"ai ɗa be fi ɗa ba, yanda Habibataɗaucikin Zuwaira wata tara ta haifeta haka na ɗau na Sudais na haifa, son da take ma ɗiyarta bekai
rabin wanda nake ma Sudais ba, amma ya kwanta yau kimanin sati uku ba ta iya zuwa ta dubashi
da jiki ba, se ita da ke da ƙugun haihuwa se in kama ƙafa zigi-zigi inje, nan nake jin zuwantadukbayan wata duba ɗiyarta, ku da ku ka ga za kuyi ta rawan jiki akan lamarin kuje kuyi banhanakowa ba, amma ni Gude ƙafana ba ze taka ko bakin ƙofar ɗakin da yarinyar nan take ba, danbasunana asaratu ba" ta idda maganan tare da kallon Sala dake zaune nesa da su tare da faɗin"kwashi kayan nan ki kai mota" ba musu ta kwasa ta fice....
"Antyn Gude ciwo ya kori komai, dan Allah matsayinki ta babba ki daina saka irin waƴannanabubuwan a zuciya" "wallahi Jummai kinji rantsuwan ɗan musulmi kenan ko ba zanje dubayarinyar nan ba, Allah ya raba lafiya" tana kai nan ta miƙe ta isa wajen Sudais dake zauneyanabin su da ido ta riƙo shi, suka nufi ƙofa, jiki a mace Jummai ta baro ɗakin...
"Ma sha Allah baiwar Allah ya ake ciki?" Babiya da ta ga fitowan wata nurse tace tare da kafetada ido, "kune waƴanda ku ka kawo Zuwaira Hamidu ko?" Tace tare da kallon su, "eh mu ne" Farisat tace tare da ƙarisawa inda take, "haihuwa ne, se dai da saura, tana hutatawa yanzuzuwaanjima se ku tafi" tace cike da kare aikinta...
"Hauhuwa baiwar Allah cikin wata takwas ne fa" Babiya tace da mamaki, "a'a Baba ya cikatarasedai in kun ɓata ƙirga" tana kai nan ta wuce, "to tabbas mun ɓata ƙirga kuwa, ku mu shiga muganta" Babiya tace tare da shigewa, bin yanda take ta sauke numfarfashi suka yi cike da
tausayawa, "sannu Zuwaira" Babiya tace da tausayawa, jinjina mata kai tayi tare da faɗin"ruwa"
da sauri Yasmin ta fara dube-duben inda za ta samu ruwa, ganin babu shi anan ya sata amsankuɗi a wajen Farisat ta fice da sauri, bin ta da ido akwai Habiba tayi bata taɓa zato ko tsammaninza su kalleta ba ma bare su tsaya mata a lamurran ta.... Da sallama Jummai ta shiga jiki a sanyaye, "kinji Jummai muna nan muna lissafin kawai, ciki yashiga wata tara" Babiya tace tare da kallon ta, "ya shiga ai Hajiya" tace tare da sauke numfashi ahankali, "au ke kin sani kenan? Ni duk a lissfina na bakwai yake, da Habi ta zo take ce munyashiga na takwas, yanzu kuma ɗaliban lafiya take ce mana ya cika tara" jinjina mata kai tayi tareda faɗin "me suka ce?" "Ai gida zamu tafi yanzu, bari Yasmin ta kawo mata ruwan ta sha tukun, kin tadda Guden?" "A'a wai an sallame su sun tafi" "Allah ya kuɓutar da su kenan, dama ɗanneman ba son zaman asibitin yake ba, duk ya bi ya ƙosa" tace tare da amsa sallaman Yasmindata shigo riƙe da goran ruwa.... A guje wata kyakykyawan yarinyar ƴar kimanin shekaru uku da haihuwa ta yo kan Lawuzadaketsaye tana sakin mata murmushi, "Ummi" tace cike da farin ciki, ɗagota tayi tare da amsanbasket ɗin hannunta, "kin cinye?" Tace da kulawa, girgiza kai tayi tare da faɗin "da saura" "okaymuje" tace tare da buɗe mata mota ta shige, bin bayanta tayi tare da faɗin "meyasa bakyasoncinabinci yanxu Iman?" "Ina ci sosai fa Ummi yana yawa ne" "to se a rage ai" tace tare da amsanjakanta....
"Ilu gida zaka kai ni" tace tare da kallon Ilu dake ta faman tuƙi, "to" yace ba tare da ya ɗaukehankalin shi akan hanya ba, a dai-dai ƙofar wani madai-daicin gida ya taka burki, buɗewa tayi ahanzarce ta sauka Iman ta biyo bayanta, "bye uncle Ilu" Iman tace tare da ɗaga mai hannu, murmushi ya saki tare da faɗin "bye Iman, riƙe hannunta Lawuza dake ta sakin murmushi tayi
suka nufi madai-daicin gate ɗin gidan, turawa tayi suka shige da addu'a a saman laɓɓa...
"Wa'alaikumussalam, ah yau ke kika ɗakkota!" Wata dattijuwan mata dake zaune samanfarinkujeran roba tace tare da kallon su, "yace ba ze samu daman ɗakkota ba" tace tare da sakinhannun Iman, da gudu ta shige parlor, "bi dai a hankali" dattijuwan tace tare da bin Imandaido....
"Sun dawo?" Lawuza tace tare da kallon ta, "ba su daɗe da shigowa ba, yau ma kaman anyi faɗane" "ƙyalesu Umma suna da lokacin yi ne, bari in koma Ilu na jirana a waje" "au na ɗauka kintasone" "tasowa yanzu! Baba Maude na da rai ai da wuya, roƙon alfarma nayi na je ɗakko Iman, sutabbata sun tafi islamiyya akan lokaci" "a'a leƙa tunda gaki Allah ya jefoki ki musu magana, danni ba jin nawa suke ba" Umma tayi magana tare da nuna mata ƙofan parlorn.... Wuce wa tayi da sauri, tana shiga ta taddasu zaune suna kallon tv, kallon macen ƴar shekaru10da haihuwa tayi tare da faɗin "damben ma yau ki ka je ki ka yi?" Tayi maganan fuska a ɗaure, saurin juyo da dubanta gareta tayi tare da girgiza kai, "damuwanki ne wannan ki cigaba dasonrashin zama lafiya, ina Sadik?" "Yana ɗaki" yaron dake zaune kusa da ita ɗan kimanin shekarubiyar yace tare da kallon ta, "to ku tabbatar 3 nayi kun fice gidan nan" jinjina mata kai sukayi
cike da ladabi, "kin canza mata kaya ko kina jiran a ce ki canza mata?" Tace fuska a ɗaure taredakallon matashiyar yarinyar, tashi tayi da sauri ta shige ɗaya daga cikin ɗakunan dake parlorn, juyawa tayi ta fice da sauri...
"Rufa'i ka fara kai mu gidan Jummai mu sauke su a can tukun" Babiya tace tare da gyara zama, "to Hajiya" yace cike da ladabi, "Hajiya ina ganin mu tafi gida tare da su, tunda ta fara labournkarya zo ya ƙara taso mata babu mota a kusa, kinga can akwai Sa'adatu za ta iya ba ta temakongaggawa kafin mu tafi" Farisat tace cike da fata....
"Eh kin fini gaskiya kam, to ke Jummai ya zamu yi dake?" "A'a bakomai Hajiya ai shawarandaFarisat ta ba da shine dai-dai da can da can gidan duk ɗaya ne" "to shikenan kai Rufa'i mutafi cankawai" "to" ya kuma cewa a natse....
Suna isa gida suka sassako riƙo hannun Zuwaira Farisat da Yasmin suka yi cike da kulawa sukanufi ciki, suna shiga main parlor suka ajiyeta a ƙasan capet, "sannu Zuwairatu" Babiya tacedakulawa, "yawwa Hajiya" tace tare da miƙe ƙafafu.... Daining area Yasmin ta wuce da sauri, zubo musu abinci tayi ta dawo cikin parlorn ta ajiyemusu, komawa tayi ta haɗo ma Zuwaira tea me kauri ta ajiye mata, "Anty Habiba ko kuma a haɗomukune?" Tace idonta akan su, "a'a bar shi masha ruwa" Habiba tace cike da haushi da takaicinkanta, "a'a akwai lemu ai" Farisat tace tare da miƙewa da sauri tayi deeprizern dake parlorn, ɗakkomusu Pepsi tayi ta ajiye tare da wuce wa ɗakin Sa'adatu, tana leƙawa ta tadda tana ta sharɓanbarci, jawo mata ƙofan tayi ta wuce na ta ɗakin.... Tunda ta koma ciki ta haye gado ba ta samu tashi ba se da kiran sallahn la'asar ya ratsa
kunnuwanta, tashi tayi baki ɗauke da addu'a ta shige toilet, fitowa tayi ruwa na ɗiga a samanfuskanta da alamun alwala tayo, daidaita tsayuwanta tayi a alƙibla ta kabbarta sallah, tanaidarda azkhar ta koma saman gado ta ƙara jan blanket, tun tana tunane tunane har barci yayi
nasaran saceta, shida dai-dai ta farka, kunna tv tayi ta koma saman sofa ta zauna, nan ta tattarogaba ɗaya natsuwanta ta ba wa tv saboda ASHIQ ANA da aka fara, ko gezau ba ta samu damanyi
ba se da aka kammala, tashi tayi ta koma toilet, ruwa me sauƙin ɗumi ta haɗa ta wanko jikintatas ta fito, shiryawa cikin riga da dogon wando me sauƙin nauyi tayi ta saka hula ta feshejiki daturare ta kabbarta magrib, ba ta motsa daga gabas ba se da ta gabatar da isha'i sannantamiƙe, dakko baby hijab pink colour tayi ta saka ta fice a natse....
Tana sauka ta tadda Maude na shirin ficewa, da sauri ta juyo tare da faɗin "barka da sakkowa" murmushi ta saki tare da faɗin "barka dai Baba Maude, ya gajiyan aiki?" "Wallahi Alhamdulillah, yanzu nake shirin faɗa miki an kammala dinner, dama shayi zani ɗakkowa" murmurshi ta saki
tare da faɗin "ba na shan shayi ai, make me fruits only" tayi maganan tare da wuce wa areandaining, da sauri Maude tayi kitchen dan haɗo mata...
Jan kujera tayi ta zauna, hankali kwance ta buɗe haɗaɗɗen coolern da ke ɗaukan ido, malmalantuwon semovita ta ɗakko ta saka a plate ɗin da ta zara, buɗe coolern miya tayi a natse, ganinmiyan ɗanyen kuɓewa yasa ta sakin murmushi tare da gyara zama, zuba dai-dai tayi ta kwashekusan rabin naman ciki, a natse ta gyara zama ta fara ci...
Shigowa Maude tayi ta ajiye mata jug ɗin da ta zubo mata a ciki tare da faɗin "afwan na daɗenasa shi a fridge ne ya ɗan yi sanyi" "ba damuwa" tace tare da mata alamun ta zuba mata, saurinɗaukan kofi daya daga cikin cup's ɗin da ta ajiye tayi ta zuba mata ta ajiye a gabanta, "nagodesosai Baba Maude, ina Lawuza?" "Ai shida take tashi, ba anan take kwana ba" Maude tacecikedagirmamawa, jinjina mata kai tayi ta ja ruwan wanke hannu dake cikin wani madai-daicinbolwdake ta zuba ƙyalli tana gamawa ta ɗau kofin niƙaƙken fruits ɗinta ta miƙe tayi sama.... Da ido Maude ta bi ta cike da mamaki, "wato wannan yarinyar dai ba ta da matsalan komai, incikinta ya ɗauka komai ma be dameta ba" ta idda maganan tare da duba abubuwan da ta ajiyewanda da alamu ko buɗe su ba tayi ba, "kin hutawa kan ki" tace tare da juyawa ta fice dankiranmasu tattarawa...
"Zama ai be ganta ba, tashi za tayi tana jijjiga jini" Lurwanu dake zaune a kusa da Yaya yacetareda kallon Babiya, "to ba dai suce haka ba, wallahi se ka ga yanda muka tadda yarinyar nan, banyi
zaton in muka isa asibitin nan za ta ƙara mintuna goma bata haihu ba, se cewa suka yi da saura" Babiya tace cike da takaicin su, murmushi Yaya ya saki tare da faɗin "Hajiya ai in lokacinbeyi baba za'a haihun ba, haka Amina tayi ta fama lokacin cikin Sa'eed, ta kai sati tana naƙuda, dukinmunje hospital abu ɗaya suke faɗa maba haihuwa da saura, har fa mu ka gaji muka daina zuwa"
"subhanallahi, wato naƙudan me dogon zango ne" tace tare da nuna zallan tausayawanta....
"Haka ne, gaskiyan Lurwanu ne ta tashi ta dinga kaiwa da komowa ze temaketa sosai" "totashi
Zuwairatu" Babiya tace tare da kallon ta, miƙewa da ƙyar tayi ta fara taku a hankali, "ke buɗeƙafa za kiyi ki taka wannan me ki ka san kina yi kenan" Balarabe yace tare da saka cake a baki, murmushi Salman ya saki tare da kallon shi, "da gaske Salman ko ban san kan aikin ba, nadai
san ba haka jijjiga jini yake ba" "ina Sa'adatu ta zo ta nuna mata mana, sune daliban lafiya" Babiya tace tare da kallonta, murmushi ta saki tare da miƙewa ta ƙarisa kusa da ita, dai-daitamata zaman ƙafa tayi tare da nuna mata yanda za tayi tana kai nan ta juya tayi ɗakinta.... Miƙewa Yasmin tayi ta riƙe mata hannu ganin kaman neman matallafi take tare da fara takawada ita, haka suka dinga kai komo, banda numfarfashi ba abinda Zuwaira ke saki, ta haɗa zufasharkaf, murmushi Yasmin ta sakin mata tare da faɗin "to zauna ki huta tukun" tayi maganantare da zaunar da ita, "sannu Yasmin, kema kin jijjiga jinin ai" Lurwanu yace tare da sakinmatamurmushi...
Zaro wayan shi dake neman agaji Balarabe yayi ganin me kira ya sa shi sakin murmushi taredaɗagawa ya sa a speaker, "hello Insu" yace cike da farin ciki, "hello Allah ya bar masu madara" tace da ƙarfi, "amen ƴar albarka, mu da madara ba gudu baja da baya, madara ai duniya ne" yacemurya na nuna zallan farin cikin da ya shiga....
Dariya ta saki tare da faɗin "kasan abu in jajircewa kayi ka koya ka fi riƙewa da daraja" "kwarai
kuwa ai me nema yana tare da samu, Christiano Ronaldo muna tare da shi iya wuya" "Madridtaku ce gaba ɗayanta" tace tare da sakin dariya, "ke na baki Ɓadamayya da kewayenta" yacecikeda jin daɗi, "godiya nake Allah ya ƙara ɗaukaka" "amen, to ya can ɗin?"...
"Allah ya shiryeki" Salman yace da ƙarfi, dariya ta saki tare da faɗin "amen Yaya Salman, YayaBalarabe Alhamdulillah ina cikin aminci se kewan ku" "muna tare da ke, kar ki damu kanki, YayaAli yace yana gama warkewa lodin nan ze yi ya zo ya ganki" "wayyo daɗi, Allah ya amincemai" tace cike da ƙaraji, "amen" yace cike da jindaɗin farin cikin da yaji ta na yi, "ke ba zaki nemonatsuwa a duk inda yake ki sawa kan ki ba ko?" Lurwanu yace fuska faɗaɗe da murmushi, "YayaLurwanu kai ma kana nan ne? Ku ce dai kowa yana nan banda ni, inba zan saka kuka" dariyayasaki tare da faɗin "kar ki yi, yanzu ma zan tashi in tafi" "a'a yi zamanka, ina Yayana? Nayi takiranwayan shi yana shiga ba'a ɗauka ba" "ga shi nan ina ga yasa wayan a caji ne" yace tare da miƙamai wayan ...
"Sweet Yaya" tace tare da sakin murmushi, "sweet Insu" yace fuska washe, "ka wuni lafiya?"
"Alhamdulillah cikin aminci" "ya aikin?" Tace da kulawa, "Alhamdulillah, na baro shi a office, segobe kuma in me kowa da komai ya kai mu" "to Allah ya bada sa'a da nasara, ya ƙara riƙe
hannunka akan tafarki na gaskiya, ya hana duk wani azzalumin da ze canza maka ra'ayinkakusantar inda ka ke" "amen-amen Dear" yace cike da tsan-tsan farin ciki, "ina sarauniya Nafisat
uwar gida kuma amarya sannan gimbiya ke mulkan zuciyan Umarul Faruk" ta idda maganancikeda zaƙuwa...
Dariya suka kwashe da shi gaba ɗayan su, saboda yanda Babiya ke jinjina kai da alamunabindatace ya shigeta, miƙa mata wayan Yaya yayi tare da komawa ya jingina da jikin kujeran dayakekai ya bisu da ido, "Insiyyah kin wuni lafiya dai ko?" Tace da kulawa, "Alhamdulillah sarauniyaNafisat, ya ku ka wani?" "To Alhamdulillahi zamu ce, ƴar uwanki Zuwairatu ce dai ta tashi danaƙuda, munje asibiti kuma sunce haihuwar da saura" "subhanallahi da saura kuma!" Tacecikeda ruɗu, "wallahi haka suka ce kar dai ki damu, ga ta ka tana zaune a na hira da ita, ya lafa" "toAllah ya sauketa lafiya, ta yi ta jijjiga jini, kar ta zauna waje ɗaya" tace cike da kulawa, "toyanzuko Yasmin ta zaunar da ita ta huta tukun, ga Goggon taku, ita Jummai dai ta koma gidantaɗazutace se gobe zata dawo" "eh tunda haihuwan be zo ba gunda ta koma ai" tayi maganan cikedamayyance...
"Insiyyah ki na lafiya?" Habiba tace murya a sanyaye, "Alhamdulillah Anty Habiba ya me jikin?"
"Da sauƙi" "to Allah ya sauketa lafiya, ki ta mata addu'a, kar ki yawaita damuwa ba mafitandazebaki" jinjina kai tayi cike da nauyi da kunyar su tare da faɗin "nagode Insiyyah" "bakomai Allahdai ya sauketa lafiya" "amen" tace tare da ba Farisat, "baby Insu ga Zuwairan ku gaisa" tacetareda karawa Zuwaira wayan a kunni, "Zuwaira ya jikin?" "Da sauƙi" tace a hankali, "sannu inshaAllah zaki samu sauƙi ki yi ta addu'a" "in sha Allah nagode sosai" tace tare da kauda kai, "gaYayaSalman" tace tare da miƙa mai, "Allah ya shiryeki, ke ba kallon ƙwallo ba se shishshigi a kai" yacetare da sakin murmushi.. Dariya ta saki tare da faɗin, "na kan ɗan taɓa in Yaya Balarabe na kallo, "to ki dai maida hankali akaratu kar ki tsaya wannan kalle-kallen" "to Yaya Salman" tace cike da ladabi... Miƙawa Sadam yayi ya yi saurin kauda jiki, dariya Yasmin ta saki tare da amsa, "bari zuwa gobemuyi magana" tace a natse, "to shikenan, ki mata haɗin da Anty ta ke yi lokacin da take labournUmar" "to in sha Allah" tace tare da miƙawa Balarabe wayan, tun kafin ya amsa ta katse, "yawwaYaya Balarabe wai Morata a wani club yake?" Farisat tace tare da kallon shi, "ke kuma meyahaɗaki da sanin hakan?" Yace cike da mamaki dan yasa ba sa kalla ita da Yasmin...
"So nake in sani" tace idonta akan shi, "wani club ne me suna Como, team ɗin italia ne" "okaynagane" tace tare da kallon Yasmin, kauda kai tayi ta maida ga Zuwaira ba tare da tace ma Farisat
komai ba....
"Ya ki ke ji yanzu?" Tayi maganan da kulawa, "na ji sauƙi da daɗin jikin sosai" tace tare da sakinmurmushi, "bari in haɗo miki abinda Insu tace ze temaka miki" tace tare da miƙewa tayi kitchen, "miƙewa Farisat tayi ta wuce daƙin Nafisat ba ta jimaba suka fito tare suka wuce ɗakin Insubatare da sun ce wa kowa komai ba...
Tana katse wayan ta saka a caji ta miƙe ta shige bathroom kama ruwa tayi ta yo alwala tafito, hayewa gado tayi taja blanket tare da fara karanto azkhairin naum....
"Amshi ki sha da zafi-zafi" Yasmin tace cike da kulawa, tana amsa ta kafa kai, fitowa Farisat tayi
tare da zama kusa da Habiba cike da kulawa tace "Anty Habiba kije ki kwanta an gyara mukumakwanci" "eh yakamata ki je ki kwanta" Babiya tace idonta akan ta, "to" tace tare da miƙewajiki a mace tayi ɗakin, tana shiga ta tadda Nafisat na ƙoƙarin fita riƙe da bokitin da ta gogetiles, "sannu da shigowa Anty Habiba tace tare da ficewa....
"Yaya 11:20, muje ka kwanta" Nafisat tace tare da riƙo hannun shi, ba musu ya tashi ya sallamesu suka wuce, sallaman su Lurwanu yayi ya tashi ya fice, "Yaya Salman ta samu in zo ne?" Yasmintace idonta akan shi, "no" yace tare da miƙewa, miƙewa Farisat tayi a natse suka rankaya tare, "good night Hajiya" Sadam yace tare da yin ɗakin shi, "Hajiya ya maganan da muka fara?"
Balarabe yace tare da kallonta, "zan tuntuɓi Hamisu tukun" tace tare da yunƙurawa tayi ɗakinta... Murmushi Yasmin ta sakin ma Zuwaira tare da faɗin "kin shanye?" "Eh" tace tare da miƙa matakofin, "yawwa bari ya faɗa miki se mu cigaba da motsa jikin" jinjina kai tayi ba tare da tacekomai
ba, haka suka raba dare suna temaka mata, in tayi ta zauna ta huta, su ƙara tashi su taya ta, inwannan ta taya ta ta huta wannna ta taya ta, hatta Nafisat ba ta rumtsa ba, kaman yandabasurumtsa ba haka Habiba ta kwana ta na leƙen su, har kuka se da tayi ba ta taɓa zaton kyawunzuciyansu ya kai har haka ba, se gab da asuba sannan suka kai ta daki, suma ko wacce tayi
ɗakinta....
Comments fans🥰🙏
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙
_We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Sixteen
A natse take taka matakalan benen takalmin ƙadarta na bada sauti me ɗaukan hankali, sanyetake da wando palazzo multicolour, wanda be buɗe sosai ba, golden t-shirt sanye a jikintawandaya ɗauki farin fatanta sosai, maroon jacket da ta ɗaura a saman shi me taushi, wanda ya kai gabda gwiwanta ya ƙara ƙawata adon, ba ta saka maɓallan ba ta sake shi ya ba da wani salonamusamman, marron ɗin veil ta saka ta saki leɓatun ɗaya, ɗayan kuma ta saɓa shi ya komatabaya.... Hannunta na hagu ta zuba mai ji awarwaro marron golden masu ɗaukan ido, hannun damakumata ɗaura agogo golden, wuya da kunni ta ƙawatasu da fashion jewel me matuƙar burgewa, taƙawata ƙafafu da takalmi golden me madai-daicin tsini, jakan goye a bayanta madai-daici
golden maroon me ɗauke da adon baby's, ta ja hannun jakan yayi ƙasa sosai, wayanta riƙeahannunta, fuskan nan fayau babu komai se lip gloss data shafa a lips ɗin ta, se nostril goldenmaroon da ta saka a hujin hancinta, banda zuba ƙamshi babu abinda take, da alamun anɓarar daruwan turare yanda yakamata..
Zuba ma matakalan ido Lawuza da sauran ma'aikatan da ke gyara parlorn suka yi, tana
bayyanuwa suka fara yaba irin kyawun da tayi a ƙasan zuci, murmushi ta sakin musu taredafaɗin "na yi kyau kuwa?" Ta jefa musu tambayan tare da iddasa sauka daga matakalan ta karyatsayuwa ta zuba musu wala-walan idanunta... Murmushi duk suka saki tare da bin ta da ido, murmushi Lawuza ta saki tare da faɗin "sosai ki kayi kyau Ma" "no ba na son wannan Ma n, sunana Insu, ba ya da wahalan faɗi, Insu" ta idda
maganan tare da bin su da ido, "ya yi mana nauyi Ma" Lawuza tace tare da sakin murmushinyanda Insu tayi da fuska ..
"Oh my god, yanzu fa na faɗa miki bana so" tace fuska a shagwaɓe, "sorry" tace aladabce, "Manda ku ke cewa shi ze sa ku yi lefi, amma in ku ka kira Insu sanyi farin ciki dan sunan da
mahaifiyata ke kirana da shi kenan" ta idda maganan tare da kallon hoton su da Anty, "inshaAllah" suka ce baki a haɗe a ladabce, "yawwa ko ku fa, har kunfi jiya kyau, ku matso mu dauselfie, ranar farko da Insu za ta fara zuwa school" ta idda maganan tare da ɗaga wayanta... Ganin suna ta kallon juna yasata faɗin "oh Allah da ku nake" tayi maganan tare da musualamunsu matso da ido, da sauri suka matso ɗaga musu selfie tayi fuskokinsu washe da murmushi...
"Yawwa kunga munyi kyau sosai, ku gani" tace tare da miƙa musu wayan, ƙarisawa ga hotonsutayi tare da kallon fuskan Anty da ya yalwata da murmurshi, murmushi ta saki tare da faɗin"ranar farko kenan Anty, na fara jiyo ƙamshin nasara" tana kai nan ta wuce ƙaramin daining,
kafin ta ja kujera Lawuza da ta amso wayan ta biyota tayi saurin jan mata tare da ajiye matawayan a kusa da ita, murmushi ta saki tare da faɗin "nagode Anty Lawuza" murmushi Lawuzatasaki tare da zuba mata dafaffan farin doyan da ya samu aikin tsafta, "wow Anty Lawuza wannandoyan wacce ƙasa ce?" Murmurshi ta sakin mata tare da ɗaukan madaidaici bowl ta zuba matamiyan hanta...
"Tea?" Tace da kulawa, no akwai sauran haɗin da fruits ɗin da Baba Maude ta mun a fridgebani
shi kawai" tace tare da fara ci cike da natsuwa, zuwa tayi ta ɗakko ta zuba mata ta ja gefetanabin ta da ido, in zata faɗi gaskiya yarinyar ba ƙaramin burgeta take ba, ga ta ƙarama me ƙarancinshekaru se dai akwai wani abu tattare da ita, iya mu'amalla, girmama na gaba, hankali, saninyakamata, da darajta wanda take tare da shi, ta zauna a ƙarƙashin mutane da dama a gidanamma ba ta taɓa haɗuwa da wacce ta san darajar ta irin ta ba ... Zaran tissue tayi ta goge baki ta miƙe tare da faɗin "Anty Lawuza wani duniyar ki ka lula haka?Ina ta magana kinyi shiru" murmurshi ta saki tare da faɗin "me ki ka ce?" "Cewa na yi ki dainayawan tunani, dan yana haifar da damuwa anan" ta ƙarishe maganan tare da nuna mata saitinzuciya, ƙaramin dariya ta saki tare da faɗin "to" "yawwa abincin yayi daɗi, kar ayi lunch, akwai
inda zan biya daga school, zaki iya tafiya gida ba zan dawo da wuri ba" tana kai nan ta nufi ƙofanda ze sadata da waje, dafa mata baya Lawuza tayi cike da farin ciki ...
Tana fita idonta ya wanke da Ibrahim dake tsaye gefen motan da Hajiya ta sa aka kawo tunjiya, zare ido tayi cike da mamaki tare da fara taka matakalan da sauri da sauri, "bi a hankali" Maudeda ta zo gaidata tace tare da saka hannu kamar zata riƙo ta, tana ƙarisawa inda yake ta tsayafuska yalwace da farin ciki tare da faɗin "Ibrahim! Da gaske kai ne dai!" Ta idda maganantaredasa hannayenta biyu ta rufe bakinta da su....
Murmushi ya saki tare da jinjina mata kai, "na kasa yarda" tace tare da sakin murmurshi, buɗemata ƙofan motan baya yayi tare da faɗin "barka da fitowa Hajiya Insu" "a'a kar mu fara hakadakai, in kana so kuma mu fara faɗan da muka saba ne ka ƙara kira na da wata Hajiya, wannanai
kaman ma cin fuska ne Ibrahim, ba Saudiyyan da na je kayi ta wani kirana da Hajiya" ta iddamaganan tare da ɓata fuska... Danne dariyar da ya kawo mai ziyara yayi tare da faɗin "sorry to Insu" "yawwa ko kaifa" tacetareda sakin murmushi, banda bin su da ido ba abinda Lawuza dake tsaye gefe ke yi, saurin juyawaciki tayi kamar wacce ta manta wani abu, taɓe baki Maude tayi ta ƙarisa wajen tare da faɗin"Hajiya har kin fito?" "Oh Baba Maude please ku na kirana da sunana, bana son wannanjajibejajiben" "to Insu kin tashi lafiya?" Tace fuska ɗauke da murmushi... Murmushi ta saki tare da rungumota cike da
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 20 Chapter of 109