za su fusataba, kallon Insu SSB yayi cike da tambayan yaya za'ayi, kara bakinta kusa da wayan tayi tare dafaɗin"uncle Jabir please ka samu natsuwa tukun"....
"Insu kar su afka musu su kashe su, zamu yi asaran abubuwa da yawa, sannan ba zamu samudaman kama jama'an dake ƙarƙashin su ba kin sani" yace cike da damuwa, "na sani ba zamubari
hakan ta faru ba, da farko a ninka tsaro a inda suke, in sha Allah Nafsii ze yi magana da manemalabarai yanzu dan kwantar ma jama'a ƙasa da hankali, zasu ba mu haɗin kai wajen gudanar daabun da muka sa a gaba" "shikenan bari in sa a turo su" yace tare da katse kiran....
Juyawa da dubanta kan SSB tayi tare da faɗin "Yaya Samir be da dama me kuma ya saki?" Murmurshi ya sakin mata tare da faɗin "zo mu kimtsa tukun daga baya maga koma me yasaki" ya idda maganan tare da cicciɓanta suka yi toilet....
Tare suka tsarkake jikinsu suka fito, kimtsata yayi kamar ko yaushe cikin sutura na mutunci
wanda ya bayyana kamalanta da haibanta, temaka mai ta yi ya kimtsa cikin sutura me nuni dawaye shi, banda zuba ƙamshi ba abinda suke, a tare suka fito hannu cikin na juna, kai tsayeparlorn tattaunawa suka nufa, suna shiga jama'an dake cike a ciki suka mimmiƙe, murmushi yasakin musu tare da wuce wa a natse ya zaunar da Insu saman one seatern dake kusa da twoseater's, ganin ta dai-daita zamanta ya sa shi sakin mata murmurshi ya wuce two seater's yazauna cike da kame girman da Allah ya ba shi.... Gaishe shi suka fara cike da girmamawa amsawa yayi a natse ba tare da garaje ba, gaida Insusuka yi a girmame amsawa tayi a mutunce, ganin duk sunyi shiru kowannen su ya sadda kai yasashi sakin guntun murmurshi tare da faɗin "mu gabatar da abinda ya tara mu ko" ba mususukasaita camera's, matsawa ɗaya daga cikinsu yayi ya saka mai mic a wuyan riga cike da girmamawaya ja gafe, gyara zama Insu tayi idanta akan shi.... Gyara murya yayi idan shi akan camera's ɗin tare da ɗaga musu sallama, cike da ƙwarewaasarrafa harshe yace "iyayena, ƴaƴana, yayyina, ƙannina, tashin hankali baya magance ɓarna, sedai ya ƙara ta'azzara shi, mulkin mu ba na zalunci ba ne, na adalci ne, alƙawari muka ɗaukaaidanun ku na zamu tsaya ma ko wannen ku tsakani da Allah, zamu zame muku bango majingina, ba zamu taɓa bari wasu su cutar daku mu zuba ido ba, ɗaukan hukunci a hannun ku ba nakubane, ku ƴan gata ne, kamata yayi ko wannen ku ya koma gida ya kwanta ya huta hankali kwancedan kuna da masu kula daku" yana kai nan ya tsahirta tare da gyara murya....
"Ku ahalina ne, ba zan taɓa bari ɗayanku ya nemi ruguje rayuwarshi ba, rayuwarku me tsadaneagare mu da kan ku, munji koken ku kuma mun ɗau muku alƙawari akan ba zamu huta ba har sekun samu adalcin da ku ke nema, matasa kune ƙashin bayan al'umma, ba a irin wajajennanyakamata mu ganku ba, muna baku haƙuri akan abinda ya faru, sannan muna muku albishir dagwamnati za ta buga dasu dan bi muku haƙƙin ku" yana kai nan ya haɗe hannun shi guri gudatare da zuba ma camera's ido, kashe camera's ɗin suka yi a girmame fuskoki washe, "a bazawannan ɗaukan tun daga yanzu dan matasan ƙasa su gani" Insu tace a natse idanta na yawoakan su, "to Ma!" Suka ce cike da amsan umurni, "madallah" tace tare da kallon SSB, murmushi
ya sakin mata tare da miƙewa ya miƙa mata hannu, kamawa tayi suka wuce a natse, da idosukabi su cike da burgesu da suka yi.... Kai tsaye office suka wuce, suna shiga ko zama ba su kai gayi ba Jabir ya ƙwanƙwaso ya shigo, daido suka bi shi kaman a ranar suka taɓa ganin shi, "an aikata duk abinda ki ka ce, se yanzunaɗansamu sassauci, dan in suka kashe mutanen nan mu suka cuta" yace tare da miƙa ma SSBipat ɗindake hannun shi, amsa yayi ya wuce saman sofa riƙe da hannunta, suna zama ya kunna taredabaza ido.... Muggan makamai ne baje a gaban su ana fasalta inda za'a shishshigar, sun bayyana a ɗaukantarmuryoyinsu ya bayyana ras, ɗago kai SSB yayi tare da faɗin "good job!" "Ai bayanin da ya rattafaa karkashin videon shine ya ƙara jan hankali dan ya bayyana duk wasu baƙin kasuwanci dasukesuna wa jama'a basaja" "yanzu ya maganan zaman?" Insu tace tare da kauda kanta daga wayan, "yana nan a gobe in sha Allah" "Allah ya kai mu" tace tare da miƙewa ta fice a natse.... Gyara zama Jabir yayi tare da faɗin "mutanen nan fa sun rikice" "tukunna" yace tare da sakinguntun murmurshi, "yanzu menene next?" "Shugabarku ce zata wakilci zaman ƙarƙashin
tsayawa gwamnati ita da sauran lawyer's ɗin da ta zaɓa dan temaka mata akan abun, a tattaramata komai a miƙa mata" jinjina kai yayi cike da gamsuwa tare da faɗin "za su ci gidansu, kuraza'a bawa ajiyan nama" murmurshi me sauti ya saki tare da faɗin "ina takardun gwangilolindaaka kammala?" "Suna office" "okay kar ka manta ka tuna mun kafin in shiga wani abun" "inshaAllah" yace cike da girmamawa, "to ta shi ka koma wajen baiwar Allah ko" yace tare miƙewa, murmurshi me sauti ya saki tare da faɗin "kar ka mun wani alaye, kai dai da baiwar Allahkejiramaza hanzarta" murmurshi ya saki me cike da ma'anoni tare da faɗin "ban san sa'ido" "ai ni
makaho ne a wajen nan" yace tare da miƙewa zuciya ƙal, dan ya jima da fahimtar SahabeeSadamna gab da dawowa....
Comments fans🙏🥰
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Sixty Seven
"Bismillah, bismillahnku!" Jabir dake tsaye a bakin ƙofar shiga parlorn tattaunawa na sirri yacetare da nuna ma Alhaji Namadi da zugan shi hayan, ba musu suka shishshige cike da dakiyanfargaban dake dukan zukatansu.... Murmurshi SSB dake zaune saman sofa yana bin su da ido ya saki cike da girmamawa taredamiƙewa a girmame ya fara ba su hannu, ba musu suka mimmiƙa na su, suna kammala gaisawayakoma ya zauna tare da zuba musu ido, "please a kawo musu abin taɓawa" SSB yace a sakeidanshi akan Jabir dake tsaye a bakin ƙofa, "okay sir" yace tare da yunƙurin fita, "a'a bar wannanranka yadaɗe ba na jin akwai wanda ze buƙaci wannan a cikin mu" former president yaceadake, shiru SSB yayi tare da zuba mai ido, murmushi Alhaji Namadi ya saki tare da faɗin "duk a ƙoshemuke, da za su ba mu wuri ina ganin hakan kaɗai ya ishe mu"....
Ya yi maganan cike da ƙwarewa a sanin makaman yaudara, murmurshi SSB ya saki tare dafaɗin"ai ba abin ƙoshi ba ne na taɓawa ne ranka yadaɗe" ya tsahirta fuska ɗauke da murmushi taredakallon Jabir, "ku ba mu waje please" jinjina kai yayi ya ma SSG magana, tattara yaranshi yayi
suka fice cike da bin umurni.... Murmurshi Alhaji Aminu da former president suka saki tare da gyara zama, ido SSB ya zubamusu cike da kallon ina jinku, gyara zama Alhaji Namadi ya yi tare da faɗin, "da farko dai zantuna maka wani abu wanda kaman kana shirin sha'afa dashi dan darajarshi be kai ka mantabamr president, kujeran nan da ka ke zaune a kai mu muka yi dalili da sanadin hawan da ka yi, kai ataƙaice zan ce mu muka ɗaura ka, mu muka zaɓeka ka hau ba jama'an ƙasa da ka ke yawanfaɗaba, inda ba mu baka goyan baya ba ba ka isa kusantarshi ba ma bare a kai ga hau, kamantadukwani abu da ka mana ya wuce kamar yanda muka manta ya wuce mu fuskanci gaba, abindayakawo mu gare ka abu ɗaya ne zuwa biyu, duk abinda ake maganganu akai mun san kana ji kumakana gani, ba ma da lokacin zargi ko da hannunka a ciki, wannan sana'a daka gani shine mu, bawani batun ƙunbiya-ƙunbiya ko ƙaryatawa, da wannan sana'a daka gani muka dafa maka har kahau kan mulkin ƙasan, kar kace zaka mana wasa da rayuwa shine rayuwar mu, ka cire hannunkaka rufe idanka sannan ka toshe kunninka, ka bar mu da duk wani me jin ɗan iska ne, munadamaganinsu"....
Tunda ya fara koro bayanin SSB be kauda idan shi daga kan shi ba se da ya dasa aya, guntunmurmurshi ya saki tare da faɗin "kayi magana me ma'ana ranka yadaɗe, se dai ka mancedaabuguda, ni Sahabee Sadam ban roƙi ɗaya daga cikin ku akan ya goya mun baya in hau mulkinba, kuda kan ku kuka roƙen akan in zo in hau ƙasa na buƙatana, ƙoƙon bara ku ka miƙo min na amsabani na miƙa muku ba, bana da matsala daku, bana takun saƙa da ɗaya a cikin ku, matsalataalƙawarin da na ɗauka ga ƴan ƙasa ne akan zan tsaya musu a ko wani abu da ya taso, kumazancika musu wannan alƙawari in sha Allah, zanyi faɗa da koma waye dan tabbatar musu da ubaneni na gari abin alfahari"....
"Ba lusari ba ne ni kaman wannan da zaku yi ƙoƙarin juyani" yayi maganan tare da nuna formerpresident, "Alhaji Namadi ban nemi jin sana'anku ba ko akan me ku ke samun kuɗin shiga, nadai
yi alƙawarin tsaftace Ɓadamayo daga dukkan dattin dake ciki, kar ka yi tunanin in aiki ya biyotakan ka zan ɗaga maka ƙafa, matuƙar ka kasance datti a ƙasata se na shareka, idan wannannedalilin zuwan ku gare ni, ina ganin zaku iya tafiya dan ina da abubuwan yi masu mahimmanci dalokuta na" ya idda maganan tare da ɗaga musu hannu fuska a muttuke.....
"Waye kai da har zaka faɗa mana wannan maganganun! In ma giyan mulki ne yake ɗibankatokasani kafin ka sha duk mun sha, shine shugabanmu gaba ɗaya, kuma shine me faɗa kowa yaji aƙasan nan har da kai dole se ka ji!" Alhaji Aminu yace a harzuƙe tare da miƙewa cike da ɓacinrai, kallon sakanni SSB ya mai kafin ya miƙe a natse cike da natsuwan shi ya nufi ƙofa, da sauri
security's ɗin da ke tsaye a wajen suka buɗe ƙofan tare da sunkuyar da kai cike da girmamawagare shi, "su fita a share a kulle" yayi maganan a dake tare da wuce wa a natse, da sauri suJabirsuka dafa mai baya.....
Cike da ɗin bin mamaki su Alhaji Namadi suka bi shi da ido, ba su san tsaurin idonshi ya kai har
nan ba, lallai akwai aiki a gaban su, wato tsayawa kallon ruwa suka yi ba su sani ba gwaɗonashirin yi musu ƙafa, ba su kai ga idda tunanin abinda ke gab da faruwa da su ba muryanSSGdaketsaye da muƙarrabanshi ya daki kunnuwansu, "bismillahnku" yace a dake ba tare da ya kalli ɗayadaga cikin su ba.... Kallon juna suka yi cike da ɗinbin mamaki dan komai na shirin ƙwace musu, sauke numfashi
Alhaji Namadi yayi tare da miƙewa a zuciye ya nufi ƙofa da sauri suka dafa mai baya jikkunanaɓari, taɓe baki SSG yayi tare da umurtan wasu daga cikin yaran shi su rakasu har se sungaficewan su....
"Amma mutanen nan ba ma su da kunya sam" Abubakar yace a zuciye, "se mu nuna musuranshi
kunyan su nafila ne na mu ne faralin" Insu da ta shigo office ɗin tace tare da wuce wa indaSSBkezaune zuciyanshi na tafarfasa, kamo hannun shi tayi bayan ta zauna tare da faɗin "Allahyahuci
zuciyan ɗaya tamkar da dubu, zakin Insun farko da na biyu, Allah ya huci zuciyan babanFarisat
kuma ɗan Farisat" murmushi ya saki cike da samun sassauci tare da rumgumeta, murmushi suAbubakar suka saki cike da yaba hankali da sanin yakamatan ta....
Se da ya gamsu dan kan shi sannan ya cikata tare da jawota jikin shi sosai, ba wanda ya nunaduhun kai a cikin su, dan ɗabi'un na su ya isa ya zama jiki a gare su, "yanzu me ne ne mafita, mutanen nan barin su suna free a yanzu matsala ne" Jabir yace cike da damuwa, lumshe idoSSByayi cike da gajiya da abun kafin yace "dama dole su shiga hannu yanzu" "ta yaya?" Yace taredagyara zama....
"Yanzu duk hojjojin nan dake hannun mu uncle Jabir tambayan ta yaya ka ke! Ai mun wucewannan wajen" "bangane ba Insu" yace cike da san ƙarin bayani, ganin yanda suka zuba mataidoya sata faɗin "na sa Yaya Samir ya turawa masu kula da handame dukiyan kasa da babakereaccount ɗin da ko wannen su ya mallaka tare da tiriliyoyin dake ciki, na biyu na tura ma masukare lafiyar ƙasa hujjojin ta da zaune tsaye da suke saka ƴan barandar su suke yi, na ukunaturama masu kare ta'addanci a ƙasa hujjojin ta'addanci da suke sawa ake yi, na hudu na tura mamasu haƙƙi akan kare ƙasa daga shigowan miyagun ƙwayoyi da kayan maye da makamai hujjoji
akan shigowan da suke da su, yanzu haka na san suna gab da shiga hannu" ta idda maganantareda baza musu ido fuska cike da murmurshi....
"First lady! Lallai ke ki ka cancanci a kira da wannan sunan daughter" Alhaji Munnir yace cikedafarin ciki, murmurshi SSB ya saki tare da matse hannunta, "nagode" tace cike da jin daɗi, "yanzumenene a gaba?" Abubakar yace idan shi akan su, "mu ba su lokaci zamu ji kyakykyawan
albishir" tace tare da bin su da ido, "saboda ba sa da kunya har da maka barazana, lallai mutanennan zasu gane kuskuren hakan da suka aikata" Jabir yace rai ɓace....
Calm down uncle Jabir, gan-gan da ta kusa fashewa zaƙi ne da ita" tace tare da sakin ƙaramar
dariya, murmurshi ya saki tare da faɗin "na yarda da hakan daughter" murmurshi suka saki cikeda farin ciki....
"Na faɗa maka wannan mutumin na da hannu akan komai, tunda ka ji haka daga gare shi tokarka yi mamakin shi ya ke mana saran ɓoye" Alhaji Aminu Siman yace a harzuƙe cike da ɓacinrai, "yanzu ba lokacin tada hankali ba ne, lokacin neman mafita ne, tunda mun san hakan wani
mataki yakamata mu ɗauka kafin ruwa ya sha kan mu?" Vice president yace a tsorace, "wannnashine" former president yace tare da kallon su, gyara zaman Alhaji Namadi yayi tare da faɗin"mafita guda ne, dole mu ɓacewa idan ƙasa a yau zuwa wani lokaci kafin komai ya gama caɓewa, yaron nan na da wani manufa a zuciyan shi" "wannan gaskiya ne, mamber's suka ce cike datsoron da ya firgita zukatansu....
"Ina muka nufa?" Ɗaya daga cikin shugabanni yace tare da baza mai ido, girgiza kai yayi taredafaɗin "ba ƙasa guda zamu ba, barbazuwa zamu yi dan kar su gano wani abu" be ƙarishe abindayake niyyan faɗi ba aka banko ƙofan tare da shigowa ciki a gurguje aka baza musu bindiguasaman ka, buɗe ido suka yi a firgice suka baza akan jami'an efcc dake tsatstsaye fuska ba wasa...
"Lafiya!" Alhaji Aminu yace murya na rawa, "lafiyar zata wanzu ne in ku ka ba mu haɗinkai" ɗayadaga ciki yace murya ba wasa, "sunana agent Kabir S Alkali, muna buƙatan ku a office dan
bincike akan wasu abu da muke zargi, in ku ka ba mu haɗin kai zamu tafi lau, in ku ka yi gardamazamu tafi jau" ya idda maganan idan shi na yawo akan fuskokin su, buɗe baki vice president yayi
da niyyan magana ɗaya daga cikin su yace "ka rufe bakin ka, ku tashi muje" haka suka mimmiƙejikkuna na ɓari suka fice da su.... Ɗago wayanta da saƙo ya shigo Insu tayi tare da zube ma screen ɗin wayan ido, wani
nagartaccen murmurshi ta saki tare da faɗin "ƙurunƙus!" Tayi maganan tare da ɗago kai, kallonme ke faruwa suka mata, "sun kamu, bari mu tafi tevel two, one ya kammala" tace tare dadannanumber Samir.... Yana ɗagawa tace bari mu shakata Yaya Samir" dariya ya saki tare da faɗin "na tausayawawandaki ka sawa ido baby Insu" murmushi ta saki tare da faɗin "gamamu" tayi maganan tare da maAbubakar alamun ya kunna tv, ba musu ya kunna ya jona duk abinda ya dace ya matsa a wajen, nan take idansu yayi tozali da su Alhaji Namadi dake zazzaune a ɗakin bincike na hukumar efccido a warwaje, murmurshi SSB ya saki tare da kallon Insu dake sakin murmushi....
Tambaya suke musu akan account's ɗin da suka buɗe a wajen ƙasa da cikin ƙasa, se dai kowannen su yaƙi yarda ya amsa yana da alaƙa dashi, murmurshi Insu ta saki idanta akansu, jagefe ɗaya daga cikin jami'an yayi tare da danna kira ya kara a kunni nan take wayan Jabir yaɗaururi, da mamaki yake bin number da ido, "bani uncle Jabir kira na ne" tace tare da miƙa mai
hannu, miƙa mata yayi ba musu cike da mamaki, ɗagawa tayi ta saka a speaker tare da faɗin"inaji" "ranki shi daɗe sun ƙi amsa suna da alaƙa dashi" yace a girmame, "to shikenan juya mususystem ɗin dake gaban jami'in ku" tace a natse, da mamaki ya dubi systemɗin nan take yafaradube-dube a wajen, murmushi su Jabir suka saki hankula kwance....
"Aikata abinda na umurce ka mana!" Tace a ɗan zafafe, "I'm sorry Ma!" Yace da sauri tare dajuyamusu, katse kiran tayi tare da ɗaukan wayanta ta kara a kunni cike da yanayinta tace "sasuaduhu Yaya Samir" murmurshi Samir ya saki tare da maida hankalin shi kacokan akan aikin...
Cikin sakannin da ba zu gaza ashirin ba kuɗaɗen account's ɗin suka fara sauka a guje, cikedarazani suka baza ido a firgice, ɗago kai ɗaya daga cikin member's ɗin yayi tare da faɗin "meyehakan!" "Me ya ta da hankalin ka? Ina ce ba me alaƙa da su anan?" Jami'in yace hankali kwanceidan shi akan fuskokinsu, girgiza kai yayi a rikice tare da faɗin "na mu ne, goben mu da nayaranmu ne!" Rumtse ido su Alhaji Namadi suka yi cike da firgici, dariya su Jabir suka kwashe dashi
yayinda SSB ya bi su da murmurshi me bayyana farin cikin da yake ciki.... Danna numbern jami'in Insu tayi fuska faɗaɗe da murmurshi ja gefe yayi ya ɗauka a girmame, "ɗayansu ya amsa Ma" yace a girmame, "okay a tambayesu ta hanyar da suka samu waƴannankuɗaɗen, sannan a shigar da ƙaran a court zuwa gobe, ku tabbata kun kammala komai a yau" "insha Allah Ma" yace a girmame tare da saurarawa dan jin me za ta kuma cewa jin ta katse kiranyasa shi komawa inda suke.... Datse gamin Samir yayi tare da faɗin "na tura miki saƙo ɗazu ki duba" "okay" tace tare da saukewayan, "yanzu za su miƙa su ga jami'an kare ta'addanci ne ko?" Alhajin Munnir yace tare dakallon ta, girgiza kai tayi tare da faɗin "mun sanar da su ne dan su yi rige-rige, duk wandabesamu daman kamawa ba ze shigar da ƙara court ka ga abubuwan sun musu yawa, ganinhakacourt zata yanke haɗe shari'an waje guda, ka ga se mu samu daman fiddo da abubuwandakeɓoye dakyau" cike da ɗin bin mamaki SSB ke bin ta da ido, ya rasa gane a ina ta samo dabarundatake amfani da su, lallai masu irin fikiranta se an duba ɗaya ce tamkar da dubu....
"Wow!" Jabir yace cike da yabawa, miƙewa tayi tare da faɗin "uncle Abubakar Mairah taceagaidaka ina ga kai ne kaɗai ban idda ma saƙon ba" murmurshi ya saki tare da faɗin "ɗazuYasminta haɗani da ita, nace tana so ta dawo tace "eh" murmurshi ta saki tare da faɗin "mu ba maso, mun bar musu ita gaskiya" harara ya dalla mata tare da faɗin "tunda ke keda ikon zartar dawannan hukuncin ba" "ah! Abun har da ƙagewa ne!" Tace tare da kama haɓa, "kin ci sa'a manamiki da sauƙi saboda ina cikin farin ciki da se kin ji wanda yafi haka" dariya ta saki tare da ficewaa a natse...
"Tabbas samun mace na gari me hangen nesa da kaifin tunani rabo ne, SSB yau zan faɗa makadaƙarfin gwiwa ta akan ka samu mace fiye da yanda ka ke so, ka samu mace fiye da yanda kakera'ayi, ka samu mace fiye da Insiyyat, da na ce ba zaka taɓa samun mace kamar Insiyyat baammayau na soke wannan zancen na ce ka samu mace fiye da Insiyyat" Jabir yace idan shi akanshi, murmushi ya saki tare da faɗin "ina sonta fiye da yanda na so Insiyyat, ina sonta friend's!" Yafurta maganan murya tcike da amo tare da bin fuskokin da ido, murmurshi suka saki cikedagamsuwa na su idan akan shi.... A natse ta shiga cikin parlorn ganin Hajiya zaune ita da Anisa ya sata faɗin "Aniy fira ake waHajiya?" Tayi maganan tare da neman waje ta zauna, "magana dai take sani, abokiyan hirantayi
nisa" murmurshi Insu ta saki tare da faɗin "wannan wani hira take Hajiya? Daga murmurshi sedariya" "a hakan dai" tace tare da bin ta da ido, "to ai sun kusa dawowa, suma sun ƙosa" tacetareda sakin murmurshi, "ah ina goyan baya kuwa" tace cike da gaskiyanta, dariya insu ta saki taredabin ta da ido....
"Ya maganan mutanen na ku? Akwai wani abu me mahimmanci ne!" Ta idda tambayan taredabaza mata ido, jinjina kai tayi tare da gyara zama, "Anisa jeki amso Insiyyah ƙarama a wajenLawiza" Hajiya tace tare da kallon ta, ba musu ta miƙe ta wuce a guje, murmurshi Insu ta saki
tare da kora mata bayanai, "ma sha Allah! Allah ya temake ku, yaushe za'ayi zaman court ɗin?"
"Wannan zamu jira Hajiya, Alkali shike da wannan hukuncin" "Allah ya nuna mana tunda suna
hannu ai da sauƙi" tace cike da farin ciki, murmurshi Insu ta saki tare da faɗin "ya jikin BabahMauden kuwa?" "Yanzu Lamunde ta fice ta tabbatar mun da sauƙi" "to Allah ya ƙara matasauƙi" tace cike da kulawa...
Tunda ya shigo ɗakin yake baza ido, ba abinda idonshi ke mararin gani se ita, buɗe ƙofanbanɗaki
tayi ta fito sanye da rigan wanka, murmurshi ya saki tare da nufarta gadan-gadan, ɗaukantayayi
ya ɗaga sama tare da faɗin "idaniya sun samu abincin su" murmurshi ta saki tare da ƙanƙameƙafaɗun shi, sakko da ita yayi tare da faɗin "wa Mrs SSB ke shirin tarba haka?" Farr tayi daidotare da faɗin "sirri ne" murmurshi ya saki cike da ɗaukan natsuwan shi da tayi tare da janhannunta ya ja stool ya ajiye ta, kai kan shi saman ƙafaɗanta na dama yayi tare da ƙureta daidota mirror, murmurshi ta saki me yalwa idanta akan shi tare da faɗin "idan Mrs SSB ta ɗausabuluta silla a jikinta to kowa ya sheda dan SSB tayi" murmurshi ya saki me faɗi tare da faɗin"menakeji ne haka a kullum! Kar fa ya tsaidamun da fitan numfashi na" juyowa da sauri tayi ta ja stool ɗinbaya tare da miƙewa ta rungumeshi ƙam-ƙam cike da tabbaci, tace "idan fitan numfashinkayatsaya ka sani tare da na Insiyyah ze tsaya, ƙarfin gwiwan fitan numfashin Insiyyah na taredafitan numfashinka ne" murmushi ya saki me yalwa tare da faɗin "ki ɗauka hakan take ga
Sahabee Sadam Ɓadamayya" ƙanƙameshi tayi da ƙarfi cike da tsan-tsan ƙaunarshi dake
fizganta....
Comments fans🙏🥰
🫀MUGUWAR TSOKA 🫀
{🫀TA'ARE KALLUƊE}
[Muscle Cramp🫀]
) عضلة سيئة (
🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_
https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466
written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم
By
Yardajjiya👩 💻
Page. Sixty Eight
Sakkowa take daga stairs sanye da baƙin abaya da ya fiddo madaidaicin cikin jikinta, kantasanyeda baby hijab fari wanda ya sakko mata har kafaɗa ya ƙara haskaka kwalliyarta, banda zubaƙamshi ba abinda take, fuskan nan kamar ko yaushe ɗauke da murmushin da ya zame matajiki....
Da fuskokin dake ɗauke da murmushi da ƙaunanta suka bita har ta idda sakkowa, kai tsayeindaHajiya ke zaune ta wuce fuska cike da ƙauna, buɗe mata hannu tayi ta shige jikinta, shafa kantatayi a natse tare da faɗin "Allah ya baki nasara, yasa ki fara a sa'a, kar ki ɗagawa magautaƙafa"
jinjina kai tayi tare da zare jiki, murmushi Alhaji Jamil da Kamil suka sakin mata, murmushi tasakin musu tare da faɗin "zamu haɗu a can ko" "sosai kuwa" Kamil yace tare da sakin matamurmurshi, jinjina kai tayi tare da faɗin "Hajiya se na dawo, kowa se na dawo" ta idda maganantare da sakin murmushi ta juya, "Allah ya dawo dake cikin amincin shi" cikin sautin dake ɗaukeda murmushi da jin daɗi tace "Amin"...
"Ammi Allah ya bada sa'a ya dawo dake lafiya" Anisa tace tare da bin ta da ido, murmushi takuma saki wanda suka jiyo sautin shi tare da faɗin "amin Aniy" ta idda amsawa tare da ficewadaga parlorn, da sauri security's suka dafa mata baya, tun da ta sako kai haraban side ɗinidantaya wanke da fuskanshi dake kan kofan fitowa, murmushi ta sakin mai tare da nufar shi cikedakarsashi... Murmurshi ya saki tare da takawa a natse suna gab da juna ya buɗe mata hannu shigewa tayi
tare da ƙanƙameshi, ganin sun ɗau
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 107 Chapter of 109