sakawa tunda ba su zo da wani ba" yana kai nan ya nufi ƙofa da hanzari ya fice, da
murmushi suka bi shi cike da jin daɗin tunanin shi....
"Wai SSB da ƴa, zamu ga yanda ze yi" A'isha tace tare da sakin ƙaramar dariya, "ban sannemanzance A'isha me ze yi kuwa?" Hajiya tace fuska yalwace da murmushi, murmushi Alhaji Munnir
ya saki tare da faɗin "dan taga yana matuƙar ƙaunan yara ne shiyasa tace haka" "to ai shi hakayake tun yana yaro, lokacin da na haifi Kausar cewa yake se na goya mai ita, duk ranar da nacebazan goya mai ba kuwa akwai daru, ya iya kula da yara haka ze damƙeta ƙaƙamyaro be faɗi ahannun shi" Hajiya tace fuska faɗaɗe da murmushi cike da tuno lokacin.... Kai tsaye airport suka wuce, suna isa suka tadda matashin saurayin da Lailah ta sa ya tahomatada danbu ya iso, amsa tayi a sanyaye ta miƙa ma Sadam tare da faɗin "se ka zo" jinjina matakai
yayi ya wuce ciki dan su Yaya sun shige tun isowan su, suna shishshiga jirgi ya tashi, ba subar
wajen ba se da jirgin ya ɓacewa ganin su, juyawa suka yi suka nufi motacin su jikkuna a mace.... Kallon Farisat dake zaune ɗage da kai sama Salman na gwada mata bp Yaya yayi da kulawatareda maida duban shi ga Salman, tun kan su iso kanta ke mata masifaffen ciwo, "ya hau ko?" Yaceanatse, jinjina mai kai yayi tare da cire ma Farisat abinda ya saka mata ya zare na kunninshi, "yanzu kin kyauta ma kan ki kenan Farisat? Meyasa bakya so a zauna lafiya ne? Dama kinsandazaman watarana Mairah dole zata koma ga ahalinta, to menene na son cutar da kan ki da ki ke?" Babiya ta yi maganan murya na bayyana ƙunan da ya riski zuciyanta....
Fashewa da kuka Farisat tayi tare da faɗin "Hajiya Mairah fa ɗiyata ce ni na raineta" "ke ki kahaifeta?" Ta jefa mata tambayan zuciya a ɓace, shiru tayi ba tare da tace komai ba, "ko uwar data haifeta ba ta da ikon hana iyayenta ɗaukanta, akan me ke zaki ɗaurawa kan ki damuwakotausayin na cikin ki bakya yi, yanzu idan akan shashancin ki ki ka ɓarar da na cikin ki fa!" Taiddamaganan rai ɓace....
"Ayi haƙurin Hajiya" Salman daya ɗago kai yace a hankali, "gyaleni da ita Salman, Farisat batagane abu ta ruwan sanyi, yanzu ba Insu ne ta haifi yarinyar nan ba? Ka duba ka gani ammabakowa yasan ita ce mahaifiyarta ba saboda kawaici da alkunya, ta cire ido ga duk wani abugameda ƴan ta bar mata duk da kasantuwarta mahaifiyarta, kuma mun san son dake tsakaninuwadaɗiyarta, amma duk ta kauda kai saboda Farisat ɗin, se ita ce zata nemi ɗaga mana hankali, meyasa bakya zurfin tunani yayin aikata abu ne Farisat? A ce har ƙanwarki ta uku ta fiki saninabinda yakamata" ta idda maganan cikin muryan rarrashi.... Ɗago kai Farisat tayi tare da kallon Yaya, murmushi ya sakin mata tare da riƙo hannunta, "har
yanzu ke Mommynta ne, ba wanda ze haye matsayinki a gunta, tana ƙaunarki za kuma ta cigabada ƙaunarki ko ba ta tare dake, ki barta ta shaƙu da iyayenta, in dai zata rayu a wajenki zatadawo in sha Allah" ya idda maganan tare da shafa kumatun ta, jinjina kai tayi murya na rawatace"ku yi haƙuri ban shiryama abun ba ne" jinjina mata kai yayi tare da jawota kaɗan ya rungume....
"Saketa Abdussamad su tattara su yi gidansu, dake Yasmin ta fita hankali ai ba ta yarda tabiyotanan ba" Babiya tace cike da takaicin Farisat, murmushi Sadam ya saki tare da faɗin "ai gundadaba ta biyo ba, wannan in ta zo nan ai wani sabon rikicin ne" murmushi Salman ya saki taredamiƙewa a natse ya miƙa ma Sadam abin gwajin ya miƙa hannu ya riƙo hannunta, miƙewa tayi
babu musu, "ta sha magani kafin ta kwanta" Yaya yace a natse, jinjina mai kai yayi cike dagirmamawa tare da faɗin "to" sallamansu tayi cikin dasashshiyar muryanta suka fice, da idosukabi su har suka ɓacewa ganin su....
Sauke ajiyan zuciya suka yi a tare cike da samun sassauci, "da tausayi ta shaƙu da yarinyar" Babiya tace idonta na tara ruwan hawaye, "kin san hakan kuma ki ka yi ta mata faɗa?" Sadamyace tare da kallonta, "inba hakan na mata ba ba zata natsu ba, yaron nan Salman ya na da
kawaici ita kuma Farisat ba ta da, in ta cigaba da damuwa zata iya cutar da na cikinta da yakefatan gani" jinjina kai yayi cike da gamsuwa tare da faɗin "suma can ba su kyauta ba, da sujiratadawo ta kimtsa a natse se ta koma" "tsoro suke kar ya zo ta ƙi komawa" Hajiya tace tare damiƙewa, ba abinda Yaya yace musu se bin su da ido da yake cike da kewan yaran na shi, miƙewaSadam yayi ya dafa mata baya ya wuce ɗakin su Sahabee dan ganin ko sun yi barci.... Numfashi me tarin damuwoyi Yaya ya saki cike da tausayin kan shi da yaran shi, gida ya komafayau kamar ba'a yi zamanin da gimbiyoyi masu cike da ababen alfahari suka rayu a gidanba, miƙewa yayi a natse ya shige side ɗin shi....
"Precious dan Allah ba zaki bar kukan nan haka ba!" Shureim dake zaune kusa da Yasmindakezaune tsakiyan gadonta dake bedroom ɗinta yace cike da damuwa, dan tunda suka dawotashigeba ta fito ba, jinjina kai tayi tare da ɗago fuskanta da ya koma ja saboda kuka ta kalleshi cikedason dainawa tace "zan daina" tayi maganan a raunane, murmurshi ya saki tare da riƙota yasakaaƙirjin shi zame ɗan kwalin kanta yayi ya fara shafa kwamtaccen kitson dake kan cike da kulawatare da faɗin "duk da ban san farkon labarin ba tsakiya na riska zan iya cewa Yaya ya fikugaskiya, wannan bawan Allahn yana cutuwa ne ta dalilin Insu kuma da igiyoyin shi akanta kinga zamantaa can yafi can-canta akan anan"...
"Sannan ita ma na san za tafi samun natsuwa a kusa da shi duk da be san inda yake ba, danƙaunarshi ke riƙe da ita har wannan lokacin, fatan ta shine komawa gare shi kullum, wannandalilin ne ya hanata amsan buƙatan yawancin mazaje in sun tinkareta da shi" jinjina kai tayi cikeda gamsuwa tare da faɗin "tana matuƙar son shi, se dai bata da tabbacin shi yana sonta, yasadaukar da soyayyan shi ga wacce ke da matuƙar mahimmaci a gareta, ba ta isa jin zafintakofito na fito da ita ba duk da ba ta raye, shiyasa ta zaɓi nesa da shi ko hakan ze saka su rayuwamecike da aminci, se dai ta kasa, ta danne rauninta dan shi ya rayu cikin aminci, a she ze fi tacutuwa
ba ta sani ba, na tabbata da Insu ta san ƙumbar ƙaramin yatsan shi ze iya cutuwa ta sanadinnisantar shi da tayi ba zata taɓa nisantanshi ba" ta idda maganan a raunane... Saurin matseta yayi dan jin kuka na taso mata, "ku yi haƙuri komai ze zama labari, na tabbatar baze bari ta zubda hawaye ba" yace a natse "ba zata zubda ba, matuƙar yana tare da ita" tacecikeda tabbaci, ɗago kai tayi ta share hawaye tare da faɗin "kayi haƙuri baka san da labarinbaseyau" murmushi ya sakin mata tare da faɗin "na san lokacin sani na ne beyi ba, da ya yi ba gashi nasani ba" murmushi ta saki tare da bin shi da ido, murmushi ya sakin mata tare da faɗin "kar ki
damu, wani abun sirrin mu ne precious ba kowa muke saurin faɗawa ba" girgiza kai tayi taredafaɗin "ba wani sirri na wanda ba zan iya faɗa maka ba Habbubi, wannan ma sha'afa nayi" murmurshi ya saki tare da jinjina mata kai, gyara zama tayi ta karanto mai komai, da zallanmamaki yake bin ta da ido, murmushi ta saki tare da faɗin "wannan shine labarin rayuwarmu"....
Jawota yayi ya rungumeta ƙaƙam tare da faɗin "sorry precious!" Murmushi ta saki tare daɗaurahannunta a saman ƙirjin shi, "nayi matuƙar mamaki" yace a sanyaye, murmushi ta saki taredaɗago kai ta sumbaci laɓɓan shi tare da faɗin "labarin cike yake da al'ajabi" jinjina kai yayi taredafaɗin "SSB dai da na sani!" "Shi" tace tare da sakin murmushi, "Allah me iko" yace da mamaki.... Ƙaramar dariya ta saki tare da faɗin "ka halarci ɗaurin auren ai" "ni!" Yace a tsorace, jinjinamai
kai tayi tare da faɗin "kana cikin shedu, ranar da ku ka zo gaisuwa ne" zare ido yayi tare dafaɗin"wai dama auren su ne!" Jinjina mai kai tayi fuska yalwace da murmushi, "lallai wannanal'amarincike yake da mamaki, kusan shekara shida fa?" "Shidan ne" tace a hankali, "Allah ya haɗa
zuciyoyinsu su fahimci irin san da suke ma juna, su rayu cikin aminci, lallai Mairah tayi sa'aniyaye, Allah yasa namu suma su yi sa'a irin nata" ya idda maganan tare da jawota, murmushi tasaki tare da faɗin "amen" a hankali, dariya ya saki tare da faɗin "buɗe murya ki amsa dagani seke" dariya ta saki tare da yunƙurin sauka....
"Ba ki isa ba se kin faɗa" yace tare da jawota ya fara mata cakulkuli, "zan faɗa" tace da ƙarfi, "to
faɗi" yace cike da nishaɗi, "to ka tsaya tukun" tace murya cike da dariya, "na san ina tsayawaguduwa zaki yi" yace tare da sakin murmushi, "a'a bazan gudu ba" tace cike da tabbaci, tsayawayayi fuska cike da murmushi tare da zube mata ido, murmushin saman fuskanta be ɗaukebatamatsa kusa da shi sosai ta shige jikin shi tare da ƙanƙameshi, ɗaga kanta tayi ta kara bakintaasaman kunnin shi tare da faɗin "amen!" Nagartaccen murmushi ya saki tare da matseta, mujemuci abinci" yace tare da ɗagata ya saka a ƙirji ya nufi ƙofa....
"Ba ka ga wayana ba?" Farisat da ta canza kaya alamun ta watsa ruwa tace tare da kallonSalmandake ƙoƙarin haɗa musu dinner, girgiza kai yayi tare da faɗin "me zaki yi dashi?" "A ramunnakaInsu zan kira in ji ko Mairah ta tashi" tace tare da iddasa shiga cikin kitchen ɗin, bin ta da idoyayi
a natse, ganin da iya gaskiyanta take ya sashi a jiye wuƙan da yake yanka albasa ya kamota...
Zaunar da ita yayi a ɗaya daga cikin chair's ɗin dake kitchen ɗin tare da faɗin "bakya ganinkaman kiranta a wannan lokacin be kamata ba? Ita ma Insun ba ta da natsuwa, in ki ka kiratayanzu ta jiki a haka zata ƙara shiga damuwa gashi bata kusa, Kushi Mairah ɗiyarki ce halakmalakhar a lahira, ba wanda ya isa hanaki kiranta ɗiyarki, dan Allah ki natsu, ki bar komai ya wuce, inki
ka haihu lafiya ma se mu ba su yaron su ba mu Mairah ba shikenan ba" ya idda magananidonshi
akan ta, bin shi da ido tayi cike da farin ciki murmushi na mamaye saman fuskanta, "da gaske!" Tace kamar mara wayau, jinjina mata kai yayi cike da tabbaci, rungumeshi tayi da sauri taredafaɗin "shikenan ma, an raba gaddama, thank you my Jannah, Allah ya saka maka da alheri, bari
ba zan kira su yanzu ba, se gobe da safe, duk da na san Mairah ma ta tashi yanzu" murmushi yasakin mata cike da jin daɗin shawo kanta da yayi tare da hitting bayanta a hankali....
Janye jiki tayi da sauri ta miƙe tare da faɗin "bari in temaka maka" ba musu ya ja baya taredabinta da ido cike da tausayinta dan yasan abu ne me matuƙar wahala faruwan abinda ya faɗa....
"Shikenan yanzu kun baro ta can!" Mommyn Hisham dake zaune ita da Hishamda su Mihnatacetare da kallon Hisham da mamaki, jinjina kai yayi tare da sauke numfashi me ɗumi, "Allahmeiko, to ya maganan karatun ta?" Tace a sanyaye, "Insoul zata koma dole, dama sun nemi mu komaamma da sauran lokaci" "Allah sarki sister Insu!" Minha tace da damuwa, miƙewa yayi a hankali
tare da faɗin "sunday me zuwa In sha Allah zan koma cikin Insoul" yayi maganan a hankali tareda wuce wa bedroom ɗin shi.... Murmushi Hamid ya saki tare da faɗin "na san za'ayi haka" dariya Amen ya saki tare da faɗin"dama ai ba makawa wannan" murmushi Mommy ta saki tare da miƙewa ta nufi side ɗinDaddy, "yanzu wai Mairah dama ɗiyar sister Insu ce!" Mihna tace cike da mamaki, "gashi ma kinji
tabbaci" Hamid yace tare da miƙewa yayi na shi ɗakin....
"Ku kuma yaushe ku ka dawo?" Kausar tace tare da bin su Asma dake ƙoƙarin zama a diningchair's da ido, murmushi Nabila da ta zauna ta saki tare da faɗin "mun jima da dawowa" hararanta Yasmin tayi tare da faɗin "maƙaryaciyar banza, wato ke Nabila ba za ki bar ƙaryabako!Yaushe ku ka dawon! Ina ce yanzu ku ka shige, ko an ce muku ban ga shigowan ku ba ne?" Taidda maganan idonta akan Nabila da ta ɓata fuska....
"Wai ma me ya zaunar da ku har wannan lokacin a can ne? Tun safe fa ku ka fice" Lubabatutaceidonta na yawo a saman fuskokin su, ɗago kai Asma tayi a marairaice tare da faɗin "ba mujimaba kam, amma dan Allah ku yi haƙuri wallahi mun tsaya tsara yanda mukeson wajen ya kasancene" tace kamar zata saki kuka, harara Kausar ta dalla mata tare da faɗin "aikin ku ne kenan?" Girgiza kai tayi tare da faɗin "a'a mun dai nuna musu yanda muke son ya kasance ne" "wallahi kushiga hankalin ku, in ku ka yi wasa wallahi zamu soke duk wani event's da ku ke zakwaɗinyi, banda rashin sanin darajar kai da ciwon sa ku ɗau ƙafa ku fice tun safe ba ku ga yakamata kudawogida ba se wannan lokacin" Yasmin tace a harzuƙe...
"Allah ya baku haƙuri" suka ce bakuna a haɗe ganin su Jabir sun doso wajen, dan sun sansukatadda zancen ba ze ƙare yanzu ba, "to wai event's nawa ma zaku yi?" Lubabatu tace tare dazaranplate, kallon ɗaya daga cikin masu aikin da ta matso dan serving ɗin Lubabatun Hajiya tayi cikeda dattako tace "kira su Nafisat a ciki" ganin ba ta gane inda maganan ya dosa ba yasa A'ishasakin murmushi tare da faɗin "baƙin da aka yi" jinjina kai tayi a girmame ta wuce dan kiransu....
"Ranar Wednesday dai suka ce za'a fara" Asma tace a hankali, "be yi wuri ba kuwa?" Yasmintacetare da kallon ta, "wallahi Mahmah be yi ba, mu gani muke yayi kaɗan" Nabila ta cafke zancencike da rawar kanta, harara Kamil ya zabga mata tare da kauda kai, zare ido tayi tare da saddakai dan ta manta sun iso wajen...
"Barkan ku da dare uncle's" Fadila tace tare da sakin musu murmushi, "barka kun dai" Jabir daAbubakar suka amsa fuskoki washe da murmushi, gaidasu Asma da Nabila suka yi a girmame, amsawa suka yi da kulawa, "ina Ibrahim ɗin?" Hajiya tace tare da kallon su, "gani Hajiya" yacetare da iddasa ƙarisowa ya ja kujera ya zauna.... Murmushi ta sakin mai tare da faɗin "daga wajen mutumin na ka ka ke?" Murmushi ya saki tareda bin Lawiza da ta iso wajen da ido, "ina jinku" Yasmin tace tare da baza musu ido, "saturdayza'agama" Fadila tace a natse, "yayi yawa, kwana goma ana abu guda bakwada hankali ne!" Tacetareda kauda kai, shagwaɓe fuska suka yi cike da magiya, murmushi Alhaji Jamil ya saki tare dafaɗin"barsu su yi abinda suke so Auta, kar dai a saɓawa mahalicci a yi komai cikin taka tsan-tsan"
jinjina kai suka yi cike da farin ciki, tare da Nafisat da Sa'eed me aikin ta dawo, da sauri Ibrahimya riƙo hannun Sa'eed ya zaunar da shi a kujeran kusa da shi, murmushi Nafisat ta saki taredajan na kusa da Kausar ta zauna a natse, kai a ƙasa ta ɗaga musu gaisuwa, amsawa suka yi fuskoki
washe da murmurshi....
"Kun kulle kan ku a ɗaki kamar wasu baƙi" Yasmin tace idonta akan Nafisat da natsuwartakeburgeta, murmushi ta saki tare da ƙara ƙasa da kai, dan ba ta san me zata ce mata ba, murmushi
Hajiya ta saki tare da faɗin "ku daina zama a ɗaki ku kaɗai, ku fito ga mu nan mu yi hira" jinjinamata kai tayi
cike da girmamawa...
"Saka musu abinda suke son ci" Hajiya tace tare da kallon ɗaya daga cikin masu aikin, da sauri tazari plate ta matsa gefen Nafisat, "me za a saka?" Tace a girmame, girgiza kai tayi fuska faɗaɗeda murmushi tare da faɗin " bari zan saka da kaina" tayi maganan tare da amsan plate ɗindakehannunta, kallon Hajiya tayi cikin rashin sanin abinda za tayi, murmushi Hajiya ta sakinmatatare da faɗin "bari tunda ta hutashshe ki" jinjina kai tayi ta ja baya, a natse ta saka musutuwomiyan kuɓewa ɗanye ta turawa Sa'eed na shi ta ja nata, wanke hannu suka yi suka fara ci anatsecike da ladabi, bin su kawai suke da ido ganin yanda suke komai a natse....
Sauke numfashi A'isha tayi tare da kallon Hajiya a natse tace "ba za'a kira ta ba?" Murmushi tasaki tare da faɗin "ina da tabbacin zata sakko" jinjina mata kai tayi ta maida ga abincin gabanta, kallon Ibrahim Lawiza tayi da ɗin bin mamaki, dan tunda su Nafisat suka fito ta cika da mamaki, dan ba ta yi zaton an bar ko mutum ɗaya ba, maganan A'isha kuma ya ƙara mata mamaki akanwanda take ciki....
INSU..
Kuka tayi sosai wanda ya gigita tunaninta ita da kanta, tana cikin sassauke ajiyan zuciya barci
yayi wuf da ita, ba ta samu farkawa ba se da kiran sallahn magrib ya shiga kunnuwanta, miƙewatayi addu'a ɗauke a bakinta, bin ɗakin da ido tayi kafin ta dira daga saman gadon tayi toilet, batajima sosai ba ta fito ɗaure da babban tewol ƙarami yafe a saman kanta da alamu wanka tayo.... Gefen da dressing mirror yake ta yi a natse babu wani garaje, jan stool tayi ta zauna ta ja lotionta fara shafawa cike da natsuwarta, tana gamawa ta miƙe ta ja stool ɗin baya kaɗan ta ɗaubodyspray's ta feshe jikinta da shi, wuce wa dressing room tayi a natse ba ta jima ba ta fito sanyedadogon hijab, wuce wa inda praymat yake tayi ta kabbarta sallah ta maida natsuwanta
ɗungurungum ga mahaliccinta.... Bata bar wajen ba se da ta sallaci isha'i, tana idar da azkhair ta miƙe a natse ta koma dressingroom ba ta jima ba ta fito cike da burgewa, sanye take da riga da siket, rigan milk colour medogon hannu, an tattara baza a gaban shi yanda ya ƙara ƙawata shi, siket ɗin brown colour, mefaɗi ya hayo har saman cikinta, sunyi matuƙar amsanta kaman a jikinta aka ƙirƙiroshi, ta ƙawatakwalliyan da baby hijab brown da yaji stone a saman kanta, hannaye sun ji ado yanda ya kamata, ɗaukan wayanta dake yashe a saman gadon tayi ta saka plat shoes dake gefe ta fice a natse...
"Kaman na san wannan fuskan" Nabila tace idonta akan Nafisat, "ba ki santa ba" Yasmintacetare da kallon ta, "a'a taya zaki ce ba ta santa ba, hotunan su dake sama na lafiya ne" Lubabatutace tare da kallon ta, "tabbas kuwa zaki santa" Yasmin tace tare da jinjina kai, "ƙanwar Insuceme bi mata" Lubabatu ta kuma cewa a natse, zare ido suka yi gaba ɗayansu cike da mamaki, "badai Nafisat ba!" Asma tace a ɗan tsorace, "ita, dama kin santa ne?" A'isha tace da mamaki, "nasanta Mommy kun manta mun je bikin Antynsu?" Asma tace cike da mamaki, "anyi haka kuwa, na manta ne" tace tare da sakin murmushi....
"Lallai Nafisat ta zama babba" Fadila tace tare da sakin murmushi, murmushi Nafisat ta saki tareda sadda kai cike da nauyi, nufo wajen ma'aikaciyan dake saɓe da Mairah a kafaɗa tayi daazamasaboda kukan da take, da sauri Jabir ya miƙe ya ja kujeran da yake kai baya ya nufeta, "meyasameta!" Yace a ruɗe tare da miƙa hannu, kauda jiki tayi da sauri tare da ƙara ƙarfin kukanalamunba ta son ya taɓa ta, murmushi Hajiya ta saki tare da kallon Nafisat da duk hankalinta yayi wajen, "tashi ki amsheta" tace cike da dattakonta, ba musu ta miƙe a natse ta nufi wajen, miƙa matahannu tayi tare da sakin mata murmushi da sauri ta miƙa na ta cike da farin cikin samunsassauci, lafewa a ƙirjinta tayi tare da sassauke ajiyan zuciya....
"Oh Allah dama ƙiwiyane ya sata kuka haka!" Yace kaman ze saki kuka, dariya suka saki ganinyanda yayi da fuska tare da bin shi da ido, murmushi Nafisat ta saki ta koma inda ta tashi tazauna a natse ta cigaba da cin abinci, "wow! Wannan kyakykyawan yarinyar fa!" Nabila tacetareda kai hannu, ƙanƙame Nafisat tayi tare da ɓata fuska, "ku daina taɓa ta dan Allah tunda bataso, in ta saki jiki ba ma se kun miƙa mata hannu ba zata zo da kanta" A'isha tace cike da damuwadakukan da take yi, "yarinyar waye Mommy?" Asma tace idonta akan Mairah dan ba ƙaraminkyauta mata ba, "ƙanwar ku ce" tace murya cike da farin ciki, "ƙanwa!" Tace da mamaki, "daughternSSB ce" Kausar tace cike da alfahari, "what!" Suka ce bakuna a haɗe ido waje, dariyan yandasukayi su Abubakar suka saki tare da kallon su, "Insu ce ta haifeta!" Lawiza tace a mugun rikice, jinjina mata kai Ibrahim da ya kalleta yayi a natse murmushi faɗaɗe a saman fuska, "Alhamdulillah" tace tare da sakin hawayen da ba ta san lokacin da suka taru ba, murmushi yasaki tare da maida idon shi akan Mairah....
"Uncle SSB! Wannan yarinyar shi ce da gaske! Insun da muka sani ita ta haifeta!" Fadila tacearikice tare da miƙewa zumbur, murmushi Hajiya ta saki tare da faɗin "zauna Fadila" "HajiyadanAllah da gaske!" Tace a ruɗe, ƙaran sakkowa daga stair's ya hana Hajiya ba ta amsa suka maidahankulan su ga gefen wajen tare da zuba ido.... A natse ta sakko idonta akan wayan da take daƙila, "Insu!" Suka ce cikin ɗin bin mamaki tareda
tashi suka nufeta a guje suka faɗa jikinta cike da kewa tare da ƙanƙameta, murmushi ta saki tareda basu masauki cike da na su kewan da tayi....
Zame jiki suka yi a natse saboda maganan da Alhaji Jamil ya musu akan su saketa ta ƙarisotaci
abinci, murmushi ta sakin musu cike da yanayinta tare da faɗin "oh ƴan matan Hajiya ne sukahaɓake haka!" Ta idda maganan cike da nuna mamaki cikin yanayinta, hararanta Asma tayi tareda faɗin "ke da ki ke da ƴar budurwa ba'a ce kin girma ba se mu ko?" Kame fuska tayi taredabanka mata harara, dariya suka saki cike da nishaɗi tare da bin ta da ido, "zo zauna ki ci abinci karki tankasu" Hajiya tace cike da kulawa, murmushi ta saki ta wuce a natse taja kujeran dakekusada Nafisat ta zauna...
Ƙarisowa wajen Lawiza tayi da niyyan saka mata abinci, ɗaga mata hannu tayi tare da faɗin"nahutashshe ki kar ki wahalar da kan ki a abinda baki da ra'ayi" murmushi suka saki gaba ɗayansusaboda fahimtar abinda take nufi, kauda kai Ibrahim yayi fuska faɗaɗe da murmushi, Lawizakuwa zaran plate tayi ta fara serving ɗinta, "ni dai ba ruwana kar ya zo me ke ya harare ni, bani
na saki ba" tayi maganan a dai-dai lokacin da Lawiza ta ja baya daga gefenta saboda gamazubamata da tayi, gyara zama tayi a natse ta gutsiri tuwon takai baki a hankali, lumshe ido tayi tareda faɗin "wow! Abinci duniya ne, Allah ya ma hannun da ya dafa abincin nan albarka" "amen" suka ce cike da nishaɗi....
"Wai dama har yanzu Insu ki na son abinci!" Asma tace da mamaki, "ai ni da suwalo akwai
ƙaƙƙarfan amintaka" tace tare da sakin murmushi, "menene suwalo kuma!" Nabila tace taredaƙureta da ido, "auh baki san suwalo ba!" Tace tare da kama haba, jinjina kai tayi tare da faɗin"wallahi ban san shi ba" "suwalo ashshi mutum" Sa'eed yace tare da sakin murmushi, dariyanyanda yayi maganan suka yi gaba ɗayan su tare da zube mai ido, murmushi Nafisat ta saki tare
da faɗin "abinci shine suwalo" "oh Allah!" suka ce cike da mamaki....
Kamo hannun Mairah da ke ta ɗagawa alamun tana son zuwa wajen Insu Nafisat tayi taredafaɗin "Ammi ta na son zuwa wajenki" ɗago kai tayi ta zube mata ido tare da faɗin "mintsilintaki
ke?" Girgiza kai tayi tare da sakin murmushi, "oh" tace tare da kauda kai, murmushi ta kumasaki
dan ta san ba zata yarda ta ɗauketa ba, ko a gida se an cika mata ido take ɗaukanta tuntanajaririya ma, kwaɓe fuska Mairah tayi tare da ƙoƙarin sakin kuka, "Insu amsheta mana, kar tayi
kuka" A'isha tace cikin muryan rarrashi, da mamaki ta ɗaga kai ta kalli Mairahn da ta taɓefuskawani sukunannen kallo ta baza mata tare da kauda kai, cif tayi ta lafe a jikin Nafisat se dai idontana kan Insun, guntun murmushi Hajiya ta saki tare da tuno shuɗaɗɗun lokuta....
A haka suka kammala dinner
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 68 Chapter of 109