tun fitowanta tare da faɗin "barka da hutawa Hajiya" "yawwa Nafisat yau da
makarantar ne?" Girgiza kai tayi tare da faɗin "se wednesday in sha Allah" "ah lallai munsamuhutu" tace cike da nuna zallan farin ciki da hakan, gaida sauran tayi cike da natsuwanta tayunƙura ta nufi Iƙilima, murmurshi ta sakin mata tare da faɗin "sannu da zuwa" "yawwa Nafisat
dama kina ciki?" Murmushi ta saki tare da faɗin "eh" ta miƙawa Mairah hannu, kamawa tayi tasaɓa ta ta juya ta koma ɗaki....
"Ita dai ba ta gajiya da keɓance kanta!" Kamil yace tare da kallon Hajiya, "sabo ne kawai tafi jindaɗin hakan, ko ta zauna anan takura kanta za tayi, musamman ma da ku ke zazzaune wataƙilain imu-imu ne ta sake" murmushi ya saki tare da faɗin "zata haƙura ta sake ne ma tunda babusirikinta a cikin mu, yawwa Dr ta kirani ɗazu tace in faɗa miki Asma sun taso wai jikin natayaƙi
daɗi" "toh! Jikin be saketa ba ne har yanzu!" Jamil yace tare da kallon shi, "haka tace" "inagashine dalilin da yasa har yanzu bata iso ba, Allah ya bata lafiya, dama tun lokacin da aka sanar darashin lafiyan na ce su dawo haka, mijin yace "ba damuwa jikin be ta'azzara ba" Lubabatutaceidanta akan Alhaji Jamil "Allah dai ya bata lafiya" Jabir yace cikin san katse batun, dan yasangaba zata iya karyo wani zancen....
"Ku jera su a madaidaicin dining ɗin kawai" Insu dake tafe da ma'aikatan dake ɗauke da treynabubuwan da ta saka su ka shirya tace tare da wutowa cikin parlorn, zama kusa da uncle Kamil
tayi tare da faɗin "wash na gaji!" Ta yi maganan a marairaice, "sannu daughter dole ki gaji ai, kozirga-zirgan nan kaɗai ya isa ya gajiyar dake" murmurshi ta saki tare da faɗin "thanks unclenaAnty Hasinat" murmurshi ya sakin mata me faɗi tare da kauda kai....
"Me aka ma Mairah take kuka haka daughter?" Alhaji Jamil yace idan shi akan Insu, ɓata fuskatayi cike da rashin damuwa da abinda zata faɗa tare da faɗin "shagwaɓa ne kawai da taɓarauncle Jamil" "a'a me girma first lady, kin bincika ba wani canjin yanayi ta samu ba?" Abubakar
yace cikin taren numfashinta....
"Ba ko ɗaya uncle Abubakar haka ta tsira yi a kwanakin nan, kuma wiya zata sha ni ba ruwana, tana girma tana komawa yarinya, wannan taɓaran bata nuna shi ba ma da take ƙarama seyanzu"tace cike da takaici, murmushi Lawiza da ta shigo riƙe da maidaidaicin trey ta saki tare dafaɗin"ba wani nan ke ce dai ki ke taɓaran ba ita ba, menene lefinta a ciki dan ta farka ba ta ga kowaa
kusa da ita ba, sannan ai har yanzu yarinya ce ba babba ba" ta idda maganan tare da ajiyetreynasaman center table ta juya....
"Wai tsaya dama barci ta tashi ba ta same ki a ɗakin ba?" Jabir yace tare da gyara zama, turabaki
gaba tayi tare da faɗin "Uncle Jabir rabu da batun Anty Lawiza neman magana take kawai" "a'aInsu" yace cike da rashin jin daɗi, saurin jawo wayanta da ya ɗau ruri tayi ta ɗaga a hanzarcetakara a kunni, "okay ku shigo kawai" tace tare da miƙewa ta zare wayan, kallon Hajiya tayi taredafaɗin "su Yaya sun iso Hajiya!" Ta idda maganan a zumuɗe, murmurshi Hajiya ta saki me yalwatare da faɗin "Alhamdulillah!" Tayi maganan tare da miƙewa, mimmiƙewa suka yi dan zuwamarabtansu....
Suna gab da ƙarisawa kofan general parlorn Yasmin dake gaba ita da Sahabee da Umar sukashigo baki ɗauke da sallama, cike da mamaki Insu ta ja ta tsaya cak dan ba ta san da su za'azoba, kafin ta fita daga cikin shock Samir da Salman da Yaya da Sadam da Hajiya Babiya sun kawojiki, da gudu ta faɗa jikin Yaya tare da faɗin "dama da su zaka zo Yaya!" Murmurshi ya saki taredabata masauki me kyau cike da ƙauna....
"Ba ma son taɓara" Salman yace tare da banka mata harara, "Yaya ka ga Yaya Salman ko!" Tacetare da goge hawayen farin ciki da suka zubo mata, "ina ga mu yakamata mu koma ba'a marabada mu" Samir yace tare da kama baki, fiddo ido tayi cike da razani tare da sakin dariya, "ehmanababy Insu babu marabanku, babu ku iso" yace tare da sakin murmushi, "to ai ku ƴan gida ne, baƙi
ake wa iso" tace tare da kamo hannun Umar, murmushi Alhaji Jamil ya saki tare da miƙawaYayahannu cike da mutumtawa, kamawa yayi a mutumce suka fara gaisawa, "Hajiya Nafi mujeciki
kar ki ce na barki a tsaye kafanki ya sage" Insu tace tare da riƙo hannunta, "na nawa kuma, sedai
kar a kuma" tace tare da sakin murmushi suka rankaya suka nufi ciki....
Nan suka shiga gaggaisawa cike da mutunta juna, kafin wuce wan wasu mintoci an cika musugaba da ruwa da abubuwan taɓawa, "Uncle ba magana" Insu tace idanta akan Sahabee dakenema ta inda ze hango ɗan uwan shi, murmushi ya saki cike da nauyi yace "ina Mairah da
Sa'eed?" Murmurshi Iƙilima ta saki tare da faɗin "yana makaranta, Mairah na tare da Nafisat, Umar je ka can ɗakin ka kirawota ta zo su gaisa ma" ta idda maganan tare da nuna mai bedroomɗin ta da hannu, ba musu ya miƙe ya wuce....
"Ina ga lokacin ɗaura auren ya gabato ko, yakamata mu halarci wajen da wuri" Yaya yace taredakallon uncle Jamil, murmurshi ya sakin mai tare da faɗin "an maida ɗaurin auren ƙarfe 2" kallonshi yayi da ɗan shakku kafin yace "lafiya dai ko!" Murmurshi ya saki tare da faɗin "lafiya lau, danku na nesa-nesa ku iso ne dama" murmurshi ya saki tare da faɗin "to ma sha Allah" "yaudai
gamu ga Yaya Samir da ake ta cika mana kunnuwa da labaran shi, Yaya Samir ɗin mu kaza, YayaSamir ɗin mu yayi kaza, Allah dai ya sa muna daga cikin masu rabon ganin shi" Nabila tacefuskacike da murmushi, murmushi Samir ya saki tare da faɗin "ni ma dai duk an bani labarin kumusamman baya goya marayu da masu uba me girma adalin shugaban mu" ya idda maganancike da girmamawa, guntun murmushi SSB da tun bayan gaisawa da suka yi ya ja bakinshi yatsuke ya saki tare da mai kallon sekonni....
"Mu ba ta baka labarin mu ba ko?" Abubakar yace tare da sakin mai murmushi, kallon tsaf yamajerin su kafin yace "ai ku labarin ku tun kan ta zo duniya ake bani" bin shi da ido suka yi cikedamamaki, "Anty ita ke bani labarinku" yace a natse murmushi suka saki idansu akan shi, sallamaNafisat dake tafe saɓe da Mairah hannunta riƙe da hannun Umar tayi a natse ta shigo ciki.... A sukunance Samir da sallaman ya ɗau wani ɓangare daga cikin natsuwar shi yake ƙare matakallo, lallai girman ɗan mutum babu wiya Nafisat ce ta girma haka, yarinyar da ya bari ɗanyashakaf yau gata matsayin cikakkiyar budurwa, murmurshi ta sakin ma Yaya tare da wucewa
gefen shi, "Mamana!" Yace cike da ƙauna, murmushi ta kuma saki tare da faɗin "sannunkudazuwa Yaya" "yawwa Hajiyata" yace tare da miƙawa Mairah dake bin shi da ido hannu, kwaɓefuska tayi ta ƙanƙame ta....
"Auh ke har yanzu baki girmi ƙiwiya ba!" Yace tare da kama haɓa, "ai tana yin su kala-kala" Insutace tare da banka mata harara, "sannu da zuwa Umma, Yaya Salman Yaya Sadambarkankudazuwa" jinjina mata kai suka yi fuska ɗauke da murmurshi me cike da kulawa.....
"Hajiya kun zo lafiya?" "Alhamdulillah takwara ya makaranta?" "Alhamdulillah" tace taredamiƙawa Sahabee hannu, kamawa yayi tare da faɗin "nayi kewa" murmurshi ta saki tare dakaudakai, "baki gane wannan ba ne?" Yasmin tace tare da nuna mata Samir da hannu fuska ba wasa, kallon inda ta nuna mata tayi a natse, ganin yanda idan shi ke kanta ya sata saurin kauda kai tareda faɗin "Yaya Samir sannu da zuwa" murmushi ya saki tare da faɗin "yawwa sannu dai gimbiyaNafisat" sadda kai tayi da sauri ƙirjinta na bugawa da sauri da sauri...
"Auh ashe dama kin san shi?" Insu tace murya ba wasa, "eh na gane shi da na ganshi" taceahankali, "kin kyauta" tace tare da juyawa ga Yasmin, "muje ku yi lunch kafin su wuce wajenɗaurin auren" ta yi maganan da kulawa "to ina su Anty Khadijat?" Tace tare da miƙawa Mairahhannu saurin kamawa tayi tare da maƙalƙaleta, "lallai Mairah abin har da ƴar haka ne?" Fadilatace tare da sakin murmushi, murmushi Yasmin ta saki tare da faɗin "kin manta shaƙuwandaketsakanin Hajiya Yasmin da Hajiya Farisat ne?" Dariya ta saki tare da faɗin "aikuwa dai nayi shirusister" murmurshi ta sakin mata tare da ma su Samir magana akan su je su ci abinci, babuwandaya musa haka suka rankaya suka nufi madai-daicin dining ɗin da aka shirya dan su....
A natse ma'aikata suka serving ɗinsu cike da girmamawa, duk da ba su saki jiki sun ci sosai babaza'a ce sun ƙi ci ba, suna kammalawa suka tatattaro suka dawo cikin parlor, suka ɗaura firanyaushe gamo tare da hiran halin rayuwa.... Miƙewa SSB yayi a natse ya wuce hanyar da ze sada shi da office ɗin cikin gida, wuce wanshi bajimawa Insu ta miƙe a natse ta bi bayan shi, da sallama ɗauke a baki ta tura ƙofan, tana shigatatadda shi zaune a saman sofa idan shi ƙyam akanta tura baki tayi cike da taɓara ta kauda kai, guntun murmushi ya saki tare da miƙa mata hannu, a hanzarce ta nufe shi, dan jiran hakankawai
take.... Faɗawa a jikin shi tayi tare da lafewa, gyara mata kwanciya yayi ta jingina bayanta da ƙirjinshi
yanda zata ji daɗin zaman tare da kamo hannunta ya fara matsawa a natse, "me yake so neyaishemu da shafwaɓa?" Yace a dai-dai saitin kunninta, "waye?" Tace tare da ɗaga kai, alamunsankallon fuskan shi, "Alhaji Sa'eed" yace a hankali, shirun sakanni tayi alamun son gano abindayake nufi ganin ta kasa ganowa ya sata faɗin "waye haka?" Murmurshin da sautin shi ya shigakunnuwanta ya saki tare da sunkuyo da kan shi ya sumbaci goshinta, ƙasa ya ƙara ya kai kanhancinta ya sumbata, jawota yayi ta haye ƙirjin shi sosai, yanda zasu iya kallon juna.... Kai hannu a natse yayi ya shafo ƙasan mararta idanshi akan ta, "gashi nan" yace idan shi nakarakaina a cikin na ta, fiddo ido waje tayi cike da ɗin bin mamaki, motsa laɓɓanta da sukayi
masifan mata nauyi tayi tare da faɗin "are you sure!" Guntun murmurshi ya saki tare da faɗin"I'm very sure" miƙa bakinta dake ɓari tayi ta haɗe bakunan su waje guda hawayen da sukacikaidanun na gangarowa.... Birkitota yayi yanda zata fuskance shi tare da ba ta dukkan gudunmuwa, se da suka ɗaudogon
mintocin da ba su san ko nawa ba kafin su janye a hankali, bin shi tayi da ido cike da tsan-tsanfarin cikin da be tsammanin gani daga gare ta ba cike da ɗoki ta riƙo hannun shi ta ɗaura aƙasanmaran tare da faɗin "Mairah zata zama Anty!" Murmurshi ya saki tare da jinjina kai idanshi asaman fuskanta dake cike da ɗoki "zan zama Ammi a karo na biyu, zaka zama Abie a karonabiyu, Alhamdulillah Allah mun gode maka da dukkan ni'imominka" ta idda maganan cike da tsan-tsanfarin ciki tare da shigewa jikin shi da sauri, ƙanƙameta yayi ya fara shafa kanta a hankali
zuciyanshi na gamsuwa tare da faɗaɗuwa da farin ciki... Haka suka yi ta taya juna murna cikin nunawa junansu kula na musamman, "bari in kira YayaSamir ku tattauna na san suna dawowa ɗaurin aure Yaya ze ce se tafiya" tace tare da zamewadaga jikin shi ta yunƙura da niyyan tashi, saurin riƙota yayi tare da faɗin "a daina ture Antydagakusa da ƙanninta Gorgeous kinga tana son jin ɗumin shine" yayi maganan cikin muryanrarrashi
hannun shi na aikin gyara mata zaman wuyan riganta da kyau, jinjina kai tayi cike da gamsuwatare da bin fuskan shi da ido, guntun murmushi ya saki tare da kai tafin hannun shi ya rufemataidanu da shi, dariya ta saki me faɗi tare da cire hannun ta miƙe ta nufi ƙofa, sauke numfashi mesauti yayi tare da lumshe ido cikin sauti me fidda tsan-tsan farin ciki yace "Alhamdulillah" ...
Tana fita ta ƙara gyatta yanayinta ta shige parlorn a natse murmurshi ta sakin ma Yasmindaketa bin ta da ido tare da banka mata hararan wasa ta wuce gefen Samir, ƙaramar dariya ta saki
tare da faɗin "ni ai yau ko ni ko ke, tunda zan fito ake jaddadamin miƙa saƙon gaisuwa ammakotambayan yanda me saƙon yake baki yi ba" fiddo ido tayi tare da faɗin "banda credit a wayakenan, riƙe bayaninki" "auh haka zaki ce!" Yasmin Ɓadamayya tace tare da kama haɓa, taɓefuska tayi tare da faɗin "Mahmah neman magana kawai take" murmushi Yasmin Bertuwatasaki
tare da faɗin "ai idan ta gamu haka take har se an rabu" fiddo ido tayi a hanzarce tare da makamata harara, dariya Yasmin ta saki tare da bin ta da ido, murmushi su Yasmine Ɓadamayyadabasu gane inda maganan Yasmin ya dosa ba suka yi tare da bin su da ido....
"Ammi Asma fa na hanya yau, jikin yaƙi" Nabila tace tare da kallon ta, "subhanallah, gaskiyayakamata ta dawo dama haka, daga honeymoon abu na shirin zama ƙajaga" tace tare da kallon
Samir "muje Nafsii na jiranka" jinjina mata kai yayi ya amshi jakan system ɗin shi dake wajenSahabee ya miƙe, miƙewa tayi tare da faɗin Yaya barka da hutawa" murmurshi ya sakinmatacike da kulawa, tana ƙarisawa ta inda su Jabir ke kwasan hira tace "uncle's Nafsii na magana" tana kai nan ta wuce ita da Samir....
"To Nafsii na magana ku tashi muje" Abubakar yace tare da sakin murmurshi, murmushi sukasaki tare da mimmiƙewa, "an aiko ni wajenki fa" Yasmin tace tare da kallon Fadila, murmurshi tasakin mata tare da faɗin "to bani a ɓoye kar Hajiya sa'idatu ta gani" tayi maganan tare da miƙewata riƙo hannunta, "aiko duk inda zaku ƙafana biye daku" Nabila tace tare da miƙewa, murmushi
Yasmin ta saki tare da faɗin "ku jira in fara miƙawa uncle da Hajiya nasu tukun" ta idda maganantare da nufan uncle Kamil dake ma Hajiya bayani..... Murmurshi Hajiya ta sakin mata tare da miƙa mata hannu cike da ƙauna, kamawa tayi ta zaunaakusa da ita a natse tare da faɗin "takwaraki tace a gaidaki da kyau" "ina amsawa tsufa ya hanatazuwa ko?" Murmurshi ta saki tare da faɗin "ta so zuwa se dai ba ta samu dama ba" "Allahyarabalafiya" "amin, jikokin ki duk sun ce in gaisheki" "ina amsawa ina gaidasu dakyau-dakyau" tacecike da jin daɗi, "zan faɗa musu in sha Allah, uncle Kamil Anty Hasy tace in gaidaka" tayi
maganan tare da juya dubanta gare shi, murmushi ya saki tare da faɗin "ina amsawa zanfaɗamata saƙo ya isko ni lafiya" murmurshi ta saki tare da faɗin "to na sauke wannan nauyinbari insauke na wan can matar ta mu" tayi maganan tare da miƙewa ta nufi su Nabila.... Da idon dake cike da ƙauna suka bi ta cike da yabawa sanin yakamatan ta,,,, shiga ciki sukayi
baƙi ɗauke da sallama, amsawa yayi tare da sassauta yanayin kamewan fuskan shi, murmushi
Samir ya saki tare da wuce wa a hanzarce ya miƙa mai hannu cike da girmamawa, kamawayayi
cike da kulawa fuskan shi na yalwatuwa da murmushi, "bismillah zauna" yace mai tare danunamai kusa da shi ba musu ya zauna cike da taka tsan-tsan....
Komawa gefen shi Insu tayi ta zauna tare da jingina jikinta da na shi, sallama su Jabir sukadokoa natse suka shigo bayan sun amsa, zazzaunawa suka yi tare da ba su natsuwansu kacokan, "Yaya Samir ka bincika wannan saƙon?" Insu tace a natse tare da kai dubanta gare shi, "ehnabincika" yace tare da zage jakan system ɗin da ke hannun shi, ciro madaidaici systemyayi yabuɗe ya kunna kai tsaye tare da faɗin "da alamu wacce ta ɗakko ba ta san me abinda ta ɗakkoyaƙumsaba ina da tabbacin karanbani ne tare da ƙwaɗayi me kai mutum ga nahallaka ya sataaikata hakan" ya idda maganan tare da juyawa SSB fuskan system ɗin, zuba ma screen ɗinidosuka yi gaba ɗayansu tare da tattara natsuwan su a kai.... Alhali Aminu ne da muƙarrabanshi su vice president ke meeting akan kasuwancin su na ɓoyewanda ba kowa ya san da su ba, sauke numfashi Alhaji Munnir yayi tare da faɗin "wato mutanennan sune matsalar ƙasar mu fa" "na daɗe da fahimtar hakan, ka ga tsoffin nan ba za su samusukuni ba har se sun tabbatar da ƙasa ta naƙasa" Abubakar yace cike da takaici, "wai abindanakesan in sani, shin me ya rage musu ne wai a duniyar? Me za su yi da irin wannan banzayenhali daɗabi'un, shekarun da suka yi fa ba maimaitasu za su yi ba wallahi" Jabir yace a zafafe, "touncleJabir su mai-maita ko kar su mai-maita wannan damuwarsu ne ba ta mu ba, mu damuwar mukuɗin ƙasa da suka yi rub da ciki da su, yanzu wannan ai shedace da za'a garƙame duk watabaƙarkasuwancin da suke da ita, saura kuma tsakanin su da mahaliccin su ne, na mu hukuncinnasihace gare su, na mahaliccin su kamu ne na zaluncin ds suka aikata in ba su tuba ba" Insu taceidanta akan su, jinjina kai Alhaji Munnir yayi tare da faɗin "ta ina zamu fara?" ....
Sauke numfashi SSB yayi a natse tare da kallon Samir dake bin su da ido, murmushi ya saki tareda faɗin "da farko dai zan roƙi afwa watakila abinda zan faɗa ba ze muku daɗi ba, nayi
karanbanin bibiyar ko wannensu da bin diddigi akan sanin wani alaƙa ko wannen su ke dashi
akan baƙar kasuwancin" "ma sha Allah!" Jabir yace tare da gyara zama, "muna jinka" Insutaceanatse, "se dai abin mamakin duk suna da alaƙa me ƙarfi da baƙar kasuwancin, ba'a ware ɗayaakan guda daya ba gaba ɗayansu suka yi tarayya akai tamkar dai wata ƙungiyace wacce tahaɗesu waje guda" "me na faɗa maka mr president!" Jabir yace cike da zaƙuwa, murmushi SSByasaki
tare da lumshe ido....
Matakin farko da na ɗauka shine gano baƙar kasuwancin nawa ne da su, to ina kan bincikawaayanzu dan waƴanda na samu tamkar sunyi kaɗan a gani na" ya idda maganan a hankali, "wanneda wanne ka samu?" Abubakar yace a hanzarce, "shigo da muggan maka mai, tare da yaɗasugaal'umman ƙasa musamman marassa hankalin ciki dan ta da zaune tsaye" "subhanallah!" SSByace murya na ɓari, riƙo hannun shi Insu tayi ta matse a hankali....
"Shigo da kayan maye tare da kasuwancinshi ga al'umman ƙasa" "Inna lillahi wa inna
ilaihirraji'un! Anya akwai imani a zukatan mutanen nan!" Alhaji Munnir yace murya na rawa, "babu Munnir babu Allah a ransu, duniya suka sa a gaba" Abubakar yace a zafafe, "gaskiyaneni
kaina ina tantaman yakasance shikenan tunda suka iya yin wannan akwai wasu ma da sukeAllahya bayyana mana, Samir tun kafin mu san waye kai me girma first lady ta ba mu dukkanbayanai
akan ka, mun kuma gamsu akan yin aiki da kai" jinjina kai yayi tare da gyara zama, nan ya shigakora mai bayani sanka-sanka, banda jinjina kai babu abinda Samir dake kafe dashi da idokeyi...
Sauke numfashi a natse yayi tare da faɗin "kaji buƙatun mu" jinjina kai yayi tare da faɗin"inshaAllah ba ze gagara ba, na ɗauki wasu video's duk da ba su da tsayi sosai se dai ina sa yaƙininzasuyi amfani, zan turo muku ku gani idan mun koma, ina ganin fitan videon ze rage kimarsudamutumcin su ga al'umman ƙasa dake musu kallon na gari, fito na fito da su bakatatan hakazehaifar da abubuwa da yawa tsakanin gwamnati da jama'an da take mulka amma idan aka musukisan mummuƙe a farko ina ga kai su ƙasa ba ze bada wahala ba" "good idea" Jabir yace taredatafamai, murmushi ya saki tare da faɗin "thank you sir" ... Murmurshi SSB ya saki tare da faɗin "duk abinda yakamata kayi, su Jabir na tare da kai, sannanka kula da kan ka dan mutanen nan za su iya komai dan rufuwar asirin su" murmurshi ya saki
tare da faɗin "in sha Allah ba abinda za su iya mun zamu kai su ƙasa, ga lawyern mu me jiran
gado nan na san za ta so a bata su a farkon aikinta dan zuba baiwar da ta kwankwaɗa tunaciki" murmushi suka saki gaba ɗayansu tare da kallon Insu data ɓata fuska tare da kauda kai, kallonagogon dake ɗaure a tsintsiyar hannun shi SSB yayi tare da faɗin "lokacin ɗaura auren ya
gabato" mimmiƙewa suka yi cike da farin cikin nasaran da suke hangowa kan su a gaba taredafara ficewa....
"Ko zaki ne?" SSB da Insu ta cukuikuye shi yace tare da kallon hannunta dake riƙe da tsintsiyanhannun shi ƙam, tura baki tayi tare da jinjina kai, wani nagartaccen dariyan da be san da
zuwanshi ba ne ya kuɓuce mai tare da bin ta da ido, dariya ita ma ta saki tare da bin shi daido, "lallai akwai aiki" yace tare da rungumota jikin shi ya miƙe suka nufi ƙofa....
"Congrat Anty Iƙilima da ɗokin in zo mu taya juna murna na zo fa!" Yamsin tace tare da kallonIƙilima dake kallonta fuska ɗauke da murmushi, "taya murnan me?" Insu tace tare da ajiyewayan da take daƙila ta zuba musu ido, "jiya Sadiya ta kira ni take faɗamun an tsaida ranar
aurenta ita da Harira" "what!" Insu tace a mamakance "Serious" tace tare da sakin murmushi, "lallai Anty Iƙilima za aji kan mu dake, wannan kyakykyawan albishir ɗin ki ka kasa faɗa mun!"
Insu tace tare da kama haɓa....
"Da abun a raina na zo, to ba mu samu zama ba, tunda na zo kina kan ƙafanki shiyasa Insu, kekinsan ba zan ƙi faɗa ba" "to shikenan wata nawa aka tsaida?" "Biyu" "Allah ya nuna mana yakawona ƴan baya" "amin, ai na taya su murna wallahi, ke na ma manta in faɗa miki, ina abokanYayaSudais ɗin nan? Yaya Abdallah da Nafi'u" "eh na gane su" "to sun bayyana ƙaunarsu ga Nafi daHalima" "wayyo daɗi! Kai bana muna da shan shagali wallah, dole mu baza capasity" Insutacetare da miƙewa, "a'a zauna dan Allah, kar garin baza capasity ki kafase mu" Hajiya tace taredakallon ta, dariyan yanda tayi da fuska Yasmin ta saki tare da kauda kai....
"Hajiya Yaya yace ku fito" Umar da ya shigo baki ɗauke da sallama yace a hanzarce, "to! Bazakuje ku ga gidan Mahmahn ba! Su Anty Lailah na can fa" Insu tace tare da kallon Yasmin, "tokozaki
tambaye shi tunda shi yace mu fito" Yasmin tace tare da sakin murmushi, "Yaya SalmandaSadam na kusa da shi ina na ga fuska" tace tare da miƙewa, "ai akwai watarana Insu inda rai seagani ko a gaba" Hajiya Babiya tace tare da sakin murmushi, "to Hajiyan Allah ya ake jin mutanenDimau?" Tace tare da sakin murmushi, "auf kin ga wannan ma mun manta to Allah ya sauki
Shafa'atu dai lafiya shekaran jiya" "ma sha Allah, lallai an sha gumurzu baiwar Allah, Allahyaraya, se mun zo suna" dariya Yasmin dake gyara zaman veil ɗin jikinta ta saki tare da faɗin"nahangoki a kusa da me jego" "baby!" Tace a taɓare, "afwan se kin zo" tace tare da wuce wa gefensu Hajiya, sallamansu suka yi a mutumce suka rankaya dan musu rakiya....
"Ki kula sosai" Yaya yace cike da ƙauna, murmushi ta saki tare da jinjina kai, "kar ki wasa dashanmagani, lafiyarki na da matuƙar mahimmanci a wannan yanayin" ya kuma cewa tare da shafakanta, jinjina kai tayi tare da sakin murmushi, "kuma saura mutanen su motsa mu sauka ki ƙi
zuwa suna" Salman yace tare da banka mata harara, "oh su malama ƴar jarida aban tausayi" tacetare da kallon shi, "a'a za dai mu gane abar tausayi tsakanin ke da ita nan gaba" fiddo idotayi
tare da juyawa inda Samir yake da sauri, dariya suka kwashe dashi tare da bin ta da kallonƙauna, "se mun zo ko se ka zo?" Tace tare da kallon shi, "a'a se na zo dai, ai zuwa kuma ya kama ni tundamahaɗin rayuwata na kusa daku" yace idan shi akan Nafisat dake magana da Sahabee da Umar, murmushi ta saki tare da faɗin "Ummi ki zo kuyi sallama da Yaya Samir za su wuce" tana iddamagana ta bar wajen ta koma gefen Sadam.... A natse ta juyo gefen da yake kai a ƙasa, matsawa kusa da ita kaɗan yayi tare da faɗin "bamamugaisa ba ko?" "Mun gaisa" tace a hankali ba tare da ta ɗago ba, "a'a ba mu gaisa ba gimbiya, koɗago ido ki kalleni fa baki yi ba" murmushi ta saki a natse tare da faɗin "Allah ya kiyaye hanya"
"amin, kina da waya ne?" Jinjina kai tayi a natse "okay bani number se mu yi magana lokacindaki ka yanke shawaran daina jin kunyar" murmushi ta saki tare da karanto mai a natse, "YayaSamir kai muke jira" Sadam yace da ɗan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Chapter 68
Chapter 69
Chapter 70
Chapter 71
Chapter 72
Chapter 73
Chapter 74
Chapter 75
Chapter 76
Chapter 77
Chapter 78
Chapter 79
Chapter 80
Chapter 81
Chapter 82
Chapter 83
Chapter 84
Chapter 85
Chapter 86
Chapter 87
Chapter 88
Chapter 89
Chapter 90
Chapter 91
Chapter 92
Chapter 93
Chapter 94
Chapter 95
Chapter 96
Chapter 97
Chapter 98
Chapter 99
Chapter 100
Chapter 101
Chapter 102
Chapter 103
Chapter 104
Chapter 105
Chapter 106
Chapter 107
Chapter 108
Chapter 109
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 104 Chapter of 109