Share this page
da SSB tayi tare da sakin musu murmurshi, "da ki tsayaki ƙara samun sauƙi, kar ki ce zaki tafi a haka" Lawiza tace cike da damuwa tare da bin yandaduktarame da ido, girgiza kai tayi tare da faɗin "my body is recovered, don't worry" ta idda maganantare da ɗaukan jakanta ta saɓa a baya, kallon Hajiya tayi tare da faɗin "Ibrahimna jirana senadawo" tayi maganan murya a sanyaye tare da sadda kai, miƙewa tayi cike da kulawa tare dafaɗin "ko za ki jira mu tafi tare gobe, wataƙila ki ƙara samun ƙarfi, ba wani ƙarfi ne dake baInsiyyah" tayi maganan cike da kulawa, murmushi ta saki tare da faɗin "I'mfeeling goodHajiyadon't worry, zan iya" bin ta kawai tayi da ido ba tare da tace komai ba, dan kowa ya gantayasanƙarfin hali kawai take, juyawa tayi a natse ta kama hannun akwatin, "kawo" Lawiza tace dasauri tare da kai hannu, murmushi ta sakin mata tare da sakin hannun akwatin cike da farin cikintemakonta da za tayi dan ta tabbata ta cigaba da ja za'a fahimci ƙarfin halin da take yi.... Kallon SSB dake zaune kaman baya wajen Hajiya tayi tare da faɗin "a haka zamu barta ta tafi! Dubi fa ka ga yanda take tafiyan kamar ana janta" murmushi ya saki tare miƙewa a natse, "let her go, she will be okay, ko ta zauna anan ɗin zuciyarta na can" yace a natse tare da takawayabi bayan su, da sauri Hajiya ta dafa musu baya, a parlor ta tadda su suna shirin ficewa, "Insiyyah!" Tace da ɗan ƙarfi, juyowa Insu da zuciyanta ya kasa barinta sukuni tayi tare da baza mata ido, ƙarisowa tayi da sauri tare da faɗin "bari Fadila ta zo ku tafi tare" murmushi ta saki tare dajinjinamata kai, "please take your medicine on time" ta kuma cewa cike da kulawa, murmushi tasaki tare da jinjina kai, juyawa da sauri tayi dan kiran Fadila, "muje kafin su fito" tace a natse taredakallon Lawiza, jinjina mata kai tayi suka fice daga parlorn, sauke nannauyan numfashi SSBdaketsaye a saman stairs yana kallon su yayi tare da juyawa a natse ya koma sama.... Tunda suka idar da sallah suka shirya kayan tafiya, fitowa sukayi janye da akwatuna, cikedamamaki Babiya tace "ina zaku haka!" "Ɓadamayya" Farisat tace murya a shaƙe, "ku ba masonrashin hankali ko za'a Ɓadamayyan dake za'a Farisat! Gobe ne fa ɗaurin aurenki" Lailahtacetareda kallonta, girgiza kai tayi zuciya a matuƙar ɓace tare da faɗin "ƴar uwata na can cikinwani mawuyacin hali ku kuma kuna kawo mun wani maganan aure! Insu ne fa ke cikin halin rayuwakomutuwa, ba wanda ze ce ga halin da take ciki amma kuna mun maganan gobe ɗaurin aure, matuƙar auren ze shiga tsakanina da ganin halin da ƴar uwata ke ciki na haƙura, na fasa bazanyi auren ba" ta idda maganan zuciya ɓace a matuƙar kausashe, zare ido suka yi gaba ɗayansusaboda kalamanta na ƙarshe ya fita a dai-dai lokacin da Salman da su Ummi suka shigo... Murmushi Salman ya saki ganin yanda suke kallon shi tare da faɗin "ni kaina hakan ne a gareni, matuƙar auren ze shiga tsakanin mu da ganin halin da Insu take ciki to mun fasa" ya idda maganan idon shi ƙyam akan Farisat dake kallon shi, "kar ku maida mu ƴan iska mana" Ali dayashigo riƙe da sandan da yake temaka mai wajen tafiya yace tare da banka musu harara, girgizakai Salman yayi tare da faɗin "Yaya Ali gaskiyan kenan, zamu je mu ga Insu, a ɗaga kawai" "sukuma waƴanda aka gayyata kuma muyi yaya da su!" Yaya dake tsaye a ƙofar da ze sada shi daside ɗin shi yace idon shi akan su, sadda kai suka yi a dalabce dan ba su ga idon magana ba, "baabinda za'a fasa" yace a natse tare da fara takowa ciki, "Alhaji Abdussamad ai ba wani abubanehakan, in dai za su samu gamsuwa" Daddyn Salman yace cike da dattako duk da na ciki naciki, "ka daina magana kaman yaro mana Alhaji Abubakar" Babiya tace tare da kallon shi, "tubanakeHajiya" yace cike da girmamawa.... "Yaya dan Allah to a barmu mu je muga halin da take ciki" Salman yace cike da magiya, "bawanda ya hanaku ai" yace a natse tare da zama a saman one seater cike da dakiyan da ya aroyayafawa kan shi, "mun gode" yace cike da farin ciki, ɗago kai Farisat tayi ta kalleshi tare damai alamun nagode da ido, murmushi ya sakin mata tare da mata alamun babu komai, kamoYasminSalwa tayi tare da faɗin "zo zauna, se 11 jirgi ze tashi yanzu kuwa 8:30 ta buga, mu jira" zamatayi ba tare da tace komai ba, zuciya da hankali na ga Insun su, 9 da wasu mintuna su Shureimsukashigo bakuna ɗauke da sallama, amsawa suka yi a natse cike da farin cikin ganin su, bayangaishe-gaishe da su ka yi, Annur ya kora musu bayani game da time ɗin da jirgi ze tashi, bawanda ya iya furta ko A se jijjiga kai kawai da suke, "Nafisat yi musu iso dining" Lailah tacedakulawa, "Alhamdulillah" suka ce cike da jin nauyi, "nan ma ai gida ne" Khadijatu tace taredakallon su, murmushi kawai suka saki ba tare da sunce komai ba, "to Sadamkai su gardensujiradan naga kaman a takure suke anan" Habiba tace da kulawa, ba musu Sadamda idonshi yaƙan-ƙance saboda tsaban kuka ya miƙe suka da fa mai baya.... Tsayawa me taxin da ya ɗakkosu yayi a bakin babban gate, sauka tayi a natse ta ba shi haƙƙinshi, sakkowa Fadila da Asma da Nabila da suka yi ta roƙon Hajiya akan suma za su har da koke- kokensu suka yi, murmushi ta sakin musu tare da faɗin "mun iso" "gunda da muka iso, ashetafiyan babu sauƙi" Asma tace tare da kallon Insu kamar zata saki kuka, ƙaramar dariya tasaki tare da zaro pass ɗinta ta ƙarisa ga su Ema, miƙa ma wanda ke tsaye a bakin gate tayi taredazube mai ido, zare ido yayi tare da ɗagowa a mamakance, "Insu!" Yace tare da sakin dariya, "yesIdris" tace tare da sakin murmushi, "ku shigo sannun ku da zuwa" yace cike da farin ciki, amsanpass ɗin tayi ta ma su Fadila dake ta bin su da ido magana suka shigo, nan da nan sauransecurity's ɗin suka ƙariso wajen, gaba ɗaya mamakin yanda ta ƙara girma suke, ramewandatayi ya ƙara mata tsayi da tsayin fuska, hancin nan ya ƙara tsayi wala-walan idanunta sun ƙarafitowa, "nagode" tace tare da wucewa da sauri ganin za su ɓata mata lokaci su Asma suka dafa matabaya... "Lokacin ma baya tafiya yanda ya kamata" Nafisat tace tare da kallon agogo, murmushi Yayadaya koma ya shiryo tsaf ya saki tare da faɗin "ze yi gudu ma Nafisat kar ki damu" jinjina kai tayi tare da maida dubanta ga agogo cike da fatan lokacin ya cika, miƙewa Yasmin tayi tare dafaɗin"ku muje, gunda lokacin ya cika muna can" kama kai Lailah tayi ganin ta nufi ƙofa tare da faɗin"Yasmin saura kusan awa ɗaya fa, haka zamu je muyi ta zaman jira? Dawo in yayi saura 20minute's se muje" tayi maganan da ɗan ƙarfi, wannan shi ya ja hankulan su Sadamdake gardensuka yo ciki, "lafiya!" Salman yace a tsorace tare da kallon Ummi da Daddy, "Yasmin ce ta ƙosa" tace cike da tausayawa, "wai muje can mu jira" Salwa tace tare da kallon Shureim, "ina gakumuje can ɗin, zata fi samun kwanciyar hankali" Shureim yace a natse tare da nufar kofar databi wanda ze sadasu da tsakar filin gidan, tana gab da isa Insu da ta gama zolayan Baba Kallataturoƙofan fuskanta yalwace da murmushi ta shigo baki ɗauke da sallama, cak Yasmin ta tsayatareda baza mata ido cike da tsoro, "oh baby zo ki rumgumeni mana" tace cike da yanayinta tareda buɗe mata hannu, "rungumeni dan Allah rumgumeni baby" ta kuma cewa fuska yalwace damurmushi, sakin wayanta tayi a guje tayi kanta ta rumgumeta ƙam-ƙam tare da sakin ƙaƙƙarfankuka.... A razane suka yo wajen gaba ɗayan su, ja gefe Shureim da ya ga komai yayi ya basu waje fuskayalwace da murmushi, kowa ya isa se ya tsaya sake da baki yana bin su da ido, faɗawa jikinsuFarisat da Nafisat suka yi tare da sakin na su kukan, haka suka yi ta rerawa cike da kewa dafargaba, "wash ƙirjina baby's" Insu tace cikin danne kukan da take da ɗan sauti, "ku sake tahaka"Sadam yace tare da fara zare su, nan suka saketa suka koma gefe suna kuka tare da bintadaido, "ban fa mutu ba, da raina" tace dan fahimtar sun ji halin da take ciki tare da goge hawaye, rumgumeta Sadam yayi tare da faɗin "shiii, mutuwa ba yanzu zata zo ba" dariya ta saki taredarungume shi ƙam-ƙam... Sakinta yayi tare da kamo hannunta ya nufi gaban Yaya da ya kasa tsaida hawayen idanunshi, "oh Allah kun ga kun sa Yaya kuka" tace tare da goge hawayenta a fakaice ta shige jikinshi, "Allah ya cigaba da kulawa dake" yace tare da rumgumeta ƙam-ƙam, haka suka bi ta sukayi tarunguma suna zubda hawaye me cike da ɗin bin ƙauna da tausayawa da kewa, "oh sarauniyaNafisat cika ni haka kar ki sa in tintsire" tace tare da sakin murmushi ta share hawayendasukazubo mata a natse.... Sakinta tayi tare da faɗin "ba na ɗau alhakin da ba na wa ba, kin zon kenan, sarki da baka munji daɗi" ta idda maganan tare da dungure kanta ta saki dariya tare da goge hawaye, "da na dawofa?" Insu tace fuska yalwace da murmushi, "se muka ƙara jin daɗi" tace tare da bin ta da kallonƙauna, "oh sarauniya Nafisatu shiyasa nake mutuwar sanki" tayi maganan tare da sakindariya, "ga su chairman ku gaisa" Balarabe yace tare da nuna mata su Shureim dake tsatstsaye a gefesuna bin su da ido, "oh Allah gaskiya ni ƴar gatace, har da zugan ƴan Aminan juna a tarbata" taidda maganan tare da takawa ta nufi inda suke, murmushi kawai suka sakin mata cike da farincikin ganinta cikin ƙoshin lafiya, "Yaya Annur amma amaryarka ta haihu ko?" Tace tare dakafeshi da ido, "oh Allah ba tambayar lafiyata kawai se ki jefo mun tambaya?" Yace tare da kamahaɓa, dariya ta saki tare da waiwayawa ta inda Shureim yake tare da faɗin "uncle ShureimdanAllah menene lefin wannan tambayan nawa? Ai wannan tambayan ya haɗa komai" "Babu" yace tare da sakin murmushi, dariya yawancin su suka saki tare da bin ta da ido, tsagaita dariyaAnnuryayi tare da faɗin "eh an samu Muhammad Shureim" "wow Allah yasa ya gaji hali da dabi'unamesunan, dan gaskiya Chairman ɗinmu adali ne, ka ga fa duk da nayi mute ɗin ku bana tare daabinda ku ke be hana ya tattaroku kun zo tarbata ba" ta idda maganan cikin yanayinta, murmurshi kawai suka saki tare da bin ta da ido.... "Oh Allah da baƙi fa nake! Ina suke?" Tace tare da fara dube-dube, "gamu a nan" Fadila dasukawa kan su masauki a three seater's tace tare da ɗaga mata hannu, "ka ga ƴan gari, kun burgeni" tace tare da sakin dariya, daga ido tayi ta sauke a kan Yaya dake bin duk wani motsinta daido, murmushi ta saki tare da kauda ido da sauri ta maida ga jama'an parlorn.... "Zo ki zauna" Salwa tace tare da riƙota, "zan zauna har kwanciya ma zanyi tukun na amma, inaSa'adatu me? Na ga kowa banganta ba" ta idda maganan tare da kallon su, "ta bar gida" Sahabeeyace tare da goge hawaye, "tabar gida!" Tace tare da kallon Yaya, "zauna tukun ki huta seakoramiki labari" Lailah tace tare da ƙarisawa ta riƙota, "please ku faɗamin me ya faru da ita? AmananAnty ne kar ku manta, ya za'ayi ku barta ta fice ba tare da ɗayan ku ya tsaidata ba?" Ta iddamaganan cike da ruɗu, "ta zaɓi tafiya riƙe ta zamu yi?" Farisat tace cike da takaici.... Girgiza kai tayi tare da faɗin "no Farisat, meyasa za ki ce haka! Sa'adatu ce fa, ɗaya daga cikinmu, ƴar uwan da Allah ya ba mu" "ba ƴar uwarmu ba ce! wacce tayi Yunƙurin halaka mana ababendamuke matuƙar so ba zata taɓa zama ɗaya daga cikin mu ba, ko da kuwa a ce mahaifiyarmucetaɗau nauyin cikinta ta sha azaban naƙuɗar haihuwarta mun yafe ta" Yasmin tace a zafafe taredawatsawa Insu kallon me cike da gargaɗi, "Yasmin" Balarabe yace tare da riƙota, dan kowayasantana da haƙuri, amma inta birkice ba kasafai ake gane mata ba, shiyasa fushi be kasance ɗabi'arta na ko da yaushe ba.... Ƙari sawa inda take Insu tayi a natse tare da riƙota cikin rawar murya me haɗe da zuwanhawayetace "Yasmin yau da bakin ki ki ke furta waƴan nan kalaman! Sa'adatun ki ce fa, wacce ki kafi kowa shaƙuwa da ita" ta idda maganan tare da rungumeta ganin yanda jikinta ke ƙyarma, fashewa da kuka tayi me ciwo tare da faɗin "ba Sa'adatun da muka sani ba ce, wannan watacedaban, ta tarwatsa duk wani ƙauna da nake mata, ta ruguza duk wani yarda da muka mata, tasaremu sara mafi muni, ta tafi ta bar mana wani tabo a zuciya wanda har mu mutu ba zamumanta da shi ba, ita ce silar wannan ramar da na gani tare da ke, ita ce silar jinyar Anty natsayinwata uku, ita ta zaɓi tafiya ta bar mu ba tare da mun mata komai ba" ta idda magana a raunanetana kuka me taɓa zuciya, ɗagota Insu tayi da mamaki tare da faɗin "waya faɗa miki haka! Ni ciwo na ne ya tashi, sannan bana jin Sa'adatu zata iya cutar da Anty.".... "Ita ce sila, ta canza miki magani lokacin da za ki tafi makaranta, da bakinta ta furta" Sadamyacetare da kafeta da ido, "what!" Tace da mamaki, tare da tuna bayanin da Ibrahimya mata akanabinda doctor yace, "to meyasa!" "Saboda banzan dalilinta mara amfani, wai Sudais ɗinAntyGude yace yana sonki" Salman yace a zafafe, murmurshi ta saki tare da goge hawaye "Allahyakyauta yanzu ina take?" "Ta na can tana amsan hukunci akan abinda ta aikata" Nafisat tacetareda kallon ta, "kar ku wani damu kan ku, shi ciwo ko ba sanadi kan iya riskan mu, bare kumanawada kowa ya sheda ze iya tashi a ko da yaushe, Allah ya shiryeta ku barta ta tafi tayi rayuwarta, nayafe mata, kar ku azabtar da ita saboda ni" tana kai nan ta wuce ɗakin Yasmin a natse idonashatatan ruwan hawaye, bin ta da ido suka yi ko wa da kalan mamakin da yake yi, kallonShureimYasmin tayi tare da faɗin "a saketa amma kar ta tafi haka kawai" tana idda maganan ta bi bayanInsu.... Comments fans🥰🙏 🫀MUGUWAR TSOKA 🫀 {🫀TA'ARE KALLUƊE} [Muscle Cramp🫀] ) عضلة سيئة ( 🌙 *MOONLIGHT WRITER'S ASSOCIATION*🌙 _We shine all over the world_ https://www.facebook.com/profile.php?id=100094397072466 written and Created ~~~~~~~~~~~~~~ ِبسم الله الرحمن الرحيم By Yardajjiya👩 💻 Page. Thirty six Buɗe ƙofan ɗakin shi yayi a hankali ya fito tare da kauda fuskanshi gefe saboda kallon da Gudedake zaune saman tabarma a saman barandar parlornta ta bi shi da shi, "ai dole ka kauda kai, dama duk bugun ƙofar nan da yaran nan suka yi kana cikin ɗakin nan Sudais ka ƙi buɗewa! Watolamarinka kullum ƙara gaba yake ko? Daga rashin sallah a jam'i ka koma ƙin sallahn gabaɗayako?" Ta idda jera mai tambayoyin cike da takaici, ɗaure fuska yayi saboda su Nafi dake zazzaunetare da faɗin "banji ba ne" "dama ina fa zaka ji, ka kwankwaɗi abinda yafi ƙarfin kayin ka badoleka ƙi ji ba, wallahi in baka gyara rayuwarka ba babu wahalallan da ze bar na shi rayuwar yazauna gyara naka, sallah! ace a kira sallah har a tada baka ba dalilinka, ina hankalce da kai tunjiyadada daddare da ka dawo gidan nan ka shige baka fito ba se yanzu, ba subhi ba Azhar ba la'asar gamagrib muna fuskanta" ta idda maganan a zafafe.... "Wai waya ce miki banyi ba!" Yace tare da kallonta a zafafe, "zo ka doke ni ne se in san na hasalaka, kayi kuwa, tunda kayi a gidan ubanka" ta idda maganan a kausashe, "kai Momy wallahi ki na da matsala, ni duk ba wannan ba, an kira ki daga gidan uncle Abdussamad?" Ya iddatambayan tare da jan kujera ya zauna a kusa da ita.... Ko ci kan ka ba ta ce mai ba se juyawa da tayi ta ma Nafi magana, "kinji Momy?" Yace cikedaƙosawa, "to akan wani dalilin za su kiran? Ka ga suna buƙatan ganina ko jinana ne a taronsu?Karka nemi ɓata mun rai, na dai bi yarinya da fatan alheri daga nan, shima dan ya zame mundolene, in ba haka ba ai se dai in zuba ido" ta idda maganan cike da jin zafin rashin faɗa mata bikindaakayi.... "Ni ba wannan ba, ba su kira sun faɗa miki wani abu ba?" ya kuma cewa a ɗan hasale, kallondaƙiƙu ta mai tare da faɗin "ba su kira ba, menene?" Shiru yayi cike da fargaba kafin yace"jiyaneSa'adatu ta kashe Insu" ya idda maganan cike da tsoro, da mamaki ta zabura tare da faɗin"kisa!"Maido hankula kansu su Nafi suka yi da ɗokacin firgici, "wallahi" yace a hankali, "waya faɗamaka!" Tace a ɗan rikice, "kinji ki ke kuma abinda a gaban mu komai ya faru" yace cikin sonkauda zancen, "na san Sa'adatu ta daɗe da barin gidan, ba kuma wanda ya san inda take, kafaɗamin gaskiya har yanzu kana tare da yarinyar nan ne?" Ta idda maganan cike da zargi, "yanzuseSa'adatu ta iya ɓacewa ganin su dan Allah, to sun gano har can muka je, kuma ta amsa lefinta, yanzu haka tana hannun sojoji, maganan ina tare da ita kuma wannan kin fi kowa sani tundaidonki a kaina yake" ya idda maganan idon shi akan ta... Sauke numfashin samun sassauci tayi tare da faɗin "Allah me iko, yanzu har za'a yi mutuwasukasa sanar da ni, to su suka jiyo Allah ya gafarta mata, ita kuma wannan yarinya aya gudaAllahya saukar musu akanta, in suna da fahimta se su gane, na jima ina nunashshesu tsintacciyar mage ba ta mage, amma se a nuna ban kan dai-dai, to ga wacce ke kan dai-dai nan ai sungani daidanunsa".... "Akan yarinyar nan wani ɗiban albarka ne Amina ba ta mana ba, har korana ta taɓa yi a gidantadan na ce yarinyar soyayyun idanun ne da ita irin na riƙaƙƙun ƴan bariki, daga ƙarshe ga shinanta kashe mata ɗiya, ai duk sanda kace tsintacciyar mage ce mage ka shiga uku, dan ma Allahbeƙaddara mata gani da idanta ba" ta idda maganan babu wani damuwa tattare da ita, "to a inataga Insun!" Nafi tace tare da kallonshi, harara ya banka mata ya kauda kai... "A'a ke kuma ba ta zo bikin ƴar uwanta ba" Gude tace tare da kauda kai, "ba ta zo ba, Hasenat tace ba ta riga ta zo ba" Halima tace tare da kallon Nafi, "kai duk kun isheni da wani batuntazoda ba ta zo ba, taya zata ganta ta kasheta in har ba ta zo ba?, ta zon kenan tunda ku ka ji hakan, ba ni ma waya inji yanda ake ciki" ta idda maganan tare da kallon Nafi ba musu ta miƙe tashigeta ɗakko mata wayan ta bata ta koma wajen zamanta ta zauna.... "Momy na shirya akan batun auren nan, wallahi ko wacce ki ka zaɓamun zan aura" Sudais yaceasanyaye tare da kallon Gude, tsayawa daga yunƙurin danna kiran da take tayi cike da zallanmamaki tare da faɗin "yau kuma!" Jinjina kai yayi tare da kallon ta, murmushin farin ciki tasaki tare da faɗin "ka kyautawa kan ka, da tuntuni ka maida hankali da yanzu ka daɗe da wucewajen, bari zan bincika yanzu tunda Dadynku ya ruguza na wajen yarinyar Jummai, ko in ce kunhaɗukun ruguza" ta idda maganan tare da danna number Jummai ta kara a kunni.... Tun daga nesa ta danna musu video tana tafe tana sakin murmushi me haɗe da dariya, Yayadasu Ali ne tsaye sun saka Farisat a tsakiya suna mata ruwan liƙi, yau father's day na bikinta, tana ƙarisowa wajen Yaya ya juyo da liƙin kanta, miƙawa Balarabe wayan tayi ta fara juyi cikinsassanyan kiɗan da aka saki, ihu jama'an dake zazzaune a gefen wajen suka saki cike da jindaɗi, nan ruwan liƙi ya fara tashi akanta, shigowa Yasmin da Nafisat suka yi cikin irin shigarta taredataya ta taka rawa, banda fidda ƙayataccen murmushi babu abinda fuskan Yaya ke yi, binsuyakeda idanun da ke cike da tsaban so da ƙauna... Zamewa tayi ta fice tare da sauke numfarfashi me haɗe da hakki da sauri Balarabe ya riƙotatareda faɗin "Are you okay!" "Yes" tace tare da ɗagowa ta sakin mai murmurshi, "mu gani muntarwatsa taron" tace fuska yalwace da murmushi tare da amsan wayanta dake hannun shi, murmushi ya saki tare da jawo mata kujera cike da kulawa yace "zauna kar kuma na ƙara ganinki a cikin filin" dariya ta saki idonta akan wayan hannunta tare da faɗin "ranar Yaya ne fa, inbanshiga ba wa ze shiga?" "Na dai faɗa miki" yace da ƙarfi, murmushi ta saki ba tare da tace komai ba.... "In taya ki zama?" Fadila da ta ƙariso wajen tace tare da kallonta fuska yalwace da murmushi, "me ze hana" tace tare da matsa mata na ta fuskan cike da murmushi, zama tayi a natse taredabin su Farisat da ido, "da ki ke Ɓadamayya ba kya jin kewan su?" Tace a natse idonta akansu, ɗago kai tayi ta kalli inda take kallo tare da sakin murmushi, maida idonta kan wayan hannuntatayi tare da faɗin "matuƙar kewa" "dole, tattare suke da so da ƙauna da shaƙuwa" tace a natse, murmurshi ta saki tare da faɗin "ba musan wani abu ƙunci ba a gidan mu se da Anty ta tafi tabarmu, shima na kwanaki mu kayi muka maidashi cikin zukatan mu muka birne, muka wanzar dafarin ciki a saman fuskokin mu, dan amsan jarabawar mahaliccin mu da hannu biyu, farinciki dakwanciyar hankali shine taken ahlinmu" ta idda maganan tare da ɗagowa ta kalleta, jinjinakai tayi tare da faɗin "na tabbatar da hakan a saman fuskokin ku, amma meyasa ki ka hana a ɗaumataki akan wacce ke yunƙurin ɗaura ƙunci a fuskokin da ke cike da farin ciki?" Ta jefa matatambayan idonta ƙyam akan na ta, guntun murmushi ta saki tare da miƙewa a natse, cikinyanayinta tace "ki ɗauke ki a matsayinta zaki samo amsa" ta idda maganan tare da shige filintazaro damin kuɗi a aljihun doguwar rigan jikinta ta fara liƙa musu tana liƙin tana sakin murmushi, ba su tashi a wajen ba se da kiraye-kirayen sallahn magrib ya fara shiga kunnuwan su.... "Ke Jummai zo ki ɗauki wayanki ya dame ni, shiyasa bana so ku bar wayoyinku a kusa dani, abu yayi ta damun ka da ƙara, dama kuna sashi a shiru ne amma haka zaku ware ƙara in an kiraƙarahar saman kayi" Babiya tace cike da takaici, "yi hakuri Hajiya, ban tsammaci kiran kowa baneshiyasa" Jummai tace tare da ɗauka ta zauna kusa da ita ta buɗe wayan, ganin wanda ta kirayasata faɗin "Anty Gude ne ma kusan 5 missed call Allah yasa lafiya" tayi maganan tare da karawayan a kunni.... Da sauri Halima ta miƙa mata tare da faɗin "tana kira" amsa tayi ta ɗaga ta kara a kunni taredafaɗin "haba Jummai meyasa duk lokacin da za'a buƙace ki ba za'a same ki ba ne!" Ta idda maganan cike da ɓacin rai, da sauri Sudais da ke shirin fita ya taka burki tare da juyowa yazubamata ido.. "Yi haƙuri Anty Gude wallahi ba na wajen ne shiyasa" Jummai tace cike da damuwa, "shikenan, dama ba jimawan nan Sudais ke faɗa min wai wannan yarinyar da Amina ta bawa daraja fiyedakowa ta kashe Insu, haka ne?" Tace babu ko wani damuwa tattare da muryanta, "a'a ba takasheta ba, ga Insu nan tana ta hidimanta, yanzu haka dawowan mu kenan daga fili, kin san yaunefather's day na shagalin bikin Farisat" ta idda maganan murya a sake, "oh to Allah shi kyauta" tace tare da katse kiran, "me tace Momy?" Nafi tace cike da tsoro, harara ta banka mata tabatawayan tare da faɗin "ka dinga neman ingancin labari kafin ka ƙaras, lafiyanta lau, tana canmatana tiƙan rawa" ta idda maganan tana jin ba daɗi a zuciya, "wow! A soke maganan nemanmatanaure, sirikar ki na cikin aminci" Sudais yace cike da farin ciki ya sa kai ya fice, "wawa, wallahi komutuwa zaka yi Abdussamad ba ze baka wannan da yake jin tafi kowa ba, kai ko su Balarabebayarda za su yi ba" ta idda maganan a zafafe.... Fesa body spray's tayi a jikinta ta ɗau baby hijab ta sanya a saman kayan barci ta fice a natsetashiga kitchen, "Baba Mari dare yayi tsayi fa ko anan zaki

Chapter 50 of 109