen" tace a hankali tare da share hawaye, ɗaukan wayanKhalid yayi tare da faɗin "Allah ya mata rahma, a wani anguwa ku ke in Allah ya yarda zamuzomuku ta'aziyya" "Balaji2" tace a hankali, "okay Allah ya gafarta mata kuyi haƙuri Allah ya bakuhaƙurin rashi" yana kai nan ya kashe kiran tare da kallon Annur dake kallon shi.... "Bana jin zaku tare da ni, dan ina da tafiyan da ya taso mun nan da one week" CMyace taredakallon su, "be ma kamata muje ba, ni a gani na" humen leader tace tare da kallon su, "a'a yakamata kam, ta'aziyya ce ba wani abun daban ba" well pere yace tare da kallon ta, "yau biyu zekasance a yanda ta faɗa, kunga gobe uku me ze haka muje gobe mu amshi sadakan ukudagananko" ɗaya daga cikin p.r.o yace tare da kallon su, "in da gaske ne ba" ƴar uwan aikin shi tacetareda kallon shi, "bana jin ba gaske ba ne, dan muryanta ya bayyana komai, se dai ba zamukwashi sauran members ba, mu kaɗai zamu koma menene zamu gani" dispiling yace tare da kallonsu, jinjina kai suka yi cike da gamsuwa, "CM kana da lokaci goben?" Sagir yace tare da kallonshi, jinjina kai yayi tare da faɗin "Allah ya kai mu" "shikenan, ina ganin uzurinta ya kai a mata afwa, amma ya zama dole ta halarci duk wani events da Aminan juna suka shirya na bikin Rufa'i daSarah" Khalid yace tare da kallon su, jinjina kai suka yi alamun gamsuwa,nan suka sallami juna, tashi yawancin su suka yi ko wa ya hau abin hawan shi ya bar wajen, gyara zama Khalid yayi tareda faɗin "Shureim(CM) ya kamata kafaɗawa gayen nan gaskiya, wai meyasa yake kakkaretane?Ko dai sonta ya ke!" Khalid yace tare da kallon shi, murmushi Sagir ya saki tare da faɗin"yamaisa dan gidan su, ya samu mu tambayo mishi auren" dariya Shureim ya saki tare da faɗin"kukasani ko biyu ze yi rana ɗaya" "yama isa" Khalid yace tare da kai mai bugu, "bari mana, ya kakeƙoƙarin cutar da mijin Laɗifa" Annur yace tare da kallon shi, "wai a ina kasan yarinyar nanne?" Zubair yace tare da kama haɓa, "a wani group ne, yanda take yawan ba da gudummuwa inantambaya yasa na ga cewa za mu sami abokiyar tafiya" "be fa taɓa ganinta ba, banda yaumuryanta ma ba taɓa ji yayi ba" Khalid yace tare da kallon Shureim dake cewa "amma gayennanka gama damu, baka santa ba ma ka ɗakkota ka sata a gidan Aminan juna! Kar ka bari p.r.oSami ta ji" harara ya dalla mai tare da faɗin "wannnan yarinyar se na koya mata hankali" "ko ta koyamaka ba, ai Bin Sadik ya tsaya mata" Zubair yace tare da kallon shi, dariya Sagir ya saki taredafaɗin "Allah yasa ba aljana ka kwaso mana garin kwashe-kwashenka ba" "in ma ita ce suƙarelafiya" Khalid yace tare da banka mai harara, "abu me sauƙi ga ruzurun cikin mu se mu ba tashi ta aura" yace tare da nuna Shureim ya kwashe da dariya, rufe system ɗin gaban shi yayi yacirowarin takalmin shi ya miƙe ya dumfareshi, tashi yayi da sauri ya bar wajen, kwashewa da dariyasu Zubair suka yi tare da bin su da ido.... "Zaune yake saman one sittern da suka ƙawata parlorn bin yanda suke fa surutu kawai yakedaido, miƙewa yayi a natse tare da kallon Hajiya, "ba dai ka gaji da hiran mu ba?" Hajiya tacetaredakallon shi, guntun murmushi ya saki tare da faɗin "a'a" "abincin ma baka ci sosai ba ma" Hajiyatace cike da damuwa, guntun murmushi ya saki tare da kauda kai, "gudun tumbi yake" Alhaji Munnir yace tare da sakin dariya, harara ya banka mai tare da kauda kai, "ka kwantar da hankalinka ba ka da zubin masu shi" wanda ya shigo riƙe da yara a hannu yace tare da sakin murmushi, kauda kai yayi tare da faɗin "Allah ya wa ƴarki rasuwa shekaran jiya, in sha Allah gobe zamuta'aziyya" yana kai nan ya nufi bedroom ɗin shi, kallon Hajiya Alhaji Munnir yayi a razane taredafaɗin "ta rasu!" Gaba ɗaya jikin su ne yayi sanyi, banda mai-maita inna lillahi wa inna ilaihirraji'unba abinda Hajiya ke yi, juyawa Alhaji Munnir yayi tare da bin shi da idoz tunda ya sanar mai dabatun zuwan shi yake neman dalilin zuwan haka baka tatan, se yanzu ya samu amsan dalilin, sauke numfashi yayi tare da kallon na kusa da shi jiki a mace yace "a shirya jirgi gobe zamutafi ta'aziyya gaba ɗayan mu" jinjina mai kai yayi ya miƙe ya ɗau waya ya fice, ba wanda ya samuzarafin furta komai a cikin su, ko wanne da yanda mutuwan ya zo mai.... Comment fans🥰🙏 🫀MUGUN TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Three Tura ƙofan bedroom ɗin da suke ciki Sadam yayi a natse tare da zuba musu ido, ba wandabeɗago ya kalle shi ba se Insu dake zaune a gefe idonta tsaye ƙyam waje guda, takowa yayi anatseya zauna a kusa da ita, kallon Farisat da idonta ya koɗe yayi fari fat yayi tare da mata alamuntaci abinci? da ido, girgiza kai tayi a natse zuciya na rauni, riƙo hannun Insu yayi a natse tare dafaɗin"Insu" ɗago kai tayi a natse ta zube mai idonta da suka daɗe da komawa na zararru, ƙasa damurya yayi tare da faɗin "dan Allah ba dan mu ba ki daure, kin manta ke jaruma ce kamar yandaAnty take faɗa? zaki iya jurewa, bakyason zame mata ƴa ta gari salaha wacce zata dinga mataaddu'a kullum, in ki ka sa kan ki a wani hali Anty ba zata yafe miki ba" ya idda maganancikedarauni tare da sakin hawayen da yake ta dannewa.... Lumshe ido tayi hawayen da suka cika mata ido suka biyo kuncinta, saka kanta a kafaɗanshi tayi ba tare da tace komai ba, gyara mata zama yayi yanda zata fi jin daɗi tare da kallon Farisat dakeshare hawaye "kinyi baƙi suna side ɗin baƙi" jinjina mai kai tayi dan zuciyanta ya gama hasasomata wanda ya zo, miƙewa tayi a natse ta gyara zaman hijabin jikinta ta fice a natse, kallonYasmin yayi tare da faɗin "ku tashi ku zubo abinci ku ci" girgiza kai tayi tare da faɗin "banajinyunwa" sauran ma kowa cewa yayi baya jin yunwa, kasa ƙara cewa komai yayi se bin su dayayi da ido.... A natse ta gitta general parlor ba tare da tace wa waƴanda ke zaune a ciki komai ba, "AllahuAkbar Allah sarki rayuwa, anwa yaran nan babban rashi, kafin su saba da wannan rashinsesunjigata, Allah ya ba su haƙuri da juriyar jurewa, su aka wa wan nan rashin, sun saba da ita, komansu ita, kukan su ita, damuwan su ita, dariyar su ita, farin cikin su ita, wa za ta iya maye musugurbinta" wata mata dake zaune a gefe tace tare da share hawaye, "daina wannan batunHajiyaSuraiyya gurbin ido ai ba ido ba ne, ba wanda zata iya ma yaran nan gatan da mahaifiyarsutamusu, ta hana su neman komai wajen kowa, duk in suka kwaso damuwar su ita ke tsaya musuhar se taga sun fita daga ciki, ai Hajiya Amina samun jajirtacciyan uwa kamanta a wannanzamanin se an duba, ko yaushe tana tare da yaranta, in zaki shigo so dubu tare za ki gansu, tazama tamkar ƙawarsu" wacce ke kusa da ita tace cike da jimami, "shima Alhaji Abdussamadyayi rashi, ai rashin mata kamanta ba abu me sauƙi ba ne" "ai kuma ya gama samun mace dagakanta, daƙyar ze samu wacce zata maye mishi gurbinta" ɗayan tace da damuwa.... "A uzubillahi da wannan batu naki, haba baiwar Allah ya zaki ce ba ze samu mace kamantaba?Ai in sha Allah se ya samu wacce tafi ta ma, Allah na tuba me Amina ta tsinana mishi a rayuwa banda sabauta rayuwar shi da tayi, ai in sha Allah yanzu ne ze samu mace ta gari ƴar gidanmutumci wacce ta san mutumci" tsohuwar dake zaune a gefe tana banka musu harara tundasuka fara batun tace cike da takaici, da mamaki suka saki baki tare da bin ta da ido, "Babiyabarsudan Allah wanda be san wacece ita ba shi ze tsaya yana wannan batun mu da muka sanwaceceita ai se dai mu bi su da ido, dan dai be kamata ayi ta tone-tone ba ne a gidan mutuwa" waccekekama da Yaya sak tace cike da rashin ɗaukan abinda ta faɗa da mahimmanci, "dan Allahkuyi tone-tone kar ku fasa, ku ne zaku tona asirin ɗan uwanku, ance muku in aka fige kaza kyangani take? shashashu marassa hankali da tunani, ko yanzu kasuwa ta tashi ɗan koli yaci riba, dankoiya nan aka tsaya Ubangiji ya nuna muku wacece ita" ƙanwar Anty me bi mata tace cike daɗinbin takaicin su, "yi haƙuri Lailah ƙyalesu" matan da ta fara magana tace tare da mata alamuntaƙyalesu, "haba dan Allah tunda suka zo gidan nan suke sakin maganganu da basu da makamadatushe, yau ko abin tsiya Anty Amina ta musu tunda ta mutu ba ta taci arziƙin ƴaƴan da ta haifada jininsu su musu kara ba" Lailah tace tare da fashewa da kuka me ƙuna.... Da sallama ta shiga parlorn, amsawa samarin da suke zaune su biyu suka yi tare da bin tadaido, zama tayi a ƙasa tare da sadda kai ƙasa ta fara gaidasu, "ya ƙarin haƙuri Farisat?" Ɗaya dagaciki yace idon shi akan ta, jinjina mai kai tayi tare da faɗin "Alhamdulillah" a sanyaye, "Allahyagafarta mata, ance haihuwa ta zo yi ko?" Na kusa da shi yace na shi idon akanta, jinjina kai tayi anatse, "Allahu akbar ashe shahidiyace, ta haihuwan?" Na farkon ya kuma cewa tare da gyarazama, "a'a ba ta kai ga haihuwan ba ta rasu" tace tare da goge hawaye, "Allahu akbar Allahyagafarta mata ya baku haƙuri da juriyar rashi" "amen nagode" tace a natse, shiru suka yi dansunrasa me za su kuma cewa, ɗago kai tayi tare da faɗin "Yaya Sudais be ji rasuwan ba ne?" Shirusuka yi dan sun rasa me za su ce mata, guntun murmurshi ta saki tare da sadda kai, "amFarisat kar ki saka hakan a zuciyanki" girgiza kai tayi cikin taren numfashin shi tare da faɗin "ba komai, tunda na iya jure rashin Anty a kusa da ni wa ye zan kasa jure rashin shi, dama ni kaɗai nakekiɗina nake rawana, shi be san ina yi ba, se dai mutuwa ta kori komai, ko be zo min ta'aziyyaawacce ke ƙaunarshi ba ya zo mun saboda matsayina na ƴar kawun shi Yayan mahaifiyar shi, bakomai Yaya Abdullahi nagode da zuwan ku Allah ya saka muku da alheri" tana kai nan ta sharehawayen dake bin saman kumatun ta ta miƙe, bin ta su kai da ido jikkuna a mace, har ta kai bakinƙofa wanda ya fi zaƙewa wajen magana yace "Farisat dan Allah kar ki ce zaki wani yunƙuri, sannan ina baki shawara duk da ba wani bane ni a gare ki, ki haƙura da Sudais ko dan karedarajar zumuncin dake tsakanin ku" juyowa tayi a natse tare da faɗin "yanda Anty ta bar duniyahaka na bar shi har abada, wanda be jajanta mun akan rashin da nayi ba be can-canci ya cigabada ganin damuwata ba" tana kai nan ta juya a natse ta fice.... "Ku kuke gudun tone-tone, ke inba din zuciya ta musulunci ba zamu zo inda gawar Aminayakene bare har mu zauna amsan makokinta" wacce tayi zubi da Yaya tace a harzuƙe, "dan Allahkarku tanka su" matan da ta hana Lailah magana tace tare da ma sauran alamu da ido, "Allahsarki rayuwa, lallai ba ku san wacece Amina ba shiyasa ku ka zauna kuna aibantata, da yake kunyabaisan ku yayi ba" wacce ke zaune kusa da Lailah tace ido na shatata da ruwan hawaye, "waceceita?Dan Allah sanar mana, matar da ta shiga tsakanin ɗa da uwar shi, ba dadin Allah baya barci badaAmina ta raba mahaifiyar mu da ɗan uwan mu, ta hana shi yayi ko wani irin motsi, shi da gidanshi ta babbake ko ina, mu da mahaifiyar mu ba mu isa mu shigo gidan ɗan uwanmu mu yi walkadami ba, sau nawa yana yunƙurin aure ta shiga ta fita ta hana, ta hana shi samun farinciki a rayuwar aure ba yan ita ba ba shi take ba, har bare sun fi mu ahalin mijinta matsayi a gidan" ɗaya a cikin su tace rai ɓace, "meke faruwa anan?" Farisat tace tare da bin su da ido, murmushi Lailah ta saki tare da share hawaye tana tuna shuɗaɗdun abubuwa, kallon Farisat tayi taredafaɗin "ba komai zo ki wuce ciki" "a'a da kun faɗa mata ai, duk da sun sa waye uwar tasu, dantabiya musu daga alif har ya'un kuma ba wacce ba ta haddace a cikin su ba, Allah dai ya jarabci Yaya Abdussamad, Allah ya ba shi ikon cin wannan jarabawar, auren da aka hana ɗauruwar shi yanzu kuma ze ɗauru, dama ance faɗin wani tashin wani" da mamaki Farisat da jikinta kerawatabuɗe baki za tayi magana muryan Yasmin da ya fita a kausashe ya hanata furta komai.... "Me ki ke cewa! Akan wa ki ke maganan banza! Anty! Ke kin san wacece ita! Mahaifiyar muce, gatan mu ce, garkuwan gidan ɗan uwan na ku da ku ke murna ya samu ƴanci ce, murnanmutuwanta ku ke! Daina murna wataran uwarku mutuwar ze kawowa ziyara, kinga se kuji daɗinmurnan da kyau, ku tashi ku bar mana gida" ta idda maganan a harzuƙe, ba su ba hatta daBabiyase da ta razana da yanda fuskan Yasmin ɗin ya canza lokaci guda, "ta bar muku gida! uwar kuceta gina gidan?" Wacce ta fi kama da Yaya tace a harzuƙe, sakin hannun Insu Sadamyayi taredayin kan wanda tayi maganan gadan-gadan, da sauri Lailah ta riƙoshi tare da faɗin "ƙyeletaSadam ƙyaleta, Allah ze saka mata irin wannan ƙazafi da sharrin da suka mata, kaman yandasuka ce Allah baya barci, bi iznillah ze ma Anty Amina adalci dan shi gwanin adalci ne" takowaanatse Farisat tayi tare da faɗin "Suwaiba ki kace gidan uwarta ta gina ko? To bari in faɗa miki uwarta ita ce mamallakiyar gidan ɗan uwan ku kara shi tayi, dan haka ku tashi ku fice yanzu" tayi magana a mugun harzuƙe, da sauri suka mimmiƙe jikkuna na rawa suka fice daga parlorn, duƙewa gaba ɗayan su suka yi tare da sakin marayan kuka, nan su Lailah suka fara rarrashi.... "Zanga yanda za'ayi yaran nan su sami mijin aure, ki na ganin fa yanda suka mana tsaye har dawacce ke amsa sunan Kaka gare su ba su ji nauyi ko kunyarta ba suka korota" me shige daYayatace rai ɓace, "bar su Gude, inda nake gode Allah se da ta ga sakayya da idonta kafin ta mutu, gasunan riɗa-riɗa har huɗu ko wacce aka kaita ɗakin miji tas zata zauna amma ba mijin" Babiyatace cike da takaici, "ai shiyasa na cewa Sudais na ƙara jin ko wayanta ya amsa se na ɓata mai, duk da yace shi be kiranta ita ke kiran shi" Suwaiba tace rai ɓace, "ina zaku?" Yaya dake tsayedaDr Hisham a bakin gate ta waje yace tare da kallon su, "ƴaƴanka sun koremu daga gidan, sunceba gidanka ba ne na uwar su ne mu fita" Babiya tace rai ɓace, "subhanallah Babiya ba dai wani maganan ku kaje kuna yi a gaban yaran nan ba!" Yaya yace cike da damuwa, cike da mamaki suGude suka bi shi da ido, Babiya ko ta ma kasa cewa komai , harara Suwaiba ta dalla mishi taredafaɗin "bana son rashin sanin ciwon kai Abdussamad, yanzu ko wani maganan mu kayi ya can- canci yaranka su mata irin wannan tijarar? Sannan tana faɗa maka kana mata wani tambayannadaban" ta idda naganan a harzuƙe, buɗe baki Yaya yayi ze yi magana Dr Hishamya tari numfashin shi da faɗin "Allah ya baki haƙuri Hajiya" ya idda maganan cike da mamakin su, "ohodai ai munyi ƙoƙari ma tunda mun kwana uku, Allah ya jiƙan waƴanda suka rigamu, zamutafi inka samu sukuni ka shigo can" Babiya tace tare da wucewa muƙarrabanta suka dafa mata baya, zuciyoyi na tafarfasa.... "Please Alhaji kar ka sa damuwan nan a zuciyanka har ya haifar maka da wani matsalan" girgizakai Yaya yayi tare da faɗin "kar ka damu Dr ya za muyi da issue ɗin Insu, tun ranar da abunnanyafaru bakinta be saɓa da wani ba, ina tsoron kar ya zo firgici da razani ya haifar mata da wani matsalan" ya idda maganan cike da damuwa, sauke numfashi me ƙarfi Dr Hishamyayi taredafaɗin "in sha Allah ba abinda ze faru da ita, sannan zuwa anjima zan tura maka magungunandaza'a mata amfani da su in sha Allah ze temaka mata" jinjina kai Yaya yayi tare da ba shi hannusuka yi musabaha ya wuce, da sauri Ibrahim ya ƙariso tare da faɗin "Alhaji baƙi sun sauka yanzuzani gate na jira isowan su" ya idda maganan a girmame, murmurshi Yaya ya saki idon shi akanshi, tare da faɗin "Allah ya kawo su lafiya" jinjina kai yayi ya wuce a natse ya nufi gate..... "Dama nan ne Balaji2 ɗin?" Zubairu dake zaune a sit ɗin driver yace tare da kallon Sagir dakezaune a kusa da shi, wato kujeran me zaman banza, "ban sani ba" yace tare da taka burki sabodaganin Annur dake gaban shi ya taka burki, fitowa suka yi tare da isa motan su Annur, "lafiyakuwa?" Zubair yace tare da kallon Khalid, "wai ba'a shiga se da pass" yace tare da sakin tsaki, "kuma ka tabbata nan ne anguwan?" Humen leader da ta sakko a nata ita da vice ɗinta tacetareda kallon su, "haka dai google ya nuna" Annur yace tare da sakkowa ya zaro waya, "malamfitokasha iska" well pere yace ma Shureim dake zaune a kujeran me zaman banza a motan Annur, bamusu ya fito tare da faɗin "to mu kuma haka Allah ya so yayi damu" dariya suka saki tare dakallon Annur da ya kara waya a kunni.... Goge hawaye tayi tare da ɗaukan wayanta dake neman a gaji, ganin me kira yasata ɗagawatakara a kunni tare da ɗaga sallama, "ƙanwata gamu mun iso amma securitys sun hana mushigowa wai se da pass" "subhanallah ku yi haƙuri bari in shigo da ku" tace tare da sauke wayan, kallon Nafisat me bi ma Insu tayi tare da faɗin "zo ki je ki shigo da baƙi" jinjina mata kai tayi tareda tashi a natse ta shige bedroom ɗin su, ba ta jima ba ta fito sanye da baby hijab light blue, kallon Yasmin tayi tare da faɗin "da me zan gane su?" Miƙa mata wayan hannunta tayi taredafaɗin "in kin isa ki kira number da na rubuta Yayana, suna ɗagawa sune" jinjina mata kai tayi taamsa ta fice, tashi wasu ƴan mata dake zaune a gefe suka yi tare da faɗin "Yasmin Allahyaƙarahaƙuri" jinjina musu kai tayi tare da faɗin "nagode sosai".... Yana isa bakin gate ɗin ya hango jerin gwanen motocinsu na dumfaro gate ɗin, da sauri yaƙarisaga securitys ɗin ya ba su pass tare da nuna musu motocin, buɗe musu gate suka yi suka shigeanatse, suna gama shiga Ibrahim ya ƙarisa motan da oganshi ke ciki, da girmamawa ya buɗebaki ze yi magana, "shiga muje" kawai ya iya ce mai, da sauri ya buɗe gaba ya shige suka nufi gidan, zare ido Zubair yayi tare da faɗin "wani suna nake gani a jikin motocin nan!" Yayi magananarazane, maida hankula ga motocin suka yi da mamaki, "SSB!" Annur yace tare da zare ido, "shi neko dai mutanen shi ne?" Shureim yace tare da kallon su, "Allah masani" suka ce baku na ahaɗecike da mamaki.... Gittawa motocin tayi suka wuce ta ƙarisa gate ɗin a natse ta miƙa musu pass ɗinta ta musubayanin baƙin da zata shigar, tana amsa ta ɗaga wayan ta danna kira, saurin dawowa dagahayyacin shi Annur yayi tare da kallon wayan, hangen su da tayi ya sata ta katse kiran ta ƙarisainda suke tsatstsaye, tana isa ta ɗan sunkuya tare da faɗin "ina wunin ku" da mamaki sukabi tada ido, "ƙanwata!" Annur yace da mamaki, jinjina kai tayi tare da faɗin "tace a shiga da ku" saukeajiyan zuciya suka yi cike da samun sasauci suka shishshige mota suka bi ta dan ta ƙi shigamotan kowa.... Buɗe musu gate Baba Kalla yayi suka shige a natse, sakkowa Ibrahim yayi da sauri ya buɗemaAlhaji Munnir dake kusa da shi ƙofa, fitowa yayi tare da faɗin "Ibrahim kayi wuyan gani" murmushi ya saki tare da sadda kai, a

Chapter 3 of 109